x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - ALIYU GADANGA

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 179

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ba ita ke dariya ba tace"Ko baku Tambayaba,dama yakamata kuji koda jin bazai muku amfani ba,Yaya captain nawane nikadai,nafi kowa sonshi harda da uwarsa nafita sonshi,Duk duniya bani da wani buri sai na yau na ganni amtsayin matar Yaya captain,nasoshi Tun banso mai ake kira soba,Na rayu da Sonshi na girma da Sonshi,kullum mafarkina na Aureshi,sai gashi kwatsam Adda Azeema tafim Shigar Sauri,saboda shi na tsani yar"uwanta naji bana  kaunarta balle nakaunar ganinta da Abun kaunata,Tunda akayi Auren naketa Shiryamata gadar zare,ammh yana Tsallakarta da ita,tadalilin haka ya dauketa daga garin nan ya maidata kaduna,ganin haka yasa na Rasa mafita ammh duk da haka ban hakura ba,kwatsam sai Allah ya jehomin ku,,naganku kuna neman agaji,sai naga kema ai kina son Abunda nakeso ne,nikuma bana barin watama ta rabi yaya captain Shiyasa Na ce ki kashe auren Azeema sabida bani da halin zuwa kaduna,ko kulla wani makirci akanta,nayi hakane kema na gama dake,Bayan ki kullah Abunda kika kullah,daga karshe zan kashe Azeema da hannuna,sai na fadama Goggo cewa kice kikayi sanadiyar mutuwar Auren Azeema bayan nan kuma kika aiko har gida aka kasheta,kinga daga Yaya captain yaji lbri zai makaki kotu a yanke miki hukunci kisa,nikuma yazo ya Aureni ya tattarani mu koma kaduna Duniya Ta budemana Sabuwa..."Tafada harda daga Hannu tana tsallen murna kamar Abun ya tabbata.

Ni"ima da Muneera sunyi matukar shock dajin wannan lbrin,kasa motsi sukayi,Muneera da Ranta ya baci tadaga hannu azuciye zata wanke Azeeza da mari Ni"ima ta damke mata hannu tana girgixamata kai hawaye na kwanroyomata Kallonta Muneera tayi kafin  tace"Meyasa kika hanani? kibarni na Sauyama jaka kamanni,Tunda ta iya sakamu muka aikata Abunda ba Halinmu bane.."Danne kukanta Ni",ima tayi Tana fadin"Barta barta Sweetheart bakiji metace ba,zata kashe yar"uwarta da suke uba daya saboda Captain,to mu suwaye da bazata iya kullah mana Sharrin dayafi wannan ba,kyaleta kizo mutafi insha Allahu Allah bazai barta ba.."Tafada tana jan hannun Muneera wacce ke hararan Azeeza,itako Tana musu dariya kamar taga mahaukata,inna Na madafa taga hucewarsu Ni"ima da hanzari,tana musu mgana, ma ko kallonta ba wanda yayi,baki ta rike kafin ta cigaba da aikinta aranta tana fadin"Azeeza duk kawayenta irin tane.."itako suna Fita tafada gado tana murna harda tsalle.

Amota haka Ni"ima ke kuka Wurjajan Tana fadin"Mun bani Sweetheart yanzu ya zamuyi da hakkin marainiyar Allah,wlh nayi Nadama,shedan ne ya zugani da kuma soyayyar Soja wlh.."muneera na driving Tana fadin"Ai komai ya Faru keki kaja,banyi Gardama ba,ammh kika nuna amincewarki game da yarinyar,nidama Tunda naga idon yarinyarnan Atsaye Nasan za"a rina Shegiya zuciyarta kamar ta kafaran Farko.."Tafada tana cije baki,dafe kai Ni'ima tayi tana kuka,kafin tayi zaraf ta dauki wayarta dake kan motar tana fadin"Kafin tafadama Captain Abunda Ta shirya nidakaina zan sanar dashi gaskiyan Abunda ya Faru  Sweetheart shine mafitanmu yanzu.."Tafada tana danna wayar,Fizge wayar Muneera tayi tana Fadin"Ke kina da Hankali kuwa,yaushema zai Saurareki balle harya gane Abunda kike nufi,kwabe waje kawai zakiyi kibari mukoma gida sai musan Abunyi kinji ko.."Gyada kai Ni"ima tayi tana kara Damke kanta kamar wacce akace Uwarta ta Rasu.

