x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - ALIYU GADANGA

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 161

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
     #Comment,share,vote....#
      #Janafty...#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


_*A big congratulation to u my Sisi of life AISHA ALTO..4Completing ur Special,Amarzing,Fantactis,Adorable and Educated Novel...GIRMAN KAI(Rawanin Tsiya) d Whole book is dedicated to me,JANAFTY...kai am out of Contol fa,don wannnan babbar kyautace wanda bazan taba mantawa da ita ba,Ina mika miki Hannun Jinjina 👍Sisinah domin kin baje dukkan basiranki da Fikiranki wajen Tsara wannan Novel din,hakika kin Fadarkar damu bayan Tarin nishadi da masu karatu sukayi, kin kuma samu nasaran isar da sakonki cikin Hanya mai Sauki,ke Tadambance awajena,Hakika salonki na burgeni kuma yana Tafiya dani,ina rokon Allah yabaki ladan Fadakardamu dakikayi bayan ya duba kuran kuran dakikayi ya yafemiki Duniya da lahira..Kaunarki Araina bata da iyaka..Bazan gaji da fada ba,bakuma zanji kunyan maimaitawa ba Nagode sosai bisa karamcinki gareni My Sisi of life gabadaya shafin na yau mallakinki ne,na baki shi halak malak..Kisani ki kara sani AISHA ALTO KINA BURGENI*_😘

*NOT EDITED*💥

      *Chapter 9*

    

        """Sati uku kenan da Tafiyar Aliyu gadanga ammh baizo gida ba,sai dai waya da sukeyi Shida goggo,ammh ba kullum ba saboda Tunda ya koma yazama yana keeping kansa busy baya zama sosai,akwai wasu bataliyan Sojoji da yake koyama Training bai samun lokacin kansa ma,balle na Tunani,ya tattara komai ya watsar da zarar Tunanin Abunda ya faru ya fadomai zaiyi Saurin Kaudashi ko Afuska baya nuna alama,hatta jabir duk nacinsa,da son gulmansa,sai da ya hakura,shiko Haisam yadai kirasa awaya sun yimagana,kuma duk Akan yayi hakuri da Abunda Allah ya kaddara maine,to ya zaiyi?ai baya da tacewa shikam Tunda haka Allah yayi dashi.

  Ni"ima kuwa sai da ta shafe Sati a asibiti kafin asallameta tadawo gida,Jikin nata da sauki ammh kullum kwana take kuka saboda Rashin Aliyu atare da ita,Maminta ne da kawarta muneera suke kokarin kwantar mata hankali,ammh ina bata ji bata gani,game da Captain dinta zata iya komai,kawai tana kokarin nuna komai ya wuce ne saboda damuwar Maminta da Abbanta da kuma kawarta muneera,ammh taci alwashin bazata bari captain dinta ya subuce mata ba,zataje koda chan kadunan taasan in ya ganta bazai iya kauda ido akanta ba,dole zai tsausayamata su dawo su kara Shirya Auren nasu akaro na biyu,duk da ta san zata Fuskanci kalubale,har zuwa lokacin Ni"ima bata San cewa Captain dinta yayi Aure ba,shiyasa take ganin shawo kanshi mai sauki ne.

  Bangaren Azeema kuwa babu Abunda ya chanza na dangane da Rayuwarta,inna da Azeeza sungama yawo da mganar a anguwa suna fadin Babanta yaga kwadayi ya auramata mara asali,kuma dan" iska,har a mkrantansu saida Azeeza taje da lbrin sai ya zamana Azeema tazama Abun nune da zunde duk sai taji duniyar tayimata kunci da zafi,ko kawayenta na anguwa haka suke kallonta suna fadin kwadayi zai kasheta ita da ubanta,Azeeza na fadn mganganun banza akanta ana mata dariya,mussaman in suka hadu a bohol taje debo Ruwa da kuka take dawowa,wajen Babanta kadai take samun sauki,sai ko wajen Baba Ade kakarta sai wajen uwa gareta goggo wanda tagama guje gujenta ta hakura taje gidan goggon wacce takamata ta Rumgumeta tana mata tsiya,ita goggo ta fadamata cewa ita ba"a Suruka take kallonta ba,a mtsayin Ya take kallonta saboda haka itama Tadauketa amtsayin uwace wacce ta haifi Aliyu da Azeema,dole Azeema ta saki jikinta duk da Nauyin da Goggo ke mata bata da yadda zatayi saboda goggo babu ruwanta hira take da ita kamar ba matar Danta ba,Tuni Azeema ta saki jikinta suka cigaba da yadda suke da goggon kamar da,agidan take Wuni sai yammah take komawa wannan bakin gida,Inna ko babu Abunda ta fasa na muzgunama Azeema sai ma Abunda yayi gaba,yanzu Azeeza Abunta yayi kamari ko mgana Azeema tayi mata tsab zata saka hannu ta shareta da mari bata da bakinn mgana don sai inna ta kusa kasheta lokacinta baiyi ba,shiyasa ko Baba bata bari yaji saboda duk hukuncin dayayima Azeeza akanta inna zata saukeshi shiyasa take hakuri tasha kukanta ta sharbe hawayenta bata da mai lallashinta,duk ta rame ta kanjame kamar ba ita ba,tayi baki,ga wasu kananan kuraje sun Fito mata in ka kalleta bazakayi Tunanin yarinyace yar shekara 20 ba,sai kayi zaton ta haurama talatin30 baya saboda wahalar rayuwa don ma goggo na tsaye kanta,Abun ne ya ishi goggo dole ta matsama Aliyu yazo gida tana son ganinshi don tanaso ya tsamo Azeema daga wannan kangin bautar datake ciki Tunda dai yanzu Shike da iko da ita,kuma tasan duk iskancin inna Ramatu tana shakar captain din.


    *************   

Sai da Aliyu gadanga ya shafe sati Shida baizo gida ba satin ma sai da ya biya gidan kawu bala suka gaisa da Ummah kawu ma bayanan ya tafi Abuja Haisam ma bayanan yana kano wajen aiki,Shiyasa bai dade ba daganan ya kamo hanyar Gombe zuciyarsa duk babu dadi saboda yaasan kiran gaggon bai Wuce mganar sokuwar yarinyarnan ba,wanda gabadaya baya son Tuna komai,Shidai burinsa da Addu"asa bai Wuce Allah ya bayyana mishi Asalin mahaifinsa ba ko zuciyarsa zata daina wannan Nauyin data dade tana fama dashi.

 
Da misalin karfe 2:30pm ya Iso kofar gidan nasu cikin lafiyayyayiyar motarsa din nan 4matic,kofar gidan ya faka motar,bai shiga da ita garejin ba nan ya barta ya bude booth ya shiga jiidan Tsaraban da yayima goggo yara na Jida suna shiga dashi cikin gidan goggo,wacce ke tsakar gida tana jin Radion ta taga Shigowar yara ko bata tambaya ba,Tunda taji dirin mota ranta ya bata gadanga ne,jikinta na Rawa ta mike har zaninta na neman Faduwa ta nufi hanyar waje Sukaci karo da gadanga ya taho jikinsa sanye da Riga da wando Rigar fara ce ammh wandon Nevy blue ce,sai takalmansa rufaffu ne, kansa babu hula gashinsa yasha gyara yana kyalli,Rumgumosa Goggo tayi tana fadin"Oyoyo gadanga..Sannu da zuwa Gadanga kusar yaki,ga soja mazan fama Ah..Soja na Azeema..."Goggo take fada tana Rumgume da Aliyun..

  
Dariya yake yana Rike da goggon yake fadin"Oyoyo goggo ta....Nayi kewarki sosai mamata.."Dunguremasa kai tayi tana fadin"bakayi kewata ba gadanga Tunda sai da nayi ta magiya kafin ka dawo.."Tafada tana Amsan jakar kayansa dake hannunsa,dariya yayi kafin ya saka hannu ya zagayo da hannunsa kan kafadanta kamar wasu kawaye suka jera zuwa cikin gida yana fadin"Haba goggo..Kefa kika haifi gadanga..Kinfi kowa saninshi ko zan manta da kowa wlh banda Uwar Ali gadanga.."Yafada yana wani lamgwabemata nishadi ya kashe goggo tana dariya,ahaka suka karisa daki,tana mai maraba,saboda murna ma goggo bata bashi Ruwa ba,saida tagama kawomai abinci kafin ta tuna,dariya ya dinga mata yana jin dadin zama da goggo sosai haka suka zauna sukaci abinci tare suna hira da dariya in ka kallesu bazakace mahaifiyarsa bace sai ka dauka Kaninta ne saboda yadda take yar daidai da ita.

Azeema data dawo daga kai nikan Alalan da inna ta Aiketa tunda tadawo mkranta ta bata nikan ko Uniform bata cire ba,tatafi kai nikn,,gashi ta tarar da layi sai da tadade bata dawo ba,tana ta sauri ta iso kofar gidan goggo gabanta ne ya fadi dataci karo da Motar yaya captain bakinta har rawa yake tana karkarwa,tana leken gidan ta yi Saurin Wucewa jikinta na rawa saboda tsoro,koda da takaima Inna nikan sai da ta mareta tace ta dade ta tsaya iskancinta bata dawo da Wuri ba,ita duk wannan bai dameta ba,duk fargaban Dawowar yaya captain ya dameta ammh ta godema Allah dayasa taga motarsa da sai ta shiga su hadu da juna,rike baki tayi tana Tuna karonsu dashi,kayan mkranta kawai ta cire tazo ta hau sharan gida,wanke wanke ta hada,ta duba rijiya babu wani Ruwan kirki,tunda rijiyar taja baya sosai babu Ruwa shiyasa take wahalam Aiki yanzu Tunda ga debo Ruwa ya karu,karamin hijabinta ta sanya Domin Riga da sikat ne ajikinta kayan ma sun mata kadan domin sun matseta,rashin wadatattcen kayan ne,yasa take sakasu har yanzu,botikai uku ta diba ta fice zuwa bohol din dake gaban gidan goggo da kadan,sai da ta leka ta tabbatar da kofar gidan goggon babu kowa kana ta fito ta wuce tana waigo koda taje wajen layi yayi yawa sosai,dayake anfara mtsalan Ruwa,idonta ne yakawo Ruwa data tuna da Abunda inna tace,tace in tawuce minti goma bata dawo ba,sai na lahira ya fita jin dadi,jikinta na Rawa ta shiga rokon yan matan dake wajen su bata da diba ko botiki daya ne,kallonta sukayi shekeke kafin su sheke da dadariya suna fadin",Ahhyyyye...Sannu isassa...Kije sojan da kwadayi yakaiki aurensa yazo ya kwatan miki,an dai ji kunya mutum yazama matar aure,ammh kullum ko karen layi bai kaishi Arha ba.."Kallonsu Azeema takeyi hawaye na zubomata domin dukkansu kannen bayanta ne,kawayen Azeeza ne,batace komai ba,sai takoma gefe tana sharan hawaye tana jiran layi ya kawo kanta ta diba.

