na mutu a matsayin bawa, amman
idan ka taimaka mani to kai zaka mutu ne a
cikin bauta.
Koda naji haka sai nayi murmushi nace na
gwammace na mutu a cikin bauta muddin
burinka zai cika, kuma nima nasan nawa burin
zai cika tunda nasan zan gaji mahaifina sarautar
Sarkin yaki.
Maharaz yayi murmushi farin ciki sannan yace
tabbas zaka gaji mahaifinka.
92
TASKARNOVELS.COM.NG
Saida mukayi kwana biyu acikin kauyen zumur
sannan mukayi shiri muka koma birnin darul
mabur mu uku kacal, Sarki hubru bai yarda abul
husuna yabamu yan rakiya ba mun isa gida
lafiya amma sai muka iski wani babban abun
bakin ciki wadda har izuwa karshen rayuwata
bazan taba mantawa dashiba abunda muka iske
shine tundaga komar gidan sarauta muka dinga
arba da gawawwaki duk inda muka duba saidai
muga jini na malala sai tarin gawa, a dimauce
muka ruga izuwa gidan sarauta sarki hubru na
kwalawa yarsa kira amma baiji ta amsaba
gabadaya hadiman gidan ma babu wanda muka
riska a raye a cikin turakar sarki hubru ne
mukaga wata wasika akan gadonsa sarki hubru
ya sunkuya yadauki wasikar, a lokacinda
hannayen sa suke karkarwa cikin karfin hali
yafara karanta wasikar kamar haka takarda
daga sarki uban sarakai gwarzon sarki dodon
mazaje wato sarki dumbazu na birnin kailus
zuwaga kaskantaccen sarki mai taurin kai,
babban abokin gabata hubru Ibn salkas ina mai
sanar dakai cewa ruwa ba sa'ar kondo bane
tabbas ina sama dakai, kodayake ka cancanci
yabo domin yau shekara goma ina kokarin
kasheka amma na kasa ayanzu na aiko gilzam
93
TASKARNOVELS.COM.NG
da maridai yaranka sun hallaka su na turo uwar
dodannin duniya itama sun hallakata toka sani
zuciyar maza ta tafasa dan haka na taso dakaina
na shigo har cikin masarautarka domin in
halakaka da hanuna amma sai akayi rashin dace
baka nan, abinda ya hanani na biyo bayanka
shine binciken danayi a tsafi in nabiyoka ragas
zanyi da yaranka, don hakane na yanke
shawarar na dauke yarka sahira na tafi da ita
izuwa fadata idan ka isa kai ubane mai son
yarsa kazo har fadata ka karbi yarka idan
bakazo ba zan yanke kan yarka na turo maka shi
nan da kwanaki talatin idan kuma kana son
yarka ta tsira toh kasa a yanko min kanka
akawo min nan fadata koda sarki hubru yazo
nan a karatun wasika saiya yanke jiki ya fadi a
kasa sumamme.
*********************
Mazan Jiya Part 13
#Cigaba
94
TASKARNOVELS.COM.NG
A lokacin da sarki hubru ya fadi a kasa sume a
dimauce muka rugo kansa munayi masa fifita
sannan yadawo haiyacinsa koda ya bude
idanunsa yayi arba damu saiya fashe da
matsanacin kuka yana mai cewa narasa yata!
narasa yata!! har abada, yaku wadannan
mazajen fama na umarce ku daku gaggauta fille
kaina sannan ku dauki kan kuje dashi wajen
bokana shabulus Ibn mukaibar domin yabaku
aljanin dazai iya kaiku fadar sarki dumbazu
kafin cikar kwanaki talatin, lallai ku damka
kaina ga sarki dumbazu domin yabaku yata
sahira ku tafo da ita nan birnin darul mahabur.
Sa'adda Sarki hubru yazo nan a zancensa sai
tausayin sa yakama mu har idanuwan mu suka
ciko da kwalla tsowon yan dakiku mukayi shiru
bamuce komai ba kuma bamu birnin sarki
hubru ba, koda ganin haka saiya daka mini
tsawa yace shin bakuda kunne ne bakuji abunda
nace ba, cikin tattausan harshe na dubi sarki
hubru nace ya shugabana ai basai mun fille
maka kai mun kaiwa sarki dumbazu ba inaso
kabamu izini muje har can fadarsa mu yake shi
mu kawar dashi, kuma mu dauko maka yarka
mukawo maka ita nan fadar ka a cikin koshin
lafiya.
95
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai sarki hubru ya
kwarara ihu ya tsalle ya tumu da kasa SBD
tsananin fusata da tashin hankali har saida
muka rikeshi yadawo cikin hayyacinsa saida
kimanin dakiku dari uku da sittin suka shude
sannan yayi ajiyar zuciya ya dubemu yace yaku
manyan gobe inda kunsan masifar datake can
fadar sarki dumbazu dakuma karfin sihirinsa da
bakuce zakuje ku yakeshi ba ina tabbatar muku
dacewa a halin yanzu kuma a wannan zamani
duk duniya babu wani sadauki mai tsananin
karfi tamkar sarki dumbazu kuma babu
matsafin daya kaishi karfin tsafi hatta bokaye da
aljanu shakkar sa sukeyi abinda yasa kukaga ya
gagara hallakani a tsawon shekaru goma shine
duk duniya babu wanda yasan sirrinsa sama
dani kuma inada wani kambun tsafi wadda
indai yana jikina dumbazu bazai taba haduwa
daniba balle yasamu daman hallakani duk
duniya mutum biyu ne rak masu irin wannan
kambu daga ni sai shi sarki dumbazu asalin
sarki dumbazu almajirin mahaifina ne shiko
mahaifina gawurtaccen matsafine Wanda ya
shahara a can wata kasa da ake kira mulubiya
wato a takaice de niba dan asalin wannan birni
bane yawon duniya ne yakawo ni nan har
96
TASKARNOVELS.COM.NG
nasamu shiga awajen sarkin garin ya amintar
dani harya aura min yarsa bayan ya mutu ne na
hau karagar sa albarkacin wannan kambun
tsafin da ubana yabani.
Babban abinda ya haddasa gaba tsakanina da
sarki dumbazu shine dumbazu yayi shekara
ashirin yana yiwa ubana bauta har yasamu ya
yarda dashi ya bashi sirrukan tsafi dayawa
dumbazu yarike amanar amanar mahaifina
hanu biyu har takai cewa mahaifina yadau keshi
tamkar dan cikinsa don haka sai wata rana saiya
kebe dashi cikin sirri yace dashi yakai dumbazu
kayi sani cewa duk a cikin almajirai na babu
wadda na yarda dashi dama dakai, kuma gashi
yanzu tsufa ta riske ni bisa binciken danayi
inada karancin kwanaki a duniya sbd haka zan
baka wani sirri na karshe wadda kaine mutum
na biyu dazai mallake shi bawani bane mutum
na farkon face dana hubru wannan sirri dazan
baka wani kambun tsafine wadda indai kana
tare dashi babu wani mahaluki daya isa ya
hallakaka komai jarumta karsa da karfin
tsafinsa mutum ko aljan aduk sa'arda makiyinka
ya tafi farautar ka bazai taba haduwa dakai ba
saidai ku yita sabani babu wani tsautsayi dazai
sameka muddin kana tareda wannan kambu,
97
TASKARNOVELS.COM.NG
duk tsananin yaki ko matsifa zaka iya ratsawa
ka wuce a yanzu haka tuni na daurawa dana
hubru wannan kambu kuma kaima ga naka.
Koda gama wannan jawabi sai mahaifina ya
bude wata tsohuwar akwati ya dauko wannan
kambu ya mikawa dumbazu hannun dumbazu
na rawa ya karbi kambun ya daura shi a
hannunsa na dama faruwar hakan keda wuya
sai mahaifina ya dubeshi cikin tsananin
damuwa yace kash! kayi babban kuskure sbd
me kadaura wannan kambu a hannun ka na
dama shin kamanta cewa komai na tsafi da
hannun hagu ake yinsa inda kadaura wannan
kambu a hannun ka na hagu da har abada baza a
iya rabaka dashi ba amma yanxu bakin alkalami
ya bushe a koda yaushe makiyanka na iya
rabaka da wannan kambu.
Koda mahaifina yazo nan a zancen sa sai ran
dumbazu ya baci zuciyar sa takama tafarfasa
yace tur!! dakai yakai wannan tsohon banza
hakika kacika tsinanne kuma la'ananne meyasa
tun farko bakace min karna daura kambun nan
a hannun dama ba, wato na fuskanci cewa kana
sane kamun wannan mugunta saboda danka ya
fifita akaina, yau shekara ashirin kenan ina
maka wahala amma shi danka baisan wahalan
98
TASKARNOVELS.COM.NG
kaba ko guda tabbas ka cuceni kuma kaci
amanata sbd haka nima dole naci amanarka
yanzu take zan kashe ka kuma komai daren
dadewa saina kashe wannan dan naka na cire
kambun nasa, nasa a hanuna na hagu. Kodajin
wannan batu sai mahaifina ya yunkura da sauri
domin ya bude wannan tsohuwar akwatin nasa
amma kafin hannunsa yakai kan akwatin tuni
dumbazu ya zare takobinsa ya fille mishi kai
nan take mahaifina ya sulale kasa matacce.
Batareda bata lokaci ba dumbazu ya dauki
wannan tsohuwar akwatin sihirin mahaifina ya
tafi ya bazama gari nema na amma duk inda
yaje sai ace dashi yanzun nan nabar wajen wato
mukayita sabani kenan lokacin dana koma gida
na iske gawar mahaifina saina sulale kasa
sumamme nan take daya daga cikin almajiran
mahaifina mai suna Kusad ya zuba min ruwa na
farfado kodana bude idanu na nayi arba da
Kusad saina tambaye shi a fusace nace wanene
yayiwa uban nan nawa kisan gilla? nan take
Kusad ya gayamin cewa shide yaga sa'adda
mahaifina ya kira dumbazu cikin turakarsa suka
kadaita kuma daga karshe ya jiyo dumbazu na
daga murya cikin fushi daga can kuma sai yaji
sautin sarar takobi kodajin haka sai kusad ya
99
TASKARNOVELS.COM.NG
la6e a bayan kofar turakar kawai sai yaga
dumbazu ya fito daga cikin turakar da sauri
rikeda akwatin sihirin mahaifina dakuma
takobin sa jini na diga a jikin ta.
*********************
Mazan Jiya Part 14
#Cigaba
Koda gama jin wannan batu saina rushe da
matsanacin kuka domin nasamu tabbacin cewa
dumbazu ne ya kashe min mahaifina babban
abun bakin cikina shine nasan cewa har abada
bazan iya daukar fansa ba akan dumbazu domin
akwai ranar da mahaifina yace dani yakai dana
ko a bayan raina kada ka kuskura kace zakayi
kokarin ganin bayan dumbazu domin bazaka
taba samun nasara a kansa ba saboda yafika
karfin sihiri, kai baka samu komai ba daga cikin
ilmina amma zan baka wata kariya wadda babu
wani mahaluki dazai iya cutar dakai.
100
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda naji haka saina dubi mahaifina nace yakai
abbana wai shin meyesa kaki ka koyamin ilmin
ka na tsafi koda mahaifina yaji wannan tambaya
sai idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye
suka zubo masa sannan yace kafin mahaifiyarka
ta rasu ta rokeni alfarmar kadana koya maka
tsafi, domin bincike yanuna cewa idan ka
mallaki irin sirrukan tsafina bazaka taba
haihuwa ba a duniya niko saina daukar mata
wannan alkawari kuma na tabbatar dashi najin
haka saina rungume mahaifina muka fashe da
kuka har izuwa lokaci mai tsawo tun daga ranar
da dumbazu ya kashe mahaifina bamu sake
haduwa dashi ba, amma a kullum acikin
farautar nema na yake har yagaji da neman ya
tafi can wata nahiyar inda yadinga amfani da
karfin sihiri yana yakar sarakuna yana mallake
dukiyar su da mulkin su a hakane ya mallaki
kasashe dayawa duk zamo a karkashin kasa
guda mai suna kailus daidai da rana daya sarki
dumbazu bai taba samun nutsuwa da kwanciyar
hankali ba saboda kawai rashin samun daman
hallakani, a kullum a cikin aiko aljanu da
sadaukan bil'adama yake domin suzo su
hallakani yakai hibru kayi sani duk lokacin
dakaga kana samun nasara wajen kare
101
TASKARNOVELS.COM.NG
rayuwata aduk sa'adda aka kawo farmaki ba
takobin ka bane take baka sa'a face kambun
tsafin dake jikin ka na hagu wannan shine asalin
yadda gaba ta kullu tsakani na da sarki
dumbazu ina mai tabbatar muku da cewa babu
yadda za'ayi kuje birnin kailus kuci dumbazu da
yaki face nayi abu guda wannan abu kuwa
bakomai bane saidai nacire kambun tsafina
nabaka kai hibru kasa a hannun ka sannan kaje
ka tari dumbazu tabbas zaka samu nasara akan
sa saidai ni daku munyi bankwana bazaku dawo
ku sameni a raye ba domin ka'idar wannan
kambu shine duk wanda yadaura shi a
hannunsa to duk ranar daya cire shi bazai kara
kwana uku a duniyar nan ba.
Koda Sarki hubru yazo nan a zancen sai
hankalin mu ya dugunzuma na dubi sarki hubru
nace ya shugabana ina dalilin salwantar da
rayuwar ka akan yarka.
Kodajin haka sai Sarki hubaru ya zubarda
hawaye sannan yace yakai sadauki dan
sadaukai kayi sani cewa nifa sarki nayi arziki
kuma na haihu duk abinda ake nema a duniya
102
TASKARNOVELS.COM.NG
na same shi haka kuma shekaruna sun tafi yata
fa yanzu ne take ganiyar kuruciyar ta SBD meye
zan bari rayuwarta ta salwanta alhali kadai
gareni idan na mutu itama ta mutu babu wani
wanda za'a kalla a tuna damu idan bakuje kun
ceto rayuwarta ba za ayi biyu babu domin bakin
cikin rashin tane zai kashe ni anan ita kuma
sarki dumbazu ne zai kasheta a can yanzu yanzu
bada bata lokaci ba nakeso kuyi shiri kutafi
izuwa ga bokana domin ya sadaku da hadimin
dazai kaiku fadar sarki dumbazu domin ku yake
shi amma kafun sannan ina mai dada jaddada
muku alkwarin dake tsakanin ku kai hibru
amanar yata na wajen ka domin kaine zaka aure
ta kai kuma maharaz na damka amanar kasata
da jama'ah ta a gurin ka domin kai zaka gaji
sarauta ta gama fadin hakan keda wuya sai sarki
hubru ya cire kambun dake hannunsa na hagu
ya miko min hanuna na karkarwa na karbi
kambun nasa a hanuna ina karba saina saka shi
a hanuna wannan shine babban kuskure danayi
a rayuwa ta domin na manta cewa duk wanda
yadaura wannan kambu toh duk ranar daya
cire shi bazai haura kwanaki hudu ba a duniya
nan take mukayi bankwana da sarki hubaru
yana kuka muna kuka domin munsan cewa mun
103
TASKARNOVELS.COM.NG
rabu har abada bazamu sake ganin juna ba kaico
babu ranar bakin ciki wacce tafi ranar rabuwa
da masoyi tabbas mun shaku da sarki hubru
koma munyi imani cewa yana matukar kaunar
mu kamar yadda muke kaunarsa amma gashi
munaji muna gani zai rasa rayuwar sa bamuda
yadda zamuyi mu kareshi lokocin damuka baro
fadar sarki hubaru muka nufi kofar gidan
shaburus Ibn mukaibar rana ta fadi magariba ta
doso kai muna isa kofar gidan muka iske boka
shabarus a tsaye yana jiran isowar mu koda
mukazo dab dashi sai mukaga idanunsa cike da
hawaye yana kallon mu kawai alamarin daya
karya mana zuciya kenan jikin mu ya karayin
sanyi boka shabarus ya dube mu cikin sanyin
murya yace lale da manyan gobe hakika kun
baro masoyina a cikin mugun hali inda nasan
wannan rana zatazo ta riske ni daban kawo
iyanzu ba kuyi sani cewa a duniya banida
masoyi tamkar sarki hubaru amma gashi an
wayi gari inaji ina gani rayuwarsa zata salwanta
babu abinda zan iyayi don kareshi yanzu bada
bata lokaci ba zan hadaku da babban hadimi na
wadda zai kaiku fadar sarki dumbazu acikin
kwana goma sha daya maimakon tafiyar
kwanaki saba'in da bakwai bisa rakumi ko doki
104
TASKARNOVELS.COM.NG
batare da an yada zango ba koda gama fadin
haka sai boka shabarus ya hade tafin hannunsa
waje guda ya kama karanta wadansu kalmomin
tsafi yana tofawa akan tafin hannun daga can sai
yayi nuni izuwa kan kasa nan take kasa ta dare
saiga wani narkeken aljani ya ratso ta cikin
kasar ya bayyana a samanta aljanin nada suffa
irinta tsuntsaye saidai kansa da wuyansa irin na
biladama ne kuma fukafukansa guda goma sha
takwas ne cikin rusunawa aljanin ya dukar da
kai kasa ga boka shubarus ya kwashi gaisuwa
shabarus ya dube shi yace angaishe ka mara'il
labarus yakai mara'il labarus kasani cewa yaune
ranar karshen aikin ka dani domin abune
mawuyaci kudawo ku riskeni a raye.
Koda jin wannan sai hankali aljani mara'il
labarus ya dugunzuma ya dubi boka shabarus
cikin damuwa yace ya shugabana ina dalilin ka
na fadan haka boka shabarus yace yakai babban
hadimi na kayi sani cewa zaka dauki sadauki
hibru tare da boka maharaz ka tafida su izuwa
fadar sarki dumbazu domin su yakeshi su kawar
dashi, kodajin haka sai aljani Mara'il labarus
yayi tsalle ya tumu da kasa ya kama kuka yana
mai cewa haba ya shugabana laifin maina maka
kakeso ka hallakani inani ina zuwa fadar
105
TASKARNOVELS.COM.NG
shugaban bokayen duniya domin a yake shi, na
roke ka daka yafemin wannan aikin kanemi
wani yayi shi amma bani ba.
Kodajin haka sai boka shabarus ya dakawa
aljani mara'il labarus tsawa yace dolene kai
zakayi wannan aikin domin kai kadai ne zaka
iya idan kuma kace bazaka yiba yanzu take anan
zan hallakaka kayi sani cewa sadauki hibru na
tareda kambun tsafin sarki hubaru don haka
babu wani tsautsayi dazai sa ku halaka saidai
zaku iya shan bakar wahala, maza ka kwashe su
ku tafi kuma ka tabbatar dacewa kun isa can a
kwanakin dasuka gaza ashirin tabbas bazaku
dawo ku riske niba domin a ranar da masoyina
zai mutu nima zan mutu, koda gama fadin haka
sai boka shabarus ya juya ya shige gidansa, koda
faruwar haka sai aljani mara'il labarus ya
suremu nida maharaz sannan ya bude
fukafukansa yayi sama sannan ya fara tsala
gudu nagaban kwatance muna gifta giza gizai
tambar wucewar tauraruwa mai wutsiya saida
muka shafe kwanaki tamkar wucewar
tauraruwa mai wutsiya, sai da muka kwashe
kwana goma sha takwas muna tafiya bisa aljani
mara'il labarus a sararin samaniya batareda
yasauko kasa ba don ya huta nikam a rayuwata
106
TASKARNOVELS.COM.NG
bantaba ganin aljani mai juriyar wahala ba
tamkar aljani mara'il labarus baisan yunwa ba
baisan ishirwa ba balle lalaci a yammacin
kwana na goma sha takwas dinne muka hango
fadar birnin kailus daga can nesa kadan a gaban
mu.
Wohoho!! tabbas fadar ta isa da akirawota da
matsayin aljannar duniya domin gavadaya ginin
ta da gilashin lu'u-lu'u akayi shi babu abinda
zaibawa mutum mamaki face ganin yadda aka
gina gabadaya birnin na kailus a tsakiyar wani
kogi abinda bamu saniba shine aljanu ne suka
zuba tubalin ginin harya fito saman kogin nan
duk inda zaka taka jauhar ne da zabar amma
indaga sama ka taho kana iya ganin yadda
ruwan kogin ya zagaye birnin gabadaya, aljani
mara'il labarus bai sauko kasa ba saida muka
iso dabda birnin sannan ya dira a bakin kofar
garin babu kowa a bakin kofar balle muyi
artabu damasu gadi kuma sai muka iske kofar a
bude wanwar sannan mukaji garin yayi tsit
tamkar babu wani abu mai rai acikin sa,
alamarin dayayi matukar bamu mamaki kenan
batareda fargabar komai ba muka sauko kasa
daga kan aljani mara'il labarus na wuce gaba ina
mai yafuo maharaz da aljani mara'il labarus da
107
TASKARNOVELS.COM.NG
hanuna ina mai cewa kubiyo ni a baya, a lokacin
ne na zare takobi na, na cigaba da tafiya ina mai
duba kowace kusurwa kuma ina kasa kunne
kozanji motsin wani abu daka iya kawo mana
farmaki sumame saida muka shafe sa'a shida
muna tafiya a cikin birnin kailus ko bera bamu
ganiba rayayye duk mutanen garin da dabbobin
su sun kame sun zamo gumaka babu abunda ke
motsi hatta kasuwa damuka ratsa ta cikin ta
mukaga mutane sunata harkoki amma kowa a
kame yake yazamo gunki, wasu suna musayar
kudi da kaya wasu kuma bakunan su a bude
alamar cewa magana sukeyi hakadai muka
cigaba da tafiya har muka iso kofar fadar birnin
anan bamuga komai ba ko gunkin dakaru babu
ma balle muji tsoron cewa zasu iya tashi akoda
yaushe su farmana, kai tsaye muka kunna kai
izuwa fadar har muka isa inda karagar sarki
take amma bamuga kowa ba bamuga wani abu
mai rai ba, kuma duk kofofin fadar nan a bude
suke bamu riski guda daya a kulle ba dazuwan
mu gaban karagar mulki sai muka dubi junan
mu mukayi ajiyar zuciya a tare na dubi maharaz
da aljani mara'il labarus nace yaku abokan
tafiya kuyi sani cewa ruwa baya tsami banza
duk yadda akayi an sanda zuwan mu kuma an yi
108
TASKARNOVELS.COM.NG
mana tanadi, nikam ina ganin cewa wani tuggun
aka shirya mana shiyasa bamuga komai da
kowa ba kafun nagama rufe bakina sai kawai
mukaji kofofin fadar na rufe kansu daya bayan
daya sannan sai mukaji an bushe da
mahaukaciyar dariya amma bama iya ganin mai
dariyar nan nan fa maharaz yafara amfani da
karfin sihirin sa domin yaga mai yin dariyar
amma sai abu ya gagara nan take cikin mu ya
duri ruwa duk da na tuna cewa ina tareda
kambun tsafi wanda sarki hubru yabani amman
sai naji banida nutsuwa da yadda dakai
kwatsam sai mukaga wadansu dakarun aljanu
ma'abota kwarjini daban tsoro sun bayyana
dayawa ba adadi sunyi mana kawanya suna
rikeda muggan makamai wadanda ko a labari
bamu tabajin irinsu ba sbd razanar damukayi
bamu san sa'adda muka kankame juna ba mu
ukun, abin mamakin ma shine aljani mara'il
labarus yafimu firgicewa domin duk ilahirin
gabban jikinsa karkarwa sukeyi kamar wadda
ake zukar jinin jikinsa, bazato ba tsammani sai
mukaga sarki dumbazu ya bayyana tsulum akan
karagar mulkin sa yana kyakyata dariyar
mugunta sannan saiga sauran dakaru na
bil'adama da duk fadawan sa sun bayyana suma
109
TASKARNOVELS.COM.NG
sunayi mana dariya, al'amarin kashe mana jiki
kenan mukaji nadama tazo mana bisa kawo
kanmu izuwa wannan birni domin mun san
cewa mun sayi ajalin mune da kudinmu, lokaci
guda sarki dumbazu ya tsuke bakinsa yabar
dariyar fadar tasa keyin tsit sarki dumbazu ya
dube mu, mu ukun yace yanzu ku uku kacal aka
turo ku yakeni wani haukane yasa kuke tunanin
zaku iya karawa dani hakika yaro baisan wuta
ba, yakai hibru kayi sannin cewa nayi nisa a
halwar tsafi sanina ya wuce na maigidana
mahaifin sarki hubru don haka wannan kambun
tsafi daya baka ka daura a hannun ka bazai
maka tasirin komai ba domin ka gamsu da
bayani na a yanxu zan nuna maka wani abu,
koda gama fadin haka sai sarki dumbazu ya
bude damtsen sa na dama saiga irin wannan
kambun tsafi wadda sarki hubru yabaiwa hibru
nan take sarki dumbazu ya cire kambun ya jefa
shi a cikin wani kasko take kambun nan ya kone
kurmus, sarki dumbazu yasake kyalkyalewa da
dariyar mugunta a karo sannan yace to