x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - MAZAN JIYA 2

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 55701 words

Category: Romance Story +18

Views 163

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

TASKARNOVELS.COM.NG

1

TASKARNOVELS.COM.NG

MAZAN JIYA
2
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part B
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

KASHE GARI da sassafe rundunar su Sarki
Dujalu suka mike suka ci gaba da tafiya, bayan
kowa ya kimtsa cikinsa.
Tun da aka fara tafiyar sai sarki Dujalu ya lura
da cewa 'yar uwarsa Hursiya bata da sukuni. A
duk sa'adda ya dubeta sai ya ga alamomin
damuwa cike a fuskarta kawai sai ya yi
murmushi, domin shi kadai ne ya san abin da ke
damunta.
2

TASKARNOVELS.COM.NG
Abin da ya bashi mamaki shi ne, mene ne ya
hanata ta baiyana masa abin da ke damunta, ba
wani abbu bane ya ke damun Hursiya ba face
tsananin son jin ci gaban labarin sadauki
Hantaru.
Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har
tsawon kwana uku. Duk sa'adda aka yada zango
sai Husiyya ta lallaba sarki Dujalu domin ya ci
gaba da bata labarin.
Da zarar ya fuskanci abin da take so, sai ya kama
gyan-gyadin karya, bisa dole Hursiya ta hakura
itama ta kwanta har barci ya saceta bata sani ba.
Da yammacin kwana na uku ne wannan
runduna ta su sarki Dujalu ta iso wani katon daji
mai ban tsoro wanda ake yiwa lakabi da
Sauratul Auzur.
Duk da tsananin yawan wannan runduna aljanu
da mutane da kuma gagarumin shirinsu sa da
kowa yaji tsoro ya shigeshi, bisa tsintar kansu a
cikin dajin Sauratul Auzur, sarki Dujalu ne kadai
bai girgiza ba.
Shi dai dajin Sauratul Auzur babu komai a
cikinsa face manya-manyan bishiyoyi da
3

TASKARNOVELS.COM.NG
manyan duwatsu masu ban mamaki. Babu inda
mutum zai je a duniya ya ga irinsu, sannan
siffofin bishiyoyin da duwatsun ma ababan
tsoro ne. Sau tari sai mutum ya ga suna motsi da
rangaji tamkar za sun haifar da girgizar kasa a
dajin gaba daya.
Daga dajin Sauratul Auzur zuwa tekun bahar
Sufiya tafiya ce ta wata hudu kacal, kuma cikin
dajin Sauratul Auzur mutun zai yi ta tafiya ta
tsawon wata hudu.
Da isowar su sarki Dujalu farkon dajin Sauratul
Auzur, sai sarki Dujalu ya bada umarnin a tsaya.
Nan take kuwa na kan dawakai suka ja
dawakansu, aljanun da ke tafiya a sararin sama
kuwa suka saki fuka-fukansu suka sauko kasa.
Nan fa kowa yai ladaf aka yi tsit tamkar babu
mai numfashi a wajen.
Sarki Dujalu yai gyaran murya sannan ya ce, "Ya
ku jama'ata kuyi sani cewa mun iso dajin
Sauratul Auzur. Daga nan zuwa tekun bahar
Sufiya inda takobin Saiful Lujara take tafiyar
wata hudu ce kacal. Ku yi sani cewa masifa da
bala'in da ke cikin wannan daji sun wuce tunani
don haka sai kowa ya gyara damararsa, domin
4

TASKARNOVELS.COM.NG
komai zai iya faruwa. Ko shakka bana yi da
yawa daga cikinmu za su iya rasa rayuwarsu a
cikin wannan daji.
Wadanda duk suka kai izuwa karshen wannan
daji a raye a cikin koshin lafiya sun cika jaruman
kwarai ababan yabo da jinjina."
Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya dubi
Hursiya ya ce, "Komai wuya da tsanani ki
tabbatar da cewa a ko yaushe kina tare da ni
Hursiya ta gyada kai tana mai nuna cewa lallai
za ta kiyaye.
Nan take sarki Dujalu ya zunguri cikin aljanin da
ke dauke da su shi da Hursiya, suka fara
wucewa kan gaba, sannan kowa ya bi bayansu a
cikin yanayin tsoro da dari-dari. Sai da aka shafe
sa'a guda ana tafiya a cikin dajin ba a hadu da
komai ba kuma ba a ga wani mugun abu ba.
Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin
mamaki ke nan domin in banda kukan kananan
tsuntsaye da kwari babu wani sauti da ke ratsa
kunnuwa.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai kawai aka
hango wata jibgegiyar halitta a can gaba ta cika
5

TASKARNOVELS.COM.NG
hanya tun daga sama har kasa tamkar za ta
tokare da hadari. Babu ta inda za a bi a wuce
face ta cikin halittar.
Ita dai wannan halitta tana kama da bil'adama,
aljan da kuma dodo, Kuma gaba dayan jikin na
ta ne yake da siffofi ukun.