*****************

*1 DIVISION NAGERIA AMRY KADUNA*

An Sauke Baki abbban sashen dayake cikin barikin,sakamakon al'amarin dayafaru da Captain Aliyu,Toh daga lokacin baida Sakin jiki,ko achan Abuja ma,yana baya baya ne,ko achan villa gefe yakoma shiyasa baima Shiga cikin bakin Sojojin ba,kamar yadda wasu sukayi,Shiyasa Jabir shima duk bai saki jiki ba,ganin Abokinsa kuma Amininsa haka,Yayi alqawarin bazai kara Tambayanshi ba,shiyasa yamai Shuru sai dai baya barinshi yazauna Shuru zai zo ya zauna yana jansa da Hira koda bazai Tankanshi ba.

Shiko Yarima Umar Tunda suka sauka Abuja yake video call da gida yana nuna musu Yadda Nageria take da kyau da Tsari,gabadaya iyalan mai maimartaba zakaga an Taru ana mgana da Umar,har Zuwanshi Villa ma haka,kannensa,Safaratu da Zafira sune yan kwakwan Nageria suna makale da yawa bini bini kadan su kira suna  fadin"yaya yarima muyi Video call muga a inda kake yanzu,shiko jiki na bari zai kira,har saukansu barikinsu Aliyu ma Da sukaga kyan wajen,harta maimartaba ba"a barshi abaya ba,dashi ake kallo,shiko yana mgana dasu yana Nuna musu Wajewaje,duk da bai yarda yayi nisa ba acikin barikin don baisan ko"ina ba.

*After 1 day*

Bayan kwana daya da isowarsu Yarima Umar,Da yammah da misalin karfe biyar na yammah Aliyu ya shiga gidan Jabir yace yazo ya rakashi cikin gari gidan kawu,zaije su gaisa sun kwana biyu basu hadu ba,baiyi gardama ya Shirya cikin irin Shigar Aliyun na Riga da wando White and blue,na kamfanin Armani,Suka Fito Ras dasu,amotar Jabir aka Fita,shiyasa shike Driving din motar,Har suka isa gidan kawu bala,Basu waji jima ba,don sun samu kawu agida,Tunda Abun yafaru sai Yau yataka kafarsa zuwa gidan,kuma kawu bai mai mgana ba,sai dai yayimai Nasiha tare da jirwaye,akan yadinga binciken Abu kafin ya zartar da Hukunci,zasu Tafi Ummah ta matsa sai sun Tsaya sunyi Dinner,sai da sukaci suka koshi kana suka baro gidan,ta wajejen Anguwar Rimi din nan,sun kawo kenan sai Danja ta tsaidasu sun tsaya,kamar ance ya waiga gefensa yaga wani Namiji bisa mashin yasaka hulan kwano dayake motar Tinted ne,ba"a ganin na ciki,har zai kauda kai,kawai sai yaga ya cire hular kwanon,kara kallonsa yayi yana Tuna Fuskarsa wanda ko Barci yakeyi Tana mai gizo Tsabar yadda ya haddaceta ido yazaro yana Fadin"Shine..."Da hanzari Jabir ya kallesa yana fadin"Shine wa? shima yana bin gayen da kallo,ganin danja ta saki ne,har yamaida hulan kwanan yafara Tafiya cikin hargitsi yace"Plz Jabir Follow dis bike...."Yafada da karfi yana nunamai Shi,da hanzari Jabir ya bi Mashin din wanda yakara gangarawa cikin anguwan Rimi Da gudu,shima da gudun yatakemai baya.



*Comment and Share...*
#Janafty..#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏


        *Chapter 28*

     Aliyu da kanshi ya dauki Azeema da hannunsa ya sakata acikin mota goggo ta Shiga baya,jabir na Driving,su Muneera ma Motarsu, suka Shiga suka Mara musu baya,Mallam lawal Bai bisu ba,yadai bisu da addu"ar Fatan samun lafiya,general Hopital suka kaita,suna zuwa aka karbeta da gaggawa,likitan yana ganin yadda take yafara Sakamata drip tare da wasu Allurai,domin yace ba Suma tayi ba,jikinta ne babu karfi sam,Jininta aka diba First,aka tafi dashi lab,domin gwadawa,itakuma Dama Ruwan daya samata saboda yataimakamata wajen samun karfin jikinta.

