kada ka sake gujemin wlh bazan iya Rayuwa baka ba,nasha wahala kafin na sameka...",Tafada tana kara kamkameshi,tanasakin wani marayan kuka.
Bambareta yayi daga jikinsa ya isa da ita kan daya daga cikin kujerun Falon ya zaunar da ita,Kichen Ya nufa yaje ya daukomata Ruwa da wani karaminn kofi ya Tsiyayamata mikamata yayi yana kallon kwanyan Idonta,Amsa tayi kafin ta sanya hannu ta share hawayenta,dan kurba tayi kadan kafin ta mikamai,kan Center table din dake Falon ya ijiye kofin kafin ya koma kujeran dake kallon nata ya zauna bayan Ya Dora kafa daya kan Daya yana Fuskarta dago da kanta tayi Tana kallonsa Shiko Remot ya dauka yana sarrafa talabijin din dake Falon.
"Soja...Nah...."Tafada cikin Rawan murya Dagowa yayi zata kara mgana yayi Saurin dagamata hannu yana fadin",Kinga nifa bani zakizo kina ma kuka ba,babanki zaki tasa kikatayima Kuka domin shi yasaka alkamashi ya datse halakan dake tsakani na dake..."Ya fada idonsa akanta Raurau tayi da ido kafin tace", i know buh..."Dagamata hannu yayi kafin ya mike yana fadin",Ki Adana kalamanki Ni"ima domin basu da muhalli awajena,Ba shakka ada na soki,na kuma so muyi,zama na har abada dake,sai dai kash Tun Ranar da mahaifinki ya watsamin kasa a ido naji kin Fita Raina,ko koda ace banyi Aure ba bazan Taba iya Aurenki ba,..."Yafada kai tsaye
Azabure ta mike hannunta dafe bisa kirji tace",Kana nufin kayi Aure ne my Captain..? Takowa yayi zuwa gabanta kafin ya sanya duka hanuwansa cikin aljihun wandonsa yana fadin"Kwarai ma kuwa ai wajen da mahaifinki yace bazai bani Aurenki ba saboda Bani da uba awajen wani Uban ya wanke yarsa ya bani,kinga ko iya karamci da hallacin yayimin,kuma koda ma ba"ayi haka ba,ni Aliyu bani da burin zama da mace Fiye da daya..So Abunda nakeson fadamiki gwara Tun Wuri kiyi Facing Realiaty Ki cireni Aranki don bazaki taba samuna ba,shawara ta karshe don Allah kada ki kara zuwa gida,ina da mutumci a idon jama"a bana Fatan ki Fusatani har na zubda wannan mutumci...',Daga haka ya juya zai Shige bedroom dinsa har ya kusa shiga ya waigo yana fadin"Armmm..In kin Fita plz close d door...",Yana fadin haka ya Shige bedroom ya banko kofa Ransa bace,kawai daurewa yake shiyasa bai Mazgeta ba,ammh azahirin gaskiya haushinta yake daga ita har Dan sandan Ubanta.
Ni"ima ko Durkushewa tayi ta fashe da kuka,kamar zata Shide,Rike kanta tayi tana girgizawa tadade tana durkushe kafin tatashi ta fice daga gidan,Direba ya kawota Jabir na gaban gidansa yana jugging ya hangi Fitowar Ni",ima Tana kuka Dan mirmshi yayi kafin yace"i know haka zai Faru dama gaskiyan nake so ki sani asauka lafiya..,"Yafada yana dan Dariya,mota ta Shige ta Umarci Direba ya taka mota suje don yadda take jin zuciyarta kamar zata Fashe saboda kunci.
