x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - MAZAN JIYA 1

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 213

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
korama.
Anan ne fa dawakansu suka yi turjiya suka
kama shan ruwa, saboda daman sun debo rana
kuma sun gaji, su kansu su hantarun sun gaji
kuma suna jin yunwa da kishin ruwa, amman
saboda dakakkiyar zuciya irin ta mazan kwarai
sai suka basar saboda kada suka cewa dayansu
ya gaza.
Lokacin da dawakan nasu suka tsaya a bakin
gabar koramar suka kama shan ruwa, sai
Hantaru da Rabbasu suka dubi juna, bisa ga
276

TASKARNOVELS.COM.NG
mamaki sai suka yi wa juna murmushi. Rabbasu
yayi gyaran murya ya ce ya kai abokin gaba ina
ganin cewa ya kamata mu yada zango anan,
domin mu huta kuma dawakanmu ma su huta,
dan na lura cewa akwai gajiya a tare da mu.
Hantaru yace kwarai kuwa ka zo da shawara
mai kyau.
Nan take duk su biyun sauka kayan su dake bisa
dawakansu kowa ya kafa tantinsa, kuma suka
bude jakar guzirinsu suka ci kuma suka sha.
Bayan sun gama kimtsa cikin nasu ne sai kuma
hira ta barke a tsakaninsu, inda Rabbasu ya dubi
Hantaru yace ya kai bakon garinmu, kayi sani
cewa ina da wata tambaya a gareka, wacce zan
so ka bani amsarta bilhakki.
Koda jin wannan batu sai Hantaru yayi
murmushi sannan ya ce fadi duk irin tambayar
dake bakinka ni kuma nayi alƙawarin zan baka
amsa iyakar gaskiyata.
Rabbasu yayi gyaran murya sannan ya ce ina
son ka fada mani alakar dake tsakaninka da
Salimat yar sarkin makera Shuraim, shin ita ce
ta haifeka ko ba ita bace?
277

TASKARNOVELS.COM.NG
Yayin da Hantaru yaji wannan tambaya sai ya
cika da mamaki kuma yayi shiru kamar ba zai ce
komai ba, sai ya ce alakata da Salimat itace ta
shayar d ni, amman ba ita ce ta haifeni ba.
Koda jin Wannan batu sai idanun Rabbasu suka
zazzaro, kawai sai ya takarkare ya kwarara
uban ihu cikin tsananin bakin ciki, ihun nasa ne
ya firgita kananun dabbobin dake cikin dajin da
tsuntsaye suka kama tashi da guje-guje wasu
suna sauya ramuka, nan take kwallar takaici ta
cika idanun Rabbasu ya dubi Hantaru yace
hakika nayi babban kuskure da banyi cikakken
bincike akanka ba, tun a farkon zuwanka garin
nan, inda nasan cewa kai ba jinin zuri'ar makera
bane da bazanyi wannan gasa d kai ba, da tuni
na kashe kaina na da huta da takaici.
Cikin tsakanin mamaki Hantaru ya dubi
Rabbasu yace kai kuwa sabida me yasa ka fadi
haka?
Rabbasu yace saboda bincike ya tabbatar da
cewa babu wani dan zuri'ar makera da ya isa ya
samu nasara a kaina, duk da cewa har a yanzu
baka samu nasara a kaina ba, in tsoron faruwar

278

TASKARNOVELS.COM.NG
hakan a nan gaba, tunda kai ba zuri'ar jinin
makera bane.
Koda jin haka sai Hantaru ya bushe da dariya
sannan ya ce ai kuwa babu makawa sai abinda
kake tsoron faruwarsa ya faru, ina mai tabbatar
maka da cewa nine zan karbi kambun wannan
gasa ta neman auren Gimbiya Larziyya.
Rabbasu shima ya bushe da dariya yana mai
cewa ai Shikenan, muje zuwa mahaukaci ya hau
kura, zanga ta yadda zaka lashe wannan gasa.
Koda gama fadar haka sai Rabbasu yayi shiru
bai sake cewa komai ba, shim Hantaru haka har
dai suka gama hutawarsu suka cigaba da tafiya.
Daman tun kafin su baro birnin Darul Habur an
baiwa kowannensu zanen taswirar hanyar da
zata kaisu zuwa kogon nan na Mazabatul
Darshal, dan haka suna tafe suna duba wannan
taswirar, haka dai su Hantaru suka wanzu suna
masu keta dazuzzuka dare da rana wani lokacin
ma basa kakkauta tafiya sai dai su kunna wutar
icce su haska wa kansu hanya, wani lokacin
kuma idan duhu ya kai duhu sai su hakura su
yada zango.
279

TASKARNOVELS.COM.NG
Duk inda tsautsayi yasa suka hadu da yan fashi
ko muggan dabbobin daji, tofa komai yawansu
cikin dakiku kadan suke ratattakasu su bi ta
kansu, su kuma wuce tamkar anyi sassabe a
gona, kai bama mutane da dabbobi ba, komai
shedancin aljani da taurin kansa, da zarar ya
hango Hantaru da Rabbasu sai kawai kaga ya
ratse ya nemi maboya, domin yasan karo da
shiryayyun maza irin su babu sa'a.
Sai da su Hantaru suka shafe kwana goma sha
tara suna ratsa dazuzzuka iri-iri sannan suka iso
dajin hayatul Maut. Shi dai wannan daji na
hayatul Maut ya fita da ban da kowanne irin
dazuzzuka da suka saba gani. Tun a farkon dajin
suka sha jinin jikinsu suka gane cewa sun shigo
cikin bala'i da masifa wacce basu da tabbacin
fita daga cikinta sai abinda hali yayi.
Komai na cikin dajin ba irin wanda ido ya saba
gani bane, gaba daya bishiyoyin dajin siffar
dodanni garesu, su kuwa duwatsu suffar
muggan dabbobi garesu, a cikin koramai kuwa
sai suka rinka ganin aljani nata nukkaya da
nutso, kai hatta ciyayin dake dajin hira suke da
junansu, har ma suna yi wa junansu rada da
zarar sunga su Hantaru sun matso daf da su.
280

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin waɗannan abubuwa na ban tsoro,
sai Hantaru da Rabbasu suka zare takubbansu
suka ci gabada tafiya suna masu kallon gabas da
yamma, kudu da arewa cikin nutsuwa domin
suka ta inda za a fara kawo masu hari.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga wani
aljani mai siffar guguwa ya taho a sama yanata
kyakyata masu mahaukaciyar dariya mai kama
da saukar aradu, hakika komai taurin kan
mutum idan yaji wannan dariya dole ne ya
razana, balle kuma idan yayi arba da aljanin
wanda saboda matukar muninsa idan ka
kalleshi zaka iya kama kumallo. Aljanin ya tsaya
a cikin iska yana jale-jale kamar idan aka
hureshi da iskar baki zai iya tarwatsewa, kawai
sai ya dubi su Hantaru ya daka masu tsawa ya
ce ku kanana kwari, wane tsautsayi ne yasa
kuka siyar da rayukanku ku ka shigo wannan
daji na hayatul Maut, shin baku da tarihin
wannan daji ne? To ku sani cewa fiye da
shekaru dubu duk halitar data shigo wannan
daji ta ratso ta nan sunanta gawa, saboda mu
tabbatar da tsaro ga takobin daraja ta Saiful
Lujara.

281

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da aljanin ya zo nan a zancensa sai
Hantaru ya tari numfashinsa ya ce da shi Kai
tsohon maketaci la'ananne, yau masu karya
tasirinku sun zo, mukam mun shigo cikin
wannan daji a raye cikin koshin lafiya, kuma sai
mun fita a raye bayan mun dauke abinda kuka
dade kuna gadi, wato takobin Saiful Lujara.
Kafin Hantaru ya gama rufe bakinsa tuni Aljanin
ya gabza masa wawan naushi a fuska, nan take
hantaru ya sulale kasa sumamme, ya fado daga
bisa dokinsa wata irin farar kumfa na fita daga
bakinsa. Koda faruwar haka sai aljanin ya dubi
Rabbasu ya daka masa tsawa ya ce Kai kuma
maza ka kashe kanka ko kuma nayi maka
abinda nayi wa dan uwanka.
Rabbasu ya maida wa aljanin nan martanin
tsawa ya ce karyarka ta sha karya dan haka ga
maza nan bisa kanka, kawai sai Rabbasu ya
tashi sama kamar tsuntsu ya bar bisa dokinsa ya
afka wa aljanin yana mai kai mashi sara da suka
cikin matukar zafin nama.
Shikuwa aljanin sai yayi amfani da dan yatsansa
guda daya jal a matsayin tasa takobin yana mai
kare saran gami da mayar da martani, idan
282

TASKARNOVELS.COM.NG
takobin Rabbasu ta hadu da dan yatsan aljanin
nan sai kaga tartsatsin wuta na tashi, wata irin
walkiya ta cika dajin baki daya, sai da suka jima
a sama cikin iska suna wannan gumurzu
dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin
daya ba, al'amarin daya fusata aljanin kenan ya
harzuka ainun, kawai sai aljanin ya rikide ya
koma dan siriri kamar zare ya nannade jikin
Rabbasu tun daga kafafunsa har zuwa kansa
kawai sai ya shiga matseshi.
Nan fa Rabbasu ya ji kamar za a rugurguza
kasusuwan jikinsa gabadaya har bai san sa'ad
da ya kurma uban ihu ba, sannan ya kama
kumbura tamkar iska ake hura masa, nan fa
shima aljanin ya fara rusa ihu domin shima ji
yayi kamar Rabbasu zai tsinkashi gida biyu. Ba
shiri aljanin ya rabu da jikin Rabbasu ya cilla
izuwa can kololuwar sama tamkar daga cikin
baka aka harba shi.
Rabbasu ya daga kansa sama take ya zama
haske ya bi aljanin da gudun tsiya, amman sai
yaga ya kasa cimma wannan aljani domin karfin
gudun aljanin yafi na tauraruwa mai jela.

283

TASKARNOVELS.COM.NG
Ba zato ba tsammani sai aljanin ya sake
rikidewa ya zamo wata irin masifaffiyar wuta
mai tsananin zafi, ya juyo da baya suka kasa
tsere da wannan haske, nan fa Rabbasu ya ji
kamar daga cikin tafasasshen mai aka tsunduma
shi, duk da cewa kuwa wutar ba ta taba jikinsa
ba. Ba shiri Rabbasu shima ya rikide ya zama
kankara, koda wutar da kankarar suka hadu sai
duk su biyun suka rinka kururuwa wani irin
sauti mara dadin ji ya dinga tashi, tamkar ana
diga ruwa a cikin tafasasshen mai. Ba shiri duk
su biyun suka rikito kasa kowa ya juye izuwa
ainihin siffarsa. A daidai wannan lokaci ne
aljanin ya shammaci Rabbasu ya narka masa
dundu a gadon baya, take Rabbasu yaji tamkar
kashin bayansa ya karye, kawai sai jiyayi yana
kumallon wahala, shi kansa kumallon ji yayi
kamar yan hanjin cikinsa zasu fito ta baki. Nan
take ya baje a kasa sumamme, shi kuwa aljanin
sai ya sauko kasa ya dira bisa turba yana mai
kyakyata dariyar murna.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaji takobi ta
tsargeshi gida biyu, tamkar yadda ake sa zabira
a keta takarda, sai ga gangar jikin aljanin nan ta
rabe gida biyu, ko wanne bangare ya fadi gefe
daya. Ba wani bane yayi wannan aiki sai sadauki
284

TASKARNOVELS.COM.NG
Hantaru, shi kansa sai kawai ya tsaya yana
kallon takobin tasa yana mamakin yadda aka yi
tayi wannan namijin aikin. Aljanin nan dai ko
shurawa bai kara yi ba, Hantaru ya dubi
Rabbasu wanda ke kwance magashiyan ko
motsawa baya yi sai kawai ya kawar da kansa
ya kama dokinsa ya haye ya cigaba da tafiya,
yana mai tunanin cewa shikenan ya rabu da
abokin tafiyarsa har abada, domin bai ga
alamun zai iya rayuwa ba.
Sai da Hantaru yayi tafiyar sa'a uku cur a cikin
dajin hayatul Maut bai kara haduwa da wani
mugun abu ba, kuma yana tafe yana duba
taswirar hanya izuwa kogon Mazabatul Darshal.
Kawai sai Hantaru yaga hanya ta bi dashi ta
cikin kogon dutse mai tsananin tsawo da ba a
iya hango karshensa, sannan da ya leka cikin
kogon sai yaga mugun duhu ne da shi baya iya
ganin komai, bisa dole hantaru ya sakko daga
bisa dokinsa ya nemi icce ya kunna masa wuta,
sannan ya sake hawa dokin nasa ya kunna kai
cikin wannan kogo ba tare da fargabar komai ba
tamkar yana shiga cikin gidansa.
Shigarsa cikin kogon keda wuya sai yaga babu
komai a ciki face kasusuwan bil'adama rututu a
285

TASKARNOVELS.COM.NG
ko'ina, ta kai dokinsa yake bi yana takawa suna
ruburbushewa, abinda ya daure wa Hantaru kai
shine wanne irin mugun abu ne a cikin wannan
kogo wanda ya hallaka miliyoyin rayukan
bil'adama haka, ga dukkan alamu abun ya dade
yana barna a cikin wannan kogo tsawon
shekara guda shekaru, domin kasusuwan
bil'adama dake wajen da yawansu sun gama
bushewa, dan da zarar an takeau sai dai kaga
suna ruburbushewa suna zama gari.
Lokacin da Hantaru ya iso karshen kogon
dutsen sai yaga a rufe yake ruf babu wata hanya
ta fita, nan take ya fito da taswirarsa ya duba,
kawai sai yaga hoton wata ƙatuwar rijiya a cikin
kogon, kuma anyi nuni da cewa rijiyarce kan
hanyar fita daga kogon, nan fa hantaru ya sakko
daga kan dokiksa ya cigaba da haske haske da
wutar iccen dake hannunsa, ai kuwa sai ya
hango katuwar rijiya acan gefe daya koda ya
hangota sai ya ruga da gudu izuwa inda rijiyar
take, da zuwa wajen sai ya maida takobinsa a
cikin kufenta kuma ya sakare wutar iccen a jikin
bango, sannan yasa hannayensa biyu a bisa
rijiyar da nufin budeta, nan fa Hantaru yaji
kamar katon dutse yake son dauka. Al'amarin
da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya kara
286

TASKARNOVELS.COM.NG
hade gabadaya karfinsa waje guda ya cigaba da
kokarin daga marfin rijiyar amman sai abu ya
gagara, domin ko motsawa ma marfin ma baiyi
ba.
Nan da nan Hantaru ya hada gumi yay sharkaf
bisa dole ya yi tagumi ya koma waje daya ya
shiga tunanin dabarar da ya kamata ya yi, yana
cikin wannan hali ne yaji takun sawu ana
shigowa cikin kogon, Hantaru ya mike tsaye
zumbur yana mai zare takobinsa, sannan kuma
ya dauko iccen wuta domin yaga mai shigowa.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaga ashe abokin
tafiyarsa ne Sadauki Rabbasu, nan take Hantaru
yaji farin ciki ya shige shi duk da cewa Rabbasu
babban abokin gabarsa ne, amman ai ko ba
komai tafiyarsa cikin wannan daji mai ban tsoro
bata da dadi, gwara dai ace su biyun ne, dan
haka sai ya ji yana murna da Rabbasu ya tsira da
rayuwarsa.
Yayin da Rabbasu yayi arba d Hantaru sai ya
murtuke fuska tamkar yaga bakin kumurci
kawai sai ya wuce cikin kogon ya kama haske
haske yana mai duba taswirar hannunsa. Nan
take ya gane wannan rijiya yake nema wato
hanyar fita dag kogon, yace koda na fuskanci
287

TASKARNOVELS.COM.NG
haka sai na koma gefe guda na zauna na zura
masa idanu.
Lokacin da Rabbasu yaga rijiyar sai ya sagale
iccen wutar a jikin garu kamar yadda nayi
sannan ya mayar da takobinsa cikin kube.
Rabbasu ya tsaya akan rijiyar sannan yasa
hannayensa biyu yayi amfani da dukkan
karfinsa domin ya dauke murfin rijiyar, nan fa
jijiyoyin jikinsa suka tashi suka yi birdin burdin,
kwanjinsa suka kumbura, da kyar da sidin goshi
ya daga murfin rijiyar kadan, amman sai murfin
rijiyar ya rinjayeshi kasa dan haka dole ya sake
shi. A wannan lokacin ne na tabbar da cewa
indai batun tsagwaron karfin damtse ne to
Rabbasu ya fini, tunda ni na kasa daga murfin
rijiyar. Abinda kawai nake gani zan iya fin
Rabbasu shine juriyar wahala, naci da kuma
Sa'a.
Rabbasu ya jaraba janye murfin daga bisa rijiyar
amman sai abu ya gagara domin har saida ya
jike sharkaf da zufa kamar yadda na yi a dazu,
bisa dole Rabbasu ya hakura ya koma gefe
shima ya zauna, duk su biyun sai suka zuba wa
rijiyar idanu suna tunanin abinda zai ficcesu.

288

TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam sai muka ji wani irin gurnani na fitowa
daga cikin rijiyar, tunda Hantaru yazo duniya
bai taba jin gurnani irin wannan ba mai matukar
ban tsoro, sannu a hankali gurnanin ya rinka
karuwa ba shiri suka mike tsaye cikin razani
suka ji kamar su ruga wajen kogon amman sai
suka yi ta maza suka tsaya dan suka ko mene ne
wannan abu dake cikin rijiyar. Kawai sai sukaga
an naushi murfin rijiyar daga cikinta, take
marfin yayi sama kamar anyi wurgi da faifai, ya
fada can gefe daya, wani shirgegen dodo ne ya
fito daga cikin rijiyar ya dira a gabansu.
Koda kafafunsa suka taka kasa, sai gaba daya
kogon ya kamar girgiza kamar zai ruguje, ni da
Rabbasu sai muka zama yan mini-mini a gaban
dodon nan kamar an ajiye yan tsaki a gaba
muzuru, Hantaru da Rabbasu suka daga
kawunansu sama suna kallon dodon nan cikin
tsananin kaduwa da tsantsar al'ajabi jikinsu na
kyarma.
Gabadaya jikin dodon a murde yake kuma gashi
da taurin gaske kamar dutse, yana da wani
dogon kaho guda daya a tsakiyar kansa tamkar
na dabbar karakanda, jelarsa kuwa
murtukekeya ce mai tsawon gaske kamar ta
289

TASKARNOVELS.COM.NG
kada, faratan yan yatsunsa kuwa zako-zako
masu tsini da kaifin tsiya, koda Hantaru ya dubi
dodon nan da kyau sai ya jinjina kai ya ce
wannan zai iya halaka dakaru Miliyan dubu a
lokaci guda, hakika yau mun gamu da gamonmu,
dan abune mawuyaci mu fita daga nan.
Koda dodon yayi arba da su Hantaru sai ya daga
kafarsa ya shallakesu ya koma bangaren kofar
da suka shigo ya tare hanya. Nan fa hantaru da
Rabbasu suka dubi juna gami da yin ajiyar
zuciya, duk da cewar a dokar wannan tafiya
tasu, babu taimako juna amman yanzu ya zama
masu dole su hada hannu domin yakar wannan
dodo.
Bayan anyi kallon kallo tsakanin dodon da su
hantaru sai kawai dodon ya wangame bakinsa
mai kama da rijiya ya bushe da mahaukaciyar
dariya wacce ta kara furgitasu sannan yace ya
ku wandannan kananan halittu, kuyi sani cewa
yau kimanin shekara dubu kenan ina gadin
wannan rijiya wacce ita ce hanyar da zaku bi
domin ku shiga kogon Mazabatul Darshal, inda
takobin daraja ta ke, duk mahalukin daya shigo
wannan kogo walau mutum, aljan ko dabba to
sai na zare masa ruhin numfashi, komai yawan
290

TASKARNOVELS.COM.NG
ayarin dakaru muddin suka shigo to sunansu
gawa, ku kuwa wanne tsautsayine ya shigo daku
wannan daji, ko kuwa kuma kunzo ne domin
daukar takobin daraja?
Sa'ad da suka ji wannan tambaya sai Rabbasu
yayi tsuru-tsuru ya kasa cewa komai, shi kuwa
Hantaru sai yayi farat ya ce Ya kai wannan
babbar halitta kayi sani cewa komai na duniya
lokacine, tabbas ka yi sharafinka har tsawon
shekaru dubu, to kayi sani cewa yanzu lokaci
namu sharafin ne, a yau kuma a yanzu zamu
halaka ka, sannan mu shiga cikin rijiyar nan mu
wuce zuwa kogon Mazabatul Darshal mu dauko
takobin Saiful Lujara.
Koda Hantaru yazo nan a zancensa sai dodon ya
sake bushewa da dariya a karo na biyu, wacce ta
haddasa girgizar kogon gabadaya ya kama
tambal-tambal, daga can sai ya tsuke bakinsa ya
dubi Hantaru da kyau yace ai sai na gwada akan
san na kwarai, mu zuba ni da ku asan gwani.
Kafin daya daga cikinsu yayi wani yunkuri, tuni
dodon ya kai masu wani wawan mangari, cikin
zafin namq suka sunkuya hannun dodon ya
bugin kogon, sai dutsen ya fara zubowa kasa,
291

TASKARNOVELS.COM.NG
al'amarin daya firgita su hantaru kenan suka
fara amfani da karfin sihiri, domin su hallaka
dodon amman si sihirin nasu ya ki aiki, nan fa
suka kasa tsere da dodon yana kai masu duka,
mangari da kuma taku da hannu da kafa, duk
inda kafar dodon ya taka sai ya haifar da rami
zururu wanda zurfinsa ya kai kamu arba'in,
fadinsa kuwa yana kai kamu ashirin, nan fa
Hantaru da Rabbasu suka kama tsalle-tsalle a
haka dai suka samu daman naushin fuskar
dodo, amman duk sa'adda suka naushe shi sai
suji kamar dutse suka nausa domin hannunsu
ma sagewa yake, kafin a jima Hantaru da
Rabbasu sun fara gajiya da galabaita, shiko
dodon ko alamar fara gajiya bai yi ba tamkar ma
kara masu kuzari ake.
Ana cikin haka ne dodon ya samu nasarar
damkar wuyan Rabbasu da yan yatsunsa biyu,
nan fa Rabbasu ya hau reto da wutsil-wutsil,
nan fa idanun Rabbasu suka zazzaro suka yi
bulu-bulu ya fara kokarin cire yan yatsun dodon
daga wuyansa amman sai ya kasa.
A wannan lokacin Hantaru ya ruga izuwa can
saman dodon ya hau kan kafadarsa ya dinga
gabza masa sara da takobi a fuska, amman shi
292

TASKARNOVELS.COM.NG
dodon ko kulashi bai yi ba domin ji yake tamkar
susa yake mashi.
Lokacin da Rabbasu yaji zahiri numfashinsa ya
fara daukewa, ya tabbatar da cewa mutuwa zai
yi, sai ya tattaro dukkan karfinsa ya kama dan
yatsa daya na dodon ya finciko shi, nan take dan
yatsan ya fice fit daga jikin hannun, aikuwa sai
jini ya fara bulbula. Dodon ya kurma uban ihu
ba shiri Rabbasu ya fado kasa.
Hakika idan mutum yaga mutuwa babu abinda
ba zai iya ba, Hantaru bai taba tsammanin cewa
Rabbasu zai iya ceton rayuwarsu ba daga
hannun wannan dodon, a wannan lokacin ne
Hantaru ya dada sallamawa Rabbasu, ya tabbar
da cewa ya cika Sadauki uban sadaukai.
Yayin da dodon ya dubi dan yatsansa ya ga jini
na shatata a jikin hannun nasa, sai ya haukace
ya cigaba da kai masu duka da mangari ta ko
ina, haka ya rika makesu suna gwaruwa da jikin
bangon kogon, cikin kankanin lokaci Hantaru da
Rabbasu suka galabaita ainun suka fita daga
cikin hayyacinsu, har ya zamana cewa babu mai
sauran kuzari a jikinsu, sai da dodon ya tabbatar
da cewa yayi masu laga-laga sai ya sunkuya ya
293

TASKARNOVELS.COM.NG
suri Hantaru yayi sama da shi da nufin ya soka
kanshi a cikin bakinsa, cikin matukar zafin
nama Rabbasu ya dauki takobinsa ya dagata
sama tamkar an cillashi daga sama, kafin dodon
ya soka Hantaru a cikin bakinsa tuni Rabbasu ya
fada cikin bakin nasa, cikin tsananin zafin nama
ya zarce zuwa cikinsa yasa wukarsa ya fara
daddatsa hanjin cikinsa. A karshe sai ga shi ya
faso ta duburarsa, kawai sai Hantaru yaga
dodon ya kame wuyansa ya kame ya sake shi ya
fadi kasa, yan dakiku kadan dodon yayi kasa
tim!
Hantaru dai bai san sa'ad da yayi wa Rabbasu
jinjina ba, yace tabbas ka cika Sadauki uban
sadaukai na sallama maka.
Koda jin
End Ads