Tambayan Aliyu yake kallonsa kafin yace"Ah Ko Azeemar bataje mkrantar bane yau..?
Sani mai KekenNapep yace"Shine Abunda yadauremin kai yallabai,ni dakaina na kaita mkranta yau da safe,ina kallo ta shige cikin haraban mkrantar,ammh Abun mamaki bayan antashesu naje daukota,ammh har duka Yan mkranta suka gama watsewa banganta ba,shine nazo nagani kodai tadawo gida da kanta ne.."Sororo Aliyu yayi kafin yace"How comes anya Azeema tadawo kuwa?bandai sani ba,buh bari na shiga na tambayi goggo naji wait for me.."Yafada da sauri yana fadawa gida,Tundaga nan yake kwalama goggo kira wacce ke daki ta zabga tagumi har lokacin dawowan Azeema yayi ammh shuru,da hanzari Ta fito,zaninta ahannun yana neman Faduwa tana fadin"Gani gadanga lafiya irin wannan kira haka? tafada cikin tashin Hankali
Gabanta yaci burki yana fadin"Goggo ina Azeema.."? Fuskar damuwa ta bayyana ga goggo tace"Nima yanzu nake Shirin kiranka awaya Tundazu lokacin dawowarta yawuce ammh haryanzu shuru bata dawo ba,bakana da nombar mai Keken ba kirashi muji kowani aiki ne ya tsaidashi baije ya daukota ba."Kansa ya dafe yana fadin"Kash..Wayyo To ai goggo ga Sanin chan,yace shima yaje mkrantar su Azeemar ammh har kowa ya watse bai ganta ba.."Salati goggo ta fara tana fadin"Na shiga uku ni Suwaiba.,To yanzu ina yarinyar tashiga kuma ba dabi"arta bane biye biye,toh ina ma ta sani balle taje.."
kallon goggo yayi kafin yace"Goggo kishiga gidansu kigani kila ta biyo yar"uwarta sun dawo tare.."Da hanzari goggo tace"Eh kila ta yuyu haka din ne,bari naje na gani.."Tafada Tana Fadawa daki,Hijabi ta sanyo ta fice da Sauri ta bar Aliyu na Dafe kansa baisan dalili ba yaji hankalinsa yatashi,goggo na fita taci karo da Dan adaidaita,yana ganinta yahau Fadin"Ah Hajiya an ganta ne..? ko kallonsa Goggo batayi ta fada gidansu Azeema tana zabga sallama ko izini ba"a bata ba,ta sakai cikin Filin tsakar gidan,nan ta iske Azeeza da Inna Ramatu suna zaune kan Tabarma suna cin dankali,suka ga goggo ta fado kai tsaye inna Ramatu ne takalli goggo tana cewa"A"a suwaiba lafiya naga kin fadomana gida, tamkar wani ya biyoki daga waje.."
hararanta goggo tayi kafin tace"Azeeza ina Azeema.."?Tun dazu bata dawo gida ba,ko kin ganta yau amkaranta.."?Tafada tana maida kallonta kan Azeeza,Jin haka yasa Ran Azeeza yayi fes Tsarinta yana tafiya kan tsari,Mikewa tayi tana fadin"wlh tallahi goggo yau kaf ban saka Adda Azeema a idona ba,dana ga banganta ba bayan antashi break,naje ajinsu ammh ban ganta ba,na tambayi yan ajinsu sukace batazo ba yau,dama taje mkranta ne yau..? Azeeza ta fada cike da makirci,baya goggo taja tana fadin"Armmm.,Bakomai.."Tana fadin haka tafice da sauri Inna Ramatu ta bita da kallo kafin ta maida kallonta kan Azeeza wacce ke mirmishi mai Fitar da amon Sauti Tabota inna tayi tana fadin"Ke nifa nashiga rudu mai wannan uwar sojan mara mutumci,take son Fada.."
