x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - MAZAN JIYA 1

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 214

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
zuciya bata da kashi, kuma
itace abar dake jefa mutum ga halaka dare daya.
Daga wannan rana Shuraim da Hantaru suka
rinka motsa jiki, yana nuna masa yadda ake yin
219

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan gasa ta tseren gudun kamo barewa a
daji, a kullum sai su wuni suna gudu a daji,
kuma suna gudun ne a bisa dawakai suna yakar
juna domin daya ya jefo daya daga bisa dokinsa.
A wannan lokacin ne Hantaru ya tabbar da cewa
lallai Shuraim ya cika Sadauki domin yayi
mamaki matuka da yaga irin juriyarsa gami da
jarumtakarsa wajen shanye duka da kuma zafin
namansa na kare sara da suka yayin da suke
gudu a kan dokin, duk da cewa girma ya fara
kamashi.
Duk irin kokarin da Hantaru ke yi a wannan
motsa jiki da suke yi, kullum.sai yaga Shuraim
baya yaba masa, domin a kullum ce masa yake
ya kai jikana ka kara kwazo domin har yanzu
baka yi rabin kwazon da Sadauki Rabbasu zai
iya yi ba yayin gasar, nasan yanayin gasar nan
kuma nasan sirrinta ciki da bai, sannan nasan
iyakar jarumtakar Rabbasu, bugu da kari duk
shekara idan za a yi wannan gasa sai Rabbasu
ya fito filin gasar ya zuba idanu yana nazarinta.
Tabbas ya fika sanin sirrinta shiyasa nake da
yakinin sai ya fika kokari dan har baka kara
jajircewa ba, gobe zan gayyato samarin
zuri'armu mu fita daji tare domin mu gwada
220

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan gasa tare da kai, a sannan ne zanga
iyakar kokarin da zaka iya yi.
Kashegari kuwa da sassafe samarin zuriar
makera suka taru a gidan Shuraim sannan suka
dunguma suk tafi daji domin jarraba gasar
tseren barewa tare da Sadauki Hantaru. Ai kuwa
ana fra wannan gasar sai Hantaru ya raina
kansa, domin kuwa kafin ya farga tuni anyi
masa fintinkau. Sabida samarin sun kware
ainun wajen sarrafa doki, kuma kowannensu ya
dade yana hora dokinsa saboda zuwan wannan
rana.
Sai da Hantaru ya zamo shine a can baya na
karshe, koda ganin haka sai hankalin Hantaru ya
dugunzuma, zuciyarsa ta harzuka ya tuno da
gwagwarmayar da yayi a baya, ya kuma tuna
cewa shifa sadaukine na kwarai, lallai idan bai
dage ba ya ci wannan gasa ba, to kamar ya rasa
Gimbiya Larziyya ne, kuma ya kasa karbo
kambun gasa daga zuri'ar mafarauta wanda
shine burin mahaifiyarsa Salimat. Hantaru yace
da kansa a cikin zuciyarsa, me zanyi na saka wa
da Salimat a rayuwa bisa shayar dani da tayi a
matsayin dan cikinta? Kuma ta rikeni amana ba
tare da tasan cewa ba dan cikinta bane ni.
221

TASKARNOVELS.COM.NG
Abinda zanyi shine ya wanke bakin cikin
zuri'arsu gabadaya wanda ya addabi zuciyarsu
tsawon shekara da shekaru.
Koda hantaru ya gama ayyana haka a cikin
zuciyarsa sai ya kara zaburar dokinsa yayi masa
kaimi ya kutsa cikin jaruman gasar nan yana
bangaje wasunsu, bisa mamaki sa sai yaga yana
matsawa gaba-gaba, sannu a hankali sai da riski
wadanda ke kan gaba wasu zakwakuran samari
jaruman gaske su uku, wadanda ya kasa
wucesu, Hantaru ya dage iya karfinsa yana kai
masu sara da suka da mangari, suma suna
mayar masa da martani, amman saboda nacinsu
sai ya kasa zubar da su a kasa, sai da suka yi
doguwar tafiya a haka har suka fara hango
barewar da aka saki tana ta tsula gudu ana so su
cimmata.
A karshe dai da hantaru da wadannan
zakwakuran samarin jarumai uku ragas akayi,
wato duk sun banke junansu sun fado kasa daga
kan dawakansu, dayansu bai samu nasarar
kamo barewar ba.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin Hantaru
kenan, ransa ya baci kuma gwiywarsa tayi sanyi
222

