yace ya fasa auren,kefa matar sarki ce maza share hawayen"Tana Fadar haka ko ta Share hawayenta ta mike tinkis tinkis ta Fice sai Shashen su goggo tana zuwa Ta fada jikin Tsohon sarki Abdulnaseer,tana kuka rikota yayi yana fadin"waye mai tsautsayin daya tabamin ke? matse kwallah tayi tana Fadin ba"Ba Ummi bace ta min Fada ba..",Baki Maimartaba ya rike yana Fadin"a.hhhh babban mgana lalle dole Ummi zata Fuskanci Hukunci kinji share hawayenki kinji amaryata"goggo dake gefe ita da Gimbiya Fasilatu suka tabe baki suna Fadin"Wannan amaryan taka ta Cika shagwaba"cewar goggo,Mele baki Afra tayi kafin tace"Sarkina ka koresu su fita"Dariya maimartaba yayi kafin yace"Angama ranki shi dade..,kutashi ku fita tunda kunji Abunda Amarsu tace",Tashi sukayi dukkansu suna Fadin"Ko bakace ba gaka gata zaka nememu ne"Mirmishi yayi yana Fadin"injiwa Ga Amaryata ni ba wanda zan nema"Yafada yana dariya itako Afra ji'iran Yarinya harda musu gwalo.
achan bangaren Afra na Ficewa wayar Azeema ta sake daukan Tsuwa jin Riging tone din mai kiran kadai sai da ta murmusa,mikewa tayi tsam ta koma cikin bedroom dinta tabar Baba lami suna chasheta ita da Anwar dama dan Rigimar tane,sai ta fada bisa gado kana ta daga kiran Tana Fadin"Allah taimaki maimartaba mai mulkan mutanen agadez..."Mirmishi yasaki mai kayatarwa kafin yace"Kin Fadi jarawabawa pretty,cewa zakiyi maimartaba mai mulkan zuciyar Azeema Shikadai,da'ace kin Fadi haka Tun Farko da kinsamu wata kyauta.."Dariya tayi mai kayatarwa tana Fadin"ko ayanzu ban makara ba bari na gyara maimartabana wanda ke mulki tare da iko azuciyar Azeema ita kadai.."Dariyan Farinciki yayi kafin yace"Maki goma pretty..."Bata Fuska tayi kafin tace"kawai maki goma Yaya captain"saurin katseta yayi da cewa"ba kawai bane preety maki goman dana baki,sunfi maki darin da wani zaici awajen jarabawan Fita daga jami"a,yanzu dai duk ba wannan ba,nayi kewarki kwana biyu ne,wlh ko zaman Fada nakasa yi,shiyasa nace atafi hutun rabin lokaci,shine na samu daman kiranki.."Baki ta rike tana Fadin"a"a Mijina,kafasan sai gobe ne zaka dawo wajena,yau Ni"ima ce keda Turaka,don Allah ka zauna,karfa ka manta akwai hakkin jama"a dadama akanka,bani so ka zama mara adalci agaresu don Allah..."Shuru kawai yayi yana jinta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace"Shikenan pretty zanyi Abunda kikace,Ammh wlh bazan boyemiki ba, nidai an cuceni an hadani da aiki ga Sarauta ga karin kwanaki kafin na kasance dake mtseww.."Kawai taji ya yanke kiran,ajiyar zuciya ta sauke tana Tunanin yaushene yaya captain zai rike Sarautar da Allah ya bashi,kullum cikin cewa yake shi an cuceshi anhadashi da aiki,daman ma tana iya bakin kokarinta da batason mai zai yi ba,tashi tayi tsam ta Wuce shashen Ni"ima don batajin dadi tun jiya tana ta fama da amai da zazzabi likita tazo ta gwada ta ta tabbatar da ciki ne da ita
