x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - KARUWAN CIKIN GIDA hausa novel by oum yesmeen

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 77751 words

Category: Tale Stories

Views 322

18 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Jawad ya iya kiwo kin ƙara girma..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' aunty Hafsah wallahi bana jin daɗin zama a cikin gidan nan nafi son zama a cikin gidan nan idan ba nan ba to gidan ya Aliyu shi bashi da takurar yaya kuma gidan sa ba aljanu wallahi aunty kirjin ciwo yake min kuma har fa shatin fingers na gani a jiki..,
ta ƙarshe maganar tana share hawayen ta.
kamo hannunta tayi ta zaunar da ita tace '' kiyi hakuri kinji ko wanne bawa akwai irin tashi jarabawar idan kika saka hakuri da juriya sai komai ya zo miki da sauki wannan damuwar ba abin da za tayi miki sai ma ta ƙara jefa ki a cikin mtsala ƙarshe ki hadu da wani ciwon bayan wanda kike dashi..,
wasa take yi da yan yatsunta tace '' insha'Allahu zan dena..,
yauwa kanwata kina abin da kuwa nace miki kiyi ..?,
da sauri ta dago idon ta da suka fara canza launi zuwa ja tace '' mene na manta wallahi..,
cikin mamaki tace '' kin manta fa kika ce min zancen shan fruit..,
zan dinga sha wata kila ma shi ya saka be dena zuwar min ba ..
cikin jin dadi aunty tace '' ko ke fa yanzu na ƙara karɓar miki wasu a gurin kawata fanna yar barno..,
ta faɗa tana buɗe wata jaka bama ta lura akwai jakar ba sai yanzu, zuba mata ido tayi tana kallon ta har ta gama fito da su tace '' wannan tsugunawa za kiyi akan sa..,
amsa tayi tana budewa wani kamshi me ya daki hancin ta me dad'i tace '' aunty ai wannan turare ne ...?,
ehmn shi akan sa zaki dinga tsugunawa na miyagu ne
cewar aunty Hafsah.
najlah tace '' ikon Allah daman haka turaren miyagu yake me kamshi a dakina zan dinga turarawa wallahi har kayana..,
karɓa aunty Hafsah tayi tana hada rai tace '' najlah ba na wannan bane ga abin da nace kiyi dashi ki wara kafarki sosai hayakin ya shiga ko ina na gaban ki..,
karba tayi tace '' to..,
dauko wani abu tayi me kamar zuma tace '' ungo shi kuma wannan sha zaki dinga yi..,
da sauri ta buɗe ta saka hannu ta lakara sha tayi tace "da dadi kamar dabino..ko?,"
uhmm shine. ta faɗa tana dauko wani magani a cikin wata kwalba tace "shi kuma wannan rabin chokali zaki dinga diba kina saka zuma da madara ta ruwa kina sha, safe da yamma..,yana da karfi karki diba da yawa"
to najlah tace mata tunda dai ba masu daci bane ba , to ai bata da damuwa dasu a rana ɗaya ma sai ta shanye su tas, tamkar aunty Hafsah tasan me take rayawa tace '' wallahi ina me ja miki kunne duk randa kika kuskura kika shanye su tas sai kin faɗawa mutanen garin ku, ballanta yadda kike ke kaɗai ba wani matayi a kusa dake , hmmmm sai an kai ki gadon asibiti wallahi...,
saboda da me aunty cewar Najlah..
Aunty Hafsah tace '' baki ji me nace miki ba yana da karfi shi a ka'ida ma amfiso asha lokacin da za'a kwanta amma ke dan ya ratsa ki tace ki sha sau biyu..,
amma aunty Hafsah maganin mene shi..?
ajiye wanda ta dauko tayi tace '' zaki tsaya tambaya ko zaki barni na gama yi miki bayani wannan abin da kika ce yana damun ki naga number ta a wani group na mace me daraja naga kuma ana ta yaba aikin maganin ta shine nayi mata magana tun daga barno ta turo min dasu wallahi najlah wa'yannan da kike gani na kashe kudi sosai duk dan na siya miki mutunci saboda ko kana da kyau ka ƙara da wanka..,
Najlah da ta kasa fahimtar zancen aunty Hafsah tace '' mutunci kuma aunty ba cewa kikai maganin miyagu bane to aini da mutunci na da wa kika taɓa ganin munyi faɗa balle har mutunci na ya zube a idon mutane...,
tab aiki game kare ka sai yanzu ta kara tabbatar da zancen Hajiya akwai matsala babba ajiyar zuciya ta sauke ta dauko wani tana cewa ungo wannan sarke zaki dinga yi dashi aina san ke bakya fada shi wannan da kike gani ²in¹ ne ba abin da baya magani..
to ta faɗa tana kwanciya akan gado.
mai da su jaka tayi tana cewa kin gane ko..?,
uhmm nagane Nagode
Hajiya ce ta shigo kallon jakar tayi tace '' Hafsah zo..,
tashi tayi tana bin bayan'ta NAJLAH kau da kai tayi da alama maganar sirri za suyi tace kwayi ku gama ba inda zan koma nasan dai ba zai wuci tace tayi min faɗa ba akan nadena cewa bana son zama a gidan yaya.
ta fada tana canza guri.
Hajiya kuwa basu tsaya a ko ina ba sai a dakin ta , ta kalle hafsa tace '' me ya saka kikai haka kinsan fa bana son wannan abu Hafsah..,
zama tayi cikin kwantar da murya tace '' kiyi hakuri bamu isa mu da katar da wannan kaddarar ba illa mubi ta da addu'a wallahi tun da kika ga kare na shinshina takalmi dauka zai yi ni banga aibun abin nan ba maganar mutane kike tsoro akwai hujja da dama to me ne abin damuwa Hajiya addu'a ce kawai taki yadda ba mutum ɗaya bace kina ganin abar abin nan haka ai akwai matsala dole a gyara ko ina....,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' Hafsah ba zaki fahimci abin da nake son ki gane ba wallahi inhar ta sani sai abin nan ya rushe wa gari ya waya daman mutane za a raba su da fadar abin da sukai niya ne..?,
hmmmm da wannan dan wannan amma da yinsa fa rashin sa ba zai canza mata suna ba , bama ma fatan haka Allah ya kawo mafita ya ganar fa ita gaskiya..
cewar aunty Hafsah.
Hajiya tace '' amin ya Allah addu'a ce magani sai mu ci gaba da fadawa Allah kukan mu Allah ya sani bawai shi nake ƙi ba halin ta nake gudu kar daga gyara azo kuma a ballo wani sabon ciwon kinga anyi ba ai ba kenan...

Wannan littafin na kudi ne duk meson 1k amina alhasan Muhammad 8141785374 opay
KU TURO DA SHEDA TA WANNAN NUMBER 08141785374.
Yan niger 1000fcfah AMINA MUHAMMAD ALHASAN KANO
My nita sai kuyi screen shot Ku turo ta wannan number 08141785374
na kusan buɗe paid group me kike jira ne Hajiya ta..?
Ina sanar muku akwai complete document na dukka littafin nan
1:.JIKAR MAMMAN COMPLETE DOCUMENT 1K
2:.HAUWA KULU WOMEN LEADER COMPLETE DOCUMENT 500
3:.DESTINY LOVE 400
4:.BINTA YAR JAGALIYA COMPLETE DOCUMENT 300
5:.YAR HANNU A LAGOS 1K
6:.GIDAN MAGAJIYA Complete document 1k
7:.UWAR GAFALALLU COMPLETE DOCUMENT 1K
8:.BAƘIN SHAFI 1K COMPLETE DOCUMENT
9:.YAN ZAMAN MAKKAH 1K COMPLETE DOCUMENT
10:.MU ZUBA MU GANI COMPLETE DOCUMENT 200
11:. KIN CUCE NI 300
Dan Allah idan kinsan ba siya za kiyi ba karki yimin magana duk maganar da za kiyi idan ba receipt evidence na gani ba bazan amsa ba dan Allah mu kiyaye
Number iya WhatsApp take yi 08141785374 ban da kira

KARUWAN CIKIN GIDA


Ga channel dina kuyi min subscribe Dan Allah wai ina masoya na suke.

