An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KARUWAN CIKIN GIDA
OUMYASMEEN
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA ME JIN KAI.
ALLAH KA BANK IKON GAMA LITTAFIN NAN LAFIYA KAMAR YADDA NA FARA LAFIYA.
GARGAƊI
________________________________
BAN YADDA WANI KO WATA SUYI AMFANI DA ƊAYA DAGA CIKIN SHASHI NA WANNAN LITTAFI BA BATARE DA IZINI NA BA 08141785374.
Copy is not allowed 🚫
Bismillahir ramanir rahim
Episode 1
ABUJA OSOKORO..
Wata sassanyar iska ke kaɗawa yayin da bishiyu ke rangaji iskar nan a hankali take ratsa jikin ta na kasan cewar kayan jikin ta marasa nauyi ne miƙa tayi ta , tashi tsaye bata da tsayi sai dai Ubangiji yayi mata kira me kyau me daukar hankalin duk wanda ya kalle ta ɗan ƙaramin tsaki ta ja , ta dauki wayar ta da take neman dauki ta ƙara a kunne tace '' eman yau bana jin zan iya attending lecture so idan kinga da faraga ki min kawai attendance..,
saurarawa tayi domin jin me eman din za tace jan ƙaramin tsaki tayi tace '' ni wallahi na manta ma gwara ni da ku yanzu kina ina ne nake jin tashin kiɗa kar dai a club kika kwana...?,
dariya eman tayi tace '' no ba'a club na kwana ba ina mai tama ni da su jee a satin nan nake so na koma gida saboda Islam tace momy ba lafiya so ina so naje naga ya jikin ta yake amma kafin nan ina so na yi solving wannan matsalar da nake ciki har yanzu ba mu cimma matsaya ba idan har ya takura zan saki video ba abin da ya dame ni abin kunya baya na bashi..,
zama tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tace '' ke wannan ita ce matsalar ki ni ga babbar matsalar da take cikin gidana wannan shegiyar yarinyar me kama da zubin karuwai wai jibi zata ta zo karatu a kuma a nan gidan zata zauna..,
wannan matsalar ita take damuwa wallahi gashi my man ya kasa fahimta ta , na fiso nayi rayuwa ni kaɗai ni da miji na , kuma kinga idan har tazo zata saka min ido ne a cikin rayuwa ta ni ina tunanin tun da ba sona suke ba C.I.D aka turo ta kuma wallahi wannan yarinyar duk bu ɗewar idanuwana ta fini.
Dariya eman tayi tace '' jawaher me kike tsoro ko dai abin da kike wa wasu kike tsoran ayi miki shi..? amma in ba haka ba ban ga abin kin ta zo ta zaunar miki ba idan tayi miki ba sai kici kuttumar uban ta ba ki nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane ba mamaki ke abin da kike yi kaɗan ne akan ta..,
shiru tayi tana sauraran ta sannan jawaher tace '' haka za a yi wallahi sai ta gwammace zaman hostel akan zaman cikin gidana yanzu idan ta zo zuwan da kuke yi kuna sakewa babu fa wannan shikkenan magana ta ƙare nima yan wa'yanda nake kawowa muke raƙashewa babu wannan kaf dangin su a rasa wa za ta zauna ta yi karatu a hannunsa sai shi.,
ke fahimtar dani akwai aure a tsakanin su ne wannan abin da kike yi yayi yawa ko dai kishi ne
Eman ta faɗa tana danne dariyar ta.
wani ashar jawaher tayi tace '' bara na turo miki picture din najlah zaki zan dole na tashi hankalina kinsan namiji dan kumana ne ba'a shedar sa..,
eman tace '' haka ne wallahi kawata karki manta ki turo min picture din ta..,
shegiya na fasa ma turo miki saboda tsabar son tsegumi har so kike na turo miki to bazan turo ba duk sanda ta zo kya ganta..