Koda Azeema ta isa shashen Ni"ima chan ta sameta kwance su Jabir nata duduma kanta,shida Sajida,Ummah kuma na gefe tana wasa,Afiya babbar banza ta zaune kan kujera tana ta lissafin banza,domin itace sak mahaifinta kwata kwata bata da yawan Mgana,ko zasu kashe kansu bazata tataba tankasu ba,tsawa Azeema ta bugamata tana Fadin"zan makeki yanzunan,wawiya kawai kina ganin bata da lafiya bazaki iya hanasu damunta ba,ammh kina zaune kamar wata sokuwa.."Narke Fuska Afiya tayi kafin tace"To ni Ummi ya zanyi dasu.."Harara Azeema ta sakarma kafin tace"Maza kwashesu sukai su Shashen momy yanzu"Dakai ta amsa kafin ta mike taja hannun Ummah da Sajida jabir kuma ya bisu abaya,don sunsan hali Azeemar bata musu da wasa saboda taga kaf masarautan babu mai Kwabamusu yara,suna ta Abunda suka ga dama,karisawa tayi ga Ni"ima wacce ke kwance ta zauna agefenta tana Fadin"ya jikin naki Uwar biyu.."Yar dariya Ni"ima tayi kafin tace"Wata uwar biyu nima Ummi wlh bani son cikin duka duka Shekaran Ummah daya fa"Yar dariya Azeema tayi kafin tace"lalle nema Mami,toh Tun Wuri ki maida wannan mganar ki hadiyeta karki bari Maimartana yaji,don ranki sai ya baci,kin manta na sanar dake su Afiya nada Shekara daya na samu cikin Sajida,ki godema Allah bata da Wani rigima kina yayeta ki mikomin ita nan,in zasu tafi nageria hutun karshen Shekara su tafi ma da Ummah da takwaranta don tana nemanta.."Jinjina kai Ni"ima tayi kafin tace" To Shikenan Allah ya kaimu yakuma saukeni lafiya"Da Ameen Azeema ta karba kafin tafara kalle kalle tana Fadin"Mami nifa wlh ina jin kamshin maimartabana,anya baya na nan shashen kuwa.?
mikewa Ni"ima tayi tana Fadin"kema kinsani yanzu haka shashenki yaje bakinan,shine ya biyo sawu,dama ana Cika awa biyu baizo ya ganki ba,ai maimartaba sai yallabiyansa.."Tafada tana yar dariya ita ta ganshi Tun sanda ya Shigo falon,hannu yasaka mata abaki alaman tayi Shuru ya make bayan labule.
yar Dariya Azeema tayi kafin tamike tana Fadin"Au kema kin biyema su goggo ne,To shikenan ni kingama tafiya ta Tunda Abun hakane.."ko taku batayi ba yayi caraf ya dagata sama yana juyi da ita,ihu taso ta saka ya damke mata baki yana dariya kwabe Fuska tayi ta Maki rawaninsa sauko da ita yayi ya rike hannunta yana Fadin"Ke baki da kunya Sarki guda kike duka ko"Hannu ta daga takara makemai kewa tana Fadin"Bakajin mgana ko bance karka fito ba,sai angama zaman fada ba? Tafada tana murde kunnensa dake cikin Rawani,rike hannunta yayi yana Fadin"Wayyo Allah yi hakauri mama Azeema.."Yafada harda matso ido,gabadaya dariya Ni"ima da Azeema suka saka harda tafawa,hararansu yayi kafin ya hade rai yana kallon Ni"ima yace"Dukkanku kallon ku nake,kwana biyun bawacce ke kula dani,ke ya nuna Ni"ima Tunda kikayi ciki shikenan kifara lalaci baki da aiki sai barci da kwanciya,ke kuma ya nuna Azeema,baki da aiki sai yima yara Fada da dukkansu,da anyi mgana sai kice kada abarsu su sangarce,ammh ga aikin mijinki bakya yin ko daya,Allah Zaku sani ne,Aure zan kara dama Sarkin Garin dosso yamin Tayin Diyarsa gimbiya Aisha.."
Azeema ce tayimai wani kallo tana Fadin"au Allah to sai me,Toh Allah kawo ta lafiya ko tazo mungama kwashe romon da sauran wani mazantakan ka sai dai Ta auri saura wlh ko Mami?"Kai Ni"ima ta gyada tana Fadin"Mema zatayi da Tsoho wanda duk baki yacika da goro.."Dukkansu suna mgana ne yana musu wani kallo,sai da suka gama kana ya rike baki yana Fadin"Kutumelisi,ke yanzu nine zaki kallah kice kungama kwashe romon ko? lalle yaron to ko Rabi baku kwasa ba kekuma kina wani narkewa kamar ta Allah ni kikecema bakina duk goro ko? Toh duk na gode da gulmata da kukayi Allah ya kamaku,daga yau duk wacce tazo min Turakata nida ita ce"Yafada yana juyawa har zai Fice ya waigo yana kallon Azeema yace"Ke...."suka dago atare,Nunata yayi yana Fadin"Wuce ki koma Shashenki ko nazo nayi kasa kasa dake.."Tura baki tayi zatayi mgana yafara takowa zuwa gareta saurin Fara tafiya tayi tana kunkuni Ni"ima dake zaune tayi yar dariya tana Fadin"Yauwa tarata kutafi,ni Allah ma yau na yafemiki zuwa turakar Ummi,ban iya Fitinar mijinki,ba daman na dan kwanta sai yace nacika lalaci,kiji dashi har cikina yayi kwari..."Saurin waigowa Azeema tayi tana Fadin"Wa..? No..No yarinya bafa zai sabu ba,ban karba ba kuma bazan karba,nima ai in inada cikin bamai daukemin hakanan nake hakuri so kema ki hakuri gaskiya..."Tafada tana hararan Aliyu dake mirmishi.
Hannuta ya warfo yana Fadin"Ke rabu da ita tama yarda tagama mungode Mamin yara,kamar kinsani dama ta rage kula dani.."Yafada yana Rumgemta kokarin kwace jikinta take,ammh ya riketa kam,itako Ni"ima ganin Abun nasu bana kare bane,sai kawai tatashi ta Shige kuryan dakinta tana kokarin maida hawayenta ta yarda takuma sani Aliyu ba kowa ya biyoba sai Azeema dama ita yazo nema,kullum kafin atashi Fada aganshi sau uku ashashen Azeema,ko agaban waye baya iya boye son da yakemata,sai dai ita Azeemar macece mai tsananin taka tsantsan,saboda Ni"ima in yayi mata wani Abun sai ta basar,ammh ko ajikinta Shiyasa tace tace taji dashi cuz tasan duk mganar dayake ita yake bukata ba ita ba,share hawayenta tayi kafin ta Furta"Alhamdulillah nagodema Allah da tarin Ni"imarsa.."
Haka Aliyu ya tasa Azeema har zuwa Shashenta,suna zuwa taja ta tsaya tana Fadin",haba...Haba wai meyasa kake hakane don Allah..."bata Fuska yayi yana fadin"Kuma Shikenan saboda ita na hana kaina Abunda nakeso,look Azeema ni bani na roketa ba ita gata ya kamata ta barmiki kwananta har ta samu lafiya,to kuma laifi ne don nanuna murnata Afili naga ke matatace kuma kowa yasani kece Fitilar raina,kinga wlh in kika karamin mganar wanchan mata billahil Azim zan iya sakinta takoma garinsu kowama ya huta,haba kinfa dameni dama kin amince in auretane don ki dinga hanani jin dadi dake ehe..."?Yafada yana daka mata tsawa idanunsa sunyi jawur,ganin haka yasa ta zabura tafada jikinsa tana fadin",Wayyo na Tuba,bazan kara ba Allah huci zuciyar Gwarzon Azeema.."Fushinsa ne ke sauka jin yadda take kara kamkamesa,Hannunsa yasa Rumgumeta yana Sauke ajiyar zuciya Wuyanta yake kissing yana Fitar da Numfashi kafin yace"Ya wuce,ammh ki kiyaye,ni banga laifi na anan ba kawai kawai.."Yake fada da alamun haryanzu Abun nacimai Tuwo akwarya.
Dagowa tayi tana Fadin"Toh naji ammh don Allah zan Rokeka alfarma daya..?hade gira yayi kafin yace"Fadi indai bazata hanani jin dadi ba.."ware ido tayi kafin tace"Bazata hanaka ba insha Allahu,dama zance ne don Allah kadaina Satar Fitowa daga fada kana zuwa Shashena,wlh kowa yana kallonka harta bayi da Fadawa suna lura da Abunda kake,kada hakan ya rage maka daraja don Allah kadaina zuwa,In kanason ganina kamin waya sai nazo Turakarka na sameka.."
