nan ba sai ki haɗa min a ciki.. right..?,
to tace dafa ta yayi suka soma tafiya tace '' wallahi yaya kamar zan faɗi nauyi ne dakai..,
bece mata komai ba har suka karasa toilet zama yayi ta haɗa mai komai ta juyo tace "shikkenan abin da kake bukata ina so naje nayi sallah..?,"
cikin yanayin rashin lafiya yace '' idan kin idar ki dawo..,
to tace mai ta fita lokacin har an tafi raka'ah ta biyu da sauri ta tada sallah bayan ta idar ko zaman yin addu'a ba tayi ba ta fito dakin sa ta koma samin da tayi a zaune da a'lama sallar ma a zaune yayi ta , tausayi ya bata tace '' yaya ko likita za a kirawo..?,
ɗagowa yayi ya kalle ta yace '' a'a insha'Allahu zan sami lafiya basai kin kirawo likita ba ko ya zo ba abin da zai iya yi min..,
da sauri tace '' yaya consultant doctor fa...?,
wallahi najlah ba abin da zai iya yi min
to shikkenan yanzu wane zai iya yi maka sai a kiro shi.
JAWAD yace '' kinga mubar maganar nan dauko min kayana a wardrobe..,
anan dakin..?
ta tambaya.
Eh anan dakin yace mata yana kallon ta.
tashi tayi ta buɗe wardrobe harta ɓangaren boxers dabam ne sosai tsarin wardrobe din ya burgeta kallon sa tayi tace '' yaya ma su nauyi zan dauko maka ko mara sa nauyi..?,
marasa nauyi domin yanzu zafi nake ji..
najlah tace '' na kunna maka A.c..?,
riƙe hannun'ta yayi yace '' a'a jeki dai ki dauko min kayana..,
to tace ta koma dauko mai wasu riga da wando tayi mara nauyi rigar ma bata da hannu ta miƙo mai, kallon ta yayi yace '' ina boxer...?,
da sauri ta kalle sa tab wallahi ba zata iya daukowa ba ja da baya tayi tace '' baga wannan ba ka saka mana..,
kallon milk trouser din da ta dauko mai yayi yace '' to idan ma saka wannan ban saka boxer ba mene amfanin sa..baki ga kafar saba me girma ce kuma bashi da tsayi idan nayi wawan zama fa..?,
rufe fuskar'ta tayi da tafukan hannayen ta , tace '' kai yaya da girman ka to ni ban gansa ba ko na kirowa aunty JAWAHEER ya dauko maka..,
kinga kawai kice baza ki dauko ma nasan da ita nace ki, dauko min yau gaba ki daya ma duk wani aikin ta ke za kiyi har zuwa gobe sai jibi zata amsa aikin ta.
turo baki tayi tace ''ni bance maka haka ba shi ne zaka faɗi haka..,
NAJLAH na gama magana fa...
kauda kai tayi ta dauko mai ta ajiye mai tace '' me zaka ci...?,
JAWAD yace ''fried yam da egg sauce..,
Juice fa ta fada tana kokarin fita daga dakin..
JAWAD yace '' zo ki zauna a nan karki yi yanzu sai an jima..,
zama tayi dan nesa dashi ƙoƙarin cire riga ya fara da sauri ta juya mai baya ya kalle kofa.
murmushi yayi tashi yayi ya saka kayan sa sannan ya juyo da ita yace '' na gama..,
a hankali ta saka hannun ta , ta ture hannayen sa da yake kan ƙafar'ta tace '' har yanzu baka fadamin ba...,
kiyi duk abin da ki kai niya..
tashi tayi tana cewa to dakin ta , ta koma tayi wanka sannan ta zauna tana azkar karfe bakwai dai-dai ta tashi ta shiga kitchen cikin sauri take komai domin bata sani ba ko zai iya karfin halin tafiya aiki.
strawberry and banana smoothie tayi mai ta saka a fridge karfe bakwai da minti arba'in ta gama komai daukowa tray tayi ta jera mai sannan ta fito cin karo tayi da Jawaher tana taku daddai koda ta ganta bata karasa saukowa daga stair case ba sai ta tsaya tana jifan ta da wani irin mugun kallo.
dauke kai tayi ta wuce dakin Jawad da sauri ta biyo ta har tuntube take yi wato shi ya saka Jawad yace ya gaji da cin abincin yan aiki duk dalilin zuwan wannan bakar dagar aikuwa yau zata yi maganin su najlah ajiye tray tayi yace '' nagode Allah yayi miki albarka..,
amin tace tamkar an wurgo jawaher haka ta shigo tana haki tace '' Jawad ban gane me kake nufi da haka ba , mun fara sharing din kane kai da najlah wato shi ya saka kace baka son abincin yan su rose ko...?,
da sauri najlah ta kalle ta ta juyo ta kalle Jawad wanda ya nuna bema son me take fadi ba cikin ɗaga murya tace '' to ke kuma yar kanzagi shishshigi ba farin jini ba zaki burge ni ba sai yau kin aure Jawad..haka dai zaki kare..,
da sauri ta ƙara kallon Jawad yana jiran taji me zai ce amma shiru najlah tace '' matsamin na wuce..,
Idan naki fa..?
ta faɗa cikin fada domin wani irin kishin Jawad ne yake taso mata.
najlah ja da baya tayi tace '' ni bazan kulla ki ba ko na yarda muyi fada domin bansan wanne irin kashi ne dake ba haka kurum na kwaso tsiya Sannan ni ba karya bace da ko da yaushe za a jini ina wan wan man your business.,
wani irin daskarewa tayi ko da wasa bata , taɓa tunanin jin wannan amsar a bakin najlah ba lallai yarinyar nan ta raina ta kallon jawad tayi tace '' kana jin me tace ko..?,
Sai a lokacin jawad ya ɗago ya kalle ta yace '' me tace..?,
haba wa jawaher ji tayi kamar ta shake shi kuka ta fashe dashi ta fita daukan waya tayi ta lalubo number UMMEE har ta katsai bata dauka ba kara kira tayi sai a lokacin UMMEE ta dauka tana cewa ke lafiya kike min kiran mafarauta da safiyar nan bafa nason rashin hankali da barikanci me ya faru...
yadda kuka san jawaher ta dannawa UMMEE ashar amma sai ta danne cikin muryar kuka tace '' wallahi UMMEE tun da yarinyar nan tazo gidan nan muke samun sabani da jawad baya gani na da gashi yadda kika san matar sa komai ita , take mai yau kuma har ce min tayi karya jiya marina yayi akan ta wallahi ummee nagaji aure ba hauka bane tafiya gidan mu zanyi idan yaso ita , ta maye mai gurbina..
Kuttumar ubancan to ga hanya nan tafi akwai wanda ya rike ki, kin manta ranar da na kira ki , kika ji daukan waya da yake a lokacin kina cikin kwanciyar hankali ga UMMEE yar iya daukan dukkan wani tension bara ki faɗa min ko to ke da ita sai naci takazar uban ku ke , wallahi ki kiyaye ni kinfi kowa sanin wace ni kallon ke kawai nake naga iya ina film din bake zai kare a wacce chapter ne ita kuwa shegiya ta samu guri ko bara ta sheka ayar ta lafiya qalau jinin farida zai zo waje batare da ya hargitsa gurin ba farida bakar annoba ce fa na tsane ta , wallahi na tsani duk wani tsatson ta shima so yake ransa ya ɓaci shi ya saka har yanzu be mai da mata da annobar ta gida ba wallahi ku bini a sannu ko ayi yakin duniya na uku a *DAN BUZU* ita kan'ta innar kallon ta kawai nake dan haka wannen ke ta shafa jawad ko yanka naman jikin yake ba abin da zai dame ni duk wanda ya iya allon sa ya wanke ya sha idan kuwa kika nemi raba ni da , ɗana wallahi sai kin bar gidan nan..,
UMMEE ɗa ko dan rana ta fada a zuciyar'ta amma afili sai tace '' ummee wallahi ba haka ba ne akwai abin da nake shiryawa ne takarda biyu ce ta rage min ban gama haɗa miki komai ba sai mu tafi plan na gama kiyi hakuri.. yanzu ma zan turo miki wasu kudade..,
UMMEE wani sanyi taji tace '' oh to maza turo min su ita kuma zanci uban'ta wallahi...farida kamar mayya ta kasa rabuwa da duk wanda ya shafe ni..tasani sarai bana kaunar ta , bana kaunar duk wani me kaunar ta amma da yake mayya ce taki rabuwa da ɗana..,
jawaher tace '' bashi take so ba kudin hannunsa take so...,
zanyi maganin ta kuwa sai an jima, ta faɗa tana kashe wayar wani sanyi ne ya ratsa jawaher ta fita tana yar waka.
cikin daki kuwa najlah fita za tayi jawad yace '' ina zaki..?,
yaya zuwa zanyi nayi breakfast...,
zauna muci tare wannan yayi min yawa kina so nayi nauyi da yawa ko..? kizo kina nayi nauyi na tsofa.
kallon sa tayi ta gefen ido tana cewa to ka riga da kayi dan kaci wannan ba abin da zai ƙara maka kuma kai kace nayi maka shi.
hmmm haka ne amma kinsan kayan kiba ne ko me makon ki ban shawara kar nace to nadai ƙara tsofa kece a ciki ni ba ruwana..
ni kuma ko aunty jawaher.
ta faɗa tana nuna kan'ta..
dafa kan'sa yayi yace "' ashe mugunta kika shirya..,"
zama tayi a ƙasa tace '' uhmm uhmm kai fa kace nayi maka yanzu kuma kazo kana challenging dina to dena ci na hado maka salad kace sai ka rame sannan kayi exercise shikkenan...,
hannun'ta ya riƙe yace '' a'a barshi nagode daga magana sai kuka..,
ƙoƙarin kwace hannun'ta tayi amma sai ya hanata haka ya riƙe hannun'ta gam bin hannun'ta tayi da kallo tace '' yaya zaka karya min hannu tun dazu kake riƙe min hannu...,
ina jin daɗin rikewar ne idan na riƙe sai naji zazzaɓin da nake ji ya ragu ko bakya so na samu lafiya ne.
kallon sa tayi tace '' to ka sassauta min rikon nan kuma ka dena shafa min fatar hannu bana jin dad'i wani iri nake ji kamar shocking..,
da sauri ya kalle ta yace " da gaske..?,
Allah yaya to nima cika ni na ci abincin.
cika ta yayi tare suka soma ci ba wanda ya kara cewa kowa komai dakin ya dauki shiru zare hannun ta , tayi tace '' na ƙoshi..,
kin koshi kuma guda nawa kika ci..?,
ya faɗa yana haɗe ran sa tamkar bashi ne ɗazu yake wannan maganar ba.
walllahi na koshi bara naje na wanko hannu na shikkenan ai ba abin da zan maka ko zan koma daki na.
okay wanko ki dawo , kin manta dazu me nace miki..
turo baki tayi ta , tashi ta wanko hannun ta, ta dawo sosai take jin bacci kwantar da kan'ta tayi a kan kujera jawad yace '' bacci kike ji..?,
kai ta daga mai yace '' okay kwashe kayan nan ki zo ki kwanta a kan gado..,
to tace mai ta , tashi domin jikin ta duk yayi la'asar bata san dalili ba dauke kayan tayi ta kai kitchen ta dawo kwanciya tayi akan gadon tana limshe idon'ta wani irin bacci ke fusgarta.
lokaci guda bacci ya dauke ta jawad tashi yayi ya wanko hannun sa ya dawo fita yayi daga dakin gaba ki ɗaya ya hau sama takardu ya dauko da laptop yana cije lips din'sa ji yake kamar ciwon na ƙaruwa saukowa yayi ya tarar da su rose yace '' ba abin da za ku girka yau..,
gaishe da suka soma yi amsawa yayi yana barin gurin.
to suka ce suka bar gurin tare da rofe kofar parlour.
ajiyewa yayi ya soma aikin sa yayi lokaci zuwa lokaci yana juyowa ya kalle najlah da take baccin ta cikin kwanciyar hankali.
tunowa yayi bata sha maganin ta ba tashi yayi ya tafi daki ya dauko mata tare da dauko mata ruwa wata kwaya ya jefa a cikin ruwan lokaci ɗaya ta narke batare da ta canza kalar ruwan ba.
ajiye wa yayi ya soma tashi ta , tashi tayi tana turo baki tace '' idan na tashi zan sha yanzu kaina zai fara ciwo wallahi..,
haɗe rai yayi yace "zaki sha ko sai ranki ya ɓaci...,"
ɓallo mata yayi ya bata amsa tayi ta sha tare da ƙara kwanciya yace '' najlah ki tashi ki zauna ya ɗan faɗa miki sai ki kwanta..,
yaya bacci wallahi nake ji.
to shikkenan ya fada yana janyo laptop din'sa.
wannan kenan.
*DEEYA NAILAH EMAN* mafita nake nema ko kalli P test din nan result din da ya bayar ciki ne fa dani..
Hmmmm wallahi kin ban mamaki ke daman akan wannan kika tara mu ni wallahi na zata wata maganar ce kina hana da aure ba baki da shi ba mene abin damuwa..
cewar deeeya.
wani kallo tayi mata tace '' bafa na Jawad ba ne..,
idan ba nashi bane sai me aure ai ya bashi Na'ilah ta faɗa tana danna wayar ta.
EMAN tace '' calm down jawaher wannan fa cikin Ubangiji ne ya baki kuma yayi haka ne domin karki tashi a tutar babu randa Jawad ya mutu tofa idan ba tumulin taka ba , ba ba abin da zaki samu, kuma kinsan yana gab da mutuwa ko da ace be shaki poison din da aka saka mai ba gubar da kike bashi kullum tana fa aiki a jikin sa , sannan kinsan dai komai nisan jifa kasa zai dawo idan asirin ki ya tono ko dan wannan yaron wallahi zai kalle yaron nan ya kasa komai bangaren UMMEE bata da komai domin a lokacin zaki nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane ki buda komai ki juya komai ya koma kan'ta ke ce barazana tayi miki, wallahi JAWAHEER wayon ki na banza ne yasin kwata kwata baki da wayo ko kaɗan sannan mu kuma yan bada shawara sai asan yadda za a yi damu bayan komai ya lafa sai ki dawo kan TJ kici uban sa dole yayi wa dan da wahala kinga da wannan cikin baƙaramin alkairi zaki samu ba wallahi..,
DEEYA tace '' wallahi EMAN bansan kina fa ƙwaƙwalwa haka ba sai yau idan kuwa dukkan wannan plan din ya tafi dai-dai ni ma kashe nawa auren zan yi tas wallahi na aika shi barzahu naci dukiya ga ta gurina ga ta gurin jawaher wallahi zaman kasar nan nafi karfin sa..,
Na'ilah tace '' to wani hanzari ba gudu ba wannan abin duk yayi daidai amma bana goyan bayan kisa haba zunubin ina zaku kai shi muma fa sai mun samu namu kason wallahi....,
jawaher tace '' gaskiya ina tausayin Jawad wallahi yana kaunar yara idan na kawo mai dan shege cikin gidan sa ban kyau ta..,
dallacan rufewa Mutane baki ashe daman baki da hankali to wallahi idan kikai mana bakin cikin shiga daular nan, yasin sai na fasa kwai kalli motar da nake hawa jiya na samu wani dan rainin hankalin saboda yana kallo na talaka zai neme ni ta baya zai bani miliyan hamsin..miliyan hamsin din taci abu takazar uban ta haka nace masa na duddura masa ashar yanzu haka wani bokan ne zai ce yayi haka zai samu kujerar dan majalisar tarayya da yake nema..,
cewar EMAN.
Na'ilah tace '' lallai eman to ai yanzu abin da ake kenan biya mun bukata na baki abin duniya kin zama two SIM kenan to su karima jos abin da suke kenan wallahi...kike ganin su suke baki sha'awa nima dan dai bana son na haɗa DAZ da kowa ne amma da wallahi kudi zan samu..,
kash amma gaskiya Na'ilah baki da hankali ko kaɗan sarai nasan abin da suke aikatawa kenan wata ran fa sai an dinga sakawa mutum pampas saboda mutum zama yake uncontrol
Cewar jawaher.
DEEYA tace '' kunga wannan duk matsalar ku ce ga wannan babban issues da muke tattaunawa ki bar cikin nan muga abin da Allah zai yi..,
wallahi bazan bari ba sai dai duk abin da za kuyo baku da hankali idan fa na mutu nazo haihuwa nace wa Ubangiji me...? idan yaron ya taso ya girma yasan gaskiya da wanne ido zan kalle sa haba gaskiya kun ban mamaki wallahi wato ku biyan buƙatar ku, kawai kuke dubawa..
tashi DEEYA tayi tace '' kan bala'i lallai JAWAHEER aikuwa idan kin ki ji ba zaki ƙi gani ba wato daman kin zo ki lasa mana zuma a baki ne ko duk kudin Jawad mi tashi a banza a wofi tumunin takaba kaɗai za a baki insha'Allahu wannan cikin namiji ne ni daman kullum addu'a nake Ubangiji ya azurta ki da samun ciki irin wannan gida ne ake sakar jiki a haihu domin gobe..
NAILAH tace '' DEEYA waya san gawar fari ban da Ubangiji...?,
kinga bana son tsohon wa'azin ki, ki zauna kiyi wa kanki idan kika dawo dai-dai sannan sai kizo ki yi min gwara ni ina zaman gidan miji ke zaman gidan mahaifinki ma ,ya gagare ki zama dan haka baki isa ba ko faɗa min dabarun zaman duniya magana ake ta kudade ma kuɗai mazaje..
sosai ran Na'ilah ya ɓaci wato daman zaman gidan mahaifi daraja ne dashi koda kuwa ke karuwa ce kina cikin sutturar ki ta kalli eman mana ta fadawa haka , ita da iyayen ta karatu suka turo ta basu san me take aikatawa ba idan zata koma gida ko mota bata zuwa da ita waya kuwa tun wayar da mahaifinta ya siya mata alokacin da za'a kawo ta makaranta, bata siyar da ita ba cire kayi kan ta , take ta ɗora ta komar musu da ita su gani..tace...
'' amma deeya kin ban mamaki har idon ki ya rufe ki faɗa min haka...?,
EMAN tace '' Please be kamata dan mun samu banbancin ra'ayi ba kuzo kuna fadawa junan ku magana kamar ba classis ladies ba kalle mu, mu hudu abin sha'awa ko wa zancen mu yake bamu taɓa samun sabani ba muna zaune tsakani da junan mu tsakani da Allah....,
zama suka yi dukkan nu daman jawaher ita a zaune take ta zuba ta gumi, tana cikin tsaka me wuya bata san ya za tayi ba gashi suna barazanar tona mata asiri tayi sake da suka san sirrin ta amma bakomai idab sun san wata basu san wata ba dukkan nin su tana da video su tace '' *DEEYA NAILAH EMAN* lallai idan kuka ce zaku tona min asiri to fa zamu tonawa juna asiri kun saka rigar karya, kun fake da business kun mai da da dalin tiktok wajen sheka ayar ku, wajen kawalci mayan mutane su ganku suyi muku DM ko kuma su bawa wani yayi muku magana ya haɗa ku da su dan haka yadda ake ganin ku da mutunci wallahi sai na tona muku asiri....za ayi yar tone tone a tiktok ko wacce update dinta zai baza duniya kowa ya gani ni za kuyi wa barazana...,
da sauri ko wacce ta kalli yar uwar ta deeya ta cire dankwali taja ɗamara tace ''miko wayar