x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 31 - ALIYU GADANGA

  • 90001 words
  • 93000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 173

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
daga ya"yan suna bugasu,nan da nan suka chanyara kuka atare,Azeema dake kwance hannunta kamkame dana gadanga taji cikinta yakara murdawa Nishi take saki tana Fadin"Yaya inaji fa akwai wani acikin cikin?Tafada tana wani nishin mai karfi,Wata nurses ce ta ankare da hanzari ta kariso tana kara ware kafafun Azeema take Fadin"Anoder one..."Take Fadi tana ihu"push oya push..."take Fadamata Azeema ko jitayi kamar zata Shide saboda azaba,dakyar ta iya wani nishi mai karfi,wanda ya Fito da kan Da'n Suka sanya hannu suka jawoshi,suna murna gabadaya dakin ya gauraye da kukan jariran wadanda Nurses din suka dagasu suka zube bisa jikin Azeema suna dariya,jikinsu duk jini ammh haka Azeema ta rikesu tana dariya lokaci daya da kwallah,Aliyu ko kamar yasuma saboda dadi,Dakyar suka koreshi waje suka kwashe mabiyan Azeema suka gyara wajen gefe daya kuma wasu suna kokarin gyaran yaran,duk da asibitin na kashi ne,ammh Nurses din sun san Abunda sukeyi,shiyasa karban haihuwan Azeeman bai basu wahala ba,duk da Abun yazo da Sauki.


Koda gari ya waye sai dai Asibiti ta cika da lbrin Majinyacin Sojan nan da"aka kawo daga Nageri,matarshi tahaifi Tripple,Mata biyu Namiji daya,kuma dukkansu sun zauna amahaifa dayane domin ko Azeema da Aliyu haryanzu sun kasa gane bambamcinsu,duk da kwana sukayi suna kare musu kallo,sun Rumgume yafi sau Biyar suna kara godiya ga Allah daya Basu wannan kyautar,Ummah mai babban daki sai dai Da Safe Dr khan ya sanar da ita haihuwan Azeema,duk da shima baya Asibitin waya akayi masa,jiki narawa suka nufa cikin Asibitin,sai dai suka tarar da Azeema zaune bisa gado tayi Ras da ita kamar ba ita ta haihu ba ga Gadanga a gefe bakin nan kamar zai yage,saboda murna Ummah mai babban daki ita takira Gida ta sanar dasu,gabadaya masarauta ta rude da murna Jikoki uku alokaci daya lalle Allah Abun godiya,Goggo ita ta kira kawu da kanta ta sanar dashi kafin kaceme haihuwan Tripple yazaga Duniya,Haisam na kano yaji lbrin ai sai ya kira jabir yana sanar dashi da zarar komai yayi daidai Aliyu ya dawo gida zasu fadama maimartaba suna so suma ayi bikinsu nan da wani lokaci domin zamowar Aliyu baban yan uku tabbas barazanane ga rayuwarsu😂

kwana biyu da haihuwan Azeema gimbiya Fasilatu da gimbiya Razeenah suka dira a india,murna ba"a mgana,ai gimbiya Fasilatu batayi shawara da kowa ba tayi saranda Taba goggo dama,Domin ta Fahimci tafi karfinta nesa ba kusa,domin tsakaninsu kamar tsakanin sama da kasa ne,duka duka Sati daya suka kara gabadaya aka Rubutama Aliyu gadanga sallama lokacin yana da wata biyu a asibitin,domin yaji sauki sosai koma nace ya warke,domin kafafunsa sun mike da kanshi yake takawa batare da Taimakon sanda ba.



Asibitin sunsha kewa love birds,Azeema da Aliyu ga kuma Tripple masu shiga rai da Ban sha"awa,haka sukayi ta hotuna da likitocin da Nurses,suna bankwana da sabo suka rabu,Azeema harda kwallaar rabuwa ita da Ummah mai babban daki sunji dadin india,sosai Dr khan kuwa sunyi exchanging din Phone number da Aliyu,da cewa da zarar ya shigo Nageria zai nemesa,haka suka rabu da matarsa kareena wacce suka shaku da Azeema da Ummah.