Wani kallon tara saura kwata yake mata kafin yace"Karma kikara hadani da Allah malama,don wlh bazai samu ba kikama bakinki kawai malama.."Yafada yana sakinta juyawa yayi zai Fice kafin yace"Ki saka ashirya kayan Yaran nan,Gobe in Allah ya yarda Umar zai biyo shida matarsa zai Wuce dasu Nageria suje suyi hutun karshen Shekara gidan Kawu.."Da kai ta amsa kafin tace"Nima dazu mukayi waya da Zafira tace,suma suna nan zuwa hutun karshen Shekara,harda Haisam da Safaru,wacce in tazo bazata koma ba,sai ta haihu.."Dan tsayawa yayi kafin ya waigo yana Fadin"Happy Family kenan can't wait naga Su Dudes an zama iyayan yara"Yafada yana yar dariya,Azeema dake tsaye taga yakara mata kyau batasan sanda ta ruga ta fadamai ba Tana Fadin"Har Abada bazan daina Fadan ni mai sa"a bace..."Dagata yayi sama yana juyi da ita yake Fadin"A"a Pretty bake bace mai SA'A nine mai sa"a dana sameki amtsayin matata kuma uwar ya"yana..."Yafada yana Sauko da ita saitin bakinta ya dora lebenshi yana sakin mata nishi,kamkameshi tayi tana wani lumshe ido,Aliyu ya riga yasan lagonta,bakin kawai ta budemai ya cafki harshenta,yafara kissing dinta in a romantic way,tsayuwa taneman fa gagaransu,ganin zata Fadi ne yasa ya Turata kadan Tafada kan kujera,cikin kwarewa ya bita ya dan Doramata nauyinsa kadan yana kallon Kwayan idonta kafin ya Furta cikin Wani yanayi.." _*PREETY KE TA MUSSAMMANCE...._*.."Yafada kafin ya maida bakinshi cikin nata,suna cigaba Da kissing din juna cikin alamun Fittan hayyaci,Ina ganin haka na Rufe littafina da Birona na juyo ina mirmishi na Fita daga masarautar gabadaya Araina inajin Dole na bar Rayuwar Azeema da Aliyunta hakanan,ina cikin jirgin da zai maidoni Nageria nayi mirmishi nima na Furta.." _MASU KARATU KUMA NA MUSSAMMANE_……'
*ALHAMDULILLAH NIMA MAI RUBUTUN TA MUSSAMMANCE.....*
*Tammat bihamdullah Duka duka Anan Na kawo karshen Littafin ALIYU GADANGA.. !Fata kuskuran dake ciki Allah zai dubi Rauni na ya yafemin,Ladan dana samu Allah ya rabamana tare dani da masu juriyan bin wannan littafin Tun daga Farko har karshensa Ameen*
_Godiya ta mussaman ga kungiyata Daya tamkar da Dubu Wato *INTELLIGENT WRITER"S ASSO* ,Allah yakara hada kanmu gabadaya...Sai godiyata zuwa ga Uwata takaina *HAUWA S ZARIA* tare da Diyata,diyar kwarai irin albarka Wato *RAHMA ABDULNASEER NIGER* LADINGOTA😘Sai ke Sahibata *HAFSART MUSTPAHA* know as HAFNAN,tare da my Sisi of life AISHA ALTO TA😘Bazan Rufe wannan littafin batare dana ambaceku ba,domin kunbani daukkan guduwarku akan wannan littafin domin yazo masu karatu yadda yakamata ina rokon Allah ya saka musu da alherinsa,yakuma bar zumunci,Bazan manta da mika Sakon godiyata ba zuwa gareku ba *HASSAN TANKO* tare dakai *HUSSAIN 80k* Bisa yadda kukayi ta jimarin yada wannan littafin kama daga Fbuk zuwa Whattsop,Ubangiji kadai zai iya biyanku ladan Abunda kukayimin Allah ya biya muku bukatanku na alheri...Sai kuma daga karshe bazan manta dakuba masoyana ba Aduk inda kuke,Hakika naga soyayyah da kauna wacce bata yankewa dalilin wannan littafin,godiya ta mussamman ga wadandan gidajen da sukayi ta jimari tare da hakurin bina Tundaga farko har zuwa yau da zamu karkareta irinsu *JANAF NOVELL 1,2,ALIYU GADANGA FANS 1,2,3,4,ZUMUNTA NOVELLA,TASKAR LITTAFAN HAUSA,AISHA ALTO NOVEL,LADINGO FANS,BENECIAL WRITER'S FANS,INTELLIGENT FANS1,2,HAFNAN NOVELLA,AUFANA TRUE FANS,SIS NAJA'ART NOVELS 1,2,FIKIRAR MARUBUTA,TASKAR MARUBUTA,ZAUREN KAHDIJA CANDY * Daga karshe zan mika sakon Jinjina tare da Lambar yabo da kokari wajen zuba comment zuwa wannan sansani ko nace zaure na *AZEEMAR GADANGA FANS* Bakina yayi kadan na mika kalmar godiyata gareku sai dai nayi muku fatan Allah yabiyaku da alheri yakuma bar zumunci har Abada_
_*Kafin nayi muku sallama gawani Albishir din danake tafe muku dashi....Akwai sabon Novel dina da zai Fita kwananan mai Suna MALIKA MALIK..(Sai na Rama..!)..Yakukaji salon,kunji sunan yagirgiza ku ko? ai daga jin sunan kusan cewa za"a zuba iko, takama girman kai tare da isa,MALIKA MALIK bata son komai sai Rayuwar jin dadi,tataso cikin gata da Dukiya mai yawa,tare da soyayyar mahaifi wanda shikadai gareta..,MALIKA MALIK,Bata ganin kowa da gashi harta ko matar mahaifinta wacce take rokonta bata taba mata kallon arziki ba,MALIKA MALIK bata girmama kowani aiki Aduniyan nan sai kasuwanci,Acikin hakane tayi Ratse ga rayuwar wani dan Saurayi wanda yake ci yasha daga Kakin DAN SANDA,ammh Rana tsaka MALIKA MALIK TA zage kakin Yan sanda tas,wands cin zarafin yayimai ciwo,wanda lokaci daya yaji yana bukatar zama DAN SANDA kodon ya nunama MALIKA MALIK ,Iyakarta sai ya Aureta da aikin yan Sanda yakuma Rataye ta dashi har karshen Rayuwarta YAYI MA KANSHI ALQAWARIN...MALIKA MALIK....(Sai na Rama..!)*_
*Yakukaji Abun,koya wannan badakalan zata kasance duk sai kun biyoni cikin Littafin MALIKA MALIK...Ammh ta hanyar Nunamin soyayyar dakukemin da N200 kachal👌Zaki sha karatunki Tundaga farko har zuwa karshe,ina mai tabbatarmiki bazakiyi Nadama ba,sannan ga wani karin garabasa,HAFSAT HAFNAN,gwanarku marubuciyar FATALWAR MIJINA,HIBBATULLAH,KAICHON SO..,Itama Tazo muku da wani lbrin cikin nata salon mai Taken KISHIN MATA💥Haba ai ku daga jin sunan ma basai na tsawaita mgana ba,kusan Abunda ya kunsa,mata ku matso kusa domin ga dama ta samu ta yarda zaki ga yadda ake kishin ilimi,ta yadda zaki kwace mijinki ta Ruwan sanyi babu boka babu mallam,kiga salon kishin wayayyin mata kiga salon yadda ake Rikita miji,kiga salon yadda zaki samu miji atafin hannunki,chai kada na cika ku da Surutu u we all wach dis in KISHIN MATA,Wanda zaki sha karatunki Shima akan NAIRA 200kachal👌ki amfana da Abubuwan da kudin kima sai da rabonki,ga kuma karin garabasa gamai bukatar Siyan biyu KISHIN MATA DA MALIKA MALIK,zai biya N300 kachal👌ammh gamai bukatar Daya zai biya N200 kachal shima...Karku manta gwanayenku ne TAGWAYEN KAWAYEN MASU ABUN MAMAKI... HAFNAN DA JANAFTY KU SUKE FATAN KUNUNA MUSU SOYAYYARKU AKANSU TA HANYAR FARANTAMUSU WAJEN SIYAN SABBIN LITTAFANSU*
_Take Note Koda kudinki sai da rabonki hajiya,biya N200 kachal ki mori Abunda da Dubinki bazaki samu ba...._🙌
*DON NEMAN KARIN BAYANI KU TUNTUBI WADANNAN LAMBOBIN*👇
09060067488 ko kuma 07065481260
*Janafty...*
*Intelligent writer's asso..*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng