da"aka Sake maimata atisayen Allah bai hadasu ba,Jabir ya sanya Ranshi kawai Raina masa wayau Aliyu keson yi don yasaba tunda Halinsane,kiri kiri kana Tambayanshi Abu,sai yayi maka banza koda yasani,ko yashiga Raina maka hankali.
*Bayan kwana biyu*
_Gombe_
Yau Azeema Tafara Jarabawarta ta WAEC sun Fara da Pratical Chemistry,karfe biyu sukaje suka dawo biyar,koda tadawo duk ta gaji,goggo nata yimata sannu,kan kujera ta Jabe tana cije baki,yanzu bata wani karfin jiki tafiya kadan takeyi taji tagaji Tafara haki,taji Sauki sosai karfin jikin ma babu laifi tasamu mganar abinci ma tanaci shima,duk da ba sosai ba,cin goribane sai Abunda yayi gaba kuma don ba raguwa yayi ba.
Sai dai Abu daya dake damunta Shine Tunda suka dawo asibitin Kewa tare da Son kasancewa da mijinta ke damunta Wani lokacin rasa inda zata saka kanta take,sai dai ta Shige daki tayi ta kuka,tana Jin haushin kanta na yarda ko ada batayi wannan Jarabar ba sai yanzu,kullum dakyar take barci saboda muradi da son kasancewa da Yaya captain ammh Abu yaci Tura,gashi kullum Abun baya raguwa saima gaba gaba yake,haka in Abun ya ciyota zata saci wayar goggo ta Shige Tiolet talalubo Nombar Yaya captain takira,sai Tafara ringing watarana ma harya dauka sai tayi Saurin takashe tana jin haushi datakaicin kanta,yanzu in yadaga sai tacemai miye? Tace yazo tana cikin Tsaninin bukatarsa? haba aiko ba abunda yahadasu bazata iya ba,balle dama Tana Fushi dashi,datayi wannan Tunanin sai tayi Saurin Fitowa tana Share kwallah tayi hanzarin Ijiyema goggo waya a inda ta ijiye,shiko yana ganin kiran goggo,in yana busy ne xai bari daya samu sarara zai kirata,da goggo ta dauka bayan sungaisa sai yace"Goggo naga kiranki,Allah sa bawani laifi nayi ba.."Goggo da mamaki zatace"Kirana kuma? anya bani bace sai dai ko in Azeema ce",Mamaki ya cikasa kullum aka kirasa da nombar goggo daya kira goggo zatace ba itabace to waye"?Azeema ce? Daya Fahimci haka dayagani, zai yanke sai yayi Saurin kira,ammh har takarishi ringing bata dagawa,wani lokacin in yayi sa"a tadauka,ammh mganar Duniya zai mata taki cewa ko Uffan,yarasa meke damun Azeemar,koda ya tambayi goggo sai cemai tayi lafiyanta kalau babu Abunda ke damunta,bai yarda ba,yadai bar mganar ne,zai yi kokarin zuwa koda a asati na sama ne.
Ko yanzu ma datake cije bakin,Abunda ke damunta kenan,Tun amkranta Abun ya isheta,dakyar ta dawo ita wlh tama Rasa wannan Jaraba,ace wai tana Bukatar Namiji Abun kamar wani Asiri,goggo data Shiga kichen ta daukomata Ruwa tazo ta isketa tana yamutsa Fuska tana wani mele baki,kallonta goggo tayi kafin tace"Wai duk gajiyan ne? kwanciya tayi kan kujeran tana Fadin",Eh goggo kaina ke ciwo..'"Tayi karya ijiye Ruwan goggo tayi tana Fadin"Ash sannu,bari na kawo miki panadol bayan kinci abinci sai kisha,sai fa ahankali yanzu keda barin laulayin nan sai ciki yayi kwari,Allah ma ya Soki bakya Miyau da Amai.."Tafada tana komwa kichen,tana Ficewa Azeema taji kuka yazomata ta danne da hannunta bataso goggo tajita ganin kukan yana so yayi karfi,sai tatashi da gudu Ta Shige bedroom ta fada Tiolet kafin ta Fito da kukanta,tarasa wazata Fadama damuwarta,kowani ciwo gareta ne,kodai zata Fadama goggo su koma Asibiti ne? don Tana Tunanin bata da lafiya,ta dade tana kuka kafin ta Tube kaya tayo wanka Ta fito,sai da tafara gabatar da sallar la'asar kafin taci abincin da goggo ta kawo mata Danbun Shinkafa da zogale,yayimata dadi dayake ta bankada yaji,har sai da goggo ta dauke Roban yajin tana Sababi,batasha mganin ba sai da sukayi issha"i kana tasha ta kwanta ammh bawai don tana jin barci ba,cikinta ne juyawa,babu Abunda take bukatar sai lafiyar yaya captain,don Hakurinta yakusa karewa tarasa meya sameta ne,kodai wata Allura akayimata asibitin? gaskiya tanajin da wata kasa😂
Lalle Azeema kina Ruwa😹Toh duk cikin gadanga ne ya jawo haka,ai shi gadanga in yaji lbri Kakarshi tayanke saka😛😂
•°•°•°••°•°•°•°•°••°•°•••°
_Babbar headquater yan sanda na garin gombe_
Ababbar Headquater su na nan garin gombe aka kai Azeema aka sakayata,babu fada ba zagi,ba duka sai dai zaman waje daya da Takura,sai kuma Rashin samun barci ga Sauro kamar mutane,ga kudin cizo ga kwarkwata,da suke bin jikin mutane,sai Rashin abinci mai kyau,watarana ma sau daya ake bata Arana,Tun Azeema na ganin Abun Wasa har ya wuce Tunaninta bata yi Nadamar Soyayyar yaya captain datakeyi ba,ammh tafara Nadamar mugun halinta Da Zigan Shedan gareta,domin Tunda aka kawota take Fama da wani ciwon kai mai Tsanani,ga Nauyi da kirjinta keyi,saboda yadda Abubuwa sukayimata yawa,bata da wani aikinyi sai kuka,Tanaji Aranta indai bata samu captain ba,toh sai dai Tarasa rayuwarta don Tun yanzu Tafarajin Alamun Rashin Captain gareta Abu ne da zai iya sawa tarasa rayuwarta.
Haryau da"a kawota aka sakayata bawanda yakara lekota,balle abi ta kanta batama kara ganin kowa ba,sai Wadanda ke kawomata abinci,basu cemata uffan,itama bata ce musu iyakarsu su ijiye Abinci su Rufeta su kara gaba,Abincin ma sai yazamana ba kullum take ci ba,sai dai tatasa Abinci agaba tana tsiyayan hawaye,Tabbas Azeema tafara Nadamar Abunda ta aikata,ammh wannan Soyayyar datakema Captain babu Abunda yaragu saima karuwa.
****************
_Kaduna_
Yau dai yawon Umar yakaishi har Wajejen da gidajen su captain suke zaune,hakika wajen ya burgesa balle yadda aka Tsara gidajen ajera komai iri daya babu bambamci,kamar wani Estate,wajen yamatukar burgesa sosai Shiyasa yake ta Daukan Gidajen hoto,Yaji yana kaunar Sojojin Nageria domin Sun Fisu moran Abubuwan yaki da Sauransu,Yau din sanye yake da kayan gida,riga da wando black and white,sai ya sanya bakar jaket kansa babu hula sai Nannadaddan gashinsa daya murde waje daya,kana kallonsa zaka san wannan Buzu ne na gaba da baya.
Ta bayan gidajen ya bullo,shiyasa bai Kawo gidan Aliyu ba,sai da ya wuce na Jabir,gidan Aliyu yana Jerin Farko ne,don Shine No5,yazo ta wajen kenan yana Daukan Hoto,tare da video,tsaye yayi cak yana bin wajen da kallo,lokaci daya yaji yanayin jikinsa ya canza,tsayawa yayi yana waige waige kafin kuma ya dawo ya cigaba da Abunda yakeyi.
Aliyu dayake sanye da kayan Jc Riga da wando ya bude kofa ya Fito,kafarsa sanye cikin wani Farin takalmi,domin duka kayan jikinsa Farare ne,yana Fitowa yaci karo Da Umar ya juya baya yana Daukan Hoto,ta bayanshi Aliyu ke kallonshi ammh sai da gabansa ya Fadi,yayi baya yana laluban wayarsa Jabir ya Turama Text da cewa",_Dude come out..I think na kama wani dan leken Asirinmu_.."
jabir dake kokarin Fitowa Jugging yaga sakon Aliyu da hanzari yakoma daki ya sako karamar bindigarsa ya cogeta abayan wandonsa Ya fito,yana Fitowa yaci karo da Umar,wanda yagama Daukan baya ya juyo ta gaba ta wayarsa yana Dauka karaf ko ta cikin Wayar ya hango Fuskar wani kamar Fuskarshi,mamaki yakamashi sai ya zata ko yamaida Abun Hoton ta gabane,ammh kuma wannan ai ba Kayan jikinsa bane,Kara ware ido yayi yana kallon Aliyu wanda ke Dago kai yana So yaga Fuskar Umar din,Da hanzari Umar ya Jaye wayar Hannunsa Fuskar Aliyu ta bayyyana Azahiri agabansa.
Aliyu dayake leken ganin Fuskar ko waye,Umar na jaye wayar ya Daskare Atsaye yana binsa da kallo daga sama har Kasa,Zuciyarsa na lagude,mai kama dashi yake gani,ammh kuma sanye da wani kaya dabam,Umar ma Kallonsa yake Yana kuma kara Bin kansa da kallo,kamar yadda Aliyu keyi,Jabir Tunda ya Fito idonshi ya Sauka kan Umar,yazata Aliyun ne,yafara Taku zuwa gareshi sai kawai ya hangi Aliyu akofar apartment dinshi,ware ido yayi yana bin kowannensu da kallo bakinsa na Rawa yama kasa mgana,sai ya kafe Aliyu da ido na Tsawon Lokaci sai yakoma ya kafe Umar da ido,nan take ya Fahimci Abokinsa na gaskiya ammh fa sai da ya Sha kallonsu dakyau.
Aliyu da Shiga mamaki yafara daga kafarsa yana takowa zuwa ga Umar,wanda Shima yake takowa zuwa ga Aliyu dukkansu sun kafe juna da ido,kowannen Zuciyarsa na bugawa Jabir dake tsaye gafe sai kawai ya saki baki yana kallonsu sanda suke kusanto juna,bala"i wannan wace irin kamace komai nasu iri dayane hatta da Gashin kansu Wlh hatta Fuskarsu iri dayace babu bambamci,sai dai Shi Umar yafi Aliyu jan Fata sosai,sakamakon Mahaifiyarsa Buzuwa ce,shiko Aliyu ya surka da Fatar goggo shiyasa sai yayi Duhu kadan,Kana Aliyu yafishi Tsawo da murdewar jiki,duk da Shima Umar din ba baya ba.
Da gudu Jabir ya karisa ga Aliyu yana Rikemai hannu yace"Shine Dude wlh Shine...",Da mamaki Aliyu ke kallonsa yana bin kuma inda yake Nunamai da hannu kafin ma yayi mgana Jabir ya rigasa da cewa"Shine nagani Ranar,na zata kaine wlh Shine..."Aliyu bakinshi ma yakasa mgana Illah kurama Umar ido dayayi Shima Umar din agaban Aliyun yaja ya tsaya yana kallonsa kur ko kiftawa bayayi,atare kowannensu yanuna dan'uwansa yana Fadin"Waye kai...? Suka Fada bakinsu na Rawa atare.
Mirmishi kowannensu ya saki ganin sun samu Gamuwar mgana atare,Jabir dake gefe yayi tsalle gefe yana fadin"Wlh Allah Dude har mirmishinku iri dayne,wai kodai Ku yan biyu ne,baka sani ba.."Yafada yana Rike haba Abun fa yabashi mamaki,hannu Aliyu ya saka a aljihu yana Fadin"I don"t Think so Dude ai da goggo ta Fadamin,ammh kuma meyasa nakejin wani Abu game dashi,inajin zuciyata na wani Rawa in ta kalleshi.."Yafada yana kallon Umar din.
Umar yayi ajiyar zuciya yana Fadin"Nima haka nakeji Araina,zuciyata tana gayamin Kai din wani ne agareni,ka taba zuwa Niger ne..?Kallonsa Aliyu yayi yana fadin"Kai daga chan kake? gyada kai Umar yayi yana Fadin"Eh ina daga cikin Sojojin gamayayyar nan,."gyada kai Aliyu yayi kafin yamikama Umar din Hannu yana Fadin"Good ni kuma Sojan Nageria ne,am *CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU* Kaifa..? Umar yaciro hannu da niyar yamikama Aliyun ammh jin Furucinsa na karshe yasa yayi Saurin dauke hannunsa kamar ya razana gabadaya idonsa awaje yana nuna Aliyun.
Jabir da Aliyu suka bisa da kallon mamaki kafin Aliyu yace"Lafiya kuwa...?Bakin Umar na Rawa ya nuna kansa yana Fadin"ni...Ni..Ma Suna...na *UMAR ABDULNASEER TAMBARI BUZU* kuma Tambari buzu masauratarmu ce,mukadai keda wannan Sunan ta masaurata,kuma mahaifina Shine *SARKI ABDULNASEER TAMBARI BUZU MAI MULKAN MASAURATAR TA TAMBARI BUZU WACCE KE YANKIN AGADEZ*...!
gabadaya daga Jabir har Aliyu daskarewa sukayi Aliyu dayaji wani Abu ya wucemai ta makogaro,yayi Saurin Riko kafadun Umar yana Fadin"Da gaske kake yi? yafada kamar yafita hankalinsa Umar ya gyadamai kai,kafin ya samu zarafin mgana Aliyu yace"Mahaifinka yataba zuwa Nageria achan baya,ma"ana katabajin lbri..? Shuru Umar yayi kafin yace"Eh Tabbas Abbah ya Fadamin shima yayi Rayuwa A Nageria,ammuh bazai iya Tuna a ina ya rayuwa ba,balle ya Tuna da Wasu Ahali yayi Rayuwa ammh Tabbas koda zan Taho din nan ya jadaddamin shima yayi Rayuwa A Nageria.."
Aliyu da Wasu hawaye masu dumi da sanyi suka wankemai Fuska,yayi Saurin Rumgume,Umar yana Kuka Muryansa abude yake Fadin"Wlh Dan"uwa ne,dan"uwa ne yau naga wani nawa yau na hadu da jinina,yau nazama kamar kowa yau zanji lbrin mahaifina,wanda banta gani ba Tunda nazo Duniya Allah na godemaka Alhamdulillahi..',Yake Fada yana kuka da duka muryansa yana kara kamkame Umar.
Umar dake tsaye,yaji Shima hawaye sun kawomai,ya kamkame Aliyu shima hawayensa na diga bisa bayansa yake fadin"Hakika zuwana Nageria yana da Babban Sanadi,da kuma sila,ammh babban dalilin Shine,domin na warwarema Abbah mafarkinshi na Shekara da Shekaru,hakika Kana da nasaba da damuwar da maimartaba ke Shiga na mafarkin wata mata da Da'n ta suna halin Neman Taimakonsa da bukatarsu,kaine Wannan Fassarar mafarkin kai ne wlh.."Yake fada yana kuka Shabe shabe,Aliyu yana jin Abunda Umar yace sai wasu hawaye suka kara gudunmai bisa kuncinsa yana Dariya da kuka ya dago yana Fadin"Kai dan"uwa ne yanzu? Ashe zanga wannan Ranar? yafada yana kara kamkame Umar din Shima kam ya rikesa yana Fadin"Ba Dan'uwa kadai gareka ba,kana da kanne da iyayye bayan mahaifa da wasu Ahali masu yawa" Kukan Farinciki Aliyu keyi kamar wanda akace zai Shiga aljannah.
Jabir dake gefe shima Sharen kwallah yake yana dariya,kawai baisan sadda ya saka hannu yana basu Tafi ba Raf raf,Aliyu ya dago yana kallon Jabir,yadda yaga yana hawaye ga Dariya yana yi lokaci daya Hannun ya mika masa yana Fadin"Taho Dude taho,Katayani murna nima yau naji lbrin Ashe nima da,ne kamar kowa ina da uba.."Yafada yana dariya da hanzari Jabir ya isa garesu Aliyu ya hadasu ya Rumgume yana Ta hawayen Farinciko,kafin ya sakeshi ya Riko hannu Umar yana Fadin"Taho muje cikin gida mganganun bana Tsayawa bane.."Yafada duka hakoransa na waje,Rikesa Umar yayi yana Fadin"Toh *YAYA..*...."Wani Farinciki ya lulllube Aliyu wanda baisan sadda ya jawo kafadan Umar ba yana mai mirmishi mai kayatarwa,Jabir dake biye dasu shima yana mirmishi Farinciki ya cikashi yana mamakin Baita ganin kukan Aliyu ba,koda kowa mai zai Faru dashi,ammh yau kam yaga kukan Farincikinsa.
__________________
*Kwana Daya daya wuce*
*Agadez masarautar Tambari buzu*
Da Sulasainin Dare ni,wajen karfe uku da Rabin agogon Niger,Maimartaba ne ke kwance bisa kayatattacen gadonsa yana barci,gefensa kuma gimbiya Fasilatu ce,don ita keda Turaka Aranar.
Kamar mafarki taje muryan Maimartaba yana kiran wani Suna,bata maida kai ba,sai tajuya zata koma barci,ammh sai taji mganar maimartaba tafara Fita yana kiran Wani Suna wanda bata gane ba,kuma da alama Sunan mace ne,da hanzari ta mike tana jijjiga Sarki take Fadin"Ranka ya dade..!Ranka ya dade.."!ammh Shuru sai Rike kansa yake yana motsi da bakinsa wani Suna yake kira,ammh bata Fahimtar meyake fadi,ai da hanzari ta diro daga kan gadon,ko alkyabba bata tsaya sakawa taja katon Mayafinta ta Rufa ta fice da gudu,tana zuwa Kofar Shashen maimartaba Fadawa suka taso Hankalinsu tashe ko Sauraransu Gimbiya Fasilatu batayi ba takama gudu sai Shashen Ummah mai babban daki,masu tsaron kofarta suna ganin gimbiya na gudu suka dare,suka bata kofa ta Shiga,Ummah mai babban daki na zaune kan sallayatar ta idar da sallah kenan tana Addu"a Gimbiya Fasilatu tashigo tana haki take Fadin"Ummah kizo maimartaba wani Abu yafaru dashi..."Da hanzari Ummah ta mike tana fadin"Innalillahi wa'inna Alaihirraju'un..Meyafaru dashi? tafada tana Jan alkaybbanta ta sanya tayi gaba tana kiran Sunan Allah,kuyangu duk suka Firfito da Fadawa suna raba ido,basa fatan ace wani Abu ne ya samu maimartaba da gudu gudu sauri Sauri suka karisa shashen nashi yadda ta barshi haka sukazo suka sameshi sai da wannan karon da karfi yake kiran Sunanta" *SUWAIBA...* "Ummah da Gimbiya fasilatu suka kalli Juna kafin su maimata Sunan atare"Suwaiba kuma...? Hawa gadon Ummah tayi tana Rikoshi addu"a take tofamai tana Shafamai bisa kai,cikin ikon Allah ya zabura ya Farka yana kuka yake fadin"Wlh na Tunata,na Tuna *MATATA SUWAIBA...* Yafada yana rike hannun Ummah.
Dukkansu sandarewa sukayi saboda namaki Ummah tabishi da kallo kanshi na bisa cinyarta,atare Ummah da gimbiya Fasilatu sukace"Matarka kuma...? gyada kai Maimartaba yayi yana Fadin"Eh na Tunata,yau Allah ya nunamin Fuskarta Suwaiba ce,lokacin dana bar gida ummah,dasu na zauna har mahaifinta ya Auramin ita,daganan ne kuma Ummah Tunani na ya Shafe na Rasa awani yanki ne ?wani gari ne,?na kasa Tunawa ummh ammah yau tabbas na Tunata Suwaiba ce wlh..."Yake Fada yana dafe kansa.
Ummah da Gimbiya Fasilatu suka kalli Juna kafin su bisa da kallo,Girgiza kai Ummah tayi kafin tace",kira Likitanshi yazo ya Dubashi yanzu...'Jin haka yasa ta Fice da Sauri ammh kalaman mai martaba Sun bata mamaki,kamar yadda suka saka Ummah cikin Rudu.
*Janafty....*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_* Oh ni Jikar Fati😿Gabadaya yau ba"a barni nayi barcin Safe ba,gabadaya Anki barina nayi Sukuni ko"ina naje GADANGA..GADANGA...Toh gashinan Dai kada asamu masu cinyeni danya ban gasu ba😂 Nasan in ban sakoshiba,Akwai masu zuwa har zaria sucini Tara,irinsu TEAM AZEEMAR GADANGA😘Happy Lahadi day😂😜Asha karatu lafiya Masoyan kwarai*_💞💖
*Chapter 30..*
""Gimbiya Fasilatu ta kira likitan mai martaba Tasanar dashi ko mintigoma baiyi ba, ya iso masauratar,kai tsaye akayi mishi iso shashen maimartaba,koda ya isa ya iske maimartaba nata sambatu yana kiran Sunan Suwaiba,bai bata lokaci ba ya nemi da su Ummah su bashi wajen don yasamu damar gudanar da aikinshi,suna Fita ya karisa gamai maimartaba wanda ke zaune yayi Tagumi yana Ta so kwalkwalwarsa Ta tunamai Sauran Abubuwa ammh Abu yaci Tura,Likitan baiyi mgana ba,illah bude akwatin kayan aikinsa ya Fito da allurai ya harda harda ya juye a Siriji yayi mai martaba ita,wanda ko minti biyar bai karaba ya sulale yana barci,koda likitan ya Fito baice masu Ummah komai ba,illah sanar dasu dayayi"Da zaran ya Farka zai Dawo daidai Ranki Shi dade.."Sallama sukayi yatafi wanda dama Likitan Shima zuru"ar Mairtaba tsohon sarki ne,da yake ga Sarki Abdulnasser din.
Har garin Allah yawaye maimartaba Bai Farka ba,yana ta barcinsa Hankalinsa kwance,Tuni lbrin ya ishi kunnen sauran iyalansa da kuma Shamaki tare da waziri da galadima,su suka sanar da Fada cewa sarki bazai samu zama ba yau sakamakon baitashi da jin dadin jikinsa,Fatan samun sauki akayimai sai Waziri ya Karbi sarki Aranar aka cigaba da gudanar da Mulkin.
*********************
Suna Shiga cikin gidan Aliyu,suka zazzauna,Aliyu bakinsa yaki Rufuwa saboda murna wayarsa yazaro yana Fadin"Dude ni nama Rasa wazan Fara kira goggo ko kawu? yafada yana Danna wayar dariya Jabir yayi kafin yace"kira kawu first shine ke kusa goggo kuma,in son samu ne ayimata Big Suprise kawai..."Dariya sukayi gabadaya.
Umar yace"Nikuma sai komai ya kammallah zan kira video call na hadaka da maimartaba nagani ko yaya zaiyi..? Shuru Aliyu yayi yana mirmishi daidai lokacin da Kawu ya daga kiransa yana Fadin"Aliyu Gadanga ya"akayi ne? Bakinsa duka abude yace"Kawu yau Allah ya gwadamin dan"uwa na,kawu yau naji lbrin dangina,Ashe nima Da"ne kamar kowa ina da uba da yan"uwa da kanne da yayye.."Yafada idonsa na cikowa Da kwallah.
Kawu Bala dake zaune a office yayi Saurin mikewa yana Fadin"Aliyu are u Serious....? Da hanzari yace"Wlh kuwa kawu kazo barrak dinmu yanzu kaga wani Abun mamaki.."Kawu bai jira cewarsa ba ya datse kiran,alokacin yana da tattaunawa da yan jaridu,ammh ya tsallake Shida tawaganshi Suka Shisshiga mota sai bariki,tun amota yake addu"a Allah yasa Abunda Aliyu yafadamai da gaskene.
Aliyu najin karar Jiniyar motocin Kawu ya Fito da gudu,baima jira yakai ga Fitowa ba ya bude mota ya Riko hannunsa yana fadin",Taho kawu kaga wani abu.."Yafada yana Jansa zuwa cikin gidan,da hanzari ya Bishi yana kara saba babbar rigarsa Suna shiga cikin Falon kawu yaci karo da Umar zaune yana mai mirmishi Zaro ido kawu yayi yana bin Umar din da kallo,Kafin kuma yakoma yana bin Aliyun da kallo,Kawu yayi tsaye kafin ya Durkushe kasa kawai yana Fadin"Sarki ya tabbata ga Allah Shugaban kowa da kowa.."Yafada yana kai goshinshi kasa yadade kafin ya dago,koda yadago hawaye ne sharkaf bisa Fuskarsa,Aliyu ne yadagosa yana Fadin"Kaima kayi kuka ko kawu,wlh nima nayi,banta zaton zan yi Farinciki