x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - MAZAN JIYA 1

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 212

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
lokaci guda aka zuba tseren gudu.
Wohoho! Idan da ace mutum yana nan yaga
yadda dakarun nan suka rankaya da gudu kura
na binsu a baya sai yayi tunanin yakin duniya ne
za a yi.
Nan fa aka fara bugun jama'a da kulake, daman
tuni an saki wata barewa a sanda aka fara
gudun ta fice da gudu ta gaban dakarun nan,
haka ko wanne badakaren gasa ya ci buri sai ya
kamo wannan barewar.
Kaicon maza! Lokacin da aka fara bugegebiya a
tsakanin tawagar nan biyu, sai al'amura suka
zamo abin tsoro kuma abin tausayi, domin sai
dai aga an mako mutum.ya fado kasa, dawakai
sun tattakeshi yayi raga-raga, wani lokacin ma
har dawakan ake makewa su fadi kasa, wasu
zaratan jaruman masu naci da tsananin juriya
ko an maka masu kulki a kasa basa yarda su
fado kasa, sai dai kaga jini na tsartuwa a
fuskokinsu suma suna mayar da martanin duka.
Al'amarin Sadauki Rabbasu da Hantaru kuwa,
tun daga lokacin da suka fara gidun ne suka
shiga bugun junansu, wato suna gudu suna gudu
239

TASKARNOVELS.COM.NG
suna bugun junansu da kulake ga kuma duka ta
ko ina, ta fuska, ta kai ta jiki, dukan da suke yi
wa junan nasu wawan duka ne, wanda babu mai
iya shanyeshi a gaba daya dakarun gasar, tunda
suka fara bugun junnasu babu wanda fatar
jikinsa ta tsage ko ta kwaile, sai dai kaji kara na
tashi kamar ana bugun bugun dawa da tabarya,
tim! Tim! Duk wanda aka zabga wa kulki sai dai
kaga ya girgije ya mayar da martani.
Kafin a samu tsawon dakika dari uku da sittin
da fara wannan tsere an zubar da fiye da rabin
dakarun a kasa, wasu sun kakkarya wuya sun
mutu, wasu kuma sun kakkarye a gabban
jikinsu, wasu kuma jikinsu yayi fatafata ba kyan
gani, ga dukkanin alamu ba zasu yi rai ba.
Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda
mutane ke ragargajewa cikin wannan gasa dole
ne zuciyarsa ta raunana. Sannu a hankali
dakarun gasa suka rinka zubewa kasa har ya
zamana cewa saura bai fi su dari uku ba, daga
cikin su dubu uku.
A wannan lokacin ne dokin Hantaru dana
Rabbasu suka baiwa sauran dakarun rtaa mai

240

TASKARNOVELS.COM.NG
yawan gaske, har ya zamana cewa suna iya
hango barewar da akeso su cimmawa.
Nan fa suka kara karfin gudu kum suka cigaba
da kaiwa junansu cikin tsananin karfin hali da
jarumta fiye da farko, aiko nantake kalaken
naku suka kakkarye saboda tsabar bugun juna
da suke yi, duk fuskokinsu sun kumbura, haka
jikinsu ma duk ya kumbura, idanunsu ta
kumbura hatta fatar idanunsu neman rufe idon
take yi saboda itama ta kumbura abun ba kyan
gani.
Lokacin da Hantaru da Rabbasu sukaga
kulakensu sun kakkarye sai suka ci gaba da
naushin juna da hannu, a duk lokacin da
Rabbasu ya naushi Hantaru a fuska sai yaga
taurarin wuya, idan tsananin zafi da zugi ya
shigeshi ya dimauce sai kaga yana layi kamar
zai fado daga kan dokinsa, amman sai kaga ya
makalkale dokinnasa shima ya takarkare ya
ganza wa Rabbasu wawan naushi a fuska,
saboda kasancewar Rabbasu ya fi Hantaru
tsananin karfin damtse da juriya, ko Hantaru ya
naushe shi baya yin layi sai dai ya shanye naushi
kuma ya mayar da martani sau uku a jere kuma
a lokaci guda.
241

TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin cikar dakiki dari uku Rabbasu yayi lagalaga da Hantaru, amman saboda tsananin naci
da juriya Hantaru yaki yarda ya fado kasa, shi
kuwa Rabbasu yayi mtukar mamaki yadda aka
yi Hantaru bai fado kasa ba, duk d cewa ya
galabaita ainun har ma kamar numfashinsa
yana neman daukewa.
Adaidai wannan lokacin ne gaba daya sauran
dakarun suka ci kasa suda dawakan nasu, ya
rage saura dokin Hantaru da na Rabbasu kadai
dauke da mahayansu sunata tsala gudu.
Mahayan na cigaba da gumurzu ga barewa a
gabansu sun kusa cimmata. Duk wannan abu
dake faruwa akwai wasu zaratan alkalan gasa su
hudu suna bin dakarun gasa a baya cikin
tsananin gudu, su dai wadannan alkalai dama
can kwararrun mahaya dawakai ne wadanda
babu kamarsu a gasar tseren doki a birnin kaf,
kuma aminttatun sarki ne, suna aiki ne ba tare
da son wani bangare ba daga cikin zuri'ar guda
biyu.
Lokacin da Sadauki Rabbasu ya waiga baya yaga
gaba daya dakarun gasar sun zube saura su biyu
tak, wato daga shi sai Hantaru. Sai ya harzuka ya
kara kaimi wajen naushin Hantaru. Da dai yaga
242

TASKARNOVELS.COM.NG
ya kasa kada Hantaru sai ya dage ya zabga wa
dokinsa naushi a ciki, take dokin ya sulale ya
fadi kasa tare da Hantaru.
Dokin nan ku shurawa bai yi ba haka ya zama
gawa, a wannan lokacin tuni Rabbasu ya fara
kyalkkyala dariyar farin ciki, yana ganin cewa
lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya kai
Hantaru kasa, kuma tsakaninsa da barewar nan
bai wuce kamu biyar ba.
Ba zato ba tsammani sai kawai sadauki Rabbasu
ya ji ana binsa a baya Daf! Daf! Ko da ya waiga
baya sai yaga ashe hantaru ne ya biyoshi cikin
wani irin azabben gudu na gaban kwatance,
wanda ko dokin ma sai haka, har saura kiris ma
ya riske shi.
Cikin tsananin fushi da mugun nufi Rabbasu ya
shiga kaiwa Hantaru duka ta bayan da mugun
nufi, amman sai Hantaru ya rinka sunkuyawa
yana kauce wa dukan, cikin matukar zafin nama
Hantaru ya daka tsalle ya haye saman dokin
Rabbasu ya rukunkumoshi ta baya suka fado
daga kan dokin tare, kafin Rabbasu ya mike
saboda tsananin nauyinsa ya ninka na Hantaru,
tuni Hantaru ya mike ya gabza wa dokin
243

TASKARNOVELS.COM.NG
Rabbasu naushi a fuska, nan take idon dokin ya
fashe ya sulale kasa matacce.
Nan fa hantaru da Rabbasu suka kasa tsere
kowannensu na kokarin ya kamo wannan
barewa, har a sannan alkalan gasa na biye da su
kuma duk sunga abinda ya faru, bisa ga mamaki
sai gudun Hantaru dana Rabbasu ya zo daya, ya
zamana cewa suna hada kafada da juna an kuma
rasa wanda zai wuce wani, kuma a hakan ne
suka ci gaba d naushin juna amman a haka
kowannensu ya ki yarda ya kai kasa.
Yayin daya rage taku biyu kacal tsakanin su
Hantaru da wannan barewa, sai suka daga tsalle
sama a lokaci guda suka kai wa wannan
barewar cafka, bisa rashin sa'a sai Rabbasu ya
kamo kan barewar, shi kuma hantaru sai ya
kama kafafunta, koda Rabbasu ya ja shima
Hantaru ya ja sai barewar ta rabe gida biyu, a
dai-dai wannan lokacin ne alkalan gasar suka
karaso gabansu a guje bisa dawakai suka yi
turjiya. Cikin zafin nama alkalan uka sakko daga
kan dawakansu, mutum biyu suka rike Rabbasu,
sauran biyun suka rike Hantaru kowannensu
yana rike da rabin barewa a hannunsa.

244

TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokacin ne shima sarki da fadawansa
suka iso wajen, sannan sai ga sauran jama'a yan
kallo suma suna karasowa wajen.
Sarki ya dubi alkalan gasar ya ce tsakanin
Hantaru da Rabbasu yace wane ya fara kama
wannan barewa da ta rabe biyu a hannunsu.
Cikin hadin baki alkalan gasar suka ce a tare
kuma lokaci guda suka kama barewar.
Koda jin haka sai wuri ya yamutse da shewa
murane suka hau fadin anyi ragas, anyi ragas...
Nan fa dajin ya rude da hayaniya, sai da aka
busa kaho sannan aka yi tsit tamkar mutuwa ta
gifta, sarki ya dubi sauran jama'a ya ce
sakamakon wannan gasa shine anyi ragas
tsakanin Sadauki Rabbasu mai wakiltar zuri'ar
mafarauta da Sadauki Hantaru mai wakiltar
zuri'ar makera, saboda haka za a sake yin
wannan gasa a shekara mai zuwa.
Da jin haka sai jama'a suka barke da shewa gami
da murna.
Al'amarin Sadauki Rabbasu da zuri'arsa kuwa
sai suka cika da tsananin bakin cika, Rabbasu
245

TASKARNOVELS.COM.NG
bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba
saboda tsananin takaici ya durkushe kasa ya
kafa kansa a kasa.
Shi kuwa Hantaru dama yasan cewa babu
wanda zai samu nasara a wannan gasa tsakanin
shi da Rabbasu, domin boka Sulbaini ya fada
masa cewa sai sunyi wannan gasa sau uku babu
mai nasara, wanda a karshe dole ne a tura su
neman takobin Saiful Lujara dan kawo karshen
gasar gabadaya a birnin na Darul Habur.
Nan take Hantaru ya yanke jiki ya fadi kasa
saboda tsananin galabaita, cikin gaggawa aka zo
aka dauek shi aka sanya shi cikin kekn doki aka
tafi da shi, saboda kumburin jiki da duruwar jini
sai da aka kwana uku ana jinyar Hantaru sai a
sannan jinin daya taru a fuskarsa da kuma
jikinsa ya bace.
Salimat ce tayita gasa masa jiki da ruwan dumi,
kuma tana dafa masa magani yana sha, kafin
jikin Hantaru ya dawo daidai a kullum idan ta
dubw shi sai ta fashe da kuka saboda ganin irin
tsananin wahalar da ya sha, hakan ne ma yasa ta
tubure akan ba zata yarda a sake yin wannan
gasa da Hantaru ba, sai dai su tattara yanasu-ya
246

TASKARNOVELS.COM.NG
nasu su koma can birnin Kisra gidan mijinta. Da
kyar d sidin goshi su Shuraim suka lallabata ta
yard zata sake zama a garin har shekara ta
zagayo.
Wannan shine abinda ya faru a can birnin Darul
Habur bayan anyi gasar tseren gudun barewa ta
neman aure da aka saba yi duk shekara.

MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part R
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

*******

Acan birnin Kisra kuwa tun daga ranar da
Shamilat da Hantaru suka bar gari sai sarki
kusaidu ya shiga cikin wani mugun hali da bakin
247

TASKARNOVELS.COM.NG
ciki, sannan yana yawan kuka bisa yawan begen
yarima Hantaru da yake yi, abu kamar wasa sai
sarki kusaidu ya kwanta ciwo kuma aka rasa
abinda ke damunsa, domin sam bai fada wa
kowa abinda ke damunsa ba.
Lokacin da ya fahimci cewa idn ya kara jimawa
a wannan hali to tabbas rayuwarsa zata
salwanta, sai ya kira wadansu amintattun
bayinsa su uku ya basu wasika yace suyi shiri su
tafi can birnin darul Habur su kai wa matarshi
wannan wasika.
Nan da nan kuwa suk yi shiri suka kama hanya a
sirrance ba tare da kowa ya sani ba, dalilin da
yasa sarki Kusaidu bai yi shawara da boka
Ardusa ba wannan karon shine yaga wani abu
da yayi matukar daure masa kai, har yaji cewar
ba zai kara yarda da shi ba har sai ya tabbatar
da abinda yake zargi.
Masu iya magana sunce shi laifi kuikuyo ne har
abada yana bin mai shi, duk abinda mutum ke yi
a boye komai daren dadewa sai asirinsa ya tonu,
musamman abinda ya shafi cin amana da danne
hakkin wani.

248

TASKARNOVELS.COM.NG
Wata rana da tsakar dare sarki kusaidu na
kwance a dakin uwar gidansa suna bacci, sai
kawai wani dan mitsitsin tsuntsu ya shigo
turakar ya tsaya a saman taga daidai saitin
Zarifa yayi wani irin kuka tamkar yana raira
waka. Koda jin wannan tsutsun sai Zarifa ta
farka daga baccin da take yi kamar dama can
idonta biyu ba baccin take yi ba, da mikewarta
zaune sai ta dubi sarki Kusaidu ta tabbatar dda
cewa bacci yake tunda gashi har yana sharar
munshari, a hankali cikin sanda ta sakko daga
saman gadon ta cire rigar baccin dake jikinta
sannan ta saka tufafinta masu kyau ta nufi bakin
kofa.
Ashe sarki Kusaidu ba bacci yake ba, domin tun
daga ranar da su Hantaru suka tafi birnin Darul
Habur bai sake samun damar yin bacci daddare
ba, sai dai kawai ya kwanta yayi lamo kamar
mai yin baccin amman ba baccin yake iya wa ba,
zuciyarsa cike da tunanin gami da begen dansa
yarima Hantaru da kuma matarsa Salimat. Duk
motsin da Zarifa ta ke yi yana jinta, kuma wani
lokaci har bude idonsa yake yi kadan ya kalleta,
da zarar yaga ta juyo sai yayi maza ya rufe idon
nasa.
249

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Zarifa ta isa bakin kofar turakar, sai
ta tsaya cak, ta juyo ta kura wa fuskar sarki
Kusaidu idanu ta sake tabbatar da cewa bacci
yake yi, sai da ta bata dakika sama da dari shida
a kofr sannan daga bisani ta bude kofar a
hankali ta fice daga cikin turakar gabadaya.
A lokacin ne shima wannan mitsitsin tsuntsun
da ya shigo wannan turakar ya fice da sauri,
koda jin ficewar tsuntsun sai sarki kusaidu ya
leka waje ta cikin taga, duk da cewa dare ne gari
yayi duhu amman duk da haka sarki kusaidu ya
samu damar hango wannan mitsitsin tsuntsun
ta cikin ragowar hasken farin wata, lokacin da
mitsitsin tsuntsun ya rikide ya zama wani aljani,
bisa ga mamakinsa kuma sai yaga matarsa
Zarifa ta haye bayan aljanin ya bude fuka
fukansa ya tashi da ita sama, kafin kifta ido sun
kule a sararin samaniya sun bace bat!
Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu
ya cika da tsananin mamaki, kuma hankalinsa
ya dugunzuma ainun ya tambayi kansa a cikin
zuciyarsa ya ce ina matata Zarifa ta tafi a cikin
wannan dare, sannan wane ne ya turo wannan
aljanin daya dauketa? Sarki Kusaidu ya kasa
baiwa kansa amsar wadannan tambayoyi dan
250

TASKARNOVELS.COM.NG
haka sai yayi shiru ya shiga sabon tunani, daga
can sai yayi ajiyar zuciya ce hakika duk yadda
aka yo matata Zarifa tana cin amanata ne,
alhalin ni ina zaune da ita da zuciya daya, kuma
ina kaunarta bilhakki, amman babu komai,
koma mene ne take aikatawa a boye da sannu
zan sani.
Haka dai sarki Kusaidu ya koma ya kwanta ya ci
gaba da tunanin su Hantaru da Salimat, bayan
kamar rabin sa'a da kwnaciyarsa sai yaji an
bude kofar an shigo, bai bude idanunsa ba,
kuma bai yi wani motsi ba sai kawai ya ci gaba
da kwarara munshari. A lokacin ne yaji an hawo
gadon an kwanta, kamshin turaren data saba
sakawa a jikinta ne ya sa ya gane matarsa ce
Zarifa ta dawo.
Nan take sarki Kusaidu yaji wani azabben bakin
ciki ya shigeshi tamkar ya hadiyi zuciya ya
mutu, amman sai ya danne zuciyar tasa ya
hakura.
Kashegari da safe sarki kusaidu bai nuna wa
Zarifa wata damuwa ba, sai ma ya tashi da farin
ciki yana mai cewa zarifa shi fa yau ya tashi da
sha'awar fita rangadi.
251

