x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - KARUWAN CIKIN GIDA hausa novel by oum yesmeen

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 77751 words

Category: Tale Stories

Views 326

18 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
haka idan kana kyankyamina uban wa yace maka kazo kayi...,
buɗe rigar'sa yayi ya zaro yar karamar wuka yace '' billahilazi ki iya bakin ki ko yanzu lahira tayi baƙuwa dan uwar ki har ni zan dinga magana kina saka baki kin dinga kaza kaza ne ke ga shegiya kina daure mata gindi tana tafiya yawon bariki ku ci gaba da abin da kuke inhar kere yana yawo zabo ma na yawo kar ku canza halin ku shegu yan kutumar uba ni zaki dinga danne wa baki san wani irin abu ne ya cakar min zuciya ba da kika ce sai kin mai magana saboda kin mai dani wanda be san ciwon kan'sa ba da har zan hana ki, kiyi mai magana kice sai kin yi...,
tafiya ta fara tabar shi yana ta faɗa, da alama yau ya shata tafi ƙarfin kan'sa.
******** YOLA
suna sauka mota ta zo daga gida ta ɗauke su NAJLAH bakin ta , tamkar me tallan makilin sai washe shi take.
suna sauka da sauri ta tashi zata buɗe murfin mota rike hannun ta yayi yace '' uwar rawar kai..,
a hankali ta zare hannun'ta daga nasa fitowa tayi tana murmushi dai-dai shugowar motar nihilah parking tayi ta fito wani irin harbawa zuciyar ta , tayi ganin Jawad abin so da kaunar ta wallahi jawaher ko za tayi hauka sai ta aure shi ajiyar zuciya ta sauke ta ƙaraso kusa da shi tace '' ya Jawad sannu da zuwa...,
ba tare da ya kalle ta ba yace '' yauwa ya aiki..,
Alhamdulilah tace tana ƙoƙarin danne hawayen ta ganin hankalin'sa gaba ki ɗaya yana kan Najlah yana miko mata wayar ta da jakar ta amsa Najlah tayi tana cewa aunty nihilah ina wuni..
bata ce komai ba ta juya ta fara tafiya cikin isa tana karkaɗa key din motar ta.........

Free pages ya kusan karewa domin shiga paid group ku hanzarta biya ki karanta cikin kwanciyar hankali....
Wannan littafin na kudi ne duk meson 1k amina alhasan Muhammad 8141785374 opay
KU TURO DA SHEDA TA WANNAN NUMBER 08141785374.
Yan niger 1000fcfah AMINA MUHAMMAD ALHASAN KANO
My nita sai kuyi screen shot Ku turo ta wannan number 08141785374
Ina sanar muku akwai complete document na dukka littafin nan
1:.JIKAR MAMMAN COMPLETE DOCUMENT 1K
2:.HAUWA KULU WOMEN LEADER COMPLETE DOCUMENT 500
3:.DESTINY LOVE 400
4:.BINTA YAR JAGALIYA COMPLETE DOCUMENT 300
5:.YAR HANNU A LAGOS 1K
6:.GIDAN MAGAJIYA Complete document 1k
7:.UWAR GAFALALLU COMPLETE DOCUMENT 1K
8:.BAƘIN SHAFI 1K COMPLETE DOCUMENT
9:.YAN ZAMAN MAKKAH 1K COMPLETE DOCUMENT
10:.MU ZUBA MU GANI COMPLETE DOCUMENT 200
11:. KIN CUCE NI 300
Dan Allah idan kinsan ba siya za kiyi ba karki yimin magana duk maganar da za kiyi idan ba receipt evidence na gani ba bazan amsa ba dan Allah mu kiyaye
Number iya WhatsApp take yi 08141785374 ban da kira
KARUWAN CIKIN GIDA
OUMYASMEEN


ga channel dina kuyi min subscribe Dan Allah wai ina masoyana suke.

https://www.youtube.com/@nasreenminallah

https://vm.tiktok.com/ZSBRtRQmN/


EPISODE ¹³

JAWAD kallon NAJLAH yayi ganin ta haɗe rai ya danyi murmushi rufe motar yayi da sauri ya riko hannunta ganin ta fara ƙoƙarin tafiya yace '' ina zaki..?,
turo ƙaramin bakinta tayi tace '' gurin hajiya ta..,
sai mun fara zuwa gurin jadda.
tamkar zata yi kuka tace '' to..,
domin ranta ne so ba babban burin'ta
ta ganta a kusa da hajiyar ta.
tamkar ance kalli sama hango yaya saif tayi a baranda ya sarke hannu wansa a kirjin'sa riga ce armless a jikin sa maroon colour da wando three-quarter milk colour murmushi yayi mata tare da ɗago mata hannu.
kallon JAWAD tayi tace '' ya jawad kalli ya saif daman yana ƙasar nan...?,
kallon inda take nuna mai yayi sai kuma ya dauke kan'sa tare da jan hannun ta bata da zaɓi da ya wuce ta bishi.
tamkar wasu mata da miji sabon aure ba ƙaramin kyau sukai ba yadda ya rike hannun ta batare da ya cika ta ba suke tafiya cikin nutsuwa da izza.
turus Hajiya Sameeerah tayi tana kallon su ta kasa danne mamakin ta da sauri ta juya ta shiga part dinta,
tana shiga cikin parlour kan sofa ta dura tamkar an jifota cikin ɗaga murya tace '' NIHILAH NIHILAH NIHILAH,
da sauri NIHILAH ta fito daga ita sai towel tace '' aunty ina cikin toilet fa kike kirana lafiya naga ranki a ɓace..?,
dauko min ruwa NIHILAH maza dauko min ruwa..
da sauro ta ƙarasa saukowa ta buɗe fridge ta dauko mata ruwa me sanyi har ya fara kankara.
shayewa tayi tas ta ajiye robar tace '' wai kuwa kin san JAWAD ya shigo garin nan ashe yarinyar nan a gurin sa take...?,
zama NIHILAH tayi tace '' wallahi aunty na gansu har gaisawa mu kayi ashe daman tana gidan sa abin nan ya ban mamaki wallahi to me jadda yake nufi ne kinsan fa shegen tsohon nan wallahi shirun sa ba alkairi bane ba... kaf dangin nan wa yake bari ya tafi wani gurin yayi karatu...,
cikin mamaki HAJIYA SAMEEERAH tace '' karatu kuma..,
sauka tayi daga kan hannun kujera tace '' aunty karatu mana nasan da karatu za su fake su gina wani rami ke wallahi wannan makarkashiya ce akwai manufar yin haka...,
hannunta ta daga ta tafa tace '' tabbas haka ne, hmmm amma idan sun san wata ai basu san wata ba kinsan wannan rawar kafar da farida take yi take kafafa ita ta raine shi ba mamaki yanzu haka so take ta bashi wannan yarinyar ta gaban ta , tunda ba wanta a gaban ta..,
kuttumar durin uwar nan lallai da anyi gagarumin bala'i cikin ƊAN BUZU lokacin da zai auri Jawaher kowa yasan ina son sa amma da yake waccan m kafar katafilar tazo aka ce abata damar ta yanzu kuwa wallahi dole nice zan aure shi kuma daga ni ba ƙari aunty....
ta gumi Hajiya Sameeerah tayi ta lula duniyar tunani mafita kawai take nema amma ko wacce hanya tabi a rufe ruf ba kofa ko ɗaya.
********
bangaren JAWAD kuwa suna shiga babbar parlour jadda bakin su ɗauke da sallama ambassador Mukhtar HASHIM BUZU ya ɗago da kan'sa da yake ƙasa ya kalli kofa lokacin Jawad ya sako kafar sa four eyes suka yi tabbas buri yayi kama da mutum dole ya ga Saif a cikin gidan nan ba mamaki tare suke da shi Lokaci ɗaya zuciyar sa ta harsaso mai wannan maganar saurin kawar da ita yayi jadda da yake kishingiɗe da sauri ya tashi zaune fara'ar fuskar'sa da annurinta sun ƙara daduwa cikin tsantsar farin ciki yace '' zo nan jikata welcome when did the beautiful queen arrive ...?
karasowa tayi kusa dashi ta zauna tace '' jadda barka da lokaci..,
jan kumatun ta yayi yace '' barka dai ja'ira duk kin bi kin cinya wa Jawad abinci gashi nan kamar ana wura miki iska..,
murmushi tayi tace '' kai jadda ni nafi son zaman nan..,
murmushi yayi ya kalli Jawad da ya tsaya a tsaye tamkar an dasa shi yace '' kai kuma aikin soja ka koma bani da labari..? ka wani tsaya kamar ka ha ɗiyi sanda aṭṭas, as-ikka, illa gesegh..,
ya ƙarshe maganar cikin yaren Tamashek (wato yaren buzaye..)
Najlah cewa tayi daddy barka da wannan lokaci.
