x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - KARUWAN CIKIN GIDA hausa novel by oum yesmeen

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 77751 words

Category: Tale Stories

Views 325

18 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sa yayi tabbas idan ya ci gaba da zama haka batare da ya nemawa kan'sa mafita ba akwai matsala tamkar me amfani da wani magnet inhar zasu kasan ce inuwa ɗaya tabbas mafarkin rayuwar sai ya canza salo duk kan wani gini da yayi sai yaji yana rugujewa tamkar ba da kyakkyawan tubali ya gina shi ba.
yana so ya koyi sarrafa rayuwar sa ba tare da an sarrafa mai ita ba ta hanyar bashi doka da oda tun daga bayyanar ta yake tunanin komai zai sauya ashe ba haka bane rayuwar dadin da yayi a baya zata juya ta zame mai ruwan zafi duk da a wani ɓangare tana nan a matsayin ta be canza mata ba guri ba a duk lokaci da ya ɗaga ido ya dube ta sai yaji wani irin matsanancin farin ciki.......
ada yana tunanin ba wanda ya fishi sa'a amma a yanzu komai ya rushe abubuwan da yake kallo sune hasken rayuwar sa ashe ba haka ba ne wa'yanda yake tunanin sune dubu a rayuwarsa kafin bayyanar ɗaya daga cikin dubu ashe su ne hasken nasa me ya saka rayuwa ta zaɓi tayi mai a haka shin wai shi bashi da Sa'a ne ko me rintsai ido yayi ya cije lips din'sa tunani na shirin haukata mai rayuwa inhar be bar sa ba dawowa yayi ya kwanta tare da canza salon kwanyar tasu.
a zafafe yake yin komai da yake baya cikin hayyacin sa.
a wannan lokaci kuka ta saka da karfin ta saboda yafi na jiya ciwo ganin numfashin ta yana fusga ga kuma lalurarta sai ya dakata tashi yayi ya dauki key din sa da wayar sa ya bar dakin.

Lokacin karfe hudu tafiya nasa part din yayi, ya shiga toilet ya sakarwa kan'sa shower kifa kansa yayi a bango yana jin yadda ruwan sanyi ke ratsa kan'sa wani irin ciwo da radadi zuciyar sa ke masa ,
wanda bashi da masaniyar me hakan ke nufi wasu abubuwa yake hangowa dafa Glass shower cubicle yayi zuciyar sa na tsananin bugu dakyar ya karasa wankan da yake lokaci ɗaya zazzaɓi da ciwon kai suka rufar mai.
buɗe wata haddiyar Glass door yayi fararen towels ne jere sai kamshi Shaghaf oud by Swiss Arabian suke ɗaukan ɗaya yayi ya daura sannan ta dauki na tsane kan'sa ya fito zama yayi a dressing mirror dauko *RITUAL HOMME 24H HYDRATNG* ya shafa tashi yayi ya buɗe wardrobe dinsa ya dauko jallabiya feshe jikin sa yayi da turaren Musik Maqam addu'a yayi ya kwanta bacci karfe biyar da rabi dai-dai ya tashi da sauri ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito a cikin sassarfa yake taka stair case domin an kusan kiran sallah.
dakin Najlah yaje yayi knocking tamkar da dutsai yake ko motsi ba tayi ba jan ƙaramin tsaki yayi ya kalli agogon hannun sa besan ko ta fara sallah ba amma bara yaje ya dawo yau ba zai zauna zaman har sai rana ta fito sannan ya dawo, da yake dazu ko da wasa be kallo kasan ta ba balle yasan halin da take ciki.......
duk bidiran yayi, yi asama yayi shi.
tafiya ya fara yana tasbihi a cikin ransa sai dai ka kula sosai sannan zaka ga yana motsa bakin sa.
ana idar da salla ya dan jima kadan sannan ya taso duk zaman da yayi tana ransa yana shigo ya buɗe dakin ko sallama be tsaya yi ba samun ta yayi ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka jin motsin sa da sauri ta taso ta rungume shi tare da sakin wani kukan har da shashsheka idanuwanta yayi jajir haka fuskar'ta ma abin ka da farar fata.
cikin tashin hankali ya ɗago fuskar ta yace '' Najlah me yake faruwa baki da lafiya ne..?,
ba bakin magana kai ta girgiza mai domin bata san ta yadda za tai mai baya ni ba.
kamota yayi ya riƙe hannun ta suka fito daga cikin dakin bataimai gardama ba ta bi shi har dakin sa zaunar da ita yayi a kan gado sannan yace '' ki faɗa min me yake damun ki, kinsan ba abin da na tsana sama da ina yi wa mutum magana yayi shiru..,
ƙara fashewa tayi da kuka tayi ƙasa da kan'ta zamewa tayi ta zauna akan carpet.
taci gaba da kukan ta zuba mata ido yayi yaga iya gudun ruwan ta,
tashi yayi ya fara shiryawa domin tafiya aiki yau akwai cases da dama a gurin sa dan haka insha'Allahu takwas a court za tayi mai...
ganin yana ƙoƙarin cire kaya da sauri ta kurawa kafar wandon ta ido tana ci gaba da kukan ta.
tashi tayi ta fara tafiya tana murza idanuwan ta tana ci gaba da kukan ta dakatawa yayi da saka wandon sa yace '' NAJLAH..,
juyowa tayi hawaye na ci gaba da bin fuskar ta , tamkar an buɗe fanfo miko mata hannu yayi a hankali ta kalli gaban rigar ta ashe a bude yake kuka ne ya ƙara kwace mata ganin kusan botira uku a buɗe kuma na saman wuyan ta wajejan kirjinta miƙa mai hannu tayi ta karaso gunsa riƙe hannun ta yayi ya zaunar da ita kwantar da murya yayi yace '' yanzu NAJLAH kuka kika zaɓa akan ki faɗa min me yake damun ki, idan ni ba ki dauke ni a matsayin dan uwa ba ina wayar ki kirawo Aliyu ko taufiq ko aunty rafi'at ko aunty Hafsah ko MUNEEF ko saran family wa'yanda kika dauka yan uwa, wa'yanda zaki iya sharing farin ciki ko bakin ciki ko kuma ga tawa wannan kirawo wanda kikai niya..,
ya ƙarshe maganar sa yana ajiye mata wayar sa a kan cinyar ta kuka ta fa tashe da shi tana girgiza kai kifa kan'ta tayi a kan gado cikin dashewar murya saboda kukan da ta yi tace '' kayi hakuri yaya ba haka nake nufi ba bansan yadda zan maka baya ni ne wallahi bazan iya ƙara kwana a cikin gidan nan ba kirjina ciwo yake min haka lips din'na duk sun kumbura suna yi min zafi baki na wani irin kamshin mouth spray yake kullum cikin dare kamar ina baby feeding...two day's kenan..,
tamkar be san me yake faruwa ba ya dan shiga tunani na wani lokaci sannan yace '' baby feeding fa kika ce..?, cikin dare ake baki yara kike basu abinci suna da girma ko basu dashi yan shekara nawa ne..?,
kanta ta dago tana kuka tace '' bafa yara bane kamar babba ne yana taɓa min breast din'na..,
kai ya jinjina yana tunani sai kuma can yace '' daman kina da breast,
kallon sa tayi sai kuma kunya ta kama ta ƙasa tayi da idon ta
dan murmushi yayi yace '' okay kina addu'a idan zaki kwanta..?,
wallahi har alwala nake yi amma baya fasa zuwa kuma anan gidan na fara haka dan Allah ka mai dani gurin Hajiya ta wallahi bazan iya ba ciwo yake min sosai...
okay mu gani ina ne yake miki ciwo
JAWAD ya faɗa yana tsare ta da idanuwan'sa.
