x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 27 - ALIYU GADANGA

  • 78001 words
  • 81000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 177

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
amfani da sunan mahaifi daya tare da sunan Masarauta,Aranar hadda Bala munyi mgana bayan ya tabbatarmin da kina raye,ni na hana agayamiki komai nafison nazo dakaina ki ganni na ganki bayan na baki lbrin duk Abunda yafaru Shekarun baya,Wannan itace mahaifiyata yafada yana nuna Ummah mai babban daki sai Matata ta fari Gimbiya Fasilatu ita ta haifarmin yaro namiji mai suna Umar gashinan,sai gimbiya Razeenah mahaifiyar su Zafira da Safaratu kenan,Bayansu bankara haihuwa ba,bani da wasu ya"ya bayansu,ina Fata da wannan bayanin zaki dubeni da idon Rahama Suwaiba ki yafemin barinki danayi na tsawon lokaci batare dana waiwayeki ba.._



Gabadaya wajen yayi tsit harda masu kwallah irinsu madina da mardiya da Ummah,Goggo kuwa kanta na bisa kafadan Kawu tana Fitar da kwallah,hatta Azeema sai ta koka,Maimartaba ma kukan yake ammh yana saka gefen Rawaninsa yana Sharewa ammh idonsa kur akan Suwaiba,Ummah mai babban daki ta mike ta isa ga Suwaiba ta dafa kadanta tana Fadin"Dago kanki Diyata...",Jiki asanyaye ta dago tana kallon Ummah mai babban daki wacce idonta ya cika da hawaye tana Fadin",wlh tallahi duk tsawon wannan Shekarun Abdulnaseer baiyishi cikin kwanciyar hankali ba,muma namu hankali ba"a kwance yake ba,kullum rokom Allah nake ya bayyana mai koma miye shi,gashi yau Allah ya amsa rokonmu kiyi hakuri kiyafamai nayi miki alkawarin bazai kara barin ki ba.."Tafada hawaye suna zuraromata Goggo da jikinta yayi sanyi ta dago tana kallon maimartaba wanda yake kallonta da tsausayawa kafin ta maida hankalinta kan Gadanga wanda ya hada hannayensa yana nuna mata alamar roko,Komawa da kallonta tayi kan su Madina taga suna gyada mata kai,balle kawu dayake ta murza kafadanta alamr lallashi,Kanta ta mayar kasa kafin ta share hawayenta tace"Shikenan...Na yafemai Duniya da lahira.."Ummah ta rumgumeta tana dariya Gabadaya wajen kowa ya sauke ajiyar zuciya harda maimartaba wanda yaketa maimaimata Alhamdulillah Aransa ashe afili yakeyi,gadanga ke kallonsa yana kunshe dariya.

Ummah mai babban daki ta dago Fuskar goggo tana fadin"Sai wata alfarma daya danike rokonki Suwaiba.?."Akunyace goggo tace"Mene ita..? Ummah na kallon Fuskar maimartaba tana Fadin"Ki Amince amaida aurenku da Abdulnaseer,In zamu koma Masarauta kibi mijinki ki koma tare dashi..."Gabadaya wajen aka Tsurama goggo ido,wacce kunya ta kamata kamar ta nutse,gimbiya Fasilatu kuwa kamar ta mutu saboda bakin ciki da kishi,Gimbiya Razeenah kuwa mikewa tayi ta isa ga goggo tana zauna tana riko hannunta take fadin"Kiyi hakuri karki ce A"a domin Maimartaba hankalinsa bazai taba kwanciya ba,balle har ya iya zaman Fada ba balle har ya gudanar da sha"anin mulki ba sai dake,don Allah ki amince amaida aurenku in zamu koma mutafi dake masarauta muzauna mu Rumgumi mijinmu don Allah..."Tafada tana kallon kwayan idon goggo,wacce saboda kunya kamar ta nutse,in tace bata son mijinta tayi karya,Shiko maimartaba idonsa na kan goggo gabansa na Faduwa kada Suwaiba tace"A'a..."