Murmushi yayi yace '' barka dai ya karatun..?,
wasa ta fara da yan yatsunta tace '' bamu fara ba..,
tashi yayi yana cewa to Allah ya saka ku fara a Sa'a..
amin tace
kallon jadda yayi yace '' jadda ka huta lafiya..,
kai kurum jadda ya gyaɗa mai kai ya tsare JAWAD da har yanzu ya kasa zama sai a lokacin JAWAD yace '' JADDA asi, ha-nna yan umidag iyyan. Ul iyyi ad awid, ad yokh, ghas ayit. Meyaɣ!"
dariya JADDA yayi yace '' ni na isa na yi maka yan ubanci Najlah tare ta gan mu zo ka zauna a kusa dani ina zan kai wannan fushin haka..,
dariya yayi ya ƙara so sun kusan gware da ambassador Mukhtar dan Allah ya rufa asiri JAWAD ya ba shi hanya.
zama yayi Najlah tashi tayi tace '' jadda ka huta lafiya ni zan tafi gurin hajiya ta..
bazan amsa ki ba wato kin zama bahaushiya ko....? kin manta da asalin ki tun ɗazu ina yi miki Magana kina bani amsa da harshen Hausa.
murmushi tayi tace Insha'Allahu zan gyara..,
uhmmm kin koma ga cuku nan ko kin manta dashi ne..?
kai ta girgiza ta dauke shi a cikin akushi me kama da bowl chokali ɗaya tayi ta limshe idon'ta tace '' masha Allah yayi dai-dai yasha zuma jadda...anni ce tayi ko...?,
murmushi yayi yace '' ke idan ba ita ba wa kike ganin zai iya wannan duk kun ruga da kun bar al'adar mu daga shawarma sai pizza kuka iya ci shi yasaka ga kunan kuke saurin tsofa idan kunji ana abinci ka maganin ka to abincin gargajiya ake nufi ba dangin fulawa ba kayan basir..,
dariya tayi tace '' jadda kenan Allah ya bar mu dakai..,
limshe idon sa yayi ya cire farin glasses ɗin sa yace '' hmmm najlah shekarun da nayi a baya bazan taɓa yin su a yanzu ba kullum girma da ɗa cinmun yake ina ƙara kusanta ga Ubangiji sai dai fatan dacewa da rahamar Ubangiji kullum dai addu'ar da nake yi Allah ya nuna min karshen warware war komai duk kan wani bara gurbi ya zama tarihi bakin shuni ya ɓace da ta dawo yanzu..,
Uhmmm jadda na tafi bazan iya da wannan zancen naka ba , wannan tsoho kaji hausa ga yadda kake shigar da hausa cikin hausa kamata yayi shashin hausa na jami'ar Bayero ya baka award.
dariya yayi yace '' ja'ira ina ne ban zaga ba tun da nayi suna a kano ai kuma zance ya ƙare duniya ta san da zamana magana ake fa ta babban dan kasuwar haƙo ma'adanan ƙasa..,
fita tayi tana cewa ni dai na tafiya jadda idan na biye maka sai mu kwana kana ban labari bayan baka zauna a kano ba sai ka kwaso jiki ka dawo Yola..
Kaniyar ki Najlah da ban dawo yola ba ai sharif na zai ga farida ba yace yana so ga inda muka fi kusancin yare dasu ina ni ina zama cikin hausa zalla duk da fa kanawa mutane ne ba garin da zaka je ka zauna ba a damu da rayuwar ka ba ko da kuwa kai ka , kawo kudi duniya sama da kano ta dabo....
hannu ta ɗaga mai tace '' na tafi kayi da yaya..,
murmushi yayi mata ya mai da hankalinsa kan jawad yace '' Jawad abin da kayi ka kyauta kenan...?,
kallon mamaki yake wa jadda nashi yana tunanin me yayi cikin danne mamakin sa yace '' jadda me ya faru...?,
ungo nan ya yi mai dakuwa.
gyara zama yayi yace '' jadda na tawo da takardun nan fa..,
yayi maganar da nufin kaucewa maganar da jadda yake son yayi mai.
a'a barsu a gurin ka ni nan ba abin da za su yi min.
cewar jadda.
JAWAD yace '' to shikkenan zan cigaba da ajiye su,
uhmm yayi haka ya iyalin naka da fatan dai kowa lafiya qalau...?
ajiyar zuciya ya sauke yace '' kowa lafiya qalau...,
badai wata matsala ya ajiya ta..
ɗago kan'sa yayi yace '' jadda kana ji da wannan ajiyar taka..,
dan murmushi yayi yace '' tabbas ina ji da ita idan lokaci yayi na sanin amfanin ta zaka sani duk da kai ma nasan zaka fahimci hikimar yin haka..,
jadda matsala fa..
dafa kafaɗar sa yayi yace '' a'a muna neman tsari da ita Jawad ka zama namijin mazaje mana kamar yadda kirar jikin ka ta nuna to zuciyar ka ta nuna haka ka dena saurin karaya da sauri baka da rauni akan abubuwa amma akan wannan maganar kana da saurin nuna raunin ka wacce aka ta ya kamata ace ka tsaya ka zama gwarzo...,