Kallonta Azeeza tayi kafin tace"Wai bakiji metake fadi bane Adda Azeema ne Tafita da niyyar zuwa mkranta,shine ta sanfe wani wajen haryanzu bata dawo ba..."Baki inna Ramatu ta kama tana fadin"Au hakane eh lalle yanzu na Fahimta,toh ammh ina Azeema zata,bata da dabi"ar yawon banza kuma fa.."Wani kallo Azeeza ta watsama inna kafin ta kama hanyar daki tana fadin"Ada kika sani,ammh yanzu baki da tabbas akan hakan.."Tana gama fadin haka ta shige daki tana kunshe dariyan Farinciki.
Goggo ko tana Ficewa sukaji karo da Gadanga awaje Shida sani mai Adaidaita,da hanzari Aliyu ya karisa ga goggo yana fadin"goggo an ganta."girgiza kai Goggo tayi tana fadin"tace duk yau bata ganta amkaranta ba,tamaje har ajinsu bata gantaba, data tambaya akace batazo mkranta ba yau.."dan yatsansa Aliyu ya sanya abaki ya ciza kafin ya waiga yana fadin"Ka tabbata Sani ka ga Shigan Azeema mkrata yau da safe.."? Rantsuwa sani ya kwaso yana fadin"Wallahi tallahi yallabai da idona naga Shiganta mkranta na Rantse harga Allah..."jin haka yasa Aliyu yin gaba yana fadin"Shiga mutafi chan mkrantan nasu,goggo ki koma gida,komai ake ciki zamu mgana ta waya.."Yafada yana Shiga Adaidaitan,Da hanzari sani ya zagaya ya shiga ya tada adaidaitan suka fice daga layin,goggo na tsaye Abun duniya ya isheta.
Suna Zuwa mkrantan kai tsaye office din principle,din mkrantan suka nufa,nan suka samu principle din bayanan ammh Vice dinsa na nan,Nan Aliyu yayimai bayanin Abunda ke tafe dashi,Cikakken Sunan Azeema ya tambaya shikuma ya fadamai,report book ya shiga dubawa nan yaga sunanta ita da Azeeza amtsayin wacce ta rakota tabada report din domin Abunda Azeeza bata sani ba kowani report sai an Rubuta kuma in bata manta ba,dukkansu sai da suka fadi sunansu da class din da kowannensu yake,Nan vice principle din ke fadama Aliyu cewa da misalin karfe 8:00am na safe sukazo suka shigar da report din, Azeema lawal bature zata koma gida sakamakon bata da lafiya wacce kuma tabada report din Sunanta Azeeza lawal bature,Aliyu bai tsaya mamaki ba,sai ya tuna Abunda goggo tace Azeezar tace,kenan duk inda Azeema Take Tana da masaniya duk Abunda yafaru da hanzari yayi sallama da vice principle din yafice saboda bacin rai yana zuwa bakin get din mkrantan,yasaka hannu ya tsaida dan Achaba,yana hawa yakalli sani mai adaidaita yana fadin"kaje kawai mungode.." daga haka yace ma mai mashin yaja suje,Sani yabishi da kallon mamaki ganin yadda yake wani huci kamar mayunwacin zaki saboda Fushi.
Shiko Aliyu gani yake mai mashin din baya gudu sosai jiyake kamar yayi tsalle yaganshi gaban Azeeza,Shiyaasa suna kawowa ko gama tsayawa mai mashin din baiyi ba ya dirarka Hannu ya sanya a aljihu ya ciro wallet dinshi 1k ya zaro ya mikama mai mashin din,yana kokarin bashi chanji ammh kamar kiftawa da bismillah ya shige gida da gudu,sai kace wani walkiya cike da mamaki mai mashin din ke binshi kallo kafin ya juya akalan mashin yana fadin"Inaga Rabo na ne kejana.."yafada yana buga mashin din ya bar layin aguje yana waige wai kada Aliyu ya fito amsan chanjinsa,Shiko Aliyu yana Shiga gidan yacikaro da goggo na zaune atsakar gida,ta zabga tagumi taga ya shigo kamar walkiya ya fada shashensa da hanzari da sauri ta mike tana fadin"gadanga..Lafiya meya faru..? tafada tana leka dakin nasa karo sukayi dashi ya fito da karamar bindiga Ahannunsa baya goggo taja tana fadin"mun shiga uku gadanga,me zakayi da bindiga kuma.."?
Kallon goggo yayi yana fadin"goggo yau wlh zanyi kisa a anguwan nan,ki matsamin daga hanya don Allah.."Yafada idanunsa sun chanza launi saboda Fitina ga naman jikinsa na cida,gabadaya Fuskar gadanga ta canza baya goggo taja tana kiran Sunan Allah da hanzari ya fice,ai da gudun hanzari goggo ta rufamai baya tana fadin"Kai kai..gadanga don Allah kadawo ka rufamin Asiri don Darajan ma'aiki.."Take fada tana binshi ko hijabi bata dashi taga ya shige gidansu Azeema ai da gudu ta maramai baya Hartana hardewa zata fadi saboda tashin hankali.
Inna Ramatu ta fito daga bayi kenan Aliyu ya fado gidan da bindiga tsirara,yana ganin inna ramatu ya nufeta ya Nunata da bindiga yana fadin"ina Yarki...? yafada cikin Tsawa,sandarewa Inna tayi saboda razana butar dake hannunta ta subuce ta fadi miyan bakinta ya kafe tana kallon Fuskar gadanga ga bindiga tana gani tsirara,wanda bata taba gani ba,sai afina finan indiya,ai batasan sadda fitsarin dabatasan yaushe yazoba, taji yana bin kafafunta kara dakamata tsawa yayi yana fadin"ina Azeeza..Nace ina Azeeza..? da ido Inna Ramatu ta nunamai Azeeza data fito daga daki jin muryan Gadanga cikin Fushi,ai yana ganinta yajuya kanta ya sakamata bindigan bisa goshinta kafin yace"Oy kneel down.."yafada yana zare mata ido,dai dai lokacin da goggo ta shigo ta haki tana fadin"bari gadanga don Allah Allurar taka tayi hakuri tabari in kakoma chan barikin ku sai tatashi kayi duk Abunda zakayi,ammh don Allah ka ijiye bindigarnan.."Take fada tana rokonsa ammh ina ko jinta bayayi itako inna dukewa tayi domin zawo da Fitsari ne suke biyo kafafunta saboda Tsoro Fuskarta kuwa ta jike sharkaf da hawaye saboda tsoron gadanga da Abunda ke hannunsa.
Azeeza dataga bindiga tsirara sai ta tsorata da hanzari tasaka gwiwanta akasa tana raba ido,Kara saitata yayi yana fadin"Duk Abunda na tambayeki juz answer me,and kuma wlh tell me d truth in ba haka i swear sai na hade kwakwalwar kanki da wannan garun..'" yafada yana kallonta baya Azeeza taja bakinta narawa tama kasa mgana,Kallonta yayi kafin yace"Ina Azeema,ina kika kaita,wlh in kika budi baki kikafadamin karya sai naci ubanki kinsan nasan komai ko? da hanzari tadagamai kai alaman hakane,Baya yaja kafin yace!"gayamin ina take,ina kika kaita bayan kun baro office din principle kin bada report kan cewa zata koma gida bata da lafiya,oya tell me daganan ina kika kaita..? Tuni Azeeza ta fashe da kukan tsausayin kanta,bakinta narawa tace"Gi...gi..dan..Ba...ba Ade.."Tace bakinta na karkarwa saboda tsoro sauke bindigar yayi ya maidata aljihu kafin yace"Toh maza ku shirya muje,goggo muje gida,bari na dauko mota muje gidan baba Ade,yau din zamu ji mai wannan yarinyar take nufi damu ne.."yafada kai tsaye yana Ficewa Kada kai goggo tayi kafin tace"Lalle karka raina mutum,Azeeza al"amarinki akwai ban Tsoro aciki,tana gama fadar haka ta fice,suna fita Inna ta rarrafo ta isa ga Azeeza tana fadin"Allah ya isa tsakanina dake,ban miki kashedi kan ki Fita harkan Azeema ba,ai gashinan kin jawoma kanki masifa kuma kin jawo mana.."Take fada tana Share kwallah,Kallonta Azeeza tayi kafin tace"Ni ba hanyar Azeema na Shiga ba inna Abun kaunata da muradina nake kokarin kwatoshi daga hannunta yazama nawa nikadai.."Tafada tana nuna kanta,Cikin mamaki inna Ramatu tace"Abun kaunarki kuma? ke Azeeza ko ganin bindigarnan ne ta saki kikafara zauncewa..? dariyan yake Azeeza tayi ba alamar nadama Aranta tace'Eh da gaske nake inna duk Abunda kika ga inayi,toh ba don kowa nake ba Sai don my Crush YAYA CAPTAIN..ina matukar sonshi Tun ina yar shekara shabiyu aduniya..'"
