x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - MAZAN JIYA 2

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 194

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kan kalmami
jikinsu ko kwarzAnewa baya yi.

Sannu a hankali Hantaru ya fara gani dishi- dishi
sakamakon jinin da ke zuba a jikinsa mai yawa
ya zamana cewa yana gudu ne kawai amma
baya ganin abin da ke gabansa. Kwatsam! Sai yai
karo da ka da wata katuwar bishiya tamkar
fyadashi aka yi a jikinta. Nan take jini yai fitar
burgu daga cikin bakinsa de hancinsa ya fado da
baya a sume ya baje a kas. Takobin Saiful Lujara
ta subuce daga hannunsa ta fadi gefe daya.

A dai-dai wannan lokaci ne wadannan miyagun
dabbobin suka iso kansa suka yi masa kawanya
suna shirin yuyyagashi. Daya daga cikin
dabbobin wani murgujejen tsohon Zaki sai ya yi
girgiza ya rikide ya zama wani tsohon aljani
wanda shekarunsa sun haura dubu ashirin.
Kawai sai ya nufi inda takobin Saiful Lujara take
55

TASKARNOVELS.COM.NG
da nufin ya dauka. Kwatsam! Ba zato ba
tsammani, sai ga wata irin guguwa mai karfin
tsiya ta baiyana ta tarwatsa gaba dayan
wadannan dabbobi tayi jifa da su can nesa har
shi kansa wannan tsohon aljani mai shirin
?aukar takobin Saiful Lujara.

Kafin dabbobin sU Sake rugowa da gudu inda
Hantaru yake kwan ce a sume, tuni guguwar ta
?auke Hantaru da takobin Saiful Lujara tayi
sama da su ta luluka a cikin gajimare ta 6ace bat
tamkar basu taba wanzuwa ba a saman. Kawai
sai wanann aljani da dabbobin suka tsaitsaya
cak suka daga kawunansu sama suna kallon daidai wajen da guguwar ya kule da Hantaru. Daga
can kuma sai suma suka 6ace 6at.

Lokacin da Hantaru ya farfado daga dogon
suman da ya yi, sai ya tsinci kansa a cikin wani
kasaitaccen ?aki kwance akan wani
luntsumemen gado mai taushin gaake.

56

TASKARNOVELS.COM.NG
Komai na cikin dakin an yi shi ne da zinare, don
haka gaba dayan dakin sheki da walwali yake.

Abu na farko da Hantaru ya fara arba da shi shi
ne, takobin Saiful Lajara jingine a jilkin bango
bisa wani ma'ajiyi. Koda ganin takobin sai
Hantaru ya saki murmushin murna ya mike
zaune sanann ya zuro kafafunsa kasa daga kan
gadon ya nufi inda take yana tafiya da kyar a
lokacin da yaji gaba dayan jikinsa ya yi tsami.

Saura kiris! Hannnunsa ya kai kan takobin sai ya
dubi wani madubi da ke kusa da takobin. Nan
take ya ga ashe gaba dayan fuskarsa a kumbure
take ba kyan gani, kuma tayi kaca-kaca da rauni
sakamakon muguwar buguwar da ya yi da
bishiya, musamman idanunsa sun yi luhu-huhu
da kyarma yake iya budesu. Koda Hantaru ya ga
yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi,
amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki
ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami
nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya
koma birnin Darul Habur sai dai a...
57

TASKARNOVELS.COM.NG

Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai
takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya
Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin
cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful
Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai
dai a daura aurensa da gimbiya Larziya.

Cikin hanzari Hantaru ya dauki takobin Saiful
Lujara ya nufi kofar fita daga dakin, kawai Sai ya
ga wata tsaleleliyar budurwa ta baiyana a
gabansa fuskarta cike da murmushi.

Cikin tsananin mamaki da firgici Hantaru yaja
da baya yana kallonta ya ce, "Mutum ko aljan?".

Ba komai ne yasa Hantaru ya yi ma ta WannAn
tambaya ba face ganin tsananin kyawunta
wanda ya ninka na gimbiya Lariya sau uku.

