gimbiya take" Imnal ya
ce na gode da hakan ma maza ku bani.
Cikin rawar jiki daya daga cikin kuyangin ta
dauko taswirar wadda ke zane akan wata
busasshiyar fata ta miqa masa ta ce "Wannan ita
ce gudummawar mu a cikin soyaiyarku kai da
gimbiya"
Koda jin haka sai murna ta kama imnal yace "Ni
kuwa nayi muku alqawari duk ranar da burin
mu ya cika ni da gimbiya sai na 'yantaku na ba
37
TASKARNOVELS.COM.NG
ku kyautar dukiya irin wacce ba.a ta6a baiwa
wani ba"
Gama fadin hakan keda wuya sai suka ji ana
kwankwasa kofar dakin da qarfi ana yi musu
tsawar su bude.
Kafin kuyangin suyi wani yi wani yunkuri sai
suka ga imnal ya daka tsalle sama kamar dan
biri ya naushi saman rufin dakin wanda akayi
shi da katako mai kaurin gaske. Take saman ya
6urma ya fice fit ta cikin sa. Koda imnal ya tsinci
kan sa a saman rufi sai ya ci gaba da gudu akan
dakuna. Ba zato sai yaji ana harbo masa kibiyoyi
cul cul cul ! In ba don karfin gudun sa ba da tuni
an sameshi, sai da yayi tafiya mai tsayi a sama
sannan ya hango wani tafkeken tafkin wanka
mai dauke da ruwa garai garai gunin ban
sha.awa.kwatsam sai ya hango gimbiya Mulaifa
a tsaye a gaban tafkinkwatsam sai ya hango
gimbiya mulaifa a tsaye a gaban tafkin ta daga
kai sama tana duba madubi.
Koda imnal yaga babu kowa a kusada ita sai ya
yadako tsalle ya fado cikin tafkin kafin ya fito
daga tafkin tuni itama ta daka tsalle ta biyoshi
ciki kawai saita danna shi izuwa kasan tafkin
38
TASKARNOVELS.COM.NG
sukayi nutso ta wuce gaba yana biye da ita sai
gasu sun biyo wani kwararo sun fito saman
wani sabon tafkin wadda yake tsakiyar cikin
turakarta babu kowa awajen face kuyangi
fitowar keda wuya daga cikin tafkin sai kuyangi
2 suka rugo suka yafa musu mayafan goge jiki
har izuwa wannan lokaci mulaifa bata dubi
fuskar imnal ba balle tace dashi wani abu kuma
fuskarta a murtuke take tamkar wadda aka
aikowa sakon mutuwa.
Al'amarin daya jefa imnal cikin mamaki kenan
amma sai yayi shiru baice komai ba bayan an
gama tsame lemar dake cikinsu sai Mulaifa ta
sake kama hannun imnal zuwa dakin baccinta
da zuwa sai dukkanin kuyangin da suke ciki
suka fito waje suka rufo kofa nan take Mulaifa ta
sharawa imnal mari ta fashe da kuka ta
rungumeshi tana mai cewa saboda mai zaka
saida rayuwarka kace sai kazo ka ganni a
wannan dare, shin mun rabune har abada
baxamu sake saduwa ba inda tsautsayi yasa ka
hallaka da tuni nima na kashe kaina.