Baya inna taja tana dafe kirji saboda yadda kalmar ta girgizata bata samu zarafin mgana ba,goggo ta Shigo da hijabinta tace"maza Azeeza taso muje yau karyanki takare insha Allahu,har ita Azeemar zata fahimci ko ke wacece..'ko dar Azeeza batajiba, tashiga daki ta dauko mayafi ta fito tana fadin"muje dama na Shiryama zuwan wannan Ranar da Sirrin boye zai Fito sarari.."Tafada tanayin gaba,goggo ta take mata baya,ai da gudu Inna Ramatu tabisu har waje agaban idonta goggo tatura Azeeza abayan motan gadanga itakuma ta Shiga gaba yaja da gudu suka bar layin zuwa gidan Baba Ade.
_______________
Itako Azeema koda taje gidan Baba Ade banda gaisuwa babu Abunda ya shiga tsakaninsu Baba Ade tayi tambayan Duniyan tayimata banza,tacemata lafiya bataje mkranta ba tazo nan,kuma ta ganta da uniform,goggon nata tasan zata zo nan din? ammh Azeema tayi mata banza daga karshe baba Ade ta zuramata ido,sai taga Rana tayi sanyi ne kana ta farama Azeemar fada kan tatashi tatafi gida kada anemeta ammh Abunda yabata mamaki sai cewar Da Azeema tayi bazata kara komawa gidan goggo ba,ita anan zata zauna,da Baba Ade tanemi jin dalili sai Azeema ta sakamata kuka harda shessheka,saboda mamaki ma takasa mgana,Abun ya dauremata kai ba kadan,Aranta kudiri niyyar tana gama Tuwon dare zata Fice zuwan gidan goggo taji ba"asin Abunda yafaru.
Fitowarta kenan daga madafi taji sallamar goggo tana amsawa bayanta gadanga ne sai Azeeza data biyo baya kamar munafuka baki Baba Ade ta rike tana musu maraba da hanzari ta bude musu tabarman dake nade akofar dakin tana fadin"maraban ku Suwaiba,daman nima yanzu nake Shirin zuwa wajenku,maraban ku,ashe harda megida,ko daman dalilinkane Sakaryachan tayo muku yaji harda kukan bazata koma ba.."Kallonta kawai Aliyu yayi kafin yace"Baba ina Azeemar..? Yafada cikin kakkausan muryan Kallonsa Baba Ade tayi kafin tace"Lafiya kuwa tana ciki,?Azeema.."Tashiga kwalamata kira.
Itako Azeema Tun Shigowarsu taji tuni gabanta yaketa Faduwa bata kara tsorata ba,sai da taji Mganar yaya captain cikin Fushi,bayan kofa ta makale tanaji baba Ade na kiranta tayi mata banza takawa yayi zuwa kofar dakin yana fadin"Barta Baba bazata Fito ba,kila sai na Shiga na Fito da ita..'Ai Azeema najin haka tayi Wuf ta fito tana raba ido,ganin goggo yasa jikinta yayi sanyi,bata kara tsorata ba,sai dataga Azeeza agefe idanunta sunyi jawur alamun tasha kuka,gefe kuma ga yaya captain sai wani banzan kallo yake jefamata baya taja tana Shirin komawa daki,taku daya yayi zuwa biyu ya cafkota kai tsaye gaban goggo ya durkusheta yana fadin"Tambayeta goggo meyasa ta aikata Abunda ta aikata,don ni in kuka barni da ita wlh zan iya Sumar da ita da duka saboda yadda takebani haushi.."Yafada yana jaddada Abunda yafada din.
Baba Ade ta dunkuremata kai tana fadin"ai yanzu kya bude baki kiyi mgana tunda ni kin rainani kin ki fadamin me akayi miki.."kuka Azeema ta fashe dashi tadago tana kallon Azeeza wacce ta kauda kai tanawani hura hanci Hannunta goggo takama tana fadin"Azeema wai meyafaru ne,tunda lokacin tashinki mkranta yayi mukaga baki dawo ba,wlh ni da gadanga bamu Huta ba,meya faru in zaki zo nan ,ai sai ki fada mu san kina nan,kada hankalinmu yatashi.."Tafada idonta ya ciko da kwallah,kallonta Azeema take kafin ta kama hannunta tajuya tana kallon Azeeza tsawa Aliyu ya dakamata yana fadin"Kimana bayanin duk Abunda yafaru,domin itadin tace yau bata ganki ba kwata kwata amkranta,alhalin kuma Areport din mkrantan yanuna tare da ita kukeje Shigar da report din zaki koma gida bakijin dadi,ko ba haka ba..?"Yafada yana kallon Azeeza sadda kai tayi batayi mgana,ba mamaki yakama Azeema bakinta na Rawa tace,"A...Zeeza....,Haka mukayi dake..? Baba Ade da tashiga Rudani takara dungurema Azeema kai tana fadin"Toh mu fadamana yakukayi da ita don mai garinku.."Kai Azeema ta sadda kasa ta kwashe duk Abunda Azeeza ta fadamata tafada takara da cewa"Ita tace nazo nan,kuma ko Baba Ade tatambayeni karnacemata komai,kawai in ta matsa na Tubure nace bazan koma gidan goggo ba,bayan an kwana biyu kuma sai nadata balli,nace...Nace..."Kice me...!"? Baba Ade ta katseta cike da takaichi Hawaye suna zubomata tace"Nace ya sakeni.."
"La'ila ha"illallahu..."Inji Baba Ade "Muhammadan Rasulillahi.."Goggo ta karishe sunayi suna kama baki lokaci daya Suna kallon Azeeza suna mamakin yadda yarinyar kamar Azeeza ta iya hada wannan makirci ko wata uwar matan albarka,Shiko Aliyu ba Azeeza ce tabashi mamaki ba Azeema ce,ashe haka take da wauta saboda haushi baisan sadda ya matso kusa ba,ba tsammani kawai Sukaji ya wanke Azeema da maruka biyu,saboda azaba da zafin marin sai da ta kife bisa cinyar goggo,Dafe kuncinta Azeema tayi da duka hannunta biyu,domin tadainaji na tsawon wasu mintina,Baki ta bare zata fashe da kuka yayi saurin dakamata tsawa yana fadin"U stupit shout up ur Mouth,wlh kikamana kuka anan wajen yadda nakejin haushinki zan tattakakine anan wajan babu Ruwana,Tunda ke kwakwalwar Tumakai kikedashi koma na beraye ne bansani ba.
Baba ade tace"na ma Tamtabaru ne inaga,ai daka karama sakara mara wayau,ace ki zauna yarinya karama tana waasa da hankalinki Azeema,sai kace wata saunah,shekara biyar fa kikaba Azeeza,aiko yaci ace duk wasu dubarun Duniya da wani tuggu kingama sani.."Rumgumeta goggo tayi tana fadin!"Ya isa Baba,ai gashi gaskiya tayi halinta yanzu sai tafadamana meye dalilinta nayin hakan..? tafada tana kallon Azeza wacce idonta ke tsakar ka ba alamun nadama ko kadan atare da ita.
