x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - ALIYU GADANGA

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 170

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
wajen Rashin lalacewar kafarsa tasa, kana daga karshe Dr kabirkhan yayaba da Jarumta tare da Dauriya irinta ta Da"nsu Aliyu gadanga,domin ya iya tsawon kwanakin daya dauka da wannan Rauninka ajikinsa tabbas ko acikin Sojojin shi na dabam ne,ammh yanzu haka yana dakin hutu kuma babu wanda zai Shiga inda yake sai nan da kwana biyu lokacin ya Farfado,kuma duka aikin nasa baza"a warwareshi ba,sai nan da wata biyu,lokacin suna saka Ran Insha Allahu komai yazama Tarihi Aliyu zai taka da kafarsa ya Fito daga cikin Asibitin nan yakoma kasarsa da kafarsa


Hakika su Maimartaba Sunji dadin bayanan Dr kabirkhan wanda yayi musu Shi cikin harshen Turanci,godiya sukayita yimishi,shima yana gode musu,kafin su Fito daga office din nasa maikama da aljannah Duniya,Koda suka Fito Abunda ya karanta musu,shi suka karanta ma su goggo dake waje hamdala kowa ya Shigayi Tare da Fatan Allah yasa anyi aikin cikin Nasara,basu koma masauki ba sai chan dare bayan sun leka Aliyu ta cikin glass,din inda gadon dayake kwance yake,gabada kafafunsa suna sagale ne jikin wani karfe,mai aiki da wasu Na"ura,haka hannunsa,shima an sagala shi,jikin wani Abu mai kama da roba,dai dai inda hannun yake anyi wani Filo,yadda hannun yayi bisa,kodaga chan suna hango Fuskarsa yadda tayi Haske,ammh yayi Rama sosai,dukkansu sunji dadin ganinshi domin yafi yadda suka taho dashi,addu"an samun lafiya sukayimai kafin su rankaya zuwa masaukinsu.


Kamar yadda Dr kabirkhan Yafada kwanan Aliyu biyu ya Farfado,kuma Alhamdulillah jikinsa yayi kyau sosai,domin koda likitoci suka gama bincikensu akanshi,suka Fito bayan sun bama su kawu damar Shiga wajensa,ammh banda doguwar mgana,koda suka Shiga sun Tarar da wata Nurse ta tadashi zaune ya jingina bayansa da wani Filo mai kyau da taushi,Yana ganinsu yafara mirmishi alamar Sauki ya samu,Tea mai zafi Nurse din ta hadamai ta mikamai,ya karba da hannunsa mai lafiya,Umar ne ya karisa da hanzari zai karbi Kofin Nurse din ta dakatar dashi kafin tace abarsa yasha da hannunsa saboda inyana motsa wannan hannun nasa,shi zai taimaka wajen Motsa wanchan hannun mai Ciwo,kai ya gyadamata alaman gamsuwa kafin ta Fice ta barsu,nan fa suka zagayesa suna hamdala,goggo ko Kallonsa take hawaye suna taruwa a idonta,girgizamata kai ya hauyi kafin yace"karki kuka goggo,kin manta kece ke man kirari da gadanga kusar yaki,ba gaba da gaba ba ko ta bayan ma karya sukeyi? yafada cikin sanyin murya dariya goggo tayi lokaci daya da mirmishi,Kofin tea din ya mika Umar yana Riko hannun goggo yace,"Toh kuma Shine kike kuka,kinsan baza su iya ba,baza su iya ja da gadanga ba,gadangan goggonsa. ba."Yafada yana Sharemata kwallah,dariya ta kubcema kowa ganin goggo na kuka tana dariya hannunsa ta kamkame tana Fadin!"Tabbas bazasu iya ba,Nasani baza su iya jada gadanga na ba,Allah ya baka lafiya"Da Ameen ya amsa kafin yace"Kawu wai muna wani gari ne,sai naga kamar nan ba Nageria bane,duba ga likitocin da suka zo suka dubani yanzu..?