Inna Ramatu taga Azeema ta dade bata dawo ba ga kullin Alala zai kumbura bata dawo ba,Ranta ya baci ta kwalama Azeeza kira,wacce ke daki tana kwance tana hutawa,tana kuma saka yarda zata zama mallakin Captain taji kiran innar,tana fitowa inna tace"Taje wajen bohol ta kirawomata Azeema tace in bazata kawo mata Ruwan bane ta sani.."Tura baki Azeeza tahauyi don ita ta tsani aike,Dakyar ta shiga daki ta sawo hijabinta ta fice afusace,Bagazan bagazan take tafiya Ranta bace Shikuma yana kokarin Fitowa daga motarsa ya bude gareji zai sakata yaga Wucewar Azeeza kamar wata jaka,baima ganeta ba,yadda yaga ta wucene ya bita da kallo,don shi ya zatama inna Ramatun ce,tsaki yaja kafin ya Rufo motar yana kokarin komawa cikin gida kamar an ce ya daga kai sai ya hangi Azeezar tsaye gaban Azeema domin Tazaran kadan ne da gidan goggon,yana hange bohol din da duk Abunda yake faruwa.

  Tana zuwa batayi watawata ba ta ture Azeema datayi nisa cikin Tunani, sai da takusa faduwa tayi Saurin dafa bango,dagowa Azeema tayi tana fadin"Haba Azeeza baki da hankali ne,kikamin wannan bangazan..",Wani kallo Azeezar ta wurgamata kan tace"Anyi miki Din,ba inna ta aikeki ba,tun dazu kinzo kin tsaya kina bin Mutane da kallo,kamar wata sakarya.."Tafada da alamar raini,gabadaya wajen suka kecemata da dariya,Azeema ta karisa wajen kawayenta suka tafa suna dariya suna nuna Azeema dake hawaye,wani saurayi ne,dan kasan layinsu ne,sunansu sulaiman Ya tsawatar musu ammh sai suka buge damai Rashin kunya,Yana ganin haka dama layi yazo kanshi botikin daya diba ya mikama Azeemar yana fadin"Karbi ki Tafi dashi gida,ni zan jira sai na kara diba.."Azeema da hawaye ya cikamata ido ta kalleshi tana fadin'Nagode.."Tafada Hawaye suna kwararomata,Daukan Ruwan tayi ta juye adaya botikin nata ta Cicciba zata dora akanta,sai ta kaasa sai Sulaimam din yasa hannu ya taimakamata ya dora mata ammh duk da haka sai da Ruwan ya jikata,har hijabin jikinta ya lafe bisa jikinta,albarkatun kirjinta duk sun bayyana waje,hawaye na zuba ajikinta ta dago tana fadin"Nagode sosai.."mirmishi yayi mata bai ce komai ba,tazo zata wuce su Azeeza suka kwashe da dariya suna nunata sai ta zargu tafara hardewa ganin haka yasa Azeeza tahowa gabanta batai wata wata ba ta sanya hannu ta tura Azeema baya ji kake chambal...!Azeema ta fadi cikin katuwar kwatamin kwatan dake wajen botikin Ruwan ya watse bisa jikinta itakuma tayi tsamo tsamo cikim kwata,gabadaya wajen ya dau ihu,Shiko sulaiman baki ya rike cike da mamaki ganin tsabar mugunta wajen Azeeza.

Takaichi Tare da bakinciki sukayima Azeema dirar makiya tana zaune cikin kwata take bin Azeeza da kallo Tana zubar hawaye,itako Azeza banda nunata tana dariya ba Abunda takeyi tana fadin"Tabdijam lallema Adda Azeema kina nufin Ruwan botikin wannan kazamin zaki kaima na gida,wlh da sake kima sake Tunani.."Tafada tana Wurgama sulaiman din wani kallo dama ta tsaneshi saboda sam ko a anguwar baya daukan Raini baya sakarmata Fuska sam.

Yanajin Abunda tace ya nufeta yana fadin"Lalle yarinyar nan baki da kunya yanzu zan koya miki hankali..."Ya fada yana karisowa,kusa da ita baiyi wata wata ba ya daga hannu zai mareta sai yaji ance daga baya cikin wata kakkausan murya..'Hey Leave her...'"Sukaji an fada daga bayansu gabadayansu suka waiga suna kallon mai mgana.

Dukkansu sai da suka Razana hadda Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka,yana Tsaye hannayensa gabadaya ya zuba su cikin Aljihun wandonsa,Fuskarasa Murtuke babu Annuri ko kadan har wani ja tayi saboda bacin rai,Azeza da kawayenta yake bi da wani wulakantattacen kallo,wanda Tuni suka Tsorace kamar su saki Fitsari awando ganin yadda yake kallonsu Jiyoyin kansa na mikewa saboda bacin rai,Kallonsa ya maida kan Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka Jikinta duk ya baci ga Shi hijabinta duk ya manne mata ajiki,baisan dalili ba,sai yaji wani mugun Haushi ya tokaresa kamar ya bita cikin kwatan ya ci ubanta Tunda ta zama solobiyo,Sulaiman kuwa yana ganin captain ya koma gefe yana dariyan mugunta domin yasan daga yanayin kallon dayake musu yau din nan sai sun gane basu da wayau..

Taku yafarayi zuwa garesu yana wani kame idonsa guda daya na salon mugunta,Tuni suka tsorata suka fara ja da baya,Azeema ko jikinta na rawa ta mike saboda atunaninta wajenta zaizo ya fara ta kanta sai ta ga yayi Pointing dinsu Azeeza yana fadin1,2,3,4,5,6....All af u come here...',Yafada cikin gadara,Ai da wani tsoro suka fara kallon junansu tsawa ya daka musu yana fadin"don't Force me to Mention my Statement..All of u will be in Tourble i swear..",Yafada yana wani buga kafansa akasa,wanda saida Mutanen wajen suka Razana.


_Wowow...Ran Maza fa ya baci..Su Azeeza kun Shiga Tarama ba Uku ba,do da Alamu Fushin sojan zai sauka bisa kanku,kilama Harda horan Sojoji zai baku😂Wayyo,Allah ya kwaceku maganinku kenan,Fans ya kuka gani kuna goyan bayan Captain yaci kaniyar su Azeeza?..Cike Tagging dinki da kayatattacen Sharhi ta hakan ne kadai zan gane kuna biye dani_



         *Comment,share and vote...*
         *#Janafty...#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


      *Chapter 10*

     ""Jikinsu na rawa suka fara takowa zuwa gabansa,kowacce tanaji kamar ta saki Fitsari awando saboda tsoro da Razana,Kafin su kariso ya sunkuya akasa ya sanya hannu ya dauko wata sanda baya yakoma daga chan wajen inda ya faka motarsa ya shiga jan Dogon layi,yana gama ja,cikin wani Fusata yazo ya wucesu kamar kiftawa da bismillah ya isa chan nesa da bohol din ma nan yaja wani dogon layi,Ko kallonsu bai yi ba,daga chan bangaren ya nunasu da hannu yana fadin"Ku yan iska ko? marasa mutumci,dama kune marasa tarbiyan anguwan ko? ok To iskancinku yazo karshe daga yau oya all of u ku fara frog jump daga inda layin chan yafara zuwa inda ya kare,kuma 50 zakuyi each zuwa da dawowa to be counting one ne..."Yafada cikin gadara da isa.

  Gabadayansu suka kalli juna ganin zasu batamai lokaci yasa ya fara taku zuwa garesa ai da gudu suka isa ga layin kowacce ta duka tafara,daga nesa yace"duk wacce batayi da kyau ba,ko ta gama sai ta sake so is better da ki zage kiyi yadda nace..."Yafada yana harde hannuwansa akirji Sulaiman dake gefe yana kunshe dariya yace"Yallabai zanyi musu couting.",Da kai ya amsamai yana cije lebe kafin yace"ka sa ido akansu..Duk wacce bata yi dakyau ba juz ka waremin ita yau zasu ci ubansu ne..",Yar dariya Sulaiman yayi yana fadin"Baka da mtsala yallabai,ya fada yana kallonsu yana fadin"Toh maza kuyi da jiki...one,two...three,wlh kika bari aka barki abaya zan tsayar dake.."Yafada yana dariya jin haka yasa suka zage sai yi suke kafin kace kwabo sun Fita hayyacinsu ko goma basuyi ba,ammh haka suke kuka da majina,Tuni layin ya cika da mutane anata dariya wasu kuma na murnan Abunda ke faruwa don daman kowa yasansu Azeeza alayin basu da kunya ko kadan,wasu sai fadi suke gwara hakan,kila daga yanzu sayi hankali.

