x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - MAZAN JIYA 1

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 206

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
daga
dukkanin irin masifun da zaku shiga a cikin
127

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan gagarumar tafiyar, kuma lallaı duk irin
wahalar da zaku sha karshe kune zaku yi
nasara, abinda bni da tabbacin yi maku
alkawarinsa shine kare lafiyarku, dalili kuwa
shine wanda kuke bautawa da wanda su sarki
duzalu ke bautawa ya kasance mai karfi kamata
kuma shine babban makiyina a duniya, tabbatas
muna yi gaba mai tsanani kwatankwacin irin
wadda sarki huburu da sarki darzuba suka yi
kafin mutuwarsu. Ina mai sanar da ku cewa
nima ina nan ina gagarumin shirin yaki domin
tunkarar abokan gaba acan tekun bahar
Suffiyya, wanda kokarinsa shine ya kare sarki
dujalu kuma ya bashi ikon da nasarar dauko
takobin saiful lujara, kmar yadda nima zan
kareku kuma na baku nasara, wannan yaki da za
a yi a bakin kogin bahar Suffiyya ba a taba yin
kamarsa ba a tarihin duniya ba, domin sai anyi
asarar dubun nan rayukan miliyoyin aljanu da
biladama da kuma dukiya mara adadi. Dole ne
cikin biyu ayi daya, kodai su halakamu ko kuma
mu mu halakasu, amman ina da yakinin cewa
mune da nasara domin nayi bincike har sau
dubu dari amman banga komai ba sai nasara a
garemu, da wannan kalami ne nake sallamarku
sai mun hadu a bakin kogin bahar Suffiyya, lallai
128

TASKARNOVELS.COM.NG
zamu gajarce maku tafiyar daga kwanaki masu
yawa zuwa kwanaki kadan.
Sa'adda darzuba yazo nan a jawabinsa sai Sarki
Maharaz ya bude baki yayi godiya, shiko Hibru
sai yayi shiru bai ce komai ba, tun sa'ar da
darzuba yayi nisa a cikin jawabinsa sai zuciyar
Hibru tta cika da wasiwasi ya tambayi kansa a
cikin zuciyarsa ya ce wai shin wannan wane irin
abune muke bautawa, wane ne haka muke
bautawa wanda basji da cikekken yakini, ai bai
kamata ace abinda ake bautawa yana shakkar
wani abu ba, kai ni a ganina ma kamar akwai
wani guda daya wanda yafi dukkaninsu karfi da
iko, inya so sai ya yake su ya kawar da su
dukkaninsu ya zamana cewa shi kadai ake
bautawa. Nikam dama can zuciyata ta dade tana
rawa akan wannan abin bautar na mu, domin
sau tari yana barinmu muna shan bakar wahala,
da kyar muke tsira da rayuwarmu, to yanzu
kuma gashi shi da bakinshi yake cewa yana da
kishiya gami da abokin gaba amman muje zuwa
sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba.
Nan dai Maharaz da Hibru suka mike tsaye suka
fice daga cikin dakin bautar, kai tsaye suk koma
bakin kofar fada suka sake tsayawa, bayan sun
129

TASKARNOVELS.COM.NG
sauka daga kan dawakai sai sarki Maharaz ya
wuce zuwa kan mimbari yayin da Hibru ke take
masa baya, bayan sun hau kan mimbarin ne sun
tsaya sun masu fuskantar jama'a sai Sarki
Maharaz ya bayanin godiya ga jama'a uma yayi
gaisuwa ga baki wadanda suka zo daga sauran
makwabtan kasashe domin kawo agajin yaki
bisa kare mutuncin nahiyar gabadaya. Daga nan
sai yayi bayani ga jama'a inda ya kara masu
kwarin gwiywa da karfafesu bisa mahimmancin
wannan yaki da za'a fita. Yana gama wannan
jawabi ne jama'a suka barke da shewa aka hau
yi masa kirari.
Nan take sarki Maharaz da sarkin yaki Hibru
suka yi wa gabadaya jama'ar jagora, wato suka
wuce gaba aka bisu duw a baya. Inda ace mutum
na nan tsaye a wajen yaga wannan rundunar ke
fitowa daga cikin birnin darul mahabur sahu
sahu bisa rakuma, dawakai da alfadarai sai yayi
tsammanin cewa gaba daya mutanen duniya ne
suka fitowa saboda yawansu.
Wannan shine abinda ya faru a birnin darul
mahabur bayan kasashen dake nahiyar gaba
daya sun hada kai sun fita gagarumin yaki dan
kare buranensu daga sharrin sarki dujalu.
130

TASKARNOVELS.COM.NG

**********************

Al'amarin Sarki Dujalu kuwa lokacin daya
durfafi hanyar kofin bahar Suffiyya tare da
dandazon dakarunsa na yaki mutum miliyan
dubu daya da suke tafiya bisa wasu zaratan
dakarun aljanu suma miliyan dubu daya.
Wohoho! Hakika tashin hankali ba a samasa
rana zuwa yake ba sallama, idan mutum yayi
arba da wannan zuga ta rundunar sarki Dujalu
zai iya haukacewa koma zuciyarsa ta buga fat
daya, saboda tsananin kwarjininsu gami da bna
tsoro, idan aka ce zasu iya tashin duniyar nan
kaf a cikin sa'a daya su baje kaf biranen to ba za
ayi mamaki ba, idan suna tafiya a kasa bisa
turba aka hangosu daga nesa kamar zango dari
sai mutum ya jiyo takun sawayensu wnda ke
haddasa girgizar kasa, idan kuwa a sama suke
tafiya sai kaga sun haddasa gagarumar guguwa
wadda ke haddasa bishiyoyi su kama rangaji
suna karyewa da zubewa kasa, koguna kuwa su
kuma tambal-tambal suna zubewa kasa.
131

TASKARNOVELS.COM.NG
Sarki Dujalu na da matan aure guda dari da
goma sha daya, amman bai taba samun haihuwa
ba, bashi da iyaye kuma bashi da sauran dangi
face wata kanwarsa guda daya wacce ta kasance
kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance wacce
suke uwa daya uba daya ana kiranta da suna
Hursiyya. A duniya babu abinda sarki Dujalu ke
tsantseni sama da kanwarsa Hursiyya, domin ko
kadan baya kaunar abinda zai sosa zuciyarta ko
kuma ya taba lafiyarta, duk inda kaga sarki
Dujalu to fa sai kaga Hursiyya a damansa sam
basa rabuwa da juna dare da rana sai dai
kwanciyar bacci, kai wani lokaci ma akan cinyar
sarki Dujalu Hursiyya ke bacci yana shafa
gashin knta gami da raira mata wakoki masu
dadin sauraro ko kuma yana bata 'abarai masu
dadi da debe kewa, ko kadan Hursiyya bata da
sadaukantaka kuma sarki Dujalu bai bata sihirin
tsafin sa ba ko guda daya, wani babban abin
mamaki a tare da ita shine gabadaya halayenta
da ra'ayainta ya sha banban dana dan uwanta
sarki Dujalu domin bata son zalunci sannan tana
da yawon tausayi. A fagen kyautavkuwa tamkar
indararo dan ko yaushe hannunta a bude ya ke,
bisa wannan halayya tata ne yasa ta samu
daukaka da farin jini a wajen talakawan kasar,
132

TASKARNOVELS.COM.NG
har addu'a suke a boye suna fatan Sarki Dujalu
ya mutu ta haye kan karagarsa saboda sun san
cewa zasu samu yancin kansu. A rayuwar
Hursiyya babu abinda ta fi so sama sauraron
dadadan labarai, jarumtaka da kuma na
abubuwan al'ajabi. Bisa halayen Hursiyya na jin
kai da tausayi ne yasa sarki Dujalu ya tsani yin
tafiya tare da ita, domin ita ce kadai
mahalukiyar da take take masa burki wajen
tafiyar da zalunci a harkokin mulkinsa. Kai sau
tari ma ko zaman fada baya son yi tare da ita
saboda tana yawan katse masa hanzari,
kasancewar baya son ganin bacin ransa duk
alfarmar data nema baya fasa yi mata, sau tari
idan sarki Dujalu ya fusata saboda irin katse
masa hanzari da take yi, ko yayi yunkurin
dukanta sai ya kasa saboda alkawari daya
daukar wa mahaifiyarsu kafin ta mutu,
alkawarin kuwa shine ya rike mata Hursiyya
bisa amana, kuma komai ta yi bazai hukunta ta
ba, sannan zai kula da lafiyarta fiye da yadda zai
kula da tasa lafiyar. A duk sa'adda Dujalu ya
tuno da wannan alkawari sai ya cizi yatsa
kwallar takaici ta zubo masa.
A ranar da su sarki Dujalu suka shafe kwanaki
goma sha takwas suna tafiya ne izuwa tekun
133

TASKARNOVELS.COM.NG
bahar Suffiyya, sai suka yada xango a cikin wani
kyakkyawan daji mai yawan ni'ima, Kasancewar
yana dauke da koramai, bishiyoyi da kuma
kananun dabbobin daji masu saukin farauta
gami da kyawawan tsuntsaye, duk irin masifar
dake cikin daji da zarar rundunar su sarki
Dujalu ta ratso cikin daji sai masifar ta nemi
mabuya saboda taga sa gudu maganin ki gudu.
Bayan an kafa tantuna a cikin wannan daji mai
ni'ima an ci abinci an huta sai Hursiyya taga
sarki Dujalu ya kwanta yayi shiru ya shiga
zurfin tunani, al'amari daya sosa Zuciyarta
kenan ta dube shi ta ce ya kai dan uwana ina
dalilin wannan tunanin naka haka mai zurfi,
shin kana wasi-wasi ne akan samun nasarar mu
ne akan wannan yaki da muka fito ko kuma
kana tunanin yadda zuwa nan gaba zaka mulki
duniya ne?
Yayin da sarki Dujalu yaji wadannan tambayoyi
daga bakin yar uwarsa Hursiyya ai yayi
murmushi sannan ya sake gyara kwanciyarsa a
saman lallausar shinfidarsa irin tasu ta sarakai,
ya dubi Hursiyya cikin natsuwa yace da ita ya ke
yar uwata kiyi sani cewa duk abinda ika fada ba
shi nake tunani ba, ina naxari ne akan yadda
134

TASKARNOVELS.COM.NG
soyayya takai Mazan Jiya zuwa ga halaka, har
suka rasa komai na duniya, bisa wannan dalili
ne nayi alƙawarin cewa bazan taba yarda naso
mace fiye da kima ba, domin ita soyayya siradin
mutuwa ce, duk wanda ya taka siradin ba
makawa sau ya hallaka, haka nan kaidin mace
yafi tsinin allura tsini kuma yafi kaifin zabira
kaifi, komai jarumtakar mutum kuma komai
karfin mulkinsa da karfin arzikinsa mace na iya
maida shi rago, fakiri kuma bawa kamar yadda
ta faru ga Mazan Jiya irin su Sadauki Hantaru.
Koda jin wannan batu sai Hursiyya ta gyara
zama sannan ta ce ya kai dan uwana na rokeka
bisa darajar mahaifiyarmu ka bani labarin
Mazan Jiya da yadda aka yi soyayya ta jefa su ga
halaka.
Dujalu ya gyada kai tare d cewa ai kin
tambayeni labari mai tsawo, wanda in muka
farashi ban san ranar gamawa ba, sai dai yana
dauke da darasi mai yawa a cikinsa domin zaki
samu ilimin zaman duniya, za kuma kiji yadda
ake yaudara ta rashin mutunci gami da
mummunan cin amana, sannan kuma zaki ji
abin tausayi wanda nasan dole ne ki zubar da
hawaye, ke idan kika ji wannan labari kin daina
135

TASKARNOVELS.COM.NG
yarda da kowa a duniya koda kuwa iyayen da
suka haifeki ne.
Hursiyya ta sake gyara zama ta ce dan darajar
tsafinka da darajar mulkinka ka gaggauta far
banu wannan kasaitaccen labarin, ina mai
tabbatar maka da cewa ko ina mai tabbatar
maka da cewa koda zamu kwana kana jawabi
bazan gaji ba, kuma bazan ji bacci ba.
Sa'adda da sarki Dujalu yaji haka sai ya bushe
da dariya sannan ya ce to shikenan bari na
jarabaki na gani idan har zaki iya jurewa, Dujalu
yayi gyaran murya sannan ya fara bada labarin
da cewa:
Kimanin shekara tamanin da suka shude, anyi
wani adalin sarki mai suna Kusaidu a birnin
Kisra, Sarki Kusaidu ya mallaki dukiya mai
tsananin yawa, sannan yana da tarin mayaka
Hakazalika akwai manya manyan birane a
karkashinsa kimanin guda 40, sarkin Kusaidu
nada matar aure guda daya jal wadda suka yi
auren saurayi da budurwa ana kiranta Bazira,
har bayan shekaru oma da aurensu amman
nasu taba samun haihuwa ba, ko kadan wannan
matsala bata damu Bazira ba. Amman shi sarki
136

TASKARNOVELS.COM.NG
Kusaidu duk sa'adda ya kalli yawan dukiyarsa d
kuma karfin mulkinsa ya kuma tuna cewa bashi
da magaji sai yayi ta kuka, babu irin neman
maganin da sarki Kusaidu baiyi ba amman abu
ya gagara, domin saida ya ziyarci ko wanne
bangare na duniya dan ganawa da manyan
bokaye amman abu ya cutura.
Lokacin da Fazira taga hankalin sarki ya ki
kwanciya bisa ga matsalar rashin haihuwa, sai
ta kadaita da shi ta ce ya kai mijina ka yi sani
cewa a duniya bani da farin ciki sai naka, kuma
bakin cikinka nawa ne, ni a tawa shawarar
tunda dai ni ban haihu da kai ba me zai hana ka
kara aure, ko a dace a samu biyan bukata?
Koda jin wannan batu sai Sarki Kusaidu ya cika
da tsananin mamaki ya ce da ita Kaicon ki ya ke
mata ta, tun kafin muyi aure kika kafa mani
dokar cewa daga kanki bazan kara ba, kuma na
amince da haka ko kin manta ne?
Da jin haka sai hawaye ya zubo wa Fazira ta ce
ai wata larurar tana kawar da wata, nidai a halin
yanzu na janye wannan sharadin in har
soyayyata da taka ka tabbata gaskiya ce to ka yi
aiki d wannan shawara tawa.
137

TASKARNOVELS.COM.NG
Yayin da Sarki Kusaidu ya ji hkaa sai yayi shiru
yana tunani ba tare da yace da ita komai ba har
izuwa lokaci mai tsawo, daga can kum sia ya
dago kai ya dubi Fazira ya ce ki dan bani
kwanaki uku zan yi shawara tukunna.
Koda jin haka sai Fazira ta cika da farin ciki
kuma ta rungume sarki Kusaidu tare da
sumbatar goshinsa kna daga bisani ta fice daga
cikin turakar tana tsalle gami da murna, ba
kaomai ne yasa Fazira farin ciki ba, sai sanin
cewa sarki Kusaidu bashi da wani abokin
shawara wanda ya wuce bokansa mai suna
Boka Ardusa Bn Zabbar. Fiye da shekaru talatin
sarki Kusaidu ake harka da boka Ardusa kuma
ya yard da shi dari bisa dari, babu wani sirri
nasa wanda bai sni ba. Sai dai abin bakin ciki da
takaici shine duk tsawon wadannna shekaru
boka Ardusa na cin amanar sarki Kusaidu ba
tare da ya sani ba. Domin Ardusa ya mayar da
Fazira matarsa ta sirri, wannan cin amana ya
samo asaline tun daga lokacin Fazira ta so ta
auri Sarki Kusaidu, kasancewarta yar wazirin
mahaifinsa amma sai sarki Kusaidu ya nuna ko
kadan baya sonta da aure, domin ya dauketa
kamar kanwarsa ta jini, dalili kuwa shine a
gidan su Fazira sarki Kusaidu yayi wasan kasa
138

TASKARNOVELS.COM.NG
saboda akwai yayan Fazira sa'ansa ne, kuma
abokinsa wanda suka shaku ainun har ya
zamana cewa basa rabuwa dare da rana
sunansa Asharab. Tun Fazira na karama jininta
ya hadu dana Sarki Kusaidu take matukar
kaunarsa, lokacin da Fazira ta cika budurwa sai
masoyanta suka yi mata ca! Sabida ta kasance
kyakkyawar gaske, ita kuwa sai ta tubure ta ce
babu wanda take so face yarima Kusaidu.
A wannan lokaci mahaifin sarki Kusaidu ne yake
mulkin birnin Kisra, kwatsam! Sai aka wayi gari
Asharab ya kamu da rashin lafiya har ta kaishi
ga kwanciya, al'amarin daya dugunzuma
hankalin Yarima kusaidu kenan ya koma gidan
su Asharab ana jinyarsa kenan dare da rana ya
zamana cewar yayi wa gidan sarki kaura
gabadaya, a ranar da Asharab ya kwana tara
yana jinya ne sai rai yayi halinsa, bakin ciki a
wajen Kusaidu bazai fadu ba, domin sai da ya
kwana uku bai ci abinci ba, kuka kuwa dare da
rana haka ya dinga yi babu sassauci, nan da nan
ya rame ya kuma lalace da kyar aka samu ya
dawo daidai ya ci gaba da rayuwa kamar yadda
ya saba, tun daga lokacin da Asharab ya rasu sai
Kusaidu ya dauke kafarsa daga gidansu Fazira
gabadaya ya daina zuwa, hakan ne ya tada
139

TASKARNOVELS.COM.NG
hankalin Fazira ta dinga biyoshi har gida tana
nuna masa soyayya, shiko ya dinga nuna mata
cewa shifa kanwa ya dauketa ba masoyiya ba,
har Fazira ta girma ta cika ya mace nan fa ta
cigaba da kokarin janye hankalin Yarima
Kusaidu amman ya ki amincewa da ita.
Sai bayan da mahaifin Kusaidu ya rasune ya gaji
sarauta sannan ta soma samun yardarsa
albarkacin boka Ardusa. Shidai boka Ardusa
hadimin mahaufin sarki Kusaidu ne, ganin haka
ne yasa shima Kusaidu ya aminta da shi.
A ranar farko da Fazira ta je wajen boka Ardusa
da bukatarta ta son auren satki kusaidu, sai ya
nuna mata bukatarta mai sauki ce amman fa sai
idan ta yarda ta bashi kanta. Sai da Fazira ta
shafe wata uku tana nazarin wannan sharadi a
karshe dai taga cewa in har bata amince da
sharadin boka Ardusa ba, to fa bazata taba
samun damar auren sarki Kusaidu ba. Kawai sai
ta abince d shi din, a ranar da abin ya faru ne
Sarki Kusaidu ya amince da batun aurenta, da
mako ya dawo aka daura auren amman duk da
cewa Fazira ta auri sarki bata daina zuwa wajen
Ardusa ba sun lalatrsu a sirrance, ita kanta
Fazira ta yi mamakin yadda ak yi ta cigaba da
140

TASKARNOVELS.COM.NG
yarda da boka Ardusa, abinda bata sani ba
shine, ya asirceta ne babu yadda za'a yi ya
bukaceta ta ki yarda. Haka dai Fazira da Ardusa
suka cigaba da cin amanar sarki Kusaidu har
tsawon shekaru sirinsu bai taba tonuwa ba.
Bayan Fazira taji cewar sarki Kusaidu zai yi
shawara sai ta saci jiki ta wuce zuwa gidan boka
Ardusa nan ta sanar d shi abinda ya faru da
sarki, ta kuma ce lallai ya baiwa sarki shawarar
ya kara aure.
Boka Ardusa ya kyalkkyale da dare tare da cewa
amman ke meye hikimarki akan bashi wannan
shawara?
Fazira ta dubi boka Ardusa cikin nutsuwa ta ce
da shi ka yi sani cewa har abada sarkk ba zai
taba haihuwa ba, tunda matsalar rashin
haihuwar daga gareshi ta ke, ni kuwa zan iya
haihuwa, idan ya auro wata matar ina so kayi
aikinka na bokaye kaga ta samu juna biyu,
inyaso cikinka da nake dauke da shi a yanzu in
na haifeshi sai ya tashi a matsayin dan amaryar
sarki, kaga kenan danmu ne zai gaji sarautar,
nasan tabbas zaka iya boye nawa cikin har na
haihu ba tare da mutane sun sani ba.
141