  Gwajin Farko ya Tabbata da Samun ciki Azeema na Tsawon Sati Takwas koda Resuilt din ya Fito Gadanga aka Damkawa murna kamar bakinshi zai zage,Rumgume jabir yayi yana godiya ga Allah,goggo ko mirmishi take na Farinciki,domin dama Tuni Ta Fahimci ciki ne da Azeemar,itako Azeema batasan wainar Da ake toyaba,tana kwance duk jikinta ba karfi,bata dade ba ta Farka tana Fadin"Goggo Ruwa..." da hanzari Goggo ta bata Ruwa,kafin ta taimakamata tatashi Tana tashi idonta na kan Aliyu wanda yakafeta da ido,yana kallonta lokaci daya da mirmishi bisa Fuskarsa,kauda kai tayi tana amsa Sannun da Ni"ima da Munnera suke mata,amsa musu tayi da kai,tana Kara kallonsu,ita Ni"imar nema ke bata Tsausayi,jabir ne yayimata sannu takarba dakai,Aliyu dayake tsaye chan gefe sai ya matso kusa da ita yana fadin"pretty ya jikin?Kura masa ido tayi tana Tuna sanda yayi Shuri da ita,Runtse ido tayi hawaye na kwararomata,kauda kai tayi tana cije bakinta,ganin haka yasa goggo ta Girgiza kai ta saka kai Ta fice,Jabir ma yabi bayanta Ni"ima ce ta karisa gaban Gadon Azeema tace"Zamu Tafi Azeema,Allah ya baki lafiya.."

     "Gyada kai tayi kafin tace"ngd..."Dakyar cikin muryan ciwo,kallon Aliyu tayi kafin tace"Captain zamu Tafi,ina Fata dai An yafemana kuran damuka aikata.."Tafada idonta na cikowa da kwallah,Mirmishi yayi yana kallonta kafin yace"Bakomai Ni"ima buh next time Kada hakan takara Faruwa ko ba akaina ba,ku koyi yaki da zuciyarku don Allah..."

gyada kai tayi kafin ta Share kwallah Tana Fadin"Insha Allahu hakan bazata kara Faruwa ba.."Gyada mata kai yayi yana Fadin"Toh Yayi kyau naji dadin haka,share hawayenki kibar kuka hakanan,komai ya wuce.."Mirmishi tayi batayi mgana ba,sai ta waiga tana kallon Azeema wacce ta Runtse ido ammh kaf Abunda suke Fada akunnanta ne,Dafata tayi tana fadin"Congratulatino Sisto Allah ya inganta.."Daga haka tajuya,muneera dake tsaye itama tayi Fatan samun lafiya kafin su Fice,awaje sukayima su goggo sallama,suka Tafi suna jin zuciyarsu tayi sanyi Tunda komai ya Wuce yanzu.

   Suna Fita ya karisa gareta lokaci daya yana harde hannuwansa bisa kirjinsa kallonta yake dakyau yadda Fuskarta tayi Fayau tabashi Sha"awa,Sunanta yakira ahankali.."Pretty..." Tana jinsa tayi mishi banza harda dan nishinta alamar barci takeyi,yana kallonta yar dariya ta kamashi,sai ya saka hannu ya dan,matse hannun Da aka sanyamata Drip,taji zafi da hanzari tajaye hannunta tana Fadin"Wash.."tafada tana Jaye hannunta bata bude ido ba,ta mirgudamai baki,dariya ta kamashi sai ya Rankwafa yana lakucemata hanci yake Fadin"Matar Sunnah bata Fushi da mijinta,kuma in yayimata laifi yakamata ta Sausautamai,koyasamu damar bada hakuri..",tana jinsa tayi mishi banza,sai ma juyamai baya datayi,Kai ya dafe yana Saka hannu abaki,kafin ya Sauke ajiyar zuciya yace"Shikenan ki Adanamin duka Fushinki pretty har na dawo,nayi alqawarin daukan kowani mataki kika Dauka akaina,ammh i want to u to know one Thing i relly miss u so much,and kinbiyani Tunda kikayi Saurin Cafkan sako na,Adaren Farkomu,Allah ya saukeki lafiya.."Yafada kafin ya duka ya bata kissa Ahannunta,ya saka kai Yafice yana mai jin Farinciki,Sai da ta tabbarta da yafita kana ta bude ido tana Dafe kirji tace"Ina da cikin yaya captain yanzu a wannan cikin? tafada Tana dafa cikinta lokaci daya tana Sakin mirmishin Farinciki,hawaye suna zubomata ta sanya hannu ta Share Tana fadin",Allah na godemaka..Ni nan da wata Tara nazama mama"Tafada kafin ta saka dariya ita kadai,shafa cikin take tana mirmishi ita kadai,kafin chan kuma ta Tura baki tana fadin"Ina Sonka,ammh ina Fushi da babanka,duk da kewarsa da Soyyyarsa bazata taba barina Fushina yayi Tasiri Akanshi,Alhamdulillah Allah nagodema.."take Fada tana mirmishi ita kadai.

Shiko Aliyu achan waje,har kasa ya dukama goggo kafin ma yayi mgana tayi Saurin dagoshi tana fadin"Tashi gadanga,Har Abada goggon gadanga bazata yi Fushi dakai ba,konayi baya zuwa ko"ina na yafema Tunranar da naje mkrantansu Azeema Shugaban mkrantar ke Fadamin kagama biyanmta komai,Tun wajen nace na yafema nayita sakamaka albarka,duk da dai Ja"irin ka batamin Rai ammh kadan.."Tafada tana mangaremai kai,dariya yayi kafin ya Fada jikinta ya Rumgumeta yana Fadin"Nayi kewarki goggo.."Kunnensa ta murda tana Fadin"Karya kayi dai kewar matarka ko? ammh bani ba.."Dagowa yayi yana kallonta Kafin ya Shagwabe yana Fadin"Ni Allah goggona nayi kewa.."Dariya tana fadin"Toh naji Nima nayi kewar gadanga ko Tsiyar damuke ankwana biyu ba"a hadu ba..",Dariya suka saka gabadaya kafin Gadanga yace"Goggo zamu koma bakin aiki.."Jinjina kai Goggo tayi kafin tace"Basai kamin bayani ba,yanzu Jabir yagamamin bayanin komai Kuje Allah ya Tsare yakuma bada Sa"a Azeema kuma zan kular maka da ita har kadawo nayi alqawari.."Da Ameen suka amsata mata kafin Suyi mata sallama Su Tafi,daganan Asibitin hanyar gombe suka dauka,dama tawagar da sukazo Tare Tun Sadda zasu kai Azeema Asibiti suka basu Umarnin juyawa gombe,toh Tuni sun damki hanya kilama Sun isa Tundazu.

  Koda goggo takoma wajen Azeema tayi barci lokaci,tatasata tayi tana ta zuba godiya Ga Allah,har saida Tafitar da kwallah,Allah sarki Gadanga,shifa Tunda yatashi baisan dadin wani Dan"uwa ba,sai Hisham,wanda kusan yanayin aikin banki da Tsanani da Takura gashi ba sakewa so basu cika haduwa ba,sai dai awaya,haduwarsa da Jabir yasa yasamu aboki sosai,gashi Allah ya ba matarsa Ciki tana Fatan cikin ya zamanto Silar Farincikin gadanga dasu gabadaya.

Kwanan Azeema daya aka sallamota ta dawo gida,bayan an kafamata dokan banda aiki mai yawa,ba daukan Abu mai nauyi,kuma anbata mgungunar Kara jini,dana saka cin abinci don goggo tace bataci,sai cika ciki da goriba,ba"a hanata cin kayan kwalamanta ba,ammh ance ta dinga cin Abinci sosai,tadai Samu ishasshen Hutu da Lokaci mai Tsawo,goggo ko duk taji bayanan likita Shiyasa suna komawa gida ta zage tayimata Tuwon Semo miyar Kubewa dayan,wacce aka daka kifi aciki,duk da bataci dayawa ba,ammh taci sosai,daddaren Mallam lawal ya Shigo duba Azeema yadade yana mata nasiha hakuri da rayuwa,tare da mata gargadin ta rike mijinta da Amana,nan yake Fadamusu Inna Ramatu tun jiya take kuka da Hajijiya tana Rokon don Allah asakomata Azeeza tatuba tabi Allah,yacema bayan Tafiyarsu saiga Baba Ade tazo,har yara Sun kaimata lbrin Abunda yafaru tazo da kukanta ni nayita bata baki,gyara zama goggo tayi tana fadin"Allah sarki ai tabar kuka,don ta kusa samun megida ko Amarya kai kuma Mallam ka Shiryafa jika na zuwa.."Washe baki yayi yana saka albarka yana kallon Azeema,itako Rufe Fuska tayi Duk kunya ya kamata,Mallam lawal yayi murna Sosai yayita Addu"ar Fatan Allah ya Raba lafiya.


