ta dark blue tayi mata kyau mayafin abayar ta daura shi duk da fuskar ta ba walwala amma ba ƙaramin kyau tayi ba.
ganin tsohuwa da sauri ta ɗurkusa tace '' sannu da zuwa..,
sakar baki da hanci Inna tayi dole malam yace zaman wannan balarabiyar akwai matsala mace har mace duwawuka sai juyawa wa suke kamar da gayya take juya su kai gaskiya jawa ta cika mahaukaciya da har bata,
bata labarin yarinyar nan ba... sai boka ne ya bata labarin ta.
jikin najlah ne yayi sanyi ganin irin kallon da take binta dashi ta tashi tsaye INNA ta saki wata dariya ta rashin gaskiya tace '' ikon Allah ɗana amma dai wannan kanwar kace kamar ta ɓaci..,
zama yayi yana cewa eh wallahi kin zo Lafiya...?
Lafiya qalau alhamdulilah na same ku lafiya.
Alhmdllh lafiya qalau gashi jawaher bata nan ta , tafi makaranta.
INNA tace '' to Allah ya dawo da ita lafiya..,
Jawad yace amin ya Allah .
Najlah kayan motsa baki ta haɗu mata , ta kawo mata gaban center table da sauri inna ta cire hijabi tana cewa yar nan sannu ya sunan ki...?,
najlah tace '' najlah .,
Masha Allah sannu da aiki naja'atou ni wallahi nafi gane sunan gargajiya wannan lankwashe lankwashen ban iya shi ba.
dan murmushi najlah tayi tace '' a'a ba naja bane najlah ne ko wanne dabam ne..,
riƙe hannun'ta tayi fatar iya da take kaushi kaushi ji tayi ta muzanta, domin har wani lubu lubu ga uban taushi taji fatar najlah nayi tace '' yar nan yi min afuwa zan faɗa miki naja wallahi ko za'a saka min huka a makoshi bazan iya faɗar wannan suna ba me uban wahala....,
najlah tace '' to..,.
ta faɗa tana barin gurin shiga daki tayi ta zauna ta zuba ta gumi abubuwa da yawa nayi nata yawa akai wayar tace tayi ringing da sauri ta dauka Hajiya ce kuka ta she dashi dakyar tayi shiru Hajiya tace '' auta bana son wannan damuwar dake kike fa me yayi zafi kamar ba a gidan dan uwanki, kike ba..me Jawad yake miki wallahi nasan Jawad ba zai taɓa yi miki abin da zai cutar dake ba.....,
share hawaye tayi tace '' hajiya ba shi bane....,
hajiya tace '' to waye ....?,
hawaye ta share tace '' wata ran sai ba kwanta bacci naji ana taɓa jiki na wallahi bakarya nake ba..,
to ni bana son irin wannan zancen addu'a zaki dinga yi kinji ko da wasa kar wanda kika kara faɗawa a haka a zuciya ake barin komai, ni da mahaifinki da yan uwanki muna yi miki addu'a ba abin da zai iya cutar da ke..
to yau fa har da sauri Hajiya tace '' innalillahi najlah yanzu me nagama faɗa miki...?,
tayi saurin katsai ta.
to ba da duk abin da yake damuna ba ina faɗa miki kuma kina ban shawara bana boye miki komai shi ne yanzu zaki ce bakya son ji kema kenan tsoran aljanun kike kar su kama ki.
najlah ta fada tana turo baki cikin shagwaɓa.
Hajiya tace '' a'a ni ba tsoran su nake ba kawai dai ki koyi rike sirrin ki najlah wata ran aure za kiyi sai duk abin da ya faru a gidan ki na dade da ba na dadi ba sai ki faɗa min...,
to ai yanzu ban yi ba.
to Allah dai ya kyauta ya Jawad yake...?
hmmm yau bashi da lafiya wuni yayi a kwance nace zan kirawo mai likita yace nabari ba abin da zai iya yi mai aunty kuma tun safe ta fita..