ganin suna wannan zancen cikin zancen na kwaso yan matan kafafuwana nace ba dani ba gaɗa a lahira to ba abin da nake fahimta. nace ke oumyasmeen gwara kiyi gaba ko kya samo wani labarin..

***********

NAJLAH kuwa tana shiga part din su ta ajiye bowl dinta akan center table saboda motsin Hajiya da tayi a kitchen saɗaɗawa tayi ta shiga ta rufe mata idon ta Hajiya murmushi tayi tace '' Najlah cika min idona bana son sangarta sai kace wata ƙaramar yarinya..,
cika ta tayi cikin shagwaɓa ta turo bakin ta , tace '' ban tsoratar dake ba ...?,
ban sani ba ke kin isa ki tsoratar dani
kai Hajiya ban da cika baki..
Uhmm sai kiyi ta faɗa tana kashe gas tare da mai da murfin tukunya.
Hajiya ta me kike dafa mana...? Ko baki san da zuwan mu ba yaya be faɗa muku ba ...?
cewar Najlah..
Hajiya tace '' to yar jarida ban sani ba zo ki bar nan gurin,
fita tayi tana dariya zama tayi akan kujera ba jimawa Hajiya ta fito kallon bowl din hannun ta tayi tana ajiye flask akan dining tace '' a'a ina kika samu cuku...?,
jadda ta bata amsa tana ci gaba da sha..
ƙara sowa tayi ta zauna tana ƙare mata kallo gaban ta na faɗuwa ganin kallon da take mata tace '' Hajiya da gaske ne kema kinga kibar da jadda yake cewa nayi...? ni dai nasan ba wata kiba nayi ba , saboda ban da zama cikin fargaba ba abin da nake bana son zama a gidan yaya wallahi..,
haɗe rai tayi tace '' ai sai ki cire hijabin da jakar tunda ba wani zai daukar miki ba..,
murmushi tayi ta cire Hajiya tace '' jiki kitchen ki ƙarasa dauko min kayan abinci ki kai dining ..
tashi tayi tana ajiye bowl din hannun ta da kallo Hajiya tabi kugunta da shi ajiyar zuciya ta saki me nauyi wani irin sanyi ne ya ratsa ta ganin abin da take zargi ba shi bane ba..
bayan ya gama kai wa ta dawo ta zauna tana cewa Hajiya miyar nan da kifi sadin kika yita ko..?
kallon ta tayi tace '' eh me ya faru..,
wallahi zuciya'ta tashi take yi, kifin badai karni ba..
gaban Hajiya ne ya fadi tace '' ke duk irin kayan kamshin da na saka anya kuwa lafiyar ki qalau Najlah...?,
dariya tayi tace '' kai hajiya wallahi lafiya qalau nake, ni dai bazan ci ba Allah ya saka jadda ya ban cuku..,
ta gumi tayi tana sauke ajiyar zuciya kullum zuciyar ta cikin zulimi take bata da iko da tuni ta dakatar da komai duk da abin da suka yi shi ne dai-dai suna da ikon yin komai..
Hajiya Hajiya firgigit ta ɗago ta kalli NAJLAH tace '' na'am..,
Hajiya tunanin me kike ne ina ta kiran ki baki amsa ba
Wayan cewa tayi tace '' ba dole nayi miki shiru ba kece idan kika fara kiran mutum tamkar makauniya..,
dariya tayi tace '' ina abbana yake...,
yana cikina, na boye shi aikin san yanzu lokacin dawowar sa ne..
Hajiya ta faɗa tana jefawa Najlah harara.
tashi Najlah tayi tace '' wallahi nayi missing dakina hajiya ina key yake na buɗe..,
ke zo..,
zuwa tayi ta zauna a ƙasa tana kallon hajiya, dauke kai Hajiya tayi tace '' me ya faru kika dawo..?,
