suko birurrakan sunyi
matukar mamaki domin basu taba haduwa da
shaidanin mutum irin hantaru ba, haka dai aka
cigabada wannan fafatawa har tsawon sa'a daya
shibai nakasa suba kuma bai kashe koda daya
daga cikinsu ba ka suma basu hallakashiba tuni
shumilat ta acikada tsananin mamakin bisa
ganin jarumtakar hantaru domin bata taba
tsammanin yakai hakaba babu abinda ya bata
mamaki kamar yadda birurrukan nan suka kasa
kai shi kasa wani lokacin har dandaxo sukeyi
waje guda su tafo da gudu domin su hallakashi
amma sai kaga ya tokare su ya watsasu. lokacin
da hantaru yaga cewa lallai idan kara sa'a daya
ana wannan gumurxun zasu iya samun nasara
163
TASKARNOVELS.COM.NG
akanshi saiya chanza salon fadan kawai sai ya
dinga kama hannayensu da kafafunsu yana
cisgewa saidai kaga jini na tsartuwa na feshi nan
birurrukan suka dinga kururuwa suna zubewa
kasa a mace.. wohohoho!! maza maganin maza
hakika birurrukan nan sunga bala'i domin kafin
su ankara hantaru ya kashe samada guda duba
biyar daga cikinsu saida takai birurrukan sun
fara jada baya kai da sukaga abin yafi kafinsu
rugawa sukayi cikin kogunan koda ganin haka
hantaru ya yunkura da nufin yabisu cikin kogon
dutsen sai shamilat ta gargadeshi kada ya bisu
cikin kogon dutsen nan domin kowa a gidashi
sarki ne, ka kyalesu kawau mu cigaba da
tafiyarmu ai nasan ba zasu sake biyomu ba
domin sun tsaga basuga jini ba.
Hantaru yayinkwafa sannan ya ce kash!
Ummina naso ki kyaleni na cigaba da yaki da
burirrikan nan har sai naga babu dayansu da ya
rage mai numfashi.
Shamilat ta yi murmushi ta ce na gaisheka dana,
hakika ina farin ciki da samunka domin ayau ne
nasan cewa ina da namijin duniya kuma jarumin
jarumai.
164
TASKARNOVELS.COM.NG
Hantaru ya ce ai dukkan godiya ta tabbata a
gareki da kika zama uwata na sha nononki har
ya zama garkuwa a gareni. Hakika dole ne nayi
alfahari da zuri'arki domin ina ganin cewa
sadaukarnan tawa a wajensu na gadota.
Shamilat ta sake yin murmushi ta ce tabbas
mahaifina gawurtaccen jarumi ne na gaske mai
tarwatsa maza a filin daga ina ganin cewa shi ka
gado kuma gashi har ma ka fishi yarinta.
**********************
Mazan Jiya Part 16
Labarin Sadauki hantaru mai takobin #saiful
lujara na mazan jiya
#Cigaba
165
TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin shumilat ta rufe bakinta sai sukaji sautin
taku daga cikin kogon dutseo nan tamkar sawun
giwa koda hantaru da shamilat suka waiga nan
take hantaru yayi arba da abinda yarazanashi
yayi matukar firgitasu ba wani suka ganiba sai
wani katoton gwaggon biri wanda girmarsa ya
ninka na wadannan birurru kan sau biyar katon
goggon birin nan ya dunfafo inda su hantaru ya
yana tafe yana nishi da gurnani takun tafiyar
tasa na haddasa karamar girgixar kasa koda
ganin haka sai shamilat ta kara rudewa tana mai
jan hantaru tana cewa zomu gudu yakai dana
tabbas bazaka da wannan birin ba hantaru ya
cije ya tsaya cak sannan ya dubi shamilat yace ai
faduwar gaba asaran namiji ce kede kijada baya
ki zuba ido kiga abinda zai faru a rude shamilat
ta juya ta labe a bayan wata bishia tana leke
sukuwa birurrukan sai suka haukan duwatsu
suka zuba idanu domin suga abinda zai faru
tsakanin hantaru da shugabansu asannan ne
hantaru ya gane cewa wannan narkeken birin
shine shugabansu kuma yaransane sukaje suka
kirawo shi a fusace shugaba birurrukan yayi
kan hantaru lokacin da sauran yaran nashi suka
fara wani irin gurnani runa mai mishi kirari
kawai sai hantaru ya dunkule yan yatsunsa ya
166
TASKARNOVELS.COM.NG
gyara tsayuwa, cikin shammaci birin ya
gabzawa hantaru naushi a fuskanshi saboda
karfin daushin saida hantaru yayi sama ya fado
kasa kuma jini yayi tartsuwa daga bakinshi har
hakorinshi guda ya fadi akasa take hantaru ya
tashi a fusace zuciyarshi ta fara tafarfasa koda
ganin haka sai sauran birurrukan ruka fara ihu
suna shewa saboda nasarar da shugabansu
yasamu akan hantaru alamarin daya kara fusata
hantaru kenan baxato ba tsammani hantaru ya
daka tsalle ya gabza mishi naushi a kasan cibiya
kawai sai akaga birin ya kame kamar an zare
duka lakar jikinsa nan take kuwa ya sulale kasa
ko shurawa bai sakeyi ba hantaru ya daga kai
sama ya dubi birurrukan na ya kwarara uban
ihu nan take suka tarwatse suna masu
fantamawa cikin daji batareda sanin inda xasu
tsayaba, Kaicon inbada wuyya ta kai wuya ya za
ayi wadannan muggan burirrikan har su guje
wa biladama guda daya jal.
Bayan birurrukan sun gudu sai shamilat ta fito
daga bayan bishiyarda take ta rugo da gudu
cikin farin ciki tana mai cewa hakika yau kayi
bajintar da bayantaba mancewa da itaba suka
rungume juna daga can sai shamilat da dauki
167
TASKARNOVELS.COM.NG
takobin Hantaru ta sare kan wannan birin ta
cire a cikin wani icce.
Koda ganin haka sai Hantaru ya dubi mahaifiyar
ta shi ya ce da ita ya ke ummina me kuma zakiyi
da kan wannan birin?
Shamilat tayi murmushi ta cw da shi ai d shi zan
tafi, kuma zanyita ajiyar kokon kan wannan
birin har iya tsawon rayuwata, domin abun
tarihi ne wanda har abada bai kamata a manta
da shi ba, ya dana kayi sani cewa kayi
gagarumar bajinta wajen kashe wannan buri.
Nan de hantaru da shamilat suka yada zango
suka kunna wuta suna jin dumi saboda sanyin
dake kadawa. kashegari da safe suka kada
rakumansu sukayi gaba su hantaru suka cigaba
da ratsa dazuzzuka iri iri a ranar kwana na
goma sha biyar ne suka shigo cikin daji mai
girman gaske abinda ya fara daukan hankalin
hantaru shine gaba daya harabar dajin komai
tsab yake babu kazanta a ko ina, sannan ga
kuma wata irin iska mai ni'imah na kadawa
koda ganin wannan wuri sai murna ta kama
hantaru ya yunkura zai sauko daga kan dokinsa
ba caraf! sai shumailat ta rike hannunsa tace
168
TASKARNOVELS.COM.NG
kadaka sauka yakai dana wannan daji baza'a
rasa aljanu acikin saba hantaru yayi murmushi
yace yake ummina inaso kisani cewa wahala ga
da namiji ibada ce, haka kuma tsoro tsanani ne
na hallaka da rashi.
Koda gama fadan haka sai hantaru ya sauko
daga dokinsa ya xare takobinsa ya rike linzamin
dokin ita kuwa shamilat saita dinga binsa abaya
a hankali tana wauge-wauge kwatsam sai
hantaru yaga wani katon lambu a gabansa
wanda ke cike da yayan itatuwa iri-iri kamar su
tuffa, inibi, fasa dabur dadai sauransu, bazato ba
tsammani sai yaga wata yarinya budurwa
kwance akan wata shimfida tana cin tufa fuskan
a cike da annuri a iya rayuwar hantaru bai taba
ganin mace mai kyan taba amma abin takaici
daya dubi kafarta sai yaga kofato koda
kyakyawar ta kalli hantaru rai ya kauda kai yaje
ya sai ya kaufa fuska yaje ya tsinki tufa guda
daya ya fara ci, alamarin dayabawa budurwar
mamaki kenan ta bishi da kallo cikin takaici ta
kuma shumailat rai taki shiga cikin lambun
alokacin da hantaru yagama cinye tafar kawai
sai yaji an rike hannunsa bawata bace face
wannar budurwar daya wuce kwance,budurwar
ta dubeshi cikin fushi tace haba bil'adama ka
169
TASKARNOVELS.COM.NG
shigo lambu na babu sallama ka tsinki tuffata ka
cinye. sa'adda hantaru yaji wannan sai kunya ta
kamashi domin yasan baiyi da'a ba kuma bai
nuna shi dane mai tarbiyya ba, cikin sanyin
murya ya dubi budurwar yace yake wannan
ma'abociyar kyau ki gafarceni hakika nayi
kuskure amma ki sani kayan marmarin dake
cikin lambun sunada daukan ido. budurwar ta
bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace
hakika kude bil'adama da rashin hakurh kuke to
kasani cewa kaciwa kanka bala'i domin abune
mawuyaci ka tsira da rayuwar ka ina yimaka
albishir cewa ka fado cikin tarkon uwar mayu ta
aljanu koda gama fadin hakan sai budurwar ta
rikide ta dawo wata tsohumaw mummunar
aljana mai matukar ban tsoro hantaru ya
yunkuri da nufin ya kaimata sara sai yaji cikinsa
ya murde ya fara ciwo kafin cikan dakika biu ya
fara aman jini nan take fadi kasa sumamme.
Koda shumailat taga abinda ya faru da hantaru
sai itama ta fadi kasa sumammiya. lokacin da
shumila ta farfado daga dogon suman datayi
saita tsinci kanta acikin wanin irin gida an
daureta da wata katuwar sarka shide wannan
gida an gina shine da zallan duwatsun wuta
kuma babu komai acikinsa face wata katuwar
170
TASKARNOVELS.COM.NG
tukuba wacce aka hada guma guman itatuwa
suna taci da wuta saman wutar an daura wani
gado yayi jawur. kwatsam sai shamilat ta jiyo
hayania daga can bangaren yammacin gidan
sannu a hankali ya ringa karuwa yana cika
dodon kunne daga can saiga dandazon wasu
yayan aljanu sama dasu million 40 sun taho da
gudu suna tsalle a tsakiyar su wannan
mummunar aljanan ne dauke da hantaru su
duka suka tunkaro inda tukubar wuta take koda
ganin haka sai shamilat ta fahimci cewa cikin
wannan gadon wuta aljanar nan zata daura
hantaru shamilat ta kurma ihu tana kuka tana
mai rokon aljanar kadata kona mata danta
aljannar bata dubi shamilat ba saida suka iso
dab da wutar sannan ta tsaya cak tana kyalkyala
daria tace yake wannan bil'adama kiyi sani
cewa idan ban gasa wannan danaki ba na baiwa
yayana sunci duk mutuwa zasuyi ayau. kuma
basu iya haura kwana 40 batareda sunci naman
bil'adama ba kinga kuwa da bai fi ɗa ba.
Kodajin haka sai shumilat ta fashe da kuka,
aljanar ta sake bushewa da dariya a karo na biu
tace ai gara kisha kukanki ki more kafin na
dawo kanki domin idan na gasaki ni kadai zanyi
walimanki domin yayana basa cin nama mace
171
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin tsananin fushi shamilat ta dubi aljanar tace
tir dake wannan la'ananniar maiya inda dana
acikin hayyacinsa yake dakin raina kanki domin
baki isa kiyi masa komai ba sa'adda aljannar taji
haka sai ta bushe da daria sannan ta dakawa
shamilat tsawa tace ke bil'adama kiyi sani cewa
agaban sarauniyar mayun aljanun duniya kike
babu wani mahaluki daya isa ya hallakani sa'ar
ki daya mijina baya nan ya tafi farautar
bil'adama dayanzu kema mun gama dake
dolene na hakura sai yadawo domin akwai yajin
dazai tafo mana dashi wanda muke jin dadincin
naman bil'adama dashi.
********************
Mazan Jiya Part 17
Labarin Sadauki Hantaru mai takobin saiful
lujara na Mazan Jiya
#Cigaba
172
TASKARNOVELS.COM.NG
Gama fadin hakan keda wuya sai uwar mayu ta
yunkara zata daura hantaru akan gadon wutan
bazato ba tsammani sai sukaga hantaru ya mike
zumbur ya daka tsalle sama daga kan tafin
hannun ta kafin takai masa cafka cikin zafin
nama ya gabza mata naushi a idon ta take
hannun nasa ya burma cikin kwarmin idanun
nata, koda ya zaro hannun nasa saiga kwayan
idanun nata ya fado kasa nanfa jini ya kama
feshi uwar mayu takama kururuwa tana katan
tanwa saboda tsananin zafi da takeji a cikin
idanun ta yayin da yayan uwar mayu sukaga
abunda yafaru da mahaifiyarsu sai sukayi caa
akan hantaru da nufin su yayyaga shi su cinye
shi danye abinda basu saniba sun gamu da
gamon su maimakon sadauki hantaru yayi
amfani da takobin sa wajen yakar su sai yayi
wurgi da takobin sa ya afka musu yadinga
cafkar wuyan su yana gwara kawunan su nanfa
kafun a jima hantaru ya hallaka sama da guda
dubu dari a daidai wannan lokaci ne uwar mayu
tadawo hayyacin ta koda taga mummunar
barnar da hantaru yayi mata saita fusata ta
runtuma sabon ihu da kukan bakin ciki shi
kansa hantaru saida ya razana sakama kon jin
sabon ihun datayi suko sauran yayan nata
173
TASKARNOVELS.COM.NG
dasuka rage sai suka ruga izuwa bayanta suka
tsaitsaya uwar mayu ta tunkari hantaru da
mugun nufi shima sai ya tunkaro ta bada jin
tsoron komai ba koda ya rage baifi taku goma su
gamu sai hantaru ya ruga da gudu yayi tsalle
sama yakai mata wawan naushi da nufin ya fasa
daya idon cikin zafin nama uwar mayu ta kade
shi da hannunta take hantaru ya maku da dirkar
gini ya fado kasa a matukar galabaice koda uwar
mayu taga hantaru a kasa ya kasa tashi saita
rugo da gudu ta daga kafar ta sama ta kawo
masa wawan taku da nufin ta mutsuke shi cikin
zafin nama hantaru ya goce saboda karfin takun
saida kafar uwar mayu ta nutse cikin kasa har
gwuiwan ta uwar mayu ta zare kafar da sauri ta
cigaba da kaiwa hantaru taku yana gocewa
kafun ajima harabar gidan ya cika da ramuka ita
kanta uwar mayu saida ta gaji ainun takama
haki a sannan ne hantaru ya samu ya mike tsaye
aiko sai suka kasa tsere ta dinga binsa tana kai
masa cafka tana wangame baki domin ta hadiye
kansa gabadaya aduk sa'adda ta karta mashi
farata a jikin shi saidai taji kamar ana karta
takobi akan dutse kuma ko korzanewa bayayi
cikin dakika kadan gidan ya hautsine hankalin
kowa ya dugunzuma domin gunguma
174
TASKARNOVELS.COM.NG
gunguman duwatsu ne na wuta ke fadowa kasa
su kansu yayan uwar mayu saida suka firgice
suna neman mafaka itako shamilat tuni dirkar
da'aka daure ta a jiki ta karye ta fadi sannan
wani katon dutse ya fado akan dirkar lokacin da
hantaru ya waigo yaga halin da shamilat ta
shiga sai hankalin sa ya dugunzuma sabona
yasan cewa idan ta dade a kasan wannan katon
dutse na wuta kasa zata iya zaftarewa a wannan
lokaci ne hantaru ya fusata don haka saiya daina
gudun yama tsaya cakk awaje daya yana
sauraron isowar uwar mayu gareshi koda uwar
mayu taga hantaru ya tsaya cak ya daina guje
guje sai murna ta kamata domin tasan cewa
yanzu zata hallakashi bada bata lokaci ba kawai
saita durfafe shi da dukkan karfinta cikin bakin
zafin nama da isowar ta dabb dashi saita kawo
masa wawan cafka da hannayen ta guda biyu
cikin tsananin zafin nama hantaru ya sunkuya
kasa ta kama iska kafun ta sake kai masa hari
tuni daka tsalle ta cikin karkashin kafafun ta ya
zagayo bayanta ya sake daka tsalle kafun ta
waigo ya dira akan kafadar ta ya gabza mata
naushi acikin kunnen ta aiko sai hannun nashi
ya lume acikin kunnen ya futo ta cikin daya
kunnen yana zare hannun jini yakama feshi take
175
TASKARNOVELS.COM.NG
uwar mayu ta sulale kasa matacciya a matukar
galabaice hantaru ya durshe kasa bisa
gwuiwoyin sa saboda tsabar wahala a sannan
ne ya lura cewa guma guman duwatsun wuta
dasuka yita fadowa daga saman ginin sun
hallaka gabadaya yayan uwar mayu dayan su
bai tsiraba da rayuwarsa hantaru na durkushe
yana haki sai kawai yajiyo ihun shamilat daga
can kasan wannan katon dutsin daya danne
dirkar ginin da'aka daure ta a jiki cikin zafin
nama hantaru ya yunkura da saurin gaske ya
ruga wajen ya kaimata dauki wani irin takun
sawu mai karfi da hantaru ya jiyo a bayansa
shine tsaida shi ya juya a firgice aiko sai yayi
arba da wata jibgegiyar halitta mai tsananin
kwarjini daban tsoro da muni bakomai ne
wannan halitta ba sai mijin uwar mayu ya dubi
yadda gidan sa ya rugurguje sannan ya hango
gawar uwar mayu a can gefe daya can kuma
saiga gawarwakin yayan sa kota ina kawai saiya
takarkare ya kwarara ihu karar ihun tamkar ana
ruwan kwaran kwatsa daga sama ak'amarin
daya kara razana hantaru kenan musamman
daya karewa mijin uwar mayu kallo sama da
kasa ya tabbatar dacewa ruwa ba sa'an kwando
bane a wannan lokacin ne kuma shamilat ta
176
TASKARNOVELS.COM.NG
cigaba da kwala ihu ashe dutsen daya danne
dirkar da take jiki ne yake kara dannawa kasa
nan fa hankalin hantaru ya rabu gida biyu ya
rasa abinda ya kamata yayi shin mijin uwar
mayu zai fuskanta suyi yaki koko wajen
mahaifiyar sa shamilat zaije ya ceto rayuwarta
harya yunkura zai ruga wajen shamilat sai yaji
an shako wuyan sa ta baya koda ya kama abun
daya shake shi sai yaga ashe wata irin doguwar
bulala ce mijin uwar mayu ya jefa mishi ta shake
shi a wuya kuma ta shake shi ne ainun ya kasa
cire ta mijin uwar mayu yafara janyo bulalar
nan domin ya kawo hantaru gaban sa shiko
hantaru saiya fara cijewa da dukkan karfin sa
domin yasan cewa muddin ya kuskura yaje
gaban sa ya damke shi saidai kuma mahaifiyar
sa ta haifi wani amma shi tasa ta kare hantaru
ya cigaba da cijewa amma saboda mijin uwar
mayu yafi shi karfi nesa ba kusa ba saiya dinga
jansa gabadaya al'amarin daya dugunzuma
hankalin hantaru kenan ya saduda domin yasan
cewa kwanan sa yazo karshe.
******************
Mazan Jiya Part 18
177
TASKARNOVELS.COM.NG
#Cigaba
A lokacin daya rage baifi saura taku biyar ba
mijin uwar mayu ya cafi hantaru da hannun sa
sai wata dabara ta fadowa hantaru ya tuno da
wata wuka dake sakale a bayansa cikin hanzari
ya zaro wukar ya yanke wannan bulala data
shake shi ya fada baya koda mijin uwar mayu
yaga bulalar sa ta yanke sai yayi jifa da ita ya
zare wani katon sungumi dake sakale a cinyar
sa ya ruga izuwa kan hantaru suka kacame da
sabon azababben yaki mai ban tsaro da ban
al'ajabi wohoho!! tashin hankali ba'a saka maka
rana saida hantaru da mijin uwar mayu suka
kwana suka tashi suna fafata yakin bala'i hatta
kasa tasha azaba domin saida mijin uwar mayu
ya ratattaka komai dake cikin gidan nan da
wannan katon makamin dake hannun sa tunda
hantaru yazo duniya bai taba shan bakar wahala
ba irin ta wannan lokaci sau bakwai yana suma
a wannan fafatawa dayayi da mijin uwar mayu
amma kafun mijin uwar mayu ya zaro shi daga
cikin karkashin kasa ya karisa kashe shi saiya
178
TASKARNOVELS.COM.NG
farfado su cigaba da gumurzu saida yazamana
cewa hantaru ya samu karaya tara a jikin sa
amma bai fasa yaki ba.
Itako shamilat tuntuni ta suma ta nutse a cikin
karkashin kasa batama san abunda dake faruwa
ba ana cikin wannan gumurzun ne mijin uwar
mayu ya samu nasarar yiwa hantaru wani irin
wawan naushi a fuska nan take numfashin
hantaru ya dauke ya baje kasa ko motsi bai sake
yiba mijin uwar mayu ya tsaya cakk yana haki
kuma ya kurawa hantaru idanu domin yagani ko
zai motsa a wannan lokaci shima mijin uwar
mayu duk jikin sa raunuka ne jini na zuba har
jiri na diban sa yana layi tsawon dakika dari
shida da sittin hantaru bai motsa ba. don haka
sai mijin uwar mayu ya tabbatar dacewa ya
mutu amma duk da haka hankalin sa bai kwanta
ba saboda bai taba ganin bil'adama hatsabibi
mai tsananin jarumtaka da naci da taurin rai
tamkar hantaru ba, nan take mijin uwar mayu
ya nufi kan hantaru kai tsaye da nufin ya cizge
kansa da karfin tsiya ya cinye, koda yazo dabb
dashi ya raba kafafun sa akan hantaru kuma ya
sunkuyo da nufin ya kama kansa sai kawai yaji
hantaru gabza masa naushi a ido, take hannun
hantaru ya burma ta kwarmin ido ya fito ta keya
179
TASKARNOVELS.COM.NG
take mijin uwar mayu ya fadi ta baya tamkar
giwa uku sun fadi a kasa, lokaci guda.
Da kyar da jan jiki hantaru ya isa inda dutsen
nan ya danne shamilat hantaru yayi amfani da
dukkan karfin damtsen sa ya dago dutsen
sannan kuma ya shiga zaro wannan dirkar gini
wadda ta nutse cikin karkashin kasa kuma
shamilat take daure a jiki saida yasake shan
bakar wahala sannan yasamu ya dago dirkar
yana gama zaro dirkar yaga shamilat a
mimmike babu abinda ke motsi a jikin ta nan
hantaru ya kurma ihu kuma ya fashe da kuka
domin a zaton sa ta mutu, wani iko na Allah sai
hadari ya gangamo adaidai wannan lokaci nan
da nan aka kece da ruwa, koda ruwa ya daki
shamilat saita farfado a wannan lokaci kan
hantaru na sunkuye yanata rusa kuka, kwatsam
sai yaji shamilat tayi tari cikin zafin nama
yadago kai koda yaganta a raye ya matsa gareta
ya rungumeta duk su biyun suka fashe da kukan
farin ciki.
Saida su hantaru suka kwana arba'in a cikin
wannan busashen gida na uwar mayu suna
jinyar cikin su sannan sukayi shiri suka cigaba
da tafiya, sannu sannu bata hana zuwa sai dai a
180
TASKARNOVELS.COM.NG
dade ba je ba tunda su hantaru suka bar
wannan daji dayayi mugun yaki dasu uwar
mayu basu sake gamuwa da wani abu ba daya
wahalar dasu har suka iso birnin darul habur da
la'asar su shamilat suka shigo cikin birnin darul
habur tundaga bakin kofar birnin shamilat ta
cika da tsananin mamaki domin komai na garin
yana nan kamar yadda tasan shi shamilat da
hantaru suka yita kalle kalle suma suka zamo
abun kallo a matsayin su na baki lokacin dasuka
ratsa ta cikin kasuwa da makera sai hantaru
yadinga ganin zaratan jarumai masu kirar karfi
sunata kera makamai iri-iri wasu kuma sunata
baiwa kansu horon kokuwa da gudu, daganin
wadannan zaratan jarumai sai hantaru yasha
jinin jikinsa yasan cewa lallai ya shigo nahiyar
sadaukai inda sai yayi da gaske jarumtakar sa
zata kwace shi, domin bai taba ganin samari
masu girma da tarin kwanji