haka sai Rabbasu yayi wurgi da
takobinsa, ya dubi Hantaru har kwalla ta zubo
masa, yayi shiru bai ce komai ba. Al'amarin daya
sa Hantaru ya dubeshi ya ce da shi ya kai abokin
tafiya ina dalilin zubar wannan hawaye naka?
Rabbasu ya koma gefe daya ya zauna yana haki
bai ce komai ba, daga can sai ya dago kai ya ce
ya kai namijin duniya kayi sani cewa bayan ka
baro ni a baya a inda muka fafata yaki nan,sai da
294
TASKARNOVELS.COM.NG
na jima a kwance kamar gawa sananne n dawo
cikin hayyacina. Ina farfadowa sai na nemeka na
rasa, sai kawai gawar aljanin nan na gani ta rabe
gida biyu.
Nan take na raina jarumtakata, kuma naji
zuciyata ta buga da karfi, tsoro ya shigeni kuma
na fara tunanin cewa abu ne mawuyaci na tsira
da rayuwata a wannan daji na hayatul Maut.
Domin na samu nutsuwa sai na dauki madubin
tsafina na shiga binceke, koda naga abinda
binceken nawa ya nuna mani sai na fashe da
kuka, ba komai na gani ba face bani da sa'a ko
kadan a cikin wannan gasa, kaine da sa'a kuma
tabbas kai zaka karbi kambun wannan gasa.
Cikin bincekena na gano cewa ba zan tsira da
rayuwata ba a cikin wannan daji, kuma a yanzu
haka mahaifina sarkin mafarauta na can a
kwance cikin ciwo, haka ma kakan Salimat duk
su biyun ba zasu rayuwa ba mutuwa zasu yi nan
da yan kwanaki kadan masu zuwa, kaga kenan
ni yanzu babu abinda zan tsira da shi a
rayuwata, na rasa ubana kuma na rasa
masoyiyata Gimbiya Larziyya, wacce tun muna
yara kanana na kamu da tsananin kaunarta,
amman sai ya zamana cewa ta tsaneni kamar
295
TASKARNOVELS.COM.NG
yadda ta tsani mutuwarta, akan haka ne na sha
alwashin sai na aureta ta kowanne hali.
Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa tun da
kuruciyata nake ta shiryeyen wannan gasa,
nayita baiwa kaina horon yaki, tseren gudu da
shanye horon duka, har izuwa lokacin dana cika
saurayi. Yau gashi na wayi gari duk wannan
tanadi da nayi ta zamo a banza, soyayyata ta
kaini izuwa ga halaka, tabbas yanzu na yarda
cewa kaine zaka zamo mijin gimbiya Larziyya
dan haka ina mai kara kara maka gwiywa akan
ka dada jajircewa wajen karasawa cikin kogon
Mazabatul Darshal ka dauko takobin Saiful
Lujara, ni kam tafiyata ta kare anan domin nayi
nadamar zurfafawa a soyayya gashi kuma
soyayya ta kaini ta baroni.
Ya kai abokin tafiya kaima ina mai baka
shawara da ka taka a hankali domin su mata da
kake ganinsu suna da matsari, da wannan furuci
nawa nake maka sallamar karshe gami da fatan
samun nasara bisa abinda ka sa a gabanka. Koda
gama fadin haka sai Rabbasu ya yunkura cikin
zafin nama, ya kama kansa da hannayensa biyu
ya murde wuyansa, nan take kuwa ya fadi kasa
matacce.
296
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin tsananin bakin ciki Hantaru ya ruga
gareshi ya rungume gawarshi ya fashe da
matsanancin kuka, duk da cewa Hantaru ya san
cewa Rabbasu abokin gabarsa ne, amman sai
yaji cewa kamar dan uwansa ne na jini ya mutu.
Nan take hantaru yaji komai na duniya ya fice
daga ransa, ya fara tunanin ya koma da baya ya
hakura da dauko takobin Saiful Lujara. Sai da
Hantaru ya shafe fiye da sa'a guda rungume da
gawar Rabbasu yna ta shara kuka, sannan ya
mike ya haka rami a wajen ya binne gawar
Rabbasu, sannan ya rubuta sunansa da jinin dan
yatsan sa a jikin duwatsun da ya rufe kabarin.
Hantaru ya zauna a gaban kabarin ya shiga raira
baitocin waka, da nuna jinjina da kirari ga
sadauki Rabbasu, yana wakar yana zubar da
hawaye har izuwa lokaci mai tsawo sannan ya
mike tsaye ya tafi izuwa cikin wannan rijiya
yana mai waigen kabarin Rabbasu yana cigaba
da hawaye a haka har ya shige cikin rijiyar. Da
shigar Hantaru cikin rijiyar sai kawai ya tsinci
kansa a cikin wani makeken kogon dutse,
wanda yafi wanda ya baro girma, tsawo da fadi
sau uku, a cikin kogon akwai rijiyoyi guda dubu
kowacce rijiya rufe take ruf da makulli, nan fa
Hantaru ya kura wa rijiyoyin idanu yana
297
TASKARNOVELS.COM.NG
ayyanawa a ransa cewa lallai takobin Saiful
Lujara na cikin daya daga cikin wadannan
rijiyoyi, abin tambaya anan shine a cikin wace
rijiya takobin take? Kawai sai Hantaru ya yanke
shawarar bude rijiyoyin daya bayan daya, nan
take ya tunkari rijiyar farko gadan-gadan.
Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu, hakika inda
hantaru yasan abinda zai biyo baya da ya
hakura da bude wannan rijiya ta farko. Lokacin
da Hantaru yasa takobinsa ya sare kwadon dake
jikin wannan rijiya ta farko sai kawai yaga wata
mutukekiyar macijiya ta taso sama, macijiyar na
da kawuna saba'in da daya, girman ko wane kai
daya ya kai na katuwar bishiyar kuka. Kafin
hantaru yayi wani yunkuri tuni kawunan
macijiyar nan guda saba'in da daya sun fasa kai
sun gabza masa sara a sassan jikinsa ko ina da
ina.
Nan take wani irin dafi ya shige shi, jikinsa ya
kama kakkarwa, kafin a jima ya jike sharkaf da
zufa tamkar an tsamoshi daga cikin kogi.
Hantaru ya sulale kasa magashiyyan kuma
jikinsa ya cigaba da kakkarwa kuma ya fara
kakarin mutuwa lokacin da wata irin kumfa ta
fara dalala daga cikin bakinsa.
298
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk wannan abu dake faruwa macijiyar na
tsaye akansa, ta zubo dukkan kawunan nasa a
kansa, tana kallonsa kawai kamar jira take ya
mutu ta cinye shi. Daga can sai ya sandare ya
daina motsi, sannan ne macijiyar ta kara
sakkowa da kanta kas da niyyar ta hadiye
Hantaru.
Ba zato ba tsammani sai kawai macijiyar taga
numfashin Hantaru ya dawo, nan take ya
amayar da duk wani dafi data saka mashi,
wanda ya kasance bakikkirin kamar an jika
shuni.
Cikin zafin nama macijiyar nan ta wangane
bakinta gabadaya dan ta hadiye Hantaru,
amman sai ya rikede ya zama katon dutse, duk
da haka sai da macijiyar ta hadiye dutsen.
Koda sarki Dujalu ya zo daidai nan a labarin da
yake baiwa yar uwarsa Gimbiya Hursiyya sai ya
fuskanci cewar dare ya raba sosai, dan haka ya
kamata su kwanta suyi bacci, amman bisa
mamaki sai yaga idanun Hursiyya a kafe babu
alamar jin bacci a cikinsu. Sarki Dujalu yayi
shiru ya kafa mata idanu kawai yana murmushi.
299
TASKARNOVELS.COM.NG
Gimbiya Hursiyya ta dubeshi cikin matukar
damuwa ta ce haba ya kai dn uwana, sabida me
zaka katse mani wannan labari, na rokeka dan
girman iyayenmu daka karasa mani wannan
labari domin naji yadda sadauki Hantaru yake
dauko takobin Saiful Lujara, kuma naji yadda zai
auri gimbiya Larziyya, sannan na ji yadda
karshen rayuwarsa zata kasance a tafarkin
soyayya.
Haka kuma ina son jin yadda rayuwar sarki
Kusaidu zata kasance da boka Ardusa, da Zarifa
ma'abota cin amana.
Lokacin da sarki Dujalu ya ji haka sai ya bushe
da dariya ya ce yake yar uwata kiyi sani cewa a
halin yanzu dare ya raba sosai, idan har zan
cigaba da baki wannan labari har gari ya waye
ba zai kare ba, zai fi kyau kiyi hakuri sai wani
lokaci idan mun sake yada zango a wani wurin
sai mu cigaba.
Alkawarin da zan yi maki shine zanyi kokari na
gama baki labarin sadauki Hantaru sannan mu
shiga labarin Sadauki shaddar na birnin Kufa,
wanda yama fi labarin Hantaru ban tausayi da
ban al'ajabi.
300
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin mamaki Hursiyya ta ce haba ya dan uwana
ya za ayi a samu labarin da ya fi na Sadauki
Hantaru ban tausayi da ban al'ajabi, ka sani
cewa tunda ka fara wannan labari nake zubar
da hawaye har ka tsaya ban daina ba.
Sarki Dujalu yayi murmushi yace aikuwa idan
kika ji labarin Sadauki Shaddadu sai hawayen
idanunki ya kare saboda zuba. Yanzu sai ki tashi
ki tafi izuwa cikin tantinki na sallameki.
Cikin sanyin jiki Hursiyya ta mike tsaye ta fita
daga cikin tantin sarki Dujalu, shi kuwa sai ya
kwanta bisa shimfida ya mike kafafunsa ya
kama aikin rago.
Me zai faru idan rundunar mayaka ta sarki
Maharaz da ta sarki Dujalu suka hadu a bakin
gabar tekun Bahar Suffiyya dan dauko takobin
Saiful Lujara?
TASKARNOVELS.COM.NG
Ta yaya Sadauki Hantaru zai dauko takobin
daraja a kogon Mazabatul Darshal?
Wadanne irin abubuwan al'ajabi dana ban
tausayi, da kuma jarumtaka ne a cikin labarin
Sadauki Shaddadu na birnin Kufa da Sadauki
Hulkas na birnin Romaniya?
Marubucin yace mu hadu a Littafin mazan jiya
Littafi na biyu.
302
TASKARNOVELS.COM.NG
303
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng