kwarara uban ihu alokacin
da jini yake shatata daga cikin kunnensa kawai
sai yasa hannunsa guda ya kawomin wawura,
niko na goce amma saida ya chakumo rigata, sai
kawai ya cillani sama saida nayi tafiyar taku
dari a sama sannan na maku akan wata bishiya
na fado kasa a matukar galabaice, awannan
73
TASKARNOVELS.COM.NG
lokacin ne naji Gilzam yana kururuwa mai
matukar razanarwa bashiri sauran dakarun
dabasu mutuba suka farfado sukayita faduwa
daga kan dawakansu saida gilzam ya shafe
dakika dari da arba'in yana kururuwa kuma
yana kokarin zare wannan wuka dake cikin
kunnensa amma ya kasa, daga can sai akaji yayi
tsitt kuma sai ya sulale kasa ya durkushe bisa
guiyoyin sa ya kame tamkar gunki, wato yayi
mutuwa irin ta manyan mazaje.
Koda ganin haka sai sarki hubru ya mike
zumbur ya rugo da gudu zuwa inda nake
kwance ya tasheni zaune ya rungumeni yana
mai tsananin farin ciki da godiya a gareni.
A iya rayuwar mu nida maharaz bamu taba
shiga cikin harabar gidan sarautaba kullum
saidai mujira sarki inya isa fada sannan
mukuma aikin muna tsaron lafiyarsa amma
awannan rana saida sarki hubru ya shigar damu
har cikin turakarshi inda muka zamo yan kauye
muka dinga kalle kalle.
Nan take yasa aka kawo mana abinci da abun
sha iri-iri wato dai ya shirya mana walima
saboda farin cikin mun ceto rayuwarsa muna
74
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin more walimar ne muka hango abinda yasa
muka tsaya cak gabarin ci da sha, duk
gabadayan mu muka kame tamkar babu mai rai
acikin mu.
A lokacin da muka kame kamar babu rai ajikin
mu bawani abu muka gani ba face wata
kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta nufo
mu tana sanye da doguwar riga, wadda aka
yiwa ado da zinare shekarunta basu haura goma
sha uku ba, koda sarki ya hango wannan
kyakkyawar budurwa saiya mike da sauri yaje
ya taro ta sannan ya kariso da ita ya zaunar da
ita abisa kujerar datake fuskartar tamu nida
maharaz muka kura mata idanu muka kasa
kauda kai har saida sarki hubru ya tabo mu
muka dawo hayyacin mu kyakkyawar bata kalli
daya daga cikin muba saita sunkuyar dakai tana
mai murmushi kawai. Sarki hubru yayi gyaran
murya yace yaku amintattun dakaru na kuyi
sani cewa tunda na zama sarki awannan birnin
babu wani da na miji da ya taba shigowa har
cikin turaka ta sai ku, saboda muhimmanci aikin
daku kayi min ayau dinnan na ceton rayuwata
daga sharrin babban abokin gabata wato sarki
dumbazu na birnin Kailus. Wannan kyakkyawar
budurwar da kuke gani a gabanku 'yatace ta
75
TASKARNOVELS.COM.NG
cikina, sunanta Sahira, tunda aka haifeta bata
taba fitowa daga harabar gidan nan ba, kuma
jama'ar gari basu san an haifeta ba, kai hatta
hadiman cikin gidan nan basu san da haifuwarta
ba kune mutane na farko da ta fara gani a
rayuwarta banda nida mahaifiyarta.
Tuntuni bincike awajen bokaye na ya tabbatar
min dacewa, acikin bayina zan samu mutum
biyu zarata wadda zasu kareni daga sharrin
makiya, kuma daya daga cikinsu zai gaji sarauta
ta, dayan kuma zai auri wannan kyakkyawar
yata, kusani cewa ba'a son raina hakan zai faru
ba, kuma banaso ace wani ya auri Yata wanda
ba basarake ba amma babu yadda zanyi
kaddara tariga fata.
Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya
zubo masa sannan ya cigaba bayani...
To nima jin wannan kalamai na Sarki Hubaru
yasa nayi kikam Kasancewar na kamu da
soyayyar Gimbiya Sahira kuma naji yana
ikirarin ba zai bazai baiwa talaka yarsa ba
76
TASKARNOVELS.COM.NG
Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai
tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi
mani magana da profile dina 08138873799.
Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya
zubo masa sannan ya cigaba bayani inaso
kusani cewa a duniyar nan babu abinda nakeso
sama da yata sahira, to amma inaji ina gani zan
rabu da ita domin bincike ya tabbatar min
dacewa rayuwata gajeriyace abune mawuyaci
na kara shekara biyar nan gaba a duniya, daga
yau na damka muka sahira a hannunku na sani
cewa a halin yanzu duk biyun kun kamu da
kaunar sahira, to amma fa kusani cewa dole
daya daga cikin ku ya hakura yabarwa dayan
77
TASKARNOVELS.COM.NG
wadda duk ya auri sahira acikin ku bazai
tabayin sarauta ba kuma zai sota samada komai
a rayuwar sa, kuma saita rigashi mutuwa wanda
yarasa sahira acikin ku shine zai gaji sarauta ta
kuma zaiyi tsawon rai a rayuwarsa har yabar
duniya haihuwa daya zaiyi sannan ya mutu
yabar abunda ya haifa, babu wani tsafi ko wani
kokari dazai sauya wannan kaddara akan mu
inaso ku kwantar da hankalinku akan fitar da
zuciyoyin ku bisa samun mulki koh auren yata
domin lokacin ne zai banbanta komai da
wannan kalami nake muku sallama daku tashi
kutafi gidajen ku amma kafin sannan akwai
kyauta ta mussamman yacce zan baku koda
gama fadin haka sai sarki hubru ya dubi yarsa
gimbiya sahira yace jeki ki dauko musu
kyautarsu cikin fara'a sahira ta mike tsaye ta
shiga wani daki tana tafiyar kasaita tamkar
dawisu jim kadan sai gata tafito da wadansu
jakukkunan fata guda biyu sahira ta matso
gabanmu tabawa kowa jaka guda koda muka
karba muka bude ashe zinare ne acike makil
nan take muka zube kasa muna gdy sarki hubru
ko kallon mu baiyiba saiya kama hannun
gimbiya sahira yashige da ita izuwa cikin
wannan dakin data dauko kudin shigewarsa
78
TASKARNOVELS.COM.NG
keda wuya sai maharaz ya rude ya rikice sbd
ganin wadannan kudade niko sai naji sam kudin
basu dameni niba.
Daga wannan rana wani abu sake faruwa ba sai
bayan kwanaki goma sha bakwai da wata safiya
sa'adda tafiya takama Sarki hubru izuwa wani
kauwe da ake kira zumur domin yaje ya dubo
wani tsohon abokinsa wadda ya kwanta ciwo
tsawon wata uku, shidai wannan aboki na Sarki
Hibru sunan sa abul husnu, kuma tun kuruciwa
suka taso da sarki hubru abinda yasa yayi
zamansa a zumur shine ya samu nasibi matuka
a harkokin kasuwanci domin mutanen garin
suna matukar kaunarsa sbd yawan taimakon sa
da kuma kyautatawa ga talakawa, akarshe ma
saida suka matsa mishi ya karbi shugaban cin
birnin Sarki hubru ne dakanshi yazo ya nada shi
a matsayin shugaban birnin akaxo akayi
gagarumin biki bayan wata daya dayin bikin ne
ciwo mai tsanani ya kama abul husuna lokacin
da lbr ya riski sarki hubru sai hankalinsa ya
dugunzuma aka nemi likitoti suyi masa magani
saida likitoci sukai kwana goma suna lura da
abul husuna basu gane irin cutar datake
damunsa ba, bisa dole duka debi nasu da nasu
sukaje suka sanarwa sarki hubru halin da ake
79
TASKARNOVELS.COM.NG
ciki dajin bayanin likitocin sai hankalin Sarki ya
kara dugunzuma akan hanyane sarki hubru ya
tafi wajen wani amintaccen bokansa ya sanarda
dashi halin da ake ciki, nan take bokan yayi
bincike nan take yayi murmushi ya duvi Sarki
yace ai wannan cuta ta abokin ka sharrin sihiri
ne ba wani bane yayiwa abul husuna asiri sai
tsohon shugaban kauyen zuhur sbd bakin cikin
an sauke shi daga mukaminsa andaura abul
husuna, shi dai wannan asiri an bunne shine a
kofar gidan abul husuna.
Abul husuna bazai taba warkewaba sai an tono
asirin kuma idan an tonoshi take wanda yayishi
zai mutu babu mai iya tono wannan asiri sai
Sarki mai karfin mulki kamarka. Ya shugaba
yazama dole kaje dakan ka kaje ka tono wannan
asiri amma kada kaje sai randa asirin ya cika
kwana casa'in da binnewa domin idan ka
tonoshi kafin cikar kwana casa'in da wanda yayi
asirin da wanda aka yiwa duk mutuwa zasuyi.
Lokacin da bokan yaxonan azancen sa sai sarki
hubru ya cika da mamaki daga can kuma sai ya
dubi bokan yace toh yanzu idan naje kofar gidan
abul husuna yaza'ayi nagane daidai inda aka
bunne asirin boka yayi murmushi yace dazarar
80
TASKARNOVELS.COM.NG
kaje kofar gidan kadaga kwagirinka na sarauta
sama kasake shi, a duk inda kwagirin ya fado to
daidai wajen zaka saka a tone kodajin wannan
batu sai sarki hubru yadauko dukiya mai yawa
yabawa bokan nasa yana mai matukar farin ciki
sannan sukayi sallama sarki ya tafi gida. A ranar
da abul husuna ya cika kwana casa'in a kwance
yana jinya mukayi shiri tareda dakaru dubu
arba'in muka tafi kauyen zumur saida mukaci
rabin tafiya mun shigo cikin wata sahara inda
babu gida gaba babu gida baya babu bishiyoyi
ko duwatsu babu ruwa sai kawai mukaji wani
irin tsananin zafi yana fesowa, nan da nan
dawakanmu suka dimauce suka kama tutsu
suna yada mahayan su suna fita da gudu wata
irin gagarumar iska ta taso ta dinga daga
mutane da dawakai suna yawo akan iska
al'amarin daya dugunzuma hankalin kowa
kenan keken dokin sarki maharaz saida ya rabu
da kasa zaiyi sama kenan na rikoshi da karfin
tsiya amma sai karfin iskar yafara rinjayata
saida maharaz ya taimaka min sannan muka
sauke shi kasa ni kaina inda badan maharaz ya
taimaka min ba da tuni iska tayi sama dani
munaji muna gani gagarumar iskar tayi sama da
dukkanin abokan tafiyar mu tayita lulukawa
81
TASKARNOVELS.COM.NG
dasu tun muna iya hango su har saida suka bace
bat ya rage saura mu uku bisa turba wato ni da
sarki hubaru wanda cikin keken doki bayan
lafawar guguwar ne sarki hubaru ya fito daga
cikin keken dokin ya tsaya a tsakiyar mu nan
take na zare takobi na kama kallon gabas da
yamma kudu da arewa ina jiran tsammani.
Shiko maharaz sai yafara kallon tafin hannunsa
yana karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar
hakan keda wuya sai mukaga wata katuwar
inuwa ta lullube mu koda muka daga kawunan
mu sama sai mukaga wata katuwar halitta tana
saukowa daga sama mai tsananin muni da
rashin son gani sannu ahankali halittar ta iso
kasa-kasa yadda kana iya ganin cikakkiwar
fuskarta koda mukayi arba da halittar sai duk
mu ukun muka firgice ainun kamar zamu
zabura da gudu dayake ita dai wannan halitta
bakomai bace face wata sihirtarciyar dodanniya
mai kawuna takwas kowani kanta guda
girmansa yakaina katon dutse gabadaya
kawunan takwas ajikin wuya daya yake shiko
wuyan nata dogo ne har karawa kanshi tsayi
yakeyi kamar yadda wuyan take kara tsawo
haka hannayen tama ke kara tsawo ga dukkan
alamu dai idanta mike hannunta guda daga inda
82
TASKARNOVELS.COM.NG
take zata iya dauko abindake can bayan duniya
daga kowace kusurwa kawai sai mukaga
