x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - ALIYU GADANGA

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 176

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
bayyana Tuni fadawa suka Zube suna Fadin"Allah karama Sarki hakuri,Allah ya Huci Ran maimartaba Ayimana Afuwa munga Abunda baidace mugani ba kai tsaye wato Farar Fusjarka mai cike da haiba da zati,Tuba muke Ranka ya dade.."Goggo data kafe idonta kan Maimartaba Taja baya da Sauri Tana Nuna hannu,Maimartaba take Nunawa tana so tayi mgana takasa dakyar ta iya Furta"Ya..Yaa...Kassn wa...Na..Ke ...Ganii...."Tafada idonta na Kafewa lokaci daya bakinta ya Subuce ya Furta... *AB...DUL....NA....SEEEEERRRRRRR......."Kafin kawai ta Sulale zata zube kasa kafin Aliyu ya isa gareta maimartaba yayi Sufa zuwa gareta ta Sulale bisa jikinsa.





*Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

     *Chapter..32...*

  ""Gabadayansu sukayi kan goggo wacce ta sulale bisa jikin maimartaba,dagota yayi yana jijjigata yana kiran Sunanta"Suwaiba..Suwaiba.."Ammh ina ko motsi batayi,gadanga ne ya Runtuma daki aguje ya dauko ruwa yana zuwa ya duka,maimartaba ya mikasa Tafin hannunsa yana kallonsa kai Tsaye ya tsiyayamai Ruwan ahannunsa yayarfe kafin ya Shiga Shafe fuskar goggo dashi,lokaci daya ta saki ajiyar zuciya kafin tafara kokarin bude ido,tana budewa taci karo da Gadanga,sai kawu sai Umaimah da Haisam,sai Jabir dake gefe,chan ga Mardiya da madina,sai Umar dake durkushe gefe,jin ta ahannun wani ne,yasa ta dago ido Fes ta saukesu kan Maimartaba wanda ke kallonta yana kara godema Allah...

Zabura goggo tayi daga jikin maimartaba tana Raba ido don ita azatonta mafarki take,Nunashi Tahauyi tana Fadin"Yaya kaga Abunda nake gani kuwa.."Da hanzari kawu bala ya karisa gareta ya rikota yana Fadin"Nagani Suwaiba ki Natsu kikuma godema Allah dayasan zaku kara ganin juna dukkanku kuna raye.."Fashewa da kuka goggo tayi tana lafewa jikin kawu,tamaki kara dagowa ta kalli maimartaba.

Aliyu ne ya Shiga daki ya Fito da wani kafet,babba da wasu manyan Tabarmu yazo su Haisam suka kamamasa ya Shimfida atsakar gidan,saman kafet din nan maimartaba yazauna da iyalansa sai Tabarmu su Kawu bala suka zazzauna wanda ke rike da goggo yana lallashinta,Da hannu Maimartaba ya yafito Aliyu,Jikinsa na rawa ya mike ya isa ga mahaifinsa Yana kokarin zama,Maimartaba ya rikosa yana Fadin"Aliyu..."Yafada yana shafa sumar kanshi,Ummah mai babban daki ta riko hannu Aliyu tana Fadin",Sannu sabon megida.."Mirmishi ya saki yana binta da kallo,Kusa da maimartaba ya zauna yana kallon Su Zafira,wadanda ke dagamai hannu suna dariya,shima dagamusun yayi yana mirmishi gimbiya Razeenah ta Dafa kan Aliyu tana mirmishi tace"Sannu magajin Sarki.."Tafada tana kallon gefen gimbiya Fasilatu wacce ta cika ta batse kamar ta fashe

Goggo ce ta dago tana kallon Aliyu,wani harara ta zabgamai kafin tace"Yana raye,ammh Shine yabarmu baitaba waiwayanmu ba tsawon wannan lokacin? Tafada tana Tsiyayan hawaye sai wajen ya dauki Shuru kukan goggo kadai akeji,Ana cikin hakane sai ga mallam lawal Shida inna Ramatu Sun fado gidan,domin inna ramatu na ganin Abunda ke Faruwa takoma gida ta sako mayafi tatafi kasuwa ta fesama mallam lawal,tatasoshi kuma agaba saboda in ba dashi ba,bazata samu damar Shiga gidan goggo ba balle hartaji mai ke Faruwa,kawu na ganinshi yatashi ya rikosa yana Fadin"Alhamdulillah barka da zuwa mallam lawal kazo akan gaba don kaima kana da jibi da wannan Ahalin..",Yafada yana kariso dashi gaban maimartaba yana Fadin"Ranka yadade,wannan mallam lawal kenan uba yake ga matar da Aliyu yake aure,kuma uwa uba shi na damkama amanar Suwaiba tun bayan dana kawota garin nan,su sukayi hidima da ita har zuwa haihuwar Aliyu,mallam lawal kai kuma wannan dake gabanka Mahaifin Aliyu ne,kuma Sarki ne na Kasar Niger"Ba mallam lawal da"ake ma bayani ba inna Ramatu ce,wacce ke tsaye ta zabura tana dafe kirji da karfi ta Furta"Mahaifinsa? kuma sarkin Niger to ya akayi haka? Tafada cikin Rudewa..