Cewar jawaher.
dariya eman tayi tana kashe wayar ta.
tashi jawaher tayi ta bar guiding tana fita wanda yake kula da gurin ya kwashe kayan da ta yi amfani da su tura kofar da zata sada ta da main parlour tayi, turus tayi ganin bakon al'amari dakyar ta iya sai ta kan'ta tace '' sweet saukar yaushe...?,
gaban ta yana lugudan uku uku har ga Allah bata son abin da ya tsira kwanan nan sai ya dinga dawowa batare da ya faɗa mata ba , zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun alfarma na parlour ta dauke kai daga kallon najlah da take danna waya .
ba tare da ta kalli inda jawaher take ba tace '' ina wuni..,
lafiya kawai tace ta mai da hankalin'ta kan mijin ta ɗaukan pillowcase tayi ta rungume ta kashe idanuwan'ta tana aika mai da wani irin kallo me rikitar da wanda aka yi domin shi murya ƙasa ƙasa tace '' sweet kace min sai jibi zata tawo chanza rana tayi kenan..?,
hannunta Jawad ya kama tare da aika mata wani irin sako yana yin messages din hannun ta .
tari najlah tayi domin ta ankarar da su basu kaɗai bane da sauri ya dawo cikin hayyacin sa. idanuwan'sa har sun canza launi yace '' jawaher kai ta dakin da zata zauna..,
tashi tayi tana sakar wani shu'umin murmushi tace '' am kanwata ki zaki iya tashi sorry fa na rage miki jin daɗin ki..,
tashi najlah ta gyara zaman hijabin da yake jikin ta ta dauki trolley bag din ta ta fara ja tsaya, tsayawa tayi batare da ta juyo ba ,
ita daman ta dade da sanin cewa zuwan ta gidan ya Jawad akwai babbar matsala tana da gudun hulakanci dan haka wallahi wata ran dole su kwashi yan kallo inhar jawaher ta ci gaba da yi mata haka , wannan wanne irin rashin hakuri ne da rashin kunya a gaban ta suna yun kurin aikata abin da ba dai-dai ba , tana cikin wannan tunani ne taji yace '' jeki zan saka a daukar miki ita , ki dena ɗaukar kaya masu nauyi..,
to kawai tace ta bar jakar ta anan bude mata dakin tayi shiga tayi ta kwanta a tamkekem gadon da yake cikin bedroom din, bin ko ina take da kallo tashi tayi ta cire hijabin ta , wayar ta , ta dauka ta lalubo number hajiya bugu ɗaya ta dauka fashe mata da kukan shagwaɓa tayi tace '' Hajiya wallahi bazan iya zama a cikin gidan nan ba auntu jawaher bata da kirki ni nafi son na zauna a gurin ya Aliyu nafi so nayi B.U.K dan Allah ku mai dani can tun da nan ko admission basu fara bayar wa ba..,
Hajiya tace ''Najlah yanzu ke da ace aure kai miki ya kenan tun da kika ji zancen tafiyar nan kika daga hankalin ki, kinsan dai halin family din abban ku duk abin da suka tsara ba wanda ya isa ya ja dashi dan haka kiyi hakuri har ki gama zama ki dinga zuwa hutu bawai dindindin zaki zauna ba..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' inna su adal suke..?,
abban ku ya tafi da su gidan anni
Cewar hajiya
Najlah tace '' idan sun dawo kice ina gaishe da su,
Hajiya tace '' to za suji insha'Allahu .
sallama su kayi ta kashe wayar ju yowar da za tayi suka hada ido da Jawad da sauri ta da baya daukan hijabinta tayi ta saka kasa cewa komai tayi kirjinta na tsanan'ta bugu har ga Allah bata son wannan kallon kulla da yaya Jawad yake mata shi ko kunya baya ji ta sha kama shi yana kallon ta sai dai ya waske.
trolley din'ta ya shigo mata da ita sannan yace '' duk wani abu da kike bukata ki yi min text messages zuwa gobe insha'Allahu ina ga zan tafi Dubai..,
a hankali tace '' Nagode sosai Allah ya ƙara arziki bana bukatar komai, komai abba ya siya mun..,
ƙafarsa ya ɗora akan gado ya jingina da bango yace '' bakya jin zafi ne..?,
da sauri ta juyo jin maganar sa waskewa yayi ganin rashin dacewar maganar da yayi yace '' baki kunna AC ba kin zauna haka..,
ajiyar zuciya ta sauke da har sai da ya jiyo lokacin da ta sauke ta fita yayi ya dafa kan'sa me yake shirin aikatawa ne .
cin karo sukai da jawaher tace '' abincin ka ya haɗu wanka zaka fara ko cin abincin..?,
kai wa Najlah nata ni sai nayi wanka zanci ban sani ba ko tana jin yunwa..
da sauri ta kalle tace '' She's just girl, ot is this house not hers? If she's hungry, she should just speak up. I'll go and prepare your bath water..,
kallon ta yayi da sauri ta hadiye sauran zancen nata kitchen ta shiga ranta duk a ɓace wayar ta ce tayi ringing da sauri ta ɗauka tace '' zan kira ki ya dawo bana cikin nutsuwa ta..,
tana kai wa wannan ta kashe wayar ta , tana sakar gauran numfashi cikin takaici ta hada komai a cikin tray zura wayar ta , tayi a aljihu ta ɗauka kai tsaye dakin Najlah ta nufa ko da tace batai knocking ba ta shiga tarar da ita tayi bata cikin dakin sai dai motsinta da ta ji a toilet tsaki taja ta ajiye a kasa zata juya Najlah ta fito daga ita sai towel gaban jawaher ne ya faɗi ta raina kan'ta wani abu ne ya tokare mata maƙogaro tabbas sai yarinyar nan ta bar gidan nan idan fa zata iya tunawa da aure a tsakanin su to idan shi ya zo ya ganta a cikin wannan hali ya ke nan dakyar ta iya saita kan'ta tace '' am gashi nan...,
thanks kawai ta ce ta zauna akan stool tana tsane gashin ta hand dry ta dauko ta fara busar da gashin ta na muzayen asali bugo mata kofa tayi murmushi Najlah tace '' mahaukaciya duk wannan abin da kike yi akan yaya ne insha'Allahu sai yayi mata har uku bayan ke..
gama shiryawa tayi ta buɗe trolley din'ta ta dauko duguwar riga ta wani material an mata ɗinkin T line daga sama rigar ta bude daga ƙasa ta tsuke kulle kofar ta tayi ganin ita kaɗai ce ba kowa kawai sai ta cire towel din jikin'ta bra ta saka da pant sannan ta saka rigar dan dai saman da faɗin sa amma duk da haka ya fito mata da kirar jikin ta tubke gashin kan'ta tayi ta saka chantili cap feshe jikin'ta tayi da turare ta zauna buɗe abincin tayi ta dan taɓe baki ita irin wa'yannan abincin na turawa be dame ta ba ɗan danawa tayi ina baza ta iya ci ba daman tun a ido taga ba zata iya ci ba gashi hanjin cikin ta har wani curewa suke guri ɗaya.
tashi tayi ta buɗe fridge ban da lemo da ruwa ba wani abu da zai iya tare mata yunwa tashi tsaye tayi ta kama kugunta to yanzu ina ta dosa kenan gaskiya ba zata kashe kan'ta ba dan haka , ta dauki mayafin'ta ta yafa ta fito ɗauke kai tayi lokacin da ta gan su hannun su a tsarke da na juna suna saukowa daga kan stair case tamkar wasu tattabari taɓe baki tayi tace '' aikin banza wannan aunty jawaher din yar uwar karuwa ce sai wani nanike mai take shi kuma tattabari sarkin aure yana biye mata ...,
tafaɗi haka a cikin zuciyar ta
Cikin barikan ci tace '' sister akwai abin da kike bukata ne....?,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' uhmm daman bazan iya cin wannan abincin ba ne zan girka da kai na.,
dafe goshin ta jawaher tayi tace '' oh na fa manta baki saba ba cin irin wannan abincin ba sai local dishes..,
murmushi tayi tace '' ai yana da kyau mutum karya watsar da al'adar sa,
good girl haka ake so ga kitchen din can kije ki dafa abin da kike so.
cewar jawaher.
bata ce komai ba ta juya tabar gurin dining table suka nufa Jawad ya ja mata kujera ta zauna shima yaja ya zauna serving ɗin'sa ta fara yi tace '' am sweet ba ka ce komai ba maganar tafiya Turkiyya da zanyi bikin zeey yana fa matsowa ya kamata muyi abin da za muyi wallahi su mami ma ni suke jira one month kaɗai fa zan yi amma duk kabi ka ɗaga hankalin ka za mu dinga video call nasan abin da kake nufi komai za mu iya ta video call...
kasa kai chokali bakin sa yayi yace '' video call me zai saka ban da ya ƙara tun zurawa ?,
wani numfashi ta furzar me wuci tace '' sweet idan ka hana ni tafiyar nan bakai min adalci ba mutane nawa ne suka amfani da video call kuma suna in joy mode din Please i begging you Ka barni yanzu siyayyar zeey na kasa zuwa ka tuna lokacin auren mu mene ba tai min ba , dan yanzu zata sake aure sai kuma ni na kasa yi mata abin da tai min bana bukatar kudi kawai so nake na taya ta zaɓen kayan dakin ta da wasu abubuwan tun da daga can har Katar za mu..,
limshe idanuwan'sa yayi ya dauki tissue ya goge bakin sa yace '' zan duba na gani..,
riƙe hannunsa tayi tace '' kai ma fa tafiya za kayi ka temaka ka barni..,
hannunta ya riƙe yace '' school fa ya zakiyi da karatun ki wa zai zauna a gidan..?,
gumi ne ya karyo mata ta san shi sarai da dabi'ar son tayi karatu tace '' am yanzu muna first semester ne so karatun be kankama ba kafin na dawo komai ya kankama gida kuma ga Najlah nan me zai faru da ita da ace tayi aure da yanzu tana gidan mijin ta ..,
kura mata ido yayi ya hura mata iska da sauri ta limshe idanuwanta.
murmushi yayi yace '' zan shiga study room zanyi aiki ki huta lafiya..,
binsa tayi da kallo ranta duk ba dad'i kullum addu'a ta Allah ya saka ya barta ta tafi wannan tafiyar tashi tayi ta shiga dakin ta ta murza key dauko waya tayi a cikin aljihunta ta lalubo wata number ta yi dialling ringing ɗaya kai picking call din cikin sauri tace '' ka bani lokaci mana har yanzu yaƙi amincewa kasan ba zan iya tafiya wank guri ba , batare da izinin sa ba amma ka kasa fahimta, ta Jawad yana da kafiya da tsayawa akan ra'ayi ɗaya na lura duk irin kokarin da nake yi baka gani kullum da kai nake kwana nake tashi idan ka faɗi haka bakai min adalci ba , mutumin nan yanzu abubuwan da take yimin kamar ya fara zargina dole mu bi komai a sannu kar kwabar mu tayi ruwa..,
shiru tayi tana saurarawa domin jin me zai ce kit taji ya kashe wayar ciro wayar tayi tana jan ƙaramin tsaki
buɗe dakin tayi ta fito bata gansa a parlour ba zama tayi akan kujera tana girgiza kafa ranta duk a ɓace idan jawad ya hanata tafiyar nan tabbas ya gama da ita ga wannan kaddarar da tazo mata kan'ta gaba ki ɗaya , ya kulle tama rasa ma za tace da sauri wata shawara ta fado mata zuciya duk yadda akai ummin jawad bata san da zuwan Najlah ba.
da sauri ta dauki wayar ta , ta samo laluban number ummi bugu ɗaya ummin jawad ta ɗauka jawaher tace '' Assalamu alaiki ummi barka da yamma ya su taufiq..,
cikin isa da nuna ƙatsai ta ummi tace '' wassalamu alaiki barka dai suna lafiya da fatan kuna lafiya..,
gyara zama tayi tace '' eh wallahi ummi lafiya qalau alhamdulilah..,
Ummi tace '' masha Allah haka ake so ya kaɗaici kuma..,
wani murmushin jin dad'i tayi domin an