TASKARNOVELS.COM.NG
akan wannan gasa. Amman sai Shuraim ya
karfafeshi akan cewar ya kara kwazo nan gaba
akwai alamar cewa zai zamo zakara.
Haka dai aka cigaba da wannan gasa ta baiwa
kai horo dan tanadin ranar babbar gasa ta
ainahi, ya zamana cewa a kullum sau biyu ake
yin gasar safe da yamma, sai da ya rage saura
kwana daya jal ranar gasar ta ainahi ta zo, a
wannan rana ne Jarumi Hantaru ya samu
nasarar banke wadannan zaratan jaruman guda
uku ya zubar da su kasa, sannan ya cimma
barewar da keso a kamo ya cafketa.
Nan fa jama'ar zuri'ar makera suka cika da
tsananin farin ciki, domin sun san cewa yanzu
kam sun samu Gwarzon da zai karbo masu
kambun gasa daga hannun zuri'ar mafarauta.
A wannan rana kwana akayi suna walima,
kadede-kadede gami da raye-raye, babu wanda
yafi Shuraim da Salimat farin ciki a wannan
rana, domin kuwa basu san iyakar dukiyar da
suka raba wa jama'a ba.
Wannan shine abinda ya faru a bangaren
makera na birnin Darul Habur.
223

TASKARNOVELS.COM.NG

*******************

Acan bngaren zuri'ar mafarauta kuwa lokacin
da sarkin mafarauta Zaharu Ibn Dauwar ya isa
gida tare da dansa Rabbasu a sume, tare da
dukkanin jama'arsu, sai suka taru a cikn fadar
Zaharu aka shimfide Rabbasu a bisa wata
doguwar kujera, nan take Zaharu ya karanta
wasu dalasiman tsafi ya tofa masa, nan take
rabbasu yayi atishawa ya farfado, a dimauce ya
mike tsaye zumbur yana mai kokarin kai duka,
domin shi a zatonsa har yanzu yana fafatawa ne
da Hantaru. Bisa ga mamaki sai yaga
mahaufinsa tre da jama'arsu a tsaitsaye suna
kallonsa kawai. A sannan ne ya dubi inda yake
ya gane gida yake ba kasuwa ba.
Cikin tsananin fusata Rabbasu ya dubi
mahaifinsa ya ce ya abbana ina abokin fadana
yake ne? Yaya akayi nazo nan gida?
Koda jin wannan tambaya sai Zaharu ya bushe
da dariya sannan lokacin guda ya murtuke fuska
kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa,
224

TASKARNOVELS.COM.NG
nan take kuma kwallar takaici ta zubo masa ya
ce ya kai dana kayi sani cewa ba wani bane ya
zo ya raba fadanku da wannan bakon saurayin
ba face babban abokin adawata boka Sulbaini,
wannan bakon jarumi ya kasance babban
barazana ga zuri'armu gabadaya, domin yazo ne
domin ya rabamu da kanbun gasar gudun
tseren barewa, kuma shi gimbiya Larziyya ke
son ta aura.
Koda jin wannan batu sai Rabbasu ya kwarara
uban ihu, wanda ya firgita kowa dake wajen,
fuskarsa ta kama kakkarwa kamar zata zazzago
ta fado kasa, cikin tsananin fushi ya dubi Zaharu
ya ce ya kai abbana ka sani cewa yau shekaru
sittin kenan ina tanadin neman auren Gimbiya
Larziyya, ka sani cewa ina matukar kaunar
Larziyya irin kaunar da in har na rasata to
lashakka sai na rasa rayuwata, yaya kake
tsammanin cewa zan bari wani yazo ya
mallaketa.
Zaharu ya dafa kafadar Rabbasu ya ce ka
kwantar da hankalinka ya kai dana, kaima ka
sani cewa babu yadda za a yi ina raye a doron
kasa hakan ta faru, ina tabbatar maka da cewa
yanzu lokaci yayi da zan baka gabadaya
225

TASKARNOVELS.COM.NG
sirrinkan tsafina sabanin da dana baka rabi
kawai, ka sani cewa abinda yasa ban baka
sirrikan tsafina ba, shine kana da tsananin fushi
da bakar zuciya, idan ka mallaki sirrin tsafina
duka cewa zaka yi zaka yaki boka Sulbaini, duk
ranar daka yaki boka Sulbaini kuwa a ranar
wannan birni namu sai ya baje kowa ya hallaka.
A halin yanzu bani da wani zabi face na baka
sirrikan tsafinnawa tunda ni bani da ikon shiga
wannan gasa, domin kare martabar zuri'armu
da kuma mallakar gimbiya Larziyya.
Abu na biyu dole ne mu baka sabon horo akan
wannan gasa, domin ka samu karfi ninkin na da
da kake da shi, dan kada abokin gabarka ya
samu nasara akan ka, ka sani cewa da mutum
dubu uku ake wannan gasa ta tsere, to amma
daga yanzu kullum zaka rinka jarraba wannan
gasa da mutane dubu shida, lallai indai ka samu
nasara akan mutum dubu shida to ba makawa
sai ka samu nasara akan abokin gabarka, wato
wannan bakon jarumin daya zo.
Koda jin haka sai Rabbasu ya cika da farin ciki.
Daga wannan rana aka soma baiwa Rabbasu
horo da mutum dubu shida, kuma kullum sau
uku ake yin gasar, safe, yamma da dare.
226

TASKARNOVELS.COM.NG
Tun a ranar farko Rabbasu ya rinka banke
zaratan dakaru, duk inda ya ratsa ta cikinsu sai
dai kaga maza na zubewa kasa, wani lokacin ma
har dawakan nasu yake bankewa kasa, saboda
tsananin karfin Rabbasu sai da ya lashe gasar
nan.
Daga ranar farko da aka fara wannan gasar
zuwa ranar karshe kullum Rabbasu ne yake
lashe gasar, kuma ko dau daya ba a taba kaishi
kasa ba.
Tabbas Rabbasu ya cika sadaukin Sadaukai
domin yafi hantaru karfin damtse, a ranar
karshe ana gobe za a yi gasar ainihi ta neman
auren Gimbiya Larziyya boka Zaharu ya sanya
dukkanin sirrikan ttsafinsa a jikin Rabbasu. Nan
take Rabbasu yaji wani gagarumin karfi ya shige
shi, tamkar zai iya nada gammo a ka a dora
masa duniyar gabadayanta. Nan take ya cika da
farin ciki, ya ji a zuciyarshi cewa dole ne ko ta
halin kakama yaci wannan gasa da za'a yi.
Acan cikin gidan Shuraim kuwa har dare ya raba
amman boka Sulbaini bai zo ba kamar yadda
yayi alkawari, al'amari daya dugunzuma
hankalin Shuraim, Samilat da mahaifiyar
227

TASKARNOVELS.COM.NG
Samilat kenan, domin sun san cewa muddin
Hantaru bai samu taimako daga boka Sulbaini
ba, babu yadda za a yi ya ci wannan gasa akan
Rabbasu, saboda sanin cewa dole ne Zaharu
mahaifin rabbasu yayi masa gagarumin shiri
irin wanda bai taba yi masa ba. Haka dai aka
kwanta cikin ta tarrabi da jimami.
Al'amarin Sadauki Hantaru kuwa ko kadan baiji
wata damuwa ta shigeshi ba, saboda koda
yaushe yana da yakinin cewa indai yana cikin
hayyacinsa babu wani tsautsayi da zai taba
lafiyarsa. Hantaru na kwanciya sai bacci ya
dauke shi, tamkar babu wani gagarumin abu
dake gabansa a gobe, daf da ketowar alfijir ne
Hantaru ya farka daga bacci, kawai sai yaga
boka Sulbaini a zaune daf da shi idanunsa a rufe
yana jan wani abu. Abinda ya daure wa Hantaru
kai shine kofar dakin da tagar dakin a rufe suke
ruf, to wai shin ta ina Sulbaini ya shigo cikin
wannan dakin ba tare da ya sani ba, kuma ta ina
ya shigo din? Koda ya tuna cewa iki ne na tsafi
sai hankalinsa ya kwanta, hantaru ya yunkura
da nufin mikewa zaune, amman sai Sulbaini ya
nuna kirjinsa da tafin hannunsa, take Hantaru
ya ji an danne shi da wani irin karfi na
musamman wanda b zak iya dagowa ba. Bisa
228

TASKARNOVELS.COM.NG
dole ya koma ya kwanta, faruwar hakan ke da
wuya sai Sulbaini ya kammala wuridin tsafin da
yake yi, kuma yayi tofi akan kirjin Hantaru, har
a sannan Sulbaini bai bude idanunsa ba, koda ya
tofa sai Hantaru yaji wani irin radadi da zugi na
shigarsa, nan take gabadaya jikinsa ya kama
kakkarwa, sannan wata irin zufa mai yawa ta
rinka kwaranyowa daga jikinsa tana zubowa a
kasa tamkar ana kwarara ruwa a wajen.
Jim kadan sai zufar ta bace bat daga jikinsa,
wanda ta zube a kasa ma ta bace. Nan take
Hantaru yaji wani irin gagarumin karfi ya
shigeshi, irin wanda bai taba jin kamarsa ba a
rayuwarsa, domin ji yayi kamar shi kadai zai iya
tunkarar gabadaya dakarun duniya, yayi yaki da
su tsawon kwanaki arba'in ba tare da ya gaji ba.
A daidai wannan lokaci ne boka Sulbaini ya
bude idanunsa cikin murmushi yace bude
idanunka ya kai sadaukin Sadaukai.
Hantaru ya mike zaune daga kan gadon suka
fuskanci juna, boka Sulbaini yayi gyaran murya
ya ce Yanzu na gama nawa, na gama baka iyakar
taimakon da zan iya baka, ya kai sadaukin
Sadaukai ka yi sani cewa na baka dukkanin
229

TASKARNOVELS.COM.NG
sirrikan ttsafinsa, ni yanzu babu abinda zan iya
yi na tsafi, domin duk karfina ya koma jikinka,
kamar yadda na boka Zaharu ya koma jikin
dansa, idan har baka ci nasarar wannan gasa da
za'a yi ba mutuwa zan yi, haka ma idan Rabbasu
bai ci nasarar wannan gasa ba, boka Zaharu
mutuwa zai yi, mu haka ka'idar tsafinmu ta ke.
Ya kai Hantaru ka yi sani cewa dukkan burinmu
mu jama'ar makera a kanka ya ke, dan haka ya
zama dole ka zage damtse ta kowanne hali ka ci
wannan gasa.
Koda Hantaru yaji wannan batu sai hankalinsa
ya dugunzuma ya dubi boka Sulbaini cikin
tsananin damuwa ya ce Ya shugabana, sabida
me zaka salwantar da rayuwarka akan wannan
bukata, kayi sani cewa mahaifiyata na tsananin
kaunar ka, yau idan aka ce babu kai zata iya
shiga cikin wani hali, ina rokonka bisa darajar
zuri'arku da soyayyarka ga kakana Shuraim ka
cire wannan shiri na tsafi da ka bani, k barni da
tsagwaran karfin damtsena, ina mai tabbatar
maka da cewa t kowanne hali sai na lashe
wannan gasa.

230

TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'ad da Hantaru ya zo nan a jawabinsa, sai
kawai yaga hawaye ya zubo wa da boka Sulbaini
daga cikin idanunsa, abinda yayi matukar bashi
mamaki da tsoro kenan.
Boka Sulbaini yayi ajiyar zuciya sannan ya ce
yakai jikana ina so kasani cewa ni nasan abinda
kai baka sani ba, akwai wani sirri babba wanda
bazan iya fada maka shi a halin yanzu ba, kuma
shine dalilin da yasa na sallamar da rayuwata
dan samun nasararka, zaka iya sanin wannan
dalili amman sai bayan mutuwata idan ka shiga
dakin tsafina.
Yace alfarmar da nake nema a wajenka ita ce
kada ka kuskura ka fada wa mahaifiyarka
Salimat cewa na baka sirrikan tsafina duka,
domin idan ka yi haka zata iya shiga mugun hali
ta rasa sukuni daga yanzu har izuwa ranar da za
a kammala wannan gasa. Da wannan furuci
nake maka sallamar karshe idan da rabon mu
sake saduwa zamu sadu bayan ka lashe gasa.
Koda kammala wannan jawabi sai Hantaru ya ji
ya kamu da tsananin tausayin boka Sulbaini,
dan haka sai ya rungumeshi ya fashe da kuka,
kuma yana mai cewa da iznin abin dogaronka
231

TASKARNOVELS.COM.NG
sai mun sake saduwa, da yardar su su ummana
ba zasu zubar da hawaye ba.

MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part Q
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

Kafin Hantaru ya gama rufe bakinsa tuni boka
Sulbaini ya ce bat daga cikin dakin, nan fa
Hantaru ya nemeshi sama ko kasa ya rasa.
Kashegari kuwa tunda duku-dukun safiya
jama'ar birnin Darul Habur suka fara tafiya
wani daji da ake kira Furja'al Maut, daga cikin
birnin Darul Habur zuwa dajin tafiya ce ta rabin
sa'a kacal, al'amarin daga daure wa jama'ar
birnin kai shine shigowar baki daga kauyuka da
birane da dama dan kallon wannan gasa, kai
harma daga wasu nahiyoyi haka jama'a suka
232

TASKARNOVELS.COM.NG
yita zuwa birnin Darul Habur tun ma saura
kwana goma a fara wannan gasa. Al'amarin da
ya janyo cunkoso a cikin birnin kenan na fatake
dama yan kasuwa.
Nan fa kasuwa ta bude, bisa tarihin birnin ba'a
taba samun arki mai yawa a kasar ba irin na
wannan shekarar ba, kuma ba a taba ganin
yawan jama'a irin na wannan shekarar ba, sai
da takaicewa babu masaukai inda baki zasu
zauna, hakan yasa har a wajen gari kafa tantuna
ake yi, kai ko ruwa mutum yake saidawa a
wannan lokaci cikin kwana uku yake zama
attajiri. Ba komai bane duk ya haddasa wannan
al'amari ba face labari ya bazu cewa Sadauki
Rabbasu ya shiga wannan gasa, wanda labarin
jarumtakarsa ya bazu ko ina a nahiyar kuma an
samu labarin cewa an samu wani bakon jarumi
da ya iya fafatawa da shi har tsawon rabin sa'a b
tare da dayansu ya samu nasarar komai akan
dan uwnsu ba.
Sannu a hankali jama'a suka rinka turueuwa a
cikin dajin Furja'al Maut suna hawa saman
manyan Duwatsu da tsaunuka suna masu
tsayawa dan kallon wannan gagarumar gasa da
za a fara a yau din. Shidai wannan daji na
233

TASKARNOVELS.COM.NG
Furja'al Maut daji ne mai girma da fadin gaske,
kuma duwatsu dake ciki sun kasance masu
tsananin yawan gaske, wasu tsaunukan ma idan
mutum ya hau shi sai a hangoshi dan mitsitsi
tamkar dantsako.
Kafin gari ya waye dajin ya cika ya batse da
jama'a babu masaka tsinke, face wacce take a
tsakiya wadda aka barwa dakarun gasa.
Bayan jama'a sun shafe kusan sa'a uku a
tsaitsaye suna jira, sai ga dakarun gasa sun
tunkaro dajin daga can nesa, tawagar farko
mutum dubu daya da dari biyar ne, sunyi shigar
jajayen tufafi, dukkaninsu suna bisa fararen
dawakai abin gwanin ban sha'awa, sannan suna
rike da kulake na duka babu dayansu dake rike
da takobi ko wani makami na karfe. Wannan
zuga ita ce ta zuri'ar makera na birnin Darul
Habur. A cikinsu gabadaya babu mai kwarjini da
daukar hankali sama da Sadauki Hantaru, su
kansu gabadaya dakarun wato yan uwansa sun
sallama masa, kai da gani kasan cewa wannan
karon sun fito gasar ne da matukar karfin
gwiywa, kasancewar suna tare da shi, sai yi
masa kirari da jinjina suke yi.

234

TASKARNOVELS.COM.NG
Jim kadan da shigewar wannan tawaga sai
kuma ga tawaga ta biyu wanda suma sun
kasance su dubu daya da dari biyar, gaba
dayansu suna sanye da bakaken tufafi haye bisa
bakaken dawakai, babu wani mai haske a tare
da su, saboda tsananin kwarjinin wannan
tawaga sai da yan kallo suka razana, wasuma
buya suka kamayi, saboda gani suke kamar zasu
iya afka wa yan kallo a kowanne lokaci, suyi
masu tamore, saboda ko kadan babu alamar
tausayi ko digon imani a bisa fuskokinsu. A
tsakiyar wannan tafiya Sadauki Rabbasu ne bisa
wani jibgegen doki da yafi na sauran girma.
Rabbasu ya shafe dukkanin jikinsa da bakin
shuni, in banda jajayen idanunsa da ake gani
babu abinda mutum ke iya gani a fuskarsa, sai
faman huci da gurnani yake kamar tsohon
mayunwacin zaki.
Wani ayari daban na zuri'ar mafarauta na biye
da su a baya, sunata buga tambura da ganguna
kuma suna raira wakoki na jinjina da kirari ga
sadauki Rabbasu.
Duk mahalukin da yazo wannan daji na Furja'al
Maut sai da hantar cikinsa ta kada a lokacin da
235

TASKARNOVELS.COM.NG
Rabbasu ya kurma wani uban ihu, mai tsananin
razanarwa face jarumi Hantaru wanda ya saba
da kuruwar manyan aljanu da dodanni, shine
kawai bai razana ba.
Suma wannan tawaga ta biyi babu makamin
karfe a hannunsu sai kulake, domin yanayin
gasar kenan, ba a yarda a xo da makamin karfe
ba.
Bayan tawagar biyun ta cakude ne sai aka fara
kallon kallo gami da harar juna.
Wohoho! Yayin da manyan mazaje suka hada
ido kuwa sai da zuciyar kowa a wajen ta buga da
karfin gaske dan kada su kacame da azabben
fada su tashi hankalin duwatsu da bishiyu dake
wajen.
Rabbasu da Hantaru suka kura wa juna idanu ko
kiftawa basa yi, kowannensu fuskarsa ta kama
gyatsine kuma jikinsu ya kama tsuma ji suke
kamar su rufe juna da duka tun gabanin a fara
wannan gasar.
Wani akasi kuma da aka samu shine Rabbasu na
daga hannun hagu shi kuma Hantaru na daga
hannun dama, har ma wani lokacin idan aka yi
236

TASKARNOVELS.COM.NG
turmutsutsu kafadunsu na gogar na juna. Jim
kadan da cakudewar tawagar biyu sai alkalan
gasar suka shigo cikin tawagar suna masu binsu
daya bayan daya suka cajesu, aka tabbatar da
cewa babu dayansu daya boye makamin karfe a
jikinsa, ya zamana cewa in banda guraye da layu
babu komai a jikinsu, to kuma sai kulkin duka.
Gama hakan keda wuya sai alkalan gasar suka
fice daga cikin tawagar biyi su hau kan duwatsu
suka tsaitsaya kafin a busa kahon fara gasar.
A daidai wannan lokacin ne kuma Hantaru ya
hango gimbiya Larziyya a cikin taron yan mata
can saman wani tsauni, tana danye da jajayen
tufafi masu ratsin fari, wato dai tayi shiga irin
dakarun zuri'ar makera, al'amarin daya baiwa
kowa dake wajen mamaki kenan, aka shiga
zunde da surutu ana cewa Me yasa gimbiya
Larziyya zata yi irin wannan shiga, alhalin tana
matsayin yar sarki, ai bai kamata ta nuna
bangaren da take so ba daga cikin zuri'ar nan
guda biyu ba.
Duk da cewa kowa yasan cewa bata son Sadauki
Rabbasu, dan ta tsaneshi kamar yadda ta tsani
mutuwarta.
237

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Gimbiya Larziyya ta hada idanu da jarumi
Hantaru, sai ta cire amawalin data rufe bakinta
da shi ta yi masa murmushi. Koda Hantaru ya
maida mata da martanin murmushin sai ta daga
hannunta ta yi masa jinjina, sannan ta rufe
fuskarta kuma ta sake daure fuska tamau ta ki
yarda ta kalli fuskar Sadauki Rabbasu.
Wannan abu da gimbiya ta yi ba karamin bakin
ciki ta dasa wa Sadauki Rabbasu a cikin
zuciyarsa ba, nan take jikinsa ya kama
kakkarwa kuma zuyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone.
Acan gefe daya kuma sarki ne da yan
majalisarsa tsaitsaye bisa dawakai bisa wani
dogon tsauni sun zuba idanu kasa dan ganin
yadda wannan gasa zata kasance.
Dama musamman aka sassabe dogayen
bishiyoyi na dajin domin a samu cikakken
samun damar kallon gasar yadda ya kamata.
Nan take wani dogon mutum ya hau kan wani
dogon tsauni da babu kowa a kansa, koda ya
kafa kahon a bakinsa ya busa, sai karar sautin
kahon ta cika dajin gabadaya.
238

TASKARNOVELS.COM.NG
Aikuwa sai gaba daya dakarun gasa suka zaburi
dawakansu a
End Ads