Ranar da suka baro india zuwa Masarautar Tambari buzu,sukowa ana chan ana gudanar da shagulgular murnan dawowar Aliyu da kuma murnan haihuwan yan"uku ,wanda ba"a tabayi ba tun sadda aka gina masarautar,Mutanen Nageria kuwa Sun dade da isa zuwansu Aliyu kawai suke jira,Hatta da jabir wanda yazo Shida Maminsa da Daddynsa,da Haisam ba"a barsu abaya ba domin sunce wlh wannan karon bazasu koma Nageria ba sai da matansu sun gaji suma,suna bukatar gwada karfin mazantakansu😂 wannan karon ma kawu da duka iyalansa,harda su Anty madina sunce wlh suma baza"a barsu abaya ba,tab uwa uba kuma ga shi Sunan yan ukun za"a hadashi ne da bikin gwagwaran biyu Wato Jabir da Haisam,kawu ya roki alfarman kuma Maimartaba baiyi gaddama ba,sakamakon yadda yake cikin Farinciki na dawowar Aliyu,ga kuma wani kyautan daga Allah.



*Ina godiya sosai masoyana ina ganin duka comments dinku daga mabambamta group dadama,bana samun binku daya bayan daya na yi muku reply,saboda ina cikin busy ne ko Typing din ma kokari nake mu kareta mu huta hakanan Shiyasa,ngd sosai kujigaba da hakuri dani Allah ya bar zumunci Ameen*


_*Sisinah Aisha Alto,keda Sahibata Hafsat Hafan ina kai gaisuwa🙋 Alherin Allah ya lullubeku aduk inda kuke*_


*D'IYATA LADINGO GA SAKON JINJINATA👍Allah yayi ma Rayuwarki Albarka can love u less diyar kwarai*



*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 38*

   "Koda suka isa Masarautan, ta dinke babu masaka tsinke,haka aka yayyabe Aliyu da Azeema kamar za"a cinyesu saboda murna da Farinciki,Triple ko sunsha dauka sai da Gimbiya Razeenah ta daukesu ita da Azeema kwacokam zuwa shashenta,inda ta sanya Jakadiya ta saka wata baiwa ta saka mata katuwar gawar da Ruwan zafi ta shiga da Azeema tiolet ta gasata dakyau sosai ita kuma Baba Ade ta wanke yaran tas,aka Shiryasu cikin kayan sanyi masu kyau,aka kaima maimartaba su,shida kawu suka daukesu suka sanya musu albarka,shiko Aliyu bayan gaishe gaishe shashensa ya wuce,shida amininnasa,yasamu yayi wanka yaci abinci ya kwanta domin Hutu,suko Su Zafira da Safaru,suna dawowa goggo ta damkama Anty madina su tace amanar gyarasu na hannunta nan da nan ko tashige dasu Shashen goggo chan kurya domin cika Umarnin goggo,Ummah ko ita dasu gimbiya Fasilatu suna Shashen Azeema suna zaune suna hira cike da Farinciki da Annushuwa,Azeema kuwa tana gama cin abinci suka kulleta cikin daki wai ta kwanta ta huta,tana kwanciya kuma sai barci.

Tako'ina masarauta ta dinke da jama"a daga mabambanta wajeje a kasar Niger,dama kewayanta harda mutanen wasu yanki,domin samun damar amsa gayyatan Da maigirma Sarkin Agadez yayima jama"a na Murna haihuwar jokokinsa har guda uku,tare da Daura Aure tilon ya"yan nasa guda biyu,dole Abun ya Wuce hasashenmu,domin fa ashirya taro ne na azo agani,Hatta da Mallam lawal da Inna Ramatu sai da maimartaba yasaka akayi visa suka taho,domin yace har abada inna Ramatu tana mtsayin mahaifiya ne ga Azeema,sai ga Inna Ramatu zaune cikin masaraurar Tambari buzu rike da ya'yan Azeema,lalle duniya Abun tsoroce kuma hausawa na Fadin Abunda yabaka Dariya watarana Shizai sanya ka kuka,Sai kuma alokacin Aliyu ke jin lbrin Rasuwar Azeeza yaji ba dadi,ammh baiwani nuna damuwarsa ba,kawai yayi jim ne,saboda kada Azeema tace yana murna da Rasuwar yar"uwanta,ammh harga Allah ya manta da wata hallita Azeeza,Fatan dacewa wajen Allah yayimata,ammh akasan Ransa Yana fadin an rage mugun iri.

  Daga Nageria Aliyu ya samu waya dadama,ciki harda waya daga Babban headquater su na Abuja,sukayimai ya jiki,bayan nan ya samu waya daga abokan aikinsa dadama,cikin wayar data tsayamai arai itace wayar da Ni"ima tayimai tana kuka,tace tayita nemansa so ba adadi bata sameshi ba sai yanzu,tadamu sosai Allah yasa ya warke babu Abunda ke damunsa,Mirmishi kawai yayi mata kafin ya sanar da ita ya warke yanzu hakama yana Masarauta nan yake sanar da ita haihuwan Azeema,da kuma Aurensu Jabir,Ni"ima taji hawaye sun taho mata tayi Saurin dannewa tana fadin!"Allah ya raya su bisa sunnah Congratulation,"Lokacin datake Fadin haka yana jinta kuka takeyi,sai ya basar yana tambayanta yakamata su Fito da miji ita da muneera Suyi Aure saboda Shine mutumcinsu,Dariyan kuka Ni"ima tayi kafin tace"Muneera zatayi Aure in Allah ya bata miji na gari,mgana na kuma bata don bazan taba yarda na auri wani namiji ba sai mutum daya,in ban sameshi ba,sai da nakoma ga Allah banyi Aure ba.."Saurin katse kiran tayi tana Fashewa da kuka,Aliyu Tunda sukayi waya da Ni'ima ya koma wani Sukuku ranar,saboda kalaman Ni"ima,hakika in yace bayason Ni"ima yayi karya,kuma in yace baya tsausayinta tabbas yasan karya yakeyi,kawai Shi ra"ayin Aurenta ne bayayi,saboda Shi mutum ne,mai zuciya da tsayawa kan Ra"ayinsa tunda yarasa Ni'ima da Farko komai na plan din Aurenta ya Rushe,sai gashi Azeema dabaitaba tsara Rayuwa da ita tazo tazama kaddaransa,gashi yau an wayi gari bayan goggo bai da wata sanyin idaniya daya Wuce Azeema yanamata Sonda baisan iyakarsa ba,saboda kirkinta da sadaukarwanta gareshi,hakadai yayita tunane Tunane har ya kareta baisamu mafita ba.

Ranar Da Azeema ta cika Sati biyu da haihuwa da misalin karfe 10:00am na safiyar Ranar jumma"a Duban mutane da sarakai,suka Shaida auren Haisam da Safaratu sai Jabir da Zafira kan sadaki mafi daraja, afarfajiyar Fadar maimartaba Sarkin Agadez Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,Daurin Auren daya amsa sunansa,wanda ba"a tabayi ba masarauta tacika makil da yan gida da yan waje,busan algaita kadai kakeji da kade kade da raye raye na Masarauta,abinci ko tako"ina kawai afitowa dashi ake,daga cikin masarauta kuma Yau din ne ake Sunan Triples,wadanda suka ci Sunaye masu daraja Daya taci Sunan goggo SUWAIBA ,Dayan kuma FATIMA,Sai Namijin yaci Sunan Maimartaba wato ABDULNASEER,Wanda ada sunan kawu akaso yace,kawun da kanshi yace maimartaba yafishi chanchantan samun takwara da farko,shima inda rai da rabo,mai sunanshi na zuwa,sunsha wanka cikin kayan alfarma,suda Mahaifiyarsu Azeema,wacce ke sanye cikin wani leshi,mai tsada da yarari,kunnuwanta da hannuwanta gabadaya Sanye da zinarai suna daukan ido,Hakama ango karni sanye da shadda fara riga da wondo harda babban Riga Shida aminan nasa,guda biyu duka shiga iri daya sukayi harda cikon Umar na Hudunsu,Ana gama Daura auren suka nufa shashen Aliyu suka gudanar da wata yar kwakwaryan walima,bayan la"asar nayi aka Fito akayi wata kayatattacan kilasa,mai ban Sha"awa Da dadin kallo,haka duka zaratan maza su hudu ke bama doki wuta sunajan limzami,kowa da kowa yafito kallo,harda maimartaba,Amare ma suna gefe,kowacce ita tarike ma mijinta limzaminsa kafin afara kilasan,Hakama Azeema tayima Aliyu gadangan kusar yaki,daga karshe maimartaba da tawagansa suka Rufe kilasa,yau hatta da kawu Bala Da mallam lawal da sun hau dokuna,Atawagan Sarki,itako inna Ramatu Tunda sukazo take Shashen Azeema ta karbi su Ummah ita ke kula da ita da Triple,Tayi nadama sosai in kuka ganta kamar ba ita ba,Abun jin dadinta ma babu wanda ya riketa da Abunda ta aikata kowa amasarautar yana bata girma amatsayinta na Uwa ga Azeema,Gadanga ne dai haryanzu bai saki da ita sosai ba,don shi mutum ne mai Ra"ayin bala'in in baya Ra"ayinka Tun Farko Abu ne mai Wahala yayi Ra"ayinka daga baya,kawai mazayewa yake saboda Uwar mata Azeema,don ya lura Tunda ta haihu takoma masifaffa,mgana kadan sai ta hau Fushi,shiko yanzu Aduniya in akwai Abunda ya tsana to yaga Fushi Afukar pretty yanzu nan zai Rasa natsuwarsa,shiyasa in gaya su Jabir na Rawan kafa kan su Zafira mamaki suke bashi,dariya kawai yake Aransa yana Fadin"Yarinta haryanzu na damun su Jabir,Allah ya kaunda Fitina,tunda daga su Jabir din har Su zafira shegen Rawan kan tsiya😂


Wajen kwana biyu aka Dauka ana gudanar da shagulgula Amasauratar Tambari buzu,saboda jiran Visan su jabir ta Fito,Ranar kwana uku da Daura Aure visan ta Fito sai haraman komawa,Haisam gidanshi na kano zai wuce da Safaratu,itako Zafira cikin Cikin barrak zasu zauna ita da jabir,sai fa alokacin ne koke koke ya tashi suna kuka sun rike gimbiya Razeenah akan su sun Fasa aure,Abun ma dariya yabama Azeema,sai da taje ta kira Aliyu yazo,tsawa daya ya daga musu kowacce ta Shiga natsuwarta.


Goggo ce da Gimbiya Razeenah zasu raka Amare,Ummah mai babban daki tace wazai zauna tab,wlh dole ne aje da ita gwara tayi amfani da lafiyanta kafin karfinta ya kare tazaga duniya😂Sai su Ummah dasu Anty madina da zasu koma,Inna Ramatu dai tana nan sai Azeema tagama wanka sukoma Tare hakama Shima Aliyu ko Shirin Tafiya baiyi ba,su suka raka Amare da angawaye har Filin jirgi,inda suka sha tsiya wajen gadanga yanata musu iskanci yana Fadin"yaga Sai rawan kafa suke,toh ko sau dari zasuyi Arana bazasu taba kamoshi ba,kuma wlh duk wanda yayagamai kanwa da yawa Allah ya isa😂🙉Jabir ya bashi amsa da cewa"Wlh tallhi yage yagema mallam,kai don Ubanka daka yaga kanwar wani wayamaka mgana,kajimin dan iskan Yaya"Dariya Umar ke tayi Shiko Aliyu hade rai yayi yana Fadin'"Yau ga surikin zamani,yanzu ni kake cema Dan"iska ko,ke Zafira zo nan"Yakira zafira wacce ke tare da goggo,ganin haka yasa Umar ya taresa yana Fadin"Allah huci zuciyar magajinmu rabu dasu,ai kowa ya sani ba wani babban Sai Baban yan ukun mu.."jin haka yasa ya washe baki yana Fadin"Allah yaso ku da na kirata nace ko kazo ta matse kafa🙈🙉"..Dukkansu baki suka rike suna kallon Aliyu shiko gwalo yayi musu yana dariya,daga Haisam har jabir binsa sukayi da gudu kowa ya dungule hannu na cin ubanshi yaje ya makale bayan kawu Bala yana Fadin",Kawu ga gansu ko,daga ina musu nasihan hakuri da Kawaici ,saboda dai wanda ya riga ka kwana dole ya rigaka tashi ko mami? yafada yana kallon Mamin Jabir tana Dariya ta amswa da cewa",Hakane Aliyu,babu kuma wanda yakamata yagayamuku gaskiya bayan Shi,yarigaku auren nan,sannan kuma yaya yake agareku Tunda kuna auren kannensa"Suna jin haka sai kawai suka juya suna hararansa,gwalo yake musu yana yar dariya,shi wlh dariya suke bashi in ya kallesu kowani shege ajirace yake da mace🤔Azeema ce tazo ta murdemai kunne ta baya yayi yar kara yana kallonta kafin yace"Pretty mugunta ko? zaki cirema Baban Triplet kunne ko? matse mai gefen ciki tayi tana Fadin"Kabarsu Jabir hakanan don Allah,tunda kai lokacinka babu wanda Yasa maka ido.."Hannuwansa yahada yana Fadin"toh angama Ranki shidade maman yan"uku"Dariya kawai tayimai ta wuce shiko yabita da kallon sha"awa azahirin batu anfara kureshi fa haba,hanya fa ba kyau,tsakani ga Allah yakamata pretty tazo taji dashi Tunkan yafita daga hayyacinsa.


Basu dawo gida ba,sai da sukaga tashin jirginsu,kana suka koma gida cike da kewa,Shashen Azeema ya rage daga Baba Ade sai Gimbiya Razeenah sai Inna Ramatu,hakama Shima Aliyu yaji shuru saboda harda Umar aka tafi zasu koma Asallamesu kafin su biyo jirgin sojojinsu su dawo kasarsu.



**************

Koda suka sauka A Nageria,direct Su goggo kano suka wuce da Safaratu,Awata anguwa mai Suna Tarauni,gidane babban kirarre,sai wanda yagani komai na alatun Rayuwa akwaoshi acikin gidan,babu Abunda zasu nema su rashashi,nan suka kwana sai washegari suka bar kano zuwa kaduna dukkansu,ammh shi kawu tun jiya yakoma kaduna abunshi,da zasu taho sai da goggo ta damkama haisam cheque dinsa na milayan uku,wanda maimartaba yabashi kyauta,tare da albishir din kujeran makka,shida Safaratu,Ummah harda guda da rawa,tana ta godiya balle su madina da sukayi ma Haisam chaa,wai yakowo su ijiyemai kudin,banza dasu yayi,shifa duk ya kosa su watse don wlh arike yake fa😂Karfe 2, da wani abu na Rana suka bar kofar gidan Haisam,suka bar shi daga shi Sai Safaratu sai halinsu sai dai Fatan Allah ya basu zaman lafiya.


Hudu da wani Abu na yammah suka Shiga kaduna direct to barikin Su jabir suka yada zango,shima din dai apartment din na jabir kamar na Aliyu komai ya mallaka,gyare gyare kawai sukayimata da Sauran abubuwa,basu kwana ba,tunda kaduna gidane,dama tuni iyayan jabir suka bi kawu bala,tun jiya suka dawo kaduna abunsu,shima irin kyautar da maimartaba yama Haisam irinta akama Jabir,tare da kujeran makka Shida zafira,Murna kam ba'a mgana basu wani jima sukayimata Abunda yakamata suka barta daga ita sai Halinta kowanne yakoma gidansa,gimbiya Fasilatu da Goggo da ummah mai babban Daki gidan Kawu bala suka sauke gajiyansu sai sungama hutawa ko zasuyi Shirin komawa Niger,saboda atsakanin nan sun yawatu aduniya ba laifi.

