x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - MAZAN JIYA 1

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 204

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
satar jiki ya shiga
daji yin farauta shi kadai b tare da ya dauki
makami ba, sai dai aka ya kamo damisa ko
bauna ya shigo da ita gari a mace bisa kafadarsa.
Nan da nan jarumtakar Hantaru ya bazu a ko ina
a nahiyar, har aka dinga zuwa kallonsa ana
mamakin sa, wani abin mamaki a tattare da
Hantaru shine ko kadan bai damu da harkar
sarauta ba, babu yadda sarki Kusaidu bai yi da
shi ba akan ya rinka zuwa fada sun zama tare
amman sai ya sulale ya tafi farauta. Baya ga
farauta abu abinda Hantaru ke so sama da
koyon yaki, dan haka sai ya like wa Sarki yakin
birnin Kisra ya zamana cewa kullum yana
gidansa yana koyon yaki. Aiko a cikin shekaru
bakwai Hantaru ya zama gagarumin mayaki har
ma yafi sarkin yaki shahara.
145

TASKARNOVELS.COM.NG
Tun sa'ar da Fazira da boka Ardusa suka fa
cewar gaba daya hankalin Yarima Hantaru baya
kan sarauta sai hankalinsu ya dugunzuma suka
shiga kokarin asirce zuciyara domin yayi watsi
da harkar farauta data koyon yakin nan. Amman
sai suka sha ruwan mamaki domin asirin da
suke masa yaki yayi tasiri akansa. Ganin haka ne
yasa Boka Ardusa ya dukufa akan binciken gano
dalilin faruwar hakan, a cikin binciken nasa ne
ya gano cewa nonon da Hantaru ya sha na
amarya shine yya janyo ashin tasirin tsafi a
jikinsa, domin ita amarya Shamilat tana da wata
kariya a jikinta wadda mahaifinta ya shayar da
ita tun tana jaririya, kuma babu abinda za a iya
yi dan lalata wannan kariya.
Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya
turnuke boka Ardusa, domin ya fahimci cewa
har abada Hantaru bai yi sarautar birnin Kisra
ba muddin baiyi watsi da harkokin farauta ba ya
kama na fada ba.
Al'amarin sarki Kusaidu kuwa da amarya
Shamilat hankalinsu yafi na kowa dugunzuma
bisa ganin yadda dansu yaki damu da komai
face harkar farauta da kuma yaki, ko kadan
Hantaru bai shaku da sarki ba sai dai
146

TASKARNOVELS.COM.NG
mahaifiyarsa Shamilat, kuma yana bata mafi
yawa daga lokitansa a gidan abokansa yayan
mafarauta na birnin, sai da sarki Kusaidu ya
gana da boka Ardusa sau 10 akan wannan
matsala, amman ko yaushe sai dai boka Ardusa
yace da sarki ai sai dai ayi hakuri amma babu
abinda za a iya yi.
Boka Ardusa bai fada wa Shamilat dalilin da
yasa tsafi baya tasiri a jikin Yarima Hantaru ba,
dalili kuwa shine idan tasan da hakan
hankalinta zai dugunzuma ta bazama neman
taimako a wajen wasu bokayen kuma a haka
asirinsa na iya tonuwa har sarki Kusaidu ya
gane cin amanar da suke masa.
Wata rana amarya Shamilat na zaune tare da
sarki Kusaidu suna fira sai ta ce da shi ya kai
mijina ka sani cewa tunda ka aureni ka raboni
da kasarmu ban taba kaiwa iyayena ziyara ba
sai dai su sukawo mani, ina son kayinmani
izinin zuwa a wannan karon, nayi kokari nayi
shiri na je. Idan da hali ma zan so na tafi da
yarima domin yaga dukkanin danginsa na can.
Yayin da sarki Kusaidu yaji wannan batu sai
yayi ajiyar zuciya Ya ce yake mata ta kiyi sani
147

