tafiya ba, ba zai
buqaci abinci ko ruwa ba har kwana arba'ing.
3... Hulkas shine mamallakin hular qarfe mai
suna Lamsara. Ita lamsara ta kasance shu'umar
hula ce in dai mutum yana sanye da ita yana iya
ganin abin da ke gabansa, haka kuma duk irin
19
TASKARNOVELS.COM.NG
guguwar da akeyi da tsananin ruwan sama ba za
su kusanci inda yake ba.
Wannan kadan ne daga cikin sihirin wadannan
makamai na Mazanjiya. Akwai sauran sirrikan
wadanda babu wanda ya san da su face masu su.
Wato mazanjiya.
A halin yanzu tuni sarki dujalu ya baro kasar sa
tare da dakarun sa na yaqi ya nufi tekun bahar
sufiya don dauko takobin saiful lujara. Daga
birnin hawaruldin zuwa tekun bahar sufiya
tafiyar shekara uku bisa doki ko raqumi ba tare
da ya da zango ba."
ko da sarki dujalu zai yi anfani da qarfin sihiri
wajen yin wannan tafiya kuma koda akan aljanu
za su tafi dole su shafe sama da shekara guda
kafin su isa tsakiyar tekun bahar sufiya. Neman
takobin saiful lujara a cikin kogin kuwa dai_dai
yake da neman jaki mai qaho, wato dai mace ce
da ciki zata iya haihuwa lafiya kuma zata iya
rasa rayuwarta. A taqaice al'amari ne na sa'a da
rabo, amma dai sai babbar sa'a sannan za'a
dace. Idan har aka sami nasarar dauko takobin
saiful lujara to lallai sauran makaman biyu ba za
suyi wahalar samu ba sosai. Duk mutumin da ya
20
TASKARNOVELS.COM.NG
hada wadannan makamai a jikinsa shi kadai
tabbas ya cika GAGARABADAU kuma sai ya
mulki duniyar na n gaba dayanta. Ba wai
mutane kadai zai mulka ba hatta aljanu, dabbobi
da dukkanin halittu sai ya iya sarrafa su har
tsuntsaye kuma babu halittar da ba zai iya yin
magana da ita ba, kuma ya bata umarni ta bi
dole.
Ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa ba mu
ga ta zama ba, dole ne mu mike tsaye mu zage
damtse don ganin mun riga sarki dujalu samo
wadannan makamai guda uku. Idan kuwa
mukayi sakaki ya riga mu samunsu to muna ji
muna gani zai zo ya baje qasarmu ya kashe
mazajen mu sannan ya gaje matan mu da
'ya'yan mu da dukiyoyin mu.
Ya zama wajibi mu aika da wannan sako ga
sauran kasashen da ke karkashin wannan
nahiya tamu domin mu sanar da su halin da ake
ciki kuma mu nemi gudunmawar su bisa
wannan gagarumar tafiya".
Sa'adda sarki maharaz yazo nan a zancen sa sai
dakin yayi tsit tamkar babu kowa a cikin sa.
21
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take dakin bautar ya watse jama'a suka tafi
suna tattauna wannan lamari a cikin firgici da
matukar damuwa. A wannan rana dai mutane
ba su da hirar da tafi ba2n shirin sarki dujalu.
Nan da nan labarin al'amarin ya fara bazuwa
sauran garuruwa birane da qauyuka da kuma
sauran qasashen maqofta. Duk jama'ar da ta ji
wannan labari sa ta rude ta shiga shirye shiryen
kare kai da bayar da dakarun gudunmawa
izuwa birnin darul mahabur.
Tun a wannan rana ne sarki maharaz ya aiki
wasu zakwakuran hadiman sa na jinsin aljanu
suka kai wasika zuwa dukkanin sarakunan da
ke muli a nahiyar. A cikin sa'o'i kadan labarin ya
riski ko in da ina sarakai suka firgice ainun
kuma suka miqe tsaye wajen fara shirye shiryen
tafiya.
Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki
maharaz bayan ya sanar da jama'ar sa jawabin
gunkin darbuza wanda aka saba yi a duk
qarshen shekara a lokacin bauta.
