kaga
yadda nayi da irin kambun nan na hannunka ko
dan haka wannan kambun darajar su daya da
takarda banza a wajena amma idan baka yadda
ba zakaga zahiri a yanzu, kafin na bude baki
110
TASKARNOVELS.COM.NG
nace wani abu tuni sarki dumbazu ya dubi
waddan nan zakakuran aljanu nasa yace ku afka
musu naga iyakar jarumtakar su, nan take
aljanun nan sukayi mana rubdugu nan fa
aljanun nan suka haumu da sara da suka
maharaz ya tare su da karfin sihirinsa yana kare
harin su shima aljani mara'il labarus niko da
karfin damtsena na taresu amma sai akayi min
kwab daya na zube a kasa sumamme ko dakika
arba'in ba'ayi ba aljanun sarki dumbazu sukayi
fatafata da jikin aljani mara'il labaru, aljani
mara'il labarus ya fadi kasa magashiyam ko ina
a jikinsa yazamo kofar fitar da jini kawai
maharaz ne yadan tabuka wani abu domin
yasamu dakika kusan dari uku da tamanin yana
fafatawa da aljanun nan sannan suka karya
karfin sihirin sa sukayi masa sara tamanin ya
baje a kasa ko shurawa bayayi.
Lokacin dana farfado idanuna suka bude saina
tsinci kaina a wata fadar a daure a jikin dirkar
gini wata irin sarkar tsafice ta daureni koyaya
na motsa sai naji sarkar ta kara matseni bisa
dole na hakura na daina motsi bisa mamaki sai
naga abokina maharaz a daure kusa dani yana
numfashi sama sama kaida gani kasan cewa
akan gangarar mutuwa yake, raunukan jikinsa
111
TASKARNOVELS.COM.NG
guda tamanin na digar da jini shiko aljani
mara'il labarus babu shima a wajen alamarin
daya tabbatar min da cewa aljani mara'il
labarus ya mutu kenan, bazato ba tsammani sai
naga sarki dumbazu ya riko hannun gimbiya
sahira yar sarky hubru sun tafo gareni sunata
hira da dariya cikin nishadi nan fa na cika da
tsananin mamaki nace a zuciyata saboda me
sahira zata saki jiki da babban makiyin ubanta
wadda a halin yanzu ya rabata da ubanta kuma
yazamo sanadin ajalin sa sarki dumbazu yakai
gimbiya sahira izuwa kan wata kujera ta
alfarma ya zaunar da ita sannan ya tafo gareni
saida yazo dab dani yadda muna iya jin
numfashin juna sannan yace dani ga masoyiyar
ka can tazamo tawa a yau zan sadaku da ita
sannan na cika alkawari na wato na kasheta a
gaban idanun ka tunda mahaifinta ya saba
ka'ida ta bai baku kansa kun kawomun ba, bisa
mamaki sarki dumbazu yaga na dubeshi nayi
murmushi sannan nace matukar bil'adama na
numfashi a doron kasa ako yaushe to baya
yanke kauna da kubuta daga kowani irin bala'i,
ya kai wannan azzalumin sarki maci amana kayi
sani cewa lallai karshen lalacewa kuma har
abada burinka bazai cika ba idan har amana da
112
TASKARNOVELS.COM.NG
soyayya sun kasance ababen gaskiya lallai
bazaka samu nasara akan gimbiya sahira ba.
Kodajin wannan batu sai sarki dumbazu ya
kyalkyale da dariyar mugunta yace yanzu kai a
tunanin ka har akwai wani tsautsayi dazai sa
nakasa samun nasaran abinda nasa a gaba duk
duniya fa babu sadauki mai karfin damtse na
babu matsafi mai karfin sihiri na wanene ya isa
yaja dani nan take dumbazu ya shiga yiwa kansa
kirari yana ihu da kururuwa a gabana yana cikin
yin hakan ne na lura da wani guru dake kugunsa
wadda ke dauke da layun tsafi akalla guda dubu,
alkyabbar dake jikin sane ta rufe gurun amma
saboda yana juyi da daga hannaye a gaban idona
sai idanuna suka hango wannan gurun, cikin
shammaci da zafin nama na sunkuya na kaiwa
gurun nan chafka da bakina aiko sai nayi sa'a na
chafke laya guda da hakorana na gatsa layar ta
fashe take gurun nan ya bace bat itama sarkar
tsafin da aka daure mu ta bace bat itama.
