x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - ALIYU GADANGA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 101877 words

Category: Tale Stories

Views 157

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH...,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘,Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

_Dis NOVEL is not for sale,plz masu bina pc suna tambaya na siyarwane,nawa zasu biya suyi Rigister,So Cool ur mine Aliyu Gadanga is a special gift to my Real Dota RAHMA😘and my mommah shiyasa yazama Free,what are  u  eating na baka is zubowa kasa,😂Na kudinfa na nan tafe,tunda naga da gaske kuke u what me to become HAJIYA JAMI😂Tanque very much my Real Fans,and a big Tanque to does prople for dere hot comments,Love u Tin Tin😍😘_

*NOT EDITED*💥

*Chapter2*

    """Gidan bikin sai yakoma gidan gulma da tsegumi,sai cecekuce akeyi kunsan mutananmu,sufa basu raina Abun gulma balle wannan dasuke jiran kiris,itako goggo tana daki tana kuka duk lokacin Data tuna kalaman Aliyu saitaji kuka na kawomata,madina ne ta shigo dakin taga halin datake ciki,ita takira mardiya suka zo suna ta bata baki,nan nema take fadamusu Abunda ya faru,dafe kai madina tayi kan tace"Oh mardiya,mutane ba kyau,to ai Shikenan Allah ma ya sakamai da wacce tafi figaggiyar ni"imar ma,don Azeema tafita komai,uwa uba ga hankali da tarbiya"

mardiya tace"Kwarai ma ko goggo,kibar damun kanki,donta Captain ne,lokaci kadan ne,zai warware.."Suka fada suna kokarin kwantar mata da hankali,dakyar tayi shuru kafin ta wanko idonta ta fito kamar ba ita ba,Ramatu ko da Aziza sunyi iya yinsu su Fahimci meke faruwa ammh Basu samu dama ba,shiyasa suka kara gyara zama har sauran tawagan Daurin Auren su dawo kila sasamu wani lbrin daga barayinsu,duk da tasan mallam ko zata mutu bazai fadamata ba,tunda yace tana da rariyan baki..

*****************

  Ni'imatullahi tana zaune cikin kaawayenta acikin Shiga ta alfarma sanye take dawani ubansu material mai tsada da yarari black and red an mata wani Fitinanne Dinki ajikinsa kanta kuma an dauremata shi da head baki,fuskarta cikin makeup mai kyau da tsari,Ni"ima gajera ce,bata da tswao ammh tana da kyau sosai domin Farace sosai mai dauke da faffadan Fuska tare da dogon hancinta,tana da jikin mata babu laifi kam ko"ina ya cika,kallo daya zakamata kasan ta fito daga gidan hutu,saboda yadda fatar jikinta ya tsumu ajin dadi,kallon idonta kawai zakayi kafahimci tana da mugun wayewa da budewar idon yan matan zamani sakamakon kaf bayan Primary bata hallarci wata mkranta a Nigeria ba,kasar waje tayi rabi da kwatan Rayuwarta.

Cikakkun kawayenta yan Duniya ya"yan masu dashi,harda diyat gwaannar jahar gwambe mai ci alokacin Falon dai cike da yan gayu na bugawa ajarida,sai shewa ake ana zolayan Ni'ima da fadin Anrigaya da an Dauramata aure Da Captain din nata,kamar yadda take kiranshi,itako sai wani Smiling take,tana wani washe hakoran jin dadi,duk sanda suka ambaci an Daura mata aure da captain dinta,suna cikin wannan Halin ne,wayarta kirar Samsumg gallezy tadauki kara cikin wakan nan U ARE MY LIFE.."Da hanzari ta sanya hannu ta jawota dama tana kusa da itane, LOVELY MUNARI..."Tagani dan tsaki taja don azatonta angon natane Kawartace babbar aminiyarta ma kuwa,wacce fitanta kenan daga falon ta sauka kasa zatayi mgana Da MAMINTA.

Dagawa tayi tana fadin"Ya how far...? Cikin wata murya Munari tace"Swhrt ki sauko kasa yanzu don Allah.."Sororo Ni"ima tayi kan tace"In sauko kasa kuma?uban me zanyi miki in na sauko,kinfa san yanzu matar Aurece ni,so taku daya in zanyi sai da izini in ba haka ba,in Shiga cikin Fushin Allah.."Tafada cikin nuna iya gaskiyarta kenan,Kai munari takama tana kallon yadda falon ya hargitse tun Shigowar Abbah falon da lbrin da suka zo dashi tace"Oh my God..Swhrt kibar mganar nan,ki sauko kiji.."

  Tsaki Ni'ima taja kan tace"mtsewww...Bazan sauko ba,in bazaki fadi Abunda ke bakinki ba to rike kayanki,sai kin hauro.."Tafada tana kokarin yanke kiran"Ajiyar zuciya munari tayi kan tace"Yanzu su Abbah suka dawo..,"Da hanzari Ni"ima ta daga tsalle tace"Da gaske,shikenan na zama matar Aliyuna,plz Friend kutayani murna na zama matar my Captain.."Tafada tana dariya gabadaya falon suka saka mata ihu da tafi,Munari ta dafe kai kan tace"Ke baki da hankali wlh,baki iya tsayawa kiji zence,ba to Abunda nakeso na fadamiki su Abbah sun dawo kuma ba"a Daura Auren ba.."

  Wani Abu mai Nauyi Ni"ima taji ya tsaya bisa kirjinta cikin wani yanayi tace"ban...ga..ne...ba..?"Tafada cikin rawan murya Munari tace"Haka Abbah yace,an fadamiki an dakatar da Daurin Auren sakamakon haryanzu ba"a ga wani daga dangin mahaifin Aliyu ba,shiyasa Abbah yace bazaya bada Aurenki ga wanda ya tashi gaban mace ba,wanda haryanzu ba"a san asalinsa ba."Ihu kawai Ni"ima ta yanka ko kafin ayi wani Abu ta zube kasa Warwas bata numfashi da gudu kawayenta suka rufu kanta suna Kiran sunanta da hanzari wasu sukayi kasa suka kira mami,wanda tanajin Abunda ya faru ta dora hannu akai,tana fadin"Na Shiga uku ni Hadiza,dama sai da nafada kwamishina wlh Ni"ima bazata iya rayuwa babu Aliyu ba,kada yayi haka,kada ya aikata haka,to gashinan dai Ga Abunda nake gudun  nan ya faru.."

  Take ta fada tana,kuka,kwamishana na gidan da hanzari aka tarairayeta aka wuce da ita asibiti ba yarda take,ai sai gidan biki yakoma gidan kuka,da gulmagulmace,tuni kawayen Ni"ima suka kama gabansu Munera ce kadai wacce da ita aka tafi asibitin, *FEDERAL TEACHING HOSPITAL GOMBE*kowa yaji ba"a Daura aure ba,sai ya Shiga mamaki yana neman jin dalili,Kafin kaceme gida ya watse sai mutanen daba"a rasa ba,wanda dama sun kasance Shakikai ne,ga kwamishina din da kuma Mami Hajiya hadiza.

Wannan kenan

________________

Sai da Su Kawu suka gama sallaman bakinsu kafin su yi ayari Shida tawagarsa da tawagar angon suka nufi gidansu Aliyun,don kawu yace Sauri yakeyi yau din yakeso yakoma Kaduna,har cikin suka shiga suna gaisawa da mutane Hajiya Umaima mata ga kawu Bala wacce suka kira Da Umma ita ta fito tana fadin"Abban Haisam wai meke faruwa ne? Tundazu goggon yara ke kuka,ga Captain chan ya dawo yana wasu maganganu don Allah wai meke faruwa ne?

Dan mirmishi kawu yayi kafin yace"Bakomai Umaima mushiga daga ciki,mallam Shigo kaima don Allah.."jin haka sai gabadayansu suka dumguma zuwa cikin dakin,Ramatu da Aziza jikinsu haryana kyarma suka rufamusu baya,saboda suna so suji kwakwam,Suna Shiga kawu yasa baki ya kira Gaggo ta fito tana musu sannu da zuwa,Kallonta yayi kan yace"Suwaiba meyasa haka? don Allah kiyi kokarin danne damuwarki,domin kibawa Aliyu kwarin gwiwa,bafa wani Abu dama Allah ya kaddara Ni"ima ba matar Aliyu bace Azeema ce matarsa.."

  Da hanzari Hajiya Umaima tace"Bangane ba,da wata Azeema aka Daura aure..'?Kai tsaye yace mata"Diyar mallam lawal,shi ya taimakemu ya fitar damu kunya,da bamusan ya zamuyi da tarin jama"ar damuka tara ba.."Ramatu dake gefe ta zaburo tana fadin"Da wata diyar mallam lawal din aka Daura Aure? badai Diyata bako? na Shiga uku ni Ramatu kowa na raba kanshi da hada zuru"a da mugun iri wanda ba"a son Asalinshi ba,ammh kai..."Ke Ramatu.."Mallam lawal ya katseta cikin Fushi yace"Dake ake mgana,wlh zan mugun sabamiki matukar nakarajin bakin ki cikin wannan mganar,Ba da yarki dakike kirarin itace taki na Aurama Aliyu ba,da Diyar kwarai wacce batagaji tsiya ba na basa AZEEMA.."Da hanzari Aziza ta dago tana kallon mahaifinta lokaci daya taji wani Abu ua tsaya mata bisa kokon rai tun lokacin dataji anfara mganar an Daurama Aliyu Aure kamar kunninta sai yajiyemata kamar Sunanta ake ambata da an Daura mata aure da Aliyu,alokacin wani farinciki ya mamayeta domin tunda tataso anguwa daya Da Yaya captain amtsayinsu na makota takamu da matsanancin sonsa,duk duniya kowani Namiji abanza take kallonsa,babu wanda takeso da buri yazama mallakinta irin Yaya captain koda take wani Abun,saboda Ramatu ne,karta fahimci inda ta dosa,ammh sai kuma gashi Mahaifinta yakira Sunan Azeema amtsayin wacce aka Daurama Aure da Yaya Captain dinta,lokaci daya taji jiri na neman kwasheta,sai da tarike hannun Ramatu kamkam tana rintse ido.

Ramatu ta mike tana fadin"Oho yanzu naji mgana Ai wlh da da yatace yanzu nan zaku warware aure nan domin bazan hada irin da Da"n mace ba mara asali .."Fita kibama mutane waje sakarya mara tunani.."mallam lawal ya katseta yana nunamata kofa Hannun yarta taja wacce ke wani hali tace"Ko bakace ba, zamu tafi,ammh dai an Fadi ba Nauyi kuma duk  wanda yahau motar kwadayi karshensa Tashar Wulakanci.."Tafada suna Ficewa.

Ajiyar Zuciya mallam lawal ya Sauke yanajin wani kunya tare da bakin ciki suna dirar mai lokaci daya dakyar ya iya cewa"Don Allah kuyi hakuri da maganganunta haka take sam bata da Tunani wani lokaci.."Mirmishin yake Goggo tayi kan tace"Bakomai mallam lawal Ai ba yau nake tare da Ramatu ba,ai yakamata nasan hallayanta babu komai kadaina biyemata don Allah,mungode sosai Allah ya saka da alheri bazan manta karamcinka garemu ba,ni da gadanga tun zuwana garin nan kake dawainiya dani,tare da gadanga saboda haka Allah ne,kadai zai biyaka Alherinka garemu.."Takarishe kamar zatayi kuka gabadaya suka shiga bata hakuri,nan kawu bala yace su tattaro suzo su koma gida tunda dai biki ya tashi nan akayi mganar tarewar ita Azeema ammh sai kawu yace abari nan da wani lokaci saboda Samun natsuwar Shi Aliyun,shima mallam lawal din yayi na"am da hakan saboda itama Azeeman yanzu take SS1 a babbar sakandiri,Goggo dai bataso ba,taso kawai Azeemar tatare a shashin da Aliyun ya gyarama Ni"ima,tunda nan zata fara zama,kafin yakoma wajen aiki chan kaduna su tafi tare,ammh babu yarda ta iya,domin bata iya tsallake Umarnin yayanta.

Haisam ne zai bi Su Ummah yakoma gida,domin sunyi sunyi Aliyun ya bude kofa yaki,Ran maza fa ya baci Dole yayi sallama da Jabir yabi su Ummh suka damki hanyar kaduna,dashi dasu madina da mardiya,Jabir kadai aka bari,Sai gobe Sunday zai koma Tunda monday akwai aiki,Dakin Goggo yakoma sukacigaba da tattaunawa akan Batun goggo tana nunamai ita tafi jin dadin wannan Auren,domin dama AZEEMAR yar dakinta ne,nan take komai nata ko kafin ma ayi hakan,shi kanshi Jabir sai yaji zuciyarshi tafi Natsuwa da Azeema domin ya santa sosai yarinyace mai hankali da natsuwa gata da ladabi da biyayyah bata da hayaniya ko kadan,Aliyu dai yana daki kwance,so yake yayi kuka ammh yakasa idanunsa ne,suka kada sukayi jajir,jijiyoyinsa kansa suka fito radau,Lokaci bayan lokaci sai ya naushi hannunsa da bango,goggo ko batabi ta kansa, ba saboda tasan halin dan kayanta,Aliyu gadanga zuciyarsa kamar kuturu in yatashi tsiyarsa sai tafita yammah da hankalinsa kafin suke komawa su daidaita.

**************

Azeema Atsorace takoma gida,tayi zaune cikin dakinsu tana sauke ajiyar zuciya data rufe ido tsawar da Yaya Captain yadakamata ke dawomata,sai tawani zabura kamar yanzu Abun ke faruwa,Ganin bata da mafitane yasata tamike tadauki tsintsiya ta share dan tsakar gidan nasu,domin tasani inda inna ta dawo ta tarar da ita batayi ba,sai na lahira yafita jin dadi,ta gama sharan kenan ta kwaso duka kwanukan wanke wanken duka gidan,amadafi tazo wajen wanken wanken nasu ta zube takarisa gindin rijiya ta zura guga ta dinga jawo ruwa sai da tacika botikai hudu,biyu takai Madafi,biyu kuma ta dauki kujera ta kada klin,tafara wanke wanke,tafara kenan taji shigowar inna Da Aziza,ta dago ido tana kallonsu lokaci daya tana fadin"Sannunku da zuwa..."

Inna Ramatu ta kalleta tana hararanta tace"Ke keda sannu,Tunda ubanki ya kashe miki rayuwa ya aura miki wanda ba"asan asalinsa ba,uwa uba gashi mara tarbiya,..."Da hanzari Azeema ta dago tana kallonta gabanta yana faduwa ta bude baki zatayi mgana kenan Aziza tazo ta wuce ta gabanta fuu ta bangajeta harsaida ta Fado daga kan kujeran datake kai,da kallo tabita harta shige daki,kwallah ta tarun mata a ido ta dago tana kallon Inna Ramatu tana fadin"Inna kinga Aziza ko? Tsaki Inna Ramatu taja kan tace"yo in na ganta mezan mata,dakika ga zata wuce meyahana ki kauce ki bata hanya,ai ke da mahaifinki Kwadayi zai kasheku don nasan kwadayin Abun Duniyane yasa ya bada Aurenki ga Dan mace nan..."Da hanzari Azeema ta mike tana fadin"Ni..Ni..Kuma ba.. ba..."Eh dake fa,saboda kwadayin Abun Duniya iyayan wanchan yarinyar sunce bazasu bashi yarsu ba,saboda ba"a san asalin dangin mahaifinsa ba,ammh dayake shashashan uba gareki wanda zuciyarsa tarigaya ta mutu ya daukeki yabada ke,ban damu ba,tunda kece Tunda kema zuciyarki irin ta ubanki ne,da dai yayi karambanin Auramasa Aziza wlh da anyi yakin Duniya na uku.."Tafada lokaci daya tana Shigewa daki,da wani kallo Azeema tabita kafin ta dafe kanta tana hada maganganun Innar in kunnenta yajiyemata Daidai kamar da ita taji inna na fadin A Dauran mata Aure da Yaya Captain,Saurin Dafe kirji tayi tana karanto Duk addu"ar datazo daga bakinta lokaci daya idanunta na zubo da kwallah,runtse ido tayi tana tuna yadda basu shiri sam da yaya captain saboda halinsa na rashin sakin Fuska da walwala uwa uba mugunta yaya captain baya da wasa kwatakwata ko asojojin shi na dabam, ne,nan da nan ta tuna karonsu na dazu,sai jikinta yahau rawa kasa karisa wanke wanke tayi,sai ta wuf ta wanke hannuwanta tafada dan karamin dakinsu gefen katifa ta zauna ta zabga tagumi tanajin kewar mahaifiyarta,domin da"a ce yau mahafiyarta na raye,da kila ta samu kafadan dazatayi kuka,ta lallasheta,ammh yanzu bata da kowa sai Mahaifinta,wanda kuma komai daga barayinsa ya fito,Har abada bazata taba bata kanta ba,bakuma zata watsama Mahaifinta kasa a idoba,duk duniya bata da wanda ya fishi,Share hawayenta tayi kafin tafice takoma ta cigaba da wanke wankenta lokaci bayan lokaci tana kallon dakin inna Ramatu tana share kwallah...

           #Comment,share and vote#
            #Janafty#
  *ALIYU GADANGA..!*
   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12
*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH..,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer's asso*✏

*Chapter3*

        *ASALIN TUSHE*

*MALLAM SHEHU AKARAMI* Sharahararren malamin Addini ne wanda yayi suna abangaren koyar da addinin Allah,Shidin ya kasance Basakawwace ne dan Asalin garin Birnin kebbi,akaramar hukumar kangiwa awani gari da"a kekira Arewa local Goverment,karatu da neman ilimi ya barosa daga garinsu,sakamakon duka mahaifanasa Allah ya amshi kayansa,yayi yawon garuruwa inda yayi karatun Allo har zuwa sauka ya karanta littafai babu adadi kafin Allah ya jehosa garin Zaria.

  Agarin na zaria ya samu masaka wajen wani malaminsa wanda ya karisa saura karatun littafai awajensa,sunyi zaman amana tare dashi,Shima malamin ba"arene wato Shima bassakwaceni ,kuma har dangin Shehun yaje,wannan dalilin ne ya saa ya auramasa diyarsa daya tilo Aisha ido,Bayan Aurensu anan zaria suka cigaba da zama,basu dade da Aure ba Allah yayima mahaifin indo rasuwa,baiyi Shekara ba matarsa ta bisa,koda aka raba gado gabadaya dukiyan da gonaki da aka mutu aka barmata duk ta mallakama mijinta Mallam Shehu wanda yagaji mahaifinta ya cigaba da koyar da almajirai karatu daga garuruwa dadama,yakasance mazaunin cikin zaria cityne Akwarbai.

  Gonakin sai yadinga Noma dasu,yana hadawa da kiwon Dabbobi domin dogaro dakai,..Bayan Aurensu sai mtsalan wabi ta biyo baya duk ya"yan da indo ta haifa da anyi suna sai sukoma ga mahallicinsu,sai da tayi takwas basu tsaya wa,har sun Fidda rai sai gashi Sun Haifi Bala,wanda basu ma sakaran zai Rayu ba sai gashi ya rayu,Shekaranshi Bakwai Aduniya Indo ta sake haihuwan Suwaiba,wanda tun daganan bata kara haihuwa ba,sai suka godema Allah bayan sun tattara ya"yansu guda biyu da Allah ya basu suka rikesu..

Koda aka haifi Suwaiba bala ya haddace alqur"ani,itama tana tasowa itama Mallam baiyi wasa da karatunta ba,Bala yayi karatun primary sch dinsa awata makaranta mai Suna Zaria acadmy,anan kuma yayi secondary sch dinsa,yana kammallawa ya fada ABU ZARIA inda yake karantar Political Science,Ayayinda Lokacin Suwaiba take SS1 anan Zaria acadmy din,itama kafin asakata mkrantar boko sai da ta haddace Qur"ani tana biya sauran littafi.

ABDULNASEER TAMBARI BUZU.."Wani Buzu ne wanda ya fado garin zaria akuma gidan Mallam Shehu akarami,Domin neman ilimi,Mallam Shehu ya amasheshi hannu bibbiyu Tunda dama yana amsan baki daga wasu kasashen kusa da Nigaria kamar su cameron da Chadi da Niger din,Babu Abunda mallam ya sani nashi sai Shi din mutamin Niger ne,ayanki agadez Sai kuma Sunanshi da suka sani,wajen shakaransa tara tare da mallam Tuni ya Sauke qur"ani yayi haddansa yakoma yanabin sauran litttafai,Shakuwa tare da sabo Tuni yayi da mallam da iyalansa bala da Suwaiba suna kallonsa ne,amatsayin dan'uwa ba almajirin mallam ba,Shiko mallam Shehu akarami yayi Shaku da Abdulnaseer sosai yakuma jarabasa ta hanyoyi dadama inda ya fahimci yana da amana da hankali bashi da mtsala ko kadan,shiyasa yasaki jiki dashi harda harkan Dukiyansa data iyalansa yana da masaniya,sai yazama shalelen malam Domin ma,sauran almajiran da Dan mallam sukemai lakabi,kwatsam batare da shawara da kowa ba Mallam Shehu Akarami ya Daurama Abdulnasser Tambari buzu Da Diyarsa Suwaiba aure Ranar datayi candy dinta Daurin Aure daya hada mutane biyar cur,daga mallam Shehu sai Abdulnaseer din,sai wani Abokin mallam din sai wasu manya daga cikin almajiran mallam din guda biyu,azauren gidan nasa,wanda mallam din da kanshi ya biya sadakin Auren nasu,Abdulnaseer shikanshi baida masaniyar Auren sai da aka kullashi kana kowa yaji,da farko bala ne dayazo Hutun Semister yaso yayi gaddama game da Aure,duba da Aure ba mganar wasa bace,taya ya za"a bama mutum aure batare da sanin asalinshi ba ko sanin wasu daga ciikin danginsa ba,ammh sai Mallam ya tausheshi da cewa lokaci kadan yake jira zasu dumguma dukkansu zuwa chan Niger din domin ganin ahalin Abdulnaseer din,Duk da bala bai wani gamsu ba,ammh sai ya share,saboda yana daraja mahaifinsa bazai iya sa"insa dashi ba,itako indo bata wani Damu ba,domin mijinta yayimata bayani,ita kuma Duk duniya babu wanda take gani da kima da daraja irin uban ya'yanta Shiyasa tabashi goyon baya dari bisa dari..
   
Abagaren Suwaiba kuwa bata wani ji wani irin ba,lokacin da Mallam yatarasu yake fadamusu,sai ma sunne kai datake tana satan kallon Abdulnaseer din,wanda kwata kwata baya da muni,Fari ne mai kalan ja,dogo ne karkarfan Namiji gashin kansa a nannade kallo daya zakamai kasan buzu ne gaba da baya,yana da kyau na daukan hankali,domin ko a anguwa yana fama da yanmata kai harda zawarawa,ciki harda manya mata wa"inda suka kusa haihuwansa,in suka gansa,kyansa yana Rudansu sukai ma tayi,ammh sai ya taka musu birki,Shima abarayinsa baiji yana kin Suwaibarba Domin bata da muni ko kadan itama doguwa ce,ammh kuma baka ce ita,tana kyanta babu laifi wanda kyan nata mai dauke dawani Sirri ne,sai da wanda yakaremata kallo yake fahimtar haka,Mallam Shi yayi alqawarin gina musu gida su tare nan Filin dake gaban nasu yasa aka tada gini,Ganin haka yasa in akayi abinci sai indo ta umarci Suwaiba data dinga dauka tana kaiwa mijinta adakinsa na zaure,to kusan sha"anin miji da mata,kuma gashi suna son juna,daya nemeta batayi yunkurin hanashi ba tabashi kanta,Ranar da Abun ya faru duk Nuku nukun Suwaiba sai indo ta gane saboda budurci ba wasa bane,ta rude ita da kanta tagasa yarta ammh kuma Abunda ya faru bai mata dadi ba batason mai zatacema Mallam ba,don yana mata fadan barinsu suna kebewa
End Ads