https://www.youtube.com/@nasreenminallah

https://vm.tiktok.com/ZSBRtRQmN/
Domin samun update kuyi following dina

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

Book ¹

EPISODE ¹⁵

Shiru aunty Hafsah tayi tana tunani can tace '' amin ya Allah..,
Hajiya tashi tayi ta fita jin sallamar Abba haka ma aunty Hafsah da kallo ya bisu yana cewa kaga uwa da yar'ta me kuke tattaunawa wa haka..
aunty Hafsah ɗurƙusawa tayi tace '' Abba sannu da dawowa..,
yauwa Allah yayi muku albarka ke da yan uwanki.
amin tace tana tashi zaune ta zauna a kan carpet Hajiya kuwa tace '' kasan damuwa ta bata wuce wannan maganar ba..,
dan murmushi yayi yace '' insha'Allahu ba zamu taɓa nadama ba ki dena damuwa..,
Allah ya yarda ta fada tana shiga kitchen buɗe fridge tayi ta dauko ruwa me sanyi sannan ta bude kitchen cabinet ta dauko glass cup ta fito buɗe mai tayi ta zuba mai tare da ajiye ragowar a kan Center table.
dai-dai lokacin najlah ta fito washe baki tayi tamkar me tallan ma-clean tace '' abba sannu da dawowa..,
ajiye kofin hannun sa yayi yana wara mata hannu yace '' daughter saukar yaushe..?,
da gudu ta tawo ta rungumshe shi cikin farin ciki tace '' dazu muku zo..,
ta faɗa tana zama a kusa da shi, tashi aunty Hafsah tayi tace '' hajiya sai da safen ku..,
Hajiya tace '' ba zaki ci abinci ba zaki tafi haka sa wuri..,
murmushi tayi tace '' ban tawo ba sai da naci abinci..,
najlah da sauri tace '' muje naga twins..nasan irfan yafi Arif girma ko..?,
ehmn sun girma dukkan su ba wanda yafi wani girma.
tashi tayi tace '' abba na tafi..,
okay sai kin dawo.
bin bayan aunty Hafsah tayi tun da suka fara tafiya ba wanda yace wa da yayiwa wani magana har suka shiga shashin ta najlah ita ce sahun gaba ta shiga bata rai tayi ganin ya jawad da yaya mutallab suna hira irfan a hannun sa yana mai wasa durkusawa tayi tace '' ya mutallab ina wuni..,
ɗagowa yayi yana cewa autar Hajiya ba zaki gyara halin ki ba , kin shigo tamkar an jefo ba sallama..
turo ƙaramin bakin ta tayi tana cewa zan gyara Insha'Allahu kayi hakuri..
ya mutallab yace '' hakuri hakuri yar lukuta..,
aunty Hafsah dariya tayi tace '' abin har da cin mutunci..,
mutallab yace "' mommy twins karya akai mata ne ga ta nan kamar bukka..,"
ba ƙaramin shaƙa najlah tayi ba idanuwanta har ya fara kawo kwallah tashi tayi ta hau kan kujera tace '' bani irfan..,
kallon ta yayi yace '' wannan arif ne irfan yana hannun Jawad..,
ikon Allah wallahi na zata shi ne to yaron ne gaba ki ɗaya kamar su ɗaya aunty hafsa kema kina gane su..?,
zama tayi tana cewa me zai hana na gane su..
jawad da tun da najlah ta shigo bece komai ba tamkar ma baya gurin sai operating wayar sa yake yi irfan ya zubawa screen din wayar sa ido yawa me fahimtar wani abu kallon sa aunty hafsa tayi tace '' jawad ba magana laifin me nayi..?,
ɗago sexy eyes din sa ya kalle ta yace '' bakomai na same mu lafiya..?,
uhmm yau sarautar ce ta motsa bara na saya kaina...anya kuwa Jawad a haka zan baka gaskiya da sake
murmushi yayi yace '' to ai ba tilas nayi muku ba hanya a buɗe take..,
dariya tayi tace '' kamar gaske da kuwa ranar ka kasa bacci..,
hmmm kawai yace yana ci gaba da operating wayar sa...
mutallab yace '' sai kace ba namiji ba kike faɗa mai wannan maganar...,
jawad yace '' yawa fada mata dai..,
aunty Hafsah tace "' akwai ranar kamu ne zan dawo muku da wannan maganar wallahi....,"
a'a riƙe abar ki basi kin dawo mana da ita ba ko Jawad....?
Jawad yace '' uhmm ani na ma rasa bakin magana sai kace wata kayan gabas..,
dariya tayi tace '' wallahi zan kama kune...,
najlah ta karbi arif da yake hannun mutallab ta shiga daki ganin ita ba gane zancen nasu take ba suna magana a juye
aunty Hafsah itama bin ta tayi tana shiga ta zauna Najlah kallon ta tayi tace '' wallahi aunty Hafsah kina da abin haushi ba sai ki kyale shi ba ya gama isar sa idan yayi niya yayi miki magana kinga sai wani wura hanci yake da wani hancin sa yawa butorami..,
dariya sosai aunty Hafsah tayi tace '' wallahi kamar ki ɗaya yadda kika san kaki yayi kema kenan haka hancin ki yake..?,
shafa hannun'ta tayi tace '' habawa ai hancina me kyau ne kina ganin sa yawa biro dai-dai misali ya samu irin hancina da wallahi ya caɓa.,
me ya saka bakya ganin kyawun jawad..?
aunty hafsa ta cillo mata wannan tambayar.
