x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - MAZAN JIYA 1

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 216

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
yake yini, shine mai nuna wa sarki
kauna fiye da kowa, hatta masu baiwa sarki
257

TASKARNOVELS.COM.NG
magani bai yarda da su ba, sai ya tabbatar da
ingancin maganin sannan yake yarda a baiwa
sarki maganin ya sha.
Wannan hali da sarki Kusaidu ya shiga sai ya
zamo tamkar samun dama a wajen Ardusa da
Zarifa suka shagala da more rayuwarsu wajen
cin amanarsa.
A duk sa'ad da Zarifa ta bukaci boka Ardusa yayi
bincike akan halin da Yarima Hantaru ke ciki sai
ya kwantar mata da hankali yace ai yarima
Hantaru yana nan lafiya lau, kuma zai dawo
birnin Kisra a lokacin da sarki kusaidu zai mutu
ya haye karagar mulkinsa.
Lallai a wannan lokaci ne zamu sanar da yarima
cewar mune iyayensa na gaskiya, kuma babu
yadda zai yi dole ne ya karbemu a matsayin
iyayen nasa, kuma ya girmamamu. Wannan
kalamai na boka Ardusa ba karamin faranta wa
Zarifa rai yake yi ba, sai kawai ta rungume boka
Ardusa su ci gaba da sharholiyarsu.
A zahirin gaskiya boka Ardusa yayi iyakar
kokarinsa wajen gano halin da Hantaru yake
ciki a cikin hallarar tsafi da mahaifiyarsa acan
birnin darul habur amman abu ya gagara, duk
258

TASKARNOVELS.COM.NG
sa'ad da ya matsa akan bincike sai madubin
tsafinsa yayi bindiga ya tarwatse. Al'amarin
daya dugunzuma hankalinsa kenan ya gane
cewa lallai akwai wani babban bokan dake boye
sirrin yarima acan birnin Darul Habur, abinda
bai sani ba shine ba wani boka bnae face
malaminsa a harkar bokanci wanda tuni ya dade
d yin gaba har ma ya baiwa yan bayansa sirrinsa
wato boka Sulbaini.
Abinda boka Ardusa ya gano a cikin bincikensa
kawai shine nan da shekaru uku masu zuwa
yarina Hantaru zai dawo gida, wannan shine
abinda yasa hankalinsa ya kwanta, ya amince da
cewar zai cigaba da jiran dawowar yarima
Hantaru.
Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, domin
inda boka Ardusa yasan abinda zai biyo baya
idan yarima hantaru ya dawo gida da ya kashe
kansa saboda munin abin takaicin da zai samesu
shi da farkarsa Zarifa.

259

TASKARNOVELS.COM.NG
Acan kuwa birnin Darul Habur bayan kimanin
wata daya da yin gasar neman auren gimbiya
Larziyya, sai bangarorin biyu suka shiga shirye
shirye gasar da za a yi nan da watanni goma sha
daya masu zuwa, ya zamana cewa sun dage
ainun dan ganin cewa idan lokaci yayi su samu
nasara. Dare da rana kuma kullum Hantaru da
Rabbasu cikin basu horo ake na kara wa jikinsu
juriya da zafin nama gami da tsananin gudu, sai
da takai cewa kowannensu na iya yin azabben
gudu wanda a cikin rabin sa'a zai shafe tafiyar
yini guda.
Haka suka cigaba da baiwa jikinsu horo har
tsawon wata goma sha daya, a tsawon wannan
watanni tsakanin Hantaru da Rabbasu Babu
wanda ya kara ganin fuskar gimbiya Larziyya
saboda sarki ya sa an tsareta a gidan sarauta,
babu wani mahalukin da ya isa yaje inda take,
kuma itama bata isa taje ko ina ba.
Da kyar da sidin goshi kuma a sirrance Gimbiya
Larziyya ta samu damar aika wa da Sadauki
Hantaru wasikar soayayya a cikin kwana talatin,
duk sa'ad da wasikar ta riski Hantaru baya
ganin komai a cikin takardar face kalaman kuka
da bakin ciki bisa dalilin rashin saduwarsu,
260