_________________
_Gombe_
Yau kimanin Sati daya kenan da komawar Azeema gidan goggo,Duk wani jin dadi da Kulawa goggo na bata,domin koda ta daukota daga gidansu Kai tsaye shashen Aliyu ta budemata tace mata nan ne dakinki Azeema,ki zauna kijira mijinki har ya dawo..Toh ya Azeema zatayi bata da yadda zatayi sai bin Umarni,Goggo da kanta ta zage suka gyara shashen suka tsabtaceshi,Washegari kuwa Goggo da kanta tadauki Azeema sukaitai kasuwa tayimata siyayyah kaya da Atamfofi da Dogayen Riguna harda masu sikat,sai kayan kwalliya da takamla duk wani Abun gayu dai na mata ta siyamata domin goggo kudi har bata sanin ina zata kaisu,in kawu yazo ya bata,hakama Aliyu,kullum Tarasu take saboda babu Abunda take siya komai na more Rayuwa sun siyamata shi ta mallakeshi,harta ta wajen gyaran kai Sai da goggo takai Azeema aka gyaramata kai aka wankeshi sosai,Ita kanta Azeema tayi Farinciki da Shigarta sabuwar rayuwa,haka Baba Ade tazo tayitama Goggo godiya harda kwallah saboda murnan chanjin Rayuwa da Azeema ta samu kamar yadda Mallam lawal Shima dauke Azeema daga gidan Yafi komai yimai Dadi.
Goggo batai kasa agwiwa ba,harta girki tazage tana koyama Azeema dawasu kissa,da dubarun yadda zaka jawo hankalin Namiji gareta,kullum bata lbrai take,tare da kawomata kissa kala kala na yadda kishi mai tsafta ya gudana agidan Annabin Rahama Muhammed Sallallahu alaihi wasallam,Tare da kissosin matan sahabbai,ba shakka Azeema na dauka shawarwarin goggo sosai don tana jin dadin xama da ita,Cikin Sati daya Azeema ta chanza kamar ba ita ba, Tuni wa"innan kuraje suka kama kansu dama wahalace ta kawosu,Tayi dan yi kiba taciko uwa uba ga chanjin abinci dana Sutura,Kullum a Sashen gadanga take kwana,ammh adayan bedroom din dake kusa danashi,wanda yake akulle Tana Tunanin makullin dakin yana hannun mai Shi ne,Watarana adakin zasu wuni da goggo watarana kuma A shashen goggo,Tunda Abun ya faru Azeema bata taka gidansu ba,kai ko Fita in ba kasuwar da sukaje da goggo ba,bata taka ko"ina ba,Babanta Kadai suke haduwa dashi in ya fito da safe zai Tafi kasuwa don yanzu yakoma cikin kasuwa da sana"arsa Ssnadin gadanga don shi ya siyamai shago ya koma chan,yanzu hankali mallam lawal akwance yake,Domin Ramatu dai bata da wanda zatayi Fitina dashi Azeema ce kuma ta barmata gidan,daga ita sai yarta suci wainarsu babu babbaka.
Azeeza kuwa Duk iya tsawon kwanakin bata taba Sarara ma kanta da Tunanin mafita ba,tabuga ta buga ammh tagagara samun wata hanyar da zata cima nasara Adaren lahadi zuciyarta tagama yanke shawaran data ke ganin tabbas ita tafi dacewa kafin tafara zartar da komai,so take ta Fara lalata Auren Azeema Tukunnah ta yadda babu wanda zai zargeta da aikata hakan.
