x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 47 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 138001 words
  • 140573 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 483

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ne kawai Jonas,har yanzu fushi yake dani” girgiza mashi kai uncle jonas yayi yana sake bashi haƙuri.
wani irin ɓacin rai ne ya rufe ya Naeem ganin halin da dady ya shiga,bai taɓa jin haushin sam irin na yau ba,dan me zai dinga wahalar masu da mahaifi dan kawai ya fahimci yana sonshi
“dady ka daina zubar da hawayenka akan shi,ni nayi maka alƙawari a yau ba sai gobe ba zamuje har California ni da Adnan,komai zai yi sai mun kawo maka shi har gida” ya Naeem ya faɗa
“ba sai kunje ba Naeem,da kaina zanje na sameshi,idan ma kashe ni zaiyi ya kashe ni,amma nagaji,nagaji!!” uncle mustapha ne ya yayi saurin cewa
“A'a baza'ayi haka ba yaya,tunda har yace zai zo nan kwana biyu,mu jirashi mu gani idan bai zo ba ni da kaina zanje na zo maka da shi,kayi haƙuri”
“baza ka gane ba mustapha,ku barni kawai na tafi,bazan iya jira har tsawan wannan kwana kin ba,ni ka ɗai na san yanda nake ji”
“na sani yaya,amma kaga baƙo ka yi bai cancanci ka tafi ka barshi ba”
“kayi haƙuri Tahir,idan ma bai zo ɗin ba sai mu tafi tare da kai” a cewar uncle Jonas,
ya Naeem ne yace“uncle to ku bari ni da Adnan ɗin mu tafi”
“A'a Naeem,babu wanda zai tafi”
lallashin dady su ka shiga yi akan ya jira nan da kwana biyu idan sam ɗin bai zoba sai su tafi,da ƙyar su ka samu suka shawo kanshi.
babu wanda ranshi bai ɓaci da rashin zuwan sam ɗin ba.
haƙuri uncle mustapha ya sake ba dady yana kamo hannunshi,bin bayan su suka yi har inda su ka yi parking motocinsu,motar uncle mustapha dady da uncle Jonas su ka shiga yayinda Alyar da James su ka shiga mota ɗaya da su ya Naeem,reverse su ka yi su ka fice daga Airport ɗin.
ya Naeem tunda su ka shiga mota yake dialing number Sam amma kiran baya tafiya
tsaki yaja,kallon shi ya Adnan dake driving yayi yana faɗin “lafiya dai ko,waye ka ke kira??” kamar jira yake ya Adnan yayi magana ya shiga surfa masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,shiru su kayi motar babu wanda yace mashi wani abu har ya gama dan sun fahimci ranshi yayi mugun ɓaci.
“ni gaba ɗaya a wannan al'amarin nafi ganin laifin dady,Allah ya bashi mu da yawa amma dan me zai hana kanshi zaman lafiya saboda shi,da ace tuntuni ya watsar da lamarinshi da bai rika ɓata mashi rai irin haka ba kuma shima da bai gujeshi ba,amma dady ko za kayi me kana bashi shawara akan Sam baya ɗauka,ya ɗauki son duniya ya ɗora mashi” ya Adnan ya faɗa rai a ɓace
“tun yaushe nake nunama dady haka amma kwata kwata baya ganewa,ya fi son depression ya kamashi saboda sam”
“dan Allah second father kuyi haƙuri,uzuri ne ya riƙe shi amma ba da gangan yaƙi zuwaba,dashi mu ka yi shirin zuwa Allah ne bai nufa ba” Alyar ya faɗa,suna matuƙar son ɗan uwansu duk sai su kaji ba daɗi da maganganun su ya Naeem,duk da suma kan su basa jin daɗin halin da ya ke nunama dady,basu da yanda za suyi ne kawai
“uhmm kana son kareshi ne kawai Alyar,amma ni na san babu wani uzuri daya riƙesa,kawai yayi ne dan yaga halin da dady zai shiga,sai dai ya sani muddin dady ya faɗi ya mutu da ɓaƙin cikinsa Allah bazai barshi ba”
“ya subahanallah,dan Allah ya Naeem ka daina faɗar haka,da badan uzurin daya riƙesa ba da babu abunda zai hanshi zuwa,amma in sha Allah yana nan zuwa soon”
“dole na faɗin haka Alyar,sam ya matuƙar ɓata man rai yau,a iya sanina baya da jahilcin addini,ya san cewa iyaye ba abun wulaƙantawa bane,amma ya koma kamar wanda bai taɓa sanin komai a addininsa ba,shi ko tsoron Allah ya kamashi da alhakin mahaifinsa bayayi??”
“haka ne second father,in sha Allah komai zai wuce,nan da two days yana nan zuwa”
“wallahi kar Allah ya sa ya zo,ai duniya ce wanda bai zo ba ma jiranshi take bare wanda ke cikinta” girgiza kai Alyar yayi baya jin daɗin kalaman da ya Naeem ɗin ke faɗa,haƙuri su ka shiga ba su shi da James, ya za suyi da halin ɗan uwan nasu lamarin nashi ne sai Adu'a.
dady tunda su ka shiga mota ƙala baice ba kana kallonsa kasan yana cikin damuwa,haƙuri uncle Jonas ya sake bashi yana sake tabbatar mashi da uzuri ne ya riƙe sam ɗin amma yana nan zuwa kafin su tafi,jinshi kawai dady yake amma ya san babu wani uzuri daya riƙesa kawai baya son ganinsa ne,kullum cikin Adu'a yake Allah ya rage mashi son shi amma ina yanzu ya fara tunanin sonshi ne ajalinshi.
har suka iso gida babu wanda ya sake cewa komai.
mom tayi matuƙar farin ciki da zuwan kawun nata sai dai ta wani ɓangaren tayi takaicin ƙin biyo su da sam ɗin yayi sai dai ba ta nuna hakan ba ta barshi akan da sun tashi tafiya ƙafarta ƙafarsu,ita za taje da kanta ta dawo da shi.
babu wanda baiji haushin rashin zuwan sam ɗin ba musamman laatifa da Nainarh,dan Nainarh ɓoyewa tayi a bedroom ɗin su tasa kuka,taci burin ganinshi amma yaƙi ya zuwa,Abbah ma yaji haushin rashin zuwan sam ɗin,har kiran wayarshi yayi amma bai sameshi ba da yake gidan shi su ka fara zuwa,uncle Jonas baiji daɗin rashin samun uncle mutallab da mom Fatilah da yayi ba,yaso ace yayi masu ta'aziyya ido na ganin ido,sun ɗan jima a gidan Abbah kafin suka nufi gidan dady,acan su ka sa mu uncle Ubaid da uncle Hashim sun zo yi ma uncle Jonas barka da zuwa ba su san sun tafi airport ba da sun je tarbosu.
Tarba ta musamman uncle Jonas ya samu daga ahalin Abbah hakan kuwa baƙaramin daɗi yayi mashi ba,ya sake tabbatar da karamcin su,ba wannan bane zuwanshi na farko ba.
Alyar basu wani jima a Estate ɗin ba su ka nufi gidan su shi da James duk da dady ya so su zauna part ɗin sam amma Alyar yace zuwa gobe za su dawo.
su uncle Ubaid sun jima sosai a gidan,fira sosai su ka sha da uncle Jonas,sai da dare yayi sosai tukun su ka yi mashi sallama su ka koma gida.
su uncle ubaid na tafiya dady ya rakashi bedroom ɗin dake kusa da nashi wanda mom ta gyaramashi,zama dady yayi,kwantar mashi da hankali uncle Jonas ya shiga dan ya lura har yanzu da sauran damuwar duk da yana ƙoƙarin dannewa,murmushi kawai dady ya mashi yana faɗin bakomai zai jirashi nan da kwana biyun,mom ce ta shigo ɗakin,tashiga ɗakin dady bata ganshi ba yasa ta zo nan,kusa da kawun nata ta zauna tana sake mashi sannu da zuwa da tambayar lafiyar mahaifiyarta da matarshi,duk suna lafiya yace mata yana tambayar Irfan da tunda ya zo bai sa shi a ido ba.
tunda safe ya fice daga gidan zuwa aso Villa,tunda aka yi rasuwar bai fita ba sai yau.
sun ɗan jima a ɗakin sosai suna buɗe wani babin firar yaushe gamo,sai da dare ya raba sosai tukun su ka yi mashi sallama su ka fice.
bedroom ɗin dady su ka nufa
“Naeem ya sanar dani komai daya faru,ni kaina banji daɗin rashin zuwan sam ɗin ba amma dan Allah kayi haƙuri ka cire damuwar sam a zuciyarka,ganin ka damu dashi ne yasa yake wahalar da kai,kuma bai kamata kana nuna tsantsar soyayyar shi a gaban ƴan uwanshi ba”
“Zulaihart ni kaina ban san wane irin so nakema sam ba,bana iya ɓoye soyayyar shi a ko ina”
“na sani ƴallaɓai amma daurewa za ka yi,ko dan saboda ƴan uwanshi,kullum burin su su faranta maka,Ni na san basa jin daɗin banbancin da kake nunawa tsakanin su da ɗan uwan su kawai suna daurewa ne yasa ba su taɓa nuna maka ba” ta san su ya Naeem kawai baza su faɗa bane amma dole suna jin ba daɗi da irin soyayyar da yake nuna ma sam ɗin
“in Allah zan gwada yin hakan”
“Allah ya sa” lallashin shi ta shiga yi tana sake kwantar mashi da hankali har bacci yayi awan gaba da su.
dady sai da ya tabbatar da mom tayi nisa a cikin baccin tukun ya tashi, toilet ya shiga bai wani jima ba ya fito,jikinshi da damshin ruwa da alama wanka yayi, dressing room ɗin shi ya nufa,mom na nan kwance tana bacci ya fito har ya shirya cikin suit silver color,wayar shi dake ajiye saman nightstand ya ɗauka,matsawa yayi kusa da ita, kissing forhead ɗin ta yayi kafin walking calmly
ya fice daga ɗakin.
lokacin da zai isa compound har driver shi ya fito da mota da alama ya jima da sanin tafiyar,back seat ya buɗe mashi ya shiga kafin shima ya shiga mazaunin driver,reverse yayi su ka ɗauki hanyar ficewa daga Estate ɗin.
tunda ya fito yake laɓe jikin Piller yana kallon su sai da ya daina ganin motar ta su tukun ya fito,baƙaƙen kaya ne complete a jikinshi,ya rufe ko ina a jikin shi,hannu ya zura cikin trouser pocket ɗin ya ciro waya,dialing wata number yayi,wanda ya kira na picking yace “boss yanzu nan ya fita daga gida” bana iya jin me na cikin wayar ke faɗa mashi sai ji nayi yace “ok sir an gama” zame wayar yayi daga kunnenshi,ya nufar bayan gidan.


*A ROUND 3 AM*

Ƙarar wayarta ne yayi sanadiyar farkawarta,hannunta ta zura tana laluben switch ɗin bed-side lamp ta kunna,hasken ne ya ɗan haska gadon,idanunta ta kai ga dady dake kwance kusa da ita ga mamakinta baya nan, tunanin ta fara ko yana toilet,
a hankali ta kai hannunta ta jawo wayar tana duba mai kiran nata,faɗuwa gabanta yayi ganin number dady, saurin kallon agogon dake manne jikin bango tayi wanda ke nuna ƙarfe 3:40 na dare kafin ta kalli wayar tana mamakin to ina yaje a wannan lokacin da har yake kiranta a waya,har kiran ya katse ba tayi picking ba wani ya sake shigowa, picking tayi tana kara wayar kunnenta,on the other side taji wata murya saɓanin ta dady nayi mata sallama,saurin sauka tayi daga saman bed ɗin gabanta na wani irin mummunan faɗuwa,to waye wannan me ya kai wayar mijinta hannunshi,da ƙyar ta samu tayi ƙarfin halin faɗin “bawan Allah waye kai,ina mai wayar yake ⁉️”
“dan Allah da katte nake magana” bugun zuciyarta ne ya tsananta jin sunan da na cikin wayar ya ambata,cikin rawar murya tace “Eh itace,waye kai,ina mai wayar yake⁉️”
“ya gamu da haɗari ne a...” ai tun kafin ya ƙarasa ta saki wayar hannunta,kamar saukar aradu haka taji zancan nasa,ficewa tayi daga ɗakin kamar zata tashi sama ita kanta bazata iya cewa ga halin da take ciki ba,tana shiga main parlor ya Naeem da ya Adnan na faɗowa,tana ganin su kawai ta yanke jiki ta faɗi.....
*INNALILLAHI WA INNAH ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA'AKLIFLI KHAIRAN MINHA,LAHAULA WALA QUWWATA ILLAH BILLAHIL ALIYUL AZIM*

