x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 35 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 102001 words
  • 105000 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 462

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
tafiya
“bai shigo ba,ku mu tafi kawai” mom ta faɗa,tun ranar da ya ƙone Nainarh yake fushi da su bai sake dawowa gidan ba.
ficewa su ka yi daga gidan,motar yumnah Fa'iza da Nainarh su ka shiga mom da laatifa kuma su ka shiga motar mom da driver zaiyi driving ɗin su,motar su mom na gaba ta su yumnah na baya su ka fice daga gidan zuwa gidan Abbah.

*UNITED STATE❤*

_*Las Vegas (Nevada)*_


tsit gidan yake baka jin motsin komai kasancewar dare ne sosai,duhu ne ya mamaye ko ina sai ɗan hasken bulbs ɗin dake compound da ya haska gidan kamar rana,ɗai ɗai kun securitys ne ke kai kawo a compound ɗin.
A tsaye take cikin garden ɗin da haske kaɗan ne a ciki,riga da wando ne haɗe da mayafi a jikinta masu santsi,ta rufe rabin fuskarta da mayafin,hannun ta riƙe da ƴar madaidaiciyar leda,ta kai tsawan minti 30 a cikin garden sai safa da marwa take da alama akwai wanda take jira,time to time take duba wristwatch ɗin dake hannuta haɗe da kallon ƙofar shigowa garden ɗin.
ganin har 2:45Am tayi yasa kawai ta yanke shawarar bazai zo ba,harta juya da nufin barin garden ɗin ta hangoshi yana shigowa.
ɗaya daga cikin securitys ɗin gidan ne,baƙaƙen kaya ne a jikinshi yayinda ya rufe fuskarshi da face mask,ko Ina na jikinshi a rufe,nannauyar ajiyar ta sauke,ƙarasowa yayi har in da take.
“am sorry ma'am”
“wannan wane irin shirme ne baka san ina jiran ka bane?” ta faɗa rai a ɓace
“tun around 1:30 am nake nan jiranka amma har tsawan 45 minutes baka zo ba”
“am very sorry ma'am,na tsaya ne dan na tabbatar babu wanda yaga shigowata nan ne,am sorry” tsaki kawai taja,leda dake hannuta ta miƙa mashi,amsa yayi yana zuba mata ido dan jin ƙarin bayani
“please ka tabbatar ka bata zuwa gobe,I hope baka manta yanda plan ɗin yake ba”
“yeah ban manta ba”
“okay,Ina wanda ya kawo shi?”
“yana bedroom”
“ohk kana iya tafiya kar su fahimci baka nan” ok ya ce yana zura leda cikin aljihun rigar dake jikinshi,ta hanyar da ya shigo ya bi ya fice,har sai da taga ficewarsa tukun itama ta bi ta wata ƙofar ta fice,cikin gidan ta nufa ta ƙofar wacce zata sadata da ɗakinta,a hankali take tafiya har ta kawo bakin ƙofar ɗakinta ba taci karo da kowa ba,kama handle ɗin ƙofar ɗakin tayi “Mrs Sophia!”
kamar daga sama taji an ambaci sunanta,wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi,a hankali ta sakin handle ɗin ƙofar,juyowa tayi tana kallon luna data ambacin sunanta,a tsaye take hannunta riƙe da bottle water
“daga Ina ki ke haka a wannan lokacin?” luna ta faɗa tana tsareta da ido
“na duba jikin Nailarh ne” ta faɗa tana juya,saurin buɗe ɗakinta tayi ta shiga,barin wurin itama luna tayi ta nufi ɗakin su.

*Washe gari*

A zaune su ke saman dinning chairs a katafaren dinning room ɗin gidan,Aunty Sophia na kusa da Nailarh tana bata abinci,kwata kwata hankalinta baya kan abincin yana kana momynta da har yanzu take fushi da ita,ko kallon in da take bata son yi.
Tissue ta yaga ta goge bakinta “sophia”ta kira sunanta,kallon malika tayi tana ba Nailarh abinci “i will travel tomorrow please take care of her”
“ok ma'am safe trave” jinjina mata kai Malika tayi,Nailarh kasa haɗiye bread ɗin dake bakinta tayi jin abun da Momyn tata tace,fushin da take da ita har ya kai ta tafi ta barta, tissue hannunta ta ajiye haɗi da ficewa daga dinning room ɗin,miƙewa itama Nailarh tayi tabi bayanta,a bedroom ɗinta ta sameta, saurin juyowa tayi jin an buɗe ƙofar ɗakin,idanunta ne suka sauka akan Nailarh dake binta da wani kallo,juya mata baya tayi tana nufar bakin window ɗakin.
A hankali ta taka har izuwa inda take,hugging ɗinta tayi ta baya tana zagayo da hannunta saman flat tummy ɗinta
“am sorry momy” Nailarh ta faɗa tana langwaɓar da kanta saman shoulder malika
“sorry mom” ta sake faɗa, ajiyar zuciya Malika ta sauke,zame hannun Nailarh dake kana tummy ɗinta tayi,juyo da ita tayi suna facing juna,zuba mata ido tayi tana kallo itama Nailarh kallonta take
“momy I'm sorry if I hurt u” kamo hannun Nailarh tayi “sorry for what?” Malika ta faɗa
“na san kina fushi dani saboda rabuwa da mijinki da na saki”
“I'm not angry with you”
“idan har baki fushi da ni mi yasa za ki yi tafiya bayan kin sa I'm not completely healed?”
“important issue ne that's why”
“please ki sa su Joseph su yi reflecting naki mana”
“dole da kaina zanje” kallonta Nailarh tayi kamar za tayi kuka “please momy ki zauna a tare dani”
“bazai yiwu ba baby,dole na tafi,but if you follow me then” Malika ta faɗa tana kallonta duk da ta san da wahala ne Nailarh ta amince zata bita, duk da itama ta fi son hakan tana so ta bata space ne ko hakan zai sa taji sauƙin abunda ke damunta
“zan biki” Nailarh ta faɗa,kallonta Malika tayi da mamaki “are u sure?”
“yeah am sure,zan tafi tare da ke”
murmushin Malika tayi mata,saurin shigewa tayi jikinta tana sake hugging ɗinta,a hankali ta ɗaura hannunta saman head ɗinta,shafa sumar kanta ta shiga yi
“baby wane lokaci ki ke ganin ya kamata muyi Aure?”
“you said next year”
“na canza ra'ayi yanzu kuma,da mun dawo daga wannan tafiyar kawai tunda kin sa na rabu da mijina”
“am sorry” Nailarh ta faɗa
“alright” nocking ƙofar ɗakin aka yi
“who there?” Malika ta faɗa
“ma'am its me,Noah” sakin Nailarh tayi ta nufi bakin ƙofar,buɗe ƙofar tayi
“is they anything?” ta faɗa tana kallonshi,ledan dake hannunshi ya miƙa mata “saƙo ne daga Dr Daniel, injection ɗin Madam Nailarh ce ya aiko da ita” amsar leda Malika tayi tana duba kwalin alluran dake ciki
“thank You” ta faɗa tana maida ƙofar ɗakin ta rufe,in da Nailarh take ta nufa
“i think tafiyar mu tare bazata yiwuba”
“why” Nailarh ta faɗa tana kallonta,leda dake hannunta ta nuna mata “allurace Daniel ya aiko da ita yanzu”
“ni fa am fine yanzu,babu wata allaura da za'a man”
“no Nailarh tunda ki ka ga ya aiko da ita tana da mahimmanci ne a gareki,kiyi haƙuri kawai ai ba jimawa zanyi ba zan dawo,karki manta we will get married soon” turo baki Nailarh tayi
“kiyi haƙuri kinji,zan ba Sophia sai ta dinga yi maki naga kamar towce ne far day, morning and evening”
“mu tafi tare da ita mana sai ta dinga man acan”
zama malika tayi tana kama hannunta “please Nailarh ki bari na tafi,time ɗin da zan dawo kinga kin ƙara samun sauƙi” lallashin Malika tayi har ta samu ta haƙura da tafiya.
Aunty Sophia Malika taba injection ɗin kamar yanda tace.
Aunty a salinta kafin ta zama nanny Nailarh a orpernage take aiki a matsayin Nurse anan Malika ta ganta har ta ɗauketa aikin nanny lokacin Nailarh na da shekara 3 a duniya,tunda ta dawo gidan Malika dan kula da Nailarh ta ajiye aikinta na Nurse,sai ta jima ba tayi allura ba ko wani abu daya shafi aikinta.