*Monday*
Monday Tushen Aiki ko bature na tsoron zuwanki,Yau Su goggo su dan makara tashi,kuma yau din ne Azeema zata koma mkranta,koda ta Shirya har 7:30am ta wuce Shiyasa kawai ta dauki jakarta tana cema goggo ta wuce,fada goggo tafara yi tana fadin ya zata tafi bata karya ba,maza ta tsaya ko Ruwan Shayi ta sha,Tura baki Azeema keyi tana fadin"Allah goggo na makara.."Fifitamata shayin goggo keyi Tanafadin"To sai me,yanzu zaki isa ni zan Rakaki har mkrantan in Tsoron duka kikeyi bamai tabaki kina matar soja..'Yar dariya Azeema tayi kafin tayi mgana Sukaji sallama suka karba atare,Daga labulen dakin akayi Azeeza ta bayyana itama jikinta sanye da kayan mkranta ga jakarta ahannu,daga Azeema har goggo da kallon mamaki suka bita,itako sunkuyar dakai tayi kafin tasaka gwiwowinta akasa Tana fadin"Don Allah Adda Azeema kiyi hakuri ki yafemin Duk Abunda nayi miki,wlh Sharrin shedan ne,Ke yar"uwatace danafi so fiye da komai Arayuwata duk inna ce,take zugani ina miki Rashin kunya,ammh bada son Raina bane,ammh yanzu na Tuba,wlh bazan kara jin zugan inna ba,don Allah kiyafemin...",Tafada tana fashewa da kuka,Kallon Goggo Azeema tayi itakuma ta gyada mata kai,da hanzari ta isa ga Azeeza ta dagota ta Rumgumeta tana fadin"Shiiii..Kidaina kuka Azeeza na yafemiki dama bantaba rikeki Araina ba,Na yadda shedan ne yakeso ya raba tsakaninmu..Bakomai Allah yayafemana gabadaya.."Lamo Azeeza tayi tana wani dan mirmishi kafin ta dago tana fadin"Duk inna..."Shiiii...Kiyu Shuru hakanan ma,karki manta inna fa mahaifiyarkice fata kawai zakimata Allah yasa ta gane itama.."
Azeeza wajen Goggo Ta nufa itama ta duka tana rokonta dagota goggo tayi tana fadin"Dukkanku ya"yana ne,babu wanda na ware acikinku,Allah ya hada kanku.."Suka amsa da Amin nan fa su Azeeza aka share kafa akayi kari mai lafiya kafin goggo ta rakasu zuwa bakin Titi su hau Daidaita Dari biyar Goggo taba Azeema tace suyi kudin Abun haawa zuwa da dawowa sauran kuma suyi kudin Tara dashi,murna sosai sukayi suna ta mata godiya har suka kulema ganinta tana Faman daga musu hannu,acikin keken napep din ma sai Hira Azeeza kema Azeema itako dayake bata da yawan mgana mirmishi kawai take mata sai ko eh ko A"a..Azeeza bata damu ba,dama komai sai Abun Ahankali juyawa tayi tana kallon gefen Hanya kafin tayi wani bazawarin mirmishi tace" Dis is juz d begining..Yanzu wasan ya fara Adda Azeema kinyi kuskure babba wajen yarda dani ganinan zuwa cikin Rayuwarki domin na wargazata...",Tafada tana cije baki har saida Taji zafi alebenta.
*Comment,share,and vote...*
*Janafty...,*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*I dash d whole page for u my Rival..👭...HUWAILATU😂😜popular Name MISS ZERK..ga page dinki nan,karki wani damu Ana tare,dama aie Abun Uwargida na Amarsu ne.....*😂😂
*Chapter 13*
---------------------Rayuwa Tana ta gudu kamar yadda muke cinye Lokaciinmu da kwanakinmu Aduniya,suke gangara suna Neman karewa,masu imani ne da masu tunawa da zasu mutu kadai suke Shiga Tashin hankali in suka Tuna hakan,ammh akasin haka ko ajikinsu To hakan ce Tafaru da Azeeza Domin koda da wayewar gari, bata taba Nadamar ko jin Abunda take Shirin Aikatawa baida kyau ba,ko taji zuciyarta ba dadi in Tayi Tuni da Cewa Azeema yar"uwanta ce.
Duk wata hanya da Azeeza zatabi ta Shigema Azeema da goggo tayi,yanzu sun bata dukkan Amanna,gidan take Wuni,sai dare take komawa gida,tare suke komai da Azeema kamar wasu yan biyu,inna Ramatu kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu,Saboda sabbin halin Azeeza tafito dashi shiko Mallam lawal Abun yayi Mai dadi don Azeeza tazo ta rokeshi gafara kuma ya yafemata Yana ta sakamata albarka,Inna Ramatu Abun ya Daure mata kai sosai kuma tayi tambayan Duniyan nan Azeeza tayi mata banza bata mata wani bayani ba,kuma bata yarda ta fadamata Abun da ke Ranta ba ko alama daga ita sai Allah kadai suka san Abunda ta binne Aranta.