goggo ta dago kanta ta bude baki zata yi mgana kenan su gadanga dasu madina suka hada baki suka ce",Karki ce A"a goggo..."Suka Fada kamar zasu kuka,kawu yace"Toh kinji suma ya'yanki suna miki sha"awar komawa Rayuwar aure wacce zaki rabauta da ita har gobe kiyama.."Yafada cikin siyasa Ummah dake gefe ta dinga Kyaftama goggo ido😂wai ta yarda goggo na jin kunya ta dago tana kallon maimartaba wanda ya Langwabe kai,alamar ki yarda dani,Saurin kauda kai tayi tana Fadin"Na Amince..."Ai gabadaya wajen ya dau ihu,Ummah ko ta ware ta dafa hanci ta saki guda,suko Fadawa nan suka fara busa algaita suna Fadin"Angaisheki giwar sarki,Angaisheki Gimbiyar Sarki...Sarkinmu na godiya ga Amincewarki Allah yabar soyayyah..."Dariya akasa gabadaya Goggo ko kunya kamar ta nuste,shiko mai martaba dariya yake har hakoransa suka bayyana waje yana kara godema Allah,addu"a Gadanga yayi aka Rufe taro da addu"a kafin abude shashenshi su Maimartaba aka Saukesu anan,itako Ummah mai babban daki tana dakin goggo ita da jikokinta ana shan hira da dariya,Ita dasu jabir da Haisam suna Fadin suma fa dole su garzayo masarauta sunga iri😜😿Ummah mai babban daki tana Fadin ba wanda zata bamawa,Suko su Zafira suna makale da Azeema wanda suke tare dasu Anty madina,Ummah ko natare da goggo wacce gimbiya Razeenah ta Shige cikinsu ana hira,Shiko maimartaba yana shashen gadanga,suna hira shida Kawu da Mallam lawal wanda kawu yake bama maimartaba lbrin Abunda ya Faru bayan tafiyan shi da dalilin barowarsu zaria yazo ya saima goggo gida anan,Maimartaba ya jinjina al"amarin kuma nan take yace zasu zaria har anguwan da suka zauna,dagachan sai ya wuce Fadar maimartaba Sarkin Zazzau,Gimbiya Fasilatu kuwa tana dayan bedroom din Gadanga tana Fama da bakinciki,Bayi kuma mata,dakin dake tsaKar gida aka Saukesu Maza kuma akwai wani daki a shashen gadanga ammh yana da kofa ta waje shi aka bude musu,inna ramatu tanajin sadda goggo tace ta amince da Auren sarki ta sulale ta fita tana zufa kafin kace kwabo tabi anguwa ta yada lbrin mahaifin gadanga Ashe sarki ne,goggo kuma matar sarki zama amaida aurensu tabishi chan masarauta.

Shiko kawu ta waya yayi mgana da kwamishinar yada lbrai na jahar gombe yayi Narrating komai ya sanar dashi yace yana so,abuga lbrin akowacce jarida bayan afitar da sanarwa akowani kafafan yada lbrai,harta kaduna sai da yayi waya ya sanar kuma yace kafin gobe yake so lbrin ya karade duniya gabadaya Maimartaba yaji dadin haka sosai,saboda masu son Shegenta masa da,yau sun sani cewa Captain Aliyu ba Shege bane yanada cikakken Asali,kuma Asalin ma daya fi na kowa.


Anty madina da Anty mardiya da Azeema da su Zafira suka Fada kichen domin yin girki saboda yau dai Ahalin yayi albarka sai wanda ya gani.




_*Ina bukatar Addu"anku daga bakunanku masu albarka,ina cikin damuwa,tare da Fuskarta wata jarabawan Rayuwa,kumin Fatan Allah ya bani ikon cinye jarabawata,in kuma Alherina ne Allah ya Tabbatarmin dashi ya kauda duk wata Fitinar dazai Tunkari al"amarin*_🙏


    
*JANAFTY*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_

*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

        *Chapter 33..*

"Abinci mai Rai da lafiya suka girka,suka zuzzuba amanyan kololi,suka kai kowani Shashe,bayan sun Hada da lemuka da Ruwan gora,Su maimarta suna dai barayin gadanda suna cin nasu,ayayinda su gadanga suka hade Shida manyan Aminan nashi,Azeema ko dasu Zafira,sai su Anty mardiya da ita da Anty madina,goggo kuwa kunya takeji takasa ci,ummah mai babban daki ita kadai takecin nata,Ummah kuma ita da gimbiya Razeenah,Fasilatu kuwa babu wanda yabi ta kanta don Tunda ta Shiga ciki bata Fito ba,bayi da Fadawa ma ankai musu nasu barayinsu.

Ko kafin yammah tayi lbri ya Mamaye gari tako"ina mutane sai Shigowa suke suna ma goggo barka tare da Murna lokaci daya,wasu gulma ke kawosu,na ganin sarki da ake fadi,don wasu gani suke duk zence ne,aikuwa Maimartaba bai hana kowa ganinshi ba, yace abarsu suyi ta Shigowa yama Fi son hakan,da dare yayi maimartaba Sarkin gombe yaso Sarki Abdulnaseer yakoma masarauta,ammh yanunamai yafiso zamanshi anan,ko banza inda Suwaiba tayi rayuwa ne,ita da gudan jininsa,Shiko Aliyu yaso kebewa da Azeema ammh babu dama,yadda gidan yacika ne yasa sukayi musu sallama suka koma hotel din da suka kama ma Umar daki da safe suka kwana da Safe koda sukadawo suna cikin Shirinsu ne,don Maimartaba yace ayau din zasu kaduna sukuma biya zaria duk atare.

Inna Ramatu kunya da Nadama duk sun kamata,yau dai ga goggo data ke zagi tazama matar sarki,yau ga Aliyu datake yawon Fadin baida Asali Ashe dane,ga Sarki,da mallam lawal yadawo ya isketa tana kuka,ko kallo bata iaheshi ba,saima gyara kwanciya dayayi,yanaji tana kuka tana rokonsa wai ya roki Aliyu don Allah yasa baki Asaki Azeema wlh tayimai alqawarin bazata kara barinta ta aikata wani Abu makamancin Abunda ta aikata ba yana jinta yayi mata banza,saima Juyamata baya dayayi,Aransa yana Fadin bai yarda da Nadamar Ramatu ba haryanzu.

Koda su Aliyu suka dawo sun iske kowa ya Shirya, Nan suka iske Baba Ade tazo, yima goggo barka da kuma taya Aliyu Farincikin Saduwa da mahaifinsa,Hatta da goggo ba"a barta abaya ba ta Shirya tsab da ita,akwatun kayansu aka saka amota ita Azeema tunda zasu dan kwana biyu inji kawu,Su Aliyu ne zasu yi Tafiyar mota zuwa kaduna,su kuma sauran Jirgin maimartaba zasu bi,Gabadaya gidan aka Fito domin Tafiya su Aliyu tuni sun mika hanya Su maimartaba ne tsaye suna bankawana da su mallam lawal,sai ga inna Ramatu ta Fito daga gida da gudu ta zube gaban maimartaba tana kuka,mallam lawal kuwa yana ganinta yafara hararaart maimartaba ne ke tambayanta Meyake Faruwa tana kuka tana Fadamai kamun da Aliyu ya sanya akama Azeeza,Jinjina kai maimarta yayi kafin yace"Ash Abu baiyi kyau ba tashi tashi insha Allahu zan shashi yasa asake yau din nan.."Yake Fada yana kallon Kawu kafin yace"Bala don Allah kiramin Aliyu.."Kawu baiyi gaddama ba ya ciro waya ya kira Aliyu wanda ke gefen Jabir yana driving,Umar da Haisam suna bayan mota,da Azama ya daga kiran kawu yana Fadin"Hello kawu.."Bai yi mgana ba ya mikama Maimartaba wanda yace"Aliyu..."Yafada cikin dattako da mulki,saurin gyara zama yayi yana Fadin"Na"am Abbah,kun taho ne..? Bai bashi amsa ba yace"Yarinyar nan daka sa akama kanwar matarka kakira waya yanzu ka saka asaketa Umarni na baka ba Shawara.."gyada kai Aliyu yayi kafin yace"Angama Ranka ya dade.."Yana fada yana katse kiran,nan take yakira DSP MALEEK KABIR KUMO,sukayi mgana kafin ya bada Umarnin sakin Azeeza,nan sukayi mganar cewa bayan ya dawo yazo nan headquater su,akwai File din da zai cike nan sukayi sallama,jabir ne kawai yasan Abunda Ke Faruwa baiyi mgana ba,ko banza ai Ta horu Shegiyan.

Daganan Fadar maimartaba Sarkin gombe Suka wuce sai da sukayi sallama kafin su isa Airport,dama jirginsu na nan,Suka Shiga suka Lula sararin samaniya,Akaduna suka yada zango Tunkafin su iso mai girma gwanna Jahar kaduna * MALLAM NASIRU AHMED YAR RUFA'I yazo da kanshi ya ya tarbeshi Shida tawaganshi,Sai da sukaje gidan gwannati kafin su wuce gidan kawu,wanda ya kasance Aljannar Duniya nan kowa ya baje,don mamaken gida ne,mai Shashe har guda uku,kowanne ya gaji da haduwa,sai lokacin su Aliyu suka kariso suma,kafin isowasu Aliyu ya amsa waya tafi dari na yan"uwa da abokan Arzuka suna tambayanshi Shin Abunda suka gani gaskiya ne,da eh kadai yake amsawa,sai Barka mutane kemai da tayashi murna,daya gajima kashe wayaryi,Ko!ina na garin gombe jaridu suna ta yawo banda gidajen talabijin din da"akayita watsawa ana nuna Hoton Aliyun dana Maimartaba Sarki Abdulnaseer,Wanda jama"a dadama sunyi matukar mamaki,ciki harda da Ni"ima da iyayanta,mami tana hawaye tana kallon Cp Ahmed Sidi na Iya,wanda yayi Tsuru duk kunya ta kamasa,itako Ni"ima daki tayi dagudu Sauri tana kokarin kiran Muneera dataga ta kirata.

Kunya duk takama Kwamishana,sai zare ido yake,Mirmishi Mami tayi tana Fadin"Ka gani ko? wannan Ranar nake jiyemaka yallabai,kabiyema Sharrin shedan da hudubar dan"uwanka gashi yau kaine,akunya yanzu duk amtsayin kaje kayi gaba da gaba da Sarki,wlh ko haka Allah yabarmu munga sakayyah,Tunda diyar tamu nan harynzu agabanmu kuma tace inba Aliyu bata ba Aure har Abada.."Tana gama Fadin haka tatashi Tafice ta barshi nan yana zufa,lalle al"amarin Allah Kenan,ashe yaron ma yawuce duk Tunaninsu ashe shi din Da ne ga Sarki yanzu haka Shidin yarima ne,Lalle ya tafka kuskure babba ma kuwa.
  

***************

Azeema ce Tunda yammah tayi take kwance Zuciyarta da gangar jikinta babu wanda suke bukata sai Mijinta gashi kuma gidan yana cike da jama"a,ita yanzu ya zatayi kwance take tarasa mafita,Duk wanda yazo ya ganta kwance sai tace batajin dadi ne,Rasa mafita tayi shiyasa ta aika hibba data aro mata wayar Anty madina,tunda ita tata ta barta Akaduna Tun Sanda Abun nan ya faru,ana kawo mata wayar ta Shige tiolet ta kulle ta lalubo lambar Captain takira wanda suke chan Wani Shashe shida su Jabir yanaganin kiran ya daga ammh kuma sai yaji Shuru anki mgana,sake duba mai kiran yayi kai Tsaye ya Furta.."Pretty..."Yafada yana Tashi saboda su Jabir da suka Tsuramai ido,Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shagwabe Fuska tace"Bawani pretty,Bayan Tun ranar baka kara nemana ba.."Kanshi yashafa,jin yadda ta kashemai jiki,yace"Ba haka bane pretty kema kinsan dalili aie,ammh koda yaushe kina Raina abar Farincikina.."Mirmishi ta saki tana Fadin"Da gaske..."Tafada tana dariya basar da tambayan yayi yana Fadin"Meke damunki ne,? kowani Abu kike bukatane pretty..? yafada yana Danne dariyansa,Hararan wayan tayi kafin tace"Ni bana bukatar komai..Kai..Kai ne nake son gani.."Tafada tana Rufe fuska,yar dariya yayi yana fadin"Yanzu kuwa zanzo Tunda Service yatashi yanzu an neme ni aie..."Yafada yana rike dariyansa jin ya ganota yasa tayi Saurin katse katse kiran tana dafe kirji kunya duk ya kamata.

Shiko daganan cikin gidan ya Shigo su goggo suna Falo ya gaishesu Rasa inda Azeema take yasa ya kira hibban madina ya tambayeta akunne,Nuna masa sama tayi alamar Tana Upstairs,Sosa kai ya Shiga yi kafin ya mike rike da hibba ya fara Taka Steps,dukkansu nuna sukayi basu gansa ba,kowcce ta dauke kanta,su Zafira suna ankare da yayan nasu,suna danne dariya,Sai da yakawo kofar dakin kana yace ma hibba"Toh maza koma wajen goggo yanzu zan dawo.."Jin haka yasa takoma da gudu tana murna,murda kofar dakin yayi ya Shiga da sallama,tana zaune kan gado,kanta babu dankwali tayi tagumi don bata zata zai zo ba,ganin ya Shigo yasa tadawo natsuwarta harda wani juya baya,Ganin haka yasa yayi Saurin karisawa gareta ya rikota yana Fadin"Am Srry pretty... ba gani ba.."Yafada yana Shinshinar wuyanta,Jin yafara chanzamata yanayi yasa ta saki jikinta itama ta rumgumeshi tana Shakan kamshinsa harda su lumshe,Matseta yayi yana Fadin! I miss u pretty.."Miss u more and more Yayana.."Kamkame juna sukayi kafin sufara sumbatar juna kamar wasu mayunwata,Azeema fa ba dama,domin Ture Captain tayi ya fada gefe tabishi ta danne tana wani kallonsa ta gefen ido,idonsa ta sa hannu ta rufe kafin ta hau zare kayan jikinta bata barshi ya bude ido ba,sai da yaji tana zaremai Rigar Shirt din dake jikinsa,Bai yi gaddama ba ya taimaka mata suka cire duka kayansu blanket ya jamusu suka Shige,Yau Azeema da zafinta take kai Farmaki Shiko yana Neman kare kansa,kafin kace kwabo an lulu barnin da bakowa ke zuwa ba Sai me rabo,.

Tsawon minti talatin kafin su samu Natsuwa Rumgumeta captain yayi yana saka mata albarka domin Duk sanda zai kusanci Azeema ji yake babu bambamci da daren Farko,abunka da mai Shigar ciki tare sukayi wanka kafin yayi wanka tsarki ya fito ya barta itama tayi,kayan jikinsa ya maida,sai lokacin kunya Abunda suka aikata ya Shigeshi yanzu taya zai iya Ratsa mutanen falon ya Fita haka dai ya kukan Kuran Fita,domin alokacin anata kira kiranyen sallar mangariba,Yana Fitowa yaci sa"a babu kowa afalo,sai su hibba suna wasa,Da hanzari ya sauko ya Fice,yana Fitowa yaci karo da su Haisam suma sun Fito zasu masallaci,suna ganinshi suka tsaya suna kallonsa yake yayi musu yana Fadin"Muje mana,ba sallah zaku ba.."Haisam ne yace ahankali"Kayi wanka kuwa..? zaro ido yayi kafin yace",Wankan me? Jabir ne ya duke yana kallon Umar kafin yace"Wankan Janaba mana.."wani dogon tsaki Aliyu yaja yana fadin"Janaban Ubanka,kudai yan iskane idonku na kan Sunnah kuna saka ido,kuka sani ni banda lokacinku kunga tafiyata. "Yafada yanayin gaba,suko suna mai dariya,Umar dake gefe yana dariyan yadda yaya Captain din ya hade rai,wai shi dole tsare gida har sukaje masallaci bai kulasu ba wai shi adole bayasaon Raini,cikinsu maimartaba dasu Kawu ya Shige dasuka mai mgana yace"Gaskiya ya lura zaman dayake acikinsu ma zubar dakaine,a mtsayinshi na magidanci mai mata harda ciki,sukuma amatsayinsu na yara kaskancine,kawai su kama kansu shima yanzu zai chanza taku ne,gwara yafara zama cikin manya Shine mutumcinsa"baki Haisam ya rike yana fadin"Kut..Kai wai ban girmeka ba..?"Wani banzan kallo Gadanga ya jefamai kafin yace"Koda ka girmeni ai baka halliceni ba.."Yafada yana wucewa ya barsu suna zaginsa shida jabir,Aransa yace",Na bar kara zama cikin yara daga yau.."yafada yana yar dariya😜😹

Tun Adaren Aliyu ya samu kiran Ni"ima Tana mai murna,bayan itama harda mahaifiyarta tabamawa mami,wacce ketayashi murna itama amsa musu yayi kafin yayi musu godiya suka yanke kiran,Shuru yayi yana Nazarin wani Abu kafin ya saki ajiyar zuciya yana ayyana Abubuwa dadama.


Washegari suka wuce birnin zaria,A Fadar maimartaba suka yada zango,Maimartaba sarkin zazzau yaji dadin wannan ziyarar ta Sarkin Agadez maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yace dama yaji lbrin zuwansa bai zaci zai zo har Yankinsa ba,An gaisa cikin mutimci sosai kafin wasu jawaban su biyo baya,Maimartaba sarkin zazzau yayi mamaki wai sarki guda ya zauna agarin zaria abaya,lalle Allah mai hikima da kari,su jabir kam sai zagaye masarauta suke,suna fadin"daliin kaza gadangare kansha Ruwan kasko,yau gashi dalilin gadanga sun shiga masarautu dadama,haka su madina ke Fadi,ummah ko baki yaki Rufuwa godema Allah kadai take,domin dalilin goggo sun taka in ba basuyi tsammani ba,daganan Fadar tare da rakiyar Adalin Sarkin zazzazu suka iso anguwan dasu Goggo suka zauna,Allahu akabar Asalin gidansu nan nan kawu ya gyarashi yasaka wasu mutane suna zauna don Allah,saboda su kula da gidan karya lalace,zuwansu gidan yasa Sarki da Suwaiba suka tuna wasu al"amura da suka gabata inda dakinshi yake awanchan karon yanzu wajen ne aka kafa famfo,Maimartaba ya kurama wajen ido,hawaye suna taruwa a idonsa hakama Goggo,mutane anguwa kuwa da lbri ya samesu sunyi matukar mamaki,akwai dattawa dake da rai haryanzu,sai kuma wadanda suka samu lbrin bayan abun ya Faru,basu jima ba suka koma masaurata Tunda Allah ya wanke suwaiba da Da'nta,daganan kaduna suka dawo saboda Shirye Shiryen Tafiya chan Masarautar Tambari buzu ammh bayan An maida Auren goggo.


Kawu da Maimartaba basuyi Shawara dakowa ba,washegari bayan sallaar Jumma"a aka maida Auren goggo da Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,akan sadaki dubu Dari biyar,wanda awajen Daurin harda Maigirma gwannan jahar kaduna,Wanda aka daura amsallacin Sultan bello,Yan mazan ne kadai suke da masaniya sai da suka dawo gida suke Fada,goggo jitayi Abun yayimata wani banbamrakwai daki ta Shige tarufe kanta ganin yaran sun Faramata shakiyanci da Amarsu😛,Gimbiya Fasilatu kam dataji lbri kamar ta mutu takeji ga Danta Shima gabadaya taga baya tsaginta yana manne da dan'uwansa kamar wani zai rabasu,ga gimbiya Razeenah itama ko ajikinta harda ita cikin masu cewa agyara musu goggo,don so suke maimartaba ya rude fa😿Ummah mai babban daki kuwa wani lokacin tafi zama cikin Su Jabir kodon yadda take sakasu dariya,suko su Zafira basu iya saakewa ciikinsu saboda yadda su Haisam da jabir ke damunsu da kallo,Umar ne ya lura har ya shafama Aliyu,dariya takamasa yana fadin"Daz great,karabu dasu lalle wasu yara zasu dawo cemin babban yaya"Yafada yana dariya har ga Allah Abun yayi mishi dadi ko banza zai samu hanyar sakamusu da Abunda sukayi mishi,kuma zumuncinsu zai kara karfi fiye da Da.


Washegari kawu ya umarci Ummah da Goggo da Azeema da Aliyu su tafi gombe su
End Ads