yace yafison koma miyene,in aka kammalla ginin Zasu je chan Niger sukaga dangin Abdulnaseer din in sundawo sai su bashi matarshi koma miye zai faru alokacin babu damuwa..,Indo boyewa mallam tayi bata bari yaji komai ba,balle Ya Fahimci wani Abu,sai dai tayima Suwaibar jan ido,tare da tsoratar da ita,akan tana sake bashi kanta zatayi ciki,kuma in mallam yagani sai ya bata mata Rai,jin haka yasa Suwaiba ta tsorata koda mijin nata yakara nemanta sai tayi gaddama,ammh kusan sha"anin rayuwa,dakuma karfin soyayyar miji da mata,da kanta takai kanta komai ya afku,ammh wannan karan bata bari indo ta fahimta ba,watansu biyu da aure Mallam ya kammallah Shirin tafiya Niger wajen Dangin Abdulnaseer din,sai me Ranar kwatsam Daga mallam ya aiki Abdulnaseer kasuwa da kudade kimanin Dubu dari biyu,yakaima wani abokin kasuwancinsa,zai tafi saro awakai ne,kuma shi ga wannan Tafiyan sai sukayi mgana kan yabashi sakon shi zai je ya siyomai,daman Abdulnaseer ke zuwa,jin haka yasa yabawa Abdulnaseer kudin ya tafi kaima mutumin,Ammh Abun mamaki Tun safe yafita har dare babu lbrinsa,Mallam hankalinsa yatashi yakira Abokin nasa ya tambayesa ko Abdulnaseer yazo,Abunda yabama kowa mamaki cewan dayayi tun safe dayace zai aikosa yake jiransa ammh shuru,hankula fa suka tashi har aka kwana babu lbrin Abdulnaseer Tuni ,Suwaiba ta rasa sukuninta sai kuka takeyi,Abu tun anaganin wasa sai gashi an shafe sati babu lbrin Abdulnaseer duk inda mallam zai saka abincikamai an bincika ammh babu amo babu lbri.
Fadin irin tashin hankalin da wannan Ahali suka shiga bata baki ne,domin Suwaiba bataci bata sha sai kuka,bala ko dayaji,kallan mallam yayi yace"Kagani ko Baba wlh Abun na gudar mana kenan Tun farko nayi Tutsu a al"amarin.."Mallam ya gyada kai yana fadin"Har yanzu jikina yaki yardan Abdulnaseer zai iya aikatamin haka,zuciyata tafi karkarta akan WANI AL"AMARI NE..,Dabam yafaru dashi,ammh babu komai Koma miye Mucigaba da gayama Allah.."
Wata daya kenan Babu lbrinsa tun ana cigiya har akagaji aka zubama sarautar Allah ido,an samu saukin damuwar ta suwaiba,sai da kuma yanzu ciwo ne ya tasota gaba,kullum da zazzabi take kwana,ga shi komai taci sai ta amayar dashi ta rame ta lashe..ganin Babu yaki ci yaki cinyewane yasa Bala daukanta zuwa ABU CHIKA binciken farko aka gano dan karamin ciki na tswaon wata biyu da kwanaki,iya razana bala ya Razana,haka mallam yaji sanda lbrin yazomai,indo batayi mamaki ba sai dai Fargaban Abunda zatafadama mallam takare kanta,haka mallam ya tasa suwaiba agaba yana tambayabta waye yayimata ciki,don shi bai kawo Abdunaseer bane,Suwaiba na kuka tace Abdulnaseer ne,da mamaki Mallam ke kallonta kafin yace mata waye Shaidanta Daga ido tayi ta saukesu kan indo,Mallam dayaga haka sai yamaida kallansa kanta yana tambayanta meta sani game da hakan,cikin kaskastan dakai indo tamai bayanin Abunda yafaru takara da cewa yayi hakuri boyemai datayi,Mallam yayi Shuru yana jinjina al"amarin,Domin basu dawani Tsumi ballatana dabara sai na barma Allah..
Mallam ya kwantarma Da Suwaiba hankali inda yace tayi kokarin kula da kanta da Abunda ke cikinta,Hankalu sunfara kwanciya har cikin suwaiba yakai wata biyar tafara zuwa awo,akuma lokacin Bala ya kamallah degree dinsa harya daura masters dinsa,sai kuma wani karin jarabbawan data bullo musu,domin mutane anguwa suka cha da maganganu na cewa Suwaiba diyar mallam tayi cikin shege,da mallam yaji batun sai da ya kwanta ciwo saboda damuwa,domin baya da ikon kare kansa da yarsa tunda kuskuren nashi ne,shaidun daya daura auren agabansu almajiransa guda biyun tuni suka koma garinsu abokinsa kuwa auren ba dadewa Allah yayimai rasuwa,baya da bakin da zaiyi mgana,karshe sai da fita ta garari indo domin duk inda taje ana tafe zundenta ana yada mata habaicin Yarta tayi cikin shege,Shiko mallam daina ma karatun yayi domin ko almajiran dayake ma karatun sun gudu,Tunda mganar ta fita,bala kuwa Shima lbri har cikin mkranta ana tafe yadawa kanwarsa tayi cikin shege,damuwa tare da tsananin ciwo ya rafke mallam kwance,dama Shine kwarin gwiwansu to shima ya kasa,Alokacin ne,kuma bala ya samu aiki a gidan Radion Nageria kaduna ashashen lbru,lokacin kuma Cikin suwaiba yakai wata na bakwai,Kwanan Mallam bakwai yana jinya jikinsa ya rikice suka daukesa suka kaisa asibitin al madina,sai dai kash kwana daya yayi mallam Shehu Akarami ya amsa kiran mallacinsa,ammh ko da ya rasu yafadama iyalansa kada su kullaci Abdulnaseer domin haryanzu zuciyarsa tana fadamai bada gangan bane ya aikata musu haka,akwai wani boyayye Al"amari,Mutuwar mallam ta girgixa mutane dadama ciki harda indo da bala da Suwaiba,wanda sukayi kuka,kamar zasu mutu saboda rashin bango agaresu,Ranar da mallam yayi bakwai kuma sai ga wata mgana wai Suwaiba ta kashe mahaifinta da bakin ciki,abu goma da ashrin gata da ciki,ga mutuwar mahaifi ga bacewar miji,ga Zunde mutane dawanne zataji,indo ko dama tuni tayi rauni dare daya Hawan jini ya fadeta ta mutu,tsakaninta da mallam kwana 70 ne,topha ta faru ta kare,maraici ya lullube Suwaiba da bala,lokacin yana gabda kammallah master dinshi,shiyasa yazama uba ga Suwaiba,shike lallashinta batare da shawara da kowa ya saida duka kaddarorinsu ya biyama mahaifansu bashi,ganin zaman zaria bazai yuyu dasu ba yasa ya saida harta komai nasu gidan dasuke ciki kadai yabari,dakanshi yahau mota ya tafi garin gombe,inda basu da kowa ya siyama Suwaiba wani dan matsikacin gida da taimakon dilallai,Koda ya dawo yafadama Suwaiba hukuncin daya yanke bata damu ba,saima dadi dataji domin garin zaria ya fitarmata akai kwata kwata,ko fita tayi yara sun dinga binta kenan wasu harda jifa,.
Bala da kansa yadauki kanwarsa yakaita garin na Gombe da kansa,ya damkata hannun makocinta wanda garun gidansu yake ahade wato Mallam lawal bature,wanda ya kasance yana da matar aure daya Fatima,ammh basu taba haihuwa,asa"a Lawal din zaiyi sa"an Bala haka itama matar nasa bata fi sa"an Suwaiban ba,Ganin yadda suka anshi amanar daya basu hannu bibbiyu ne yasa ya zaunar dasu ya karanta musu komai na tarihin rayuwarsu daga karshe yabar amanar kula da Suwaiba da Abun zata haifa awajensu Tunda shi zaikoma ne,Saboda aikinsa da kuma hada kan karatunsa,sunmai alqawarin kula da Suwaiba tare da riketa tamkar nasu,yaji dadi sosai anan ya kwana washegari yayi sallama dasu yakoma kaduna bayan ya jibgemata kayan abinci da kudi harda siyayyar haihuwa suka rabu tana kuka yana kuka,wayyo rayuwa kenan..
Yana komawa yamaida kai ga hada kwalin master dinshi,yana kuma cigaba da aiki a gidan Redio Nageria kaduna,gefe daya kuma yana harka da yan Siyasa tunda yana hira dasu,kuma yana musu tallace tallacen siyasa nan da nan Sunan Bala shehu Akarami yayi Fice kowa ya Sansa,duk bayan sati biyu yake zuwa gombe ganin Suwaiba,ana wannan halin ne ya siyamata waya saboda wata mtsala in tataso basai ansha wata walaha ba,yafadama su mallam lawal da tafara nakuda suyi kokarin kaita asibiti.
Haka akayi Watan biyu da komawa gombe wata ranar jumma"a da yammah tafara Nakuda Allah yasa Fatima na kusa da ita,tabazama waje ta kira mallam,dayake dan sana"ar saida kayan gwari yake,anan kofar gidan,da hanzari ya nemo mota suka kaita asibiti,Suwaiba tasha walaha don sai da ta kwana ta wuni kana ta haifo santalelenta danta mai kama da Ubansa sak,kato dashi wanda yana fitowa Duniya Bala yana karisowa asibitin,lokacin da aka miko masa Yaron kura masa ido yayi,yana ganin tsabar kama dayayi da mahaifinsa Abdulnaseer,yaron ko yana harba kafa,alamar karfi,nan da nan Bala ya rumgumesa yana fadin"Sannu da zuwa Duniyarmu *ALIYU GADANGA...*
#Comment,share and vote..#
#Janafty#....
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of yuong soldier man)_
Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:Janaf*
*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘 Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent writer's asso*✏
_*Special Thanks to Hussain80k😝 and HassanATK...Sakallahu Filjannah Dudes😘*_
*NOT EDITED*💥
*Chapter4*
""Kwanan Suwaiba biyu a Asibitin kafin asallamota tadawo gida,Bala yayi Namijin kokari akan Suwaiba domin Duk Abunda uba ke ma da,da Abunda miji zai ma matarsa sai da yayimata shi,mallam lawal da matarsa Fati suma sunyi namijin kokari kan Suwaiba,Fatima nan take wuni sai dare take komawa gida,ita zata sanyama Suwaiba ruwan wanka ta juyemata,kafin tazo tayima Aliyu wanka wanda Sunan da bala ya sanyamai kenan,Suwaiba bata nemi komai tarasa ba na bangaren rayuwa,bangaren yar"uwa kuwa Fatima ta koremata dukkan kishirruwan su.
Kwanan Bala uku agarin Gombe yakoma Kaduna bakin aikinsa,Ranar suna tana zagayowa aka Yankama Aliyu raguna guda biyu,makota da yan"uwan Fatima dana mallam lawal sunzo tayasu murna,dayake suma din yan Asalin Yan gombe ne,Anyi Abun cikin Mutumci da jin dadi,Suwaiba tacigaba da kula da kanta tare da Danta,duk da mutanen anguwa sunata zunde cewa tazo anguwan da ciki ta haifeshi batare da nuna alamun tana da Aure ba,domin ada sun zata Bala ne mijinta,ammh sai daga baya suka Fahimci cewa yayantane ba mijinta ba,duk da haka Suwaiba ta toshe kunnanta bataji bata gani,ta dauki nasihan dan"uwanta daya cemata ta maida hankalinta wajen kula da kanta da Abunda ta haifa.
Aliyu nada Shekara uku aduniya babu inda baya zuwa yayi wayau haryafara Tafiya,alokacin ne kuma Bala yayi Aure da matarsa Umaima yar kadunane Haifaffiyar Kabala ce,mahaifinta shima tsohon dan siyasa ne,tunda shine tsohon mataimakin gwamna a gwannatin data sauka,Akwai girmamawa tsakaninsa da Bala,tun mahaifisu na raye yasan mallam,tunda yace sunyi karatu wajensa,to shigowar Bala harkan Siyasa ne,yasa suka sanjuna,kuma shida kanshi yayimai tayin Auren diyarsa tasa Umaimah,anyi biki lafiya amarya tatare agidanshi dake Anguwan Dosa,gidan yana da girma wanda Bala yadau tsawon lokaci yana ginashi,bayan Aurensu da wata biyu ya dauketa yakaita gombe don ta gana da Kanwarsa Suwaiba,hakika Umaima ta tsausayama Suwaiba ganin inda takoma da rayuwa daga ita sai Da"nta Aliyu wanda yana girma wayonsa da kwazonsa da Karfinsa tare da kamaninsa da mahaifinsa suna kara bayyana,awannan zuwan ne Bala ya sanya Aliyu awata mkranta da"a ke kira MATRIC INTERNATIONAL SCHOOL GOMBE..,Mkrantace mai tsada domin sai ya'yan wane da wane,kowani kusa agwannati ko yan siyasa,Cikin nasara da hazaka Aliyu yafara karatunsa Koda akayimai interview Malaman mkarantan sunyi mamakin kaifin basiran yaron,duk da ance baitaba hallartan mkranta,ammh dayake Suwaiba bata wasa zama take dashi takoyamai Dak da iya Abunda tasani na boko dana Arabi,Nursery 2 aka sanyasa saboda yadda sukaga yaron da kaifin kwakwakwa,kafin Aliyu ya rufe shekara sunansa yayi Tambari a mkranatar nan saboda yadda Allah yayima yaron baiwan karatu Shiganshi Shashen primary yasa sunanshi yakara fitowa domin koda yakeda kankantar shekaru ana zuwa dashi gasan mkranta.
Watan Umaima tara ta haifo santalelen Danta mai kama da ubansa sak,Ranar suna yaro yaci sunan HAISAM,wanda tsakaninsa da Aliyu shekaru hudu ne,bayan shi tazo tayi yan biyu, MARDIYA DA MADINA,Daganan bata kara haihuwa ba, haihuwar Haisam dai Suwaiba bata samu zuwa Kaduna ba saboda mkranatar Aliyu,sai haihuwar yan biyu ne taje kaduna saboda lokacin su Aliyu sun samu hutun mkaranta,sati daya sukayi akaduna kafin Su dawo gombe,Suwaiba tasan yarda take da Aliyu,tun yana yaro,yana da kiriniya da kuma son wasa,ammh bata bari yana Fita,sai dai in zai fita wajene ya zauna wajen mallam lawal,kokuma Fatima tatafi dashi gida,ammh kuma baya zama,da fari ta sanyashi a islamiya anan anguwan ammh sai yaran mkranta suka fara kyamatarsa da kokarim kiransa da wanda bai da uba,Kullum da kuka yake dawowa,yana fadama Suwaiba Abun na damunta,tana tsoron kada su sanyama yaronta wani banzan Tunani,sai kawai ta cireshi ita takoma malamarsa tunda daidai gwargwardo tana da ilimin Addinin harda na boko,sai takoma tana koyar dashi agida,tun yana yaronsa Suwaiba ta fahimci Danta yana da bala"in zuciya gashi tun yana karaminsa yake da bala"in karfi kamar doki,shiyasa take binsa ahankali,Abu dayane yake cimata tuwo a kwayar irin sunan da yan anguwa suka sanyama Danta wai DA'N MACE,tun Abun bai damunta harYafara damunta,shiko Aliyu tun yana dukan yara in sun kirashi da sunan haryakura yafara amsawa,saboda ya yarda shi din Da'n mace ne,ammh kuma macen ta bambamta da sauran mata saboda jajircewanta akan Rayuwar Dan"ta.
Aliyu nada shekara Tara Aduniya Fatima ta samu ciki,wanda ya kasance yana bata wahala,farinciki wajen mallam lawal d Fatima ba"a mgana,ita kanta Suwaibar tana murna da hakan,don ita da Fatima tamkar yaya da kanwace,Saboda laulayin data fama dashi mai zafi ne,yasa mahaifiyar Fatima BABA ADE Tadawo nan gidan tana zaune da ita,tana bata kukawa,duk da itama Suwaiban data gama aikin ta zata rufo gidan tashiga gidan mallam lawal tana taimakama baba Ade dawani Abunda ba"a rasa ba,Cikinta yayi girma sosai kuma yabata wahala,wata tara nayi ta haifo yarta mace santalele da ita,bayan bakar azaban dataci asibiti,wanda Bala shi yayi wannan dawainiyar saboda alherin Mallam lawal da matarsa Fatima garesa dashi da kanwarsa,harta hidiman suna da Kayan babby dana maijego Duk bala yayi su,ranar suna kuma ya yankamata katon ragonta yarinya taci suna AZEEMA..,Sai da tayi arba"in kana Baba Ade takoma gida tabar Fatima nakara kula da yarta,Tare da taimakon suwaiba,wacce tadauki son Duniya ta dorama diyar Fatima,sabida suwaiba na son Diya mace arayuwarta,ammh Allah bai bata ba,sai yabata namiji,Saboda Amintakar dake tsakanin Fatima da Suwaiba ne,yasa Fatima tayima suwaiba tayin Auren mallam lawal,mganar data kawo rudani sosai,suwaiba taki yarda.hartayi ikirarin barin garin gombe,Bala ya shiga mganar yace Fatima tayi hakuri suka cigaba da zumuncinsu,tunda Suwaiba taki,dole Fatima tabar mganar ammh harga Allah tana kaunar suwaiba aranta.
Shekaran Azeema biyu Aduniya Fatima tafara wani ciwo,daga ciwon nono,shikenan sai cancer ciwon Daji,Tun ana ganin abun dawasa har babbar magana tazama babba,mganin gargajiya aka fara ammh Abu yacitura nono sai zagayewa yake,harya harbama dayan ma,Suwaiba da kanta takira bala ta fadamai kan yazo ya taimaki,Fatima koda yazo yaga halin datake ciki sai da ya zubarmata da kwallah,nan da nan aka dauketa zuwa babban asibitin jaha,sai koda sukaje likitoci kin amsanta sukayi,suna ta fada suna fadin sai da ciwo yagama cinyetane za"a kawo musu,bazasu amsa ba,ran Bala yabaci yace adawo da ita gida washegari sai sutafi da ita kaduna,Allahu Akbar Allah yaga Abunda yagani ne,ya takaitama musu wahala Karfe 3:00am na dare Fatima ta karbi kalmar shahada tarasu agaban mahaifiyarta da mijinta mallam lawal bayan ta bayyana amanar diyarta ahannun Suwaiba,wanda Aranar sai wajen sha biyu takoma gidanta,itada Aliyu da Azeema wacce keta kuka,shiyasa ta dauketa suka tafi gidanta takwana awajenta,alokacin mallam lawal ya bugama Suwaiba kofa dayake Bala na nan shi ya fito,nan yake shaidamai rasuwar Fatima,sanda Suwaiba taji sai da ta suma gau,saboda jimami da sabo,Tayi kuka kamar ranta zai fita,babu Abunda take tunawa sai irin sabon dasukayi da Fatima da zaman amanan da sukayi,tunda take da ita bata taba batamata da gangan ba,macece mai hakuri da sanin yakamata,balle mallam lawal dayayi kuka rasa nagartattaciyar mata irin Fatima,ita kanta Azeemar ta fahimci rasuwar mahaifiyarta nata,haka ta wuni kuka,Suwaiba na lallashinta Aluyu ma yasan lokacin da"akayi rasuwar,saboda yana da shekara 12 alokacin Domin har yakammallah karamar primary dinsa sai wucewa gaba,Baba Ade ma takoka domin itakadai ne yarta gashi Allah ya amshi Abunsa,Anayin bakwai Baba ade tatafi da Azeema wajenta,dayake basu da nisa saman anguwansu,shiyasa kullum sai Azeemar tazo wajen Suwaiba,wanda ko Azeema batajeba Suwaiba take wanke kafa taje ganinta Haka kurum Allah ya doramata son yarinyar da tsausayinta,shiyasa komai zatama Aliyu tare take hadawa da Azeema.
Fatima tayi Arba"in da Rasuwa Bala yazo yatafi da Aliyu zuwa kaduna domin hallartar mkarantan daya neman masa Wato COMMAND SECONDARY SCHOOL KADUNA..,Makarantar sojoji dake kaduna,Babu yarda Suwaiba zatayi Tunda Aliyun yanuna yana son mkranatar na Sojojin,dole tanaji tana gani ya hada kayansa yabi kawunsa zuwa kaduna,wanda awannan karon yayan nata yaso tabiyoshi sukoma kaduna ammh suwaiba taki,tace tafi sabawa da Gombe bazata iya barin garinba,shikuma bayason takuramata sai ya rabu da ita,ammh duk Abunda zata bukata sai da ya barmata kafin su tafi,Da shi da Haisam aka sakasu amkranatar dayake anyima HAISAM din jamping din aji shiyasa sukayi Daidai akaratu.
Shekaran Fatima daya da Rasuwa yan"uwan Mallam lawal suka matsamai sai ya kara aure zama hakan bai yuyuwa,Dole tasa ya sake aure da wata yar saman layin dasuke RAMATU,Ramatu Mai awara ne Sunanta saboda awara take soyawa akofar gidansu tana yawan zuwa wajen mallam lawal siyan kayan miya shiyasa suka saba,Ramatu bazawarace tayi aure Allah yayima mijinta rasuwa,ammh bata haihu ba,Ramatu bata da uwa bata d uba,ahannun kakarta take,gabadaya rayuwarta tataso babu kwaba ne,ballatana tsawawartawa,Komai taga dama shi takeyi babu ruwanta,tunkan Auren ta na farko idonta yake abude,irin matanan ne marasa mutumci,da kamun kai,gata bata da kunya sam,ko mallam lawal din ita fara nunamai alamun so,don haka zata dinga aikamai da awara ko yabata kudi bata amsa,da taganshi zata hau sunne kai kamar munafuka,Ko lokacin dayazo da izinin neman amincewarta batayi gaddama ba Ta amince ko wata ba"ayi ba aka Daura aure tatare agidan mijinta,adakin dake gefen na fatima,dayake gidan,gidan laka ne,dan karami mai dakuna biyu da kichen sai dan filin tsakar gida,sai rijiya dake gefe,gidan babu siminti sai dai tarin kasa,ammh dayake lokacin Fatima nada kokarin tsabtaceshi shiyasa sai kasan ta kwanta kamar an daddadeta,.Satinsu biyu suna cin amarci kamar Abun arziki ammh daga Ranar da mallam Lawal ya fadamata zai dauko Azeema ya kawomata ranar basuyi barci ba,don Ramatu cewa tayi bazata rike diyar da bana nata ba wlh,shikuma yace bata isa ba,gata kuwa bazai barma Baba Ade wahala ba,dole tanaji tana gani ya tattarro Azeema ya dawo da ita gidan da zama,Suwaiba bataso haka ba,domin tuni taji lbrin Ramatu bata da mutumci sam,kuma tasani cewa Azeema bazataji dadin zama da ita ba.
Illai kuwa Domin Tunda Azeema tadawo hannu Ramatu take gana mata azaba,duk da karancin shekarunta domin lokacin tana da shekara biyar ne aduniya tayi girma dayake tana da tsawo,gabadaya aikin gidan nan ita keyinshi,da gari ya waye zata jawo ruwa tacika duka botikan gidan,kafin tazo tayi shara,tare gidan gabadaya takoma dakin mahaifiyarta inda yazama wajen kwananta ayanzu,bayan nan takoma kichen ta hura wuta ta sanya ruwan koko ta dama,ta zubama Babanta da inna Ramatu,kuma bata da ikon sha sai Ramatu taga dama,da kananan shekarunta tasaba da wanki na Ramatu da Babanta duk ita ke wankesu,Mallam lawal baya da yadda zaiyi domin kamar Ramatu tafi karfinsa ne,domin yana mgana zata tasomai kamar zata dakeshi,baya da yadda zaiyi sai ya dinga bama Azeema Hakuri,itako ko afuska bata nuna,bataso mahaifinta ya shiga damuwa saboda ita.
wajen datake samun sauki guda biyu,daga gidan Baba Ade sai wajen Suwaiba,wanda tazama tamkar mahaifiyarta,Ramatu tunda ta lura Azeema najin dadi in taje gidan Suwaiba sai ta hanata zuwa,inko taje asace Ranar sai ta kusa kasheta,ko wani Abun amfani Suwaiba tabata to Ramatu zata kwace ta saida,da Suwaiba ta fahimci haka sai ta daina bata sai dai in zatayi amfani dashi taje gidan Suwaiban da Dauka,Suwaiba da hannunta ta sanya Azeema amkaranta awata mkrana dake nan garin gombe G.D.S.S.S GOVERMENT DAY SCIENCES SECONDARY SCHOOL GOMBE,mkrantace mai kyan gaske,saboda tana hade da private ce,sakamakon