Maimartaba ne yayi mirmishi yace!"Alhamdulillah Tunda yanzu kadawo hayyacinka,yanzu haka muna babbar birnin india,New Delhi,acikin wani Asibitin kashi.."Gyada kai yayi yana mamakin duk yaushe sukazo nan,kawu ne ya karbe da cewa"kuma kwananmu biyu yau da zuwa,kuma sai yau ka Farfado bayan aikin da"akayi maka Tun bayan zuwanmu.."gyada kai yayi yana bin Su Jabir da Haisam da kallo,wadanda sukayi wani kalan Tsausayi,dariya ta kamashi ya daga hannu yana Fadin"hey ya'n kannena,ban mutu bafa naga kunyi wani kalan Tsausayi ne..",Hararansa Haisam yayi kafin yace!Suwaye kanneka...? kai tsaye yace"Kumana.."Jabir ya yi Saurin Dunkule hannu zai sakamar bisa ciwo,da hanzari Aliyu yace"Kai Dude Don Allah bari wlh kuna gaba dani.."Yafada yana Zaro ido,sauke hannunsa Jabir yayi yana dariya gabadaya su goggo dariyan suke,na ganin diramar su Aliyu,mai hali dai baya chanza halinsa.


Suna Shirin tafiya masauki ne,Aliyu yakira goggo wacce ke Shirin Ficewa dawowa tayi tana Fadin"gani gadanga ko kana bukatar wani Abune? girgiza kai yayi yana Fadin"A'a goggo.."Kallonsa tayi kafin tace'"Toh mene ne? lumshe ido yayi kafin yace",Ammr,nace ba goggo banga Azeema bace ko ba"a zo da ita bane..."?Yar dariya goggo tayi kafin tace"Allah sarki ai nasan zaka tambaya,wlh Azeema na gida,bamu Taho da ita ba,kai batamasan Abunda ke Faruwa dakai ba gaskiya don ni na hana a sanar da ita,tunda aka nemeka aka Rasa,Azeema ta shiga kunci,gashi kuma cikinta ya Tsufa,kaga kuma sanar da ita kamar kara mata damuwa ne.."Dan Ware ido Gadanga yayi kafin yace"Cikin yayi kato ne goggo..? kansa ta dungure kan tace "Ban sani ba in tazo sai ka ganninma idonka..."Washe baki yayi yana Fadin"Da gaske pretty zata zo wajena.."Gyada masa kai tayi kafin tace"Haka nake so,da zarar mun koma zasu zo ita da Gimbiya Razeenah da Baba Ade,Allah barshi sai ta zauna anan har ta haihu,lokacin kuma nasan kai Alhamdulillah kasamu lafiya sai ku tattaro ku dawo gida,ko baiyi ba.."da hanzari Aliyu yace"Hakan ma yayi goggo Allah ya kara girma.."kansa ta Shafa kafin tace"Sai da Safe Allah ya kara Sauki..."Tafada tana fita daga dakin,dayake Asibitin basu da bukatar wani mai jinya,sai dai in daga nesa kukazo,ku kama masauki kuna zuwa kuna ganin majinyacin har ya samu lafiya,ammh ba'a yarda da kwanan Asibiti ba.



Haka ko akayi Sati daya Su maimartaba Sukayi Akasar india kafin su tarrara su koma Niger,Tunda jikin Aliyu Alhamdulillah,kullum yau yakan Fi jiya,Abun mamaki harta hannunsa mai karaya yana iya motashi,hakama kafafunsa,yana iya motsasu,ammh ahankali cikin dabara,Jabir ,da umar kadai aka bari,ammh dukkansu suka koma,daga Niger kawu ya hayo jirgi shida Haisam suka koma Nageria,inda suka kaima su Ummah lbri mai dadi na cigaban da'aka samu game da Ciwon na Aliyu,wanda sai lokacin hankula suka kwanta.


Mganar da goggo ta yanke na zuwan Azeema wajen Mijinta,ta Sanar da maimartaba baiyi gaddama ba ya amince da shawaran goggo,don ko bakomai taga mijinta shima yaga matarsa,ko Allah yasa ta kwantar da Hankalinta ta haihu lafiya,koda goggo ta sanar da ita mganar Tafiya india ammh bata sanar da ita wajen Aliyu zata ba tadai sanar da ita cewa zata tafi ta haihu achan ne,Tura baki Azeema ta hauyi,daganan sai kuka wai ita ba inda zata,ana so tatafi ne,azo da gawan yaya captain abinne Shine asoke ayimata wayau,Fafur fa Azeema tace babu inda zata,dakyar da sa bakin maimartaba ta yarda zataje,nan da nan ko akayi musu Visa,kwanan su Goggo hudu da dawowa sukuma suka tafi ita da Gimbiya Razeenah da Baba Ade,sai Ummah mai babban daki,datace wlh bamai barinta sai taje taga halin da maigidanta ke ciiki,sai su Zafira da Safaratu,wadanda suka sakama Sarki kukan sai sunje sunga Yaya captain suma hankalinsu zai kwanta,mirmishi maimartaba yayi yace duk suyi ta Tafiya Allah ya kaisu lafiya.

Koda suka sauka A babban birnin Delhi,Jabir da Umar su sukazo da motar Asibitin suka daukesu Diret zuwa masauki,Azeema tayi ta kalle kalle tana yabawa da kasar ta india,isarsu masauki ba wuya kowa yayi wanka sukaci abinci suka dan huta kafin Su jabir su ce Su Fito su tafi cikin Asibitin,ita azaton Azeema likita zata gani Shiyaasa,bata nuna wata damuwarta ba.


Umar da Jabir suna gaba sukuma suna biye dasu,har dakin da Aliyu yake suka Tura kofa suka Shiga,yana kishiginde,yana motsa hannunsa babu komai ajikinsa sai boxers,yana ganinsu yashiga washe baki,don Su Jabir basu sanar dashi,gasu zuwa ba,gaisawa sukafarayi suna tambayanshi yajiki yana amsa musu da sauki,Ummah mai babban daki ta shafa kanshi tana Fadin"Megidana gawa taki rami.."Dariya akasa,shima mirmishin yayi kafin yace"Kwarai don sai kin rigani wucewa wlh.."Yafada yana yar dariya Wajen Umar takoma ta dafosa Tana Fadin",Da tsohuwar zuma ake mgani ko Na gaban goshina.."Yarfe hanunta yayi yana Fadin"Tabdijam bawani nan,ai da sabuwar ma anayi,banan kika watsamin kasa a ido ba,nima aje gaba wlh bani so.."Dariya suka samata gabadaya ganin yadda Tayi Da Fuska,Aliyu dai sai waige yake yana Jiran yaga ta ina Azeema zata bullo,lura da hakan Da gimbiya Razeenah tayi itace ta waiga tana Fadin"Wai ina Azeema ta tsaya ne?Batare da ita muka Shigo nan ba..? jin Abunda Gimbiya Razeenah tace ne yasa Aliyu saukar da ajiyar Zuciya,yana lumshe ido.

Zafira ce ta fita waje,sai kawai taga Azeema zaune kan wata kujera ta wani hade rai,saboda duk a tsammaninta wajen likita suka kawota shiyasa tayi Ficewarta tana Tura baki,don yanzu wlh haushi kowama takeji,Zafira ce ta karisa garera tana Fadin"princess dinmu kizo Ummah na kiranki.."Kauda kai tayi kafin Tafara kokarin mikewa Zafira tana taimakamata harta mike,rike da hannunta gam suka Shiga dakin,bata direta ko"ina ba sai gaban godon Yaya Aliyu kafin ta kauce tana Fadin"Jita tanawani Fushi da mutane mufa taimakonki mukayi wajen mijinki dakike begen gani muka kawoki.."Tana Fada tanayin gefe gadanga dake kwance ya bayyana agabanta.

Kallonsa take,shima yana kallonta daga sama har kasa,tana sanye da wata doguwar rigar Abaya baka,sai Gyalen kayanta data nadashi bisa kanta,ga cikinta nan ya turo yayi kato,kamar gobe zai Fito Duniya bayan ta cika tayi Fam,kamar ba Azeema ba,itako kallonsa take cikin Fitan hayyaci,tundaga Samansa har zuwa inda kafafunsa suke asagale,Tsoro ya kamata tayi baya tana sanya duka hannuwanta ta danne bakinta dake rawa da karfi ta Furta.."Ya..Ya..Cap...tain...",Tafada idonta gabadaya awaje,Mirmishi ya sakarmata mai Sauti kafin yace"Na"am pretty..,Nine cijeni kiji ba mafarki kikeyi ba.."Yafada yana mikamata hannunsa mai lafiya,ai da hanzari ta karisa garesa sai jiyayi Ta fadomai kai tsaye hartana bugemai hannun dake da ciwo,gefe yayi da hannun yana Fadin"Wash pretty bi sannu,kinsan yanzu mijin naki yadawo sai allallaba fa"Yake fada yana zagaya bayanta da hanunsa mai lafiya,kuka kawai Tafashemai dashi tana fadin"Yaya captain Ashe zan sake ganinka arayuwata? nazata ka mutu ne su goggo ke boyemin?Bayanta ya Rumgume yana Fadin"Ban mutu ba pretty,sai dai nasha wuyane kawai.."yafada yana yar dariya dago kanta tayi daga kirjinsa tana kallonsa hawaye shabe shabe Afuskarta tace"Har wani tsawon lokaci kadauka kana cikin wannan halin? tafada muryanta na Rawa,Rausayar dakai yayi yana kallonta kafin yace",Bansani ba pretty wlh bansani ba,Abu daya nasani shine nidai na Farfado na ganni anan wajen"Kuri tayi masa da ido,kafin takoma tana bin Raunikansa da kallo,tana hawaye na Tsausayinshi,hannu ta sanya zata taba kafafunsa yayi Saurin rike hannunta yana Fadin"Pretty ciwo ne da zafi.."Yafada Ashagwabe,dariya tayi tana hawaye,tayi Saurin Shammatansa,ta dan ture hannun dayake da ciwo,baya yayi yana Fadin"Wash pretty .."Saurin Fadamai tayi tana fadin"Srry kaji bazan kara ba.."Tafada tana mai dariya hancinta yaja yana Fadin"kinganki ko,so kike kiga kukana ko,toh bazaki gani ba.."Dariya sukayi gabadayansu yana kara rikota,kiss ya sakarmata bisa kai yana Fadin"I miss u Pretty,i miss u like crazy..."Hawayenta suka karu ta dago tana kallon bakinsa,lebenta ta saka anashi tana tsotsa na kusan minti hudu kafin ta cire tana Fadin"Miss u more and more Mijina.."Shima idonshi ya kawo Ruwa da hannunsa mai lafiya yasa ya Fado da ita jikinsa ya rumgumeta kam,duk da tsinin cikin na hanata isa gareshi ammh haka ya matseta yana Sauke ajiyar zuciya,koda suka waiga daki bakowa,ashe tun Rumguman Farko kowa ya Fice batare da wani ya yi Shawara da wani ba😂


"Cikinta yake Shafawa yana Sauke tagawayen ajiyar zuciya kafin ya fizgo mganar"pretty cikin nan yayi kato da yawa,anya ba yan uku bane na baki,kinsa fa ni akwai lafiyan mazantaka ko? dariya takamata,mintsilinsa tayi AGefen ciki ya zille yana dan ihu,yake Fadin"kefa muguwace wlh daga fadar gaskiya sai muguntarki yatashi haka ake jinya dama"Bata dagoba illah kara lafemai datayi tana shafa kirjinsa da hannunta har zuwa nipple dinsa,salon datakemai ne yashashi Saurin rike hannunta yana fadin"pret..ty.."muryansa ta karaya,bata samu zarafin mgana ba illah"Umh..Umh..Umh..Mmmm.."Datake ta cemai,Mirmishi yayi mata yana kara damke hannunta yace"Bari mana pretty kinji,kinga fa halin danake ciki,karki kwantomana kura,wlh ko kin kwantota babu amfanin da zan miki.."Yafada yana cije baki,da Sauri ta dago tana Tura baki tace,"Ni yaushe nace haka...? Saurin Rikota yayi Yana Fadin"wayace kince,nine naji yanayi na chanzawa dat why am srry kinji pretty bazan kara ba.."komawa tayi bisa kirjinsa tana dauke hawayenta,domin data dago ta ganshi Ko"ina sagale sai taji kuka yazomata,kankame juna sukayi tamkar wani zai kwace musu juna,yana rike da ita yake bata lbrin Kafarsa daya harbin bindiga ne,daya kuma karaya ne,sai hannunsa,shima dake da karayan ammh Alhamdulillah ana samun cigaba.