☼☼☼ ☼☼☼ ☼
22
TASKARNOVELS.COM.NG
Al'amarin imnal da mahafin sa sarkin yaki hibru
kuwa, tun da suka baro dakin bauta suka nufi
hanyar gida sai duk suka yi shiru suna tunani a
cikin zukatan su ba tare da sun ce kala ba.
Shi dai sarkin yaki hibru ba komai ya ke tunani
ba face kiyasta rayukan da za'a yi asara yayin
wannan tafiyar gami da irin dukiyar da za'a
6arnatar. Haka kuma yana jimamin tafiyar da
za.ayi abar mata yara da tsofaffi kawai a birnin
ba tare da an bar musu dakarun tsaro ba wanda
hakan na iya janyo komai ya faru, duk da cewar
sadauki hibru ya san cewa bashi da mata, kuma
bashi da sauran dangi a fadin kasar gaba daya
sai yaji takaici da baqin ciki suka mamaye
zuciyar sa saboda ya san cewa wannan
gagarumin yaki da za'a fita ba karamar masiba
bace da koma bayan ci gaban nahiyar gaba daya
domin zai janyo karyewar tattalin arziqi kuma
masoya za su rasa masoyan su, iyaye za su rasa
'ya'yansu 'yan uwa zasu rasa 'yan uwansu.
Koda hibru yazo nan a zancen sa sai idanunsa
suka ciko da qwalla saboda tausayin halin da
jama.a za su shiga.
23
TASKARNOVELS.COM.NG
Shi kuwa sadauki imnal ko kadan tunaninsa ba
irin na mahaifin sa bane. Abin da yafara fado
masa a rai shine wai shin ya za.ayi ya mallaki
wadannan kayan yaki guda 3 na MAZAN JIYA?
Koda ya gama aiyana hakan a zuciyarsa sai ya
yiwa kansa dariya ya ce Amma fa bani da
hankali akan wane dalili ne ma zan nemi abin da
ya gagari manyan sarakunan duniya masu
taqama da komai.
Gama aiyana hakan ke da wuya sai gimbiya
mulaifa ta fado masa a rai ya ce to wai shin
yanzu za'ayi tafiyar nan tare da gimbiya mulaifa
kuwa? Lallai zan kasance mai tsananin baqin
ciki idan ba a tafi da ita ba. Idan kuwa aka tafi da
ita sai na fi kowa farin ciki a fadin duniya.
Haka dai imnal yayi ta saqe saqe a zuciyar sa
har suka isa qofar gida. Dama imnal ne akan
gaba har ya sanya qafar sa a cikin qofar gidan
sai ya dakata ya waigo ya dubi hibru fuskar sa
cikda alamun damuwa koda ganin haka sai
hibru ya tsaya cak ya kura masa idanu sannan
ya ce mene ne ya faru?
Imnal ya ce ka gafarceni ya abba na nayi babbar
mantawa dazu a dakin bauta sarki ya ce min na
24
TASKARNOVELS.COM.NG
fada maka muzo ni da kai yana neman mu a fada
da yammacin gobe.
Ko da jin wannan batu sai hankalin hibru ya
tashi yai shiru ya sunkui da kansa qas .daga can
kuma sai ya dubi imnal ya ce ka gaya min
gaskiya shin kayi wani laifi dazu a dakin
bauta???
Jin wannan tambaya sai imnal ya sunkui da
kanasa alamun rashin gaskiya ya ce qwarai
kuwa nayi laifi. Domin na tashi daga inda nake
zaune naje wajen gimbiya Mulaifa....
Koda jin haka sai hibru ya dafe kai yana mai
ajiyar numfashi, sa'annan ya ce tabbas na san
cewa ruwa baya tsami banza. Ni dai a sani na
sarki bai ta6a neman shawarata ba sai dai kawai
a gaya min cewa za'a fita domin naya shiri.
Tabbas ka aikata babban laifi don haka dole ne
ka fuskanci mai tsanani saboda wannan laifi don
haka ni babu ruwana, tsuntsun da yaja ruwa shi
yake duka. Koda jin wannan magana sai imnal
yayi murmushi ya ce indai akana soyaiya ta ga
gimbiya Mulaifa ne a shirye na ke don na kar6i
horo koda kuwa na mutuwa ne, cikin tsananin
takaici hibri ya dube shi a fusace, kawai sai ya
25
TASKARNOVELS.COM.NG
wuce zuwa turakar sa ya bar imnal tsaye a kofar
gida.
Da yammaci kuwa fadar sarki maharaz ta cika
makil da jama.a masu amsa gaiyatar tafiya yaki,
duk da cewa adadin jama.ar da suka taru bai kai
daya bisa goman masu tafiya yaqin ba sai da
fadar ta cika ta batse sai da ya zamana duk inda
ka duba kawunan bil'adama ne rututu.
Tun a farkon yammacin ne sarkin yaqi tare da
dansa suka amsa kiran sarki suka hallara a
fadar, shi kuwa sarki maharaz bai fito ba sai da
kowa ya gama zuwa. Da fitowar sarki kowa ya
miqe tsaye don girmamawa a gare shi har sai da
ya zauna sannan kowa ya zauna.
Sarki ya dubi dubun mutane da suka amsa kiran
sa sai ya cika da farin ciki, da ya duba 6angaren
da su imnal suke tsaye sai ya murtuke fuska ya
6ata rai.
Bayan fadawa sun zube sun kwashi gaisuwa ya
rage sauran sarkin yaki hibru da dansa Imnal,
kawai sarki yayi nuni da hannun sa izuwa ga
wani badakare yana maiyi masa nuni da yazo da
imnal gabansa, nan take badakare ya tasa keyar
sa yazo da imnal gaban sarki.
26
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokaci gimbiya Mulaifa na zaune daf
da sarki. Koda taga an tasa keyar Imnal anzo
dashi gaban sarki sai hankalinta ya tashi domin
ta tabbatar da cewa lallai hukunci za'ayi masa.
Gaba daya jama'ar dake fadar kuwa sai suka
cika da mamaki suka zuba ido don su ga irin
hukuncin da za'a yiwa Imnal yaron da ba.a ta6a
ganin yayi wani laifa ba. A kullum shi da
mahaifin sa ba su da wani abin da ya wuce
biyaiya ga sarki, Sarki maharaz ya mike tsaye
daga kan karagar mulkin sa ya dubi jama'a ya ce
ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa
wannan yaro Imnal d'a ga sarkin yakin mu
hibru ya kasance mai ladabi da biyayya a
garemu kamar yadda mahaifin sa ya kasance,
kuma bamu ta6a kamashi da wani laifi ba,
amma sai gashi a jiya ya aikata wani babban laifi
wanda bamu ta6a zaton zai aikata shi ba. Laifin
kuwa shine a jiya sa'adda kowa ya sunkui da
kansa kas a dakin bauta sai shi ya miqe yaje
inda nake zaune ya zauna kusa damu. Wannan
shine karo na farko da wani mahaluki ya karya
dokar maigirma darbuza a cikin kasar nan, don
haka dole ne ayi masa hukunci gwargwadon
laifin sa.
27
TASKARNOVELS.COM.NG
Mai girma darbuza ya ce a daure imnal a sama
jikin katako kuma a cikin rana tun daga
hudowar ta har zuwa faduwar ta ba tare da an
bashi ruwa koda makwarwa daya ba har tsawon
kwana uku. Idan kuma ya sake aikata irin
wannan laifi hukuncinsa zai zamo kisa ne.