Kowa kallonta yake,yana mamakin kalamata,su Maimartaba ma sun zata mahaukaciyane,ganin yadda ake kallonta ne,yasa Tayi Saurin dukar dakai tana Raba ido,Fadawa ne suka dakamata tsawa suna Fadin"Hattara dai Diyar talakawa ba"a mgana indai sarki bai bada izini ba hattara Dai..."Inna Ramatu da jikinta ke rawa ta duke ta kyarma ganinsu da bulalai,kawu ne yasa baki yace"Ku kyaleta maidakin mallam lawal ce"Shiko yana gaban Sarki durkushe kamar ya kwantamai,idanunsa sun cika da kwallah,Mikasa hannu maimartaba yayi yana Fadin"Mu gaisa Tukunnah..."Kasa mikamai hannu Mallam lawal nokewa yakeyi yana Fadin",A"a Ranka ya dade,Talaka kamata baidace na yi hannun dakai ba,Allah yakarama yawan Rai.."Mirmishi kadai sarki yayi yana Fadin"Ina Surukata take.."Yafada yana kallon goggo,wacce kanta ke duke tana Sharan kwallah.

Azeema dake Gefe tana Raba ido,Kowa yasama ido ganin yadda suke kallonta ne yasa duk taji kunya,sai tahau Sunne kai,Hannu maimartaba yadaga yana Fadin"Taho diyata taho nan ki zauna.."Jikin Azeema amace tamike ta isa gaban maimartaba ta durkushe kanta ya Dafa yana sakamata albarka,nan Ummah mai babbar daki tajawota tana Fadin"Taho nan kishiyata,dani zaki zaman kishi don kinganni nan,inba Aliyu ba sai Rijiya mai gaba dubu..",Dariya aka saka,itama Azeemar yar dariya tayi Kusa da gimbiya Razeenah ta zauna ta Sunne kai,itako gimbiya Razeenah ko ajikinta ta Rumgume Azeema tana mata rada akunne,tsam naga tatashi takoma kusa dasu Zafira wadanda ke gefe sun kame,Su jabir dake Facing dinsu su suka kurama ido suna yaba tsari da kyan yan matan,Washe baki sukahau yi Suna Fadin" Our princess daya tilo A masarautar Tambari buzu.."Dan ware ido tayi tana kallonsu kafin ta Shiga tambayan sunayensu suna Fadamata tana gyada kai...
 

Kawu Bala ne yayi gyaran murya yana Fadin"Ranka ya dade zamu so muji meyafaru ne,Tun bayan aiken da mallam yayi maka baka dawo ba,munyi nemanka har ba Adadi har muka cire da cewa baka da rai ne.."Maimartaba yayi Shuru kafin ya gyara zama yana Fadin"Ko baka Fadamin ba, Nasan cewa Allah ya karbi Ran mallam da inna..",Gyada kai Kawu yayi yana fadin"Dalilin Shiga damuwar Batanka da bullowar ciki ajikin Suwaiba Shiyayi sanadiyar Jininsa har ya hau,bai dade yana jinya ba,Allah ya karbi Abunsa itama inna bata dade ba tabishi Tsakaninsu kwana 52 ne.."Yafada yana Share kwallah,don ji yake kamar yanzu Abun ke Faruwa..

