ka maidani..Toh kona ina akuyanci bazan bi iyalinka ba.."Ko kallonsa Aliyu bai yi ba yace"Kaji dashi dai."Jabir yace"Muji dashi dai,Wai Dude ya mganar zuwa wajen yarinyar nan kafa san don ita nazo garin nan.."wani kallo Aliyu ya watsamai kafin yace"Dama ni kake jira na rakaka..? gyada mai kai yayi dan mirmishi Aliyu yayi kafin yace"U are not Serious,Tunkan dare yayi maka mallam kanemi mai rakaka,Ban da kana ajawo gaja harwata budurwace zaku hadu awaya kafara Dating dinta kuma wai harda zuwa zaka wajenta,toh bada niba Allah kiyaye hanya.."Yafada yana buga kafadanshi.
hararansa Jabir yayi kafin yace"Toh ina Ruwan mutum..Karkaje kar Allah yasa ka rakani nima ba bako bane a gombe,mganar budurwata kuma ka iya bakinka don daga yanayin muryata nagane cewa babbyn Ta hadu wLh.."Dariya Aliyu ya fashe dashi kafin yace"Allah mazaje.Toh anjuma ka Shirya muje sai na ganta."Riko kafadansa yayi kafin yace"Da gaske Dude.."gyadamai kai yayi Alamar da gaske ne,Hannu jabir ya bashi suka kashe kafin yace"Tanque Dude...,"Bakomai yima kaine ai.."gadanga yafada Saurin mikewa Jabir yayi yana Fadin"bari na kirata nabata Suprise kasan bata san na Shigo gombe Ba.."Kallonsa kawai Aliyu yayi kafin yace"yakamata mr love.."ya fada yana bin Jabir din da kallo yadda ya wani rabe gefe yana rage murya girgiza kai kawai Aliyu yayi yana tsausayawama Jabir don ya shiga tsaka mai wuya kafara soyayyah da wacce baka taba gani ba.
Yana nan zaune yana latsa wayarsa yaji karan mashin agabansa,kamar zai Share sai kuma yaji ya kasa yana dagowa yayi mugun gani Azeema ce da Azeeza sukayi 2parking kuma Azeema ce a tsakiya ga Azeeza nada jiki duk ta cinye wajen Shiyasa aka matse Azeema ajikin mai mashin,kutumar ubanchan Galala Aliyu yayi yana kallon yadda kirjin Azeema ya manne da bayan mai mashin,Azeeza data Fara sauka ta gefen ido ta kallon Aliyu tana ganin yadda kacokan hankalinsa yana ga bin Azeema da wani kallo,Addu"a take aranta Allah yasa yazo ya mareta,domin Tun asaman layi Azeema taso su sauka Azeeza ta hana kamar ta sani suna shaho kwanar layin tahangi jabir,kafin ta hangi yaya captain da gayyah takara matse Azeema ta kara hadewa damai mashin kuma taki yarda asaukesu ko"ina sai kofar gidan goggo,itako Azeema bata lura da Abunda ke Faruwa ba ta dirko daga kan mashin tana laluban jakarta zata dauko kudi,daga bayanta taji ance"kai..."gabadayansu suka waiga har mai mashin din,yana tsaye ya harde hannuwansa bisa kirji da hannu ya nuna mai mashin din kafin yace"kai..Come here,karka bari nazo domin Abun bazai yi kyau ba.."