Koda sarki maharaz ya zo nan a zancensa sai
idanun Mulaifa suka ciko da qwalla suka fara
zubar da hawaye. Hibru da imnal kuwa ko a
jikin su maimakon ma hankalinsu ya tashi sai
suka kama murmushi domin sun san cewa
wannan horo ba komai bane akan irin horon da
hibru ya bashi tun yana dan karami. Sarki
Maharaz yaci gaba da bayani .. Sai gobe za'a fara
wannan horo ga Imnal, kuma washe garin ranar
da aka gama horon ne zamu dunguma gaba
dayan mu mu tafi izuwa gagarumin yaki da ke
gaban mu. Domin mu riga sarki dujalu dauko
takobin saiful lujara. Ina mai kira ga dukkanin
jama'ar mu da a ci gaba da shirye-shirye babu
sassauci domin tuni dakarun gudunmawa sunzo
da yawan su mu kawai suke jira a tafi...
Ko da gama wannan jawabi sai sarki Maharaz da
Mulaifa suka shiga gida sannan jama'a kowa ya
kama gabansa.
28
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da imnal da hibru suka isa gida sai
hibru ya aika imnal kasuwa don ya sayo masa
zugazugi na wutar Qira sabo da nasa ya lalace.
Imnal ya hau doki ya tafi kasuwa tun kafin ya isa
kasuwar sai yaga duk inda ya ratsa jama'a na
kallonsa suna magana akan hukuncin da sarki
zai yimasa.
Kafin ya isa kasuwar ne ya hadu da wadansu
kuyangin gidan sarki suna tafe suna hira. Koda
suka ganshi sai suka sha gabansa suka shiga yi
masa kirari suna kodashi. Al'amarin da ya
matukar bashi mamaki kenan ya dubesu ya ce
ya ku wadannan kuyangi ku kuwa mai yasa
kuke kodani haka alhali kuwa banyi wani abin
al'ajabi ba? Suka ce ai kuwa kai ne kayi babban
abin al'ajabi tunda har ka siye zuciyar gimbiya
Mulaifa a halin bata ta6a nuna tana son wani da
namiji ba face kai. A yanzu haka tana can gida
tana kuka sabo da jin za'ayi maka horo na
kwana uku bisa laifin da ka aikata.
Babu irin rokon da gimbiya ba tayi wa sarki ba
akan ya janye wannan horo amma yaki, saboda
bakin ciki ne shi yasa ta kasa ci ta kasa sha
kuma ga dukkan alamu haka zata kwana a
wannan hali yau.
29
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda kuyanga ta zo nan a zancenta sai
hankalin Imnal ya dugunzuma ainun ya rasa
abin da ke masa dadi a duniya, sai kawai ya dubi
kuyangin ya ce da su idan kun koma gida ku
shaidawa gimbiya cewa wanda take kuka
dominsa yana bakin ciki bisa zubar hawayenta
da kuma rashin ci da shanta.. Lallai shi ma ba zai
ci kuma ba zai sha ba a yau har sai yazo ya ganta
ta kowane hali...
Jin wannan batu sai kuyangin suka zazzaro
idanu cikin tsananin mamaki wacce tayi magana
dashi tace taya zaka iya shiga gidan sarauta har
ka ganta ahalin akwai tsananin doka da tsaro?
Imnal yai murmushi ya ce ko mutuwa ke tsaro a
yau sai na ga gimbiya Mulaifa kuje ku gaya mata
cewa komai dare ina nan tafe a yau. Koda gama
fadin haka sai imnal ya kada linzamin dokin sa
ya wuce izuwa kasuwa ya siyo zugazugin ya
koma gida sannan ya ci gaba da taya hibru kera
wasu sababbin makaman yaki tamkar babu
wani abu da ke sosa zuciyarsa.
Nima zan so ganin yadda Jarumi Imnal zai iya
ratsawa ta cikin wannan tsaro na gidan sarautar
30
TASKARNOVELS.COM.NG
birnin darul mahabur har yaje ya sadu da
Gimbiya Mulaifa, masu karatu ko zan samu dan
rakiya kuwa?
Da fatan kuna hutun karshen mako lafiya,
sannan duk wanda yake son complete na
Littattafan yaki harma da na soyayya zai iya
tuntubata ta wannan number 08138873799
whatsapp kadai pls banda kira
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part C
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Da tsakar dare lokacin da gari yayi tsit ba kajin
komai face kukan gyare. Da daidaikun sautin
31
TASKARNOVELS.COM.NG
tsuntsaye, imnal ya miqe tsaye dama ko runtse
ido bai yi ba bare yayi barci. Cikin sanda ya debo
wadansu bakaken kaya ya sanya sannan ya rufe
fuskar sa da bakin rawani, takalmin da ya sa
kuwa na fata ne kasansa gashi ne yadda duk
abin da ya taka ba za.aji sautin komai ba.
Ko allura bai dauka ba a matsayin makami, ya
bude kofar dakin sa ya fita ba tare da hibru ya ji
motsin sa ba, maimakon ya bude kofar gidan sai
kawai ya daka tsalle kamar dan biri ya dira akan
katangar gidan, duk da cewa tsawon katangar
ya kai kamu sittin. Kafin ya tafi ya tanadi kayam
da ya cire daga jikinsa a cikin 'yar qaramar jaka
kuma shifidar da ya kwanta sai yatara
tsummokarara yai musu siffar mutum ya
lullu6esu tamkar mutum ne a kwance.
Dama tuni ya daure dokinsa a kofar gida bai
shiga da shi ciki ba saboda dama yasan cewa zai
yi amfani da shi yayin da dare ya raba. Koda
imnal ya dirgo daka kasa daga kan katangar sai
yaje ya kwance dokin ya haye kansa ya
zabureshi ya nufi hanyar da zata kai shi gidan
sarki tuni ya aiyana a ransa ba zai wuce rabin
sa.a ba zaije ya dawo.
32
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin matsanancin gudu imnal ya ci gaba da
tunkarar gidan sarautar sai ya sauya hanya
domin ya 6ullo ta bayan katangar gidan, cikin
kakanin lokaci ya hango katangar gidan da sauri
ya sauko daga kan dokinsa ya daureshi a cikin
bishiyoyi masu duhuwa sannan ya 6uya a cikin
duhuwar, ya kurawa katangar idanu yana kallon
dakaru kuma yana nazarin hanyar da zai bi ya
shiga gidan ba tare da wani ya ganshi ba.
Al'amarin da ya qara tayar da hankalinsa kenan
domin bai ga ta yadda hakan zata iya faruwa ba.
Sai imnal ya dan jima yana nazari sannan
dabara ta fado masa.
Nan take ya hau kan bishiya ya karyo itatuwa
sannan ya sauko ya daddaure itatuwan da
6awon bishiya yayi siffar mutum mutumi ya
dora shi kan dokin sa ya kora shi, dokin ya fita
da gudu ya wuce ta gaban wadannan dakaru
dake tsaitsaye a bayan katangar.
Ko da suka ga mutum a sukwane ya wuce ta
gaban su sai suka bi shi gaba daya da gudu
domin su kure masa gudu, damar da imnal ya
samu kenan ya fito da gudu daga cikin duhuwar
da ya 6uya.. Ko da ya rage saura taku uku ya
33
TASKARNOVELS.COM.NG
riski katangar sai ya daga tsalle yai sama tamkar
tsuntsu ya kama karshen katangar, yana kama
katangar sai ya ji ta da tsananin santsi har
hannun sa ya su6uce zai fado sai ya sake jefa
daya hannun nasa ya kamo katangar ya dafa
kafafun sa sama ya dirga akan katangar, koda ya
leqa qasan katangar izuwa cikin gidan sai ya ga
akwai tsawo sosai in yace zai fada zai iya
karyewa.
A dai dai wannan lokacin ne ya jiyo dawowar
dakarun da suka bi dokin sa sun dawo da gudun
tsiya. Nan fa zuciyar imnal ta buga da karfi
domin ya san cewa babu mamaki sun bi dokin
ba su ga kowa a kan sa ba sai itatuwa, sai baban
su ya ce lallai ma ko waye mai dokin nan ya
raina mana wayo, sai ya daka ma sauran
dakarun tsawa ya ce kowa ya koma malafar sa
ya ci gaba da aiki don akwai alamar zuwan baki
gidan nan.
Imnal ya ringa bin katangar har ya hango wani
tafki a jikin katangar daga cikin gidan sai yayi
sauri zuwa wajen keda wuya sai yaga bakin
tafkin 12dakaru ne suke kaiwa da komowa,
amma sai yayi ta maza ya daka wawan tsalle sai
ya fada cikin tafkin nan ji kake Zundum..
34
TASKARNOVELS.COM.NG
Al'amarin da ya juyo da hankalin kwamandan
dakarun nan sai ya umarce su da su shiga cikin
tafkin su lalubo abin da ya fada su fito da shi.
Nan take suka bi umarninsa suka shiga tafkin
nan.. Koda imnal ya ji dakarun nan sun shigo
cikin ruwan, cikin zafin nama ya samu guda
daga cikin dakarun nan ya suburbudeshi ya
bishi da mazga, nan take ya suma sai ya cire
kayan jikin sa ya sanya masa shi kuma ya sanya
nasa, sakamakon dakarun duk kayan su iri daya
ne. Can sai gaba daya suka yo sama su shaida
ma sugaban ba su ga kowa ba, sai ya ce kowa ya
koma ma6uyar sa imnal ne na karshe ya fito
daga cikin tafkin ya ruga izuwa cikin wani
sashen gidan sarautar. A lokacin da imnal ya fito
daga ruwan ne ya ruga akayi akasi shugaban
dakarun ya waigo kawai sai ya hango imnal ya
ganshi dan karami kamar wada. Al'amarin da ya
ba shi mamaki kenan domin ya san cewa duk
cikin
yaran sa babu gajere ko wada. To ya ya akayi
aka samu wannan? .
A gigice shugaban dakarun ya ruga izuwa bakin
tafkin kawai sai yaga nasa badakaren a saman
35
TASKARNOVELS.COM.NG
ruwa a sume.Shugaban dakarun yayi sauri ya
kwala wa yaransa kira suka firfito daga malafar
su a guje suka taru a gaban tafkin. Ya dubesu
yace lallai muna da baqo a cikin gidan nan ku
bazama neman sa.
Nan take dakarun suka bazu izuwa kowanne
sashe na gidan sunan dube dube.
Lokacin da imnal ya ruga cikin gidan sarautar
yana la6e la6e sai ya rasa hanyar da ya kamata
ya bi saboda bai san 6angaren turakar gimbiya
mulaifa ba. Kawai sai ya bi kan wata
matattakalar bene da gudu. Da zuwa ya ga
dakaru za su gan shi sai ya nemi wuri ya 6uya. A
haka ne yayi ta wuce dakuna barkatar yane leke
leke ta cikin tagoginsu. Wani lokacin sai kaga
saura kiris a ganshi sai kuma ya duka kasa ko ya
shige cikin wani lokon ya 6uya.
Yana cikin haka ne ya hango wani daki kofar sa
a bude kuma fitila a kunne. Koda ya leqa tagar
dakin sai ya hango kuyangin nan guda biyu a
zaune cikin tararrabi idanun su a bushe babu
alamar sunyi barci ko suna jin sa, cikin zafin
nama imnal ya fada dakin ya rufo kofa. Koda
kuyangin nan biyu suka ganshi sai sukayi sauri
36
TASKARNOVELS.COM.NG
su kashe fitilar dakin, cikin rada daya daga cikin
su ta matso dab da shi ta ce hakika ka cika mai
sa.a yaya akayi ka shigo cikin gidan nan ka
tsallake duk tsaron waje da na ciki?
Imnal yayi ajiyar zuciya ya ce ni dai yanzu bani
da lokacin amsa tambaya ,abin da nakeso da ku
kawai kuyi mini jagora izuwa inda turakar
gimbiya take.
Cikin hadin baki suka ce"ta6dijan ka rufa mana
asiri indai ba so kake a hallakamu ba shin ba ka
jin guje gujen dakarun tsaro ne? Nan din nan ma
da kake ciki hadari ne ga rayuwar mu idan aka
shigo aka ganka. Abin da zamu iya yi maka
kawai shine mu baka zanen taswirar gidan nan
mai dauke da nunin inda