TASKARNOVELS.COM.NG
gami da baitocin waka na kara kaimi da kuma
shawara kan lallai ya kara kaimi wajen ganin
cewa ya samu nasara lashe wannan gasa da za'a
yi ta neman aurenta a karo na biyu.
Baya ga haka kuma a koyaushe tana yi masa
tuni bisa alkawarin daya daukar mata guda uku,
alkawari na farko;
Shine komai rintsi ba zai janye ba, alƙawari na
biyu kuwa shine duk alfarmar data nema a
wajensa zai yi mata, alkawari na karshe wanda
shine cikon na uku kuwa shine a duk halin da
suka cintsi kansu a ciki ba zasu guji juna ba.
Ko sau daya Hantaru bai taba saba wa aika wa
da Gimbiya Larziyya amsar wasikarta ba, kuma
a koyaushe yana kara tabbatar mata da cewa
alkawarinsu yana nan babu abind zai tashe shi
har abada.
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a
je ba, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da
suka ce rana bata karya sai dai uwar diya ta ji
kunya, a kwana a tashi sai ranar gasa karo na
biyu ta dawo.

261

TASKARNOVELS.COM.NG
Ai kuwa a wannan rana sai da hankalin
gabadaya mutanen birnin Darul Habur ya
dugunzuma saboda tsananin yawan al'ummar
da suka cika wannan gari, tamkar mutane
duniya ne suka hallara.
A wannan rana anyi muguwar bakar gasa ta
tashin hankali, wacce ta zamo sanadiyyar ajalin
gaba daya dakarun gasar face na mutum biyu
rak wato Hantaru da Rabbasu, suma din sai da
kowannensu ya suma sau uku, kuma a karshe
suka sake yin ragas kamar yadda al'amarin ya
faru a gasar farko, wato a lokaci guda suka kama
barewar gasa kuma suka tsinkata gida biyu. A
wannan rana Sadauki Rabbasu kwana yayi yana
kukan bakin ciki, haka dai ya rungumi kaddara
bisa dole ya cigaba da hankoro zuwan Shekarar
gaba.
A takaice dai sai da aka yi gasa sau uku ba
zakara sai ragas ake yi tsakanin Hantaru da
Rabbasu, a ranar da akayi gasar ta uku ne
shugaban alkalan gasar wato sarkin birnin
Darul Habur wato mahaifin Gimbiya Larziyya ya
yi bayanin cewa tunda dai wadannan zaratan
jarumai sunyi ragas har sau uku akan gasar
neman auren yarsa, to yanzu za suyi gasa ta
262

TASKARNOVELS.COM.NG
karshe mai tsananin wahalar da ko dayansu
yayi nasara ko kuma duk su biyun su hallaka,
idan kuma suna ganin cewa b zasu iya yin gasar
ba to sai dai duk su biyun su hakura da neman
auren Gimbiya.
Sarki yayi gyaran murya sannan ya cigaba da
cewa ita dai wannan gasa ta karshe bata komai
bace sai ta tafiya izuwa kogon mazabatul
hirsham dake can karshen dajin hayatul Maut
dan dauko takobin Saiful Lujara.
Koda sarki ya zo nan a jawabinsa sai filin gasar
ya rude da hayaniya da ka-ce-na-ce saboda
sanin masifun dake dajin hayatul Maut.

Dajin hayatul Maut yayi kaurin suna a ko ina a
wannan zamani, domin dajine fiye da shekaru
dubu da suka gabata babu wata halitta da ta
taba shigarsa ta fito, duk abinda ya shiga cikinsa
ya shiga kenan, har abada b za a sake jin
263

TASKARNOVELS.COM.NG
duriyarsa ba, walau mutum ko aljan ko dabba
ko tsuntsu, kai bama cikin dajin hayatul Maut
ba, hatta gefen dajin ba a bi.
Lokacin da filin gasar ya rudu da ka-ce-na-ce sai
sarki yasa aka busa kaho kowa yayi tsit tamkar
mutuwa ce ta gifta. A sannan ne sarki ya dubi
Hantaru da Rabbasu wadanda ke duke a
gabansa cikin mugun yanayi na galabaita mai
kama da suma y ce Ya ku wadannan manyan
zakuna ababan kwatance, kuyi sani d cewa daga
yau har duniya ta nade ba za a manta da
jaruntakarku ba, to amman fa ba zaku cika
mazan jiya ba sai idan kunyi wannan gasa ta
karshe, dayanku ya samu nasarar dauko takobin
Saiful Lujara, shin kun amince zaku siyar da
rayuwarku domin neman suna da neman auren
yata?
Koda jin wannan tambaya sai Sadauki Rabbasu
yayi farat ya ce ya shugabana kayi sani cewa
rayuwata bata da wani amfani muddin ban
mallaki gimbiya Larziyya ba, kuma ban kare
martabar zuri'ata ba ta mafarautan wannan
Birni, saboda haka na amince na siyar da raina
domin cikar burina da burin zuri'ata.

264

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai jama'a suka sake
barkewa da sowa, aka hau buga tambura da
ganguna ana yiwa Rabbasu kirari da jinjina, sai
da sarki yasa aka sake busa kaho sannan jama'a
suka yi tsit a karo na biyu.
Sarki ya dubi Sadauki Hantaru ya ce ya kai
wannan namijin duniya ka ji abinda abokin
gasarka ya fada, kai kuma me zaka iya cewa?
Hnataru yayi ajiyar zuciya ya ce ya kai wannan
sarki mai daraja, ka yi sani cewa a duniya babu
wani abu mai daraja wanda yakai faranta rab
masoyi, lallaı bani da masoyi wanda ya kai
mahaifiyata da kuma abar begena Gimbiya
Larziyya, mahaifinta bata da wani buri face ace
yau kambun gasa ya dawo hannun zuri'arsu ta
makeran wannan birnin, haka kuma masoyiyata
bata da wani buri da ya fi ace yau nine zakaran
gasar neman aurenta, bisa wannan dalilai dana
wassafa na amince na sallama rayuwata domin
faranta ran zuciyoyin wannan masoya nawa
guda biyu.
Koda jin haka sai jama'a suka sake barkewa da
shewa gami da ihu, masu buga ganga nayi, masu
busa algaita da tambura ma nayi. Sai da aka dan
265

TASKARNOVELS.COM.NG
jima ana cashewa sannna aka busa kaho kow
yayi shiru, saannan sarki yayi gyaran murya ya
ce to jama'a kunji abinda zaratan jarumanmu
suka fada, saboda haka kofa a bude take ga
dukkanin jarumi wadanda suka ga zasu iya
shiga wannan gasa wato su bi su Rabbasu izuwa
dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul
Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Ko da
mutum bai yi nasara ba, zai yi suna, idan kuma
suna bai samu ba rayuwa zata salwanta, wanda
duk yake ganin zai iya bin wadannan Sadaukai
ya bayyana kansa yanzu.
Koda gama fadin haka sai sarki yayi shiru ya
kama kalle kalle yana mai duban gabas da
yamma kuma kudu da arewa ko zaiga wani
jarumin da zai fito ya kawo kansa, tsawon lokaci
ba asamu mutum daya da ya fito ba.
Ko da ganin haka sai sarki yace na sallami kowa
da kowa, domin ta tabbata cewa wadannan
zaratan jaruman guda biyu sune kadai zasu yi
wannan tafiya, da wannan furuci nake sallamar
kowa, sai kuma bayan kwana talatin zamu yi
sallama da jarumanmu biyu domin su tafi dajin
hayatul Maut, zamu ba jaruman mu adadin
kwanaki arba'in wanda duk ya dawo daga dajin
266

TASKARNOVELS.COM.NG
hayatul Maut dauke da takobin Saiful Lujara a
cikin kwanaki arba'in din a cikinsu to shine zai
zamo mijin ya ta gimbiya Larziyya, kuma ya cika
namijin duniya Sarkin Sadaukai wanda har
abada tarihin jarumtakarsa ba zata taba
gushewa ba, kuma idan yaso zai iya mulkar
duniya gabadayanta saboda sihirin dake jikin
wannan takobi da ya mallaka ta Saiful Lujara.
Koda jin wannan batu sai jama'a suka cika da
tsananin al'ajabi kowa ma yaji inama zai iya
saida rayuwarsa ya tafi neman wannan takobi.
Nan dai mutane suka yita fadar albarkacin
bakinsu, aka kwashi Hantaru da Rabbasu a
matukar galabaice tamkar wadanda suka
shekara suna jinyar cuta aka tafi da su gida,
haka yasa taro ya watse kowa ya kama gabansa.
A wannan karon ma Samilat ce ta yi jinyar
Hantaru har tsawon kwanaki ashirin, sannan
jikinsa y dawo daidai ya samu lafiya. A kullum
dan Salimat ta dubi Hantaru ta tuna saura
kwanaki kadan su rabu, Rabuwar da babu
tabbacin su sake saduwa sai ta fashe da
matsanancin kuka. Da kyar da sidin goshi
Hantaru yake rarrashinta ya kuma bata baki
sannan take daina kukan. A koyaushe Hantaru
267

TASKARNOVELS.COM.NG
yana kara kara mata gwarin guiwa da cewa ya
ke ummina kiyi sani cewa da zarar na dawo ne
zamu koma can birnin Kisra tare da amarayata
Gimbiya Larziyya ki sadu da mijinki, mu cigaba
da sabuwar rayuwa, kuma a sannan ne zanyi wa
boka Ardusa da mahaifiyata larifa hukunci da ya
dace dasu bisa cin amanar mijinki da suka yi.
A duk sa'ad da Hantaru yayi wannan furuci a
gareta sai ta sake fashewa da kuka ta ce ya kai
dana ka yi sani cewa har abada komi lalacewar
iyaye, iyaye ne. Kada ka kuskura kace zaka
hallaka Ardusa da Larifa bisa cin amanar d suka
yi wa mijina, kai dai kawai ka tona masu asiri
domin su zamo abin kwatance ga al'umma
kuma darasi ga al'umma, ni dai bukatata a
gareka ita ce, duk matsayin da ka kai a duniya
kada ka gujeni, domin bani da wani face kai, duk
da cewa banice na haifeka ba, ina jin a raina
cewa ko a nan gaba bazan so dan da zan haifa
kamar yadda na so ka ba. Ya kai Hantaru ka rike
ni a matsayin uwa mahaifiya, kuma ka sani
kamar yadda kowanne da ke son uwarsa, burina
shine koda mai rabawa zata rabamu mu rabu da
soyayyar juna.

268

TASKARNOVELS.COM.NG
Yayin da Hantaru ya ji wannan batu sai ya
rungumeta kuma ya fashe da kuka yana mai
cewa har abada bazan gujeki ba yake ummina,
kece uwata a zahiri, kuma kece uwata a badini.
Kaico! Hakika kowa ya rasa masoyi yayi kuka, a
duniya kaf babu abinda yafi farin ciki kamar
samun masoyi, inda ace mutum na nan a lokacin
da wadannan masoya suka rungume junansu
sun kuka dan alhinin rabuwar da zasu yi nan
bada daddewa ba, dole ne tausayinsu ya kmashi
har ya zubar da hawaye, domin shakuwar dake
tsakaninsu da sabo da juna ya wuce ayi misali
face abinda zuciya ta kintata.
A ranar da kwanaki talatin suka cika ne Hantaru
ya gama shirya kayansa domin tafiya izuwa
dajin hayatul Maut dan dauko takobin Saiful
Lujara, lokacin da yazo yin bankawana da
Salimat da kuma iyayenta, sai zuciyarsa ta
karaya ya fashe da kuka ya kasa cewa komai a
garesu, koda ganin haka sai duk su ukun suka
fashe da kuka suma suka rungumeshi suna
masu kankame shi a jikinsu tamkar ba zasu
barshi yayi wannan tafiya ba.

269

TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam sai suka ji alamar motsin tafiya ana
shigowa cikin gidan, cikin hanzari suka wauga
suka yi arba da wanda ya shigo, ba kowa bane
sai boka Sulbaini mahaifin Shuraim.
Sulbaini ya tsaya cak yana kallon Hantaru shi
kadai, a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla
sannan sai ya dubi Salimat ya fara zubar da
hawaye.
Koda ganin haka sai Salimat da Hantaru suka
ruga gareshi suka rungumeshi shi tare da
fashewa da matsanancin kuka har zuwa lokaci
mai dan tsawo, daga can sai Salimat ta janye
jikinta daga nasa, suka fuskanci juna sosai
sannan ta ce ya kai kakana mene ne dalilin da
yasa kake kuka a yanzu, alhalin kaine ya kamata
ka karfafi zukatanmu bisa wannan tafiya da
dana zai yi.
Sa'ad da Sulbaini ya ji wannan tambaya sai ya
kama hannu Salimat ya jaya gefe guda inda babu
wanda zai ji abinda zasu tattauna da ita, ya
shiga yo mata wadansu bayanai, tunda ya fara
bayanan Salimat ta fara kuka, aiko yana gamawa
sai ta rushe da matsanancin kuka, kuma ta
rungumeshi tana mai kankameshi a jikinta
270

TASKARNOVELS.COM.NG
kamar wani zai kwace mata shi, da kyar Sulbaini
ya cire jikinsa daga nata sannan ya taho gaba
hantaru ya tsaya daf da shi har suna iya jin
numfashin juna, Sulbaini yayi murmushi mai
taushi ga Hantaru sannan ya ce ya kai namijin
duniya kayi sani cewa nazo ne domin muyi
bankwana, kuma nayi maka tuni bisa abinda na
fada maka a baya idan baka manta ba, a ranar
da kuka je gidana nayi maka gargadi akan kada
ka kuskura Gimbiya Larziyya ta umarceka da
yin abinda zai lalata alakar ka da jikita wata
Salimat, bayan ka samu nasarar dauko takobin
Saiful Lujara, idan ka kuskura ka aikata hakan
tabbas zaka yi biyu babu a rayuwa, domin zaka
rasa masoyanka kuma ka rasa daukakarka, har
ya zamana cewa ka gwammace mutuwa da
rayuwa, saboda haka ka kiyaye kuma kayi
matukar nazari a duk lokacin da Gimbiya
Larziyya ta zo maka da bukatarta.
Lokacin da Hantaru ya ji wannan batu sai yayi
murmushi yace kada ka damu ya shugabana,
lallai zaka samenk mai kiyayewa bisa wannan
shawara daka bani.
Gama fadin haka keda wuya sai ga wani manzo
yazo daga gidan sarki. Da zuwansa sai ya fadi
271

TASKARNOVELS.COM.NG
gaban Shuraim ya ce ya shugabana sarki ne ya
aikoni yace na sanar da kai cewa ana juran
Hantaru a fada domin a sallamesu shida abokin
tafiyarsa Rabbasu.
Koda jin wannan batu sai Hantaru ayi wa
mutanen gidan sallama karshe, ya kama doki ya
hau ya tafi izuwa fada yana waugen su Salimat
yana zubar da hawaye, suna zub da hawayen
suma, masu daga masa hannu nayi haka dai har
ya mace masu da gani.
Lokacin da Hantaru ya isa fadar Sarki sai ya iske
tuni Rabbasu na zaune a gefe daya cikin
gagarumar shigar yaki yana muzurai tamkar zai
ci babu, da zuwa sai Hantaru ya wuce gaban
Sarki ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, sannan
ya koma gefe daya ya zauna shima, inda suka
fuskanci juna shida Rabbasu.
Koda suka hada ido sai Rabbasu ya daka wa
Hantaru harara, wacce inda karamin jarumi yayi
wa ita zai iya tsurewa ya kama gudawa, shi
kuwa Hantaru sai yayi murmushi kawai ya
kawar da kansa ga barin kallon Rabbasu.
Ashe duk abinda ya faru sarki ya lura dan haka
shima sai yayi murmushi ba tare da yace komai
272

TASKARNOVELS.COM.NG
ba. Nan take sarki ya tura aka kira Gimbiya
Larziyya ta zo ta zauna daf da sarki, a wannan
lokaci fada ta cika taf da jama'a babu masaka
tsinke face inda sarki da jam'arsa ke zaune.
A wannan rana dai Gimbiya Larziyya ta ci ado
na gaban kwatance irin wanda ba a taba ganinta
da shi ba, kuma ta bar fuskarta a bude sabanin
rufeta da take yiko gaishe. Wohoho! Lokacin da
Gimbiya ta fito ta nufu inda karagar sarki ta ke
tana yin tafiyar kasaita, sai ganadaya jama'ar
dake fadar suka zuba mata idanu, kuma take
suka dimauce saboda ganin tsananin kyawunta,
da yawan jama'a basu san sa'adda yawu ya ka
dalala da cikin bakinsu ba tamkar basu taba
ganin gimbiya ba.
Hatta Hantaru da Rabbasu ai da suka firgice
suka bita da kallo, ko kifta ido basa yi, domin
basu san cewa kyawunta ya wuce yadda duk
suke zammani ba sai yau. Kai shi kanshi
mahaifin nata binta yayi da kallo ya kama wasiwasi a zuciyarsa yana mai cewa anya kuwa
wannan Larziyyata ce, yaya aka yi naga
kyawunta ya zarce na kullum a yau?

273

TASKARNOVELS.COM.NG
Abinda sarki bai sani ba shine tsananin
kwalliyar data yi ne gami da tsaba adon da ta yi,
suka kara mata kyau na ban al'ajabi, domin idan
kyau ya hadu da kyau sai idanuwa su kasa
banbance wanda yafi wani.
Bayan Gimbiya Larziyya ta zauna kan wata
kujera ta alfarma wacce ke kusa da karagar
sarki, sai sarki yasa hannu a cikin aljihunsa ya
dauko wani dan karamin madubi na tsafi ya
ajiyeshi a tskiyar fadar, sannan yayi gyaran
murya ya ce ya ku jama'ar birnin Darul Habur,
kuyi sani cewa ayau ne masoyan yata Gimbiya
Larziyya wato masu neman aurenta, zasu yi
gagarumar tafiya dan tabbar da gasa ta karshe a
tsakaninsu, domin fitar da zakaran da zai zama
mijin Gimbiya, kowa ya sani wannan gasa b
komai bace face tafiya zuwa dajin hayatul Maut
dan shiga kogon Mazabatul Darshal a dauko
takobin Saiful Lujara. Duk wanda ya dauko
wannan takobi ya zo da ita tsakanin Hantaru da
Rabbasu shine mijin ya ta.
Koda sarki yazo nan a zancensa sai fada ta rude
da shewa, sai da sarki ya daga hannu aka yi tsit
sannan ya dubi Hantaru da Rabbasu ya ce kunga
wancan madubin tsafin dana ajiye a tsakiyar
274

TASKARNOVELS.COM.NG
fada? Shine alkalin wannan gasa da xaku tafi,
duk abinda zai faru a cikin wannan tafiya zamu
gani a cikin wancan madubin saboda akwai
dokoki da zamu shimfida maku a yayin wannan
tafiya. Duk wanda ya karya doka daya daga cikin
dokokin koda ya dauko takobin Saiful Lujara to
ba zai auri Gimbiya ba, doka ta farko ita ce;
Babu yaki a tsakaninku, wato ba a yarda
dayanku ya cutar da dan uwansa ba.
Doka ta biyu ba a yarda dayanku ya taimaki
abokin tafiyarsa ba, abinda ake so shine kowa
karfin damtsensa dana sihirinsa ya cece shi.
Doka ta uku wacce ita ce ta karshe wanda duk
ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, to
kada ya tsaya ko ina face anan fadarmu. Da
fatan zaku kiyaye wannan dokoki domin
tabbatar da burinku, da wannan furuci nake
maku bankwana da fatan samun nasara ga
dukkan mai sa'a a cikinku.
Koda gama wannan jawabi sai sarkk yasa aka
kosassun dawakai kuma ingarmu guda biyu
baki da fari, kowanne da guzuri akansa, ya dubi
Hantaru da Rabbasu yace kowanne ya zabi
wanda yake so.
275

TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin hanzari Rabbasu ya tashi tsaye yaje ya
kama bakin dokin ya haye, shi kuwa Hantaru sai
ya kama farin dokin ya haye.
Nan take suka jera suna tafiya tamkar abokai
suka nufi hanyar fita gari, jama'a na biye da su
duu... Kamar kiyasai. Sai da aka raka su Hantaru
har izuwa iyakar gari sannan aka tsaitsaya ana
kallonsu suka kutsa kai cikin daji. Tun ana
kallonsu har sai da suka kule suka bace bat!
Hantaru da Rabbasu suka cigaba da tafiyya a
jere suna ketawa ta cikin kwazazzabai da
duwatsu, sai da suka yi tafiyyar sa'a shida cur
dayansu bai ce d dan uwansa kala ba, sannan
suka iso bakin wata
End Ads