__________________

_Kaduna_

  Yau kimanin kwana hudu kenan da zuwansu barikin baitaba yin nesa daga Sansaninsu ba,iyakarsa Dan haraban wajen,sai jiya kuma da Sukaje bayan bariki sukayi Atisayen Harbi,yau Tunda yatashi yakejin sha"awar zagaye barikin nan duka duk da baisan ko"ina ba yasan baya bata ba,cikin Kakinsu na chan ya Fito yafara Tafiya duk inda yabi yana Daukan Hoto ko video din wajen da Rantsatsiyar Wayarsa kirar Samsumg,Duk inda ya Shiga sai Binsa ake da kallo Abunda yabashi mamaki Wasu Sojojin jahar ta Nageria har kamemai Sukeyi Saboda Su bihakki da gaskiya Dauka Suke Captain Aliyu ne,duk da kuma da bambamcin Uniform din da Suka gani,Abun ya Daureshi mishi kai,sai yakoma daya Hadu dasu yaga sun Kamemai Sun Saramai,kawai sai ya Daukesu Selfe ya wuce yana dariya,suko suyi ta mamaki don Asaninsu Captain Aliyu baya dariya Sai dai mirmishi ko kaga yadan murmusa kumatu kadan.

Yana Tafe yabada baya yana Daukan wani lafiyayyan Titin daya Shararo,wajen ya burgeshi yadda kasan ba"a Nageria ba,kamar akasar Turai saboda Haduwansa gashi so quit,ga wasu Fulawoyi dasuka kawata wajen,sojojin dasuke wucewa kadan kadan ne,sakamakon Lokacin da Safe ne sosai ba'a Fito Training ba.

Jiyayi ya bangaji Mutum harsaida wayar dake hannun Wanda sukayi karo da Umar din,tafadi kasa da hanzari Umar ya sanya wayarsa a aljihu ya duka ya Tattaroma mutumin wayarsa wacce ta watse yana fadin"Am so Srry did know u are coming Srry...",Yafada yana dagowa karaf ko suka hada ido da Jabir wanda ke Tsaye yana karemai kallo sama da kasa kafin ya zaro ido yana Rike baki yace"Kambu Dude,basaja kakoma kuma,yau Abun naka harda komawa Sojan Niger.."Yafada yana Dariya galala Umar yayi rike da waya yana kallonsa bakinsa na motsi yace"ni..Ni..Bansan meka ke mgana akai ba fa? Kafadansa Jabir ya daka da karfi yana fadin"Kai Dude dawo hayyacinka kasan dai ni bazakamin layan zana bako?any why yau fa kasan akwai Atisayen gudu ina kuma zaka naganga ta nan? Umar ya lumshe ido kafin ya bude,baiyi mgana ya Rike hannun Jabir ya damkamsa wayarsa yana fadin"Ba wanda Kake Tunani bane,Ni Sunana Leuitenant Umar Abdulnaseer Tambari buzu ina daga cikin bakin Sojojin da suka sauka Shekaranjiya.."Kuramsa ido Jabir yayi kafin ya warci wayarsa yana Fadin'Kajimin dan iska,Umar kuma kakoma? Toh in bakai bane waye,Nikaga Tafiyata mallam,dama kai baka Rabo da Maida mutane yan iska..",Yana Fadin haka ya juya ya cigaba da Tafiya ko waigowa baiyi ba,Galala sake da baki Umar ke binsa da kallo kafin ya rike baki yana Gyada kai,mamaki yakamashi,ammh sai bai ba Mamakin matsungunni ba,juyawa yayi yakoma,ammh kuma Abunda yafaru ya tsayamai Aranshi.

