x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - MAZAN JIYA 1

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 205

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
a cikin
wata tsohuwa rijiya gaba-dubu (1000) dake can
karkashin wani kogi dake birnin sin, itadai
wannan rijiya duk duniya babu mahalukin dazai
iya shigarta sai ni da abbana mu kadai, tabbas
zanje na tono wannan asiri amma sai idan kayi
alkwarin cewa zaka hada karfi da karfe dakai da
danka imnal ku dauko takobin saiful lujara da
mashin galilul haras da kuma hular lamsara kun
bani su a hanuna, ina tabbatar maka dacewa
bincikena ya nuna min cewa sarki dujalu da
sarki maharaz bazasu iya dauko wayennan
55

TASKARNOVELS.COM.NG
makaman ba amma kaida imnal zaku iya,
lokacin da aljana luzaira tazo nan a zancen ta sai
hankalin hibru ya dugunzuma daga can saiya
dago kai ya dubi luzaira yace wato de yanxu
bangare ukune suke son mallakar wayan nan
kayan yaki na #mazan jiya bangare na farko
shine sarki dujalu sai sarki maharaz sai na uku
kuma keda abban ki, abinda na fahimta shine
idan muka samu nasarar dauko wadannan
makamai nida dana muka damka miki zaki
rikesu ne amfanin kanki ke kadai koko zaki
kaiwa abban ki? Kuma tambaya ta biyu agareki
itane shin kina nufin mai girma darbuza bai san
da zuwanki ba, kuma baisan duk abun dake
faruwa tsakanin mu? yayin da aljana luzaira taji
wadannan tambayoyi saita bushe da dariya
sannan ta murtuke fuska tace yakai sadaukin
zamani kayi sani cewa duk wani boka da amsa
sunan sa bashida wani burin da yuce ya mallaki
wadannan makamai na Mazan JIYA, karshe
kuma batun aljani darbuza shin yana gani koh
yana jin mu bai tasoba sbd idan yanada ikon
ganina da banxo ba domin bazai taba bari nayi
hulda dakuba.
Sa'adda aljana luzaira taxo nan a zancen ta sai
sadauki hibru yayi shiru yana tinani kansa a
56

TASKARNOVELS.COM.NG
sunkuwe sannan ya dubi can inda ke daure a
sama yaga ya sake suma na biyu, sai takaici da
bakin ciki yasake mamaye zuciyar sa cikin
karfin hali ya dubi aljana luzaira yace ki tafi sai
bayan mun fito daga wannan yaki ki dawo
izuwa gareni kiji amsar dazan baki idan zakizo
kijo min acikin tsakar dare, koda fadin haka sai
ya mike tsaye ya kwashe shimfidar sa ya nufi
hanyar dazata kaishi gidan shi ko sau daya bai
sake waiwayowaba balle yaga halin da imnal ke
ciki. Bayan tafiyan hibru sai aljana luzaira ta
tashi sama taje daidan fuskar imnal ta hura
mishi iska a bakin ta wadda tasa gashin kansa
ya tarwatse yana kadawa acikin iska tamkar ana
guguwa mai karfi take imnal ya farfado yana
mai ajiyar numfashi aiko yana bude idanun shi
sai yayi arba da luzaira ta kura masa idanu tana
murmushi babban abun mamaki shine duk
ciwon dayakeji ajikinsa ya gushe haka yunwa da
ishirwa ma duk sun gushe batare da fargabar
komai ba imnal ya dubi aljana luzaira yace
wacece ke? kuma menene ya kawoki wajena?
ina mai rokonki da kadakiyi kokarin fitar dani
daga cikin wannan halin danake ciki.
Koda jin haka sai aljana luzaira ta bushe da
dariya ta tankwashe kafafunta tamkar tana
57

TASKARNOVELS.COM.NG
zaune a kasa bisa buzu ta fiskanci imnal sosai
sannan tace yakai jarumin gobe kayi sani cewa
lbrn yana tsawo amma idan kanaso kasan ni
wacece ka tambayi abbanka bayan ka kubuta ka
tambayeshi lallai ni mai amfani ne ga cigabar
rayuwar Ku ina mai yimaka sallama yakai
jarumin gobe sai gani na biyu in mun sake
saduwa, gama fadin hakan keda wuya sai aljana
luzaira ta bace bat kaman bata wanzuwaba
awajen.
Bayan Kwanaki uku fadar sarki maharaz ta cika
ta batse bakomai ne ya haddasa haka ba face
ayau ne za'a dugunzuma bakidaya dakarun
birnin dana sauran kasashe makwabta wadanda
aka gayyato saboda yin gagarumar tafiya izuwa
kogin bahar sufiya don dauko takobin Saiful
lujara saboda yawan jama'ah da kyar sadauki
hibru ya kutsa ta cikin jama'ah ya isa inda aka
daure imnal da zuwa sai ya iske imnal lafiya
kalau acikin hayyacin sa, kuma babu yunwa ko
ishi atare dashi cikin hanzari hibru ya hau kan
wannan dogon mumbari ya kunce igiyar data
daure hannayen imnal sannan ya sabo shi a
kafada ya sauko kasa, gabadaya dandazon
jama'ar dake wajen suka zubawa hibru idanu
duk inda yabi sai kaga ana darewa ana bashi
58

TASKARNOVELS.COM.NG
hanya ana masa jinjina da kirari domin ansan
yaune rana irin tasa wato ranan dazai jogaranci
rundunar mayaka izuwa yaki, dayawa daga
cikin mutanen garin sunyi bakin cikin hukuncin
da aka yankewa imnal dan hibru kuma sun san
cewa imnal gwarzon mayaki ne wanda ake
takama dashi yanzu gashi raunata shi a
lokacinkirari daza tafi yaki a lokacin da akewa
hibru da dansa kirari ne sarki maharaz da yar sa
suka fito daga gidan sarauta, nan fah kallo ya
koma kansu kowa ya zuba musu ido cikin
matukar mamaki bakomai ne ya haddasa
mamakin ba sai ganin irin shigar da sarki
maharaz yayi dakuma irin wacce mulaifa tayi
dukansu sun sanya jajayen sulke sun rataye
takuba a bayansu komai na jikin su jane hatta
dawakansu kowa yasan sarki da mulaifa basu
kasance mayaka ba amma ansan cewa sarki
maharaz kasurgumin matsafi ne, lokacin da
hibru ya isa inda dokin sa yake saiya zaunar da
imnal a kasa ya jingina bayansa a jikin gini ya
bude wata jaka ya fiddo da garin magani ya
mika masa sannan yace karbi wannan ka shanye
ya kai dana domin raunukan sudaina maka zogi,
imnal ya dubi hibru cikin murmushi yace ya
abbana ai babu inda yake min ciwo a jikina
59

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma ko kadan bana jin kishirwa da yunwa
koda jin haka sai hibru ya dubi imnal cikin
mamaki yace menene ya kawo maka agaji a
tsakanin dare uku zuwa wayewar gari?
Imnal yace wata aljana ce mai suffa wadda
kasha kwatantamin data mahaifiyata kuma
tazomin a cikin suffar mutane ba aljanu ba tace
a wajen ka zan samu labarin ta wacece wannar
aljana ya abbana? Hibru yayi ajiyar zuciya yace
kabar wannan magana tukunna har sai bayan
kasamu lafiya gama fadin hakan keda wuya sai
hibru yaji an busa algeta alamar sarki ya tsaya a
gaban jama'ah zaiyi bayani da hanzari hibru ya
mike tsaye imnal ya riko hannun hibru yace
shin gimbiya mulaifa ma tafito kodajin wannan
sai hibru ya dubi imnal a fusace yace na rabaka
da gimbiya mulaifa amma ka ki to kasani cewa
idan ka kara min maganar ta ko kuma kanuna
min kana kaunar ta zamu raba hanya yayin
imnal yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko
da kwalla ya dubi hibru yace ka gafarceni yakai
abbana naimaka alkawari daga yau bazan sake
maka magar gimbiya ba kuma bazan sake nuna
kauna agareta ba.

60

TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin farin ciki hibru ya sumbaci goshin imnal
yace ubangijin daya halicci darbuza ya
albarkace ka gama fadin haka keda wuya ya nufi
inda karagar sarki take har saida yaje dab da
sarki ya tsaya sarki ya dubi gabas da yamma,
kudu da arewa a lokacin da filin fadar yayi tsit
tamkar babu mai rai a wurin sannan yayi
gyaran murya yace yaku jama'ar birnin darul
mahabur tare da jama'ar sauran kasashe
makwabta a wannan nahiya tamu ina mai yiwa
kowa barka dazuwa fadata kuma ina gdy
dakuka amsa gaiyatata domin nuna kishin kasar
Ku dakuma dukiyar ku data jama'ar ku Kamar
yadda kuka sani cewa gagarumar masifa da
bala'i na tunkarar mu idan bamu fita wannan
yaki ba ina mai kira agaremu damu jajirce iya
karfin mu dan ganin munje mun riski babban
abokin gabar mu a can tekun bahar sufiya
domin hanashi dauko takobin saiful lujara a can
ne zamu yake shi don tserar da rayuwar mu da
jama'ar mu kafin yasami nasarar mallakan
kayan yakin mazan jiya kamar yadda kuke gani
a yanzu nida yata munyi gagarumar shigar yaki
alhali bamu kasance mayaka ba ko sadaukai
kuyi sani cewa ayau munfito ne da dukkan
karfin sihirin mu don tunkarar masafi dujalu a
61

TASKARNOVELS.COM.NG
halin yanzu na baiwa yata mulaifa dukkan
sihirina na tsafi guda dari tara da casa'in da
Tara(999) na cikon dubun ne ban bata ba SBD
wani dalili mai karfi na bata wadannan sirruka
ne sbd ta taimaka min awannan yakin domin
abokan gabanmu yawansu ya wuce misali ina
mai sanar daku cewa yanzu haka sarki dujalu
tareda miliyoyin dakarunsa sunyi nisa a tafiyar
su ta zuwa tekun bahar sufiya kuma suna
amfani da alkaluman tsafi wajen gajarce nisan
tafiya muma zamuyi amfani da namu sihirin don
gajarce nisan tafiyan yanzu nabaiwa dukkan
ninku sa'a daya daku gama kimtsawa domin
sa'a dayar na cika hadiman zasu iso daga karshe
ina mai kira ga sarki yaki na hibru bn imlas
dayazo yanzu ya sameni a cikin dakin gani
domin muyi tattaunawa na musamma akan
yadda yaka mata mu bullo wa wannan yaki
koda sarki maharaz maharaz yazo nan a zancen
sa sai filin fadar nan ya rude da sowa. Nan de
sarki maharaz ya kama hannun gimbiya mulaifa
suka wuce izuwa cikin dakin gani shiko sadauki
hibru saida ya koma wajen imnal ya sanar dashi
cewa zaije wajen sarki su gana..

62

TASKARNOVELS.COM.NG
Kuyi haƙuri kwana biyu kun jini shiru ko,
wallaahi laifin Hadejawa ne dan kawai munje
bakunta garinsu sai bari dai nayi shiru da
bakina

Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai
tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi
mani magana da profile dina 08138873799.

MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part E
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

63

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokaci da hibru ya shiga dakin gani sai ya cika
da tsananin mamaki domin sarki Maharaz
kawai ya gani da gimbiya Mulaifa babu sauran
yan majalisa, kuma maimakon yaga sarki akan
kujerar daya saba zama akai sai yaganshi a kasa
bama akan kujara ba, ita Mulaifa a dab dashi,
koda hibru ya hada idanu da sarki sai yaga
idanunsa acike suke da kwalla, al'amarin da yayi
matukar girgiza hibru kenan, ya karasa gurin su
sarki Maharaz jikinsa a sanyaye shima saiya
zauna a kasa suka fuskanci juna, maganar farko
da ta fito daga bakin sarki Maharaz itace yaya
jikin Dana imnal?
Kodajin wannan tambaya sai ran hibru ya baci
bai san sa'adda ya dubi sarki a fusace ba yace ya
shugabana kayi magana akan abun dayake
gaban mu amma ba batun imnal ba, Yace domin
ina ganin bashida wani amfani a wannan yakin
da zamu je, mu barshi anan gida saboda yayi
jinyar jikinsa.
Koda gama fadan haka sai Hibru yaga hawaye
ya zubo daga cikin idanun sarki Maharaz cikin
razani Hibru yace ka gafarceni yakai shugabana
idan har wannan furuci nawa ya kona maka rai.

64

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai sarki Maharaz ya tsam daga
inda gimbiya Mulaifa ke zaune sannan ya dawo
dab da Hibru ya dafa kafadunsa suka kurawa
juna ido sannan yace yakai babban aminina
kuma abokina, ayau ina mai neman gafara
agareka duk abin dakaga nayi maka ko nayi ma
danka ba'a kan kiyayya bane sai domin soyayya
da kuma bin umarnin mai girma darbuza dana
marigayi sarki hubaru, a halin yanzu baka
kaunata acikin zuciyar ka, yakai abokina kayi
tinani zuwa shekarun baya da suka gabata tun
sa'adda muna yara kanana kawo izuwa girman
mu da yadda akayi nazamo sarkin birnin nan da
kuma yadda akayi kazamo sarkin yakina, lallai
ayau ne zan fada maka wani sirri daban taba
gaya maka shiba, amma sai bayan ka bawa
Mulaifa labarin rayuwar mu ta baya da yadda
akayi na auri mahaifiyarta, da kuma yadda na
shiga tashin hankali bisa rashin samun haihuwa.
Lokacin da sarki Maharaz yazo nan a zancensa
sai idanun Hibru suka cika sharkaf da hawaye
ya dubi Mulaifa cikin tsananin tausayi yace yake
'yarmu ki saurara da kyau kiji wannan labari
mai dauke da dimbin abun tausayi da ban
alajabi, kuma kisan irin dangartakar dake
tsakani na da mahaifinki.
65

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai Mulaifa ta tattara hankalinta
waje daya ta kurawa Hibru idanu.
Shi kuma saiya shiga bata labari kamar haka "A
wasu shekarun baya da suka gabata zamanin da
sarki Ruzba ke mulki a wannan birni Darul
Mahabur, nida mahaifinki mun kasance
fadawan sarki ruzba wadanda aikin mu kawai
tsaron lafiyar sarki, duk inda sarki zaije muna
tare dashi kuma ko kuda bama bari ya sauka a
jikinsa, mahaifin sarki ya kasance kasurgumin
matsafi dan haka ya gaji tsafi kuma ya shahara,
bisa wannan dama daya samune sarki ya zabe
shi acikin dakaru masu tsaron lafiyar sa, niko
mahaifina shine sarkin yaki birnin Darul
Mahabur, a wannan lokaci tsufa ya riske shi har
yakai baya iya fita yaƙi, awannan lokaci ban
wuce shekaru sha biyar ba don haka ni nake
wakiltar mahaifina a yakuna, sau uku muna
tseratar da rayuwar sarki ruzba a lokacin da
wani babban abokin gabarsa yake kawo masa
hari don ya halaka shi, hari na farko a wani
yammaci ne da sarki ruzba ya fita rangadi izuwa
bayan gari inda muka shiga wani daji da ake
kira Furuz, a rayuwar sarki ruzba babu abunda
yake sha'awa kamar yin suu acikin kogi kuma
dakan shi yakan shiga kogi yayi kamun kifi.
66

TASKARNOVELS.COM.NG
Acikin dajin Furuz akwai wani babban kogi da
ake kira bahar zur, shidai wannan kogi yana da
girman gaske da muggan halittun ruwa a cikin
sa, lokacin da mukazo zamu gifta ta gaban kogin
tare da tawagar mu, sai sarki ruzba yace a tsaya
a bakin kogin.
Kodajin haka sai hankalin dakarun mu ya
dugunzuma domin sun san halin sarki zai iya
cewa sai an shiga cikin kogin yayi suuu. Nida
maharaz ne kawai hankulanmu basu tashiba
domin mun yarda da kanmu, kawai sai sarki ya
dubeni ya dubi maharaz yace inaso na shiga
cikin kogin nan nayi suuu. Don haka sai Ku
biyoni ciki domin nasan cewa Ku kadai ne zaku
iya biyoni.
Nan take sarki ya sauko daga kan dokin sa ya
dauki fatsarsa ya fada cikin kogi, cikin sauri nida
maharaz muka bishi. A duk dakika biyar sai
Maharaz ya dubi hannunsa domin ajiki yake
ganin abinda ke karkashin kogin, da zarar yaga
wani mugun abu ya tafo inda sarki yake saiya
sanar dani sai nayi nitso a kasa na tarar da abun
komai hazarinsa na kashe shi, acikin abinda bai
kai rabin sa'a ba na kashe manyan kadodi biyar
saida sarki ruzba ya shafe sa'a guda amma ko
67

TASKARNOVELS.COM.NG
kifi daya bai kama ba, har ya hakuri da nufin ya
daina ya fita da cikin kogin sai yaji fatsar sa tayi
nauyi matuka ta yadda bazai iya dago taba, cikin
mamaki ya dubi Maharaz yace yakai boka dan
boka wai shin wani irin kifine na kamo mai
girma da nauyi da har na kasa dago shi sama?
Maharaz ya dubi tafin hanunsa yaga babu komai
acikin fatsar cikin kaduwa da zaro idanu
maharaz ya dubi sarki yace nikam banga komai
acikin fatsar nan ba, tabbas muna cikin tashin
hankali, duk yadda akayi wani abune mai
mugun sihiri ya shiga fatsar ka, kafin ni koh
sarki ruzba muce wani abu sai mukaga an fisgi
sarki ruzba anyi kasa dashi izuwa karkashin
kogin, ba shiri muma mukayi nitso izuwa
karshin kogin, kawai sai mukayi arba dawani
wani katon mutum ya shake sarki ruzba da
hannu biyu har sarki ya fara kakarin mutuwa,
cikin zafin nama na kafa hannayen wannan
maridi na fara kokarin banbaresu daga wuyan
sarki, nan kwanjin maridin ya kumbura idanun
sarki ruzba sun kumbura ga kuma rashin
numfashi shima Maharaz yana kokarin kashe
maridin da karfin tsafi, amma duk abinda ya
watsa mishi basa tasiri, kawai sai maridin ya
juya baya ya gabzawa Maharaz naushi a fuska
68

TASKARNOVELS.COM.NG
take Maharaz ya sulela sumamme ya tafi izuwa
karkashin ruwa.
Al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na
tattara karfina gabadaya na gabzawa maridin
naushi a kunnensa na hagu, sbd karfin naushin
saida jini yayi tsartuwa ta kunnensa na hagu, ba
shiri ya saki wuyan sarki ya kwarara ihu cikin
zafin nama na kamo sarki ruzba sannan nayi
kasa na kamo Maharaz sannan nayiyo sama,
kafin maridin ya dawo hayyacinsa tuni na fito
dasu bakin kogin muka zube wanwar a gabar
kogin duk mu ukun muna cikin mugun hali, ni
ina numfashi sama sama Sarki da Maharaz kuwa
duk a sume suke, cikin gaggawa aka shiga yi
musu fifita.
Koda na mike tsaye sai naga wannan
basamuden katon yayi fitar burgu tamkar an
chillo shi daga cikin baka, take ya dira akan
turba ya tsaya kyam kawai yana murmushi, har
asannan jini na diga daga kunnensa, koda
sauran dakaru sukayi arba dashi sai suka razana
suka dinga fantamawa cikin daji, mutumin ya
dubeni ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda
amsa kuwarta ya cika dajin, daga can sai
murtuke fuska cikin kakkausar murya yace kai
69

TASKARNOVELS.COM.NG
yaro kayi kuskure da kake zaton cewa zaka kare
sarki ruzba, tabbas sai nayiwa sarki ruzba kisan
wulakanci a gabanka kuma kaima sai nayi filla
filla da sassan jikinka..
Kodajin wannan batu sai zuciyata ta kekashe
gabarin tsoro na dubeshi a fusace nace karyarka
tasha karya yakai wannan azzalumi, kai waye
dakake tinanin zakayi mana kisan gilla.
Maridin ya sake bushewa da dariya a karo na
biyu sannan yace sunana Gilzam sadaukin
sadaukai na maridan duniya, musamman sarki
darbuza na birnin kailus ya dauko hayata domin
na kashe sarki Hubru ayau, bisa yarjejeniya
aduk kwanaki bakwai zai dinga bamu mutum
dari nida iyalina muna cinyewa, domin naman
mutane ne abincin mu, babu wani bala'i dazai
hanani kashe sarki hubru ayanzu, idan kuma
kuna gani zaku iya toh ku jaraba.
Kafin na bude baki nace wani abu tuni gilzam ya
zare wadansu zabga zabgan takubba guda biyu
ya durfafo mu, girman kowace takobi ya wuce
misali, nauyin ta kuwa saidai karti ashirin su
dauka, dama tuni jikin sarki hubru dana
Maharaz ya fara karkarwa sbd tsananin razanar
70

TASKARNOVELS.COM.NG
da sukayi bisa ganin gilzam da kalamansa,
amma sbd tsabar tsoro sun kasa mikewa ma su
gudu. Cikin matukar karfin hali na zare tawa
takobin na tunkari gilzam duk dayake ni kaina
nasani gilzam yafi karfina nesa ba kusaba amma
saina tari aradu daka...
Gilzam ya nufo kaina gadam gadam nima na
nufeshi acikin dakewar zuciya, takun sawun
gilzam tamkar na toron giwa ne amma hakan
batasa na razana ba, koda muka hadu ya kawo
min wawan sara da takuba biyu da nufin ya fille
min kai da kafafu saina goce da dukkan zafin
nama na, takobin farko saita samu wata bishiyar
dibino mai tsawo take bishiyar ta rabe gida biyu
ta ratattake akasa, takobi ta biyu kuwa sai ta
karci kasa, nan take ta haifar da girgizar kasa da
zabtarewar ta, koda ganin faruwa wannan
alamari sai hankalina ya dugunzuma na
tabbatar dacewa yaufa na gamu da gamona.
Sarki Hubaru da Maharaz kuwa sai suka sake
tsurewa domin sun gama saduda sun san
mutuwa tazo, niko danaga haka ban karaya ba
sai na dada durfafan gilzam, shi kansa gilzam
yayi mamaki dan bai taba haduwa da mutumin
dabai taba razana akan shiba sai ni, abinda yafi
71

TASKARNOVELS.COM.NG
daure mashi kaima shine na kasance yaro mai
kuruciwa dan shekaru goma sha, cikin matukar
fusata gilzam ya tasomin da dukkan karfin sa
yana mai kawomin sara da suka da muggan
makaman sa, nikuma ina gocewa amma ko
kadan na gagara maida martani saboda karfin
harinsa da zafin namansa ya ninka nawa, kaini
kaina nayi mamakin yadda ma nake gocewa
harinsa nan gilzam ya tashi hankalin dajin
gabadaya ya haddasa kamawar wuta da girgixar
kasa. Sai da muka shafe sa'a guda cif nida gilzam
muna fafatawa shi baisami nasarar hallakani ba
balle ya koma Kansu sarki hubru.
Bayan ansamu sa'a gudan ne naji na fara gajiya,
shiko Gilzam kamar a lokacin nema ya fara
gumurzun, alamarin daya dugunzuma hankalina
kenan na tabbatar dacewa saura kiris tawa ta
kare. kwatsam! sai muka jiyo kururuwan
mazaje daga bayan mu cikin sauri muka waiga
sai naga ashe dakarun da muka fito rangadi
dasune sukaje suna neman daukin sauran
dakarun darul mahabur, sama da mutum
miliyan biyu ne suka durfafo mu suna ihu da
karaji, karar sukuwar dawakan suma kawai ta
isa ta razana mutum ya dauka yakin duniya
akeyi.
72

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Gilzam ya hango wannan runduna ta
durfafo shi sai yayi murmushi ya ruga garesu,
tun gabanin su riske shi. Kaico!! yayin da Gilzam
ya ratsa ta cikin dakarun saiya dinga zubar dasu
tamkar yana shara, sai dai kaga takobinsa na
datsa mutane tana raba dawakansu gida biyu,
nanfa ya bude kasuwar daukar rai sai hangowa
nayi jini na tsartuwa yana malala akasa, kafin na
ankara tini gilzam ya kashe sama da dakaru
miliyan daya da rabi da dawakansu.
Ko da na hango wannan barna saina fusata
ainun na falfala da matsanacin gudu Irin wadda
bantaba yin irinsa ba, domin har ji nake kamar
zantashi sama, na nufi inda gilzam yake wannan
barna, yayin daya rage saura taku uku na isa
gareshi sai na daka tsalle sama na sauka akan
wuyansa, kafin yasa takobinsa ya kadoni tuni na
soka masa wuka a kunnensa na hagu take
wukar ta lume acikin kunnensa ya bullo ta daya
kunnen. Gilzam ya
End Ads