Duk Zuwan da Azeeza take gidan goggo bata taba katarin,ganin Azeema Shashen na yaya captain ba,wanda Abunda take ta jira kenan,kullum sai dai su Tare dakin goggo susha hiransu,yau dai kam Tayi sa"a domin tana Rafka sallama atsakar gidan Azeema ta daga labulen Shashen gadanga tana fadin"Azeeza Shigo nan.."Tafada kai tsaye tana mata mirmishi Ran Azeeza yayi sanyi jikinta na Rawa ta nufi Dakin Tana washe baki,bude mata kofar Azeema tayi tana fadin"Yau goggo barci ke cinta,Har na dawo,bata sani ba shiyasa na Shigo nan don kar na dameta.."Dariyan yake Azeeza tayi tana fadin,"eh gaskiya ne..."Tafada tana bin makeken falon da kallo,wanda yaji lafiyayyun Royal chair,idonta wurgawa kawai yake tana karema Falon kallo,Azeema ce ta Kalleta tace"Zauna Azeeza bari na kawo miki Ruwa kinci Abinci? tatambayeta girgizamata kai Azeeza tayi ta kasa mgana saboda wani hoton gadanga data gani bisa wani tebur din glass,dake chan jikin bango,kyam tayi ma hoton tana kallo,itako Azeema bata lura ba kichen Ta nufa tana Fadin"Bari na dafa miki indomie..Nima ita nagama ci yanzu.."ko jinta Azeeza batayi ba hankalinta yatafi ga hoton Yaya captain,A hoton yana sanye da wasu fararen kayan hatta cambos dinsa fari ne, safa ma haka,acikin wani fili ne akayi hoton kamar dai asansanin horarwa ce,yayi tsalle yana dariya aka dauki hoton,Azeeza saboda shauki batasan sadda ta karisa kusa da hoton ba ta saka hannu ta dauki Frem din tana kallo,hannunta ta sanya tana shafa hoton sai ga Azeema ta fito tana fadin"Yanzu zata nuna na zuba miki,yunwa ba dadi..'Tafada tana karisawa kusa da ita.
Saurin waskewa Azeeza tayi tana fadin"kinga hoton danazo kallo Adda Azeema Allah yaya captain yayi kyau sosai ahoton nan.."Mirmishi Azeema tayi kafin ta amshi hoton tana fadin"Gaskiya yayi kyau kam.."Tafada itama tana kallon hoton kafin ta ijiyeshi inda yake,Talabijin din dake dakin ta kunna tana fadin"Muyi kallo Azeeza mu rage zaman Shuru.."Yake Azeeza tayi kafin tataho ta zauna tana satar kallon bedrooms din dake jere Shuru ya biyo baya Azeema ita hankalinta na wajen kallo yayinda Azeeza ke saka yadda zata fara dakan Ruwan Cikin Azeemar batare data sani ba.
Zuwa chan wata dabara ya taso mata sai tayi Farat tace"Adda Azeema nace ba..",Dagowa Azeema tayi kafin tace"mekike son Fadane Azeeza..? Yar dariya Azeeza tayi kafin tace"Wai nace yaushe yaya captain zai dawo ne..? Kai tsaye Azeema tace"Wlh bansani ba Azeeza..",Wani sanyi ya Shiga zuciyar Azeeza murna ya cikata sai ta barsa,lokaci daya ta bata rai Tana fadin"Toh meyasa Adda? bakwa waya ne.."?Jin Abunda Azeeza tacene ya sata Dagota kanta tama Azeeza kuri da ido,sai taji kunyan cewa basa waya..Cikin in ina tace"Eh..Armm..Munayi mana..'Tafada kafin tayi zaraf ta mike tana fadin"Bari na dubo miki,kila yanzu Ta isa yi.."Tafada kafin ta fada kichen,Tana Shiga Azeeza ta buga kafa tana fadin"yes...Komai na tafiya kan Tsari.."Take fada tana dariya Sai ga Azeema ta fito dauke da filet wanda ta zubo indomie aciki sai Lemon cway data daukomata ta kawomata nan Azeeza Ta share kafa ta warba tana ma Azeema hira wanda Rabin hira duk na dakan Ruwan cikinta ne,itako Azeema bata ma iya maida mata amsa sai dai tayi mirmishi ko ta gyada kai,wai Azeeza harda tambayanta ya lbrin Ni"ima Saboda mamaki sai da Ta bude baki tana kallonta,harda cemata wai ta mike tsaye don tagane yaya captain haryanzu yana Son Ni"imar,Rike baki Azeema tayi tana auna kankantar shekarun Azeeza ammh tana mganar manya,sai kuma mganar data Fada ta tsaya mata arai...Sam bataji dadin Jin Abunda Azeezar ta fada akan Yaya captain yana Son Ni"ima haryanzu ba, Batasan dalili ba,sai taji duk zuciyarta babu dadi..Lura da haka da Azeeza tayi sai tayimata sallama takoma gida ammh Ranta Fes Domin tayi hakane ta tusama Azeema tsanar yaya captain koma tana Sonshi ta cire Tunda zuciyarsa na ga wata..Kuma taga alamun Nasara kodaga yadda Azeema tachanza Tun lokacin dataji mganar...
________________
Ta Sauka daga keken napep kenan Tabashi kudinshi Ta nufo kofar gidan Kamar a Mafarki taga wani kamar gadanga zaune bisa bayan motarshi Jabir na tsaye agefe,dukkansu suna sanye da Riga da wando,wandon blue ne sai Rigar Farace kafafunsu sanye cikin booth,Kowannensu hannushi dauke da wani ubansu agogon Fata na kamfanin Rado,Fuskarsu cike da Annuri,Hannayensu dauke da gorunan Ruwa suna kurba,Da hanzari Goggo ta karisa Gadanga ne ya fara hangota da hanzari ya diro daga motar yana cema Jabir"Ga goggo chan ta dawo.."Yafada yana karisawa gareta,Maida kallonsa Jabir yayi inda goggo ke tahowa tana ta washe baki,dariya yayi yabi bayan Gadanga..
Suna karisowa goggo Ta Rumgume gadanga tana fadin"Oyoyo gadanga..Kai ammh kai ja"irin yaro ne ka iya zuwan da Annabi ya hana..Au tare ma kuke da jabiru kai marabanku da bakin sassafe.."Ta fada tana Sakin Gadanga takamo hannu jabir wanda ya duka yana gaisheta Fuskarsa Gadanga ba walwala yace"Wai goggo daga ina kikene da wannan Farar safiyan..",? Bata Fuska tayi kafin tace"ya'yana na Raka mkranta sun makara suna Tsoron duka,shine naje mkranta na fadamusu basu da hankali ne,matar auren zasu daka,kuma ma matar Auren matar soja,Aliyu gadanga.."Tafada kai tsaye ko ajikinta galala Gadanga yake kallonta kafin yace"Wasu ya"yan naki..? asakarce goggo ta kalleshi don ta gane tambayan Rainin wayau yayi mata,kauda kai tayi kafin tace"Matarka Azeema da kanwarta Azeeza ko ba ya"yana bane..? tafada tana zubamai ido,Bata Fuska gadanga yayi kamar zaiyi kuka,Tsaki goggo taja kafin tace"Ohon maka kabar wani tabe Fuska kamar kaga kashi,ni wlh al"amarinka wani lokaci na ban mamaki,bansan wakake tabema Fuska ba,mganata ko ni din kaina..? dariya ta kwacema Jabir yace"kai goggo ya"za'ayi ya tabe miki Fuska,kila mganar ne bataimai dadi ba..'Yafada yana kallon gadanga Ta wutsiyar ido wanda yayi gaba yana fadin",Don Allah goggo kibar wannan mganar juz open d door.."Harara Ta zabgamai kafin tace"Alqur"an Sai ka fasasara mai kace daga karshe,kasan dai na hanaka juyamin yare ko"Ta fada a fusace,dariya ta kullema Jabir ciki yace"Goggo cewa fa yayi ki bude kofar.."Dariya goggo tayi kafin tace"oh yanzu nagane,nima fa da inajin Turancin nan miyar kuka ne suka danneshi wlh,ammh da in na Fara Turanceku harshi gadanga sai na kureshi.."Ta fada tana bude kofar gidan wanda ta samai kwado sanda zata Fita,Dariya takama Aliyu,sai dai ya share Shiko Jabir harda kaiwa kaasa saboda dariya,Aliyu ne ma ya kwashi jakukkunansu ya Shiga dasu Kafin yakoma ya Shigar da mota gareji,Shiko Jabir yana chan wajen goggo yana janta da hira suna dariya datace zata dora musu girki cewa sukayi akoshe suke..Komawa goggo tayi ta zauna Aranta tana fadin"Dama banyi niyyah ba,kwaci kaniyarku don Ni ina da Sauran dan wake na najiya wanda Azeema tayimana.."tafada Aranta tana mirmishin mugunta,tunda ta lura daga gadanga har abokin nasa yan Air ne,komai sai sun Tsara suke aiwatarwa.