da sauri Najlah ta ɗago ta turi bakin ta tace '' a'a ba sai ka gani ba..,
kai ya jin jina yace '' yau ina tunanin zan tafi Yola akwai case din da nake bincike acan ina tunanin zani gida baki da abin da za a tawo miki dashi..?,ina tunanin zan iya kwana uku zuwa biyu..,
Ihu ta saka tare da buga ƙafafuwan a ƙasa kamar wata ƙaramar yarinya tace '' dan Allah ka tafi dani kar ka barni wallahi bazan iya kwana ni kaɗai ba a gidan nan yayi min girma dan girman Allah ka tafi dani yaya..,
kura mata ido yayi tabbas NAJLAH yarinya ce a ko yaushe wautar ta da yarintar ta ƙara fitowa suke ga uwa uba kuruciya da take diban ta ban da haka mene na wani yin buri har da buga kafa a ƙasa , bayan yanzu ta gama kuka yanzu kuma ya dena ta manta da wannan maganar dauke idon sa yayi yace '' idan kuma da gidan kine ya za kiyi kike cewa yayi miki girma bakya ganin bake kaɗai bace akwai cleaner's akwai security ba abin da zai cutar da ke idan ba ikon Allah ba..,
yaya to ai kaga ban girma ba idan na girma nayi gida sai na kwana ni kaɗai amma dan Allah ka tafi dani..
haɗe rai yayi domin ya lura ta mai da maganar sa wasa yace '' ba inda zani dake au shi ya saka kike taɓa kenan ke har yanzu baki girma ba amma ai kin iya soyayya har kike zabar wanda zaki aura..,
Kuka ta fara tace '' wallahi ba saurayina bane shi ɗan Allah kayi hakuri ka tafi dani...bazan iya zama ba ni kaɗai ba ..,
Oh kenan idan kika tashi aure me mata zaki aura..?
shiru tayi bata ce komai ba tashi yayi yace '' ki fita zan shirya na riga da na gama magana..,
fita tayi a guje tana kuka tana shiga dakin ta kayan ta , ta soma haɗawa a trolley din'ta hijabi ta saka idan taje gida tayi wanka ko wanke fuskarta ba tai ba duk jirwayen hawaye jin alamun saukowar sa da sauri ta fito tana jan jakarta tana nishi...
turus yayi haɗe ran'sa yayi ya daka mata tsawa ihu ta saka mai ta durkusa ƙasa tana hawaye haɗe rai yayi yace '' ga kudi nan akan dining idan kina da bukatar wani abu sai kiyi amfani da su idan sun yanke miki kiyi min magana zuwa jibi zan dawo...,
banza tayi mai tana kuka ganin bata da niyar magana ya dauko bandir din kudin ya ajiye mata a kusa sa da ita ture kuɗin tayi tana ci gaba da kuka ce mai a kayi tana bukatar kudi zai bata, tafi son zuwa gida...
ajiye briefcase din'sa yayi ya lura idan be tauna tsakuwa ba domin aya taji tsoro Ba zata denai mai wannan iskancin ba yawa wata yarinyar goye daukan cable din caza yayi yayo kan'ta da sauri ta tashi amma bata bar gurin ba duk tabi ta wahalar da kan'ta tausayin ta ne ya kama sa.
zama yayi yace '' zo.,
hawaye ta goge tace '' dan Allah kai hakuri ka tafi dani..,
kizo na miki...
Ko ranki ya ɓaci.
zuwa tayi tana raragefe duban agogon'sa yayi yace '' ki gyara gidan nan zuwa karfe uku zan dawo sai mu tafi zan mana booking na jirgi ayanzu office zani..,
kallon sa tayi tace '' dan girman Allah da gaske kake...?,
na taɓa faɗa miki karya ne kina ɓatan lokaci NAJLAH.
da sauri ta tashi tana jin dad'i tashi shima yayi ya dauki briefcase din'sa cikin jin dad'i tace ''a dawo lafiya Allah ya tsare hanya ta bada abin da ake nema..,
murmushi yayi ya girgiza kai ya fita yana fita ta dafa indomi taci Sannan ya yi wanke wanke abincin da taci jiya ta ajiye ya lalace.
zuwa tayi a cikin dustbin harta saman sa sai da ta gyara ta dawo ƙasa dakin Jawaher ne dai bata taɓa ba, ba ruwanta wanka tayi ganin jinin ya ɗauke tayi wankan tsarki ta fito shiryawa tayi cikin wani material milk colour da adon flowers gold rigar bubu ce da wando falazo.
Lokacin karfe ɗaya sallah tayi ta zauna tana kallon agogo a hankali ta furta lokacin ma , baya sauri.
kwanciya bacci tayi da yake bata jin yunwa ɗaukan wayar ta tayi tana charting basma CE tayi mata magana Mutanen abuja ganin ko sai ancike form da wowar ku, kuwa sai baba ta gani.
dariya NAJLAH tayi da taga wannan messages din shiga tayi ta tura mata sticker dariya 😂🤣 bata ce komai ba kashe datar ta , tayi ta kwanta bacci ne ya dauke ta.
ƙarfe 3:02 ta tashi da sauri ta kalli a gogo jikinta ne yayi sanyi tana tunanin anya kuwa zai zo zuba ta gumi tayi jin karar buɗe get da sauri ta fito harabar gidan tun daga nesa ta hango shi washe baki tayi tana murmushi ma'aikatan gidan zuwa sukai suna mai sannu da zuwa ƙarasawa tayi tana biye dashi a baya ne nuna ya ganta ba suna zuwa wajen kofar da za ta sada su da parlour gidan ya janyo ta ya shigo da ita cikin faɗa yace '' NAJLAH bansan wanne irin kunne ne da ke ba wallahi bakya ji yanzu haka kika fito ba kunya duk yawan mazan da suke gidan nan kika ratsa su kika tsaya a bayana NAJLAH gadi na aka baki bani da labari ne wallahi sai na fasa tafiyar dake inga ta tsiya..,
kwalla ce ta taru a idon ta , tace '' dan darajar annabi kai hakuri na dena wallahi..,
Banza yayi mata ya zauna yace '' kawo min ruwa..,
da sauri ta shiga kitchen ta dauko mai durkusawa tayi tace '' gashi yaya...,
amsa yayi yana cewa dauko kayan ki kala uku ki tawo..
tashi tayi tane cewa ina da wasu a can.
Okay idan za mu dawo kya kwaso su akan me zaki ajiye musu shirgi ,
da sauri ta kalle sa idanuwanta sun taru da kwalla tace '' shikkenan na bar gidan kenan...? idan aka bada hutu bazan dinga zuwa hutu ba shi ya saka na bar kayan acan..,
kallon ta yayi, yayi wani murmushi na gefen baki yace '' ehmn kin bar gidan ke da zuwa gidan sai dai ziyara kin zo nan kenan mu biyu a cikin gidan nan yayi mana yawa gwara mu ƙaro wani mu zama mu uku tun da Allah be bamu yara ba..,
da sauri ta kalle sa sai hawaye shar shar ya soma bin fuskar'ta ta kasa ma magana..
sakar baki yayi yana kallon ta yace '' Najlah zama da nine bakya so kome..?,
juyawa tayi tabar gurin toilet ta shiga ta wanko fuskar ta ta saka hijabi ta fito cikin shirin ta shi kuma lokacin ya sauko daga sama cikin farar shadda gezner an masa dinkin babbar riga ya saka bakin glasses aikin jikin ta ma baki ne dan haka adon wular sa ma akwai baki a jiki takalmin sa Hermes shima baki da sauri tace '' na manta ba dauko wayata ba..ina zuwa..,
da sauri ta shiga cikin dakin ta dauko jaka ta saka wayar ta , ta zuge zip din ta rataya ta.
fitowa tayi ta tace yaya ganin bata gansa ba a guje ta kwasa yana tsaye a kusa da da dining room yana kashe fitilun dakin da sauri ya kalle ta , yace '' NAJLAH..,
juyowa tayi tana dariya tace '' na zata ka tafi ka barni..,
girgiza kan'sa yayi yace '' Allah ya shirye ki...,
tsayawa tayi ya karaso kallon luggage din'sa tayi tace '' yaya kwanaki da yawa za muyi kenan..?,
a'a akwai takardu a ciki na fada miki bincike zai kai ni za kuma muyi meeting.
kai ta gyaɗa kai tayi tana turo baki.