Lalle masu iya mgana sukace Abun namu ne,toh haka tafaru da Aliyu da Azeema,don mantawa sukayi da kowa da komai suna rike da juna,suna hira gefe daya suna shan soyewarsu,har dare dakyar su Ummah mai babban daki suka tara Azeema suka koma masauki,ammh da Farko kuka tafara wai ita ba inda zata wajen Aliyu zata kwana,baki Ummah ta rike tana Fadin"Wai naji yaran zamani,toh in kin kwana,ina zaki kwanta gado dayane dai adakin,kuma yana kwance ko'ina tallabe? ko kallonta batayi ba ta fice tana Tura baki,Aliyu ko baitabajin haushin Rashin kwanan masu jinya ba sai yau,saboda Tafiyar Azeema ranar ko barcin kirki baiyi ba saboda kewa da damuwa,Tun safe ya ke ta kiran Jabir awaya don Allah ya kawo masa prettynsa Jabir sai yayi tsaki ya yanke kiran yana Fadin"wannan gayen Tunda yafara samuwa sai Allah kuma.."daga karshema kashe wayar yayi don yace yana barci bamai tashinsa,itako Azeema tun sallar Asuba bata koma tayi wanka ko karyawa batayi tatafi dakin su Umar tahau kwankwansa musu,Umar ne tafito,tana Neman yin kuka tana rokonsa yazo yarakata cikin Asibitin,ganin zatamai kuka ne yasa ya koma daki ya Shiryo yazo yatafi da ita ko Shiga baiyi ba ya juyo ya dawo yana Fatan Shima Allah yabashi mata wacce zata soshi ta kula dashi kamar Matar Yaya Aliyu.

Gadanga na zaune Yana Tunanin Azeema,ko Shigowanta baijiba,sai kawai yajita ajikinsa ta fadomai tana Fashemai da kuka,rumgumeta yayi ta lallashinta itako Fadi take wlh bazata kara Tafiya anan zata dinga kwana,cikin kunar rai yace"Kwarai da gaske kinanan wlh keda mijinki sai ahanaki kwana dashi,watafi chanchanta tayi jinyata inbake ba,bari likitocin suzo ko susan Abunyi ko kuma su sallameni mukoma gida gabadaya"Yake Fada Ransa bace.

Haka ko akayi Dr kabirkhan na zuwa Aliyu yayi cikiciki da rai ba Annuri,kuma yaki sakin Azeema yana kamkame da ita,Dariya Da sha"awa Abun yabaiwa Dr kabir khan da Sauran likitocin,Yasaketama Adubashi yaki sai Fadi yake,Asan yadda za"ayi dashi ko ayima prettynsa waje ta rinka kwana dashi tana bashi kulawa,ko kuma Shima sallameshi su tafi gida tare,itako Azeema harda dagowa tana Sharbe kwallah,shiko yana lallashinta,Tafi indiyan likitocin suka saka saka musu suna dariya Dr kabirkhan yace cikin Harshen Turanci" Umh very nice LOVE BIRDS..."Yake Fada yana musu Dariya,nan da nan yayi waya daga cikin Asibitin ya bada umarnin kawo wani karamin gado,kafin kace me har an Shigo dashi an kafashi kusa dana Aliyu anyimai Shimfidun alfarma,hardasu blanket da Filo mai kyau kallonsu Dr Khan yayi kafin yace"Is ok ko,mrs Patient ankashe rigimar zamu iya dubashi yanzu?yafada yana dariya tashi tayi tana gyada kai,cikin yar kunya,kuma wai tana wani Share kwallah,suko suna musu dariya kusan fa indiyawa akwai Bama soyayyah muhimmanci,gefe Azeema ta koma har suka gama Duba Aliyu suka fice suNa musu dariya suna tsokanansu da love birds.


Koda su Jabir suka iso,suka iske sabon lbrin baki suka rike,Jabir da bai iya Shuru yace"Wai yau naga bariki umar,yanzu Kaduba gayen nan,duk Wahalan damukayi dashi baitaba nuna damuwarsa ba inzamu koma masauki,ammh yau Azeema tazo harda tada rigiman kota dinga kwana dashi ko asallameshi yadawo gida? hararansa Aliyu yayi yana Fadin",Eh din,to daman ku gardawa dakune zan so ku kwana dani,Allah kyauta kai ni ko yanzu kuka tattara kuka tafi,Ayashe ta gaida Assha ko pretty? yafada yana kallon Azeema,wacce ke kunshe dariya ganin yadda Jabir ke hararansa,Jabir ya yi kuri yana kallonsa kafin yace"Toh ai ba damuwa ba basai ka koremu ba,zamu tafi kuma wlh zaka nemi ni banza mara mutumci kawai.."Dakin ne akasa dariya gabadaya ganin yadda Jabir yaji zafin Abun,Waje yafita yana ta zagin Aliyu shiko hardamai gwallo,Zafirace ta lallaba ta bi bayan Habibitan,Su ummah ko Aliyu sukayita ma Tsiya shiko ko ajikinsa don Abun yanzu ne yayi mai daidai.



Azeema duk da tsohon cikinta bata nuna kiyuwa wajen kula da Megidanta Aliyu,itace bashi abinci,goggemai jiki sabida yaji dadin jikinsa saboda Rashin wanka,akwana hudun da zuwansu garin aka kwance Karayan hannunsa,kuma Alhamdulillah komai yayi kyau masha Allah,sai da kokarin yafara anfani da hannu,wanda wannan aikin Azeema ce,itace keta kokari kan haka kuma yana kokarin motsa hannu,koda daukan Abune na mara karfi,itama Asibitin suna kokarin kula da ita amtsayinta na mai ciki,tunda duk sun saba da likiticin kamar DR khan sun Shaku dashi,inkaga yadda suke hira da Aliyu sai kuce sun shekara aruaru da haduwa ne.


Sati Daya su Gimbiya Razeenah sukayi suka koma,harda Jabir da Umar,Ummah mai babban daki tace ko ba inda zata zata,har sai Azeema ta haihu Aliyu ya warke kana ta biyosu su dawo,saboda itama ta kula dasu,toh ya suka iya dole suka barta sai Gimbiya Razeenah Tabisu suka koma tare,Ita kuma Ummah Dr khan yace ba"a barta ita kadai ahotel ba,gidansa dake cikin Asibitin nan Yakai Ummah mai babban daki,tazauna ita da matarsa mai Suna KAREENA,suna da kirki sosai,duk da Ummah batajin Turanci tana jin labarci,sukuma sun iya saboda sun zauna da larabawa sosai saboda yanayin aikin Shi Dr khan din,itama kuma Azeema aka barta ita da mijinta tana kara kula dashi..



_________________

*BAYAN WATA DAYA*

Sauki tare da cigaba yana samuwa abangaren Aliyu,wanda har an kwance duka aikin da"akayimai akafafunsa,hannunsa kuma Tuni ya yawarke garas,in ka ganshi bazakace yataba samun Rauni ba,Kafafunsa kuwa haryafara koyon Tafiya dasu Duk da tafiyan bata nuna Sosai ba,ammh sakamakon sanduna guda biyu,suna taimakamai Sosai wajen Nunar da Tafiyar nashi,kullum safe da yammah Azeema ke Fitowa dashi suna zagaya Haraban Asibitin,suna tafe suna soyewarsu babu Ruwansu da kowa,Tuni sukebama duk wanda ke asibitin sha'awa ganinsu bakaken Fata,ammh kuma suna mutumta soyayyah da daraja Aure haka,Ba yadda Ummah mai babban daki batayi ba,akan Azeema tadawo tahuta Tunda cikinta ya isa haihuwa ammh fafur taki,wai Tunda lafiyanta kalau ita bazata ta zauna ba,dole ta zura mat ido toh yazatayi Allah ya hadata da yaran zamani.


Awani dare Azeema tatashi da Nakuda,Hankali Aliyu yayi bala"in Tashi ganin halin datake ciki,ko kafin ya danna Madannin kiran likita Azeema tafara Wani irin nishi,ko kafin Nurses din su kariso Azeema tayi wani nishi mai karfi sai ga Kan d'a ya Fito,Allah ya taimake Nurses din suna shigowa Kan Da'n na Fitowa da hanzari suka karisa suka saka hannu suka jawosa,ai basu bar wajen ba,Azeema ta bankare tana salati nishi take mai karfi sai ga wani kan yakara Fito,suka saka hannu suka jawosa,Aliyu dake gefe yahada zufa kota ko'ina yana rike da Azeema,wlh har sai da yayi mata kwallah,ai suna jawoshi,takoma takwanta tana maida numfashi,Ihu suke suna
End Ads