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa b laifina bane ki kai wannan ziyara, ina
tsoron dazuzxukan dake kan wannan hanyar ne
kafin a isa birninku, ni kaina sau daya nabi
wannan hanyar lokacin da naje neman aurenki.
Lokacin da zanje sai da akayi gagarumin shirin
yaki na dakaru masu yawan gaske, kuma sai da
Boka Ardusa yayi mani rakiya dan tabbatar da
tsaro.
Yayin da shamilat haka sai ta yi murmushi ta ce
ya kai mijina indai dan tsautsayin hanya ne ka
kwantar da hankalinka, ina mai tabbatar maka
da cewa babu abinda zai samemu, domin tun
ina yarinya karama iyayena suka bani tsari na
musamman, bama ni ba hatta dana da ya sha
nono na ya samu wannan tsari, kaima daka
aureni ka samu wannan tsari, indai kana cikin
hayyacinka to babu wani mahaluki daya isa ya
cutar da kai. Ni nasan cewa baka son rabuwa da
yarima daidai da rana daya shiyasa baka son
nayi wannan tafiya
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubo wa
sarki Kusaidu ya ce Tabbatas kin fadi gaskiya
yake mata ta, amman ki sani a halin yanzu babu
abinda ke damuna sama da rashin shakuwata
da Yarima, ko kadan bai damu da ni ba tamkar
148

TASKARNOVELS.COM.NG
ba ni na haifeshi ba, duk shawarar dana bashi
baya amfani da ita, har gwara ma ke naga yana
matukar kaunarki, kuma baya son yaga bacin
ranki.
Sa'adda sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai
tausayinsa ya kama Shamilat, ta dafa kafarsa ta
ce kada ka damu ya kai mijina nayi maka
alƙawari da zarar munje garinmu mun dawo
zakaga sauyi a tare da Yarima zai kaunaceka
kamar yadda ko wane da yake kaunar ubansa
Hakazalika zai shaku da kai, sannan zai ajiye
harkokin farauta ya rungumi na sarauta.
Da jin haka sai sarki Kusaidu ya dubi Shamilat
cikin tsananin mamaki ya ce Ta yaya hakan zata
faru?
Shamilat ta ce kakana shahararren boka ne
wanda babu kamarsa a nahiyarmu, ina mai
tabbatar maka da cewa ko Boka Ardusa aka sai
dai suyi kunnen doki a karfin sihiri, kai ina da
tabbacin kakana yafi Ardusa tarin ilimin tsafi,
lallai nasan zai taimakemu ya juyo da hankalin
yarima zuwa kan tafarkin da muke so.
Yayin da sarki Kusaidu ya ji wannan batu sai ya
cika da farin ciki kuma ya amince da batun
149

TASKARNOVELS.COM.NG
tafiyar Shamilat. Tun kafin dare yayi Shamilat ta
tura aka kira mata Yarima Hantaru tayi masa
albishir da tafiyar da zasu yi a gobe ita da shi
izuwa can mahaifarta ta darul maabur.
Koda jin haka sai Hantaru ya cika da tsananin
farin ciki domin a rayuwarsq bashi da wani buri
da ya wuce yayi doguwar tafiya wacce zai ratsa
ta cikin dazuka masu ababan hadari, kamar yan
fashi da muggan dabbobin daji, ba dan komai ba
sai don ya jaraba iyakar tsawagaron ku riyarsa
da kuma shan wahalarsa, ya kuma ga iyakar
karfin damtsensa, tunda ya ke sau daya ya taba
halartar yaki a birnin Kisra kuma lokacin da
yaje filin yakin ma saura kiris a gama da abokan
gaba, a takaice dai Yarima Hantaru yana so yayi
doguwar fafatawa da aboka gaba. Saboda
tsananin dokin da yarima Hantaru yake saboda
tafiyar da zasu yi tun a daren ya kimtsa kayansa
sannan ya daura wa dokinsa sirdi sannan ya
tanadi kayan yakinsa. Lokacin daya kwanta
bacci sai idanunsa suka bushe ya kasa bacci
saboda tunanin tafiyar ta gobe. Bisa wannan
dalili ne yasa ya tafi dakin mahaifiyarsa
Shamilat, da shigarsa cikin turakar sai ya isketa
a zaune tayibshiru tana tunani sai faman
murmushi take yi kamar wacce take magana da
150

TASKARNOVELS.COM.NG
wani. Har Hantaru ya zauna kusa da ita amman
bata san ya shigo ba, sai da ya dafa hannunta
sannan tayi firgigit kamar wacce ta farka daga
bacci, Hantaru ya dubi Shamilat cikin mamaki
ya ce ya ke ummina tunanin me kike yi ne haka
wanda har ya hanaki ki kwanta kiyi bacci.
Sa'adda Shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi
murmushi sannan ta ce Ya kai dana kayi sani
cewa tsananin murna ce ta hanani na kwanta
nayi bacci, saboda ina murnar cewa zanje naga
kakana wanda ya haifi ubana Boka Sulbaini Bn
Ukash. Kayi sani cewa a hannun Sulbaini na
girma har nayi wayo, daga baya da za a yi mani
aure aka rabani da shi, a ranar da za'a rabamu
da shi munsha kuka tamkar ranmu zai fita
saboda sabo da juna, rabona da shi yau shekara
16 kenan, nasan cewa yanzu ya kara tsufa ainun
babban burina shine na sake saduwa da shi
kafin rai yayi halinsa.
Koda Shamilat ta zo nan a zanjenta sai hawaye
ya zubo mata, take Hantaru yaji tausayinta ya
kamashi har shima kwalla ta zubo masa,
Hantaru ya rungume Shamilat gana mai cewa ya
ke ummina ki kwantar da hankalinki domin naji

151

TASKARNOVELS.COM.NG
a jikina cewar wannan kaka naki na nan a raye
kuma tabbas zamu je mu riskeshi.
Tsawon yan dakiku duk su biyu suka yi shiru
babu wabda ya ce kala, daga can sai yarima ya
janye jikinsa daga jikin nata suka dubi juna
sannan ya ce Ya ke ummina shin ba kya bani
labarin yadda rayuwar mutanen birninku take
ba?
Lokacin da shamilat ta ji wannan tambaya sai ta
yi murmushi sannan ta gyara zamanta ta ce Mafi
akasarin mutanen birninmu mafarauta ne da
kuma makera, mahaifina shine sarkin makera
kuma shine galadiman sarkinmu ana kiransa da
suna Shuraim Bn Alkas. Tsakanin zuri'armu ta
makera data mafarauta babu kyakkyawar
fahimta ko zumunci mai karfi, kuma babu
auratayya mai yawa. Babu abinda yafi burgeni a
garinmu face wata al'ada da aka saba yi duk
karshen shekara, al'adarvita ce za'a zabo
budurwar data fi dukkanin yan matan garin
kyau a sa gasar neman aurenta a tsakanin
jaruman samari, masu ji da sadaukantaka.
Yanayin gasar shine za a saki barewa a daji a
kasa tsere duk saurayin da yafi kowa gudu ya
kamonwannan barewa to shi zai auri wannan
152

TASKARNOVELS.COM.NG
kyakkyawar budurwa. A lokacin da ake tseren
gudun an yarda samarin su dinga bangaje juna
duk wanda ya fadi kasa to ya fita daga cikin gasr
kenan.
Gabadaya mutanen garin banda al'karan gasar
suna hawa kna wani dogon tsauni ne su tsitsaya
dan su hango abinda ke faruwa, su kuwa alkalan
gasar suna bin bayan mahayan ne, lokacin da
shamilat ta zo nan a zancenta sai Yarima
Hantaru yaji soyayyar darul maabur ta
lullubeshi domin ya fahimci cewa can ne ya dace
da yanayin rayuwarsa, dan haka sai ya sake cika
da tsananin farin ciki.
Yadda yarima yaga rana haka yaga dare, wato
har gari ya waye bai runtsu ba, washegari da
sassafe ya tashi tunma kafin alfijir ya keto yayi
wanka ya kuma sanya tufafinsa, yana gama
kimtsawa kuyanga ta kawo masa abincin kalaci,
amman yana yin lokamar farko sai yaji ya koshi
dan haka sai ya mike ya bar abincin ya tafi dakin
Shamilat, yana zuwa ya iske ta, tuni itama ta
gama shiryawa shi take jira kawai.
Nan take kuyangi suka fito da kayayyakin
Shamilat har da guzurin da zasu tafi da shi da
153

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma tsaraba, duk wannan abu da ke faruwa
Zarifa bata sani ba sai a lokacin da sarki ya fito
daga cikin turakarsa ya riski Shamilat da
hantaru tsaye cikin turakarsa, kawai sai ta riske
sarki Kusaidu yana bankwana da shamilat har
yana rungume yarima Hantaru yana zubar da
hawaye.
A gigice zarifa ta taho da gudu ta karaso garesu
ta kama hannu Yarima Hantaru ta rike tana mai
cewa ya kai dana ina zaku tafi haka amman
baku fada mani ba?
Yarima ya dubi Zarifa a wulakance ya ce zamu
tafi garin kakannina ni da mahaifiyata.
Koda jin haka sai Zarifa ta ji zuciyarta ta buga da
karfin gaske, har bata san sa'adda ta kama
surutai ba tana cewa ai bai kamata ku tafi yanzu
ba, zai fi kau ku bari ayi maku shiri na
musamman.
Yarima Hantaru yq ce ai babu abinda zai hana
mu wannan tafiya a yau, sai dai fitar ruhi daga
cikin gangar jiki. Gama fadin hakan keda wuya
sai Hantaru ya kama hannun Shamilat ya ja ta
suka tafi, barori ba biye da su da kaya niki-niki.
154

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai Zarifa ta sulale tq fice daga
cikin gidan sarautar ba tare da kowa ya sani ba.
Cikin hanzari Zarifa ta haye bisa doki ta ruga
izuwa gidan Boka Ardusa domin ta sanar da shi
halin da ake ciki dan yasan matakin da zai
dauka kada asirinsu ya tonu.
Boka Ardusa na zaune shi kadai a cikin harabar
gidansa ya zuba wasu alkaraman sihiri a
gabansa yana nazari sai kawai yaga Zarifa ta
shigo da gudu kuma a gigice har tana tuntube
zata fadi kasa. Koda ta iso gabansa sai ta zube
kasa tana mai faman haki, kuma ta bude baki
zata yi magana sai kawai Boka Ardusa ya daga
mata hannu yana mai yi mata nuni ta yi shiru.
Bisa dole zarifa tayi shiru bata ce komai ba,
kuma ta kura sama idanu har sai da ya gama yan
tsubbace-tsubbacensa. Boka Ardusa ya juyo ya
dubi Zarifa ya ce da ita ai nasan abinda ke tafe
da ke, kuma tun a jiya nasan da batun tafiyar
amarya Shamilat da danmu Yarima. Ki kwantar
da hankalinki tamkar tsumma a randa domin
babu abinda zai faru. Ina mai tabbatar maki da
cewa muddin ina numfashi a doron kasa har
abada asirinmu bazai tonu ba. Ki saki ranki kije
kita bacci harda munshari, da sannu burinmu
155

TASKARNOVELS.COM.NG
zai cika danmu ya zama sarkin birnin darul
maabur.
Koda jin wannan batu sai Zarifa ta kyalkkyale da
dariya, can kuma sai ta hade fuska ta yi shiru
kamar tana nazari.
Boka Ardusa ya dubeta cikin damuwa ya ce
tunanin me kuma kike yi, alhalin na fada maki
cewar babu abinda zai faru?
Zarifa ta yi ajiyar zuciya ta ce ni abinda nake
tsoro shine kada yarima yayi zamansa acan
birnin darul mahabur yaki dawowa nan gida,
abu na biyu ni fa yanzu na shiga matsananciyar
damuwa saboda dana yarima bai san cewa nice
mahaifiyarsa ta gaske ba, shin kana tsammanin
cewa nan gaba zai karbeni ne a matsayin uwa ?
Boka Ardusa ya ce kwarai kuwa, kuma sai ya
kaunace mu fiye da kowa a rayuwarsa nayi maki
wannan alkawari, kedai ki ci gaba da hakuri
al'amarine na lokaci, idan muka ce zamu yi wa
lamarin gaggawa to fa lallai burinmu ba zai cika
ba.

156

TASKARNOVELS.COM.NG
Haka dai Boka Ardusa yayita lallamin Zarifa har
hankalinta ya kwanta, suka aikata cin amanar
da suka saba sannan ta tafi.