Goggo ma kuka take sosai,domin mutuwar iyayan nata sun dawo mata sabuwa,Maimartaba daya dukar dakai ya dade bai dagoba yana dagowa Sai ga hawaye shar suna zuba Fadawa keta kirari suna Fadin",Allah huci Zuciyar maimartaba,Allah ya sanyaya zuciyar Adalin Sarkinmu.."Hannu ya sanya ya share kwallar yana Fadin"Hakika munyi Rashi,Allah yajikan mallam da Inna Allah ya sanya sun Huta.."Da Ameen aka amsa,wajen yayi Shuru kafin Maimartaba yayi gyaran murya yana Fadin"

  "Kamar yadda kuka sani Nazo garin nan bani da kowa,nazauna a hannun mahaifinku har na tsawon wasu Shekaru,kafin yarda da aminci yasa ya dauki Auren yarsa yabani.." yadanyi Shuru kafin ya Numfasa yacigaba da Fadin"Tabbas koda nazo garinnan bani a hayyacina sakamakon kurciya da"akayi min,kuma aka hadamin da Sammu,wanda zan manta Asali na ,banda sunana ba"a barni na Tuna komai ba..",Gabadaya suka zubamai ido suna kallonsa,bai wani damu da kallonsa da sukeyi ba,har goggo wacce ta maida hankalinta kanshi,tayi tagumi da hannu bibbiyu,Ya cigaba da Fadin.


   *SHEKARUN BAYA*

_LABARIN MASARAUTAR TAMBARI BUZU_

 
   _Ashekarun baya Anyi wata Masaurata Akasar Niger a yanki Agadez,awannan yanki anyi wata masarauta mai Dimbin Tarihi,Tun Ada Masauratane datafito daga tsatso mai Asali,tsatsoce ta jinin sarakai,tunkan zuwan Addinin musulunci,Mutane dadama sun mulki Garin,Adalai masu kaunar talakawa da kawoma Masarauta cigaba,Wannan Masarautan Sunanta MASARAUTAN TAMBARI BUZU,Sunanta ta samo Asali ne,daga sudin buzaye ne gaba da baya,kuma sunkasance dukkansu Farare ne,dogaye masu zati da haiba,suna da jarumta uwa uba kuma Masarautane mai Dimbin Tarihi na Kudi da Arziki ko ada chan,suna da hadin kai da Sanin mutumcin juna,ba"ta samun Sabani ko Rabuwan kai ba,sai da Manya suka Fara tafiya Mulkin yafara komawa hannun kananan_


  _Masarautar ta samo Asali ne Daga mulkin Sarki ABDULGANIYU D'AN HASHIM,wanda ya mulkin Garin na Tsawon Shekaru arba"in da wani Abu kafin Allah ya dauki Ransa,bayan mutuwarsa aka Nada babban D'ansa Wato BADAMASI D'AN ABDULGANIYU,amtsayinsa na babban Dansa,kuma ya chanchanta da zama Sarki bisa la"akari da duk Abunda ake bukata ya mallakesu,Kuma yakasance Shikadai ne Namiji Awajen Sarki Abdulganiyu,Sauran Duk matane_

  _Shekaransa goma ne akan karagar mulki Ya rasu,Bayan Mutuwarsa Anyita Rigima kafin Anada Wani sarki Wato YAKUBA D"AN BADAMASI ,Jika ga ABDULGANIYU D"AN HASHIM,Wand Shibashi daga cikin wadanda suka nemi Sarauta alokacins saboda baya Ra"ayinta kwata kwata,kuma Shine na hudun ajerin mazan,kuma duka yayyin nasa su uku ba wanda bai Nemi Sarauta ba,ammh basu samu ba sakamakon basu chanchanta ba,kwatsam sukaji an nada YAKUBA bisa chanchantarsa shi yakasance yana da ilimin boko har matakin masters,duk da bai yawaita ba awanchan lokacin,sabaninsu na Arabi"an kadai garesu,sannan yafisu sanyi Hali,duk dayake karami acikinsu Adai komai ya chanchanta Toh wannan al"amari Shine tushen komai don Shima yasama Sauran yan"uwansa hassada da kyashi Aransu,acikin yayyin nashi akwai IDRISA, sai KAMALLUDEEN Sai NASAR Sune manya kuma sune suka nemi Sarautan aka hanasu,kuma gabadayansu ba ya"yan mutum daya bane,Tunda alokacin matan Sarki hudu,Mahaifiyar yakuba ne karama_

  _Su aganinsu yaya za"ayi Adauko Yakuba abashi mulki,Alhalin gasu,an nuna musu yan ubanchi,daga wannan lokacin Zaman lafiya ya kare awannan masarautan inda su Idirisa sukasha alwashin ganin bayan wannan mulki na Yakuba,bayan an Nada Yakuba,Talakawa na jin dadin mulkinsa,sakamakon yayi gadon mahaifinsa akyawawan dabi"u,ba yadda baiyi ba don ya sansanta da Yan"uwansa ammh ina Abu yaci Tura,Har Sarauta yaso ya ijiye, yatarama manya masu ruwa da tsaki a masarautar,su suka nunamai Ahir dinshi,saboda shima bayason Abunda zai kawo Rabuwan kai shida yan"uwansa,mahaifiyarsa akullum Addu"arta Allah ya tsaremata da'nta toh Ana wannan Hali Allah yayi mata Rasuwa mutuwar data girgiza sarki Yakuba yazama maraya gida da waje,toh daman yana da matansa ,uwargidansa UMMUKHAIRI yar wani tsohon Wazirin Sarki Badamasi ne,sai GIMBIYA KILISHI yar wani Sarki dake gaba da yankinsu,bayan An danashi Sauratane Yacike da MASHASHATU itama yar sarki ce sai takarshensu yar wazirinsa ne ya Auramasa ZULAIKA_

  _Allah da ikonsa Da"n sa Namiji kwara dayane tak Duka haihuwan da Matansa keyi wabi suke Uwargidansa UMMUKHAIRI ita ta Haifasa masa Shi Wato ABDULNASEER,sarki yakuba ya dauki Son duniya ya dorama Abdulnaseer,kuma hakan ya samo Asali ne daga soyayyar dayakema mahaifiyar Abdulnaseer din,girman Yaron ne aka gane babu inda Hallayar mahaifinsa Yakuba Natsuwarsa da son Talakawa Shine dalilin dayasa mutane suke kiransa da MAGAJIN SARKI,toh wannan shiya taso da Wutar kiyayyar Dake tsakanin Yakuba da yan"uwansa,akan bazasu yarda Wani dan yakuba yazo ya mulkesu ba,suka dora daramar Kwatar mulkin kota halin kaka,awannan yanayin Masarautar Tambari buzu tatashi da wani Firgici na Mutuwar Sarki Yakuba,an kwanta dashi lafiya kalau Akatashi akaga gawarsa Bisa binciken likitoci sun gano cewa ta hanyar Filo aka kasheshi tunda gayinan akokarin kasheshi da Filon har sun jimai ciwo awuya alamar sai da sukayi kokuwa da makashin_

   _Topha wannan al"amarin yasa Jama"a Dadama acikin Rudani,Ummah tayi kuka sosai,ita da tilon da'nta kai ba ita kadai ba kaf Masarautar Tambari buzu sai da ta girgiza,balle talakawan dake Yanki na Agadez,Harga Allah Ummah ta zargi wani Abu ammh sai ta boye,wanda Tun sarki yakuba na da Rai akecemata Ummah mai babban daki,sakamakon itace uwargidan sarki kuma mahaifiyar Yarima Abdulnaseer,Bayan mutuwar Sarki Yakuba aka Fara mganar Nadin sabon Sarki Alokacin Nagama Digree na akan political Science,karatun Addini kuwa Tuni nayi nisa_

   _Azama na Farko An tabbatar dacewa anine mutum na farko da"aka  kawo wanda ya chanchanta abani Sarautar masauratar Tambari buzu,domin na gaji mahaifina,wannan Shiya kara harzuka su Idirisa,wanda sun kara neman mulkin akaro na biyu,Manazarta da magabatan Zauren wakilai na zaban Sarakai basu tsaya bata lokaci ba suka Fitar da sunana amtsayin Sarkin Garin Agadez,harga Allah bani so,kuma mahaifiyatama bata so,Saboda tana zargin mutuwar Mahaifina yana da nasaba da Sarautar garin,Abisa wannan dalilin aka Fitar da Ranar daza"ayi min Nadin Sarauta amtsayin Sarki,sai Aranar Nadin Sarautar aka wayi gari da magajin Sarki an nemi ko sama ko kasa ba"a ganni ba,har angaji anfidda rai,dalilin an kwashe wajen wata biyar bani ba lbrina yasa aka Nada IDIRISA Masaurata tazo hannunsu sai yadda sukaga dama da ita_

    _Bacewata ta girgiza Zuciyar mahaifiyata wanda na kasancemata Da daya tilo Aduniyan nan rashi biyu alokaci daya,mahaifiyata tadauki dangana tare da maida kukanta ga Allah,tana Fatan in ina raye Allah ya karematani,ya kaddara saduwarmu,wannan Shine dalilin barin gidana,zuwana Nageria da Fadowata hannun Mallam duk banda masaniya akansa,Nasan dai na zauna daku,kun rikeni tamkar dan"uwanku har zuwa bani Auren Suwaiba da Mallam yayi_

   Gabadaya wajen aka sauke ajiyar Zuciya,Kawu ne yayi Saurin cewa "Ranka ya dade ka yanke wani Abu daga cikin lbrin,yaya akayi sammun da kurciyan suka sake ka har ka iya komawa gida,har tsawon wannan lokacin..? Daman tambayan dake zukatan mutane kenan.

Maimartaba yayi mirmishi yaciga da cewa………"

   _Daman Na fadamuku kurciya sukayimin  na barin gida,tare da sammu bazan Tuna asali na ba balle har wadanda zasu tsinceni suyi Tunanin maidoni gida,Bayan mallam ya aikeni da kudi nakai sako,nidai nasan na hau mota har nasauka,sai dai kafin na karisa cikin kasuwar wani al"amari yafaru dani,naji kamar Amciremin wani Abu atsakar ka,na zabura ina bin ko"ina da kallo,lokaci daya ina kallo kaina,kaina ya Daure,meyakawo nan,nan dai ba garinmu bane,nan ba Masarautarmu bane,kuma sannan wadanan mutane ban garinmu bane,kuma suma din ba Ahalina bane to ina ne nan?Tambayan dana dinga yima kaina kenan,ammh bansamu wanda zai bani amsa ba,inda Abun ya sakeni,daganan bankara daga kafata ba,tsaye nayi ina ta zare ido,kana ganina zaka Fahimci bana cikin hayyacina ga damuwa data bayyana zahiran acikin idanuna,wani bawan Allah ne yazo wucewa sai yaganni kamar cikin damuwa,koda ya tambayeni meke damuna ina zani? ban iya mai mgana ba illah FasheWa da kuka danayi,hankalinsa ya tashi ya Shiga tambaya Abunda ya faru,bazan iya maida komai illah na sanar dashi ina Tunanin Sato ni akayi,domin ni dan Niger ne,ayanki Agadez,jin wannan lbrin nawa yasa yatafi dani gidanshi da alqawarin Taimakamin nakoma gida,kwana biyu nayi agidanshi,kuma har nagama kwanakina banta tambayansa wani gari bane,kudin da mallam yabani na aike dashi mutumin yayimin kudin mota zuwa niger bayan na tabbatarmai da zangane gida,Sauran kudin kuma na dankamai,Tunda ni duk Atunani daga Masarautarmu aka satoni da wannan dukiya,Allah bai basu sa"ar cinma burinsu akaina ba,cikin dare na isa garin kai tsaye masarauta na dosa,ina kuma Shiga sashen mahaifiyata nafara isa,wacce na isketa tana tsayuwar dare,ganina datayi bata razana ba,takamani ta Rumgume tana kuka tana godiya ga Allah,tace tasan cewa zan dawo ko bajima ko badade,bawanda yasan lbrin dawowata gida sai washegari da safe,kuma adaren Ummah na Tafadamun duk irin mulkin kama karyan da IDIRISA Yake aikatawa Tare ta taimakon yan"uwansa,da irin yadda suka lalata komai na Masarautarmu,koda ummah tatambayeni ina naje,kuma awani gari na zauna,Abu daya na iya gayamata Cewa mutumin daya tsinceni ya sanar dani ina Nageria ne,ammh bayan nan bazan iya dora komai ba game da barina gida ba_