Sa'adda imnal yaji wannan batu na mulaifa sai
gabadaya jikin shi yayi sanyi nan take yaji
kaunar mulaifa ta kara mamaye zuciyarsa kawai
39
TASKARNOVELS.COM.NG
saiya janye jikinsa suna masu fuskantar juna
yace yake abin begena kiyi sani cewa sa'adda na
samu labarin halin da kika shiga sbd hukuncin
da aka yanke min sai hankalina ya dugunzuma,
naji bazan iya yin komai ba sai nazo na ganki
burina na ganki da idanuna koda kibiyoyi dubu
zasu nutse a cikin gangar jikina, sa'adda imnal
yazo nan a zancen sai mulaifa ta sake
rungumeshi cikin tsananin farin ciki tana mai
cewa tabbas kaine zaka zamo abokin rayuwata
gama fadin hakan keda wuya sai sukaji Sarki
Maharaz na kwankwasa kofa yana cewa a bude
alamarin daya dugunzuma hankalin imnal da
kuyangun ita kuwa mulaifa ko a jikin ta kawai
saita dafa imnal da dan yatsanta guda na hagu
take imnal ya rikide yazamo kofin zinare irin
wadda ake saka furanyi aciki faruwar hakan
keda wuya sai mulaifa ta umarci kuyangin nata
su bude kofar. Sarki maharaz ya shigo a fusace
yana haki nan take ya kama kalle-kalle yana
nazarin ko wace kusurwa batareda yace komai
ba. daga can sai Mulaifa ta duci sarki tace babu
wani bako daya shigo wajena koda jin haka sai
sarki maharaz yayi murmushi ya matsa dab da
Mulaifa ya dafa kafadunta yace yake yata a iya
sanina baki taba min karya ba ashe za'a wayi
40
TASKARNOVELS.COM.NG
garin ranar da zaki min karya saboda soyayya
inaso kisani cewa na fahimci akwai soyayya
tsakanin ki da imnal dan sarkin yaki tabbas
shina nake zargi da shigowa gidan nan ahalin
yanzu na tura dakaru zuwa gidan sarkin yaki
idan sukaje suka iske baya nan tabbas toh shine
yazo... hukuncin kisane zai tabbata akan shi
maimakon horo.
Koda mulaifa taji haka sai hankalinta ya
dugunzuma amma saita dubi sarki maharaz
batare da nuna wani damuwa ba tace ina mai
tabbatarka imnal na gida a kwance, sarki
maharaz yayi murmushi har ya juya zai fita sai
idanunsa suka kai kan wannan kofin zinaren
sarki maharaz ya kura kofin kurawa kofin idanu
yana nazarinsa, a lokaci ne zuciyar Mulaifa ta
fara bugawa.
Lokacin da sarki maharaz ya kurawa kofin
zinaren nan idanu yana nazarin sa a lokacin
zuciyar Mulaifa ta fara bugawa da karfi bayan
sarki maharaz ya gama nazarin wannan kofin
saiya juyo ya dubi mulaifa yace yaushe kika
samu wannan kofin? Nide asanina bantaba sayo
irinsa ba mulaifa tayi murmushi tace ai
musamman na aika birnin shamrun aka kera
41
TASKARNOVELS.COM.NG
mini shi koda jin haka sai sarki maharaz ya
karisa inda kofin yake ya daukeshi yana mai
jujjuya shi a hanun shi yace amma fah ya bani
sha'awa sosai shin zaki iya bani kyautarsa
mulaifa tayi murmushi tace ya abbana ai komai
kake so daga gareni basai ka tambaya ba dauka
yakamata kayi kawai amma akwai wanda zaifi
dacewa dakai nasa akera maka shi zaizo nan da
kwana Bakwai, yayin da sarki maharaz yaji
wannan magana sai jikinsa yayi sanyi kuma ya
kasayin gardama kawai saiya ajiye kofin sannan
ya sumbaci goshin gimbiya mulaifa ya fice daga
cikin turakar. Fitarsa keda wuya sai kuyangi
suka rufe kofar turakar. ita kuma mulaifa saita
ruga ta dauko wannan kofin zinare nan take ta
karanta wadansu dalamisan tsafi ta tofa akan
kofin faruwar hakan keda wuya sai kofin ya
tarwatse kamar an watsa hoda, sannu a hankali
hodar ta dinga disashewa ta bace bat kawai sai
gimbia mulaifa ta tafi izuwa kan gadonta ta
kwanta domin sai a sannan ne hankalinta ya
kwanta.
Al'amarin imnal kuwa shide kawai ya tsinci
kansa ne kan gadon cikin dakinsa kawai sai yaji
ana magana da mahaifinsa hibru a kofar dakin
ga dukkan alamu ran hibru a bace yake domin
42
TASKARNOVELS.COM.NG
yana magana ne cikin daga murya da fushi
maganar da imnal ya fara ji daga mahaifinsa
itace, yanzu niza ayiwa haka to kusani cewa tun
safe ina tareda dana kuma yanxu haka yana
cikin dakinsa yana barci wata kakkausar murya
tace "Ya shugabana kayi hakuri mu yan aiken
sarki ne dan haka bai kamata kaga laifin mu ba
saboda bin umarni ne, yanzu dolene ka bude
mana mugani idan yana ciki musan amsar daza
muje mugayawa sarki, idan kuma bazaka bude
ba dolene mu bude da kanmu".