Hajiya bani kaɗai bace ni da yaya ne dan Allah hajiya ki saka baki kar na koma gidan yaya wallahi bana son zama..
hade rai tayi tace "' shi ya saka kika bar kayan ki ko..? to da su zaki koma ko dan kwali ban yarda kin bar min ba a cikin gidan nan ba.."
kuka ta saka ta kwantar da kan'ta a kafar Hajiya shafa bayan ta , tayi tace '' Najlah me ya saka bakya son zaman can naga dai yaron nan ba dukan ki yake ba balle zagi amma duk kin ɗaga hankalin ki sai kin dawo nan..,
cikin shashsheƙa tace '' wallahi bana son zama yaya ya fiye faɗa matar sa yar hulakanci ce ..,
murmushi tayi tace '' kina yin rashin ji ko..? najlah me son ka ne fa zai faɗa maka gaskiya ita kuma matar sa , yau da gobe zata hakura har ku saba da ita..,
share hawaye tayi tace '' Hajiya aunty Hafsah bata faɗa miki ba..?,
ɗago haɓarta tayi tace '' a'a me ya faru..,
hawaye ne ya ƙara zubo mata daga cikin idanuwan'ta tace '' kirjina ke min ciwo..,
subbanallah me ya faru kin faɗawa Jawad ..
na faɗa mai amma yace na ɗinga addu'a..
ajiyar zuciya ta sauke saboda sam bata kawo komai a ranta ba ta zata ciwon kirji ne wanda ta sani tace '' ya faɗa miki gaskiya domin addu'a ita ce gaba da komai..,
kwantar da kan'ta tayi tana jan ajiyar zuciya...
TAUFIQ ne ya shigo da sauri ta tashi tare da rungumshe shi cikin farin ciki ashe ba shi kadai bane tare yake da JAWAD dakyar ya iya ɗaga kafar sa ya shigo da ita cikin parlour durkusawa yayi yace '' Hajiya ina wuni na same ku lafiya..,
Cikin farin ciki da sakin fuska tace '' lafiya qalau alhamdulilah ya iyalin naka..?,
tashi Jawad yayi ya zauna a kasan carpet yace '' lafiya qalau alhamdulilah...,
Masha Allah ko ba tare da ita kuka zo ba..? Wannan yarinyar ta zo ta tisa ni gaba da kuka..
murmushi yayi yace '' a'a ba tare muke ba nazo wani aiki ne shine na tace ba zata iya zama ita kaɗai ba sai ta biyo ni..,
harararta Hajiya tayi tace '' ke dai najlah naga ranar da zaki girma to cika shi kin wani makale mai..,
murmushi tayi ta fara tafiya TAUFIQ zama yayi a ƙasa kusa dashi ta zauna Hajiya tace '' Allah ya temaka jawad sai hakuri halin najlah kana ta yi da baki ko..?,
a wannan karon kallon najlah yayi sai kuma ya kalli Hajiya yace '' wata ran zata dena ne Insha'Allahu..,
hmmm Allah ya saka......
Amin ya Allah cewar Jawad
Hajiya kallon najlah tayi tace '' kawo mai abinci...,
tashi tayi ta shiga dining room ta zuba mai dai-dai wanda tasan zai iya ci ta kawo mai shiga kitchen tayi , ta dauko mai lemo da ruwa ta kawo mai tashi hajiya tayi TAUFIQ ma tashi yayi yana cewa yaya sai an jima ai kana nan ko..?
Insha'Allahu ina nan sai gobe zan fita.
to shikkenan ka huta lafiya ya faɗa yana fita najlah gama ajiye mai tayi zata , tafi ya riko hannun ta da sauri ta kalle sa idanuwanta har sun fara tara kwallah.
kama kunnen ta yayi yace '' bakya ji ko..? yanzu mene ba wani rungume taufiq..?
cikin rawar murya tace '' na dena
End Ads