x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - MAZAN JIYA 1

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 49662 words

Category: Adventure Stories

Views 181

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

TASKARNOVELS.COM.NG

1

TASKARNOVELS.COM.NG

MAZAN JIYA
1
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part A
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude
a cikin daular larabawa anyi wata kasaitacciyar
kasa mai suna DARUL MAHABUR. Kasar Darul
Mahabur na da matuqar girma da fadi kuma ta
qunshi manyan birane a karkashin mulkin sarki
guda daya mai sun MAHARAZ IBN SULEDENI.
Birnin darul mahabur ya bunqasa da karfin
arziki, yawan alumma da kuma kasuwanci har

2

TASKARNOVELS.COM.NG
ya zama abin kwatance a ko ina cikin duniya.
Sarki
Maharaz ya kasance mutum mai tausayi,
taimako da jin kan al'umar sa, Allah ya hore
masa arziki mai dunbin yawa gami da kaifin
hankali da kuma hasashen gaba yana da matar
aure guda daya kacal mai suna SHALIFAT kuma
basu sami haihuwa ba sai bayan shekara 11 da
yin aure don haka a yanzu 'yar su qaramar
yarinya ce 'yar shekara 8 a duniya wadda ta
kasance kyakkyawa ta gaban kwatance ana
kiranta da suna MULAIFA.
Tun daga lokacin da Allah ya baiwa Maharaz da
Shalifata Mulaifa sai suka dauki soyaiyar duniya
suka dora akanta ya zamana ko quda basa son
suga ya sauka a kanta.tun da mulaifa ta taso ake
tsantseni da ita kuma komai sai dai ayi mata
koda ruwa zata sha sai dai a bata a baki batun
jin dadi dai da hutu masana sunyi bincike sun
tabbatar da cewa a wannan zamani babu 'yar
gata kamar mulaifa ko kadan sarki maharaz bai
kasance Sadauki ba hasalima bai ta6a yin yaqi
ba, amma yana da Sarki yakk wanda ake kira
HIBRU IBN IMLAS.

3

TASKARNOVELS.COM.NG
Hibru ya kasance babban masoyin sarki
maharaz wanda a koyaushe a shirye yake da ya
sadaukar da rayuwar sa don kare ta sarki da
mutuncin sarki. Sai dai wani abin mamaki shi ne
duk irin wannan kauna da Hibru ke nunawa
sarki tazama a banza don sarki yaqi yaja shi a
jikinsa.Sharifa matar sarki maharaz ta sha yi
masa fadan akan sabo da me yaki yaja hibru a
jikinsa amma bai ta6a gaya mata dalili ba.sun
sha samun sa6ani akan hakan har ma rai ya
6aci, akwai ranar da ta harzuqa sarki baisan
sa.adda ya mare ta ba.
Cikin tsananin mamaki sharifat ta ruqe kuncinta
ta dubeshi a lokacin da qwalla ya cika idanunta
tace "Ya kai mijina kayi sani cewa 2n da ka
aureni baka ta6a gayamin baqar magana ba
bare zagi,amma yau gashi ka mareni lallai
dalilin da yasa ka mareni shine yasa baka son
kowa yasan sirrin dake tsakaninka da saduki
hibru, ni kuwa nayi maka alkawari komai daren
dadewa sai na bincika wannan sirri na san shi"
Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki
Maharaz ya dugunzuma ya risina a gaban
sharifat tamkar qaramin yaro sannan ya ce "Ya
ke matata ki yafe min bisa dora tafin hannuna a
4

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma a lokacin bana cikin haiyacina hakan ta
faru ki ina cewa tunda muka hadu ni da ke ban
ta6a rokon ki alfarma ba hakane?
Cikin sanyin jiki sharifat tace "Kwarai kuwa"
Sarki ya durkusa bisa guiwoyinsa a gabanta ya
rike hannayenta a lokacin da idanunsa suka ciko
da kwalla sannan yace "Na roke ki don darajar
iyayenki da soyaiya dake tsakanin mu da 'yar
mu kada ki binciki wannan sirri domin ubangiji
darbuza ya hanani yin hakan."
sa.adda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai
jikin sharifat ya qara yin sanyi ainun kuma ta
cika da tsananin mamaki daga wannan rana
bata qara yiwa sarki maganar hibru ba.
Shima sarkin yaqi sau daya ya ta6a yin aure a
rayuwar sa kuma matar tasa ta sami shekara 7
da mutuwa amma ta bar masa da guda daya
kyakkyawan matashi dan shekara 12 ana
kiransa IMNAL.
Ya gado mahaifinsa a fagen sadaukanta har ma
ana ganin cewa nan gaba idan ya girma sosai sai
yafi mahaifinsa jarumtaka domin 2n yana da
shekara 7 yake dakawa maza gumba a
5

TASKARNOVELS.COM.NG
hannu.duk sa,adda za.a fita yaqi dashi ake fita
kuma yana taka muhimmiyar rawa irin wacce
manyan mayaqan hibru ya raina abokan gaba
sai yayi zamansa ya 2ra imnal ya wakilceshi
wajen dakarunsa. Hakika duniya tana da fadi
take haka kuma abin cikinta yawa gareshi a can
wata nahiyar daban kuma akwai wani
gawurtaccem sarki mai suna Dujalu Ibn
Shardud wanda ke mulkin birnin hawaruldin.
Sarki dujalu ya kasance mashahurin mayaki,
sadaukin sadaukai yana iya yakar mutanen gari
guda ya kashe su ya kama matansu a matsayin
bayi, ya kuma kwashe dukiyar su a matsayin
ganima ta wannan hanya ce ya mallaki
garuruwa da yawa a qarqashin mulkinsa kuma
yana tara dukiya mai qazamin yawa. Bugu da
kari sarki dujalu ya kasance qasurgumin matsafi
wanda babu kamar sa a nahiyar.
A lokacin da sarki dujalu ya ga ya qasaita sai yai
bincike a cikin halwar tsafinsa don yasan
matsayinsa a akan sauran sarakan duniya. Sai
da ya kwana arba'in sannan ya kammala
binciken inda hankalinsa yai ma2qar tashi ya
rasa abin da ke masa dadi a duniya. Ba komai ya
gani ba illa sarki maharaz shine yayi dai dai
6

TASKARNOVELS.COM.NG
dashi komai da komai. Koda sarki dujalu yaga
wadannan al.amura sai ya kamu da baqinciki ya
aiyana a ransa dole ne yayi 2nanin hanyar da zai
bi ya rushe daular sarki maharaz ya zamana ya
kawar dashi daga doron qasa kuma ya gaje
dukiyarsa da mulkinsa ya hada da nasa domin
ya zama babu kamarsa a duniya. Bisa wannan
dalili ne ya sake shiga halwa ta kwana saba'in
don ya sami mafita. Mafitar itace dole ne ya
mallaki wandansu makaman yaqi na #
mazanjiya wadanda zamaninsu ya shude
shekarun baya, wadanda ba a ta6a yin mayaqa
tamkarsu ba,kuma ba.a ta6a samun makaman
yaqi masu qarfin sihirin nas ba.
Makami na farko shine wata sihirtacciyar takobi
mai suna Saiful Lujara mallakar Sadauki
Hantaru na Birnin Kisra sai mashi mai suna
Galilil Haras mallakar Sadauki Shaddadu na
birni kufa.
Sai wata hular tsafi mai suna lamsara mallakin
sadauki hulkas na birnin romaniya .

☼☼☼☼☼☼☼☼☼
7

TASKARNOVELS.COM.NG

Ita dai takobin saiful lujara duk abin da aka sara
da ita sai ya tsage gida 2 koda dutse ne ko qarfe,
kuma koda shafar jikin mu2m akayi da ita sai ya
mu2 saboda mugun dafin da ya ke jikinta. A
yanzu haka takobin ta na can ajiye a qarqashin
tsakiyar tekun Bahar dufiya a ƙarƙashin tsaron
dakarun aljanu dubu 90.
Tun bayan mutuwar Sadauki Hantaru
wadannan aljanu suka dauko takobin daga
gidan hantaru suka kawota tekun bahar sufiya
suka ci gaba da tsaronta. Ba za su gushe akan
wannan aiki ba face izuwa qarshen rayuwar su
don aduniya ba su da abin bauta face wannan
takobi. Tun a lokacin da bokan ya qerata mutum
uku kacal za suyi amfani da ita. Yanzu mutum
daya yayi amfani da ita ya bar duniya ba a san
sauran mutum biyun da suka rage ba. Duk
wanda ya mallaki wannan takobi har abada ba
za.a cishi da yaqi ba koda zai shekara miliyan a
duniya. Su kuwa wadannan aljanu guda dubu 90
an gutsuri ruhin kowannen su an sa a cikin
sinadarin qarfen da akayi wannan takobi, shi ya
sa suka mallaka rayuwar su a kan babu wanda

8

TASKARNOVELS.COM.NG
ya isa ya iya rabasu da ita face yana cikin
mutane 3 da ke da damar anfani da ita.

☼☼☼☼☼☼☼☼

Mashin Galilil haras mallakin Sadauki Shaddadu
na Birnin Kufa, a halin yanzu yana ajiye a can
wani kogon sihiri dake birnin kufa, fiye da
shekara dubu tun da aka ajiye mashin ba wani
mahaluki da ya sake shiga kogon.
Shi dai kogon a cikin ƙarƙashin kasa yake
mutum bai isa ya ga inda kofar kogon take ba
face ya zo da takobin saiful lujara wajen ita ce
zata sa shi a kan hanya ta shigar da shi har cikin
kogon ta bude masa kofofi 99 ya isa inda aka
ajiye mashin galilil haras.
Haka kuma mashin na iya rikida ya zama abin
hawan mu2m doki ko rakumi wanda ba zai gaji
da tafiya ko yunwa ko kishin ruwa har kwana
40.

9

TASKARNOVELS.COM.NG
☼☼☼☼☼☼☼☼

Ita kuwa hular lamsara shu'umar hula ce wadda
idan mutum ya sanyata yana iya ganin abin da
ke gaban sa nisan tafiyar kwana 40 tamkar abin
a gabansa yake, haka duk irin guguwar da akeyi
ko tsananin ruwan sama ba zasu kusance shi ba.
Sai dai ka ga yana tafiya amma babu su a inda
yake.
Hular lamsara na ajiye a cikin wani gida na
kayan tarihi da ke birnin romaniya, in da aka
ajiye kayan tarihin dukkanin sarakunan birnin
wadanda suka shude, babu wani tsaro akan
hular amma komai hatsabibancin mutum bai isa
ya dauke ta ba face ya shigo dakin dauke da
mashin galilil haras.
Bayan sarki dujalu ya gama nazarin wadannan
kayan yaqi na # mazanjiya sai ya cika da
tsananin farin ciki yayi ta kyalkyata dariyar
murna.
Kashe gari kuwa da sassafe yasa a ka shirya
dakaru miliyan dubu suka kama hanya suka nufi
nahiyar da tekun bahar sufiya take domin dauko
10

TASKARNOVELS.COM.NG
takobin saiful lujara, sannan su wuce birnin
kufa da birnin romaniya don dauko mashin
galilil haras da hular lamsara.

*****************

A can birnin darul mahabur kuwa yau ne a ke
bikin qarshen sheka na bautar gunkin darbuza.
Tunda duku-dukun safiya dakin bautar ya cika
da jama.a maza da mata duk inda mutum ya
hanga sai dai yaga kawunan bil'adama ne rututu
babu masaka tsinke, shi dai wannan dakin bauta
yana da ma2qar girma da fadi.domin ya kai
girman wani garin.A duk shekara mutane na
zuwa daga dukkan sauran qasashen dake
nahiyar domin neman tubarraki.
Saboda haka duk shekara akwai wakilan wadan
nan manyan sarakuna tara dake zuwa wadan
nan dakin bauta.
A wannan rannan rana sadauki hibru da dansa
imnal sunzo bautar da wuri-wuri. Ba komai ne
yasa hakan ba face imnal ne ya sa matsawa
11

TASKARNOVELS.COM.NG
hibru akan lallai su zo da wuri don su kusanci
gunkin darbuza.
Maganar gaskiya ita ce ba don su kusanci
darbuza bane sai don kawai yaje kusa da
gimbiya mulaifa ta ganshi ya ganta. 2ni imnal ya
sha alwashin cewa llai a yau ne zai furtawa
mulaifa cutar da take addabar zuciyar sa tsawon
shekara bakwai kuma a shirye yake ya dauki
duk irin horon da za.ayi masa.
Cikin sa.a kuwa su hibru suka kusanci inda
gunkin darbuza yake ya zamana tazarar da ke
tsakaninsu da inda su maharaz ke zaune ba ta
wuce taku biyar ba.
Gaba dayan dakin bautar tayi tsit,kuma kowa ya
rufe idanunsa ya sunkuyar da kansa qas. Dama
haka qa'idar dokar bautar take kuma sai an
shafe a qalla sa'a guda a haka,sannan sarki
maharaz zai miqe yayi bayanin jawabin da
gunkin darbuza yayi masa, ma.ana ya isar da
saqon darbuza ga jama.a. Dama duk shekara
gunki darbuza yana bayani ne akan abubuwan
da sa su faru a nahir na alheri ko na tsiya. Kua
duk abin da ya fada suna faruwa ne ba a ta6a
samun akasi ba. Game da abubuwan tsiyan da
12

TASKARNOVELS.COM.NG
za su faru sai ya fadi abin da za ayi domin
neman tsari ko sauqi.
A wannan lokaci da kowa ya sunkui da kansa
qas kuma ya rufe ido akayi tsit ne, imnal ya dago
kansa ya bude idanunsa wato ya karya dokar
bauta. Kawai sai ya miqe tsaye ya tafi cikin
sand'a yana tsallake mutane har isa inda
gimbiya mulaifa ke zaune su biyu rak. Kawai sai
imnal ya zauna daf da mulaifa ya dauki
hannunsa guda ya d'ora akan nata cikin firgici
mulaifa ta d'ago kai don taga wanda ya ta6a ta,
koda tayi arba da imnal sai ta qura masa idanu
ta qame tamkar ba ta da rai . Nan take taji ta
kamu da tsananin qaunar sa bata san sa.adda ta
dafa hannun sa da nata d'ayan tayi masa
murmushi sannan tasa bakinta akan kunnensa
tayi masa magana a cikin rad'a "tabbas kaine
imnal d'an sarkin yaqi hibru"
ko da jin wannan ba2 sai mamaki ya kamashi
don haka sai shima ya kara bakinsa a kunnenta
yace "tabbas maganarki gaskiya ce amma ya
akayi kika sanni alhalin nayi imani cewa baki
ta6a ganina ba?".

13

TASKARNOVELS.COM.NG
Mulaifa ta ce ansha bani labarinka a siffanta
mini kamanninka. Na dade ina kwatantaka a
cikin zuciyata.kamannin da nake gani a
mafarkina su na gani a yanzu. Kai kuwa menene
dalilin da yasa ka karya dokar bauta kazo har
wajena? Shin baka tsoron sarki ya sa ayi maka
horo mai tsanani?
Imnal yayi murmushi ya ce ya ke ma.abociyar
kyau da kwarjini ki sani cewa zuciyar da ta
kamu da begen masoyi makauniya ce kuma
kurma ce. Haka zalika ba ta tsoron komai a
duniya muddin za ta sadu da abin begenta.
Lallai na dad'e ina begenki a zuciya ta tsawon
shekaru bakwai kuma a yaune nayi alqawarin
sai na furta miki ciwon zuciya ta ko da kuwa
bayan nai hakan za.a tsireni nan gaban
miliyoyin wannan jama.a.
Da taji wannan zance sai idanunta suka ciko da
qwalla ta ce "godiya ta tabbata ga ubangiji
darbuza wanda ya cusa min qaunar ka a
zuciyata 2n kafin na ganka da ido na."
ya kai masoyina ka sani daga ranar da na fara
jin labarinka ni ma naji na kamu da tsananin
qaunar ka kuma nima yau shekara bakwai
14

TASKARNOVELS.COM.NG
kenan ina fama da begenka a zuciyata,bani da
burin da ya kai na ganka da idanuna amma
damar hakan bata samu ba sai yau.
Da yaji wannan ba2 sai ya kamu da tsananin
farin ciki kuma yaji sonta ya qaru a ransa d'ari
bisa d'ari, kawai sai suka rungume juna.'
a dai dai Wannan lokaci ne sarki maharaz ya
d'ago kansa sama ya bud'e idanunsa sharkaf da
hawaye.'
ba zatao ba tsammani sai ya ga Mulaifa da Imnal
a kankame da juna. A dai dai wannan lokaci ne
sarki maharaz ya dago da kansa sama ya bude
idanunsa domin ya yiwa jama'a bayanin sakon
darbuza, idanunsa sharkaf da hawaye.

Nima ganin yadda sarki Maharaz ya dago da
jajayen idanunsa yayi matukar bani tsoro yasa
na tsaya cak da typing, sai Allah Ya kaimu gobe
mu cigaba.

Zan ci gaba.
15

TASKARNOVELS.COM.NG

Da fatan anyi sallah lafiya, sannan duk wanda
yake son complete zai iya tuntubata ta wannan
number 08138873799 kira ko whatsapp.

MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part B
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

Ba zato ba tsammani sai ya ga mulaifa da imnal
a rugume da juna daf da shi al.amarin da ya
matukar firgitashi kenan,kuma ya cika da
tsananin mamaki, ya tambayi kansa,
"ya ya akayi imnal ya tsallako yazo har nan inda
muke? Kuma ya akayi mulaifa ta yarda dashi har

16

TASKARNOVELS.COM.NG
ta rungumeshi alhalin ta kasance mai ji da kanta
da kare martabarta"?
Gama aiyana hakan ke da wuya sai mulaifa ta
dago kai tayi arba da sarki yana kallonsu cikin
razana ta janye jikinta daga na imnal. Al'amarin
da ya sa shima ya juya kenan ya yi arba da sarki
maharaz ya daka masa harara ba tare da ya ce
da shi uffan ba. Imnal ya juya da sauri ya koma
can wajen mahaifin sa ya zauna ya kara sunkui
da kansa kas, ita ma gimbiya Mulaifa sai ta
sunkui da kansa qas ta rufe idanunta zuciyarta
na ta daka.
A sannan ne sarki Maharaz yai ajiyar zuciya
gami da gyara murya. Koda jin gyaran muryar
tasa sai kowa ya dago da kai aka qura masa ido.
Da aka ga hawaye na zuba a idanun sarki sai
hankalin kowa ya dugunzuma,sabo da ba a ta6a
ganinsa a cikin irin wannan hali ba.
Sarki Maharaz ya qara yin gyaran murya a qaro
na biyu sannan ya dubi jama.a cikin tsananin
tashin hankali, domin mai girma darbuza ya
gaya min cewa rayuwar dukkanin jama.ar dake
wannan nahiya na cikin mugun hadari, sa6o da
akwai wani gawurtaccen sarki mai suna dujalu
17

TASKARNOVELS.COM.NG
wanda ke mulkin birnin hawarul din. Bincike ya
tabbatar da cewa a halin yanzu da ni da sarki
dujalu mun yi kunnen doki a qarfin mulki, arziki
da girman kasa. Bisa wannan dalili ne kishi ya
kama sarki dujalu ya sha alwashin cewa sai ya
rushe daulata ya mallake mulkina da arziqina
sannan sai ya mamaye duk kasashen da ke
wannan nahiya tamu. Ba ma nahiyar mu kadai
ba gaba daya duniyar yake son ya mallaka sabo
da biyan wannan buqata ne sarki dujalu ya
shiga halwar kwana saba'in ya samo mafita bita
bisa samun biyan buqata.
Mafitar kuwa ita ce dole ne yaje ya samo
wadansu sihirtattun makaman yaqi guda wadan
su zaqaquran sadaukai uku MAZAN_JIYA
wadanda a zamaninsu ba a sami kamar ba.
Wadannan mutane su ne, kaura Shaddadu na
birnin kufa, sadauki Hantaru na birnin kisra, da
kuma Hulkas na birnin romaniya. Wadannan
barade sun cika MAZAN JIYA domin har yau har
gobe ba a sami jarumai ba kamar su kuma har i
zuwa qarshen duniya ba za a ta6a mancewa da
tarihin su ba.
Shi sadauki

18

TASKARNOVELS.COM.NG
1... Hantaru yana amfani da wata sihirtacciyar
takobi ce mai laqanin Saiful Lujara, kome aka
sara da ita sai ya dare gida biyu tamkar a sa
wuqa a yanka lemon 6awo koda kuwa a takobi
sai ya mutu saboda kaifin dafin da ke jikinta.
2...Shaddadu yana amfani da wani sihirtaccen
mashi ne mai laqanin Galilil Haras, duk
mahalukin da ya mallaki wannan mashi komai
yawan abokan gaba shi kadai zai iya hallakasu
da mashin, domin a duk sa'add ya cillashi
cikinsu sai ya burma cikin mu2m dubu arba'in a
cikin dakiku kadan, sannan zai dawo hannun sa.
Mashin galilil haras yana da tsananin haske don
haka komai duhun waje in dai aka shiga da shi
sai anga komai ko da kuwa allura ce ta fadi
qasa.bugu da qari mashin na iya rikidewa ya
zama abin hawan mamallakin sa walau doki ko
raqumi kuma ba zai gaji da
End Ads