ko ki mutu..."Jabir yabata amsa Aranshi,yana yar dariya daidai lokacin da Aliyu ya fito daga tiolet daure da wani karamin Towel akugunsa,daya yana kansa yana tsane Ruwan dake diga daga kan nasa,yana ganin jabir da wayansa,ya tsaya cak yana jifansa da wani dirty look,shiko yana ganin haka,sai yayi hanzarin bude wayar a sepeaker,daidai lokacin da Muneera ta amshi wayar tana fadin
"Don Allah jabir do ur best wlh Sweetheart she seriously Sick yanzu haka muna Hopt tun jiya dataji Abunda ya faru,ta samu heartfailure,kabashi hakuri is not her Fuilt,yazo ya ganta ya lallasheta ko tabar kuka,wlh Tun data farfado take ta kuka tana kiran Sunansa plz Jabir..."Jabir yayi kasake yana bin Aliyu da kallo wanda ke rollin din idonsa yana wani cije baki,takowa yayi sai da yakusa gabda jabir kana yace da dan karfi.."Plz Dude tell dem to stay away From me..."Yafada muryansa na rawa,kallonsa jabir yayi sai yaga idonsa yayi ja,jijiyoyin kansa sun mike,Ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Kunji ko,plz karku sake kira,sai na nemeku don Allah,kubarsa Abun ya sakesa tukunnah,Ni"ima may Allah (SWA) Shifa u Ameen..."Yana fadin haka ya datse kiran,dagachan bangaren Ni'ima tanajin muryan Aliyu sanda yake mgana,batama gama jin Abunda jabir ke fadi ba,takara tsananta kukanta,kallonta Muneera tayi kan tace"Don Allah Sweetheart kibar kukannan hakanan,kiduba halin dakike ciki,in Mami tadawo ta tarar dake cikin wannan Halin u know bazata ji dadi bako? so plz Wipe ur tear don Allah ba karshen rayuwa ba kenan,kuma da yardan Allah zaki auri Aliyu.."Idonta jawur ta dago tana kallonta kafin tace"Are U sure..."Gyadamata kai Muneera tayi kafin tace"100%Sure Sweetheart..."Share hawayenta tayi kan takoma ta kwanta ta kurama Drip din da"ake sakamata ido tana kallon yadda yake diga sannu ahankali,lokaci daya ta runtse idonta kwallah na zubomata,ta rigaya data sani tayi bankwana da dukkan wani Farinciki Tunda Aliyu ya bar Rayuwarta.
Suko Anasu barayin Jabir na yanke wayar yafada wanka,Shiko Aliyu agurguje ya Shirya cikin wasu riga da wando black and white,kafarsa ya sanya wani bakin takalmi booth,sai kansa ya sanya wata bakar p-cap,ya dau katuwar jakarsa ya rataya yana Daura agogonsa na kamfanin Rado baki ahannunsa,Jabir ya fito,ganin Aliyu atsaye yasa shima ya shirya agurguje,shima yayi shigan Riga da wando,ammh nasa Neavy blue ne,shima jakarsa ya rataya suka dumguma suka fito,makulli Aliyu ya sanya Ya rufe shashensa,suka fada barayin goggo wacce ke kichen tana kokarin hada musu Abun kari,taji sallamarsu Fitowa tayi tana amsawa fuskarta na bayyana farincikinta data ciki.
Ganinsu tsatsaye kuma ga kaya yasa tatsaya Tsurus tana fadin"Lafiyanku naganku da wata uwayen jaka.."Dukawa Sukayi dukkansu Aliyu na fadin"Ina kwana goggo,zamu koma kaduna ne,bakin aiki.."Yafada yana sunkunyar dakai,karisowa tayi tazo tazauna kan daya daga cikin kujerun falo tana fadin'"Kai ku kalleni nan bani son iskanci,ina zaku yanzu da farar safiya,kamar ana koronku,ina fa madafi Tundazu ina kokarin hada muku Abun kari ne,wlh baku isa ba,bazaku barni dashi ba.."Tafada cikin fada,Mirmishi Jabir yayi yana mikewa yace"Kwantar da Hankalinki Goggonmu basai kin bata ranki ba,zamu ci kalacin dakike Shiryamana kafin mutafi,medame dame aka Tanadarmana.."Yafada yana zama kusa da ita.
Washe baki yayi tana fadin"Yauwa Dan Albarka Kunun Shinkafane Sai Fanke danake soya muku,akwai Ruwan Tea wanda yaji citta,sai ku hada dashi.."Tafada tana kallon Aliyu dake duke,Mikewa tayi ta isa garesa tana fadin"Taso taso Gadanga,bar damuwa hakanan,ban hanaku tafiya ba,ammh ku karya tafiya da yunwa babu kyau,tunda gida kuke ba daji ba.."Tana fadi tana rikosa,mikewa yayi yana kallo goggo kafin yace"Karki cikamin ciki goggo,nakaasa jagorantan Bataliyan yaki na gaba.."Sajensa ta shafa tana fadin"Da"n nema kaida yakamata sai sati na sama zaka koma,tunda kana cikin Hutun amarci ne",bata rai yayi yana fadin"Soja baya Daukan Hutu goggo,koda yaushe burin sojan nageria kare dubban rayuwa daya rantsuwa wajen amsan kaki,saboda duk Abunda ya shafi kare hakkin kasata da al"ummata goggo bana jin son jiki a al"amarin...",kansa ta dafa tana fadin"Nasara tana tare dakai Gadanga,insha Allahu sai kasarka tayi alfahari dakai kamar yadda take alfahari da Sardauna.."Amsamata yayi da Amin,kan sukarisa ta zaunar dashi kusa da jabir tana fadin"Bari na kawo muku kalacin."Tafada tana fadawa kichen Jabir da Aliyu suka bita da kallon kauna da tsausayi.
Tana rawan jiki ta jera musu komai,basu ci da yawa ba,ammh goggo sai da ta dura musu kunun shimkafanan cikin wani karamin Flaks,sai Fanke ta zuba musu cikin wani karamar kula ta basu,tana fadin ko ahanya sukaji yunwa su tsaya su ci,amsa sukayi jabir na dariya,shiko uban gayyar yasan hali mirmusawa kadai yayi,sallama suka mata,Aliyu yaba goggo 10k dakyar ta amsa,wai yaya yabata kudi,har waje ta rakosu Aliyu ya Shiga garejin ya fiddo musu da motarsa 4matic baka,Suna kokarim Shigane sai ga mallam lawal ya fito daga gida,da hanzari Aliyu ya dakata bayan ya saka jakarsa abayan motan ya nufi mallam lawal yana dan Sakin Fuskarshi yana zuwa kusa dashi ya rankwafa yana fadin"brka da safiya Baba."Rikosa Mallam lawal yayi bakinsa washe yana fadin"Tashi Tashi gadanga,Lafiya kalau,ya katashi,yakuma kwanan goggonka.."Mikewa yayi yana fadin"Tana lafiya baba,dama zan wuce saboda ankira bakin aiki akwai wata bataliya da zan jagora zuwa yankinnan na zamfara ne,shine nakeson mu shiga kaduna da wuri.."Gyada kai mallam lawal yayi yana fadin"Eh gaskiya to Allah ya taimaka Allah ya doraku bisa kansu,kukuma Allah yayi musu albarka.."Da Amin Amin Aliyu ke amsawa kafin yamikama mallam lawal hannu sukayi musabaha,yana fadin"Zan Tafi baba,..Arrrm *AZEEMA* tacigaba da zuwa mkrantanta both islamiya da boko,in tana bukatar wani tashiga wajen goggo,Don Allah Baba ayi hakuri da yanayin aikinmu sai na dawo sai munsan Abunyi.."Girgixa kai mallam lawal yayi yana fadin'"Ah babu komai Aliyu Fatanmu Allah yabaku nasara,sai ka dawo.."Da haka suka rabu cikin mutumci,yana tsaye har motansu Aliyu ta bace Alayin,kafin ya fara share inda zai basa kayan gwarinsa,yana yi yana girgiza kai in ya tuna tijaran da Ramatu tayi yau da safe,Abun sam babu dadin ji.
*********
*NIGER REPUBLIC*
Awani babban masarautace dake yankin *AGADEZ* Da misalin karfe 3:00pm na silasailin dare ne lokacin adaidai lokacin acikin kayatattaciyar masaraurar wacce takwafa tarihin na tsawon shekaru hamsin da doriya ta mulkan yankin na agadez.,masauratace babba wacce take kunshe da tarihai masu dimbin yawa tunkam zuwan addinin musulunci,Yanzu da ilimi ya yawaita akasamu yan boko suka mulki masarautar ansamu chanje chanje masu dimbin yawa,ciki harda rushe masarautar zuwa na ginin zamani mai kayatarwaa,kana dumfaru masarautar gininta da yanayin tsarinta zai burgesa yakuma baka sha"awa,uwa uba yadda take da uban dakarin yaki da masu tsaronta,masaurautace babba mai cike da bayi da wadanda suka jibamceta.
A babban shashen dayafi kowani shashi girma da kyau da tsari Wanda ya kasance shashin Ranka ya dade maigirma sarki kenan,wanda yake kwance akan makeken wani mulmulallan gadonsa mai kyau da tsari,wanda yaji Shimfidu Na alfarma Adalin sarkin ne da kansa kwance yana barci kamar kullum mafarkin daya saba yine yau ma yakeyin irinshi na yau ma yaso ya bambamta dana koda yaushe domin Fuskar matar hartaso ta bayyana garesa sai kuma yayi Firgigit ya farka daga barcinsa nasa yana salati lokaci daya zufa na ketomai kota ko"ina,Gimbiya FASILA ce yau aturakar ta Sarki da hanzari ta mike tana kallonsa kan tace"Ranka ya dade Allah kara lafiya meya faru ne,naga ka mike afirgice kana salati..? tafada tana kunna hasken dakin wanda ya gauraye lokaci daya.
Kallonta yayi baice komai ba,illah zuro kafafunsa dayayi ya sauka daga kan gadon ya zura wani takalmi mai gashi ya dumfaru wani dan daki da gefe,tabe baki tayi takoma ta kwanta aranta tana mamakin meke damun yallabai ne haka,duk kusan matan nasa ba wacce bata fuskartan wannan mafarkin nasa duk ranar girkinta,in baiyi wannan karon ba,wani zagoyowar zai faru,kuma ko kayi tambayan Duniyan nam baya kulaki ballatana ya baki amsa,Tana kallonsa ya fito Fuskarsa da farin gashinsa na digan ruwa alamar alwarla ya dauro ko kallonta baiyi ba ya isa ga wani dan korido inda wani shimfidaddan cafet yake mai kyau da tsari gefe daya carbi ne,sai daga baya wani cabinet ne,mai dauke da qur"anai da sauran littafai,bai bata lokaci ba ya cire fararan kafafunsa cikin takalmin na sarauta ya isa ga cafet din ya daidai sahu ya tada sallar,sai da yayi raka"a goma sha uku kana ya sallame ya zauna yana lazimi tare yima Annabi salati,aransa yana fatan Allah ya bayyanasa komai miye yake so ya bayyanass masa cikin mafarki Aransa yanaji kamar wani nauyi ne,da hakkin akansa wanda ya rataya awuyansa shekara da shekaru baya saukewa domin da alamun matar dayake ganinta tana bukatarsa cikin mafarkin kuma Abunda yafi daure masa kai yaron dayake tare da ita,wnda kowani lokaci yaron yana so ya iso garesa ammh kuma nisa da tazaran dake tsakaninsu baya barinsu su iso garesu da zarar kuma haske ya bayyana garesa domin ganin Fuskarta sai ya farka daga mafarkin wanda ya dau tsawon shekaru Ashirin da biyar yanayinshi,dayake shi mutum ne mai riko da addini bai yarda da duba ba,babu abunda yasa akayimai ko masu fassaran mafarkin da Ummansa mai babban daki ta sanya ayimai hanata yayi,yace ta barma Allah koma miye Allah zai yayi duhu cikin haske.
Yadade yana addu'oinsa kafin ya shafa gabda gabatowar asuba cigaba da zamansa yayi yana kwaroroma Allah kirari yana kiran anyi kiran sallar farko ya nufi masallaci domin duk sanda yayi wannan mafarkin barci kaurace ma idanunsa sukeyi.,Itako gimbiya fasilatu Tuni takoma barcinta ko ajikinta domin inda sabo sun saba da wannan al"amarin yallabai Adalin sarkin mijin nasu
#Comment,share,vote...#
#Janafty.....#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*DEDICATED DIS PAGE TO U KHADIJA CANDY❤(Mama)😘*
*Chapter 8*
"""Karfe 3;00pm na yammah motarsu ta saka kanta cikin kayataccen barikin na sojoji,wanda bariki ne,wanda ke kula da barikokin kaduna,kano,katsina zamfara da Sokoto Shine babban bariki na North a west wato *1 DIVISION NIGERIA ARMY KADUNA*...
Agaban wasu manyan gidaje daga chan yammah daga cikin barikin suka faka motarsu gidajene jere kamar estate saboda yawansu kuma dukkansu iri dayane komai da komai nasu illah nombobi ne kadai ya rabasu kowani gida dan madaidaicin flat ne mai kyau da tsari dauke da babban Falo da 3 bedroom kowanne da tiolet aciki sai babban kichen dake wajen falo,sai wajen Dining,daga waje Componud kowanne akwai parking space da dan Fili na motsa jiki ko Buga ball,tsakanin kowani apartment akwai dan tazara kadan bada yawa ba,kowani soja an makala masa sunansa da Nombarsa acikin babban kofar part dinshi,ina daga kai naga an saka da manyan baki cikin wani dan anani *CAPTAIN A.A TAMBARI BUZU* naga ansa kenan wannan gidan mallakinsa ne.
Suna gama Parking Tsirarrun Sojojin dake wayo aharabar wajen da hanzari suka kariso suna rige rigen bude musu mota,lokaci daya suna kame musu ko kallonsu Aliyu baiyi ba,jabir ne,ya daga musu hannu bayan ya nuna musu bayan motar inda kayansu yake,da hanzari suka bude suka kwashi jakukkunansu da hannu Aliyu ya nuna su,kawai sai naga sun rabu biyu,wasu sun nufi Apartment din Aliyu,wasu kuma Sun nufi apartment din dake kusa dana Aliyu dauke da jakar Jabir alamun nan ne barayinsa,Aliyu bayansu yabi duka hannuwansa cikin aljuhun wondonsa yana wata tafiyan takama bayanshi jabir yabi jin alamun tafiya yasa Aliyu ya waigo yana bin Jabir da wani Suprise look,shiko jabir gyara tsayuwa yayi yana fadin"Muje ko.."Akaikaice Aliyu yanuna shi da hannu yana fadin"to go where? dallah mallam kama gabanka,nan din gidanka ne.."? Wata dariya jabir yayi yana fadin"Nifa taimakonka zanyi,naga baka da lafiya,kana cikin damuwa kana bukatar wani akusa dakai..."Rike baki Aliyu yayi yana kallon jabir kafin yadan ware idonsa yana fadin"Don mai garinku nina fadamaka ina cikin damuwa? comon mallam kakama gabanki,yasin karka shigomin gida Ngd da Taimakon..",yafada yana Wucesa da sauri yar dariya jabir yayi kafin ya juya yana fadin"Kai kasani ga damuwa Aranka,ammh tsinannan iskancinka yasa kana wani basarwa chan ta matse maka gara kawai.."
"Aliyu bai waigo ba,yace"Ta matse maka dai azariyan wandonka banza Dan saka ido kawai.."Yafada daidai lokacin daya dauko dan makulli daga aljihun wandonsa ya zura akofar yana bude kofar falon,Sojan dake biye dashi daga bakin kofa ya tsaidashi ya karbi jakarsa saramai, yayi ammh Aliyu ko daga kai baiyi ba,sai ma shigewa ciki dayayi ya banko kofa,Sojan bai damu,domin duk wani Soja dake barikin yasan miskilancin Aliyu gadanga,shiyasa babu wanda ma ya damu dashi...
Yana Shiga falon bai tsaya ba,ya isa ga bedroom din,jefa jakarsa yayi kan gadon daya mamaye dakin yayi,kafin yafara tube takalmin kafansa,zuwa duka kayan jikinsa,boxers kadai yabari ya fada bedroom din,bai dade ba ya fito kugunsa daure da wani karamin Towel,yana Fitowa wayarsa tafara neman agaji ta wutsiyar ido ya hango mai kira *Swt Ni"ima* yagani wani dogon tsaki yaja yanajin wani daci aransa,wayar bata gama Ringing ba,ya yanke kiran bayan ya shiga ya sakata cikin blacklist,dama kawarta tun safe ya sakata,saboda bayason Takura sam,Shi yanzuma duk Abunda zai Tunamai da wata Ni"ima ma haushi kamasa yake,Da karamin Towel din ya fice zuwa wajen compound din Flask din da goggo tabasu da kulan Fanken ya duba bai gani ba,Rike kugu yayi yana hangen Apartment din Jabir saboda yasan shi ya dauka,kai gayen nan Dan mtsala ne yanzu yajamai sai ya dafa indomie Tunda bazai sake fita ba,ya dade tsaye yana Tunanin wulakancin dazaima gayen chan kafin yakoma ciki,wani guntun wando ya sanya 3quater ko riga bai dashi Ya fada katon kichen din Gas ya kunna ya dora wata karamar Tukunya,ya zuba Ruwa,lokaci daya yabude wani drower ya dauko indomie cherry guda biyu ya farka ya saka,bai fita daga kichen din ba,saima jawo wani Stool da yayi ya zauna yana ajiyar zuciya kamar wanda yayi wani auki,yunwa yakeji bai wani tsaya indomie ta tsotseba,ya sauketa da ruwa ruwa ya juyeta cikin Filet ya bude fridge ya dauko lemon cway ya fito,bisa daya daga cikin kujerun falon ya yada zangon yana daukan Remot bayan ya kunnah Talabijin din,kallon falon yake,yana ganin yadda yayi kura,karamin tsaki yaja aransa yana fadin"yasin ba sharan da zanyi am tired.."Yafada kamar wanda akasashi Dole,hakanan ya shiga Tura indomie har ya kusa cinyewa kafin ya ture filet din ya mike,ya karishe shanye Cway din,bedroom yakoma ya fada bisa gado,yana damke hannusa bisa kirji bayan ya kulle idanunsa,yashiga Tunanin Abunda ya faru daga jiya zuwa shekaranjiya,yana ta mamakin kansa,Ahaka barci ya kwashesa...
***********
_Gombe_
Tun karfe 4:00Am na Asuba Azeema ke tashi sakamakon tasan yau monday Sunada mkranta,kuma matukar bata tsaya tagama duka aiyukanta ba inna bazata taba barinta tatafi mkrantanba,sai ta kammallah komai koda zataje amakare ne,Shiyasa take tashi da wuri tagama duk Abunda takeyi kafin lokaci ya kuremata Tunda Azeeza dama yar gatace bata changal agidan,sai dai taci ta kwanta da Rashin kunya kadai ta iya.
Kafin 7:49am ta kammallah duk Abunda zatayi tayi wanka ta sanya Riga da wando da hijabi kalan Uniform din mkrantan,Madafi takoma ta dibe Tuwonta tazo tazauna tanaci,Lokaci bayan lokaci tana kallon Azeeza take kwance tana jin shesshekan datake alamar kuka takeyi,Gum Azeema tayi Domin tun dazu take mata mgana tatashi tayi sallar tayi Shirin mkranta ammh Azeeza tamata banza,ganin bazata iya barinta haka ba yasa bayan tagama cin Dumamen Tuwonta tamaida kwanon madafi tazo ta wanke hannu takoma dakin tana fadin"Azeeza keko wani irin barci ne,haka takwas fa takusa ammh baki tashi ba,ni harna Shirya zan Wuce mkranta.."Azafafe Azeeza ta tadago kanta daga kwance idanunta sunyi jawur Fuskarta ta kumbura Saboda kuka tace"Wai miye Ruwanki da Rayuwatace Adda Azeema? kin takuramin kin isheni,baza"ayi sallar ba,in kike da aljannar inna tashi shiga ki tare ni karna samu shiga.."Tafada tana mata wani banzan kallo,Azeema baya taja tana daukan jakarta wacce ta kasance ta hannu ne tana fadin"Allah ya baki hakuri...",Tafada cikin sanyin murya kafin ta dumfari kofar Fita,karaf inna Ramatu ta dago labulen dakin tana fadin"Kai Ni wannan bala"in ya isheni wlh,ke dai in da diyar wani Shehi ne,da anga kinibibi,to sai kuma kikayi dace ke diyar mallam lawal ne mai Saida kayan gwari,ina Ruwanki da yata,bakiga bata da lafiya bq ne,in tatashi Uwarki zatayi miki.."Tafada tana zabgamata harara,dukar dakai Azeema tayi kafin tadan Rankwafa tana fadin"Ina kwana inna..."Ko kallonta inna batayi ba,saima karisawa datayi cikin dakin tana fadin"Azeeza tashi,ya jikin ki? take fada tana tarairayota jikinta,Ko kallonsu Azeema batayi ba,ta fice kofar dakin inna ta tsaya tana sallama,mallam lawal dake ciki ya amsa bayan yabata izinin Shigowa,Shiga tayi bayan tacire sandal dinta mallam lawal dake kan gadon mai Rumfa ya sauko daidai lokacin da Azeema ta duka tana fadin"Ina kwana baba.."Ya amsa yana fadin"Lafiya lau diyar albarka,har anyi Shirin mkrantar..? ta amsa da cewa "Eh baba.."aljihunsa ya laluba ya fito da Naira hamsin ya mikamata yana fadin"Kin mkara ki hau mashi ko Keken napep,saura ko ruwa kyasha amkranta.."Noke hannu tayi tana mikewa tace"a"a Baba kabarshi Ban mkraba yanzu zan isa insha Allahu,ruwa kuma akwai fa famfo baba Amkrantar.."Tafada tana juya,Sunanta yakira ta waigo tana amswa mikata yayi yana fadin"Karbi diyar albarka bansanki da gaddama ba.."Hannu ta sanya zata karba taji an warje kudin bayan an Dunguremata kai,Inna Ramatu ne tsaye take kallonsu tana hararansu kan tace"ehe sannu mai diya,ammh yanzu kagama cemin baka da kudi,ammh dayake kan wannan banzar yarinyar ne,ai ka ciro ka bata,kuma dakake kokarin bata kudin ka manta kayi Auren jari da ita,Inashi mijin nata da bai bata ba.."Tafada cikin gatsine,Kallonta mallam lawal yayi yana fadin"Wai ke Ramatu meke damunki ne,koda tana da miji ni ba Mahaifinta bane,bata da hakki akaina ne? "Harzukomai tayi Tana fadin"Bata da hakkin akanka,don yanzu ba"a karkashin ikonka take ba,Azeeza ce ke karkashinka yanzu sonkai ne yamaka yawa shiyaasa baka ganin haka,uhm ayi mugani indai mune muna zaune zamu gani,kowa yana gudun hada zuru"a da bara gurbi ammh kai ka Rumguma yaron da"akace Rikakken Dan"iskane bai da aiki sai tara karuwai Achan kaduna.."Salati mallam ya saka yana fadin"Ramatu ina kika samu wannan lbrin kuma,oh ni lawal,yanzu baki Tsoron Allah yayi miki hisabi akan kazafin dakikayi masa.."Babu kazafi illah gaskiya in ba iskanci ba,ubansa yakeyi achan sai yadau lokaci bai zo gida ba,..."Azeema batagama ji ba,ta fice tana kwallah ko waiwaye batayi ba,ta fice daga gidan zuciyarta na kuna,Hanyarta ta dumfara kawai tana tafe tana lissafin zuci,Kamar ta biya gidan Baba ade Ammh kuma sai taga ta mkra sai tace bari sai ta dawo ta biya,Duk saurinta sai da Seniors suka tsaida ta tayi piciking kafin ta isa ajinsu duk wanda yaga Fuskarta sai ya Fahimci tana cikin damuwa kawai boyewa takeyi.