Shiko Aliyu yana Shiga Sashensa Abunda ya bashi mamaki abude ya gani bai kawo komai Aransa ba,sai ya ce kila goggoce ta bude don tagyaramai ammh sai mai ko"ina tas sai tashin kamshi,ga remot kan kujera ga Talabijin akunne,bai gama mamaki ba sai da ya leka kichen yaga komai net..Ga kuloli nan da alamu ba"a dade da wankesu ba,baki ya rike yana Tunani ko goggo ta dawo shashenshi da kwana ne,don ya san zata aika,Da hanzari ya fice zuwa dakin goggo suna tsaka da hira da jabir ya Fado yana Fadin"goggo chan Shashen kika koma da zama kuma? akarkace goggo ta kalleshi kafin tace"me..?meka gani hala.."yace"alamun mutum na Rayuwa awajen..'tsaki goggo taja kan tace"ji wata tambayar banza,dama da mutum mana,ka manta ka ijiye mata...Toh Azeema ce ke zaune aciki..'Tafada kai tsaye tana Hararanaa,Tsaye yayi yana zare ido,don shifa ya manta da wata Azeema balle har ya Tuna da Abunda ya faru dafe kai yayi kafin yace"Toh goggo miye laifin barayinki,naga dai kema kina da dakuna.."goggo tace"Eh na saukan baki ba,ammh ba wajen ijiye matar gadanga ba,.."Tafada tana kallonsa,yanajin Abunda goggo tace yafice saboda yasan halin goggo ta kan wannan mganar sai ta maida Abun ya zama babba,yana Fita jabir ke tambayan goggo dama Azeema tatarene,nan fa goggo ta gyara zama ta kwashe From A to z bata rage komai ba.mamaki yakama jabir don ko kadan Aliyu bai Fadamai ba Fatan Alheri yayi musu da Fatan zama lafiya.
Shiko Aliyu saboda bacin Rai waje yakoma ya zauna akofar gida yana latsa latsen waya saboda Haushi,yasan Halin goggo tsaf zatamai tas agaban Jabir shikuma ya samu Abun Tsokanarshi,shiyasa ya fice daga gidan ko Ransa zaiyi sanyi,yafi awa biyu har aka kira sallar azahar yatafi massllaci yayi achan suka hadu da jabir suka dawo Tare nan kofar gidan sukaci burki Aliyu Daure Fuska yayi saboda ya riga yaasan Goggo ta fadamai komai Saboda bakin goggo fa Sikat ne yariga ya santa Sarai Shiyaasa yasha kunu kallonsa jabir yayi kafin yace"Kai Dude ashe Azeema tatare,Toh yanzu ina zan Dinga sauka Tunda yanzu kayi iyali.."Kai Tsaye Aliyu yacemai"Nima Tunanin danakeyi kenan,gwara na saman maka wani waje don bazan iya hadaka shashe daya da iyalaina ba.."kallonsa Jabir yayi kafin yace"Kan ubanchan,yo meye Nufinka bunsuru