da sauri najlah ta ɗago ta kalle ta , tace '' bakin halin sa kinga komin kyawun mutum inhar yana da bakin hali mummuna ne kinga wallahi yaya MUNEEF ya fishi kyau kaf gidan nan fa shi a ka tarawa muni..,
zaro ido auntu Hafsah tayi tace '' uhmm akwai ranar da zan tuno miki wannan maganar idan kika ce idan ba Jawad ba sai rijiya..,
kai aunty ina neman tsari wannan idan ba matar sa ba wazai iya dashi ki dena ma yi min wannan zancen.
na dena ta faɗa tana karbar arif da yake neman abinci zaro mamanta tayi ta soma bashi najlah zuba musu ido tayi tana tunani to wai aunty Hafsah bata jin zafi ne ko me ko ita dan dai ba yaro bane ko kuma na aljanu ne yafi zafi..kauda kan'ta tayi tana cewa aunty Dan Allah ki bawa su abba hakuri kar su mai dani gidan yaya wallahi bana son zama.
zuba mata ido tayi tace '' najlah ki kwantar da hankalin ki, Jawad ba zai taɓa cutar dake ba..,
uhmm najlah tace tana kwanciya kiranta jawad yayi shiru tayi mai har sai da ya kira ta sau uku tashi tayi tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki ta fita dan nesa dashi ta zauna tace '' yaya gani..,
ki zama cikin shiru gobe idan na dawo da wuri zan mana booking ki cikin dare ne mu isa gida, na gama duk wani abu da zanyi sauran meeting shi ya zaunar dani da ace bashi da gobe da wuri za mu tafi..
ya mutallab ta kalla tuni idon ta ya kawo kwallah tace '' bafa inda naje ko gurin su basma banje ba balle gidan aunty rafi'at ta dawo hutu..dan Allah ya mutallab ka bashi hakuri shi ya tafi zuwa wani satin Allah zan dawo da kai na ai nasan hanya ko kuma sai na yiwa isa driver magana ya kai ni..,
ya mutallab dariya ce ta kubbuce mai Allah me iko wannan dreamer ta jawad da najlah besan lokacin da zata ƙare ba yawa masu ganin hanjin junan su najlah bata kaunar ganin ta kusa da jawad ko kaɗan yace '' a'a auta kunfi kusa tare ba ganku..,
najlah tana jin wannan magana ta saka kuka da sauri aunty hafsa ta fito tace '' Najlah lafiya kike kuka..?,
shiru tayi mata tamkar magana take yi da dutsai kallon Jawad tayi tace '' Jawad me ya faru dukan ta kayi...?,
tashi yayi yana zura wayar sa a aljihu yace '' kar Allah ya saka na dawo baki shirya ba kiga yadda zanyi dake a cikin gidan nan..,
tuni aunty Hafsah ta dauki haske dariya tayi ta , ta zauna tace '' kiyi hakuri kinji goben ki shirya duk inda zaki sai ki je kafin ya dawo ku tafi. ,
banza tayi mata taci gaba da kukan ta sai da tayi me isar ta , sannan ta tashi ba sallama ta bar shashin nata ji tayi an bangaje ta da sauri ta juyo nihilah ce daukan hannu tayi da zummar zata zabgawa najlah mari ya saif ya riƙe hannun ta yace '' ban da bangaje ta da kika yi har zaki dauki hannu ki mare ta me tayi miki ai ita ya kamata ta mare ki ba ke ki mare ta ba..,
saif ka cika min hannu na ina ruwan ka dani baka ga take min kafata yi ba tana tafiya tamkar wata ballagaza..,
dan murmushi yayi yace '' ko makaho ya shafa ya san najlah ba ballagaza bace tun da bata nufin kowa da sharri ko tana bin mazan banza..,
Wannan maganar da saif yayi mata baƙaramin ciwo tayi mata a raina cikin mamaki tace '' saif ni kake jifa da irin wannan kalaman..?,
ko baki jiba na ƙara mai maita miki..?
ya faɗa yana sakin hannun ta.
NAJLAH bata ce komai ba tabar gurin duk abin da yake faruwa akan idon jawada ne da yake tsaye a baranda hannun sa rike da magazine yana dubawa.
ganin najlah tabar gurin ya zauna akan kujera yana ɗora kafa ɗaya kan ɗaya wayar sace tayi ringing da sauri ya dauka ganin me kiran ƙarawa yayi a kunne yana cewa ummi barka da yamma..
ina ka tafi kai da najlah.
ko amsa gaisuwar sa ba tayi ba taje fo mai wannan tambayar da ta saka hanjin cikin sa kaɗawa.
cikin dakiya yace '' najlah kuma ummi waya faɗa miki wannan zancen..,
jawad kar ka mai dani ban san me nake ba tambayar ka nayi ina kuka tafi bance ka mai dawa farida yar ta ba, wallahi jawad idan na ji wata magana yasin zan iya tsine maka.
kan'sa ne yayi wani irin sarawa bakin sa na rawa yace '' ummi tsinuwa kuma..?,
da kyau tunda kaji abin da na fada maka ta faɗa tana kashe wayar ta.
bin wayar yayi da kallo ya dafa kan'sa besan ya zai ba yana cikin tsaka me wuya sai dai fatan da yake Ubangiji ya fidda fashi ummi uwa ce a gare shi haka hajiya ko wacce da irin nata matsayin.
besan me ya saka ummi ta tsani Hajiya ba duk da alkairin da tayi mai kamata yayi ta so ta ta kaunaci jinin ta.

*******ABUJA. OSOKORO..

Jawaher bata tashi ba sai bayan sallar isha lokacin abin da ta sha ya sake ta daukan wayar ta , tayi da sauri ta dafa kan'ta da yake juya mata kiran ummi ne sai kiran jawad su kaɗai ta gani sai wata bakuwar number...
ajiye wayar tayi tana cewa wannan jarababbiyar matar idan ban gama yi mata aikin ta ba , baza kyale ni na shaki iska ba ke mece makomar ki wata zuciyar ta jefo mata wannan tambayar lokaci guda.
gumi ne ya fara tsassafo mata ta dafa kanta a fili tace '' anyi kitso da kwarkwata tab wallahi akwai saki aini banyi wannan tunanin ba shikkenan na tashi a *ZERO* dole a sake saban lale.
tashi tayi tana dafa bango ta fita kai tsaye kitchen ta nufa tana zuwa ta buɗe fridge kamar wasa abin da take nema bata gansa ba gaban tane ya fada a fili ta furta na shiga uku kar dai ya gani da sauri ta shiga fito da komai na cikin fridge din sai da ta gama tas amma bata ga komai ba zare ido ta fara tana riƙe da kugu ko shugaban ma'aikatan gidan zata kirawo to amma ai ta bawa ma'aikatan part din ta hutu su saran da ba a kasan ta suke ba basu da hurumin shigowa part din ta tana cikin wannan tunani ne sunan Najlah ya fado mata a rai.
ranta ne yayi mugun ɓaci tasan nawa ta saka ta siya da zata dauke mata ita wata kila ma ta faɗa mai ko da yake
End Ads