Kowani ango awannan daren ya maida amayarsa cikakkiyar mace,Abun ba ragowa ko kadan da alamu dai sunji maza,Ammh dukkansu sun tsinci kansu cikin wani nishadi mara misalatuwa jabir ne yace aransa"Dama Tuni irin wannan Dadin gayen chan ke kwasa,lalle dole yacemana yara,ammh wlh danasan haka aure keda dadi da Rahama da wlh Tun da na balaga zanyi aure,domin na mori Abun da kyau😂kuji fa jabir daga Shiga sau daya yafara sambatu,shidai Umar Tuni ya wuce sansaninsu,ammh shima kasan Ransa yana Cewa ne daya koma kasarsa zai nemi mata yayi aure,shima ai ba Dutse bane.


Sati daya cur su goggo sukayi suna hutawa kafin sukoma kasar Niger,koda suka koma Tuni yan uku sun kara girma da yau kamar ba yan wata daya ba,Fati itace suke cema Afra,sai suwaiba suna kiranta Afiya,sai Namijin suna kirana Anwar,Azeema kuma na cigaba da samun kulawa sosai gimbiya Razeenah na kokarin saka ido akanta kada tayi danyen jego,shiko Aliyu yayi nacin da bin,ko zai samu ya samu Ritsa Azeema ita kadai babu dama,ko gaishesu yazo yi da safe,su Inna Ramatu na wajen da Baba Ade,kuma Abunda ke bashu haushi suki tashi daga wajen,Abun na bakantamai rai Shiyasa kwana biyu yayi musu yaji,da Azeema taga haka sai dauki waya ta kirashi yana dauka ya balbaleta da masifan ta rabu dashi yaji da Abunda ke damunshi kawai ya yanke kiran,itakuma sai ta zuciya kan mene zai mata tsawa haka alhalin yana sane ba laifinta bane,kuma tayaya zata bashi kanta alhalin jiya jiya ne tayi tsarki,kuma ko samun damar zuwa Shashensa bata dashi saboda Baba Ade bata barinta Fita ko'ina suna tare da ita toh ya zatayi,toh dalilin yasa kowa ya Share kowa kenan harsu goggo suka dawo ana gaba,duk da sai su shafe kwana uku basu hadu da juna ba,don ko Su Afiya sai dai ya aiko jakadiya ta daukan mishi su,ko shashen Azeeman bai kallah saboda takara batamai rai saboda ta rainashi ko zuwa ma tabashi hakuri batayi ba,kuma ya sake kiran wayarta tanagani taki dauka,kwafa yayi aransa yana ayyana yadda zaiyi mganinta.


Su goggo basu Rufe sati da dawowa ba Aliyu yace shifa ya shirya zai koma bakin aiki,Abun yaba kowa mamaki,bama kamar goggo,wacce sukayi mgana yace sai Azeema tagama wankan yara sunyi kwari zasu koma tare da ita,da goggo ta tunamai sai ya bata rai yace ya chanza ra"ayi ne intagama wankan tazo daga baya ganin yadda ya mtsane yasa maimartaba ya amince aka neman masa Visa,Shida mallam lawal wanda maimartaba yayi yayi dashi yadawo masarauta su zauna tare yaki,yace abarshi a inda yake saboda yafi sabawa da chan,kuma ko ahaka babu Abunda zaice sai godiya ga Allah,ta sanadin Suwaiba da Azeema bazai kirga alheran daya samu ba,gashi ayau saboda ita zai je kasa mai tsarki lalle Allah ne Abun godiya.


Daga Aliyu sai Mallam lawal suka bi jirgi suka koma,domin goggo tace Inna Ramatu ta zauna,in za'a maida Azeema sai ataho tare da ita,Abun bakinciki Azeema batama san Tafiyar Aliyu ba sai washegarin daya tafi taji suna waya da goggo,lokacin tana bawa Anwar nono wlh dawani bakin ciki ya Turniketa batasan sadda ta ture anwar ba tatashi da gudu ta shige daki tana kuka ba,Baba Ade dake wajen tayi Saurin daukansa tana lallashinshi,tunda fizgoshi daga Nono tayi,Abun yama Azeema ciwo,itako mai tayima yaya captain da zafi haka har zaiyi iya komawa
End Ads