irinsu ba abunda
yafara fadowa hantaru a rai shine batun gasar
nan na gudun kamo barewa nanfa ya shiga
tunanin al'amarin a cikin zuciyar sa.
Lokacin da hantaru yake ta wannan tunani itako
shamilat farin ciki ne ya lullube ta sabona
tsintar kanta a cikin mahaifarta in banda
murmushi da kalle-kalle babu abunda shamilat
181
TASKARNOVELS.COM.NG
takeyi hakadai suka cigaba da tafiya bisa
dawakan su rakuman su na gaba, kwatsam sai
daya daga cikin rakuman su hantaru yaje yana
shinshina wata katuwar randa dake cike da
ruwa yana kokarin ture marfin ta, dama
rakuman na fama da kishirwa sunfi kwana
talatin rabon su da shan ruwa domin sun dade a
cikin sahara suna tafiya, ruwan dasu hantaru
sukayi guzuri bashida yawa, a garin ture marfin
randar ne rakumin ya bangaje randar gabadaya
ta fashe karar fashewar randar ce tasa mai
randar ya fito a fusace daga cikin rumfarsa
rikeda takobi, koda yaga rakumin daya masa
wannan barna sai yayi kansa zai sare shi cikin
zafin nama hantaru ya zare takobin sa ya daka
tsalle daga kan dokinsa ya dirka a gaban mai
randar ya tare wannan sara takubban su suka
hadu suka fitar da kara gami da tartsatsin wuta,
nan fa aka tsaya ana kalon kallo tsakanin
hantaru damai randar a iya rayuwar hantaru bai
taba ganin saurayi mai tsawo da kauri da
murdewar jiki kamar wannan saurayi ba,
sannan yanada matukar kwarjini koda sauran
jama'ar dake cikin kasuwa sukaga abinda ke
shirin faruwa sai hankalin su ya dugunzuma
kowa ya baro wajen sana'ar sa aka rugo inda su
182
TASKARNOVELS.COM.NG
hantaru ke tsaye aka tsaitsaya ana kallo cikin
tsananin fushi wannan saurayi ya dubi hantaru
yace shin kazabi karasa rayuwar kane akan na
rakumin ka hantaru yayi murmushi yace inason
rayuwa ta, kuma inason rayuwar rakumi na
idan saboda akan randar ka kakeso kadauki ran
rakumi na toh gaskiya ka fadi kudin randar ka
ko nawane zan biya kodajin haka sai saurayin
yadakawa hantaru tsawa yace kai bako waye
Kaine harda zaka nuna min gadara a cikin birnin
mu lallai yau zakasan cewa ka tabo zaki uban
dawa kuma dodon maza dakai da rakumin
nakan duk yanzun nan takobi na zata sha jinin
ku, kafun hantaru yace wani abu sai saurayin ya
daga takobin sa cikin zafin nama ya kaiwa
hantaru wawan sara a ciki da nufin ya tsarga shi
biyu hantaru ya jada baya takobin ta sari iska
nanfa suka kacame da azababben yaki,
al'amarin dayayi matukar firgita shamilat kenan
ta fara kuka tana rokon jama'ah dasu raba
wannan fada amma babu wanda ya saurare ta
face gudu da jama'ah suka ringayi domin wuri
ya hautsine tsautsayi na neman afkawa kan
kowa.
Koda ganin haka sai Shamilat ta zaburi dokinta
ta nufi gidan mahaifinta sarkin makera Shuraim
183
TASKARNOVELS.COM.NG
ibn Alkasim domin tq sanar da shi abinda ke
faruwa.
Wohoho! Jarumtaka ta hadu da jarumtaka dole
ne fafatawar ta zama abar tsoro, nan take
Hantaru da saurayi suka hargitsa kowa da
komai dake cikin kasuwar, suka rinka rushe
rumfunan suna dagargaza dukiyar jama'a, nan
fa jama''a suka dinga guje-guje da iface-iface,
kafin a juma labari ya cika gari, Hantaru da
wannan saurayi suka rinka kaiwa junansu sara
da suka cikin tsananin zafin nama juriya da
bajinta ba kakkautawa, sai da suka shafe kusan
rabin sa'a amman dayansu bai samu nasarar
koda kwarzanar jikin dan uwansa ba, har
takubbansu suka dakushe. Al'amarin daya
fusatasu kenan suka zubar da makamansu suka
sake ruguntsumewa da azabben gumurzu da
bugun juna da hannu da kafa, nan take kuwa
kowa ya hada wa kowa jini da majina.
A daidai lokacin ne Shamilat da mahaifinta
Shuraim tare da wasu jama'arsu suka iso wajen
a guje bisa dawakansu, aikuwa sai ga wata
jama'ar da ban bisa dawakai a sukwane, ba
kowa bane yake jagorantar su ba face sarkin
mafarauta na birnin wanda ake kira zaharu ibn
184
TASKARNOVELS.COM.NG
Dauwal, nan fa rundunonin nan suka ja tunga
suna masu fuskantar junansu ga dukkanin
alamu so suke su yaki junansu, abinda ya
hanasu shine kallon fafatawar da su Hantaru ke
yi.
Zaharu ibn Dauwar shine mahaifin wannan
saurayi dake fafatawa da Hantaru, kuma
tsakaninsa da Shuraim gaba ce mai tsanani tun
iyaye da kakanni, kuma ba komai bane ya
haddasa wannan gaba ba face wannan gasa da
ake gudanarwa duk karshen shekara ta tseren
gudun kamo barewa, domin auren budurwar da
babu kamarta a birnin, duk shekara idan aka yi
gasar zuri'ar mafarauta ce take cinye gasar,
zuri'ar makera basu taba cinye gasar ba, saboda
an fisu zakwakurarun jarumai masu
sadaukartaka.
Shuraim n da wani da guda daya mai suna
Hurais, a duk fadin birnin babu kyakkyawan
saurayi kamarsa, kuma ya kasance mai matukar
kwarjini a cikin al'umma, Hurais kanin Shamilat
ne, dan Lokacin da aka yi mata aure bai wuce
shekaru bakwai ba.
185
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Hurais ya girma ya zama saurayi sai
soyayya mai zafi ta kulli tsakaninsa da wata
kyakkyawar budurwa mai suna Marilat, wacce
ta kasance kanwa ga wannan saurayi da ke yaki
da Hantaru.
Shi dai wannan saurayi ana kiransa da suna
Rabbasu, ma'anar sunan shine mai karfin zaki.
Bayan soyayya ta yi karfi tsakanin Hurais da
Marilat sai iyayensu suka farga, nan fa iyayen
kowanne daga cikinsu suka taka masu burki,
aka hanasu ganin juna domin babu yadda za'a yi
a bari suyi aure tunda akwai gabar asali a
tsakanin dangin nasu.
A asirce Hurais da Marilat ke haduwa a daji
suna tattauna yadda zasu bullo wa wannan
al'amari kan soyayyarsu, a karshe dai sai suka
yanke shawarar cikin dare su sulale su gudu
zuwa wani garin suyi aurensu. Aikuwa cikin
tsakiyar dare suka sullae suka bar garin, koda
gari ya waye sai aka nemi Hurais da Marilat aka
rasa, nan fa rigima mai karfi ta kacame tsakanin
dangin mafarauta da kuma dangin makera har
ta kaisu ga yakar juna, wanda sai da takai cewa
anyi asarar daruruwan rayuka, da kyar sarkin
garin ya raba wannan rigima.
186
TASKARNOVELS.COM.NG
A karon banza aka kamo Hurais da Marilat acan
wani kauye waishi Gabril, a lokacin da suke daf
da daura wa kansu aure.
Daga wannan rana Hurais da Marilat basu sake
ganin juna ba, a dalilin aka ne duk su biyun suka
shiga mugun hali suka kwanta cuta, a karshe dai
ciwo yakai ciwo rai yayi halinsa duk su biyun
suka mutu a kuma rana guda. Marilat ce ta fara
mutuwa, aikuwa Hurais na samun labarin
mutuwarta sai shima ya hadiyi zuciya ya mutu.
Bakin ciki a wurin dangin makera dana
mafarauta ba sai an fada ba domin sai da
kowannne bangare suka shafe kwanaki talatin
suna kuka da bakin ciki na wannan abu daya
afku, wannan shine sanadin daya kara zafafa
kiyayya da gaba a tsakanin dangin guda biyu.