*ABUJA NIGERIA💋*


After Asr prayer gaba ɗayan su su ka hallara a katafaren meeting room ɗin gidan dake part ɗin Abbah.
Abbah na daga kan royel sofa a zaune yayin da gaba ɗayansu suke zaune a ƙasa saman rug carpet sun harɗe ƙafafunsu kamar ma su ɗaukar karatu,Nainarh na daga zaune kusa da Aunty Mariya da tunda ta zo gidan take maƙele da ita,har da ɗan faɗa ta mata saboda rashin zuwa gidanta da bata sake yi ba,mom a zaune take kusa da dady idanunta ta sauke akan Irfan da kwana biyu kenan rabon data sa shi a idonta,yana na daga zaune gefen ƙafanfun Abbah,kanshi a ƙasa,ƙallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar damuwar da yake ciki,kwana biyu kacal amma duk yabi ya rame kamar ba shi ba,wani irin tausayin shi ne ya rufeta,amma ya za tayi,rabashi da Noor shi yafi Alkairi a gare shi,kallon ɗin Noor dake kwance saman jikin momynta tayi,itama duk ta fita hayyacinta,itama ba ƙaramar rama tayi ba abunka da mara jiki duk sai ta koma wani iri,har wani haske ta ƙara,sauke idanunta tayi ƙasa tana jin wani iri a zuciyarta.
Mama Ameenah tunda ta zauna wajen idanunta ke kan mom tana Binta da wani kallo mai cike da tsana,gaba ɗaya kallon da tayi ma Irfan da Noor akan idonta.
Laatifa suna wuri ɗaya zaune ita da su Aunty Nafisat,Aunty Nadeya da Aunty kainart sai Noha matar ya Usman ɗiyar Aunty Safeenah, baiwar Allah tunda su ka shigo parlorn idanunta ke kan dadynta da yayi kamar bai san da zamanta ba ko kallon inda take baiyi ba,idan ka cire su mamy da mom data san abunda ke faruwa,ba bu wanda bai tambayi ina mom maimunatu da Balqis ba, amma sai uncle Hashim yace ma su Balqis ce ba lafiya shiyyasa ba su samu zuwa ba.
Laatifa sosai hankalinta ya tashi jin ƴar uwarta ba lafiya,ta kira wayar su ya fi a ƙirga amma bata samu ba,wayar balqis na ringing amma ba tayi picking ba,mom maimunatu kuma tata a kashe,hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba.
Gyaran murya Abbah yayi gaba ɗayan su su ka kai dubansu gare shi,ya Naeem dake ɗayan gefenshi ya kalla yace ya buɗe masu taro da Adu'a,tashi yayi kamar yanda Abbah ya umarta,tsit parlorn yayi har ya kammala Adu'a ya koma mazaunin sa, gyara zama Abbah yayi cike da Dattaku da kamala ya fara magana
“Alhmdllh gaba ɗayan ku ina maku Barka da juma'a,da yawan ku nan sun san maƙasudin wannan zaman ɗai ɗai kun cikin ku ne ba su sani ba” tsit parlorn ya sake yi kamar mutuwa ta gitta “na tara ku nan ne saboda abun farin cikin daya same mu wanda nake fatan ɗorewar sa har bayan raina” tunda Abbah ya fara magana mom fatilah ta haɗe girar sama da ƙasa irin ba mutuncin nan
“shekarun baya da su ka wuce munyi ire ire wannan taron wanda da yawan ku sun hallara ƙalilan daga cikin ku ne basa nan,to kamar dai shekarun baya yau ma cike da farin ciki da fatan ɗorewar irin wannan taro nake sanar daku maganar Auren ƴan uwanku Irfan da Nurjahan . wanda za'ayi nan da wata uku idan Allah ya sa muna da rai da lafiya sai Waseef da Kairiyyah” Abbah na kaiwa nan yayi shiru, murmushi farin ciki ne ya bayyana akan fuskokin su dady,babu wanda a cikin su baiyi farin ciki da wannan haɗin ba,Irfan da Noor bugun zuciyarsu ne ya tsananta,abunda zai biyo baya daga iyayensu mata kawai su ke tsoro,ɗaga ido ya Naeem yayi yana kallon mom da kallo ɗaya zaka mata ka hango tsantsar damuwar da take ciki,mom fatilah tunda Abbah yayi shiru ta shiga aikama Irfan harara Kamar zata tashi ta rufe shi da duka.
“kamar ko wane lokaci bazan hana ku iyayen yara faɗar ra'ayin ku ba,ranar da aka tsaida tayi maku ko da mai abun cewa a cikin ku?” Abbah ya faɗa yana bin su da ido.
dady Ahmad da dady Mustafa wanda sune wakilan Irfan da Noor su ka yi saurin cewa
“babu wata matsala Abbah,duk lokacin da aka tsaida rana hakan yayi,Allah ya nuna mana lokacin bikin lafiya” da Ameen su dady su ka amsa,mom fatilah sai wani cika take tana batsewa,ji take kamar ta shaƙi wuyan uncle Mustafa da yayi maganar.
kallon dady da uncle mutallaf Abbah yayi
“ku fa hakan yayi maku?” dady ya bashi amsa da “ai ƴaƴan su ne Abbah,duk hukuncin da suka yanke yayi”
“to Masha Allah hakan yayi, shi kuma Waseef sai munji daga dangin mahaifin Kairiyyah,muji su kuma yaushe ne za su sa ta su ranar,sai ku iyayen su mata idan da mai abun cewa to” Abbah ya faɗa, tunda Abbah ya faɗi haka uncle mutallaf ke jefa ma mom fatilah wani irin kallo mai cike da gargaɗi amma sai ta kauda kamar ma bata san yana yi ba,tsit parlorn yayi babu wani wanda yayi making any move har Abbah ya fara tunanin ko ba mai abun cewa ne a cikin su,mom fatilah tana son magana amma uncle mutallab yaƙi bata space ga Noor daketa faman haɗata da Allah kan karta hanata farin cikinta
“kamar yanda muka haɗu haka Allah ya nuna mana ranar Auren lafiya” Abbah ya faɗa da Ameen duka su ka amsa.
kallon ya Naeem Abbah ya yi yace ya rufe masu taro da Adu'a,miƙewa yayi Naeem yayi
“Abbah ina ne Alfarma kafin a rufe taro” mom ta faɗa kanta a ƙasa,gaba ɗaya parlorn su ka kai dubansu gareta,wani irin mummunan faɗuwa gaban Irfan yayi haka ma Noor dady kuwa zuba mata ido kawai yayi
“muna jinki Zulaihart, wace irin alfarma ki ke nema,faɗi muna saurarenki”
dady sai kallonta yake burin shi ta ɗago ta kalle shi ko ya hanata abun da take shirin yi amma taƙi bashi Accesse ɗin da zai yi hakan
“ina mai baku haƙuri gaba ɗayan ku,Alfarmar da nake nema ba lallai taima wasu daga cikin ku daɗi,amma ina fatan ku fahimce ni ku kuma yi man uzuri”
“ba komai Zulaihart muna sauraren ki” kallon su uncle Ahmad tayi
“a karo na biyu ina mai sake baku haƙuri,ban so a wannan karan nayi jayayya akan wannan hukunci da ku ka yanke ba amma ya zama dole,Irfan ɗanku ne kun isa ku yanke ko wane irin hukunci akansa,amma a matsayina na mahaifiyar shi ina neman alfarma maganar Auren shi da Noor a barta” dady ne yayi saurin cewa
“amma Abbah tana so...” saurin dakatar da shi Abbah yayi “barta tayi magana” shiru dady yayi,yana jin wani iri a ranshi bai taɓa tunanin haka daga gareta ba,Abbah dama tunda ta shigo part ɗin ya fahimci kamar akwai abunda yake damunta,sai yanzu ya fahimci mike damunta,tunda ya ke da ita wannan ne karan farko data nuna hukuncin da ya yanke bai mata ba,har ta kasa haƙuri ta iya faɗa da bakinta,ko bikin su ya Naeem bata so ba amma tayi haƙuri,a wannan karan ya kamata suyi mata uzuri kamar yanda ta buƙata
“ba'a san raina naƙi amincewa da umarnin ku ba sai dai bani da wani zaɓi ne,ni kaina zan so zumuncina da mutallab ya ƙara ƙarfi sai dai haƙura da Auren shi ne mafi Alkairi sama da ɗaura shi,nayi haƙuri na jure komai da Auren Naeem sai dai a wannan karon nakasa wannan haƙurin da juriyar,ku gafarce ni idan har alfarmar dana nema batai maku daɗi ba,ina mai baku haƙuri,banyi hakan da nufin wani abu ba”
“babu komai Zulaihart ai ɗanki ne,babu wanda zai mashi Auren da baki amince da shi ba,babu damuwa Allah yasa hakan shi ya fi zama Alkairi”
Irfan tunda Abbah ya faɗi haka wata irin zufar tashin hankali ta rufe shi,gaba ɗaya ji yayi duniyar ta daina mashi daɗi,Noor ma maƙale momynta ta yi jikinta na wani irin shaking kamar wacce fever ta kama,su uncle Mustafa babu wanda maganar mom tayi ma daɗi,amma duba da abunda ya faru rannan a gaban su sai su ka yi mata uzuri,wannan ne karan farko data taɓa nuna ƙin amincewarta akan wani abu.
mom fatilah har wani sauke Ajiyar zuciya take tana sakin murmushi,su mamy babu wanda fasa Auren bai ma daɗi ba,kallon juna su ka yi ita da mom halima suna sakin murmushi,ba ƙaramin daɗi suka ji ba.
tashi ya Naeem yayi ya rufe masu taron da Adu'a kamar yanda Abbah ya bashi umarni,yana kammalawa matan su ka fara tashi suna fita.
kama hannun Noor mom fatilah tayi amma taƙi tashi, duƙawa tayi tana kallonta “Noor lafiya, tashi mu tafi mana” kallon Momyn ta ta tayi numfashinta na sama da ƙasa
“Noor lafiya?” ta faɗa tana jijjigata ganin yanda ta fara gasping Kamar breath ɗinta zai ɗauke she's asthmatic since she was a child
kamota tayi ta ɗago da ita amma kwata kwata jikinta ba ƙwari gaba ɗaya ta koma ƙasa gasping ɗin da take na tsananta,dafe chest ɗinta tayi,hankalin mom Fatilah ba ƙaramin tashi yayi ba,hankali a tashe ta shiga kiran sunanta gaba ɗaya su dady su ka yo kansu su mom har sun fice ba su san ma mike faruwa ba, hankali a tashe uncle Mustafa ya shiga yi mata fifita da gefen rigarsa,ƙirjinta sai sama yake yana ƙasa,Irfan kasa motsi yayi daga in da yake zaune,shi kanshi bazai iya cewa ga taƙamaimai yanda yake ji.
ruwa uncle mutallaf ya shiga bata amma ina numfashinta neman ɗaukewa yake,hannu biyu uncle Mustafa yasa ya ɗauketa,ficewa yayi da ita daga parlorn gaba ɗaya su ka bi bayan shi Irfan da Waseef kawai aka bari,magana yake ma Irfan ɗin amma kamar baya hayyacin sa,kama hannunshi yayi su ka fice daga parlorn,lokacin da su ka zo parking space da yawan su sun tafi gida mom ma sun tafi ita da su Aunty laatifa da Aunty Kainart da za taje gidan saboda Laatifa,gaba ɗaya ta sanar da ita abunda ya faru bata ɓoye mata ba,su dady kuma hospital su ka nufa tare da Noor, Nainarh da yumnah da Fa'iza kuma sun wuce gidan ya Naeem wanda shi yace Nainarh ta sameshi su ka rakata.

♠♣♠♣♠♣♠♣♣

“haba laatifa mi yasa zaki man haka,kin tada man hankali sosai”mom maimunatu ta faɗa wacce a gidan su ka sameta tunda taga text ɗin da mom ta tura mata kancewa laatifa na nan ta wanko ƙafa ta zo.
“kiyi haƙuri mom ba ni da wanni zaɓin ne bayan nayi nesa da ku, bazan juri ganin tsanar da mahaifina yayi man ba”
“amma ai Laatifa sai ki duba halin da ni zan shiga idan babu ke”
“yanzu kiyi haƙuri maimunatu tunda har Allah ya sa su ka yi shawarar cewa ta zo nan ta kwana,kiyi haƙuri ba inda Laatifa zata tafi ta barki” mom ta faɗa
“hakane mom, ba tayi shawara da kowa ba ne shiyyasa amma da ba zamu bari har Sam yayi mata booking flight ba” kainart ta faɗa tana sake kwantar ma mom maimunatu da hankali
“yanzu ya jikin balqis ɗin naji barrister yace bata jin daɗi” mom ta faɗa
“wacece kuma Balqis,ni ban sani ba,na bar masa gidansa da yarsa tun jiyan”
gaba ɗaya su ka kalleta jin abunda tace “amma munarh saboda me,bai kamata ace kin bar gidan saboda haka ba” mom ta faɗa cike da nuna rashin jin daɗinta akan abun
“zulaihart ba za ki gane ba,Hashim ya wuce inda ki ke tunani shiyyasa kawai na yanke shawarar rabuwa da shi”
“kul karki faɗi haka dan Allah,ko dan saboda ƴaƴanki ai kya zauna,duba fa ki ga shekarunki,dan
End Ads