Cikin zafin nama na zare takobina, haka kuma
sai aba daya dakarun aljanun nan sarku
Dumbazu sai naga suna narkewa kamar ana
narka man shanu a kasko, kafin kiftawar ido
duk sun zama ruwa a kasa. Su kuwa fadawan
113
TASKARNOVELS.COM.NG
sarki Dumbazu sai duk suka firgice suka
mimmike tsaye jiki na kyarma. Sarki Dumbazu
ya tsaya kyam a waje daya ko motsi bai yi ba.
Kawai sai ya suddar da kansa kasa yana mai
zubar da hawaye, ni dai har wannan lokacin ina
rike da takobina banyi yunkurin yin komai ba,
daga can sai Sarki Dumbazu ya dago da kai ya
dubeni cikin tsananin fushi fuskar nan tasa a
murtuke, a wannan lokacin ne naga gimbiya
Sahira ta mike tsaye zumbur tana kalle kalle a
cikin fadar kuma tana kallon jikinta, ga dukkan
alamu ta dawo cikin hayyacinta na ce a cikin
zuciyata. Wato a da an juyar mata da tunaninta
ta manta da kanta da kuma komai nata.
Sarki Dumbazu ya kura mata idanu har wannan
lokacin hawaye bai daina zub daga cikin
idanunsa ba, kawai sai ya bude baki da kyar ya
ce "Ya kai yaro hakika ka cuceni, ka ruguza Mani
tsafin dana kwashe sjekaru da dama ina shirya
shi, yanzu bani da suran sirrin tsafi a tare da ni,
lallai sai na yi maka kisan gilla irin wanda ba'a
taba yi ma wani a wannan duniyar ba, kayi sani
cewa ko bani da sirrin tsafi ai in da na karfin
damtse wanda babu kmaarsa a kaf nahiyar nan,
dan haka maza bisa kanka yi kokari ka cice
rayuwarka na gani. Cikin wani irin azababben
114
TASKARNOVELS.COM.NG
zafin nama sarki Dumbazu ya zare takobinsa,
takubbanma guda biyu ne ya kawo mani wasu
tagwayen mugayen sara, duk da nayi sauri na
kauce amman sai da takubban nan suka zarge
rigar dake jikina, kuma suk yi mani dogon yanka
akan kirjina har jini yana tsartuwa. Kawai sai na
tafi da baya taga-taga zan fadi kasa ana layi.
Koda Dumbazu yaga ya samu wannan
gagarumar nasara sai ya sake dako tsalle domin
ya dura a kaina da nufin ya gididdiba sassan
jikina, amman sai na yunkura cikin karfin hali
da matukar juriya na yi tsalle can gefe guda
yayinda takubban nasa suka sari wata kujera
take ta ragargaje.
Nan fa muka ci gaba da azababben yaki yayi ta
kokarin ya gididdibani ni kuma na himmatu ina
mai kare hare-harensa, ina zuluyewa gami da
kaucewa amman ko kadan na saka mayar da
martani ko da sau daya ne kuwa. Domin zafin
namansa da karfin saransa sun wuce misalin ta
yadda bazan iya taresu ba har na mayar masa
da martani.
Sai da muka shafe sa'a tara muna wannan bakin
Artabu Dumbazu ya kasa samun nasara a kain
115
TASKARNOVELS.COM.NG
ni ma na kasa maida mashi da martani koda sau
daya ne kuwa, hakika duk wanda ya fika
jarumta to fa ya fika har abada, domin baka isa
ka kamoshi ba.
Koda sa'a tara ta cika muna wannan gumurzu
sai gajiya ta riskeni har ya zamana cewa da kyar
nake iya daga takobina na kare saran da
Dumbazu yake kawo mani, shikuwa ko kadan
bai gajiba domin kmar ma a sannan ne ya fara
gumurzun. Yayi da yaga na fara sarewa sai ya
cika da murna ya ci gaba da kawo mani hari a
sannu yana murmushin mugunta, sai da ya kaini
jikin bango ya tareni sannan ya buge takobina ta
fadi kasa sannan ya labta mani wawan sara a
cinya, ban san sa'ar da na kwarara uban ihu ba
tare da durkushewa a kasa ba cinyata na zubar
da jini.