HAJIYA tace '' najlah bana son rashin hankali ki kula dashi sosai ki tambaye shi me yake so domin nasan halin ki ba lallai ki kula da shi ba..
wallahi Hajiya duk nayi mai na bashi wayar ki tambaye shi.
da sauri tace '' Allah me iko a'a Allah ya shirye ki gabanta yawa yar fari ni wallahi najlah idan ace a yar fari kika zo ban san me za kiyi ba..,
Hajiya yaya tsoho yana da gabon ta ne shima ai ɗan fari ne..
ta faɗa tana danne dariyar ta..
cikin rashin fahimta Hajiya tace '' wane kuma yaya tsoho najlah..?,
yaya fa ta faɗa tana dariya..
Hajiya tace '' hmmm Allah ya kyauta duk randa ya jiki ba zaku kare ta dadi ba ki ci gaba ban hana ki ba wallahi.
kai Hajiya to shikkenan sai an jima.
sallama suka yi da sauri tace '' yaya ya bani sarkar gold kiyi mai godiya ki fadawa abbana..,
Hajiya tace '' to zan mai Godiya ina taya ki murna.
to ngd sosai ta faɗa tana kashe wayar.
parlour kuwa.
INNA kwashe cinyoyi tayi tana cin kazar da najlah ta kawo mata sai ta kora da lemo me sanyi ba irin abin da bata wassafa ba a zuciyar ta domin taga guri ba dole fata ta koma katifa ba mutum yana cin wannan abubuwan dadin.
Jawad fitowa yayi ko a jikin INNA hatta dan kwali ta cire wata kananan kalbace wacce akai mata da zaren riƙe gashi domin kanta kamar hammatar ɗan iska yake ko kunya bata ji ba daukan dan kwalinta tayi ta daura tana Barka da saukowa Alhaji.
kunya ce ta kama Jawad yace '' inna sannu da hutawa..,
wayar sace tayi ringing be jira me zata ce ba ya kauce daga gurin domin yaga kiran daga asibiti ne Allah ya saka lafiya gaisawa suka yi sannan aka sanar mai abin da ya sami Jawaher.
wani irin rawa zuciyar sa tayi amma Bama su sanar mai zubewar cikin ta ba.
godiya yayi masa yace gashi nan zuwa sannan ya kashe wayar.
dawowa yayi yace '' INNA gama cin abinci ki shirya nakai ki inda jawaher take..,
bata kawo komai aranta ba tace '' to..,
ci ta gama yi tas sannan ta goge hannun ta jakar kayanta ta dauko Jawad yace ta kawo ya shiga da ita daki.
batai musu ba ta bayar da jaka bayan ya kai daki ya sauko fita suka yi najlah tace a dawo lafiya..
kallon yayi yace '' yauwa najlah sako hijabin ki mu tafi..,
da sauri tace '' ga mayafina nan bara nayi rolling..,
wani irin kallo yayi mata tuni ta koma ta dauko hijabinta tana kunkuni
INNA tace '' naja gata yayi miki naga duk ranki ya ɓaci gwara ana kare mutunci wallahi mazan yanzu yadda kika san masu gindin ayu haka suke barin ma irin ku masu komai masha Allah,
kunya ce ta kama najlah tayi shiru Jawad kuma nunawa yayi be ma san me yake faruwa ba ma..
buɗe mota yayi da sauri Inna ta shiga gaba najlah dan murmushi tayi domin abin ya bata dariya ta shiga baya.
ko direba me tsaya jira ba yayi wa motar key a hankali ya soma tafiya horn yayi me gadi ya buɗe mai gate.
sosai najlah take mamaki to me ya sami Jawaher gaban tane ya fadi lokacin da taga sun shiga asibiti parking yayi INNA ta sauko tana wage wage budewa najlah murfin mota yayi sosai najlah tayi mamaki yaya ne ya buɗe mata murfin mota Allah me iko haka ta raya a zuciyar'ta fitowa tayi ta sakar mai murmushi shima martani ya mayar mata hana rike hannunta jerawa suka yi suna tafiya abin sha'awa Inna na bin bayan su tana kalle kalle wani Bature ne ya wuce da sauri tace '' lah bature ikon Allah har masu jajayen fata zuwa asibitin nan suke..,
bata da me bata amsa duk abin da taci karo dashi sai tayi Magana har suka isa word din da Jawaher take.
