x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - KARUWAN CIKIN GIDA hausa novel by oum yesmeen

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 77751 words

Category: Tale Stories

Views 336

18 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tabo mata inda yake mata kaikayi tace '' yama dawo ɗazu abin da ya sakani dad'i ma tare suka dawo da Najlah za tayi karatu anan..,
da sauri ta tashi hadiman da suke mata tausa a kafa sai da suka tsorata saboda tashin da tayi na baza ta da kuma hanzarin ta tamkar ta ga wani abin ƙi cikin tantance zancen jawaher tace '' wacce NAJLAH..? yaushe JAWAD ya dawo ƙasar nan ban sani ba kuma be sanar dani ba..?,
murmushin jin dad'i tayi tace '' Najlah Hajiya Farida ɗazu ya dawo be dade da dawowa ba ina ga sai ya nutsu zai kira ki ya sanar da ke...,
cikin tsananin ɓacin rai tace '' yanzu haka tana cikin gidan ki lallai yaro be san wuta ba sai ya taka , da zaki ce kina ga sai ya nutsu wannan wanne irin kinibibi ne tafiya yayi fa YOLA daga dawowar sa ina JALINGO be sanar dani ba balle ya zo Nagode da sanar da ni da ki kayi sai an jima...,
kit ta kashe wayar ta wani tsalle dad'i jawaher tayi tare da rawa wannan game din tasan ita ce za tayo winner wata kila zuwa gobe ta yardar da kwallon mangaro ta huta da guɗa ummin JAWAD lafiya ce.
Wannan boom ɗin tasan gaba ki ɗaya ahalin alkali mudassir ɗan muzu da su zai tashi sai ummi ta ya mutsa hazo zama tayi tana cewa duk mutumin da zai hanani kwanciyar hankali a gidan miji na to tabbas ina da boom me tashin rayuwar mutum gayawa jini na wuce.
wata dariya ce ta zo mata , ta mugunta lokacin da taga NAJLAH da plate ta fito daga kitchen uhmm babu a house ta faɗi da dan karfi domin NAJLAH ta ji ta.
sarai ta ji furucin ta sai dai bama ta nuna tasan me take faɗi ba.
wuce ta tayi ta koma dakin ta.

WANNAN KENAN

JALINGO TARABA STATE.

Sai zaga ye tamkeken parlour take wanda ya cika da kayan alatu na jin daɗin rayuwa tun da sukai wannan maganar da jawaher take buga number JAWAD amma a bata shiga.
Altab ne ya shigi daga shi sai riga armless sai wando three-quarter ga wata uwar sarka a wuyan sa kai kace jikan bambaline shi cikin sauri yace '' ummi lafiya naga kina ɗawafi...,
Altab ba dole kaga ina ɗawafi ba Wallahi lamarin dagin mahaifin Jawad ya ishe ni dole muyi fito na fito da su haba wannan wacce irin jaraba ce su barmin ɗana ba ruwan su dashi.
zama yayi yace '' ummi kenan Allah ya kyauta amma dai lokacin da kika tafi kikai fushin zuciya wa ya rike miki shi ni wallahi duk irin wa'yannan abubuwan dama zaki gane ki dena saka kanki a ciki..,
ji tayi tamkar ya zuba mata wuta a fusa tace '' lallai altab sai yau na kara tabbatarwa shaye shayen da kake yi ya ta ɓa maka kwakwalwar ka fice ka bani guri wanda baya kishin kan'sa..,
tashi yayi yana sosa sumar kansa da ta sha gyara yace '' kudin hannu na sun ƙare me zan samu ne...,
Ubanka za ka samu altab, wallahi nagaji nagaji ka nemi sana'a ka fara yi kudina bana shalholiya bane bana tara matan banza bane idan ka yi zuciya ka tafi ka nema a, duk wani abu da kake yi a guest house ina sane dakai wallahi ka guji ranar da zan faɗawa jawad.
altab yace '' to shikkenan kar Allah ya saka ki bayar wallahi ba zaki ƙi gani ba tun da haka kika ce zan ɗin gima miki babban aiki na bar ƙasar badai kin fara tsanata ba dan ina faɗa miki gaskiya da kuma munafukai da suke wure miki kunne any way dake da su za ku gani yasin daga nan zuwa karshen shekarar nan kowa zai ga abin da zai faru da shi..,
EPISODE 2
Dan Allah altab karka fasa abin da kayi niya me ka mai dani banki ko me kullum kace na baka kuɗi to wallahi zan kirawo JAWAD ya zo ya raba ni dakai da me zan ji..
be ce mata ƙala ba ya wuce yana cewa za dai ki gani har su munafukan naki..
Dafa kan'ta tayi tace '' altab ni kake faɗawa haka..,
fita yayi yana sakar fito zama tayi tamkar wacce ruwan sama ya jiƙa ta bata san yadda za tayi da altab ba yana neman ya gagare ta , da sauri ta tashi cikin sauri ta sau stair case shiga bedroom din ta , tayi da sauri ta bude wata loka wani key ta dauko ta ma yar ta rufe fitowa a hankali take saukowa saboda jin alamun kamar akwai baki a ƙasa aikuwa ilai Hajiya rukayya ce haɗe rai tayi ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya akan kilishi tace '' Hajiya rukayya nasan tun jiya sakona ya isa kunne ki amma me yasaka sai ya zu kika zo..?,
Wani murmushi Hajiya rukayya tayi tace
"It's only now that I got the time"
Ummi hannunta ta ɗun kule waje ɗaya tace '' okay yayi kyau zaki iya tafiya na riga da na gama so yanzu bani da bukatar ki, daman kwaɗayi ya kawo ku kowa ya san kuɗa gurin kwaɗayi yake mutuwa..,
What ni kike faɗawa haka...? ya cutar min da yarinyar ki dinga faɗa min haka lallai ma Hajiya bilki good yayi kyau tun da haka kika ce kuje ku ɗa Allah dakin ya kusan kashe min ya' ki dinga faɗa min haka..
da sauri ummi ta ɗago tace '' to kima godewa Allah da be nakasa ta ba in banda iskanci duk wani abu ai tayi shi a waje ta shigo da yan iska cikin gidan sa ta tunda tunanin ba zai iya yi mata komai ba saboda gata yar gwal suna mai shaye shaye wannan wacce irin rayuwa ce..,
dariya Hajiya rukayya tayi tace '' da yar tawa da ɗan naki ai dan jumane da yar jummai sittin ce take dukan saba'in..,
wani kallo tayi mata tace '' dan haka dole ya je ya samo yar mutunci ya aura...,
wata uwar buɗa Hajiya rukayya ta saki tace '' wallahi karya kike baki isa ki canza ayar Allah ba Ubangiji ne yace Az-zāninī laa yankihu illā zāniyatan aw mushrikatan, waz-zāniyatu laa yankihuhā illā zānin aw mushrik; wa hurrima dhālika 'alal-mu’minīn wallahi, you're lying The relationship between Altab and Samha hasn't even started. No one has the right to enter this house,,
Haka kika ce ga hanya nan zo maza ki barmin gida na tun kafin na ci miki mutunci...
Cewar ummi
tashi Hajiya rukayya tayi tace '' au cin mutuncin na nawa kuma ɗan haka ina me sheda miki tun da sheɗanin dan ki ya lalata min ya' to wallahi zama yanzu suka fara shi, duk ba shi ya cutar min da yar tawa ba mene be koya mata ba , itama rashin jin ta ga samari nan nawa suka fito suka ce za su aure ta daman dole zaman su ya zamo da zargi saboda an riga tun a waje an lalata zamantakewa ba ta yadda za ayi a cikin gida ta ginu wallahi ko yawo kike yi a kan dutsai tsirara altab be isa ya saki samha ba shi da ita mutu karaba talmin kaza da kike cewa son abin duniya mu kayi ke da ba kya so ki zubar dashi a ƙasa ban da rainin da kukai mana kuna ganin mu talakawa ne , amma har kya budi baki, ki faɗa min haka kamar yadda kike son ɗakin haka nake son ya'ta in ban da rainin hankali har mu zaki kalla kice son abin duniya ya rufe mana ido Hajiya bilki kin manta amintar da take tsakanin mu kin rufa idon ki, kin ci min mutunci bayan kice kika zo kina lallaɓani akan auren nan shima haka to wallahi ba ku isa ku mai damin yata ba bazzawara..,
cije lips din tayi ji take tamkar ta shaƙe ta har Hajiya rukayya ta fita bata ce komai ba ji tayi kamar tayi cille da wayar ta da sauri ta dauki key da mukullin da ɗazu ta fito da shi ta fita daga cikin part din ta cikin sauri take komai har ta isa part din altab shiga gate ɗin farko tayi sannan ta bi ta wata kofa nan ne ta shiga ainin farfajiyar gidan ga motar altab a ajiye a parking space kai ta gyaɗa da alama yana cikin gidan,
tura kofar parlour sa tayi jin kiɗa na tashi tamkar a shahararren club din america..
jirine ya kusan kwasar ta dafe kan'ta tayi da yake juya mata a gurin ta sulale a ƙasa numfashin ta na kaiwa yana kawowa da sauri ya ƙaraso gurin ta.
ɗago mai hannu tayi tace '' basai ka taɓani ba zan iya tashi...,
dafa bango tayi dakyar tana tafiya limshe danuwanta, tayi da suka cika da kwalla bata so ta zubarwa da altab hawaye domin hawayen ta masifa ne a rayuwar'sa biyota yayi tace '' wallahi tun kafin ranka ya ɓaci ka kawshe matan da kakawo cikin gidan nan ban da iskanci da wulakanci gidan auren ka zaka kawo mata kuna shaye shaye..,
to shikkenan ummi zan kwashe su amma bazan je na tawo da matata..
da sauri ta juyo jin zancen da ya furta anya kuwa kan'sa ƙalau lallai, ɗazu ma da ta mara mai baya dan dai Hajiya rukayya ta nuna mata rashin mutunci ne amma ko dukan da yayi wa samha bata ji dad'i ba duk da itama da laifin ta idan mace za tayi aure komai barin sa take yi a waje ta shigo gidan mijin ta da kyakkyawar niya amma ita bata san wannan ba ta dinga tara matan banza kuma bata kunyar wani ya gani suna shaye shaye ajiyar zuciya ta sauke tace '' ga hanya nan tafi wallahi yan uwanta sun shirya tsaf kana zuwa zasu kama ka haka kurum ka kama yar mutane ka naɗa mata duka ita , duk abin da ake aikatawa me take maka..? wallahi ko da wasa kar na kara ji ka saka hannu ka daki yar mutane mace da kake gani daraja ne da ita..,
shiru yayi har ta gama zancen ta , ta fita da sauri hany ta biyo bayan sa tace '' Man what is happening..?,
shafa gefen fuskar'ta yayi yace '' no bakomai ke da su mufee ku tafi zan neme ku ko wacce ta turo account number din'ta..,
da sauri ta riƙe mai hannu tamkar za ta shiga jikin sa tana mai wani irin kallo tace '' amma didn't you say we would spend the night here today? How many of us are even here?,,
matsar da ita yayi daga jikin sa yace '' Please hany kuyi abin da nace kafin raina ya ɓaci idan kuka kika ce ba in da ki tafi wallahi sai na farfasa miki jiki da duka ba ku ga abin da take shirin faruwa ba oh da ba mahaifiyar ki bace shine ba abin da ya dame ki to duk iskancina ina son mahaifiyata bana so na rasa ta..,
bata ce komai ba ta juya ta bar gurin samin su mufee tayi suna zaune sun yi ɗare ɗare akan gadon sa suna busa shisha tace '' maman My man ta bashi umarni ya fitar damu daga cikin gidan nan ku taso mu tafi yace ko wacce ta turo mai account number din'ta...,
ransu be so ba suka tashi suka bar gidan bama suyi mai sallama ba..

*OSOKORO........*
*STUDY ROOM....*

tunda ya shiga yake aikin office da ya tarar mai kwana biyu da yake yayi busy ba ya ƙasar sai yanzu ya samu yake rage wa kan'sa ne ya dauki chaji gaba ki ɗaya wayoyinsa ya kashe su, yana bukatar hutu da kaɗaici domin yayi aikin sa ba kuskure..
ji yayi an yi knocking kofar sa yasan wace dafa goshin sa yayi yace '' abu ɗe yake..,
jin haka da sauri ta murɗa handle din ta shigo zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun da suke study room din tace '' ummi ce ta bugo duk layin ka a kashe yake ce maka..,
ajiyar zuciya ya sauke shi ya amshi wayar tare da karawa a kunne yace '' Assalamu alaiki ummi barka da yamma...,
JAWAD riƙe gaisuwar ka bana so bana so wallahi ai baka mai dani mutum ba wayancan Mutanen da na raba ka dasu sune mutane har ka iya zuwa yola baka zo gurina ba ina matsayin mahaifiyar ka , ka kyauta dole suyi min abin da suka ga dama su nuna min ban isa da kai ba sai su, suka isa dakai ban ce maka ba , na rabaka da duk ahalin ɗan buzu musamman ma Hajiya farida bani da wata wacce na tsana sama da ita dan haka kai gaggawar mai da mata da yar ta , wallahi wallahi wallahi JAWAD idan ka sake kayi abin da na ke zargi to bani ba kai ban da iskanci tun wuri ka rabu da ita mana to wallahi alkali mudassir ya taro abin da yafi karfin sa domin duk abin da yake faruwa ina sane wato za su fage da guzuma su harbi karsana ko to sunci karya bakai ba jinin Hajiya farida da Alhaji Sharif..,
kifa kansa yayi akan table rasa ina zai saka kan'sa yayi anya kuwa Mahaifiyarsa, tana tsoron Ubangijin'ta me wannan baiwar Allah tayi mata tun da ya taso be san dadin uwa ba , watan sa takwas ita da mahaifinsa suka rubu dan haka bata tafi dashi ba ta bar shi ba ruwanta ya mutu ko yayi rai sai bayan ya kammala digree dinsa na farko yana shirin tafiya egypt ƙaro karatu ta bayyana be rayu da ita ba , tun daga bayannara ta zuwa yanzu kullum cikin saka shi take a damuwa da farko da ta bayyana yaji dadi be taɓa zaton ba hajiya ce mahaifiyar sa ba suma haka su NAJLAH sai a lokacin suka san me yake faruwa ajiyar zuciya ya sauke yace '' ummi insha'Allahu zan kiyaye duk abin da kika shinfiɗa min wallahi bawai haka kurum naje yola ba a'a na can na sauka gobe nake so na zo mu gaisa..,
kashe wayar tayi saboda ai ta riga da ta isar da sakon'ta miƙa wa jawaher yayi,
amsa tayi tace '' amma sweet lafiya ko ba wani abu ne ya faru ba..?,
bece mata komai ba ya nuna mata hanyar fita sum sum ta fice tana danne dariyar ta ,
ci gaba yayi da aikin sa bayan ya gama ya tashi ya fito ba kowa a parlour kai tsaye bedroom din sa ya nufa tana kwance tana waya tana ganin sa ta katsai wayar tace '' badai la gama ba ? Amma kuwa idan haka ne kayi saurin gamawa...,
zama yayi bakin gado yace '' eh na gama kije kice NAJLAH ta haɗa min coffee..,
tashi tayi tana cewa to an gama oga kiss tayi mai a kumatu tace Allah ya bar min kai ya makantar da idon yan mata akan ka...,
dan murmushi yayi mata yace '' amin...,
da sauri ta dawo ta zauna riƙe hannun sa tayi tace '' idan har hasashena ya faɗa min gaskiya kamar akwai abin da yake damun ka amma kaki sanar min idan ma tafiyar ce baka so nayi sai na fasa shikkenan magana ta ƙare amma wannan haɗa ran ban saba da shi ba kullum na fiso mu ɗore cikin so da kaunar juna da fahimtar juna shekara biyu da auren mu bamu taɓa samin matsala ba kar yanzu akan tafiyar nan mu samu beb idan haka ne ni wallahi na hakura ma da nayi tunani ko wani abu ummi ta faɗa maka da na kuma ƙara wani tunanin sa naga ita uwa ce me son farin cikin ɗan ta ba za ta taɓa faɗa maka abin da zai saka lokaci kali lan ba ka shiga cikin damuwa , ina kyautata zaton nice sanadin komai,
saukowa tayi ƙasa ta damƙe hannuwansa idanuwan'ta ya taru da kwalla fal sakin hannuwansa tayi ta haɗe hannuwanta biyu alamar ban hakuri ta ci gaba da cewa.
Dan Allah ka yafe min mijina bana so ka kwana kana fushi da ni bana so na zama sillar bakin cikin ka , ka dawo daga tafiya kamata yayi na faran ta maka be kama ta na bakan ta maka ba...
Kwantar da kan'ta tayi yasha kan'ta yayi yayin da wani sanyi yake ratsa zuciyar'sa hakika annabi yayi gaskiya da yace idan namiji ya dace da mace ta gari to kamar ya samu rabin addini ne yana kaunar jawaher yana son ta fiye da son da yake wa kan'sa baya iya kallon ko wacce mace a matsayin mace , Hakika jawaher rabin jikin'sa ce.. cikin daddaɗan sauti yace '' wallahi baki yi min komai ba idan ma kwai na yafe miki sweet stress ne yayi min yawa ina bukatar hutu amma ni baki min komai ba jeki, ki faɗa mata , ta haɗa min kafin na fito daga wanka..
Hmmm ku biyoni dan jin wanne darasi wannan labarin ya kunsa
# KURUWAN CIKIN GIDA
EPISODE 3
Ɗago idanuwan'ta tayi cike tab da hawaye share mata yayi yace '' bana so na ganki cikin damuwa..,
Murmushi tayi ta tashi, ta karasa share hawayen ta , fita kai tsaye bedroom din NAJLAH ta shiga turawa tayi ba tare da tayi sallama ba , tana kwance wayar ta na hannun ta taɓe baki tayi ta kalle tace '' sweet yace ki haɗa mai coffee..,
ajiye wayar hannun ta , tayi bata ce mata komai ba ta miƙe ganin haka ita mata fita, tana shiga tarar dashi tayi ya shiga wanka zama tayi tana charting da wayar ta fitowa yayi yana tsane jikin sa batare da ya kalli inda take ba yace '' kin faɗa mata..?,
ajiye wayar ta , tayi tace '' na faɗa mata amma bata ce min komai ba bama ta kalli inda nake ba balle nasan taji me na faɗa..,
ajiye towel din hannun sa yayi ya fita a hankali yake saukowa cikin nutsuwa kamar ba sauri yake ba yana sauka kai tsaye bedroom din NAJLAH ya nufa murɗa handle din kofar yayi da sauri ta dago tare da ja da baya tun da take dashi a rayuwar'ta bata , taɓa ganin sa acikin makamancin wannan yanayi ba ko exercise zai yi da dogon
End Ads