Koda jin haka sai hibru yayi ajiyar zuciya yace ai
bama sai takai haka ba.
Nan take ya bude kofar dakin aiko saiga imnal
yanata sharar barci abunsa kamar ma baisan
abinda akeyiba sai jikin dakarun sarki yayi
sanyi babban cikinsu mai kakkausar murya ya
dubi hibru yace ka huta lafiya ya shugabana
kawai saiya juya ya fita daga cikin dakin sauran
dakarun kuma suka rufa masa baya, cikin
hanzari hibru yaje ya kullo kofar gidan sannan
yadawo cikin dakin imnal ya dubi imnal yace
yakai dana tashi muyi magana nasan idanunka
biu kuma tabbas ka fita daga cikin gidan nan
cikin dare.
43
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai imnal ya mike zumbur ya
kurawa hibru idanu cikin mamaki sannan ya
sunkuyar da kanshi kasa cikin alamun kunya da
rashin gaskiya.
Koda ganin haka sai hibru yace yakai dana kayi
sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dolene ya
rigaka tashi a ka'idar rayuwata duk tsakar dare
nakan farka na duba ko'ina na gidan nan kuma
na fita kofar gida na kwanta, tun kafin a haifeka
nake wannan al'ada kuma mahaifiyar ka
batasan inayi ba, yauma kamar kullum hakan
tafaru kuma dana duba cikin dakinka sai naga
baka nan kuma dana duba waje sai naga babu
dokinka, hakan ya tabbatar min dacewa ka fita
cikin daren nan abinda bansani ba ina katafi?
yanzu na samu amsar inda kaje tunda dakarun
sarki sunzo don su tabbatar da cewa ko kaine
kaje gidan sarki yakai dana mai yasa kake jefa
kanka cikin rigima da tashin hankali mai kajeyi
gidan sarki shin kamanta ne cewa kanada
babban kaifi kuma a gobene za'ayi maka
hukuncinsa.
Sa'adda hibru yazo nan a zancensa sai jikin
imnal yayi sanyi, daga can sai yadago kai cikin
alamun nadama yace yakai abbana ka gafarceni
44
TASKARNOVELS.COM.NG
kayi sani wannan kuskuren danayi bayin kaina
bane zuciya ce ta ribance ni ina mai tabbatar
maka ayanzu nida gimbiya mulaifa bazamu iya
rayuwa ba idan bama tare da juna.
Koda jin wannan batu sai hankalin hibru ya
dugunzuma ya mike tsaye ya juyawa imnal baya
lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla, imnal
ya mike tsaye ya zagayo gaban hibru ya tsaya
kawai saiya durkusa bisa gwuiwoyinsa ya kama
tuba da neman gafara hibru kuma kama kafadan
imnal yayi suka fuskanci juna a lokacin da
hawaye ke zuba da idanunsu hibru yace yakai
dana bakayi min laifin komai ba kayi sani cewa
in bah soyayya ba da nine sarkin wannan birni
namu, amma saboda na zabi soyayya nayi watsi
da mulki in badan soyayya ba da maxan jiya
guda uku wato jarumi hulkas mai hular
Lamsara, Kaura Shaddadu na birnin Kufa mai
mashin galilul haras da sadauki Hantaru mai
takobin Saiful Lujara da basu mutu a banza ba
tabbas soyayya tushen wahala ce sai mai sa'a da
rabo ke tsallake shaukin cikinta ina tsoron kada
rayuwar ka ta kare irin yadda tawa takare da
kuma yadda ta mazan jiya takare, ya kai dana
kayi sani cewa na ziyarci bokaye da dama kuma
sun tabbatar min dacewa zaka samu daukaka
45
TASKARNOVELS.COM.NG
anan gaba. Da wannan furuci nake maka
sallama sai ka je ka kwanta ka rintsa muga
abinda zai faru dakai gobe, gama fadin hakan
keda wuya sai hibru yaja kofar dakin ya rufe
Imnal ya koma kan gadonsa ya kwanta.
Tab! Gaskiya nima fa na fara tsorata da sha'anin
soyayya dan haka zan ajiye dukkan wasu
kalamaina na soyayya a wajen guda tunda ga
jarumai ma masu dakakkiyar zuciya sun mutu a
banza saboda tafarkin soyayya ballantana mu
, amman dai wace irin shawara zaku bani
shin na cigaba da soyayya ko kuma na hakura
da ita gudun kada abinda ya faru da mazan jiya
ya faru da ni.
Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai
tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi
mani magana da profile dina 08138873799.
Zan ci gaba.
46
TASKARNOVELS.COM.NG
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part D
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Al'amarin sarki hibru kuwa tunda duku dukun
safiya ya shirya abincin kalaci ya shiga dakin
imnal sai ya iske shi acikin mafarki har yana
surutai a fili, ba komai yake ambato ba face
sunan gimbiya Mulaifa yana fadan kalamomin
soyayya. Hibru ya daki kafar imnal yana mai
daka mishi tsawa yace mai kakeyi har yanzu
baka tashi ba, to kasani saura kiris mu makara
zuwa fada, kashirya ka sameni a falo muyi
kalaci, gama fadin hakan keda wuya sai hibru ya
juya ya fita, shiko imnal sai yayi sauri ya kimtsa
ya riski hibru a falo sukayi kalace sannan suka
fita kofar gida domin su tafi izuwa fada. Da
fitowarsu sai hibru ya shiga cikin bsuma ya
kamo dokinsa da nufin su hau tunda na imnal
baya nan, har sun yunkara zasu hau sai imnal ya
47
TASKARNOVELS.COM.NG
hango nashi dokin ya tafo da gudu shi kadai,
cikin gaggawa imnal ya rugo ya riske shi kawai
sai yaga wasika a karkashin siddin dokin cikin
zafin nama ya zare wasikar ya boyeta acikin
rigar sa saboda kar hibru ya gani, nan take
imnal ya hau kan dokin shi shima hibru hau kan
nashi suka tafi fada.
Fada ta cika makil babu abunda mutum zai gani
sai kawunan bil'adama lokacin da hibru da
imnal suka shigo cikin fadan kowa ya gama
halatta har sarki kuwa sai da yazo, kuma a
wannnan lokaci shi ake jira a hankali suka
cigaba da tafiya bisa kafafunsu suka durfafi inda
sarki yake. Sarki maharaz da gimbiya Mulaifa na
zanne sun zubawa su hibru idanu shi dai sarki
maharaz fuskar sa acike takeda murmushi
amma na mugunta ita kuwa gimbiya Mulaifa
fuskarta acike take da tsananin damuwa kamar
zata fashe da kuka. Koda hibru da imnal suka zo
dab da karagar sarki sai suka zube kasa suka
kwashi gaisuwa. Sarki maharaz ya amsa
gaisuwan cikin murmushi yana mai kauda kai
ga kallon su kawai saiya dubi wadansu karti
biyu majiya karfi da suke tsaye a gefe daya yayi
musu inkiyar su cika aikin su, nan take kartin
biyu suka kama imnal suka daure shi ajikin
48
TASKARNOVELS.COM.NG
wani murtukeken ice mai gwafa dake kasa
sannan sai suka yayyage rigar jikin imnal da
karfin tsiya suka daga murtukeken icen sama
suka soke shi acikin rami mai zurfi saiga imnal a
sama.
Koda kammala haka sai sarki maharaz ya miki
ya fiskanci gabadayan jama'ar da suke fadan
yace yaku jama'ar darul mahabur, kamar yadda
kuka sani fiye da shekaru talatin da suka gabata
muna bautan mai girma darbuza a kasar nan, ba
ataba samun wanda ya karya doka ba, sai a
wannan karon da imnal dan hibru ya aikata
wannan laifi kusani mai girma darbuza shiya
yanke hukunci dakansa hukuncin kuwa shine za
ayita shara masa bulala har sai fatar jikinsa da
kwoilewa kuma ana zuba mishi gishiri acikin shi
har sai ya suma. Ba za'a kunce shiba sai ya
kwana, kuma babu ci babu sha har na tsawon
kwana uku.
Koda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai
gimbiya Mulaifa ta fashe da kuka ta kama rokon
sarki maharaz da ayi wa imnal afuwa, sarki
maharaz ya dakawa mulaifa tsawa yace kinaso
nima nayi laifi ne ga mai girma darbuza, lallai ni
mai biyayyane ga mai girma darbuza idan
49
TASKARNOVELS.COM.NG
kikaga ba ayiwai imnal wannan hukuncin ba to
tabbas bana nunfashi ne, nan take sarki
maharaz ya sake duban karti guda biyu kawai
sai suka daiki bulala da gishiri acikin wani katon
kasko suka hau kan wani dogon munbari mai
matattakala, Wanda yake dab da inda aka daure
imnal suka fara cika aikinsu, yazama cewa daya
ya fara zabgawa imnal bulala shi kuma dayan
yana manna mishi gishiri a fatar jikinshi,
maimakon jama'ah suji imnal na ihu da kuka sai
sukaga ya kurawa gimbiya mulaifa idanu yana
mai murmushi, ita kuma mulaifa in banda kuka
babu abunda takeyi awannan lokaci a sannan
jamma'ar dake wajen suka tabbatar da cewa
akwai soyaya tsakanin imnal da gimbiya
Mulaifa.
Kafin ajima bayan imnal yayi kaca kaca da jini,
komin rashin imanin mutum idan yaga yadda
akewa imnal dolene ya tausaya mishi, lokacin da
Mulaifa taga azabar da akewa imnal ta wuce ta
hankali sai ta mike zumbur ta ruga izuwa gidan
sarauta kash!! inda gimbiya Mulaifa tasan
muhimmancin zamanta awajen da bazata
tashiba domin kallon fuskarta da imnal keyi shi
ya hana shi jin zafin azaban da akeyi mishi, aiko
tana shigewa gidan sarauta imnal yaji tamkar
50
TASKARNOVELS.COM.NG
numfashinsa zai dauke sbd azaba amma saboda
juriya da jarumtaka saida imnal ya shafe sa'a
uku acikin wannan hali sannan ya suma, duk
abinda ke faruwa sarki yaki hibru na tsaye a
gefe yana kallo yana murmushi tamkar zuciyar
sa bata sosuwa akan abinda ke faruwa, a badine
zuciyar hibru a tafasa take kamar zata kone
saboda takaicin da bakin cikin ganin yadda sarki
ya rufe Ido yake horar da dansa, babban
takaicin dake damunshi shine yasha bakar
wahala awajen taimakon sarki maharaz harma
ya kusa rasa ranshi a lokacin da sarki maharaz
yake neman haihuwa ruwa ajallo yau gashi
sarki bai damu danashi danba. hibru ya tambayi
kanshi wai menene amfanin biyayyar dana
kewa sarki, akan wani dalili zan cigaba dayin
bauta ga Wanda baisan halacci ba, na kubutar
da rayuwar yar shi amma shi gashi yana so ya
salwantar da dana hakika lokaci yayi dazan
daina wannan bauta a yayin da muka bar gida
don tafiya wannan gagarumin yakin, adaidai
wannan lokacin da sadauki hibru yazo nan
azancensa imnal ya suma saboda azabar da'ake
masa.
Koda kartin biyu sukaga ya suma sai suka daina
masa azaban suka sauko daga mumbarin a
51
TASKARNOVELS.COM.NG
sannan ne sarki maharaz ya sake mikewa cikin
farin ciki yace yanzu mun cika umarnin mai
girma darbuza hankali ya kwanta dan haka da
sallami kowa, shiko mai laifi za'a bar dakaru
masu tsaronsa don karwani yakawo masa dauki
lallai ahaka zai kwana uku batare daci ko shaba
koda gama sai sarki ya juya da nufin ya shiga
gidan sarauta kawai saiya hada idanu da sarki
yaki hibru nan take maharaz yaji zuciyar shi ta
buga da karfi, bakomai ne haddasa haka ban
face tunda sarki maharaz suke tare da hibru bai
taba ganin ya harare shiba sai ayau bayan shigar
sarki maharaz cikin gidan sarauta fada ta watse
babu kowa face and wadansu dakaru 300
wadda suke tsaron imnal.
Shiko hibru saiya tafi can nesa kadan da filin
fadan yayi sumfuda ya zauna inda yana iya
hango imnal, nan fah hibru ya shiga sakar zuci
wata zuciyar tace dashi ya afkawa wayennan
dakarun dake tsaron imnal ya kashe su sannan
ya kunce imnal ya tafi dashi in yaso subar kasar
gabadayan su, wata zuciyar kuma sai tace dashi
ai bai kamata yayi hakan ba tunda shima yayi
imani da darbuza zaifi kyau ya bari sai antafi
yaki sannan sukama gabansu haka dai hibru ya
cigabada zancen zuci ya kulla wannan ya kunce
52
TASKARNOVELS.COM.NG
wancan har yamma tayi likis bai gusa daga inda
yake zaune ba kuma bai nemi abinci koh abin
sha ba har dare ya raba hibru nanan zaune a
inda yake bai gusa ba cikin halin damuwa da
bakin ciki kuma koh alamar bacci a idanunsa
babu a lokacin ne hibru yaji tsani sarki maharaz
da darbuza domin baiga amfanin biyayyar
dayake mishi ba. Adaidai wannan lokacin ne
iska mai sanyi ta soma kadawa wadda ta zoma
sanadin farfadowar imnal daga doguwar suman
da yayi, imnal ya bude idanunsa da kyar yana
gani dishi-dishi sai kawai yaji wata irin
izababbiyar ishirwa nan fah ya fara kiran ruwa!
ruwa!! tun yana fadi a hankali harya bude
makokoron sa yana fadi da karfi koda hibru ya
jiyo sautin muryar imnal yana kiran ruwa saiya
mike zumbur a firgice ya lalubi sulkar sa ya
yunkura da sauri da nufin ya ruga zuwa inda
imnal yake kawai sai yaga matarsa wato
marigayiya mahaifiyar imnal ta bayyana a
gabansa cikin tsananin tsoro hibru ya fadi kasa
ya kama ja da baya yana mai nunata da dan
yatsa yana karkarwa. Koda ganin haka sai
marigayiyar ta dube shi cikin murmushi tace
kwantar da hankalin ka yakai sadaukin zamani
kayi sani cewa niba matarka bace na kasance
53
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin jinsin aljanu sunana luzaira yar salbas,
nazone gareka acikin suffar matarka domin
nasamu damar hanaka abinda kake son yi
domin idan ka kaiwa imnal agaji wannan lokaci
tamkar ka ruguza cigaban rayuwar sane, cikin
rashin yadda hibru ya dubi luzaira yace ta yaya
zan yarda dake kuma akan wani dalili zaki min
wannan taimako shin bakya ganin halin da dana
yake ciki ne sakamon kishirwar dake addabarsa.
Koda aljani luzaira taji wannan batu sai tayi
murmushi tace duk irin wahalar da imnal zaisha
bazai mutu ba bincike ya tabbatar da cewa
danka zai girma ya shahara a duniya nan gaba
lallai ya zamo wajibi ka yarda Dani idan har
kana son ka cika burinka na rayuwa inko kaki
acikin bautar sarki maharaz zaka mutu, ina
sanar dakai cewa a duniya darbuza bashida
wani makiya wadda yawuce ubana sarki salbas
mai mulkin birnin Shulai a kullum suna farautar
juna Kuma wannen so yake ya kama dayan su a
raye domin samun sinadarin da zasu cika
burinsu, nazone sbd mu taimaki juna zan
taimake ku kusamu yancin kanku daga sarki
maharaz da aljani darbuza, ni kuma da
taimakon kadai zan iya taimakawa mahaifina
domin mu kama darbuza a raye sa'adda aljana
54
TASKARNOVELS.COM.NG
luzaira taxo nan a zancen ta sai hibru ya sake
rudewa kuma ya cika da mamaki yace yanzu
kina nufin darbuzan da muke bautawa aljani ne
kamarki?
Luzaira tace ko shakka babu tace ai dayawan ku
bil'adama mu kuke bautawa sbd kuna ganin
munayin abunda ku bazaku iyaba hibru yayi
ajiyar zuciya yace to yanxu tayaya zan iya
taimakonki ke kuma tayaya zaki iya taimakona?
Aljana luzaira tayi murmushi tace har abada
bazaka taba kubuta daga cikin bautawa sarki
maharaz ba sai an karya wani asiri daya maka
shidai wannan asiri anyi shine silin gashin
kirjinka guda daya kuma an bunne shine