Ma'ana fuskarta da gangar jkinta da
hannayenta.
Koda aka yi arba da wannan halitta sai gaba
dayan dakarun sarki Dujalu suka firgice suka
tsaya cak! A waje daya Aljanin da ke dauke da
sarki Dujalu wanda ake kira Rauzuf sai ya fara
kada fuka-fukansa a hankali alamar shima ya
tsorata, amma bai fasa tunkarar halittar ba
saboda gudun fishin sarki Dujalu, amma gaba
dayan jikinsa karkarwa yake tamkar wanda ya
kamu da zazzabi mai zai."
Koda sarki Dujalu ya fahimci halin da aljani
Rauzuf ke ciki sai ya daka mäsa tsawa ya ce, "Ya
kai Rauzuf a kul ka kuskura ka. ja da baya ko
kuma ka tsaya ga ci gaba da tafiya idan kuwa ka

6

TASKARNOVELS.COM.NG
tsaya ni da kaina zan zare maka ruhin
numfashi"
Koda jin wannan batu sai aljani Rauzuf ya kara
karfin tafiyarsa ya tunkari wannan katuwar
halitta kai tsaye. Sai da suka iso daf da halittar
ya zamana cewa tazarar da ke tsakaninsu ba ta
wuce kamu uku ba, sai halitar ta wangame
katon bakinta mai kama da kofar gari ya buso
wata irin iska mai karfin gaske tamkar guguwa.
Take aljani Rauzuf ya fado kasa tim! Sarki
Dujalu da Hursiya suka tuntsuro kasa daga
kansa suka baje a kas.
Hatta sauran dakarun da ke bayansu sai da iskar
ta tarwatsasu, na sama suka rikito kasa, na kasa
kuwa suka baje.
Daga can sai katuwar halittar ta bushe da
mahaukaciyar dariya mai tsananin ban tsoro
wacce ta sa kowa da kowa ya sume face sarki
Dujalu.
Gaba daya dajin ya hautsine ya kama
rangaji,wuta ta kama bishiyoyi. Babu abin da ya
rage a tsaye bisa duga-digansa face sarki Dujalu.

7

TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokacin ne shirgegiyar halittar ta
bude idanuwanta fala-fwala masu kama da
girman rami ta dubi Dujalu cikin tsananin
mamaki.
Fiye da shekaru dubu da doriya wannan halitta
ke tsare wannan hanya, duk abin da ya zo
gabanta in dai tayi wannan dariya sai abin ya
fadi kasa sumamme amma yau ga wani
takadarin bil'adama guda daya a tsaye cak a
gabanta ko girgiza bai yi ba.
Cikin wata irin gaggausar murya halittar ta dubi
aljani Dujalu ta daka masa tsawa. Duk da cewa
sarki Dujalu gwarzon namiji ne wanda bai san
tsoro ba sai da hantar cikinsa ta kada shi kuwa
aljani Rauzuf take ya kara sumewa a karo na
biyu.
Halittar ta dubi Dujalu cikin nutsuwa ta ce, "Ya
kai wannan hatsabibin biladama wane ne kai
kuma wane tsautsayi ne ya shigo da ku cikin
Wannan daji na Sauratul Auzur alhalin kun sin
cewa ba a taba ratsowa ta cikinsa be?" sarki
Dujalu yaji wannan tambaya sai ya bushe da
dariya sannan ya murtuke fuskarsa kamar
wanda aka aikowa da sakon mutuwa ya ce, "Ni
8

TASKARNOVELS.COM.NG
ne sarki Dujalu mai mulkar kasar Hawarul din.
Ya kai wannan babbar halitta ka sani cewa na
yarda daa kaina domin ni ne DODON MAZA ne a
wannan zamani, magajin MAZAN JIYA. Duk
bala'in da ke cikin wanann daji na san da shi
kuma sai na ketare ta cikinsa domin na isa
tekun bahar Sufiya don na dauko takobin Saiful
Lujara."
Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa sai
katuwar halittar ta sake bushewa da dariya a
karo na biyu sannan ta ce, "Sama da mutum
dubu dari ire-irenku wato masu irin wannan
buri naka sun hallaka bisa wannan tafarki
wadanda duk abin da kake takama da shi sun
fika. Babu wanda ya taba haye bala'in bare har
ya shafe sauran tafiyar da ke cikin wannan daji
na Sauratul Auzur ya ketare sauran masifun da
ke cikinsa ya isa bakin tekun Bahar Sufiya. Ina
mai shawartarka da ka juya da baya kai da
jama'arka domin kada ka janyo asarar miliyoyin
rayuka a banza."
Sarki Dujalu ya yi murmushi mai nuna yarda da
kai, sannan ya ce, "Ko mutum daya daga cikin
Jama'ata ba zai rasa rayuwarsa ba. Ni kadai zan
samar mana da hanya mu wuce gaba saboda
9

TASKARNOVELS.COM.NG
haka ina mai shawartarka da ka kauce daga kan
hanyarmu idan har kana son ka tsira da
rayuwarka don ban ga abin da ya isa ya hanani
ratsawa ta cikin wannan daji ba."
Kafin sarki Dujalu ya gama rufe bakinsa tuni
katuwar halittar ta mike tsaye. Al'amarin da ya
sa gaba daya dajin ya yi lumshi tamkar rana ta
fadi, ashe da can a zaune take ba a tsaye ba. A
sannan ne sarki Dujalu ya daga kansa sama ya
dubi halittar sai ya ga cewa a wannan karon
baya hango kanta.
Nan take halittar ta sake buso iska ga sarki
Dujalu, wannan karon sai iskar ta dagashi sama
ta fara gwarashi a jikan manyan bishiyoyin dake
dajin. A dai-dai wannan lokacin ne Hursiya da
sauran Dakarun gaba daya suka farfado daga
dogon suman da suka yi suka ga abin da ke
faruwa. Koda suka ga sarki Dujalu a sama ana
gwarashi a jikin bishiyoyi har ya fara galabaita
sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka
karaya.
Ita kuwa Hursiya sai ta fashe da kuka domin ta
tabbatar da cewa shi ke nan ta rasa dan uwanta.

10

TASKARNOVELS.COM.NG
Gaba dayan dakarun dai sai suka cika da
mamaki saboda a yadda suka san
sadaukantakar sarkinsu da karfin sihirinsa
amma sai gashi duk sun zamo a banza ya kasa
ceton kansa ma bare suma ya cecesu. Nan fa
wasu daga cikinsu suka fara tunanin su ja da
baya don kada wannan halitta ta gama da sarki
Dujalu sannan ta dawo kansu. Kafin su yanke
hukunci ne wani abin mamaki ya faru, kawai sai
gani suka yi shima sarki Dujalu ya yi nuni da
hannunsa izuwa ga wannan iska mai karfi da
take wujijigashi take wata irin iska ta fito daga
cikin hannun nasa ta kama daya iskar mai
wahalar da shi suka kama gumurzu. Nan fa kallo
ya koma kan iskokin biyu suka rinka tsiri a
sama suna fitar da wata irin tsawa da kugi mai
razanarwa. Wani lokacin idan iskokin suka yi
sama sai ka ji sun fado kasa fat! Tamkar giwa ta
fadi.
Katuwar halittar da sarki Dujalu sai suka zuba
idanu kawai suna kallon gumurzun da iskokin
ke yi.
Nan fa dajin ya kara ruguntsumewa domin a
duk sa'adda iskokin suka hada jiki sai ka ga
wuta feshi da tartsatsi. Al'amarin da ya sa gaba
11

TASKARNOVELS.COM.NG
dayan dakarun suka dimauce ke nan suka kama
guje-guje a cikin dajin suna neman maboya.
Kafin a jima filin wajen ya dade babu kowa face
sarki Dujalu sai aljaninsa Rauzuf da kuma
Hursiya wadda jikinsu ke makyarkyata saboda
tsananin tsoro, shi aljani Rauzuf ma bai san
sa'adda ya fara sakin fitsari ba, amma bisa
mamaki sai ya ga na wannan feshin wuta da
tartsatsin basa zuwa inda suke shi da Hursiya
sai dai su zuba a gefensa.
A duk sa'adda iskokin biyu suka fado kasa
kauwa, sai gaba dayan dajin ya kama tambaltambal tamkar jirgin ruwa akan kogi sa'adda
igiyar ruwa ta kada.
Haka dai aka ci gaba da wannan dauki ba dadi
har tsawon sa'a guda. Daga karshe ne iskokin
biyu suka kankame juna suka kama da wuta
suka kone kurmus suka zama toka. Koda
faruwar hakan sai aka fara kallon-kallo tsakanin
sarki Dujalu da katuwar halittar a ya yin da ta
sauko da dogon kanta kasa tamkar zalbe ya leko
da wuyansa waje daga cikin tagar daki.

12

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda sarki Dujalu ya yi arba da mummunar
fuskar halittar sai yaji zuciyarsa ta buga da
karfin gaske.
Wannan shi ne karo na farko de sarki Dujalu
yaji tsoro ya shigeshi arayuwarsa. Bisa dole
Dujalu ya ja da baya taku uku, amma saboda
yana da dakakkiyar zuciya sai ya ki gudu ya
tsaya ya zare takobi, kuma ya gyara tsayuwa
akan aljani Rauzuf. Ya yin da babbar halittar ta
ga abin da Dujalu ya yi sai ta bude hannayenta
biyu ta dagasu sama kai kace tagwayen
tsaunikane ke yawo a samaniya sannan sai ta
wangame katon bakinta ta kwarara uban ihu
wanda ya zamo sanadin sake ruguntsumewar
dajin fiye da ko yaushe. Shi kansa Dujalu bai san
sa'adda ya kara ja da baya ba. Ita kuwa Hursiya
sai ta kankame Dujalu ta baya ta fashe da kuka.
Cikin kwarin zuciya Dujalu ya 6an6areta dag
jikinsa ya zaunar da ita kasa bisa kan aljani
Rauzuf sannan sai ya tashi sama kamar tsuntsu
ya juyo ya dubi aljani Rauzuf ya ce, "Ku dan ja da
baya kadan ku zuba ido ku ga abin da zai faru.
Idan na sami nasarar hallaka wannan halitta sai
mu ci gaba da tafiya idan kuma ta hallakani ku
13

TASKARNOVELS.COM.NG
koma da baya ku nemi sauran abokan tafiya
domin ku koma can birnin Hawarul din, gimbiya
Hursiya ta gaji karagata".
Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya
yunkura da dukkan karfinsa ya tasamma
katuwar halittar ya kai ma ta wawan sara a
hannunta na hagu."
Koda takobin Dujalu ta sari hannun sai
tartsatsin wuta ya tashi gami da wata irin kara
tamkar karfe da karfe. Halittar ta yi girgiza
tamkar susa aka yi ma ta.
Dujalu yaja da baya kadan, koda ya dubi kaifin
talkobinsa sai ya ga ta dakushe. Al'amarin da yai
matukar girgiza hankalinsa kenan ya gamsu
cewa lallai yau ya gamu da gamonsa.
Dujalu ya kurawa halittar idanu yana tunanin
irin dabarar ya kamata ya yi don ganin ya kawar
da ita. Abu na farko dai shi ne, ya tabbatar da
cewa in dai batun farfin damtse ne ba zai iya da
ita ba, don ko ba a gwadaba linzami yafi karfn
bakin kaza. Haka kuma idan batun karfin sihiri
ne nan ma ya san babu nasara tun da an gwada
an yi RAGAS.
14

TASKARNOVELS.COM.NG
To wai shin mene ne zai kwaceshi a hannun
wannan halitta? Ai babu mafita face sa'a. Kafin
sarki Dujalu ya gama aiyana wannan furuci a
bakinsa sai halittar ta yi masa wawan mangari
da hannunta guda a fuska saboda karfin dukan
sai da sarki Dujalu ya ga taurarin wahala a
idanunsa, numfashinsa ya sarke a lokacin da yai
sama tamkar an janyeshi da kugiya Dujalu ya
gwaru da bishiya har keyarsa ta tsage ta fado
kasa a cikin wani irin mugun hali mai kama da
rabin suma.
Koda jibgegiyar halittar ta ga ta sami wannan
nasara sai ta bushe da mahaukaciyar dariya.
Koda gama fadin haka sai Hursiya ta kwarara
uban ihu ta fashe da kuka, domin zuciyarta ta
gama karaya ya sallama cewa dan uwanta ya
gama halaka, Shi kuwa aljani Rauzuf sai ya
yunkura da nufin ya bude fuka-fukansa ya gudu.
Ai kuwa shima sai ji ya yi an fyadeshi ya baje a
kas, sai ga jini na zuba ta cikin hancinsa da
bakinsa, ko motsi bai yi ba tamkar gawa.
A dai-dai wannan lokaci ne katuwar halittar ta
fara tako kafafunta ta nufo inda sarki Dujalu ke
kwance da nufin ta mitsttsikeshi da kafarta,
sannan ta hallaka Hursiya.
15

TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin karfin hali Hursiya ta ruga kan Dujalu ta
fara kokarin janyeshi daga inda yake kwance,
don kada halittar ta cimma nufinta.
Hursiya na cikin jan sarki Dujalu sai kawai taji
ya cije. Nan take ya bude idanunsa ya dubeta ya
ce, "Ma za ki mike ruga izuwa baya, yanzu za mu
fara gagarumin yaki ni da wannan halitta wanda
zai iya janyo hallakar duk wani abu mai rai da
ke cikin dajin nan saboda haka kiyi ta gudu
iyakar iyawarki har sai inda kuzarinki ya kare,
kar ki damu dani, nai miki alkawari lallai zan
riskeki a duk inda kike kuma a raye."
Koda jin wannan batu sai Hursiya ta mike
zumbur ta falfala da gudun tsiya.
A dai-dai wannan lokaci ne halitar tayi taku
daya jal, ta isa daf da Dujalu ta daga kafarta
guda sama za ta mitsttsikeshi. Yadda Dujalu ya
ga fadin kafar halittar tamkar katon tsauni ne
zai danneshi cikin tsananin zafin nama sarki
Dujalu ya daka tsalle ya haye kan saman kafar
halittar ya kama azababben gudu akanta, yabi ta
kan kansakalin kafar ya bi ta cinya tamkar
kadangare na hawa bango.

16

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda halittar taji Dujalu na tafiya a jikinta sai ta
rinka kawo masa duk da tafin hannunta. Da
zarar ta kawo dukan ya goce sai ka ji wata irin
kara fau tamkar an buga tambura, wani irin
gagarumar iska na tashi. A haka ne Dujalu ya
samu ya isa kan kafadar halittar, sai da ya yi irin
gudun rabin sa'a uku akan kafadar sannan ya
iso inda fuskar take ya sake daka tsalle sama ya
sari habar halittar da takobinsa. Sautin karar
haduwar karfe da karfe ne ya tashi kawai.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Dujalu ke
nan domin shi zatonsa halittar za ta ji sara a
fuska. Nan fa aka fara sabon gumurzu a
tsakaninsu ya zamana cewa Dujalu na ta tsalletsalie akan halittar tamkar mai
yawo a cikin katon daji. Ita kuwa halittar ta
rinfka kai masa duka da cafka, aka rasa wanda
zai sami nasara a cikinsu. Sai da aka shafe sa'a
tara ana wannan gumurzu. A sannan ne sarkı
Dujalu ya gaji ainun, ita kuwa halittar ko kadan
babu alamar gajiya a tare da ita tamkar ma a
sannan aka fara artabu.
Koda sarki Dujalu ya fahimci cewa idan fa aka ci
gaba da wannan gumurzu a haka izuwa tsawon
17

TASKARNOVELS.COM.NG
sa'a daya jal zai sare ya kasa komai, halittar ta
sami nasarar hallakashi sai hankalinsa ya
dugunzuma ya fara tunanin abin da zai
fissheshi. Tsawon rabin sa'a Dujalu bai yi
tunanin mafita ba.
A dai-dai wannan lokaci ne halittar ta shammaci
Dujalu ta mangareshi ta baya ya rlkito kasa daga
kan kafadarta. Koda ganin haka sai halittar tayi
shiri tana jira kawai Dujalu ya fado kan turba ta
murkusheshi da guiwarta yadda za ta talitseshi.
Saboda nisan
End Ads