galala mai mashin din ke kallon Aliyu kafn yace",Kai mallam dawo Natsuwarka domin ni bakaga nayi kama da lusarin Namiji ba,anki azo din zokayi Abunda zakayi don uwarka..."Jin Abunda yacene ya kusa saka Azeema Fitsari awando,saboda tsoro baya taja kafin tace"Armmm...Yayan mune fa mallam..,"Tafada bakinta na Rawa shiko Aliyu mamaki ya daskaran dashi,saboda jin kai tsaye wani banza ya zaganmai uwa Takowa ya farayi yana kallon mai mashin din yana wani cije baki,ganin haka yasa Azeeza Saurin Rumgume Azeema tana fadin"wayyo Adda Azeema kibama yaya captain hakuri,sai da nace mudaina hawa mashin ammh kullum sai kice sa mun hau ai ga irinta nan.."Wani banzan kallo Aliyu yabi Azeema dashi ashe bata da hankali bai sani ba,duk duniya babu Abunda ya tsana irin yaga mace ta hau mashin koda ita kadai,wato ita saboda taceewa su biyu suke hawa saboda wulakanci ko,yau zai koyamata hankali,shikuma mai mashin din daga yau bazai kara Dauka wata mace ba sai dai ko in matarshi ce.
Itako Azeema mamakin Azeeza ne ya cikata,ita yaushe take cewa su hau mashin sau biyu fa suka taba hawa,yau din ma babu abun hawa ne,wannan din ma dakyar suka samu Shiyasa suka hau su biyu,ammh ji Abunda take fada,bata samu zarafin mgana saboda yadda gadanga ke hararanta yana jifanta wani dirty look,itako Azeeza bayan Azeema takoma tana leke Farinciki Duk ya cikata burinta daya yanzu Shine Ya kifkifama Azeemar mari.
*Comment share,vote...*
*Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*I Dedicated dis page to u guyzs KHADIJA CANDY NOVELS..(mama)❤,BENEFICIAL WRITERS💕,JANAF NOVELLA 💖1and2,ALIYU GADANGA FANS 1,2,3 and REAL LADINGO FANS😘 Tanque all For u Hot comments Sakallahu Filjannah HABIBATIES*😍
*Chapter 14*
Yana karisawa kusa da mai mashin din ya dunkule hannu ya tokare mai hanci da baki lokaci daya yasaka hannu ya matsemai baki,jinin daya Fito daga bakinsa da hancinsa sai da ya sashi ya hadiye kafin ya sakeshi,baya yayi kamar zai Fadi saboda yadda yaji kansa yayi Aliyu yasaka hannu ya taroshi yana fadin"mekace ne dazu? dan maimaitamin banji dakyau ba..."Yafada yana kallonsa,mai mashin daya sha wuya yakalli Fuskar gadanga zuwa hannunsa yaga yadda Naman jikinsa ke jida saboda Fushi ai bakinsa na Rawa yace"ban..bance komai ba yallabai.."Wani killer smile Aliyu yayi kafin yace,"Next time kakara dauko mace daya ma,ba biyu ba zaka ga yadda zanyi dakai.."mai mashin yace"Bama zan kara dauka ba yallabai wlh maza kawai zan koma dauka.."good.."inji Aliyu kafin yajuya yana Fadin"oya Sauka daga kan mashin dinka ka dauketa bisa kanka karka sauke har saika bar layin nan.."Sororo mai mashin yayi Tsawa ya dakamai ai da gudun hanzari ya daga mashin din da hannu bibbiyu ya wuce yana waige Jabir dake gefe yana waya Tikar dariya kawai yake,yana ba budurwan Nasa lbrin Abunda ke faruwa,su ko su Azeema Tuni suka Shige gidan goggo suna Rawan jiki,Da goggo ta tambayesu Azeema kasa mgana Tayi Azeeza ce ta maida bayani Yadda akayi Dariya goggo tayi tana fadin"Banda Abun gadanga miye na Sauke Fushin kan mai mashin,.."Abun yaba Azeeza mamaki yadda lbrin yaba goggo Nishadi,suna cikin maida mganar ne sai gadanga ya shigo yana Shigowa kai tsaye Azeema ya nufa sai da yazo gabanta kafin yace"Ke..."Dago kanta tayi kafin tayi Saurin sadda kai,Nunata yayi dayatsa yana fadin"ke babban banza ce ashe bansani ba,..To dis one wil be d last time