Kusa da ita Aliyu ya matso yana fadin"good girl,gaskiya kin burge gaki da kananan Shekaru,ammh Tunaninki ya girmi wayonki,oya tell us mekike nema awajenmu,shin bayan Azeema kikeson gani kokuwa bayana..Ehen fadi munajinki,in ba sokike na tilastaki fadi ba.."Dan mirmishi Azeeza tayi kafin tace"Hmm,ai ko baka tambayeni ba yazama dole kowa yasan wannan gaskiya,Tafada tana haki kan taciga da cewa"Azeema ba itace tadace data mallake ba,nine nan..."Tafada tana nuna kanta,da mamaki goggo da baba Ade ke kallonta balle Azeema data bar jin zafin mari saboda kalaman Azeeza.,shiko Aliyu ko ajiknsa don dama Tuni hasashensa yabashi hakan
Cigaba tayi da Fadin",Ni nafara Sonshi Tun bansan me ake kira da wata aba soyayyah ba,nasoshi Tun in yarinyata,da sonshi na tashi dakuma shi na girma ya gini ajikina,duk duniya babu wanda nakeso da kishin irin yaya captain Aduniya na tsani in ga wata mace na rabanshi koda mahafiyarshi ce,na tsaneki Adda Azeema wlh banta miki kallon yar!uwata ba sai makiyiyata,Ko shiga jikinki danayi duk don nacimma burina ne,na mallakan muradin Raina ne,ammh kash Duk wani gadan zare dana kullamiki sai ki tsallake,ta hanya yaya captain,wannan karon na dauka bazaki sha ba,sboda sanin yadda kwakwalrki take kamar dussa saboda Rashin lissafi,ammh sai gashi komai ya kwabe,ammh duk da hakan ban sare ba,don hankalina bazai taba kwanciya ba matukar igiyar ukun Aurenku da yaya captainn na Reto Akanki saboda haka kisani nan Duniya kece babban makiyiyata kuma ba wacce na tsani gani kamar ki..."Tafada tana Fashewa da kuka.
Daskarewa Goggo da Baba Ade sukayi itako Azeema tayimata zura kamar wacce aka sassaka,shiko Aliyu mirmishi yake saki kafin yataka zuwa gabanta ya tsugunnah yana fadin"Ban wani ji mugun mamaki ba,mamaki na daya na yadda duk kudin da baba da goggo suka kashe akanki asara kadai sukayi daga bokon har islamiyyah baki gane komai,in banda tsabar jahilci kina tsammanin zan saki Azeema ne,ke sa ma na saketa kina nufin zan Aureki ne,gaskiya ta wannan fannin kina da tunanin kifaye walh toh ai koda Azeema mutuwa tayi kuma matan Duniya kaf sun kare,wlh sai dai ki mutu na mutu ba aure bazan taba Aurenki ba,Domin nafi tsanarki Fiye da yadda na tsani mutuwata......!!!!!!"yafada cikin Tsawa da amo mai sauti kafin lokaci daya ya mike yana saka kafa ya sharbo kafafunta ta zube kasa yace!Kin san Allah kinci daraja daya,ke diyar mallam lawal ne mahaifi ga Azeema,da ba don haka ba,uhmm da yau kin gwammace kila da karatu,ammmh wannan yazama na karshe da zanyi miki kashedi kan Azeema,kifita daga hanyarta in kika kara shigowata gonata har na kamaki toh ki Rubuta sunanki Matatta,oya get out shegiya Tanayi da Fuska kamar mutuniyar arziki.."
Mikewa Tayi tana dariya lokaci daya hawaye suna zubomata tace"Ki Rubuta ki ijeye zan dawo gareki,ko ba yanzu ba.."Tana gama fadar haka ta fice da gudu goggo ta bita da fadin"Aniyar tabiki mai bakin halin insha Allahu sai sharrinki yakoma kanki.."Itako Baba Ade gabadaya lamarin ya tsorata tama kasa mgana,Azeema kuwa kuka takeyi sosai kamar wacce ta zauce,Yau ita yar"uwanta ke neman ganin bayanta,Tunda suka taso batataba jin zuciyarta tabata wani mugun nufi akan Azeeza,kullum tana kallonta amtsayin kanwarta mafi soyuwa gareta,ammh ashe ashe ita babu hakan Aranta,wani Abun takaichin ma wai mijinta take so oh duniya ina zaki damu ne,haka Baba Ade keta maimatawa kafin tace"Toh Sakarya ko nace Sauna kindaiji da kunnin ke ko? toh sai ki zama mutum kinaji kinagani itace makiyarki mai son ganin bayanki,in zaki mike ga kanki ki zama mai wayau da lura da abubuwa toh,in kuma zaki cigaba da sakarcin ne,Allah yabaki sa"a Kice