Fitowa suka yi ya kulle kofar parlour shigewa gaba yayi tana binsa a baya direban da zai kai su airport tun dazu yake jiran sa yana ƙarasowa da sauri ya bude masa kofar baya shiga ya fara yi sannan sai NAJLAH kullo kofar yayi cikin sauri ya shiga yayi wa motar key tuni me gadi ya wangale musu gate hawa kan titi suka yi suka fara sharara gudu har suka isa airport NAJLAH sai murmushi take bakin ta yaƙi rufuwa fitowa suka yi yayi sallama da driver suka shiga reception tararbar sa suka yi cikin mutuntawa da yake sun san sa fuskar sa ba boyayyiyar fuska bace sosai NAJLAH tayi mamaki yadda suke mutunta shi.
Checking din kayan su aka yi sannan suka fara ƙoƙarin fita daga gurin domin hawa jirgi lokaci yayi tamkar daga sama yaji SAN juyowa yayi EMAN ce.
tana sanye da wasu arnan riga da wando kurawa NAJLAH idanuwa tayi ta saka wani katon glasses ganin sa ta cire shi kan'ta ba dan kwali sai taunar chingum take ga wani namiji a kusa da ita da alama tare suke kallon ta yayi yace '' eman ya karatu..
murmushi tayi tace '' alhamdulilah ina wuni ya aiki ..,
alhamdulilah ya hidimar biki Jawad yace yana mamakin EMAN shifa
shi ya saka tun farko ya tsani alakar su da Jawaher amma na tuna na mai ba haka ba , ba wanda zai kalli EMAN yayi mata kallon Musulma murmushi tayi tace '' alhamdulilah su Jawaher suna can sun amshe mu ni kuma ina nan ina nana abubuwan ne ya hadar mana da yawa wallahi yanzu ma daga lagos nake akwai oder kayan da muka yo to acan ta sauka...
okay Allah ya temaka
Amin tace tana murmushi in kiya tayi wa TJ da ido kauda kai yayi yana miƙawa JAWAD hannu gaisawa suke ya tambaye shi ya aiki TJ yace '' Alhamdulillah.,
masha Allah EMAN tace '' amma wannan sister ka ce kuna kama wallahi..,
dauke kai Najlah tayi tana jin tsanar eman a ranta yawa ba musulma ba JAWAD yace '' eh ..,
sallama yayi musu ya riƙe hannun NAJLAH suka hau jirgi eman kuwa tace '' kut amma Jawaher bata da hankali wallahi TJ kalli yarinyar nan ka gani iya mace ta cika ta tafi gantali ka barta a cikin gidan ta tasan mijin ta ba dutsai bane Allah ya saka na kura bace da fatar akuya suka ajiye mata a cikin gidan ta daga ganin wannan yarinyar yar iska ce kana ga ko kallon inda muke ba tayi ba..,
taɓe baki yayi yace '' me ruwan ki da ita Insha'Allahu sai ya karo mata aure dan kuttumar uban ta badai ni za taci amana ba , yau auren su yayi shekara biyu koma sama da biyu amma da yake ita shegiya ce bata san mahimmanci riƙe alkawari ba ai gashi nan ta rashe gindi ta zauna ita da tace min ba zama taje yi ba ki faɗa min auren nan na Jawaher da me ya amfanar dani..?,
Wallahi kana da matsala TJ baka da hakuri ko kaɗan yanzu wanne irin abu ne bana yi maka kaman ta da ita muci gaba da rayuwar mu...
kedin da kike hannu biyu wallahi ki guji ranar da Ubangiji zai kama ki ke fa nifa wallahi kyankyamin ki nake yi yasin
wani kallo tayi mai ba shiri ta tofar da chingum din da yake bakin ta tace '' amma dai kai anyi dan akuya wallahi ni ban ce maka ina kyankyamin ka ba sai ni zaka faɗa min haka good yayi kyau ai na gama buɗe baka kaci ba dare ba rana yanzu kuma ni zaka fadawa
End Ads