dazanganki bisa mashin din wani kato,daga yau ki dinga hawan Keken Napep tunda na lura sakarcin naki gaba yake ba baya ba.."Yafada kafin ya juya,Galala goggo tayi tana kallonsa itako Azeeza kamar ta kurma ihu saboda murna baki goggo ta rike kafin tace"toh wayace maka Azeema na hawa mashin,Toh na tabbata rashin Abun hawa ne,bata da zabi ammh Azeema bata hawa mashi yo Allah na tuba inamatake zuwa balle ta dinga hawa mashin..."Cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallon Azeema yadda take kuka hawayenta na diga Tsausayinta ya kamashi maida kallonsa yayi kan Azeeza nan da nan Tayi wiki wiki da ido tsuramata ido yayi yana nazarinta,itako Tuni jikinta yahau mazari Abunka ga mara gaskiya,takowa yayi zuwa gabanta yana karemata kallo kafin yace"Ke..."Dago kanta tayi tana wani kifta ido matse goshi yayi kafin yace"Ni sa"an wasanki ne.. ? Shuru tayi tana Raba ido tsawa ya dakamata kafin yace"Nace ni sa"an wasanki ne..? da sauri Azeeza ta girgiza kai tana ja da baya,Wani tsawan ya dakamata kafin yace"Oya get out..Wannan yarinya wlh idonta na kama dana mayu,"Yafada yana kallon goggo ai da hanzari Azeeza ta fice ko waigo dariya takama goggo sai da dara gimtse Fuska Aliyu yayi kafin yace"Wai don Allah goggo meyasa kika sakarma wannan yarinyar Fuska ne,nifa banyarda da ita ba sam,idonta namin kama da na munafukai ne wlh.."Rausayar dakai Goggo tayi kafin tace"Toh mai gani hanji kai kowa bai maka ba,toh ko dole ka sota Tunda kana Auren yayarta.."baiyi mgana ba kawai ya fice cike da takaichin yadda goggo takasa Fahimtarsa sai yana ji ajkinsa tamkar yarinyar Tafi Azeema iya Duniyanci da wayau bayaso wani Abu yafaru agaba...
Goggo ita tayita lallashin Azeema har tayi Shuru ammh takasa daina jin Haushin kanta da mamakin Azeeza,itako Azeeza kwana tayi takaichi da bakinciki domin yaya captain yazo ya Rusata mata komai ammh ba komai yanzu tasaka kafa babu gudu babu ja da baya,bayan mangariba Jabir ya shirya Shida gadanga suka wuce Gra domin haduwa da budurwan ta jabir wacce suka hadu ta waya,ba laifi yarinyar tana da hankali da kunya babanta dan kasuwa ne,yarinyace bazata wuce sa"an Azeemar ba itama SS2 take a babban sakandiri Abun na jabir yaba Aliyu mamaki yadda yaga yana wani Rawan kafa agaban yarinya saboda Haushi mota yakoma yana game awaya Don yaga lalacewar na Jabir yayi yawa.
..
Sai pas ten suka dawo,koda suka dawo Goggo da diyarta tuni sun dade da kulle shashensu Sun kwanta suma basu bi ta kansu ba Aliyu ya kargame kofar gida suka fada shashenshi domin kwanciya,Abunda yabama Aliyu mamaki Jabir suna shirin kwanciya ya dasa waya da yarinyarnan kamar wani namamajo Ko gajiya basuyi Haushi yakama Aliyu ya fice daga dakin ya Shiga dayan bedroom din ya kwanta,nan yaga kayan Azeema da kayan kwalliyarta wadanda goggo ta siyamata,tsayawa yayi yana kallon kayan yana wani Tunanin yama Rasa ta ina xai Fara Taimakama rayuwar yarinyar don ya lura tana bukatar wani akusa da ita,Bata da sakewa ko kadan,bata da sani kan komai,shibaima san meke damunta ba,kullum kai asunkuye ko kuma ka ganta tana kuka,ada yana tsausayama kansa na Rashin cikakken Asali ammh yanzu yafi tsausayama Azeema Domin ita tana da uban ammh maraici da rayuwar Rashin yanci ya dabaibaye Rayuwarta uwa uba bata taso tare da kowa ba,Shiyasa wautarta tayi yawa,kwana yayi yana Tunanin mafita da yadda zai bulloma al"amarin.