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Fazira tazo daidai nan a batunta sai
boka Ardusa ayi shiru, ya fada dogon tunani
gami da nazari, daga can sai ya bushe da dariya
harda buga kafa a kasa yana mai cewa Hakika
ku mata ababan tsorone, ta yaya kika iya kulla
wannan dogon makircin acikin dakiku kadan?
Nikam tunda nazo duniya ban taba ji ko ganin
yaudara da makirci irin wannan ba.
Fazira ta bushe da dariyar murna tare da cewa
ai bakaga komai ba sai nan gaba tukunna
sannan ne zaka gane mu mata mune muke
sarrafa duniya da duk abinda ke cikinta, muke
haddasa zaman lafiya da rashinsa, kai ko yaki
idan kaga ya barke ba zato ba tsammani idan ka
yi bincike zakaga snadinsa mune.
Koda gama fadin haka sai Fazira ta mike da
sauri, tayi wa boka Ardusa sallama domin a
wannan lokacin yamma ta yi likis, ta tashi tayi
tafiyarta, kuma a wannan lokaci an kusa tashi
daga fada, tana tsoron kada sarki ya nemeta
bata nan.
Kamar yadda Fazira ta shirya makircinta haka
al'amuran suka kasance, wato sarki Kusaidu ya
auro wata kyakkyawar budurwa jinin sarauta
142

TASKARNOVELS.COM.NG
mai suna Shamilat acan wata kasa dake
makwabtaka da birnin Kisra mai suna Darul
Maabur. Wata uku da tarewar amarya Shamilat
sai ga ciki ya bayyana, amman abin mamaki
shine ko kadan amarya bata ji wani sauyi a
jikinta ba, kuma bata yin wata lalura irin ta
masu ciki.
Sannu a hankali ciki ya rika girma har ya cika
wata tara rana daya sai nakuda tazo wa
Shamilat, mata suka taru akanta amman saida
Shamilat ta kwana ta wuni tana nakudar bata
haihuba. Al'amarin da yayi matukar dugunzuma
hankalin sarki kenan ya kasa zaune ko tsaye.
A lokacin da shamilat ta samu juna biyu irin
farin cikin da sarki Kusaidu yayi ya wuce gaba
tunani, domin sai da ya kusa zaucewa saboda
tsananin farin ciki, ya rika kyautar dukiyarsa
dare da rana, kai sai da takai hatta suturar dake
jikinsa yana cirewa gami da baiwa barorin dake
gidan sarautar, har sai da aka kulleshi a daki
kuma aka hanashi fita.
Yayin da nakudar amarya Fazira ta ki cinyewa
sai ga uwargida Shamilat ta zo dakin haihuwa,
da zuwanta sai ta kuri duk matan dake baiwa
143

TASKARNOVELS.COM.NG
Shamilat agaji ta ce duk basu san aikinsu ba ma,
kawai sai ta kulle kofar dakin ya zama cewa
daga ita sai mai nakudar a cikin dakin, nan take
ta shafa cikin amarya Shamilat ai kuwa sai
hankalinta ya gushe ta suma, Fazira ta shafi nata
cikin kawai sai ga tsohon cikinta ya bayyana
kuma nan take nakuda ta zo mata, bayan kamar
rabin sa'a Fazira ta haifo santalelen yaro
kyakkyawan gaske, cikin hanzari ta gyara jikinta
sannan ta gyara jaririn ta ajiyeshi daf da
amarya, daga nan ta sake shafar cikin anarya a
karo na biyu sai ga jinin haihuwa na zubo wa
daga jikinta. Jim kadan amarya ta farfaɗo aiko
sai ta ji jariri na tsala kuka a kusa da ita.
Koda sauran mutanen gida suka jiyo kukan
jariri sai suka rugo izuwa dakin haihuwar suna
shewa gami da murna, cikin matukar mamaki.
Ai kuwa labari na riskar sarki sai kuwa ya fito
daga cikin turakarsa tare da fadawa dakin
haihuwar ya dauki jaririn ya rungumeshi yana
kukan farin ciki.
Sai da aka kwana talatin ana bukukuwa da
walimar farin ciki a birnin Kisra saboda murnar
wannan haihuwa da akayi wa sarki Kusaidu.

144

TASKARNOVELS.COM.NG
A kwana a tashi dan da amarya ta haifa mai
suna Hantaru ya fara girma ya cikq shekaru
biyar, Hantaru ya taso yaro kyakkyawa mai
jarumtaka tq ban al'ajabi, domin tun yana da
shekaru iyar yake iya daukar abubuwa masu
nauyin gaske, idan kuwa yana wasan kokawa a
cikin sa'anninsa babu mai iya kada shi. Kai sai
da takai cewa yaran da suka girmeshi ma kada
su yake yi. Lokacin da Hantaru ya cika shekaru
tara sai ya zama cewa yana
End Ads