dodanniyar nan ta wangame bakinta guda ta
kama gabadaya dakarun namun nan guda dubu
arba'in harda dawakansu sunata zubowa kasa a
mace anan tayita amarsu suna zubowa tamkar
an dafa su acikin tukunya har tururin zafi ne ke
fita daga jikinsu SBD tsananin zafin dake jikin
dodanniyar bayan dodanniyar tagama
amayarda abunda cikinta saita dube mu da
idanunta kwala-kwala ta tuntsire da
mahaukaciyar dariya maikama da saukar aradu,
muka kara firgicewa muka hau kakumar
junanmu lokaci guda ta turbune fuska tace
kaicon yaku wadannan kananan halittu yau kun
gamu da uwar dodannin duniya dayan ku bazai
tsira daga bala'i naba duk saina zare muku
ruhun numfashi, kuyi sani cewa sarki dumbazu
na birnin kailas ne ya aikoni na hallaka sarki
hubaru, labari ya riske ni cewa anturo gilzam
kun hallaka shi to kusani cewa nina gagari
dukkan sadaukan duniya da duk matsafan
duniya, yau shekarata dubu tara ina tare
mutane da aljanu a can dajin sarbusa ina
cinyewa ankasa ganin bayana yanzu Sarki
dumbazu yayi min alkawari cewa in dai na
83
TASKARNOVELS.COM.NG
hallaka sarki hubaru zai dinga bani mutane
dubu ina cinyewa basai nayi wahalar farautar
suba, burina shine naci adadin mutane miliyan
dubu saba'in a sannan ne zan iya haifan yayana
wadanda bazasu bazama ko inaba a duniya sai
sun cinye komai da kowa a kwana tara
yazamana cewa babu wani abu mai rai a doron
kasa saini dasu kawai.
***********************
Mazan Jiya Part 11
#Cigaba
Koda uwar dodanni tazo nan a zancen ta sai naji
dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyata kawai
saina dubi sarki hubru da maharaz nayi musu
inkiya dasu fada cikin keken doki aikuwa sai
sukayi wuf suka fada suka rufe kansu niko saina
zare takobi na, na fuskanci uwar dodanni nace
ai saiki fara gamawa dani kafin ki gamada sarki
hubaru koh! nikaina nasan bakin rijiya yafi
gaban wasan yara dan haka tsaurin ido kawai
84
TASKARNOVELS.COM.NG
dakuma jarraba sa'a nayi amma ko kadan
banasa ran cewa zan iya tabuka wani abu saidai
nasan ance mai rai baya rasa motsi watakila
nadan iya bata mata lokaci.
Lokacin da uwar dodanni taji nayi wannan lafaji
a gabanta saita sake bushewa da mahaukaciyar
dariya a karo na biyu wadda har zaida walkiya
tayita fita daga bakinta tartsatsin wuta yadinga
fita cikin dacin rai da shammata ta mangareni
da hannunta guda sbd karfin dukkan saida nayi
sama na gwara baya ajikin wata bishiya ita
kanta bishiyar saida ta tunbuko har jijiyoyin ta
daga cikin karkashin kasa muka fadi kasa tare
na baje wanwar a sume koh shurawa ban sake
yiba azaton uwar dodanni kasusuwan bayana
sun karye na mutu don haka saita zuro hannun
ta a hankali ta balle kofar dakin keken dokin
dasu sarki hubru ke ciki sukayi arba da fuskarta
kawai saita kama musu dariya alamarin daya
firgita su kenan mussan da suka hango a can
gefe daya a kwance a mace ana cikin wannan
haline na farfado akayi sa'a kuwa banyi
yunkurin mikewa ba yadda hankalin uwar
dodanni zai dawo kaina, a sannan ne tazuro
hannun ta cikin keken dokin ta damko sarki
hubru da maharaz tayi sama dasu da nufin takai
85
TASKARNOVELS.COM.NG
kawunan cikin bakinta ta gutsure su kwatsam
sai uwar dodanni taji motsi akan jelar ta abinda
bata saniba shine nine na ruga na hau kan jelar
naketa tsala matsanacin gudu domin na isa kan
kafadarta kafin hannunta yakai bakinta, koda
uwar dodanni taji motsin yana karuwa saita
fara kai duka faruwar hakan ne tasa uwar
dodanni tasamu jinkirin kai hannunta izuwa
cikin bakinta ta gutsure kawunan su sarki
hubaru koda taga motsin yaki karewa saita
maida hankalinta wajen kai hannunta cikin
bakinta guda saura kiris ta zuro kawunan su
sarki hubaru a bakinta na iso kan kafadar ta
aikuwa saina daka tsalle daga kan kafadarta
nakaiwa hannunta sara wanda ke dauke dasu
sarki hubaru take takobi na ya zabtare hannun
nata ya fado kasa su hubaru suna cikin
yankekken hannun nan kuwa ya kama tsartuwa
da feshi daga cikin dulgul min hannun tamkar
magudanar ruwa ta balle tsananin zafi da zogine
da uwar dodanni tajine yasa tahaukace ta
makance tahau kaiwa iska duka tana ruri da
kururuwa mai tsananin firgitarwa, koda naga ta
dimauce saina dinga saran sassan jikinta da
takobina nikaina nayi mamakin yadda nasamu
wannan nasara cikin gaggawa haka bayan
86
TASKARNOVELS.COM.NG
sassan jikin uwar dodanni ya gama faduwa kasa
sai sarki hubaru da maharaz suka fito daga cikin
keken doki suka kuramin ido kawai suna mai
matukar mamaki na sarki hubaru ya dube ni
yace wai shin wannan yaro anya kuwa kai
mutum ne tayaya kake yin wadan nan
abubuwan alajabi wadanda sunwuce gaban
tsammani. Koda jin haka sainayi murmushi na
goge jinin dake jikin takobina na sumbaci
takobin nace ya shugabana kaga wannan
takobin inhar dai ina tare da ita bana shakkar
tarar kowani irin bala'i asalinta ta kaka nane na
uku indai kaga an cini da yaki to bana tarene
takobin nan nayi imani da haka sarki hubaru ya
kurawa takobin nawa ido dakyau ya girgiza kai
baice komi ba.
ayi hakuri da wannan zancigaba zuwa anjima.
**********************
Mazan Jiya Part 12
#Cigaba
87
TASKARNOVELS.COM.NG
A sannan ne muka dubi gawarwakin dakarun
mu dake zube a kasa sai takaici ya turnuke mu
bamu san sa'adda idanunmu suka ciko da
kwalla ba nan take muka cinnawa gawarwakin
wuta sannan muka hau keken dokin sarki hubru
muka cigaba da tafiya har muka isa kauyen
zumur bamu sake haduwa da wani tashin
hankaliba kamar yadda bokan sarki hubru ya
fadi haka alamura suka kasance da isarmu kofar
gidan yadaga kwagirin sa na sarauta sannan ya
sake shi ya fado kasa aiko sai kwagirin ya cake a
karkashin kasa bai fadi kasa ba koda ganin haka
sai sarki hubaru ya dubeni yace maza ka tone
daidai inda kwagirin ya cake, nan take na cika
umarni koda nayi rami mai zurfi kamu uku
saiga wadansu layu ina fito dasu sai maharaz
yayi nuni ga hannunsa akan layun take suka
kone kurmus faruwar hakan keda wuya said
juyo shewar mata acikin gidan take abul husuna
ya fito daga cikin gida ya takawa da kafafunsa
cikin koshin lafiya, koda yayi arba da sarki
hubru sai yacika da tsananin farin ciki ya rugo
gareshi suka rungumi juna abul husuna yace
lale marhabin da aminina dama nayi mafarki
88
TASKARNOVELS.COM.NG
zan warke daga wannan cuta a ranar daka
kawomin ziyara.
Koda jin haka sai sarki hubaru yayi murmushi
yace aiko mafarkinka gaskiya ne tunda gashi ya
tabbata nan take sarki hubaru yabawa abul
husuna duk abunda yafaru tsakaninsa da
bokansa akan rashin lafiyansa koda jin haka sai
abul husuna ya cika da tsananin mamaki yace
aiko shi makiyi bashida kama domin aduk fadin
garin nan babu mai nuna min kauna samada
tsohon shugaba ashe kaunar ta karyace da
yaudara, rufe bakin abul husuna keda wuya
saiga matar tsohon shugaban da yayan sa sun
rugo da gudu suna kuka da zuwa sai suka zube a
gaban abul husuna suka bada lbr cewa ga
maigidan su can yayi wata irin mutuwa mai ban
tsoro, koda jin haka sai sarki hubru ya dubesu
yace kuje ku kone gawar maigidanku domin
sharrin dayaso yayi abokina abul husuna ne ya
koma kansa, koda jama'ah sukaji lafazin da sarki
hubaru ya fada akan tsohon shugabansu sai
duka hai tsine masa da murna akan muturwar
sa, nan take abul husuna ya shigar damu cikin
gidansa ya kaimu har izuwa turakarsa zaman
mu keda wuya sai wata tsaleleliyar budurwa
wadda muka gani tamkar hussainar gimbiya
89
TASKARNOVELS.COM.NG
sahira ce sbd tsananin kyawu shi kansa sarki
hubru baisan sa'adda ya kura mata idanu ba dan
tsananin alajabi itadai wannan budurwa
bambamcinta da sahira kawai tafita shekaru ne
akalla zata girmeta kamar da shekaru biyu
budurwa ta nufo mu da farantin abinci sannan
ta durkusa har kasa ta gaisheda sarki hubru
sannan muma ta gaishe mu sannan ta koma
cikin gida har sarki hubaru ya bude baki zaice
wani abu sai abul husuna yace kada kace komai
yakai abokina wannan budurwa dakuka gani
yata ce ta cikina sunanta husna kamar yadda ka
boye yarka ga jama'ar kasar nan haka nima na
boye tawa kuma bokan da yamaka bayanin
cutata shine yasa na boye tawa yar kuma ya
gayamun cewa duk ranar daka kawo min ziyara
tare da matasa biyu masu tsaron lafiyar ka to
acikin sune yata zata samu mijin aure sa'adda
abul husuna yazo nan azancensa sai sarki
hubaru ya cika da tsananin mamaki. Daga can
sai sarki hubaru ya kallemu yace ku tashi ku fita
inason ganawa da abokina.
Haka muka tashi muka fice duk kuwa da cewa
muna matukar jin yunwa kuma ga abinci mai rai
da lafiya an kawo. Bayan fitarmu daga gidan
Abul Husuna sai muka samu waje muka zauna
90
TASKARNOVELS.COM.NG
muka yi shiru dayanmu bai ce uffan ba, daga can
sai na dubi Maharaz nace da shi ya kai abokina
nifa abubuwan nan dake faruwa da mu suna
jefamu cikin rudani da rikittarwa, kaga dai ance
dole a cikinmu ne daya zai auri Gimbiya Sahira
sannan ance a cikin mune daya zai auri wannan
budurwa Husuna, ina ganin tun yanzu ynaa da
kyau kowanne daga cikinmu ya banbance
zabinsa, kai yanzu a cikin yan matan nan biyu
wacce ta kwanta maka a rai.
Yayin da Maharaz ya ji wannan tambaya sai yayi
murmushi yace ya kai abokina kayi sani cewa ai
ni bani da zabi sai abinda ka zaba, dan kada na
zabi wacce kake so a ranka, nikam duk wacce na
samu babu matsala.
Da jin wannan batu sai hankalin ya dugunzuma
nace da shi a'a ba za a yi haka ba, inaso ka yi
sani cewa idan ka auri gimbiya Sahira ba zaka yi
arziki ba, kuma ba zaka yi sarauta ba, alhalin
tun tasowarka baka da wani buri da ya wuce ka
zama attajiri kuma ka yi sarauta, amman idan ka
auri Husuna tabbas wannan burika naka zasu
cika, saboda haka ka yarda ka auri Husuna ko
dan ka cika wadannan urika naka.
91
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Maharaz ya ji wannan batu sai ya
rungumeni ya kuma fashe da kuka yana mai
cewa lale maraba da abokin na gari wanda ke
son ganin cikar burin abokinsa.
Cikin kaduwa na janye jikin daga nasa muka
fuskanci juna nace da shi "Ya kai abokina ina
dalilin wannan kuka naka?"
Maharaz ya sunkuyar da kansa kas y ce ban taba
sanin cewa kana kaunata fiye da yadda kake
kaunar kanka ba sai yau, tabbas ka dakusar da
taka rayuwar dan daga tawa, tuni nima nayi
bincike a wajen bokan mahaifina ya tabbatar
mani da cewa kaine kadai zaka iya taimaka
mani domin cimma burikana, idan kwa ka ki
tofa sai dai