Lokacin da rundunar biyun ta tsaya ana kallon
ffaatawar da akeyi tsakanin Hantaru da
Rabbasu sai kowa ya cika da tsananin mamaki,
domin ba'a taba ganin jarumin da yayi gaba da
gaba da Rabbasu ba har ya iya yakatsa ba sai
yau, saboda tsananin jarumtakarsa da iya
yakinsa.
187
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda yake shi kansa Hantaru ya raina
jarumtakarsa domin bai taba haduwa da jarumi
bil'adama kamar Rabbasu ba, kai ko yakinsa da
mijin uwar mayu bai bashi tsoro ba kamar
wannan gumurzu da yake yi da Rabbasu, domin
ya tabbatar da cewa indai aka kara sa'a guda
nan gaba sai dai cikin biyi ayi daya, kodai suyi
ragas ko kuma daya ya kashe daya.
Babban abinda ya tayar wa da Rabbasu hankali
shine aduk sa'ar da ya sari jikin Hantaru sai dai
yaji kara kal! Takobin nan bata tasiri a jikinsa
sai dai wajen daya sara din ya dan kunbura.
Shiko Hantaru abinda ya dugunzuma hankalinsa
shine ko sau daya ya kasa samun nasarar
yankar jikin Rabbasu.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka
hango wani mahayi bisa wani farin doki ya
durfafo wajen, tun kafin ya karaso wata irin iska
mai karfi ta dinga tarwatsa mutane ba shiri aka
buda masa hanya domin an gane kowane ne. Da
isowar mahayin wanda ke rike da wata farar
sanda sai yayi nuni da sandarsa izuwa ga
hantaru da kuma Rabbasu, nan take duk su biyu
188
TASKARNOVELS.COM.NG
suka zube kasa sumammu, wato suka yi
rabuwar dole ga barin yakar junansu.
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part N
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
A sannan ne mahayin dokin ya tsaida dokinsa ya
dubi rundunar su Zuhairu da kuma ta su
Shuraim yace kowa ya dauki nasa ku tafi gida,
na raba wannan rigima a yanzu amman fa bata
kare ba, domin za'a yi babbar fafatawa ta karshe
nan gaba tsakanin Rabbasu da wannan bakon
jarumi a ranar gasar tseren gudu, ta neman
auren Gimbiya Larziyya, to nan ne za a yi
wannan fafatawar ta karshe.
Ko da gama fadin hakan sai mahayin yayi
girgiza ya bace bat! Shi da dokinsa, b wani bane
189
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan mahayin sai kakan Shamilat wato boka
Sulbaini ibn Hukaish. Bacewar boka Sulbaini ke
da wuya sai ko wanne bangare suka dauke nasu,
wato su Shuraim suka dauki Hantaru suka tafi,
su kuma Zuhairu suka dauki Rabbasu suka tafi
da shi.
Lokacin da hantaru ya farfado yana bude
idanunsa sai ya tsinci kansa bisa cinyar Shamilat
ta zuba mashi idanu tana zubar da hawaye, a
gefe daya kuma sai yaga wani dattijo dogo siriri
kuma kyakkya a tsaye a kusa da shi kuma wata
dattijuwar mace ce sun kura masa idanu suna
murmushi gami da zubar da hawaye.
Hantaru ya dubi ko wacce kusurwa yaga a cikin
wani kyakkyawan daki yake, cikin matukar
mamaki ya mike zaune zumbur! Ya dubi
Shamilat ya ce yaya aka yi nazo nan, sannan
wadannna mutanen su waye?
Koda jin wannan tambaya sai Shamilat ta share
hawayenta ta ce ya kai dana kayi sani cewa
kakana boka Sulbaini ibn Hukaish hine ya zo ya
raba yakin da kuke yi da wannan sadaukin
saurayin, nan dai Shamilat ta baiwa Hantaru
labarin Rabbasu da mahaifinsa Zuhairu da kuma
190
TASKARNOVELS.COM.NG
irin gabar dake tsakanin zuri'arsu da ta su
Rabbasu. A karshe ta shaida masa cewa boka
Sulbaini yayi bayanin cewa za a sake fafatawa
da Rabbasu ta hanyar tseren gudun kamo
barewa, bisa takarar neman auren Gimbiya
Larziyya.
Sa'adda da Shamilat ta zo nan a jawabinta sai
hantaru ya kuma cika da mamaki ya ce wace
kuma gimbiya Larziyya?
Kafin Shamilat ta bude bakinta ta bashi amsa sai
Shuraim ya riga da cewa ya kai jikana Hantaru
ka yi sani cewa ba wata bace Gimbiya Larziyya
face yar sarkin garin nan namu Uhairu ibn
Sabus, kuma a halin yanzu a gaba daya nahiyar
nan babu wata mace mai kyawunta, ya kai
jikana kayi sani cewa mahaifiyarka Shamilat ta
bamu labarin jarumtakarka data gani da
idanunta a yayin tafiyarku tsakanin birnin sarki
kusaidu zuwa nan. Hakika kayi gagarumar
bajinta irin wacce wani bai taba yi ba, domin
fiye da shekaru hamsin baya, babu mai iya
ratsawa ta wadannan dazuzzuka ya fita lafiya
face ayarin dakaru masu yawa kuma masu
karfin sihiri, amman kai gashi kai baka da
sihirin komai face na kariya irin wanda muka
191
TASKARNOVELS.COM.NG
shayar da mahaifiyarka tun tana karama, shi
wannan kariyar kawai kake da shi.
Haka dai aka cigaba da fira tsakanin Shuraim da
Hantaru suna cikin tsananin farin ciki, daga
karshe sai Hantaru ya dubi Shuraim ya ce ya kai
kakana yanzu ya ya za a yi naga gimbiya
Larziyya?
Shuraim yayi murmushi yace wai shin me kake
ci ne na baka na zuba? Ka kwantar da
hankalinka zaka ga gimbiya Larziyya da
idanunka amman sai bayan mun dawo daga
gidan mahaifina boka Sulbaini, domin yace da ni
lallai mu kaika gidan shi gobe da safe.
Koda jin haka sai murna ta kama Shamilat dan
dama bata da burin daya wuce ta sadu da boka
Sulbaini, ba tre da bata lokaci ba Shuraim da
matarsa Shaulat suka shiga hidimar shirya
walima ta musamman dan murnar dawowar
Shamilat da jikansu Hantaru. Nan take aka
yanka rakumi da raguna guda uku, Sannan
Shuraim ya aika wasu kuyanginsa kasuwa, suka
je suka yi cefane. Nan fa aka shiga dafe dafe da
soye-soye, daman tuni an aika da sakon gayyata
192
TASKARNOVELS.COM.NG
ga yan uwa da abokan arziki da kuma
makwabta.
Tun kafin a gama shirye-shiryen jama'a suka
fara hallara a gidan Shuraim, nan da nan kuwa
gidan ya cika da jama'a, wasu abokan ma na
Shuraim rabonsu da zuwa gidan an fi shekara
goma, sai da kowa ya zauna a inda aka tanada
sai kuyangi suka fara fito da abinci da na sha
aka fara walimar, bangaren maza da ban haka
na mata da ban.
Sai da aka fara walimar annan Shamilat, Shaulat,
Shuraim da Hantaru suka fito daga cikin daki
suka fara gaisawa da jama'a, Shuraim na
gabatar da Shamilat da danta Hantaru ga
wadanda basu sansu ba, kuma suma bakin ana
gabatar d su ga su Hantaru, ana gaggaisawa.
Ana cikin wannan gaggaisawar ne sai Hantaru
ya hango wata mace can tsaye, wacce ta rufe
fuskarta da mayafi, idanunta kadai ke iya gani,
ita dai wannan macen ita kadai ce, bata ci kuma
bata shan komai, kuma ya lura da ita cewa
Shuraim take satar kallo. Yayi tunani a zuciyarsa
ya ce to shin wace ce wannan? Kuma me ya
193
TASKARNOVELS.COM.NG
kawota wannan taro, tunda bata damu da komai
ba na walima? Hantaru ya tambayi kansa.
Bayan gama gaisheshe ne sai Hantaru ya saki
wuri shima ya zauna ya fara cin abincin, a
lokacin ne sai gaba daya samarin dake wajen
suk zo suka lullubeshi suna masu yi masa jinjina
bisa gagarumar bajintar da yayi ayau, na
fafatawa yaki da Rabbasu.
Al'amarin da ya baiwa Hantaru mamaki kenan
ya ce wai shin shi wannan Rabbasu har shayinsa
ake yi a garin nan?
Wani saurayi mai suna Kumais ya ce ai a tarihin
jarumtakar Rabbasu a nan grin ba a taba samun
gwarzon daya taba tararshi ba, balle har su
fafata yaki ba sai kai kadai, kai a takaicema
gabadaya nahiyar nan babu kamarsa a
sadaukantaka, sannan kuma bashi da imani ko
kadan shiyasa kowa ke shakkarsa, babu mutum
daya isa ya fada masa magana yaji face boka
Sulbaini, shima dan babu yadda zai yi d shi ne,
domin kura ta san gidan mai babbar sanda.
Hantaru ya jinjina kai sannan ya ce wai shin
Rabbasu yana shiga gasar gudun tseren barew
da ake yi duk shekara ne kuwa?
194
TASKARNOVELS.COM.NG
Kumais yabce ai Rabbasu bai taba shiga gasar
ba, saboda baya son ya auri kowacce budurwa
face gimbiya Larziyya. Ita kuwa Larziyya
mahaifinta sarki yace ba zai aurar da ita ba, sai
bayan shekarar da za'a yi gasa ta arba'in sannan
zai aurar da ita.
Wannan shekara da muke ciki itace shekara ta
arba'in din, a yanzu haka saura kwanaki ashirin
aidai ayi wannan gasa. A daidai wannan lokacin
ne su Hantaru suka ga wannan macen mai satar
kallonsu ta baro inda take tsaye ta durfafo inda
suke tsaye. Koda ta zo daf da Hantaru sai ta
mika masa wata takarda. Hantaru na karbar
takardar sai kawai budurwar ta juya da sauri ta
fice daga cikin gidan.
Hantaru ya mike d sauri da nufin yabi bayanta,
amman sai Kumais ya rikota yace da shi kafa ka
bita, kuma kada ka duba takardar sai bayan ka
kadaita a cikin dakinka kai kadai, cikin mamaki
Hantaru ya dubi Kumais ya ce shi shin kasan
wannan matar data kawo mani wannan
takardar ne?
195
TASKARNOVELS.COM.NG
Kumais yace eh nasan kowace ce, amman bazan
fada maka ba, domin nasan ba zatayi bayanin
kanta ba a cikin takardar fata baka.
Koda jin haka sai Hantaru yayi shiru bai sake
cewa komai ba, kuma ya sanya wannan ta karfa
a cikin minti goma, kuma ya saki jikinsa aka
cigaba da walima kamar babu abinda ya faru.
Ita dai wannan walima tunda hantsi aka farata
amman sai bayan magrib sannan kowa ya watse
suka tafi suna son barka.
Hantaru na zaune shi kadai a harabar gidan
bayan kowa ya tafi aka barshi shi kadai a zaune
yana tunani, ba tunanin komai yake ba face irin
rayuwar daya baro acan birnin Kisra da kuma
irin wacce ya tarar a birnin darul Habur, abinda
Hantaru ya fara ayyanawa a ransa shine ina ma
ace ba sarki Usaidu bane mahaifinsa, gwara ace
mahaufina dan usulun wannan birni ne na darul
Habur, domin rayuwata ta fi dacewa anan, da
tuntuni na share hawayen kakannina na
takaicin rasjin cin gasar d suke yi. Amman dai
tunda yanzu na zo nan to komai ya zo karshe, ta
kowanne hali a wannan shekarar nine zan zama
zakaran wannan gasa.
196
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Hantaru ya gama ayyana haka a
cikin zuciyarsa, sai yaji alamun ya soma jin bacci
dan haka sai ya mike tsaye ya shiga cikin
dakinsa, har Hantaru ya kwanta akan shimfida
dmin yayi bacci sau ya tuno da batun wasikar
nan da mace mai rufaffiyar fuska ta bashi.
Hantaru ya mike zumbur ya zaro wasikar daga
cikin aljihun rigarsa ya warwareta sannan ya
fara karatu kamar haka:
Takarda daga Gimbiya Larziyya zuwa ga bakon
jarumi mai ban mamaki, ya kai taurarn shekara
kayi sani cewa nayi matukar farin ciki da
zuwanka wannan birni, kuma dama can na dade
ina sauraron wannan rana ta zuwanka. Hakika
wannan rana ta fiye mani komai a duniyar nan,
ba komai bane yasa nake farin cikk da zukanka
ba, face sanin cewa kai kadaine zaka iya yaye
bakin cikin da ya addabi zuciyata tsawon
shekara da shekaru.
Ina mai tabbatar maka da cewa Sadauki
Rabbasu ya dade yana sona, tun muna yara
kanana, amman daidai da dakika ban taba jin
ina kaunarsa ba, a kaidar wannan birni namu
babu wanda zai auri wata mace kyakkyawa dole
sai ya shiga gasar gudun barewa. Tunda sadauki
197
TASKARNOVELS.COM.NG
Rabbasu ya zama saurayi bai taba shiga wannan
gasa ba domin a kaina kadai yayi tanadinta,
wato ya kudurce a ransa cewa ba zai shiga gasar
ba sai idan akaina ake yinta.
Tabbas bokaye da masu hasashe sun tabbatar
da cewa duk sa'adda gasar aurena ta zo, indai
Rabbasu ya shiga gasar babu wanda zai samu
nasara akansa. Ni kam dadai na auri Rabbasu
gwara ace na rasa rayuwata ma gaba daya.
Ya kai Gwarzon jarumi ina mai rokonka saboda
mahaifiyarka Shamilat da kuma kakanka sarkin
makera Shuraim da ka taimakeni ka ceci
rayuwata ka shiga wannan gasa, koda kuwa ba
zaka samu damar aurena ba, ni dai babban
burina shine ace Rabbasu ya rasani, idan har ka
amince zaka yi mani wannan taimako, to mu
hadu a dutsen kufainu dake can bayan gari a
gobe da yammaci daidai lokacin faduwar rana
domin naji amsata a bakinka, daga karshe ina
mai kira a gareka daka rungumi kaddara bisa
wani mummunan labari da zaka ji daga bakin
kakan mahaifiyarka wato boka Sulbaini, domin
labari ne mara dadi kuma zai yi matukar jefaka
a cikin bakin ciki da damuwa.
198
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Hantaru yazo daidai nan a karatun
wsikarsa sai hankalinsa ya dugunzuma ya shiga
sabon tunani, har ya zamana cewar dare ya raba
amman ya kasa bacci, abinda ke wa Hantaru
zarya a cikin zuciyarsa shine wai shin wane irin
mummunan labarine boka Sulbaini zai labarta
masa wanda zai kefashi cikin bakin ciki.
Abu na biyu kuma shine, ta yaya zai samu
nasarar lashe gasar tseren kamo barewa na
karshen shekara domin kubutar da rayuwar
Gimbiya Larziyya. Haka dai Hantaru ya cigaba
da wannan tunani a cikin zuciyarsa, bai gushe
ba yana tunani har alfijir ya keto bai anakara ba.
Bayan anyi kalacin safe kowa ya gama kimtsawa
sai Salimat, Shuraim da Hantaru suka yi hawa
suka tafi izuwa gidan boka Sulbaini, da yake
akwai yar tazara tsakanin gidan Shuraim da
gidan Boka Sulbaini basu isa can dinba har sai
da hantsi ta yi. Gidan boka Sulbaini a bayan gari
yake a saman wani katon dutse wanda ana iya
hangoshi daga kowanne sashi, wato bangaren
gabas da yamma, da kuma kudu da arewa. Daga
nesa mutum zai iya hangoshi dan mitsitsi
amman da zarar ya gabato sai ya fuskanci cewar
yana da girma ainun.
199
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da su Shuraim suka iso bakin kofar
gidan boka Sulbaini sai suka sauka daga kan
dawakansu suka dauresu a jikin bishiyoyi,
sannan suka haye saman dutsen suka durfafi
gidan boka Sulbaini. Shuraim ne akan gaba
sannan Shamilat sai kuma Hantaru, da isarsu
kofar gidan wanda hantaru ya kura wa idanu
yana mashi kallon mamaki saboda ganin yadda
aka gina shi da zallar dutse na murjani, sai
Shuraim ya kunna kai, Shamilat ta bishi a baya.
Koda Hantaru ya mika kafarsa zai sa a cikin
gidan, sai yaji a daka masa tsawa wacce tasa
tsigar jikinsa mikewa, bai san sa'adda ya janye
kafar tasa ba kuma ya koma da baya, Shuraim
da Shamilat ma sai suka razana suka koma da
baya, kawai sai sukaga kofar gidan ta rufe da
kanta. A sannan ne kuma boka Sulbaini ya
bayyana tsulum a gabansu kamar walkiya,
idanunsa cike da kwalla ya kurawa Hantaru
idanu.
Al'amarin daya