Mazan Jiya Part 15

#Cigaba

A lokacin da shumilat da yarima hantaru suka
fita kofar gari sai suka kama hanya batareda
fargabar komaiba su kwana nan su tashi chan
saida suka bar birnin darul maabur da shiga su
daji na fark6 wanda ake kira sujud sai shamilat
taja linzamin dokinta ta tsaya shima sadauki
hantaru saiya tsaida dokin nashin, shamilat ta
kasa kunnenta bataji motsin komai ba sai
tayiwa yarima hantaru magana cikin rada tace
akwai muggan yan fashi a wannan daji kuma
sun iya nada muggan tarkuna sai mun kula da
kyau koda jin wannan magana sai hantaru yayi
mata nuni data sauka daga kan dokinta
batareda wata gardama b shamilat ta sauko
157

TASKARNOVELS.COM.NG
shima saiya sauko daga kan nashi. kawai sai
yasaki dokin nasa yayi gaba koda dokin nasa
yayi tafiyar kamar taku talatin saiya zurma cikin
wani wawakeken rami mai zurfin gaske saiga
wadansu samudawan yan fashi suna mai
rugowa daga cikin maboya suna zuwa bakin
ramin suna tsayawa adadin yan fashin ya haura
300 dukkaninsu sun kasance majiya karfi kuma
suna daukeda muggao makaman yaki sun shafe
fuskokinsu da bakin shuni bayan yan fashin sun
gama yiwa wawakeken ramin kawanya rai suka
fuskanci cewa yaufa karensu bai kama zomo ba
domin doki ne kawai ya fada cikin ramin babu
mahayi akan dokin babu dukia cikin tsananin
fushi shugaban yan fashi ya dubi sauran
dakarun ya daka musu tsawa yace tsayuwar me
kuke maza ku baxama neman mai wannan
dokin kafin yagama rufe bakinshi sun tarwatse
sun rarrabu acikin dajin, ashe dvk abin da akeyi
hantaru da shamilat na labe acikin wani
duhuwa suna hangowa koda hantaru yaga yan
fashin nan sun rarrabu suna farautarsu sai ya
cewa shamilat ta dada buya acikin wannan
duhuwa shi kuma sai yakama wata doguwar
bishia yakama hawa samanta hantaru yayi lamo
acikin ganyen bishiyar duk dan fashin dayaxo
158

TASKARNOVELS.COM.NG
inda shamilat ke boye sai hantaru ya diro ta
bayansa ya masa mangara daya ya fadi
sumamme sannan ya kwashe makanshi yayi
sama dasu a haka saida ya sumarda sama da yan
fashi 50 koda yaga zasu gano inda shamilat ke
boye saiya sauko kasa ya dauke ta daga wajen
ya ruga zuwa inda wawakeken ramin nan yake
wanda dokinsa ya fada ciki!! wohohoh nan take
hantaru ya shiga cikin ramin nan ya dauko
dokinshi kafin hantaru ya juya ya daura
shamilat akan dokinsa sai yaga yan fashin sun
masu kawanya kimanin su 300 da doriya tuni
shugaban yan fashin dora wata wuka mai
tsananin kaifi akan wuyan shumilat cikin firgici
hantaru ya dubeshi yana mai daka mishi tsawa
yace ku kwashi duk abinda kuke so daga dukiya
amma inamai gargadinku da kadaku kuskura ku
tuba lafiyar mahaifiyata koda jin haka sai
shugaban yan fashin yace aiko sai mun dauki
fansar yan uwanmu daka sumar ka kwashe
musu makamai yanxu xan kashe mahaifiyartaka
sannan kaima nayi maka kisan gilla na kwashe
dukiyar taku kafin hantaru ya budi baki yace
wani abu tuni shugaban yan fashin nan ya
dadara wukar nashin akan wuyan shumilat bisa
mamaki sai yaji kamar akan dutse ya dadara
159

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka
ajikin shi Cikin zafin nama hantaru ya zare wata
wuka ajikinshi ya cillata ta cake a goshin
shugaban yan fashin ya sulale kasa matacce
koda ganin haka sai sauran yan fashin suka
afkawa hantaru suna masu kai mishi sara da
suka ta koina kaicoh! inda yan fashin nan sun
san abinda zai biyo baya da dukkaninsu sun
nemi gudu tsira. koda sukayiwa hantaru
kawanya kawai sai yayi wuf yakama kafar daya
acikinsu ya maidashi makaminshi da kuma
garkuwanshi ya dinga tare sara dashi kuma
yana maida martani dashh nan danan suka
daddatsa dan uwan nasu duk wanda hantaru ya
makawa dan uwan nasu sai kaga ya fadi
sumamme koh matacce nan fah akarasa mutum
daya daga cikinsu wanda zai iya koda lakutar
jikin hantaru saboda tsananin zafin namanshi
da karfin bugunshi kafin cikar sa'a dari biu duk
ya bazar dasu akasa mattatu a sannane ne
hantaru ya dubi shumilat cikin matukar mamaki
yace yake ummina yaya akayi wuka ta kasa
yanka ki? shamilat tayi murmushi tace shin
kamanta cewa ubana
sarkin makerane babu wani karfe dazai iya
huda jikina koda kaima kanka karfe bazai
160

TASKARNOVELS.COM.NG
cinkaba saboda kasha a nono shin kataba jarba
karfe acikin ka? hantaru yace Aah amma barina
jarraba yanxu nagani nan take hantaru ya zare
takobinsa ya yanki dantsen hannunsa aiko sai
yaga ko kortsanuwa bai yiba kawai sai ya cika
da tsananin mamaki. batareda bata lokaci ba
suka hau dawakansu suka cigaba da tafiya suna
masu kada dawakan gaba suka bar yan fashin a
zube a kasa matattu ru hantaru suka cigaba da
tafia har tsawon kwana sha daya basu sake
haduwa da wani mugun abuba da tsakar ranar
kwana na shadayan ne suka shigo cikin wani
bakin daji mai ban tsoro domin babu komai
acikin shi tsaunuka masu tsawo da kwazazzabai
da shigarsu cikin dajin hantaru ya aiyana a
ranshi lallai baza'a rasa muggan halittu acikin
shiba koda gama aina haka sai ya zare
takobinshi yaceda shamilat ta dawo nashi dokin
shamilat batayi wani gardama ba tayi yadda ya
umarceta yin hakan keda wuya sai sukaga
wadansu manyan gwaggon biri sunata fitowa
daga cikin
kogunan dutsen nan suka cigaba da bullowaa
kamar bazasu kare ba koda ganin gwaggunan
birin sai hankalin shumila da hantaru ya
dugunxuma domin basu taba ganin birrai masu
161

TASKARNOVELS.COM.NG
girma da muniba kuma koba komai sarkin yawa
yafi sarkin karfi hantaru yasake kankame
takobinshi dakyau yana ainawa arranshi cewa
yau komin rintsi da tsanani baxai bari a taba lfy
mahaifiyarshi ba adaidai wannan lokacin ne
shamilat taji nadama tazo mata abisa wannan
tafia zuwa birnin iyayenta nan take ta tunoda
zancenda mijinta a lokacin da yake fadamata
hadarin dayake kan wannan hanya. sannu a
hankali birurrukannan suka cigabada matsowa
suna yiwa dawakansu hantaru kawanya
sukansu dawakan saida suka kama ruri da
haniniya bisa gani birurrukan,shiko hantaru
koh gizo baiyiba yaci gaba da rike linzamin
dokinshi da hannu daya dayan hannun kuma na
rikeda takobi wannan birran dai sunfi shekara
arba'in acikin wannan dajin idan maza suka
kama take suke kashe su inko mata ne sai su tafi
dasu cikin gidajensu suna lalata dasu koda
birurrukan suka tasan ma hantaru sai shima
yayi kansu yana mai saransu yana bangajesu da
kafa suna zubewa kasa bisa mamaki sai hantaru
yaga ai takobi bata tasiri acikinsu duk sa'adda
ya sara sai yaji kamar dutse ya sara nan fah
birran suka fara kokarin su hallakashi amma sai
yazamo musu alakakai yayinda hantaru ya gano
162

TASKARNOVELS.COM.NG
nufin birran nan kuma yasan takobinsa batada
wani amfani sai zuciyarshi ta harxuka yayi jifa
da takobinsa cikin zafin nama ya goya shamilat
a bayansa sannan ya diro kan dokin aka
cigabada gumurzu mai ban alajabi domin duk
inda hantaru ya kai duka saidai kaga birurrukan
sun zube a kasa duk yawan nasu sai yaxamo na
banza domin sun kasa koda lagutar jikinshi da
faratunsu babban abinda ya tayarwa hantaru
hankali dazarar ya zubar da birurrukan a kasa
sai sumike zunbur su sake afka mishi runa masu
kai mishi cizo da yakushi
End Ads