  Azeema na gefe tana barin jiki Tana kallonsu Azeeza yadda suke kuka harda majina,Dasun bude baki zasu yi mgana sai captain yace +anoder 50 din,dole sukayi Shuru da bakinsu domin Wannan wahala tayi kama da wahalan gidan yari ne,Shiko yana gefe ya harde hannuwa bisa kirji yana kallonsu yana dan murmusawa,Da kallo yabi Azeema yadda tayi wani kalan Tsausayi nufota yayi sai ta hau ja da baya,tana ganin ya kariso sai ta duka ta kama kunni tana fadin"Don Allah kayi hakuri nima zanyi..Zanyi.."Take fada tana kokarin Fara tsallan kwado tsawa ya dakamata yana fadin"Stand..."mikewa tayi jikinta na bari,Tsaki yaja kafin ya juya yana fadin"Ina abubuwan dakika zo dasu diban Ruwa.."Bakinta na rawa ta nunamai botikan guda biyu,don dayan kam ya fashe,bai kara kallonta ba ya isa garesu,da hanzari ya isa ga bohol din yasa hannu ya ture layin dake kai ya aza botikinta Yasa dayan laullausan hannunsa yafara buga bohol din,Jikin Azeema na rawa take binshi da kallo yana zubamata ruwa bai dauke hannunsa ba,sai da ya cika duka botikan guda biyu,da hannu biyu ya daukesu atare,ya nufota cike da mamaki mutane ke binsa da kallo yanayin komai cikin Jarumta da takama,sai da yazo gabda da ita kafin yace"Wuce muje bush girl kawai..."Yafada yana huci jikinta na rawa ta mika hannu tana fadin"ba..Bari na dauka.."Wani dirty look ya watsamata kafin yace"Leave dis place now..."Yafada a tsawace,da hanzari tashiga gaba tana bin su Azeeza da kallo wadanda sukayi chanza kammanin saboda wahala ga Sulaiman Shiko ba mutumci da gayyah sai yace basuyi daidai ba,sunyi yafi ashirin ammh yace biyar ne,mai kyau sauran sai sun sake,Bayanta yake bi dauke da ruwa,Ransa na masa kuna banda An raina masa wayau wai wanna ce matar da"aka Aura masa,kullum gantali alayi kamar wata karya,Saboda cin mutumci harda Debo Ruwa saboda Rainin wayau,Kallonta yake tana tafiya wani takaici ya makarosa ji yake kamar ya shakota ya kifkifamata mari saboda haushi,Suna zuwa kofar gidansu taja ta tsaya tana so ta kalleshi ammh tsoro yahanata,Kanta na kasa tace'Don..Allah ka..kayi hakuri ka..."Bata gama Rufe baki taga ya wuceta ya shige gidan dauke da Ruwan baki ta rike tana bin bayansa da kallo,kafin jikinta asanyaye tabi bayansa.

  Inna Ramatu na zaune bisa kujeran Tsugunno atsakar gida tanata bala"i ita kadai ba Azeemar babu Azeezar ba wanda ya dawo,kawai sai ganin tayi Tsulum Mutum ya shigo gidan bai dire ko"ina ba sai agabanta ya ijiyemata botikan Ruwa ta dago ta kallonsa cike da mamaki,kafin ta mike tana zare,ido lokacin idonta ya sauka kan Azeema data shigo ta rabe gefe tana hawaye,Cikin wani masifa inna Ramatu ke fadin"Kai mallam lafiyanka kuwa zaka shigo gidan matan Aure babu Neman izini.."Tafada tana binsa da harara,domin ta
End Ads