***************
Washegari da Safe da wuri Azeema ta Shirya domin wucewa mkranta Bayan ta karya ta zauna tai zuru tana jiran ko Azeeza zata biyo mata su Tafi ammh Shuru goggo na lura da ita bata dai mata mgana bane ta tsayane taga iya Gudun Ruwanta zata fasa zuwa mkrantan ne saboda Azeeza bata biyomata ba ko yaya ne? Tana nan zaune Aliyu yayi sallama ya Shigo dakin goggo jallabiya Mai Ruwan Tokace ajikinsa,Tanajin sallamasa tayu zumbur ta mike tana mazurai Sau daya ya kalleta yakauda kai kusa da goggo ya isa yazauna ya gaisheta amsawa yayi yana Riko hannunta Da hanzari Azeema ta duka tana gaisheshi a dakile ya amsa kafin ya kalleta yace"Goggo metake jira bata tafi mkranta ba 7:30 fa ya wuce.."Kallonta goggo tayi kafin tace"Yauwa gwanda da Allah ya kawo ka gatanan,tambayeta nima Tundazu naga ta Shirya ammh ta nemi waje ta zauna bansan metake jira ba.."Sunkuyar dakai Azeema tayi Aliyu zai yi mgana kenan Jabir ya Shigo dakin Shima yana Sanye da jallabiya baka yana ganin Azeema ya washe baki yana Fadin"Ah ZEEMA kin tashi lafiya.."Dan Rankwafawa tayi tana gaisheshi Ansawa yayi cikin sakin Fuska yana fadin"Lafiya lau Zeema ya mkranta hop dai ana maida hankali.."Gyada kai tayi cikin kunya Gadanga dake zaune yayi Wuf ya mike yana fadin"Ke muje.."fuska ba walwala kallonsa jabir yayi kafin yace,"Toh miye nawani cewa kuje naganeka bakin ciki kake don ta dan Rankwafa dazata gaidani ko? hararansa Aliyu yayi kafin yace"Eh.."Adakile Akarkace Jabir ke kallonsa kafin yace"Dalili..? ko kallonsa Aliyu bai yi ba yabi bayan Azeema data fice da Sauri har zai Fice ta waigo yana fadin"kaji dan Rainin wayau ni dana rakaka zence jiya Budurwanka tama gaisheni ne,kunata rawan kafa ko Tunawa dani ai bakayi ba.."Yafada yana dariyan keta kafin ya fice Baki Jabir yakama lokaci daya yana Sosa kai goggo dake zaune gefe tace"Au zence kukaje jiya ko? to ai Allah yakamaku ja"irai.."tafada Tana dariya Sosa kai kawai jabir yake kafin yayi Wuf yafice yana fadin"Goggo ma gaisa da Rana."Yar dariya goggo ta sakeyi kafin tace"kai Jabiru da gadanga bansan wanda yafi wani Shegantakaba.."Take fada kan tatashi ta fada kichen domin ta kwaso musu Abun karinsu.
shiko Aliyu Tiryan Tiryan yake bin Azeema abaya suka fita daga gidan har zuwa bakin Titi kanzil bai cemata ba,itako tsoro yahanata ko waigo Suna zuwa ya taran mata wani dan adaidaita suka gaisa cikin mutumci kafin yadan duka sukayi mgana,ya fadamai ne Nawa zai Dinga biyansa yana zuwa yana dauka Azeema kullum yakaita mkranta ya dawo da ita,nan mai Adaidaita yace ya yarda buh ammh sai dai yafison adinga biyanshi Duk sati saboda halin Rayuwa..Nan take gadanga ya amince yace yakaita ya dawo sai suyi mgana bayan ya nunamai gidan da in yakaita zaizo ya sameshi,baya yayi yana kallonta kafin yace"oya ki Shiga yakaiki.."tsam tayi kafin tafara waige waige lura da hakan dayayine yasa shima ya waiga yana fadin"wakike nema..? bakinta na rawa tace"Az...Azeza.."bata Fuska yayi kafin yace"Wai Shin tsaya na tambayeki Azeezar nan ita ta haifeki ne? kokuwa dai ke Sakarcin ki haryanzu bai nuna miki kina zubar da kanki bane come get in kafin ki bani haushi.."dago kanta Azeema tayi idonta sun ciko da hawaye kafin taji kawai taji baki ya bude tace"Ban da kowa fa,ita kadai ce wacce zan daki kirji na nunata amtsayin yar"uwanta ba sakarci bane yaya captain kulafuncin yanuwantakane..",Tafada hawaye suna gangaromata,kuramata ido yayi baisan dalili ba,sai yaji kalamanta sun sanyarmai da jiki kallonta yake cike da tsausayi kafin ya jinjina kai yace"it ok wipe ur tears..Kije kidawo daga mkranta zamuyi mgana kinji.."yafada cikin sanyin murya gyada kai tayi tana Share hawaye kafin ta shiga adaidaita din Hannu ya sa aljihu ya ciro 1k yamikamata kin amswa tayi illah nuna mishi Hannunta datayi tana fadin"Goggo ta bani.."Kallonta yayi yadda idonta suka cika da ruwa sam baiji dadi ba juyawa yayi yana fadin"Ok Tunda kinfi son ta ringa baki da hannunta zan barmata sai ta baki..Take care of u self.."Mirmishi kawai tayi tana bin bayanshi da kallo har suka bacema ganinshi,har takai mkranta tana Tunanin yaya captain ita kadai sai sakin mirmishi take in ta tuna da wani Abun.
Itako Azeeza bata hakura ba Domin Tana Shiryawa tana Fitowa daga gida tazo gidan goggo,daga kofar gida ta tsaya ta faman leke,hango yaya captain tayi ya fito tsakar gida yana waya bayi da riga dagashi sai dogon wando gabadaya Sirrin jikinsa ya bayyana awaje,Azeeza dake labe Tuni taji ta manne da bango saboda shauki kirjinsa ta kurma ido lokaci daya tana wani lashe baki tama manta damai tazo yi Shiko yajuya baya ta jikin kofar goggo ya hango Azeeza ta leke bayan yajuyamata baya dayake kofar tanada glass daga samanta ne,mamaki yacikasa bai yanke wayar ba ya juyo yafara taku zuwa wajen yanayi yana dan kallon gefe Azeeza batama Fahimci cewa gadanga ya taho ba daga kanta kawai taji ance"Ke..."Cikin tsawa firgigit tayi saboda razana tasaka kafa zata zura da gudu gadanga yayi Wuf ya riko hijabinta yajawo ta baya ya watsar da shegiya kasa yana binta da wani banzan kallo,ammh mayyar hankalinta naga kan Suran jikinsa tana wani kifkifta ido nunata yayi kafin yace"ke ubanwa kike nema da kike ma Mutane labe..? bakinta na rawa tace"Adda Azeema.."tabe baki yayi kafin yace,"Oh yanzu kikasan da Adda Azeemar yaushema ta zama Addarki mara mutumci,ke nifa ban ma yarda dake ba gayamin waya Turoki ko Uwarkice taturo kizo ki cutar da Azeema..? yafada yana dukawa daf da ita baya Azeeza taja tafara tsorata da yaya captain din tsawa ya dakamata yana fadin"Zaki gayamin kokuwa sai na Fasa kanki da bindiga.."Jin zencen bindiga yasa Azeeza Saurin cewa"Armmm..A"a ba wanda ya Turoni.."Tafada idonta kyam akan kirjinsa sai alokacin ya fahimci inda idonta ke kai,mikewa yayi lokaci daya yajefa wayarsa cikin aljihun wandonsa yana jinjina kai yake fadin"Oho Yanzu na ganoki ke ashema ba iya rashin kunya kika tsayaba harda bin maza ko? Saurin girgiza kai tayi zatayi mgana ya dakamata tsawa yace,"Rufe min baki don ubanki zan miki karyane,kina kafe ne da ido kamar kin ga wani tsohon customer dinki ko? shegiyar daga ganin yadda kike kallona tsab aka kyaleki watarana zaki iya zama magajiyar karuwai,wlh tallahi kinji Rantsuwar dan musulmi in nakara kama idonki cikin nawa sai na fito da kwakwalwar kanki,Uselless kawai.."Yafada kan yasa kafa ya shureta yana fadin"Ur way out..Kar in kara ganin kafarki agidan nan.."Yafada yana nunamata kofa da Azama Azeeza tamike zata fice hawaye sun cikamata ido,Harta kusa Fita yace"ke tsaya..,kinga ko Azeema naga wani chanjin dabi"a awajenta ko naji wani lbrin wani Abu yafaru wanda ba halinta ba i swear daga ke har mahaifiyarka karnuka zasuyi watanda da Naman jikinku.."Yafada yana kadamata hannunsa,Azeeza tayi waje da gudu saboda kukan daya tasomata mkrantan data fasa zuwa kenan Inna Ramatu Ganinta kawai tayi ta shigo tana kuka,kuma tayi tambayar Duniyanan ammh Azeeza tayimata banza Kyaleta tayi,Saboda Yanzu kwata kwata tadaina gane kan Azeezar yanzu,itako kuka take da Duk Abunda tashirya sai Yaya captain ya Ruguxamata shirinta Kuka take da takaichi sai taga alamun Nasara sai kuma komai ya kwacemata.
Jabir da Aliyu suna cikin karyawa jabir ya samu waya daga Amminsa tana Fadamai mijin kanwarta dake jos Allah yayimai Rasuwa sakamakon hadarin mota yanzu hakama chan zata wuce yayi kokari yazo ya samu jana"iza Babu ko bata lokaci suna gama karyawa suka Shirya suka kama hanya Aliyu yayima Jabir din rakiya goggo tabisu da Fatan alheri tare da Addu"ar Allah yajikan wanda ya Rasu..Suna tafiya ba dadewa sai ga kawu bala ya zo,dayake ya shigo gombe yazo wani taro ne na Siyasa sai ya biyo nan wajen Suwaibar suka gaisa nan take fadamai yanzu su gadanga suka Dauki hanyar jos,Fatan isa lafiya yayi musu,Nan ya zauna sunata hira har bayan Azahar,har sai da Azeema tadawo mkranta ta tarar dashi,nan goggo ke koramai bayanin Duk Abunda ke Faruwa hakika ya tsausayama Azeema kuma yayi jinjina ga hikimar gadanga nan yayita ma Azeemar Nasiha tare da Shimata albarka da zai Tafi 30k yabama goggo Azeema kuma 10k yabama goggo 10k ta ijiyema mallam lawal saboda bazai iya jiransa har yadawo daga kasuwa ba,sallama sukayi cikin so da kauna tare kewa kafin su dau hanya shida tawagarsu goggo na bada sakon gaisuwa ga Umaima.
Aliyu kwana daya yayi ajos yadawo gombe yabar Jabir achan,shigan yammah yayi don bai shigo gombe ba sai Wajen biyar na yammah koda ya shigo gidan Azeema kadai ya tarar agidan wai goggo batanan Tatafi gidan kakarta Baba Ade bata da lafiya itama wainar Fulawa ta tsaya soyawa Goggo ko tace wlh bazata jirata ba,in tagama tazo daga baya toh tana kichen tana ta Faman Sauri taji shigowar yaya captain gabantane yayanke ya fadi Ras..,Sai da ta dafe saitin zuciyarta dakin goggo ya Shigo yana mamakin jin babu alamun mutum Agidan Motsin dayaji akichen ne yasashi Nufar nan Yana shiga yacikaro da Azeema tana tsaye tana kwashe wainar Fulawan Tsaye yayi yana kallonta itako ganinshi ya sata ta Rude bakinta na Rawa ta Furta.."San..nnu