58

TASKARNOVELS.COM.NG

Budurwar tayi murmushi wanda ya kara
baiyana kyawunta karara har Hantaru ya kara
dimancewa sannan kuma sai ta murtuke fuska
ta dubeshi ta ce,

"Haba gwarzon shekara wane irin sauri kake yi
haka? Shin baka ga yadda fuskarka take bane
har kake tunanin komawa birnin Darul Habur
cikin wannan sifa? Yaya masoyiyarka gimbiya
Larziya za ta kasance idan ta ganka a cikin
wannan siffa? Bai zamo dole ba ma ta shaidaka
ba, kamanninka gaba daya sun sauya. Ka sani
cewa jikinka a cike yake da raunika da kuma
taruwar jini, idan ka ce za ka cigaba da tafiya a
haka wa?annan mugayen dabbobin na kogon da
takobin Saifal Lujara take za su sake binka su
rabaka da takobin, kuma su hallaka ka, kaga
kenan kayi biyu babu, babu ranka, kuma babu
takobin, duk wahalar da ka sha a baya ta zama
ta banza.' Burin dangin mahaifiyarka na cin gasa
bai cika ba, kaima burinka na auren gimbiya
Larziya ya rushe, bare kuma har ka koma birnin
Kisra ka sadu da mahaifnka sarki Kusaidu
59

TASKARNOVELS.COM.NG
wanda kullum dare da rana a cikin begenka
yake."

Sa'adda kyakkyawar budurwar tazo dai-dai nan
a jawabinta sai Hantaru ya cika da tsananin
mamaki ya kura mata idanu kawai yana mai
kara kankame takobin Saiful Lujara a kirjinsa.
Sannan ya ce,ya ce, *Ya ke wannan kyakkyawa,
wace ce ke, kuma me yasa
kika ceto rayuwata daga hannun wadannan
dabbobi na kogon
da wannan takobi take ciki kika kawoni nan?".
Koda jin wadannan tambayoyi sai buduwar tayi
ajiyar zuciya
sannan ta ce, "A gaskiya ba zan iya gaya maka
amsar
wadannan tambayoyi ba a yanzu, sai bayan ka
sami lafiyar
jikinka gaba daya, wato ranar da zamu yi
bankwana ka tafi

60

TASKARNOVELS.COM.NG
izuwa birmin Darul Mahabul. Wata kila daga
Wannan rana ba zamu sake saduwa ba, wata
kila kuma daga wannan rana ba zamu sake
rabuwa ba". Hantaru yai shiru a karo na biyu
yana nazarin abin da ta fadi. Amma bai fahimci
komai ba, kawai sai ya dago kansa ya sake
dubanta ya ce, "Tsawon kwana nawa ne zan yi
na gamna jinyar jikin nawa na tafi?", Budurwar
ta ce, "A kalla kwana goma sha hudu. A sannan
ne fuskarka za ta yi fes ka koma ga masoyiyarka
cikin kyakkyawar siffa, Koda jin haka sai
Hantaru ya yi murmushi. Amma da ya dubi
budurwar sai ya ce a ransa. "Ina ma ace gimbiyu
Larziya ce da kyau irin na Wannan budurwa, da
na gama morewa a duniya, domin na tabbatar
da cewa a duniya kaf ba za a sami kamarta ba.
Ashe har akwai wadda tafi Larziya kyau a cikin
wannan duniya?".
Hantaru ya tambayi kar sa a cikin zuciyarsa.
Kamar budurwa ta San irin Zancen Zucin da
yake yi sai ya ga tayi masa murmushi sannan ta
tako kafafunta a hankali cikin tafiyar kasaita
tamkar dawisu tazo daf da shi ta kamna
hannayensa ta jashi izuwa kan gadonta ta
zaunar da shi ta ce, "Ya kamata yanzu ka ci
61