  Jabir da hanzari yakoma barayinsu yana zuwa kofar Apartment din Aliyu ya ganshi ya Fito sanye da kayan gudu,cogewa yayi agabansa yana kallonsa Abun ya bashi mamaki,toh wannan Aljanine,yanzu fa ya ganshi Aliyu dake tsaye yaga yadda Jabir ke kallonsa Tsaki yaja yana Fadin"Kai fa dan iskane lafiya kawani kuramin ido,bafa wannan kwailar budurwantaka bace"Yafada yana hade rai,Hararansa Jabir yayi kafin yace"Durun uwar kwailar,Ai kwaila bata Wuce Azeema ba.."Dirowa Aliyu daga saman Apartment dinshi ya Naushi Jabir agefen ciki kafin yayi gefe yana fadin"Ai Azeema Ta wuce kwaila Tunda ta iya daukan Nauyi na,har gashi tana Dauke da ciikina,kuma wannan ne last time dazaka kara kiran Sunan matata gatseai ba sakayawa,Tunda ba sa"arka bace.."Jabir dake duke yana rike da gefen cikinshi ya dago yana Fadin"Allah ya isar min mugu kawai,don kaga kai ka fara kokarin ijiye kwanka aduniya Shine ni zakamin mugunta Rasa nawa,ta Allah bata mutum ba.."dariya Aliyu ya saka mai kayatarwa yana Fadin",Au kudai zauna yanzu nagama yima gayen nan Hisham,nace ya zauna aikin banki ya daskararmai da kwan haihuwa,ko kuwa zama waje daya da Wuni cikin Ac,ya Lusarar dashi,sai bayan anyi Aure aji mata ta gudu taga ba bayani"Dashi da Jabir din suka saka dariya atare harda Tafawa Jabir yace"Kai Dude kasan kan Tsiya fa"Yafada yana Fada kadafadansa kafin yace'Kai Dude Seroious Fa,kana aiki da Aljanune,yanzu fa naganka sanye da kakin Sojin Niger,yanzu kuma na ganka da kakin Sojan Nageria kuma banga sanda kadawo harka chanza kaya ba,wai kodai layan zana gareka.."Kallonsa Aliyu yayi yana Fadin"Tsiyana dakai kwakwalwarka bataja,Ni da yanzu Fitowata kenan,kuma banda Abunka meya hadani da Sojojin Niger da har zan sanya kakinsu,..? Rantsuwa Jabir ya jero yana Fadin"Wlh da gaske,wai bakai bane Harfa kacemin Sunanka Umar Abdulnaseer Tambari buzu fa? Har Aliyu ya juya Yafara Tafiya jin sunan da Jabir ya ambata sai dayaji yanayin jikinsa ya chanza,waigowa yayi yana fadin"Ni kuma? kai mallam kafara Rudu wlh,bani bane kaji na Rantse maka ma,yanzu dai duk ba wannan ba kashiryo kazo muje Atisayen gudu da za"a gudanar yau.."Yana gama Fadin haka yayi gaba da dan gudunsa.

Tsaye Jabir yayi yana mamakin wannan al"amarin Hannunsa bisa baki yana fadin"Bashi bane to waye? yafada yana kada hannu Alamar Abun yabashi mamaki,tsaki yaja kafin yace"Mtsewww shege shine fa,so yake yayi Wasa da Tunanina"Fadin haka yasa ya juya yashiga part dinshi da gudu domin Shiryawa domin Atisayen na yau na musamman ne,domin Duka Shuwagabannin kowani bangare zasu Koyar da Atisayen na yau,duk acikin salon Dabarun yakin daza"a koya musu ne, na Tsawon Sati daya duk da su sun dade da kwarewa game da Aikin,ammh dalinlin bakin Sojojin dakuma Turasun da gwannatin Nageria zatayi zuwa wajejen da yan boko haram suka mamaye.



*JANAFTY*😘
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

           

           *Chapter 29*

    ""Har aka gama Atisayen gudun Gadanga da Umar basu hadu ba,sakamakon Filin ya cika da Sojojin Nageria,dana cameron Chadi,da Niger,kuma akallah kowacce tawaga zata kai kimanin Mutane Dari uku,shiyasa ba wanda yahadu da wani acikinsu tunda ba"a Batch daya suke ba,Jabir ko shima yayi Dube Dubenshi baiga ga Wanda yagani dazu ba,sai ya barshi atabbas Aliyun yagani ba wani ba,ko awashegari
End Ads