_Bata Fadama kowaba sai Awashegarin An zauna zaman Fada kwatsam sai gani na Shigo,gabadaya Aka mike ananeman guduwa,don kowa ya cire rai da ina raye,nan take kuma Sarki ADIRISA yamike jikinsa na rawa daga kan karagar mulki,yana nunani da hannu,yana so yayi mgana ammh yakasa,nan da nan sai bakinshi ya karkace yafadi yana makyarkyata anan take yasamu ciwon Shanyewar barin jiki,wanda hakkina ne ke bibbiyarsa da kuma asirin da sukamin na barin gida,Domin da bakinsa yafadi Abunda suka aikata agareni dasa hannu yan"uwanshi da iyayensu mata,da Hadin bakin Jakadiya suka kashe mahaifina Sarki YAKUBA,Tare da yimin kurciya na bar kasar gabadaya bayan sun hadamin da mugun sammu,wanda banda sunana da kasata bani da ikon Tuna komai,kuma ko bayan kurciyan ta sakeni sammun dake jikina bazai barni na Tuna wani Abu bayana ba,sai wanda zai Faru agaba,Sun sanar damu cewa sammun yana dadewa jikin mutum kafin ya sakeshi,shine dalilin daya samu damar hayewa karagar mulkin MASARAUTAR TAMBARI BUZU,jin jaka yasa al"ummah yankin Agadez da Masarautar Tambari buzu tayi tir dasu,Sarki IDIRISA Kuwa sati daya yayi Allah yayimai Rasuwa,saura yan"uwansa kuma hukumar gidan Sarauta ta hukuntasu,harda jakadiya wadanda ta yanke musu hukunci kisa ta hanyar sare musu kai,suko iyayansu mata masarauta ta koresu daga yankinta gabadaya Fadawa suka rakasu har wajen gari suna jifansu da Allah tir dasu,bayan an gargadesu da har abada kada sukara tako kafarsu zuwa masarauta_



_Bayan lafawar komai,akama bama mai wuri wurinsa ma"ana akayi min Nadin Sarkin Yanki Agadez Amsarautar Tambari buzu wanda aka kwana ana shagali,wanda al'ummah suka nuna Farincikinsu,Talakawan Agadez sun nuna murnansu sosai wanda aka dau tsawon sati daya ana Shagalin Nadin Sarautata,zuwa wannan lokacin da"a ka nadani amtsayin Sarki nakasa gane meke damuna,inaji ajikina akwai wani babban al"amari dake damuna ammh nakasa gane komiye shi,dama kuma ba"a Nadani Sarki ba sai da Na auri GIMBIYA FASILATU wacce ta kasance diyace ga sarki yankin Yamai,dake kusa damu,Bayan Nadin Sarauta ta kuma na Auri GIMBIYA RAZEENAH,wacce ta kasance jikar sarki Dosso ce,Bayansu bankara jin ina sha"awar kara aure ba,duk da sarakai suna ta kawomin Tallar Auren ya"yansu ammh na Fadama ummah cewa subarni haka bana bukatar kowa ayanzu,bayan hawa mulkina nayi canje canje sosai kama daga jakadiya dakuma masu zaman Fada duk munafukan dake tare dasu Sarki IDIRISA saida na saukesu nayi sabon Nadi tare da sabbin mukkarabai_


_Akullum matana da mahaifiyata sun san ina da damuwa Araina Ni kaina ko sun tambayeni bani da amsan da zan iya basu,nikaina cikin wani sarkakiyane nakasa gane meke Faruwa,shekara ta daya Da komawa gida nafara wani mafarki wanda ke tsayamin arai,amafarkin ina ganin wata mata da danta suna kuka suna mikomin hannu,nikuma ko ina da niyyar Zuwa wajensu domin taimakamusu sai wani hayaki ya lullubesu koda hayakin zai washe,sai na nemesu na rasa,Tundaga ranar inda zan kwanta barci sai nayi wannan mafarki,kuma Allah baita nunamin Fuskar matar ba,kullum cikin mafarkin nan nake,tun Abun baya damuna haryazo yana damuna,balle matana wadanda ke tare dani,mahaifiyata tashiga damuwa sosai,tayi tasakawa ana kawo mata malamai wai suyi mata duba su gani meke damuna,ammh ko sun zaunar dani sun Tambayeni bana iya cemusu komai,Nidai Abu daya na sani babu maiyi sai Allah toh gareshi na maida al"amarina Shi zai yayemin duhu zuwa haske,na dau tsawon Shekara talatin ina wannan mafarkin Allah baita warwareminshi ba,sai acikin wannan Sati Allah ya bayyanamin Fuskarki amafarkina Suwaiba ina ganinki na Tuna,bayan na Farka ina kiran sunanki,Sai matana da mahaifa suke ganin kmar nayi gamone,kwana biyu akwance ko Fada bana zuwa,ina zurfafama kaina Tunanin kozan iya Tuna awani gari muka zauna dake,ammh tabbasa na tuna kedin matatace,toh ina cikin wannan halin sai na samu kiran Da'na Yarima umar ya sanar dani Ragowar Abunda ya Shigemin Duhu,na ganin yaron da kika haifamin,bayan Tsananin kamaninsu kuma suna
End Ads