Dumbazu ya sake dankara mani wani saran a
dayar cinyar tawa na zube kasa wanwar a
matukar galabaice nan fa idanuna suka fara gani
dishi-dishi. Dumbazu ya sake dag takobinsa da
nufin ya fille mani kai, amman kawai sai naga
hannun nashi ya sandare ya kasa labta mani
saran, da kyar da sidin goshi na juya baya kawai
sai naga wuka ta nutse a tsakiyar gdon bayansa
116
TASKARNOVELS.COM.NG
jini na burbulowa ta tsakiyar girjinsa, tsaye a
gaban Dumbazu gimbiya Sahira ce jikinta na
karkarwa, a sannna ne na gane cewa ita ce tayi
ta maza ta rugo ta caka wa Dumbazu uka a
gadon bayansa. Nan take Dumbazu ya sullae
kasa matacce ko shurawa bai yi ba, a sannan ne
nima idanuna suka rufe na sume a wajen.
Lokacin dana farfaɗo sai nayi arba da gimbiya
Sahira tsugunne a gabana ta rusar kuka,
raunikan dake jikin cinyoyina an saka masu
magani, a gefe daya kusa da ni kuma Maharaz
ne a kwance har wannan lokaci yana numfashi
da yar duk da cewa an sa masa magank a jikin
raunikan nasa.
Koda na daga kina na dubi gabas da yamma,
kudu da arewa sai naga ashe gaba daya
mutanen birnin Karlus ne suka rufemu sun
tsura mana idanu suna kallonmu kawai, a gefe
daya kuma fadawan Sarki Dumbazu ne a
tsaitsaye sunyi tsuru-tsuru kamar ace kyet su
fice da gudu. Ashe duk mamakinmu suke yi
yadda akayi har muka iya ffaatawa da sarkinsu,
har ma kuma muka samu nasarar hallaka shi.
117
TASKARNOVELS.COM.NG
Saida muka yi kwana arba'in muna jiyyar
raunikan mu a birnin Karlus ni da Maharaz
sannan muka warware, amman duk da haka
bamu warke sumul ba, sai a sannan
hankulanmu suka dawo jikinmu har na samu
damar baiwa gimbiya Sahira llabarin dukkan
abinda ya faru tsaninmu da mahaifinta gami da
wasiyar da ya bamu mu shaida mata.
Koda gimbiya Sahira ta gama jin bayanina sai ta
fashe da matsanancin kuka kuma ta rungumeni
tana mai ci gana da kuka. Da kyar na lallasheta
daga can sai ta dubeni ta ce da ni tana so tayi
wata magana ta sirri da Maharaz.
Cikin matukar mamaki na dubeta nace da ita
"Ke kuwa wace irin magana ce wannan da zaki
yi da abokina wacce bakya so na ji?
Koda taji wannan tambaya ai hawaye ya zubo
mata ta ce ka yi hakuri ya kai mijina na gobe,
wannan magana da zanyi da maharaz sakone
daga mahaifina zuwa gareshi, kuma ya
gargadeni da cewa komai rintsi da tsanani kada
na kuskura na sanar d kai.
Koda gama fadin haka sai gimbiya Sahira ta tafi
wajen maharaz tayi masa rada a kunnensa,
118
TASKARNOVELS.COM.NG
gabadaya jama'ar dake wajen babu wanda yaji
abinda ta ce masa, faruwar hakan keda wuya sai
kawai muka ga Aljani Mara'il Labarus ya sakko
daga sama tare da tsirga a gabanmu, al'amarin
da yayi matukar bamu mamaki kenan domin mu
a zatonmu ya dade da mutuwa, hakan yasa ko
neman inda gawarsa take ba muyi ba.
Yayin da Aljani mara'il labarus yaga muna
mamaki da ganinsa a raye sai ya bmau labarin
cewar ai dama dogon suma yayi, lokacin daya
farfado sai yaga babu kowa a wannan fada ta
farko da muka fara shiga, dan haka sai ya tashi
da yar ya tafi can bayan birnin Karlus ya boye
knsa a cikin daji yayita jinya har saida ya warke.
Koda jin wannan labari sai muka cika da farin
ciki, a daidai wannan lokaci ne wazirin sarki
Dumbazu ya zo gaba ya tsaya tare da cewa ya
kai wannan sadauki mai abun mamaki, tunda
har ka samu nasarar kashe sarkinmu, yanzu
abinda ya kamata kayi shine ka maye mana
girbinsa. Da jin wannan batu sai nayi murmushi
n ce ai ni bnai da bukatar mulki ko dukiya,
abinda nazo nema na samu, kuma ba komai
bane face masoyiyata kawai, sai nayi nuni izuwa
ga gimbiya Sahira, ita kuwa sai ta rugo gareni
119
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin farin ciki gami da murna ta rungume ni.
Daga nan sai na dubi wazirin Dumbazu nace da
shi mukam yanzu mun kammala aikin da aka
turomu yi a birninku, saboda haka muna yi
maku sallama sai ku zabi shugabanku a
tsakaninku.
Gama fadin hakan keda wuya sai Aljani mara'il
labarus ya rankwafa bayansa muka hau mu uku
muka zauna, sannan ya bude fuka fukansa guda
18 yayi sama da mu, kafin kiftawar idanu mun
bace bat a cikin gajimare. Tun daga wannan
rana sai naga abokina Maharaz ya daina sakin
jiki da ni, ya daina yin hira da ni, hatta abinci
baya yarda muci tare, al'amarin daya
dugunzuma hankalina kenan na rasa binda ke
mani dadi a duniya, a duk sa'ar dana
tambayeshi shin ko nayi masa wani laifi ne? Sai
yayi murmushi ya ce sam banyi masa laifin
komai ba.
Tsawon kwanaki 17 da muka shafe muna tafiya
a sararin samaniya daga birnin Karlus zuwa
birninmu na darul mahabur bamu yi hirar rabin
sa'a ba nida Maharaz. Muna isa birnin darul
mahabur muka iske sarki Hubaru da boka
karlus sun mutu an binne su, muna kuka muka
120
TASKARNOVELS.COM.NG
isa inda kabarinsu yake, sai da muka shafe sa'a
uku cur muna a gaban karin muna kuka sannan
da kyar aka kawar damu daga bakin kabarin aka
tafi da mu izuwa fada.
Kashegari da safe aka dora Maharaz akan
karagar sarki Hubaru kuma aka daura aurensa
da Husuna yar sarki Hubaru, bayan an gama
bikin nadin Sarki Maharaz ne aka daura aurena
da gimbiya Sahira sannan ya bani sarautar
sarkin yakinsa, na cigaba da yin bauta gami da
biyayya ga sarki Maharaz tsawon shekaru,
kuma duk bukatar da ya zo mani da ita ina binta
ga dukkan iyakar karfina ban taba nuna masa
cewa na gajiya ba, na sha bakar wahala akan
biyan bukatunsa musamman a lokacin da suka
rasa haihuwa shida matarsa Husuna, domin sai
da na kusa rasa rayuwata a kakarina na nemo
masu maganin haihuwa. Duk wannan iyayya da
bauta da nake yiwa sarki Maharaz bai taba yi
mnai godiya ko sau daya ba, kuma gabadaya
abotarmu da kusancinmu sai ya yanke su, ko
magana bana samun damar yi da shi face in
mun zauna dakin gani tare da sauran fadawa
idan bukatar hakan ta taso. Har yau har gobe
ban san dalilin da yasa sarki Maharaz ya nisanta
da ni ba. Yake gimbiya Mulaifa wannan shine
121
TASKARNOVELS.COM.NG
tarihin rayuwata data mahaifinki da kuma
dangantakar dake tsakanina da shi. Masu iya
magana suna cewa ranar wanka ba'a boyon cibi,
yanzu dai gani ga shi kuma yace zai fada mani
wani sirri wanda bai taba fada mani ba a yanzu,
wanda shine sanadin da yasa ya nisanta
abotarmu.
Lokacin da Hibru ya zo nan a labarinsa sai
hawaye ya zubowa sarki Maharaz ya matso daf
da shi yadda suna iya jin numfashin juna sannan
ya ce ya kai abokina hakika abinda kake zargi
tabbas haka yake, idan baka manta ba a ranar
da gimbiya Sahira ta kashe sarki Dumbazu acan
birnin Karlus ta fada mnai wani sako a cikin
kunne na cikin rada ko ba haka ba? To wannan
sako ba wani abu bane face wasiyya daga
mahaifinta wacce ya sanar da ita tun kafin sarki
Dumbazu ya zo ya saceta, abinda ya fada mata
shine, lallai ta sanar da ni cewar dole ne na
nisnta da kai tun daga ranar da n zama Sarki
birninmu na darul mahabur, idan kuwa naki to
tabbas mulkina zai rushe, kaima kuma burinka
bazai cika ba, domin ba zaka zama Sarkin yaki
ba, kuma duk mu biyun ba zamu samu haihuwa
ba har abada, bisa wannan alilai ne yasa na
yanke abotarmu kuma na nisanta kaina daga
122
TASKARNOVELS.COM.NG
gareka, amman a kullum sai na shiga turakata
na kulle kaina nayi ta kukan bakin ciki ba tare
da kowa ya sani ba. Ya kai abokina ka gafarceni
inaso ka fahimta cewa dole ce tasa na aikata
hakan a gareka bawai a son raina bane kuma
dama ance kada na sanar da kai gaskiyar
al'amarin sai a lokacin da naga gagarumin yaki
ya taso wanda bamu da tabbacin samun nasara
akan shi. Sa'adda Sarki Maharaz ya zo daidai
nan a jawabinsa sai Hibru ya rungumeshi, take
duk su biyun suka rushe da matsanancin kuka
suna masu daɗa kwakumar juna.
Mulaifa dake tsaye tana kallonsu sai ta kamu da
tsananin tausayinsu, itama sai ta fashe da kukan
aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninsu.
Bayan sun jima a cikin wannan hali sai Sarki
Maharaz ya janye jikinsa daga na Hibru suka
sake kallon juna a karo na biyu sannan ya ce ya
kai abokina kayi sani cewa abotarmu ta zama
samu kamar yau muka fara ta, kuma ina neman
alfarma guda daya a wajenka.
Cikin murmushi Hibru ya ce fadi duk abinda
kake so zanyi maka shi, sarki Maharaz ya ce ina
so kabar yata Mulaifa tayi jinyar Sadauki Imnal
a cikin wannan tafiya da zamu yi, lallai tare da
123
TASKARNOVELS.COM.NG
ita za a yi wannan tafiya. N sani cewa Imnal
yana matukar kaunar Mulaifa idan har tana tare
d shi sai ya fi saurin warkewa, samun kafiyarsa
da wuri shine samun kwanciyar hankalinmu,
domin bincike ya tabbatar da cewa rawar da
Imnal zai taka a wannan yaki ko ni da kai ba
zamuyi rabinta ba.
Da jin haka sai Hibru ya yi murmushi tare da
cewa na amince da haka. Nan take farin ciki ya
lullube Mulaifa da sarki Maharaz, har suka
rungume juna tare.
Sadauki Imnal na kwance a cikin dandazon
mayakan da zasu fita yaki izuwa tekun Bahar
Suffiyya, sai kawai akaga kuyangi da dakarun
sarki Maharaz sun rako gimbiya Mulaifa suna
masu ratsowa ta sansanin dakarun yakin, nan fa
aka zuba ido aga wajen wa kuma gimbiya ta zo,
kunyangin dake yi wa gimbiya Mulaifa su 12 ne,
6 na dauke da faratin abinci da abinsha iri-iri,
ragowar 6 kuwa suna dauke da magunguna,
shimfidu da kuma tanti. Kai tsaye gimbiya
Mulaifa ta durfafi inda Sadauki Imnal yyake
kwance, al'amarin daya baiwa kowa mamaki
kenan a wajen, da isowar Mulaifa gaban Imnal
sai ta durkusa daf da shi, ta dubeshi tare da
124
TASKARNOVELS.COM.NG
sakar masa wani tattausan murmushi ta ce da
shi nice baiwar daka bukaci mahaifinka ya samo
domin yin jinyarka.
Koda jin haka sai Imnal ya yunkura da nufin ya
mike tsaye, amman sai Mulaifa tayi sauri ta
danne kafadarsa ta maida shi kwance, Imnal ya
ce wane ni na kalleki a matsayin baiwa, ai nine
bawanki, haba ya shugabata ki kula fa domin
kina gaban talakawanki kike kada kije kiyi abin
kunya.
Koda jin haka sai Mulaifa ta bushe da dariya
tare da cewa ya kai masoyina, kayi sni cewa shi
so makahone kuma kurma ne, wanda duk yayi
zurfi a cikin kogin so to baya ji kuma baya gani,
nayi nisa a cikin kogin kaunarka dan haka babu
abinda zai sa naji kunyar wani mahaluki yayi
kyautata maka. Ina son k saki jikinka ka daina
dari-dari da shakkar komai, domin mahaifina ne
ya turoni gareka da kansa kuma ya umarceni da
nayi jinyar ka a yayin wannan gagarumar tafiya
da zamu yi har izuwa lokacin da zaka samu
lafiya ka warke sumul. Ina mai dada yi maka
albishir da cewa a halin yanzu abotar
mahaifinka da abbana ta dawo sabuwa kamar
da. Nan take Mulaifa ta baiwa Imnal labarin duk
125
TASKARNOVELS.COM.NG
abinda ya faru a dakin gani tsakaninta da sarki
Maharaz da kuma sarkin yaki Hibru.
Koda ta gama bashi labarin sai nan take yaji
wani irin farin ciki ya lullube shi irin wanda bai
taba jin kamarsa ba, kwatsam! Sai suka ji an fara
busa algaita gami da kida tambura alamar cewa
sarki ya fito daga cikin gida domin a fara
wannan gagarumar tafiyar.
Nan take kowa ya nutsu aka mimmike tsaye,
masu dibar kya na diba, masu hawa dawakai
suna hawa, wasu kuma ana tattara dukiya da
guzuri ana laftawa rakuma, dawakai da kuma
keken doki.
Koda sarki Maharaz ya fito daga gidan sarauta
sai aka ganshi tare da abokinsa sarkin yaki
Hibru bisa kan fararen dawakai biyu, duk sunyi
gagarumar shigar yaki kala daya suna tafe suna
fira cikin nishadi abin gwanin ban sha'awa.
Gabadaya jama'ar dake filin fadar sai suka cika
da matuƙar mamaki, domin rabon da aga
Maharaz da Hibru a haka tun kafin su samu
sarauta, maimakon sarki Maharaz da Hibru su
tsaya gaban jama'a suyi bayanin karshe na
wannan tafiya, sai suka wuce kai tsaye wata
126
TASKARNOVELS.COM.NG
hanya da zata kaisu zuwa dakin gunki darzuba.
Da isarsu kofar dakin bautar sai suka sakko
daga bisa dawaknsu, bayin dake biye da su
sukayi sauri suka kama dawakan suka rike.
Maharaz da Hibru suka shige cikin dakin bautar
rike da hannun juna, a haka har saida suka isa
inda gunki darzuba yake, isarsu keda wuya sai
suka durkusa bisa gwiywoyinsu sannan suka
suddar da kawunansu kas, kuma suka rufe
idanunsu.
Bayan sun dan jima a haka kawai sai suka
yunkura da nufin su fece daga cikin dakin
bautar, ba zato sai suk ji muryar darzuba yana
mai cewa "Ku dakata mana tukunna yaku
abokan asali, kuma masoyan gaskiya, sannan
aminan zahiri. Cikin hanzari suka koma suka
durkusa kamar yadd suka yi a farko.
Darbuza ya ce hakika a yau ina mai matukar
farin ciki da dawowar abotarku, domin kuwa
kunyi hakuri da dukkanin kunci gami da
takaicin da muka jarabceku da shi, domin
inganta rayuwarku da nuna amincewarmu bisa
karbar bautarmu da kuke yi ba dare ba rana.
Nayi maku alkawari zan tsare rayukanku