TASKARNOVELS.COM.NG
kasha sannan ka sha magani ka kwanta ka
huta". Kafin Hantaru ya ce wani abu sai ya ga
wadansu kyawawan kuyangi guda biyu Sun
baiyana tsulum a gabansa. Daya na dauke da
katon faranti cike da abinci iri-iri dayar kuwa
kayan shaye-shaye ne kala-kala har da na
magani. Har a Wannan lokaci budurwar na rike
da hannayen Hantaru,
wani irin laushi da yaji a hannayenta ne yaji ko
kadan baya son ta saki hannayensa, domin bai
san sa'adda ma ya fara lumshe idanu ba amma
da zarar ya dubi fuskarta sai ya ga tana rikida
tana zama gimbiya Larziya. Kaico! Hakika
soyayya dafice wadda idan ta ratsa sassan jikin
mutum, fitarta sai yaki.
Duk tsananin kyawu irin na wannan budurwa
wanda ya ninka na gimbiya Larziya sau uku bai
sa Hantaru ya fi sonta ba akan Larziya saboda
tuni zuciyarsa ta gama cika da begen Larziya
babu sauran gurbi wanda wata za ta samu! Ba
tare da bata wani lokaci ba kuyangin suka ajiye
farantan biyu bisa kan wani tebur da ke
gabansu Hantaru sannan suka bace 6at!
Bacewarsu ke da wuya sai budurwar ta fara
ciyar da Hantaru da hannunta kuma tana ciyar
62

TASKARNOVELS.COM.NG
da kanta. A haka sai da suka koshi sannan ta
baiwa Hantaru ruwan magani kala shida ya sha.
Yana gama shan maganin sai ya dubeta ya budi
baki domin ya tambayeta sunanta amma sai
yaji bakin nasa ya yi masa nauyi ya kasa
magana, idanunsa kuwa sai suka kama
lumshewa kawai sai ya tuntsure akan gadon ya
kama barci. Koda ganin
haka sai budurwar ta kura masa idanu tana
murmushi, daga Can kuna sai idanunta suka
ciko da kwalla ta fara zubar a hawaye. Jim
kadan kuma sai ta fashe da matsanaicin kuka sai
da ta shafe sa'a guda tana ta kukan tamkar
wacce ta rasa ivayenta a lokaci guda sannan ta
mike tsaye ta fice daga cikin dakin tana waigen
Hantaru kamar har abada ba Za ta sake ganinsa
ba.
Daga Wannan rana kullum Wannan kyakkyawar
budurwa na tare da Hantaru dare da rana tana
jinyarsa kuma tare suke cin abinci safya, rana
da dare, sannan su yi ta hira basa rabuwa face
ta ga Hantaru ya soma jin barci sannan tayi
masa sallama ya tafi turakarta. Tsawon
kwanaki goma sha hudu, Hantaru bai taba fita
ba daga cikin dakin da ake jinyarsa face ya
63

TASKARNOVELS.COM.NG
shiga Wani kewaye idan bukata ta kamashi.
Hatta wanka Hantaru ba ya yi da kansa
budurwar ce take yi masa don haka ne suka
shaku ainun suka saba da juna amma babu wani
abu da ya taba shiga tsakaninsa. Wani abin
mamaki shi ne a tsawon kwanaki goma sha
hudu basu taba yin hirar soyayya ba kuma
Hantaru bai taba jin sunan budurwar ba a duk
sa'adda yaso ya tambayeta sunanta sai ta
bagarar da zancen ta sauya hirar da suke. A iya
rayuwar Hantaru in ka ?
auke Salimat wadda ta raineshi a matsayin
mahaifiyarsa bai taba samun kusanci ga ya mace
ba gami da sabo face wannan budurwa. A ranar
da kwanaki goma sha hudu suka cikane,
Hantaru ya tashi da sassafe daga barci koda ya dubi kansa a cikin madubi sai ya ga fuskarsa da
jikinsa sun yi kyau matuka kuma sannan ya yi
haske da kiba har
wani irin sheki fatar jikinsa ke yi. Nan take yaji
wani irin farin ciki ya baibayeshi musamman da
ya tuna cewa yau ne zai bar Wannan gida
domin ya tafi izuwa birnin Darul Mahsbul.
Hantaru na tsaye a gaban madubi yana kallon
kansa sai kawai ya ga wannan budurwa tsulum
64

TASKARNOVELS.COM.NG
a gabansa, idanunta sun kada sun yi jawur kai
da gani ka san cewa ta dade tana kuka,
Al'amarin da ya matukar ?ugunzuma hankalin
Hantaru ke nan yaji kamar ya fasa tariya a yau,
kawai sai ya budi baki da nufin ya tambayeta
dalilin da ya sa ya ga idanunta sun yi jawur,
kawai sai budurwar ta juya masa baya ta dauko
takobin Saifal Lujara ta mika masa ya karba
sannan ta kama hannunsa ta jashi suka fita
daga cikin dakin. Nan fa suka kama yawo a
cikin harabar gidan, su shiga nan su fita can.
Nan fa Hantaru ya cika da matukar al'ajabi ya
zama cikakken dan kauye, saboda ganin irin
daular da aka shirya gidan ko a tarihi bai taba
jin labarin gidan sarautar da ya kawatu ba
kamar wannan.
Duk wani abu na jin dadin duniya an tanadeshi
a cikin gidan har da ma wanda ido bai ta6a
hasashen gabaninsa ba. Sai da guka shafe sa'a
ukU suna shiga sako sako, lungu-lungu na gidan
amma Hantaru bai ga alamar Sun kusan kure
gidan ba. A?amarin da ysa yaji ya kagu ke nan,
domin hankalinsa na kan tafiya birnin Darul
Habul. Koda budurwar ta fahimci halin da
Hantaru ke ciki sai ta ruko hannunsa suka tsaya
65

TASKARNOVELS.COM.NG
cak kuma suka fuskanci juna, kawai sai ya ga
hawaye ya zabo daga cikin idanunta. Alamarin
da ya matukar baahi mamaki ke nan ya dubeta
cikin kaduwa ya ce, "Ya ke Wannan
ma'abociyar karamci da kyawu ina dalilin
zubar wannan hawaye nak?i?"
Koda jin wannan tambaya sai ta yi murmushi
mai taushi a gareshi ta ce, "Ya kai jarumin
jarUmai, gwarzon zamani, kuma traron wannan
shekara, kayi sani cewa sunana Hayatul
Lumhas. Na kasance 'ya guda daya jal ga sarki
Thibur na birnin Hindu. A halin yanzu masAna
bincike sun tabbatar da cewa duk duniya babu
wata mace mai kyau kamata,
amma tun ina jaririya mahaifina ya boyeni a
cikin dakin tsafinsa ban taba fita ko Ina ba har
na girma na cika shekara goma sha takwas, shi
yasa a duniya ba a sanni ba. Kaine Damijin
fark? da na taba gani a rayuwata ban da
mahaifina, hatta mahaifiyata ban taba ganinta
ba, ban San ta ba umn ban sha nononta ba har
aka kawoni wannan gida kimanin shekaru hudu
da suka gabata sa'adda nake da shekaru goma
sha hudua duniya. Lokacin da mahaifina ya
kawoni wannan gida ya ajiye ni a sannan ne na
66

TASKARNOVELS.COM.NG
ga ya dubeni ya fashe da kuka. Al'amarin da ya
dugunzuma hankalina kenan na ruke kafadarsa
cikin matukar damuwa na ce, "Ya kai Abbana
ina dalilin kukanka, kuma me yasa ka kawoni
cikin wannan gida wanda ke tsal kiyar dokar
daji?. Sa'adda mahaifina yaji wannan tambaya
sai ya share hawayensa sannan ya ce,
"Ya ke yata ki yi sani cewa ba komai ne ya sani
wannan kuka ba face sanin cewa yau ne ranar
da zan rabu da ke rabuwa ta har abada, domin
yau saura kwana bakwai kacal na bar duniya.
Abin da ya sa na kawoki nan na ajiyeki kuwa
shi ne, anan ne kadai ZA ki iya zama lafiya har
izuwa karshen rayuwari, idan na barki a can
kasarmu kika gaji karagata ta mulki duniya ba
za ta zauna lafiya ba domin gaba dayan
sarakunan duniya za su tayar da hankalinsu a
kan sai sun mallakeki saboda tsananin
kyawunki,
al'amarin da zai janyo yakin duniya ke nan ayi
asarar rayuka da dukiya wacce bata da adadi.
Bisa wannan daili ne yasa na rabaki da
mahaifiyarki tun daga ranar da aka haifeki
kuma na Boyeki da karfin sihiri yadda babu
wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya
67

TASKARNOVELS.COM.NG
ganinki bare bar ya kai labarinki wani wajen.
Baki san kowa ba, kuma ba ki shaku da kowa ba
face ni, yau gashi lokacin rabuwarmu ya yi, don
me ba zan zubar da hawaye ba? Na yi bincike a
cikin taskar tsafii na gAno Cewa nan da shekaru
hudu za'a sami wani gawurtaccen jarumi wanda
zi shiga kogan mazzabatal Dulshul wanda ya
gagareni shiga ya dauko wata takobi da ake kira
Saiful Lajara
WaR'nnan jarumi zai sha bakar wahala a cikin
kogon tamkar zai rasa rayuwarsa da kyar zai
iya guduwa daga cikin kogon. Aljanun da ke
gadin takobin Saifal Lujara za su biyoshi domin
su halaka shi, a sannan ne nake son ki je ki ceci
rayuwarsa ki kawoshi nan gidan tare da
takobinsa ta Saiful Lajara. Na sani cewa wannan
jarumi idan ya ganki dole ne yaji yana sonki,
fatana shi ne ki zamo abokiyar rayuwarsa
domin shi kadai ne zai iya aurenki ya iya zama
da ke lafiya".
(Sai kuma ni mai typing Shuraih 99%)?
Sa'adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na
dubeshi cikin mamaki na ce, "Haba Abbana ta
ya ya zan iya zuwa na ceto rayuwar wanan
jarumin alhalin ban kasance jaruma ba kuma
68

TASKARNOVELS.COM.NG
bani da wani sihirin tsafi?". Koda jin haka sai
mahaifina ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya ke 'yata
kiyi sani cewa yanzu tate zan baki dukkan
sihirin tsafina sannan mu yi bankwana na koma
kasata na jira mutuwata".
Koda naji haka sai na fashe da kuka na rungume
mahaifina sannan na ce, "Ya kai Abbana me
yasa baka nuna mini mahaifiyata ba koda sau
daya ne mun ga juna kafin ka kawoni nan tunda
gashi yanzu kaima za ka rabu da ni rabuwar da
ba zamu sake saduwa ba". Koda jin wannan
tambaya sai mahaifina ya kamu da tsananin
tausayina har ya kasa cewa komai ya fashe da
matsanaicin kuka har izuwa lokaci mai dan
tsawo. Daga can sai ya janye jikinsa daga cikin
nawa muka fuskanci juna ya ce,
"Ya ke yata kiyi sani cewa ka'idar sihirin tsafina
ce ta hanani na hadaki da mahaifiyarki idan
kuwa na karya wannan kaida shikenan sihirin
tsafina Zai rushe, duk dukiyar da na mallaka za
ta salwanta. Da wannan furuci nake yi miki
sallamar karshe." Koda gama fadin haka sai
mahaifina ya dada kankameni a kirjinsa ya sake
fashewa da matsanaicin kuka. Al'amarin da ya
karya zuciyata ke nan nima na kama kuka, Ina
69

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin wannan hal? ne naji wani irin gagarumin
karfi yana shiga jikina. Kafin na gama shiga sai
mahafina ya bace 6atl Na nemashi sama da kasa
na rasa. Nan fa na rushe da kuma na kama gujeguje da iface- iface a cikin Wnnan gida. Kawai
sai Da...
MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part E Na
Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh
AlQuyraemey
Nan fa na rushe da kuka na kama guje-guje da
iface- iface a cikin wannan gida. Kawai sai naga
kuyangin gidan sun baiyana a gabana sun
kewayeni suna rarrashina, sannan suka yi
sujjada a gareni suna cewa, "Ya shugabarmu ki
?auki hakuri da kaddara, ki sani cewa mu masu
debe miki kewane da biyan duk bukatunki daga
nan har izuwa karshen rayuwarki". Koda naji
haka sai na dubesu cikin mamaki na ce, "ldan
kuma mutuwa ta daukeki waye zai ci gaba da
kula da ni?". Cikn hadin baki suka ce
"Ai mu ba mutane bane kamar ke, mun kasance
aljanu, muna dadewa a duniya fiye da ku
bil'adama. Daga Wannan rana ne na shiga
sabuwar rayuwa a cikin wannan gida kuma ya
70

TASKARNOVELS.COM.NG
zamana cewa ina yin abubuwan al'ajabi cikin
karfin sihirin tsafi wadanda ni kaina nake
mamaki. Haka na ci gaba da rayuwa cikin,
koshin lafiya da kwanciyar hankali amma duk
sa'adda na tuna da mahaifina sai na fashe da
kuka, haka kuma idan na tuna cewa ban taba
ganin mahaifiyata ba sai naji wani irin bakin
ciki yai katutu a cikin zuciyata.
Haka dai na kasance a cikin wannan matsayi har
tsawon shekara hudu. A ranar da na ga hoton
duk abubuwan da suka faru gareka a cikin
kogon Mazubatul Dulshal ne naji na kamu da
tsananin kaunarka don haka sa'adda wadannan
aljanu suka biyoka za su hallaka ka sai na bi
umarnin mahaifina na zamo guguwa naje na
daukeka kafin su illataka na kawoka nan, nayi
jinyarka kawo
izuwa yanzu tsawon kwana goma sha hudu har
ka sami lafiya. Wannan shi ne takaitaccen
tarihin rayuwata ya kai jarumin jarumai, kayi
sani cewa na gani a cikin bincikena na tsafi
cewar idan har ka koma wajen gimbiya Larziya
za ta umarceka da ka aikata wani mummunan
aiki wanda zai zamo sanadiyyar batawarka da
Salimat matar da ta rene ka har ka girma a
71

TASKARNOVELS.COM.NG
matsayin danta na cikinta sakamakon hakan
Salimat za ta kashe kanta. ldan hakan ta faru za
ka tsani kanka kuma za ka tsani komai a duniya
ya zamana cewa soyayyarka da gimbiya Larziya
ta rushe, wato dai ba za ku yi ure ba. Ina mai
shawartarka da ka mance da batun Larziya ka
zauna anan tare dani mu yi aure mu more
rayuwarmu cakin dadi da kwanciyar hankali.
Ka sani cewa na fi Larziya kyawu, asali da
matsayi a duniya, kuma duk abin da kake nema
a rayuwarka walau dukiya ko daukaka in dai
kana tare da ni tamkar ka samesSu ne. Sa'adda
Hayatul Lumhas tazo nan a zancenta sai
Hantaru ya yi murmushi gami da ajiyar zuciya
sannan ya ce, "Ya ke ma'abociyar kyawu,
matsayi da daukaka,
kiyi sani cewa babu ruwan S0 da kyawu ko
matsayi, don haka martabar gimbiya Larziya a
cikin zuciyata ta ninka taki sau dubu. Larziya ce
mace ta farko da ta fara samun gurbia cikin
zuciyata kuma ita ce za ta zamo ta karshe
domin ba zan taba son wata ba face itan. Duk
bayanin da ki ka yi na gamsu da shi, amma ban
yi imani da shi ba domin na yarda da cewa zan
iya sauya kowacce irin kaddara da ta sameni
72

TASKARNOVELS.COM.NG
anan gaba muddin tsafi bai daina tasiri a doron
kasa ba. Ki sani cewa idan suna nake nema a
duniya na gama samunsa tun da gashi na dauko
takobin Saiful Lujara a cikin kogon Mazabatul
Dulshal aikin da ya gagari dubunnan sadaukai a
tsawon dubunnan shekaru da suka gabata. Idan
dukiya nake so ko mulki duk zan iya samunsu
da karfin Wannan takobi da na dauko saboda
haka ni yanzu baki da wani abu wanda zai
janyo hankalina har yasa har na manta da
masoyiyata abar
begena dare da rana wato gimbiya Larziya.
Abin da nake bukata daga gareki kawai shi ne ki
fitar dani daga cikin wannan gida naki ki ?orani
akan hanyar da ZAn nufi birnin Darul Mahabul
domin naje na ida sauran burin rayuwata. "Ya
yin da Hantaru yazo nan a zancensa sai hawaye
ya zubowa gimbiya Hayatul Lumhas tayi shiru
bata ce komai ba tana mai sunkui da kanta kas
saboda tsananin bakin ciki da takaici.
Daga can sai ta dago kai ta dubi Hantaru ta ce,
"Ya kai abin
End Ads