*ina dady zashi,waye ke sanar da fitowarshi,wa yake sanar mawa,ta ya akai wannan haɗarin ya faru da shi⁉️*
*Shin bari mu koma baya*
*Wacece wannn baturiyar data haihu a ɗakin hotel har tayi sadaka da ƴarta ba tare da ko taji ɗumin jikinta ba,sannan su waye mata da mijin data yima sadaka da ƴarta⁉️*
*Su waye ke bibiyar rayuwar Nainarh,taya akai Abid ya rayu bayan an shida ma court mutuwarshi,wane flash ne mahaifin Nainarh ya bata,ina Flash ɗin yake,shin da gaske ne yumnah ce ke bibiyar Nainarh,su waye su ka kashe mahaifin Nainarh⁉️*
*Shin da gaske Zaabith na tare da uncle Mustafa ko dai kawai zargi ne⁉️*
*Waima waye ya kashe Noor,wace masifa ce tasa kanta a ciki,su waye bayin Allah data taimaka,menene a cikin Flash ɗin data ba Irfan,wane zaɓi ne take cewa tayi mashi⁉️*
*Shin kuna ganin hukuncin da uncle mutallab ya ɗauka akan mom Fatilah ya dace❓*
*Wacece Carol ne❓*
*shin kuna tunanin Nailarh ta rayu bayan duka da Allurar da mahaifiyarta tasa aka mata,waye CEO dake bibiyar Nailarh,wacece Aunty Sophia,Allurar mecece taba Noah ya ba Mrs Malika,waye mijin Mrs Malika,wane yara ne Nailarh ta gani a container lokacin da mahaifiyarta ta turo masu da kaya,Mrs Malika wace irin uwa ce ita dake neman ƴarta,wace irin uwace da zata lalata rayuwar ƴarta,wane irin business ne ma take yi⁉️*
*Club ɗin waye su Irfan ke kula da shi,wacece yarinyar da aka yima opretion su waye su ka yi mata opretion ɗin,shin kuna ganin mom maimunatu zata koma gidan uncle Hashim ⁉️*
*Wanene SAM,me ye asalin abunda ya haɗashi da dady,shin duk laifin da dady yayi mashi ya cancanci yayi fushi da shi,kuna ganin zai zo kuwa bayan two days ɗin da su Alyar su ka ce⁉️*
_Masu karatu tambayoyin fa da yawa,kuma ko wacce na buƙatar amsa,dan jin wannan amsoshin kukasance dani taku Queen Kainart a cikin wannan labari mai taken SHIRYAYYAR ƘADDARA,ku kasance dani a season two dan samun amsoshin tambayoyin ku._

*Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh anan na kawo ƙarshen littafin shiryayyar Ƙaddara season one game buƙatar two 500 ne za'a tura kuɗin ta wannan asusun 9131306012 Hadiza mukhtar opay bank sai a tura shaidar biya ta wannan nambobin 08133650574/09163957890*

*Daga Alƙalamin Queen Kainart...✍*
*Chat me via WhatsApp*
*08133650574/09131306012*












An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads