x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - MAZAN JIYA 1

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 211

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
daure wa Shuraim, Shamilat da
Hantaru kai kenan, Shamilat ta dubi Sulbaini
cikin matukar mamaki da damuwa ta ce Haba ya
kai kakana, shin baka shaida ni bane? Ka tuna fa
yau kusan shekara ashirin da doriya kenan
rabon da muga juna, ina ta dokin nazo naganka
200

TASKARNOVELS.COM.NG
domin na nuna maka dana, amman sai ka
tarbemu da tsawa, Kaicona! Inda nasan haka
zaka karbeni da bazamu zo gareka ba.
Sa'ad da Shamilat ta zo nan a zancenta sai
hawaye ya sake zubowa Boka Sulbaini ya
dubeta cikin takaici da damuwa sannan ya nuna
Hantaru da hannu ya ce Yake jikata abar
kaunata, kiyi sani cewa wannan yaro ba jininmu
bane, ina nufin ba kece kika haifeshi ba, kiyi sani
cewa duk wanda ya kasance ba jinina ba idan ya
shiga cikin gidan nan hallaka zai yi, wannan ne
yasa na yi muku tsawa domin bana son ya
hallaka.
Koda jin wannan batu sai Hantaru, Shuraim da
Shamilat suka zazzaro idanu, hankalinsu ya
dugunzuma ainun. Nan take idanun Hantaru
suka ciko da kwalla ya dubi boka Sulbaini yace
wace shaida ce da kai wacce zata gamsar damu
cewa ni ba jininku bane?
Koda jin wannan tambaya sai tausayin Hantaru
ya kama Boka Sulbaini har hawaye ya zubo
masa, sannan ya ce tabbas kuwa nike da babbar
shaida, na umarceku da kuyi duba izuwa

201

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan bangon gidan nawa domin ku ga yadda
al'amarin ya kasance.
Ba tare da gardamar komai ba su Hantaru suka
dubi bangon gidan, shi kuwa boka Sulbaini sai
yayi nuni da hannunsa izuwa bangon, take
hoton birnin Kisra ya bayyana a kai, aka fara
nuno wasu ababuwa da suka gabata tsawon
shekara da shekaru, da farko a nuno lokacin da
matar sarki Kusaidu wato Zarifa ta kadaita da
Boka Ardusa ta ce da shi lallai ya baiwa sarki
shawarar kara aure domin su cimma burinsu,
wato suyi shirin da zasu baiwa sarki dan da
suka samu ta hanyar lalata ta cin amanar sarki a
matsayin dan cikinsa ba tare da ya sani ba.
Daga nan aka nuno lokacin da sarki Kusaidu ya
zo birnin darul Habur har ya shiga gasar neman
aure kuma ya samu nasara a tseren gudun
barewa, sanadin Salimat ta zamo matarsa aka
daura aure ya tafi da ita birnin Kisra.

Ina yi maku barka da wannan lokaci sannan ina
baku hakuri na shiru da kuka ji hakan ya faru ne
202

TASKARNOVELS.COM.NG
saboda rashin lafiya da na kwanta tun bayan
sallah, amman yanzu AlhamduLillahi

Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya
Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta
Ko Kuma Complete Document zasu iya mani
magana ta whatsapp 08138873799

MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part O
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

Sannu a hankali aka nuno yadda boka Ardusa ya
saka wa Salimat juna biyu na sihiri da kuma
yadda ya boye cikin zarifa na gaskiya har izuwa
lokacin haihuwarta ba tare da kowa ya sani ba.
Daga nan aka nuno ranar da Shamilat ta kamu
da ciwon nakuda, ta kwana ta yini a ciwon
203

TASKARNOVELS.COM.NG
nakuda, har sai da zarifa ta shiga dakin
haihuwar ta kori matan dake yi wa Shamilat
unguwar zoma, ya zamana cewa su biyu ne rak
a cikin dakin.
Nan take ta sumar da Shamilat ta kama tata
nakudar, ta haifi santalelen jariri, ta ajiye wa
samilat nata jaririn ta fice daga dakin haihuwar,
daga nan ne fa sai jama'ar gari suka rude da
farin ciki Salimat ta haifi da, daga nan aka ci
gaba da rainonsa har ya zama Hantaru.
Koda hoton duk wannan al'amari yazo daidai
nan sai boka Sulbaini ya sake yin nuni da
hannunsa izuwa ga bangon, take hoton komai
ya bace. Nan take Hantaru ya kwarara uban ihu
cikin takaici da bakin ciki, kuma ya fashe da
matsanancin kuka. Itama samilat sai kawai taji
jiri ya kwasheta, kafin su ankara ta sulale kasa
sumammmiya.
Cikin hanzari boka Sulbaini yayi tsafi ruwa ya
zubo daga cikin yan yatsunsa ya yayyafa mata,
sannan ta farfado ta fashe da matsanancin kuka
mai tsuma zuciya.
Sulbaini da Shuraim suka kamu da tsananin
tausayin samilat har basu san sa'ad da suka
204

TASKARNOVELS.COM.NG
kama kuka ba duk su hudun, haka suka yita
wannan kukan. Sai daga can Hantaru ya zo gaba
samilat ya durkusa bisa gwiywoyinsa ya kama
kafadunta itama sai ta kama kafadunsa a lokacin
da hawaye ke zuba daga idanunsu yace ya ke
Ummina hakika yanzu na gamsu cewa ba kece
kika haifeni ba, amman kiyi sani cewa har abada
kece uwata domin nononki nasha na rayu har
na girma, dan haka bazan taba daukar waccan
ba da boka Ardusa a matsayin iyayena, kuma a
halin yanzu ina jin cewa bani da makiya a
duniya sama da su, kuma bani da wani buri a
duniya da ya wuce na zare masu ruhin
numfashinsu, domin sunci amanar mijinki sun
cuci rayuwata sun kuma yi mani babbar barna
da har abada bazata gyaru ba.
Lallai bayan naci gasar tseren gudu sai na koma
Birnin Kisra na kasheta ita da Ardusa sannan na
fada wa sarki Kusaidu gaskiyar al'amari na ce
masa ni ba dansa bane ga yadda akayi aka same
ni.
Bayan d Hantaru yazo nan a zancensa sai
samilat ta rungumeshi, sannan ta fashe da sabon
matsanancin kuka, shima sai zuciyarsa ta
karaya ya cigaba da kukan, daga can sai samilat
205

TASKARNOVELS.COM.NG
ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna
sosai ta ce ya kai dana ina son k tuno da tsantsar
kaunar dake tsakaninka da sarki Kusaidu, ka
tuna cewa ba a son ransa na taho da kai nan
garin ba, saboda baya son rabuwa da kai daidai
da na kwana daya, yanzu idan kaje ka sanar da
shi gaskiyar al'amari yaya zai ji, kuma wane irin
hali kake tunani zai shiga?
Ina mai tabbatar maka idan yaji wannan labari
zai iya hadiyar zuciya ya mutu, domin gabadaya
zai ga rayuwarsa bata da wani amfani a duniya,
tunda mutumin daya amincewa fiye da kowa a
duniya wato boka Ardusa ya ci amanarsa.
Sannan babban burinsa na duniya ya wargaje,
tunda bai samu haihuwa ba, matarsa d suka yi
auren saurayi da budurwa wacce yake kauna
fiye da kansa, kuma ya bata amanar kansa
tsawon shekaru yau itama ta ci amanarsa, ya
kau dana ina mai rokonka da komai rokonka
komai rintsi da tsanani kada ka bari sarki
kusaidu yasan wannan sirri, idan har ka dauke
ni a matsayin uwa ina so ka sani cewa ina
kaunar mijina fiye d duk yadd kake tsammani,
saboda haka lallai ina so na koma birnin Kisra
na cigaba da rayuwa da shi cikin farin ciki, ban
206

TASKARNOVELS.COM.NG
hanaka yiwa boka Ardusa da waccan mata
hukunci ba, amman kayi sani cewa tana
lafiyarta dai-dai yake da taba lafiyar mijina, idan
kuwa kayi haka to babu ni babu kai sai dai ka
sauya uwa.
Sa'ad da Samilat ta zo nan a zancenta sai
Hantaru ya rungumeta a karo na biyu ya fashe
da kuka saboda bakin ciki da takaici domin
yasan cewa ba xai iya ketare wannan doka ba
data kafa masa.
Bayan Samilat da Hantaru sun dade suna kuka
na bakin ciki sai boka Sulbaini ya janyeshi daga
jikin Salimat, sannan ya jashi gefe daya inda su
Salimat ba zasu ji abinda zasu tattauna ba.
Sulbaini ya dubi Hantaru cikin natsuwa sannan
yace ya kai wannan Gwarzon jarumi, namijin
Duniya, kayi sani cewa na hango maka mugun
hadari a cikin rayuwarka da kuma mummunan
karshe amman fa sai idan kayi sakaki soyayya ta
rudi zuciyarka, na sani cewa Gimbiya Larziyya
ta baka wasika a jiya sa'ar da aka yi walima a
gidan Shuraim, kuma ta gayyaceka zuwa bayan
gari tana son ku hadu a dutsen kufainu, ko ba
haka bane ?

207

TASKARNOVELS.COM.NG
Hantaru ya gyada kai cikin mamaki yace haka
al'amarin yake.
Boka Sulbaini yayi ajiyar zuciya sannan ya ce
yakai wannan jarumi ka sani cewa Gimbiya
Larziyya kyakkyawar mace ce ta gaban keatance
dan haka da zarar ka yi arba da ita zaka ji ka
tsunduma a cikin kogin soyayyarta, kuma zaka
iya salwantar da rayuwarka kai data kowa ma
dan kawai ka mallaketa, gargadin da zan yi
maka shine, kada ka yarda ta umarceka da yin
abinda zai sa ka rushe alakar dake tsakaninka
da jikata Salimat anan gaba bayan kaci gasar
tseren gudun barewa, idan kuwa ka kuskura ka
aikata haka to kaima halaka zaka yi, kuma
daukakarka zata tafi a banza, sai dai kawai a
dunga tuno da kai a tarihi.
Lokacin da boka Sulbaini ya zo nan jawabinsa
sai hankalin Hantaru ya dugunzuma fiye da
koyaushe, yayi shiru yana tunani har izuwa
lokaci mai tsawo, daga can sai ya dago ya dubi
boka Sulbaini yace lallai zan kiyaye bisa dukkan
wannan shawara daka bani.
Cikin farin ciki boka Sulbaini ya rungume
Hantaru yana mai cewa madalla da da mai
208

TASKARNOVELS.COM.NG
halacci ga jikata, wanda naso ace ya zamo jinin
jikata. Koda jin haka sai Salimat ta taso da gudu
daga inda take tsugunne ta rungume Sulbaini da
Hantaru suka kankame juna su uku suka fashe
da sabon kuka. Shuraim dake tsaye yana
kallonsu shima sai ya fashe da kuka aka rasa
wanda zai rarrashi wani a cikinsu.
Shuraim, Salimat da Hantaru basu yi sallama da
boka Sulbaini ba sai da la'asar ta yi, lokacin da
suka zo yin sallamar ne sai Sulbaini ya dubi
Hantaru ya ce da shi ya kai Gwarzon namiji ina
son kayi sani cewa zaka sha bakar wahala a
wannan gasar tseren da zaka yi, kuma kai da
Sadauki Rabbasu kunnen doki zaku yi a cikin
gasar, saboda haka sai kunyi gasar sau uku, kaga
kenan dole ne ka zauna a wannan garin tsawon
shekara uku, idan ma har zaka lashe wannan
gasa to sai bayan kaje ka samo wata
sihirtacciyar takobi wacce babu kamarta q fadin
duniya. Tabbas kai da Sadauki Rabbasu zaku tafi
neman wannan takobi, duk wanda ya riga dan
uwansa mallakar wannan takobi to shine zai
auri gimbiya Larziyya. Tabbas sai ka jajirce
ainun sannan zaka iya samo wannan takobi da
ake yiwa lakabi da Saiful Lujara.
209

TASKARNOVELS.COM.NG
Asalin takobin Saiful Lujara wani hatsabibin
boka ne ya kareta da ruhin wasu babaken aljanu
guda dubu casa'in, a rabar da bokan ya
kammala takobin ne ya mutu, sakamakon
tsananin wahalar daya sha a kokarin kerata,
saboda sai da ya kwana hudu ba ci ba sha,
tsananin yunwa da kishin ruwa ne suka
kasheshi, yanzu haka takobin na nan a cikin
wannan kogon da bokan ya mutu, kuma babu
wanda ke iya zuwa inda wannan takobi take
saboda tsananin masifun dake cikin dazuzzukan
kafin a ketare a isa kogon, da kuma shi kanshi
bala'in dake cikin kogon face sadaukin da ya
yarda da Sadaukantakarsa, kuma ya zamana
cewa yana da matukar karfin sihiri. Daga
lokacin da makerin takobin Saiful Lujara yya
mutu kawo izuwa yanzu shekara dubu uku
kenan, kuma a kalla sadaukai sama da guda
dubu sun tafi dauko wannan takobi amman har
yau har gobe dayansu bai dawo ba.
Ya kai Hantaru ni kam nayi alƙawarin cewa zan
taimaka maka da dukkan karfin sihirina, kamar
yadda sarkin mafarauta zai taimaka wa dansa
Rabbasu da dukkanin karfin sihirinsa domin
yaje ya samu damar dauko takobin daraja ta
Saiful Lujara.
210

TASKARNOVELS.COM.NG
Ka sani cewa bani da wani buri da ya fi naga
kambun gasar tsere ya dawo zuri'armu ta
makera.
Sa'ad da boka Sulbaini ya zo nan a zancensa sai
jikin Hantaru yayi sanyi kuma hankalinsa ya
dugunzuma domin ya fuskanci cewar duk
wahalar da ya sha a baya kamar somin tabice
akan wacce zai sha a nan gaba, saboda samun
nasarar sa akan sadauki Rabbasu a wannan gasa
da kuma dauko takobin Saiful Lujara wannan
abu ba karamin jidali bane.
Nan dai boka Sulbaini yayi wa Hantaru sallama
a matsayin ba zasu sake saduwa ba sai nan da
kwanaki goma sha takwas wanda ya rage saura
kwana daya ayi gasar tseren gudun barewa.
Ba tare da bata lokaci ba Shuraim da Salimat
suka yi wa Sulbaini sallama gami da godiya
sannan suka sakko daga kan dutsen suka
kwance dawakansu duk su ukun suka hau
sannan suka nufi hanyar gida.
Salimat na waigen gidan boka Sulbaini wanda
ke saman dutse, ta tuno da rayuwarta a gidan
tun tana yarinya karama kafin rasuwar matar
boka Sulbaini, abinda salimat ba zata taba
211

TASKARNOVELS.COM.NG
mantawa ba shine kullum sai sunyi wasan yar
boyo ita da matar boka Sulbaini, wani lokacin
ma har wasan doki suke yi, ta hau gadon bayan
Sulbaini tana sukuwa. A daidai wannan lokacin
ne hawaye ya zubo wa salimat taji ace inama
zata iya dawo da abinda ya wuce amman ina ai
babu dama.
A lokacin da su Hantaru suka iso mararrabar
hanya ne, inda ta rabu gida uku; daya zata kaisu
izuwa cikin gari, daya izuwa dajin kufainu,
dayar kuma izuwa inda suka baro. Sai Shuraim
ya nuna wa Hantaru hanyar da zata sadashi
izuwa dajin kufairu.
Yace ya kai Gwarzon Sadaukai wannan hanyar
ita zaka bi kaje inda gimbiya Larziyya ta ke,
maza kaje ku hadu, sannan ka tabbatar ka dawo
gida da wuri kafin dare yayi sosai.
Koda jin haka sai Hantaru yayi murmushi
sannan ya dubu salimat ya ce zan tafi izuwa ga
Gimbiya idan har kinyi izini a gareni ya ummina.
Salimat ta mayar masa da martanin murmushi
sannan ta ce jeka abinka ya kai dana, ina goyon
baya dari bisa dari.
212

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai Hantaru ya zaburi dokinsa
cikin farin ciki ya sukwaneshi izuwa cikin dajin
kufairu. Yar gajeriyar tafiya hnataru yayi ya iso
inda dutsen yake, tun daga nesa Hantaru ya
hango gimbiya Larziyya a bisa dutsen a zaune
tana sanye da wasu kurayen tufafi, masu
tsananin kyau da ban sha'awa ta lullube kanta
gaba daya da mayafin kayan.
Koda Larziyya ta hango Hantaru ya durfafo inda
take, sai ta mike tsaye, mikewarta keda wuya sai
iska ta dauke mayafin data rufe kanta da shi ta
yi kasa da shi, a wannan lokacin ne hantaru yayi
arba da fuskar Gimbiya Larziyya, tsarki ya
tabbata ga ubangijin daya daidaita gabban jikin
gimbiya Larziyya, a iya sanin Hantaru ko a bakin
ma'abota labarin duniya, bai taba jin wanda ya
wassafa mace mai kyau na Gimbiya Larziyya ba,
saboda tsananin kyawun fuskarta dana kirar
jiki. Idan mutum yayi arba da ita sai yayi
tsammanin cewa ba mutum bace aljana ce.
Hantaru dai bai san sa'ad da ya ja linzamin
dokinsa ya tsaya cak ba, daga kasan dutsen suka
kura wa juna idanu suna sun murmushi. Nan
take yaji kibiyar so ta sokeshi a kahon zuci
kuma yaji cewa a haukansa ko mutuwa bata isa
hanashi mallakar gimbiya Larziyya ba.
213

TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin natsuwa da tafiyyar kasaita Larziyya ta
sakko daga saman dutsen kufairu, tazo daf da
Hantaru ta tsaya sannan ta ce lale marhabun da
Sadauki uban sadaukai, tauraron zamani mai
haska duniya. Ya kai Hantaru ka yi sani cewa
yauce ranar da tafi kowacce rana farin ciki a
rayuwata, domin a yau nayi arba da masoyin
zuciyata wanda na dade ina begensa tun
gabanin naga fuskarsa, ina godiya daka amsa
gayyata ta bisa muhimmiyar wannan rana ta
saduwarmu.
Shin daka ganni a yanzu kaji kana sona, kamar
yadda na dade da kamuwa da kaunarka?
Lokacin da Hantaru yaji wannan tambaya sai
yaji dariya ta kubuce masa, itama sai ta kama
dariyar kamar su duka biyun sun zautu.
Lokaci guda suka daina dariyar kuma suka kura
wa juna idanu, Hantaru yq ce yake wannan
mafifiyar ma'abociyar kyawun, kiyi sani cewa
babu wani mahaluki walau a mutane ko a aljanu
da zai ganki bai kamu da tsananin kaunarki ba.
Tabbas a yanzu ina ji a jikin cewa zan iya
salwantar da rayuwata domin farin cikinki ko
domin na mallakeki.
214

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Larziyya ta
cika da tsananin farin ciki, nn take rungume
hantaru suka kankame juna har izuwa wani
lokaci mai dan tsayi, daga can sai ta janye jikinta
daga nasa suka fuskanci juna ta ce ya kai
masoyina kayi sani cewa yau saura kwana goma
sha tara ayi gasar neman aurena, kaine kadai
mutumin da zai iya share mani hawayena, ya
hana Sadauki Rabbasu samun nasara a wannan
gasa, idan har kaunar da kake mani ta gaskiya
ce ina so ka daukar mani alkawarika guda uku a
yanzu, alkawari na farko shine; duk wuya duk
rintsi ba zaka janye takarar neman aure na ba,
alƙawari na biyu duk alfarmar da na nema a
wajenka zaka yi mani ita, alkawarina na uku
kuwa shine a duk halin da muka tsinci kanmu
ba zamu guji juna ba, idan har ka amince da
wadannan alkawaruka to nima na yi maka
alkawari cewa zan sallamar da rayuwata domin
ka, kuma har abada babu wani da namiji da zai
sanni ya mace face kai, haka kuma duk irin
bala'in da zaka shiga zan bika mu shiga tare
koda kuwa zan hallaka.
Sa'ad da Gimbiya Larziyya ta zo nan a bayaninta
sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfin
gaske, abinda ya fara fado masa a rai ne shine
215

TASKARNOVELS.COM.NG
batun alkawarin daya daukar wa mahaifiyarsa,
Hantaru ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa
anya kuwa alkawarin dana daukar wa ummina
ba zai zamo kishiyar wanda Gimbiya Larziyya ta
ke so na daukar mata a halin yanzu ba kuwa?
Nan fa ya rasa irin hukuncin da ya kamata ya
yanke.
Lokacin da Larziyya taga Hantaru yayi shiru bai
bata amsa ba, kuma ya sunkuyar da kansa kasa
yana tunani, sai ta dafa kafadarsa ta ce kai nake
sauraro ya masoyina, wane hukunci ka yanke
game da alkawarin da muka daukar wa
junanmu.
Hantaru ya dago kai cikin murmushi yace yake
abar kaunata kiyi sani cewa kinzo mani da
babban alƙawari, wanda yafi gaban na yanke
hukunci yanzu take, saboda haka ina neman
alfarmar ki bani lokaci nayi tunani.
Koda jin haka sai Larziyya tayi murmushi
sannan ta ce na baka lokaci, daga nan har izuwa
ranar da za'a fara gasar neman aurena, amman
sai kayi alkawarin cewa ba zaka yi shawara da
kowa ba, sai da zuciyarka kadai.

216

TASKARNOVELS.COM.NG
Hantaru ya maida mata da martanin murmushi
sannan ya ce nayi alkawarin ba xan yi shawara
da kowa ba face da xuciyata, cikin tsananin farin
ciki Larziyya ta sake rungume Hantaru a karo na
biyu sannan ta sumbaci goshinsa. Kawai sai ta
tafa hannayenta biyu take wani bawan sarki ya
fito daga cikin duhuwa janye da keken doki.
Larziyya ta dubi Hantaru cikin wani irin
murmushi mai dagula tunanin da namiji ta ce
daga yau ba zamu sake saduwa ba sai ranar
gasa, lallai a ranar ne zaka bani amsoshin
tambayoyina, da wannan kalami nake maka
sallama ya madubin zuciyata, sai lokaci yayi.
Koda gama fadin haka sai Gimbiya Larziyya ta
juya ta nufi inda keken dokinta yake tana mai
waigen Hantaru, shi kuwa sai ya biya da kallo
kawai ya kasa cewa komai har ta shiga cikin
keken dokin ta zauna.

Ina yi maku barka da wannan lokaci da fatan
kuna cikin koshin lafiya

217

TASKARNOVELS.COM.NG
Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya
Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta
Ko Kuma Complete Document zasu iya mani
magana ta whatsapp 08138873799

Bawan ya kafa linzaman dawakan dake jan
keken dokin suka nufi hanyar cikin gari. Tun
Hantaru na hango keken dokin har ya bace wa
ganinsa, sai da Hantaru ya dade a tsaye yana
mai nazari da tunani sannan shima jaye ya hau
dokinsa ya nufi cikin gari.
Da isar Hantaru gida sai ya iske tuni Salimat ta
shirya masa abinci a ajiye a dakinsa. Bayan
Hantaru ya zauna ne ya huta kuma ya ci abinci
sai ya fada cikin kogin tunani, ya kasa yi wa
kansa zabi bisa amsar da ya kamata ya baiwa
Gimbiya Larziyya a ranar da za a yi gasa. Yana
cikin wannan hali ne Salimat ta shigo cikin
dakin ta riskeshi a cikin halin tunani.
Cikin matukar damuwa Salimat ta zauna daf da
shi sannan ta ce ya kai dana na sani cewa ka
kamu da kaunar Gimbiya Larziyya domin babu
218

TASKARNOVELS.COM.NG
wani da namiji da zai yi arba da ita ba tare d ya
fada tarkon begenta ba. Ya kai dana ka fada
mani dukkanin abinda kuka tattauna kai da ita,
ni kuma zan baka shawara wacce zata fissheka a
rayuwa.
Koda jin haka sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga
da karfi ainun, kuma ta gargadeshi akan kada ya
fada wa Salimat gaskiyar maganar da yayi da
Gimbiya Larziyya.
Hantaru ya dubi Salimat cikin murmushi yace
yake ummina kiyi sani cewa babu abinda muka
tattauna face kalmomin kauna gami da
alkawarin zamu so juna da gaskiya.
Koda jin haka sai murna ta kama Salimat ta sa
masa albarka sannan ta mike tsaye ta fice daga
cikin dakin.
Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda
Hantaru yasan abinda zai biyo baya bisa
boyewa Salimat gaskiyar al'amari da bai boye
mata ba. Tabbas
End Ads