dakin da likitan ya faɗa masa ya shiga INNA ihu ta saka tace na shiga uku jawa kece a haka da sauri su deeya suka tashi suna gaishe da ita amsawa tayi tana shafa kafar jawaher da aka sakale..
deeya tace '' INNA sai hakuri muma munyi kuka kamar ba gobe tare za mu tsallaka titi sai tace bara ta fara yi gaba shi ne me mota ya buge ta wallahi ko tsayawa beba ya gudu ashe ma tana da ciki cikin tas ya zube..
zaro ido INNA tayi ta shiga uku mafarkin da kullum take yi gashi wani tsinanne ya zubar da shi...
INNA tace '' wallahi ba zan yarda ba tunda har ya zubar min da jika na yasin bazan yarda ba kai idan Alhaji zaka yarda ni ba zan yarda ba shekara nawa Allah be baku haihuwar nan ba sai yanzu sai wannan shegen ya zubar da cikin nan..,
kuka take sosai su deeeya ma kama kuka suka yi sai kace mutuwa aka yi.
najlah mamaki ne ya ishe ta daga anyi bari sai kuka Allah da ya bata zai ƙara bata..wani Jawad juyawa yayi bece komai ba ya tafi gurin likita.
Na'ilah tace '' kanwata zo nan ki zauna kya zatsa ya a tsaye...,
shigowa tayi tana gaishe su hadi da tambayar ya me jiki amsa mata suka yi suna sharar hawaye..
zama tayi a lokacin jawaher ta buɗe idon ta a hankali haɗa ido tayi da INNA Inna da take kallon ta tace '' sannu jawa Allah ya tsinewa wanda ya buge ki har ya yanyo mana wannan asarar...,
KARUWAN CIKIN GIDA
Ga channel dina kuyi min subscribe Dan Allah wai ina masoya na suke.
https://www.youtube.com/@nasreenminallah
https://vm.tiktok.com/ZSBRtRQmN/
Domin samun update kuyi following dina
Book ¹
EPISODE ²5
Da ido kawai *JAWAHEER* ke binta ba bakin magana domin ko iya buɗa bakin ta ba za tayi ba.
zama *INNA* tayi tana share hawayen ta ba ƙaramin bakin ciki taji da wannan abu ba.
*NAJLAH* zaman gurin gundurarta yayi sai kallo suke binta dashi tamkar ba mutum irin su ba suke gani, *JAWAD* ne ya shigo tare da likita kara dubata yayi sannan yace '' Sakamakon kan'ta da ya bugu bata son hayaniya hakan zai ƙara nata ciwon kan da take fama da shi ɗan Allah kar dukkan ku, kuce zaku kwana mutun ɗaya ma ya isa shima ɗan ya zama dole ne , amma muna ma da ne kula da patient a asibitin nan..
Karab INNA tace '' ni zan zauna da ita ,su sai ko wacce ta koma gida lada ya isa godiya nake da kuka tsaya kuka kula da ita..,
taɓe baki deeya tayi tana tashi tace '' ku taso mu daman yanzu muke shirin tafiya Allah ya kara sauki..,
wani kallo *INNA* tayi mata tana cewa amin idan gaske kike yo tilashin wuya makoko kun ga abin alkairi shi ne ko wacce ta nade ƙafafuwan ta , tamkar wasu majiyata kuka ɗane kan gado kun gama ci kun koshi Ni wallahi da na shigo na zata suma marasa lafiya ne kukan da suke yi da bayanin da suke yi shi ya wayar min dakai yan bantan uba anzo cin banza banza bata samu ba..maza Umma ta gaida ashsha gayyar na ayyah....
*JAWAD* wata iriyar kunya ce ta kama shi me *INNA* take faɗi haka mutanen da suka tsaya akan yar'ta kamata yayi suyi daraja a idon ta.. zura hannu yayi a aljihu ya kirgi kudi yace '' Nagode sosai Allah ya bar zuminci ungo kwasha mai..,
Wuf *INNA* ta karfi kudin tana cewa a'a wannan yayi yawa ba'a abu dan Allah sai ka biya su gaskiya ɗana hakan be kamata ba ko wacce zan bata dubu ɗaya ya isa ta hau mota har ta , samu canji sauran kudin zan ajiye ba fata ake ba ba'a san inda wannan ciwo na jawa zai tsaya ba duk kabi ka ƙarar da kudin ka yake nan wa'yannan masu zubin jar hudu fuska kamar an gasa ɗayan nama sama sama ko kobo ba za su baka ba. dan haka ke ungo.
banza sukai mata dan dai da *JAWAD* ne amma wallahi da taji bakar magana matar nan ashe haka take da rashin mutunci gaskiya *Jawaher* gado tayi cewar *DEEYA* a zuciyar ta.
gaba ki ɗayan su basu amsa ba suka fita sai ruwan Allah ya isa da sukai mata Jawad cije lips din'sa yayi ya ja kujera ya zauna kusa da najlah.
da sauri *INNA* tace sannu dannan da alkunya zo ga wajen matar ka kaga na gaje maka guri.
da zauri najlah ta kalle ta sai kuma ta kalli yaya sosai abin yake bata mamaki wannan wacce irin uwa ce Jawad yace '' a'a barshi nafi jin daɗin zama a nan..,
to , to am dan nan dan Allah ina so a kawo min jakar kayana kaga ni zan dinga kula da ita har Allah ya bata sauki.
Jawad yace
"to insha'Allahu zan kawo miki ita...,,
yauwa dan nan kiran sallar magariba aka yi. tashi Jawad yayi ya tafi masallaci najlah ta dauro alwala ta shinfida prayer mat ta tada sallah INNA na aikin cin abinci tamkar zai gudu ya barta bayan ta idar Jawad yazo yace '' to inna ni zan koma zuwa gobe zan dawo na kawo miki kayan ki..,
to shikkenan ba matsala tashi najlah tayi da sauri tace '' ina kuma zaki ba tare za mu zauna ba ya za a yi ki zauna gida daga ke sai namiji..,
da sauri najlah ta kalli INNA tace '' dan uwana ne fa..,
dan dan uwanki ne uwa ɗaya uba ɗaya kuke..?,
najlah tace '' ni ban iya zaman asibiti ba , bazan kuma fara ba..,
tana sane tayi mata haka domin taga matar bata da mutunci ko kaɗan
murmushi Jawad yayi bece komai ba ya riƙe mata hannu suka fita yaya wannan matar halinta bashi da kyau ni wallahi bazan ƙara dawowa cikin asibitin nan ba.
kallon ta JAWAD yayi yace '' saboda me..?,
baka ga abin da take fadi ba , bata iya magana ba kaga abin da tayi wa wa'yannan be dace ba..
buɗe mota yayi bece mata komai ba shiga gidan gaba tayi ya shiga mazaunin driver ya tashi motar tafiya yayi me dan nisa sannan ya iso bakin gate din asibitin horn yayi me gadi ya buɗe mai kofa.
hawa kantiti yayi kunna karatun Alkur'ani yayi a hankali yake tashi a cikin motar.
sai ka lura sosai zaka ga yana bib karatun da alama yana jin daɗin bin karatun domin wani annuri fuskar'sa ke yi kallon sa najlah tayi.
sai kuma ta dauke kan'ta ta mai da kan'ta ta kwantar a kan cinyar ta , har suka isa gida bata kara ce mai komai ba ,
saukowa tayi ta fito riga shi barin gurin tayi domin ya tsaya hira da ma'aikatan gidan..
cire hijabinta tayi ta kwanta a kan gado tana sauke ajiyar zuciya wayar ta , ta dauko zaro ido tayi ganin har 20 miss call na ya muneef da sauri ta kirawo shi amma har ta katsai ba dauka ba tana katsaiwa ya kirawo ta , dauka tayi tana cewa kai hakuri bana kusa da wayar naje dubiya asibiti.
muneef yace '' bakomai wane bashi da lafiya..?,
gyara kwanciya tayi, tace '' matar yaya..,
okay Allah ya bata lafiya daddy ma bashi da lafiya naje ma duba shi jiya wallahi yana jin jiki..,
Allah sarki Allah ya bashi lafiya da yake kuna kusa ko...?,
a'a bama kusa tsakani na dashi kamar ace miki kano da Kaduna..
ikon Allah ai naza ta kuna kusa da juna..ashe ba haka bane kana lafiya..?
MUNEEF yace '' hmmm lafiya qalau alhamdulilah wallahi najlah ji nake kamar kinyi min nisa nazan taɓa samun ki ba kullum cikin fargaba nake dan kafin na tafi akwai wata magana da naji ƙarshen ta lokacin naje gurin jadda to har yanzu ban samu amsar ba..shi ya saka kin ganni duk na rame wallahi idan na tuna karshen abin da kunnuwana suka ji ina shiga tashin hankali...,
haba yaya muneef ba abin da zai faru insha'Allahu. me kaji jadda na fadi..?
dan jim yayi tamkar me tunanin ya faɗa ko karya fada sai kuma yace '' manta kawai da maganar.. kina lafiya ya karatun kin fara kuwa..?,
a'a dan girman Allah ka faɗa min.
tonda kin gamu ki sani cewa naji kamar jadda yana cewa ko yayi miki miji yana faɗawa Abba to badai naji suna ba amma wace a gaban abba idan bake ba..
dariya sosai najlah tayi tace '' gaskiya kai sai addu'a kasani ko maganar auren ya TAUFIQ suke yi bada yusrah aka haɗa su ba..?,
wani sanyi ne ya ziyarce shi yace '' wallahi na manta da wannan zancen haka ne kuma kinji kuwa yadda naji i love You so much..,
ɗagowa tayi tana cewa amma da ka tsaya kana wani tunani sai anjima kar yaya yazo yaga ina waya.
okay sai an jima ya faɗa yana mata sallama itama tayi mai ta , tashi zaune Jawad ne ya shigo fuskarnan ɗaure tamau yace '' bani wayar ki..,
jikin ta ba wani kwari ta miƙa mai wayar ta amsa yayi, yana dubawa ɗazu ya shigo bama tasan ya shigo ba , shine sai da ta gama wayar sannan ya dawo history call ya je ya duba sweetheart ya MUNEEF.
wannan suna da ya gani ba ƙaramin dakar mai zuciya yayi ba , kasa tsayuwa yayi da ƙafafuwan sa yaja stoll ya zauna yana mai da boyayyiyar ajiyar zuciya
zura wayar yayi a aljihu abubuwa da yawa sub wa kwakwalwar sa yawa ha zubewar cikin jawaher..ga abin da ya tarar najlah tayi, rintsai idanuwan'sa yayi yana neman dauki gurin Ubangiji.
ko tukin da yaya karfin hali kawai yake mafarkin da yake na samun yara ya samu kuma ya rushe amma bakomai Ubangiji da ya ba shi, shi zai ƙara bashi wani.
ita kuma yau najlah zai cire duk wani tausayin ta , ya hukunta ta dai-dai da abin da tayi daman Ubangiji ya sani ƙarfin hali take yake kawar dakai to yanzu takai shi bango...
tashi yayi ya fita ba tare da yace mata komai ba tausayi ya bata tasan ba a cikin hayyacin sa yake ba maganar zubewar cikin jawaher dole ta bugi zuciyar sa , Allah ya bashi wani..
yana fita daga dakin najlah study room ya shiga zama yayi yana dauko laptop din sa ta ci gaba da aikin da yake ɗazu..
kiran sallar isha da aka yi shi ya taso dashi ya bar study room ya dauko alwala ya fito.
ko kallon inda dakin najlah yake beba ya fita Masallaci.
Najlah da tana la'akare dashi tsoranta ɗaya karya sauke fushin sa a kan ta , ganin ya fita, ta rufe kofar ta tana sauke ajiyar zuciya tada sallah tayi gaban ta na tsananin bugu bata san dalili ba haka kurum jikin ta yayi sanyi ta shiga cikin wani irin hali itama bata san dalili ba.
bayan ta idar da sallah. ta dauki karatun Alkur'ani tana karantawa ta dade tana zaune sannan ta daga hannu ta