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai Zarifa ta yi caraf ta ce aiko
nima ina sha'awar fita rangadi sai mu fita tare
kenan?
Sarki Kusaidu ya dubeta cikin damuwa ya ce a'a
gwara dai kiyi zamanki a gida domin wannan
rangadin da zan fita ni kadai zan fita ba tare da
dakaru ba, kuma zan iya yin nisan zango, kinga
Kenan bani da tabbacin zan iya kare lafiyarki
idan kika biyo ni.
Cikin matukar mamaki Zarifa ta ce kai kuwa
saboda me zaka fita rangadi kao kadai, shin ka
mnta ne cewa kai sarki ne? Baka tsoron
magauta su kawo maka hari?
Sarki Kusaidu yayi dariya ya ce ai ni bana tsoron
harin magauta domin na tabbatar da cewa ina
tare da tsarin boka Ardusa, ke nake ji saboda
baki da tsari irin nawa.
Koda jin wannan batu sai Zarifa ta yi shiru bata
kara tankawa ba.
Ba tare da bata wani lokaci ba, sarki Kusaidu ayi
shiri shi kadai, cikin batar da kammani ya fice
daga cikin birnin Kisra. Sarki Kusaidu ya durfafi
wata hanya da zata sadashi da wani kauye da
252

TASKARNOVELS.COM.NG
ake kira da Raufal, daga cikin birnin Kisra zuwa
kauyen Raufal tafiya ce ta rabin sa'a kacal,
amman sai sarki ya zaburi dokinsa da sauri
domin yana son ya isa kauyen cikin kakanin
lokaci. Da isarsa kauyen kai tsaye ya wuce zuwa
wajen wani bakon boka wanda bai wuce kwana
uku da sauka a kauyen ana kiransa da suna
Hulubul Auzar.
Yau kwana biyu kenan rak da sarki Kusaidu ya
samu labarin saukar boka Hulubul auzar, kuma
ya samu labarin bokan ne a wajen wani
amintaccen yaronsa da yake masa fatauci mai
suna Ramzal.
Ramzal ya tabbatar wa da sarki kusaidu cewa
yaga bokan da ya fi boka Ardusa karfin sihiri,
domin a gabansa boka Hulubul auzar ya warkr
da wani mara lafiyya wanda ya shekara ashirin
a kwance sakamakon wani asiri da aka yi masa,
wanda yasa ya makance kuma ya kuturce, babu
irin kokarin da boka Ardusa bai yi ba akan yaga
cewa ya warkar da wannan mara lafiya amman
ya kasa, sai ga shi a dare daya boka Hulubul
auzar ya zo ya warkar da shi

253

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da sarki Kusaidu ya iso kofar gidan da
aka sauki boka Hulubul auzar sai ya iske bakan
a tsaye ya zubo masa idanu fuskarsa cike da
annuri.
Tun kafin sarki Kusaidu ya karasa gareshi sai
boka Hulubul auzar ya rugo da gudu izuwa ga
sarki Kusaidu yana mai yi masa lale marhabun,
kuma ya kama mashi dokin ya sauko, nan take
suka shiga cikin gida suka kadaita a cikin wani
daki.
Har sarki Kusaidu ya bude baki zai ce wani abu
sai boka Kusaidu ya tari numfashinsa ybace ya
kai wannan sarki kada ka bata yawun bakinka
wajen yi mani bayanin abinda ke tafe da kai,
nasan kazo wajena ne domin nayi maka bincike
bisa zargin da kake yi akan matarka Zarifa ko ba
haka bane?
Cikin tsananin mamaki sarki Kusaidu yace
zancen ka dutse ya kai wannan boka mai daraja.
Hulubul auzar ya dubi Sarki Kusaidu yace ya kai
wannan arki mai daraja kayi sani cewa sau tari
wadanda muka dauka a matsayin masoyanmu,
kuma abokan shawararmu sune manyan
abokan gabarmu masu son ganin bayanmu, mafi
254

TASKARNOVELS.COM.NG
akasarin mutanen da muaka yi wa rana su kuma
sai suyi mana dare, in mai bakin cikin sanar da
kai cewa fiye da shekaru ashirin baya, boka
Ardusa da matarka Zarifa suna cin amanarka ta
hanyar lalata da junansu, kuma dan da matarka
Salimat ta haifa Hantaru ba danka bane dan
boka Ardusa ne da Zarifa.
Ko da jin wannan batu sai sarki kusaidu ya dubi
bokan cikin tsananin mamaki da rsahin gasgata
zancen shi yace to amman ta yaya aka yi
wannan abu ya faru haka?
Maimakon boka Hulubul auzar ya bashi amsa
sai kawai yayi nuni da hannunsa izuwa jikin
bango, nan take hoton dukkan abunda ya faru
tsakanin boka Ardusa da Zarifa ya bayyana akai,
tun daga ranar da suka fara cin amanar shi
kawo izuwa ranar da zarifa ta haifi Hantaru ta
ajiye wa Salimat, yayin da Salimat ke nakudar
sihiri wanda boka Ardusa ya sanya mata ba tare
da ta sani ba.
Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu
ya fashe da kukan bakin ciki, yaji duniyar gaba
daya ta yi masa zafi, kawai sai ya zabura ya zare
wuka daga jikinsa ya daga sama zai burma a
255

TASKARNOVELS.COM.NG
cikinsa, cikin hanzari boka Hulubul auzar ya
rike hannunsa ya fisge wukar ya ce haba ya
shugabana, ai idan ka kashe kanka makiyanka
sun samu nasara akanka cikin ruwan sanyi,
inason ka dauki dangana ka koma gida ka kuma
cigaba da rayuwarka kamar yadda ka saba yi a
kullum, sannan kada ka nuna wa zarifa sauyin
komai, kada ka raba shimfida da ita, daga nan
har izuwa ranar da amaryarka da kuma danka
Hantaru zasu dawo gida, a sannan ne ido zai
raina fata ayi maka ramuwar gayya, wacce tafi
ta gayya ciwo.
Kada kace zaia dauki wani mataki a yanzu akan
Zarifa da Ardusa, domin ba zaka iya ganin
bayansu ba, kuma idan ka matsa zasu kawar da
kai ne su gaje mulkinka da dukiyarka a banza.
Ko ni dinnan ban isa na kareka daga sharrin su
ba. Ina mai tabbatar maka da cewa boka Ardusa
ba karamin hatsabibi bane ni kaina ba zan iya
da shi ba duk da cewa na fishi karfin sihiri.
Alkawarin da zan maka shine zan cigaba da kare
lafiyarka da kuma rufe sirrinka bazai taba sanin
cewa ka san sirrin abinda yayi maka ba a yanzu
har sai lokacin da Hantaru zai dawo gida.
Tabbas Hantaru ne zai yi masu hukunci daidai
256

TASKARNOVELS.COM.NG
da abinda suka aikata, domin har abada bazai
taba karbar ba a matsayin iyaye, kuma ya
tsanesu tamkar yadda ya tsani mutuwarsa.
Daga wannan rana sarki Kusaidu ya cigaba da
rayuwa mara dadi, ciwo kuma ya kara tsananta
a jikinsa, kullum sai dai a kwantar a kuma tayar
baya iya yiwa kansa komai, a duk sa'ad da boka
ardusa yazo duba shi inya dubi fuskarsa sai yga
kamar kura yake gani, ita kuwa Zarifa a duk
sa'ad da tazo kusa da shi sai yaga kamar bakar
macijiya ce take fasa kai zata sareshi, baban
qbnida ya kara susuta sarki shine aminttatun
bayinsa da ya tura zuwa birnin Darul Habur dan
kai wasika ga matarsa Salimat tunda suka tafi
basu dawowa ba har tsawon wata shida babu su
babu duriyarsu.
Al'amarin da ya kara jefa matsanancin ciwo
kenan ga sarki Kusaidu, ya zamana cewar
kullum fadawansa ma jira suke kawai ace rai
yayi halinsa su san wanda zasu dora akan
karagarsa.
Babu abin takaici face kullum boka ardusa a
turakar Sarki
End Ads