x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 446

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
brisster ta fito tana faɗin “kar ku barta ta wuce”


umarnin mom su ka bi, duk yanda nainarh ta so shiga cikin court room ɗin hanata security su kayi ƙarshe data gaji zubewa tayi ƙasa tana fashewa da wani matsanancin kuka,kamata mom tayi ta miƙar da ita tana lallashinta su ka nufi mota, itama daurewa kawai take yumanh da yake saurin kuka ne gareta har ta fara matse ƙwalla abun tausayi, motar da su ka zo ita da nainarh ta shiga nainarh kuma a tare su ka shiga da brisster, kuka take kamar ranta zai fita tun brisster na daurewa har itama ta kaida zubar da ƙwalla, a tamanin security guard ɗin su ka shiga motocin su, da gudun gaske su ka fice daga court ɗin.



tun daga farkon shigowa anguwar zaka tabbatar da anguwa ce ta manyan mutane masu faɗa aji a cikin ƙasa,manyan gine gine ne ta ko ina,tun daga nesa ƙarar jiniyar motocin su ka cika anguwar,da wani irin matsiyacin gudu su ka shigo anguwar, miƙe titin su kayi shantal sai da su ka kusa kai ƙarshen shi tukun suka karya kwana,tun daga farkon street ɗin da su ka shigo check point ne na sojoji,kowanen su ƙatuwar bindigace a hannunshi yayin da wasu ke soke a ƙugunansu, tun kafin motocin su ƙaraso sojojin dake zaune bakin ɗan gate ɗin da su ke sawa su ka buɗe masu, suna isowa babu jira suka wuce,tafiyar kusan minti goma sha biyar su kayi a ƙalla sun wuce check point na sojoji da ƴan sanda kusan guda goma kafin su ka kawo bakin wani ƙatafaran gate,ba sojojin dake gadin gate ɗin ba shi kanshi gate ɗin abun kallo ne, wani irin zungureren gate ne ƙaton gaske.


ga wasu irin manya manyan sojoji dake gadin shi, kwata kwata babu ɗigon imani a fuskar su,sojojin dake zaune saman bench ne suka miƙe da sauri lokacin da motocin su ka ƙaraso bakin gate ɗin,wani mahaukacin horn akayi da motar dake gaba da sauri wani soja ya danna wani abu dake hannunshi mai kama da remote nan take gate ɗin ya shiga zugewa zuwa gefe ɗaya,da gudun gaske suka danna kan hancin motocin zuwa ciki, masha Allah na furta a yayin da nayi arɓa da ƙaton Castle ɗin da su ka shigo,gidajene a cikin shi na alfarma hagu da dama aƙalla za su kai kimanin guda hamsin kusan a jere suke sai dai akwai tazara mai ɗan yawa a tsakanin ko wane gida, security guard ne ke yawo a cikin Castle ɗin ta ko ina,babu abun da babu a ciki kama daga clinic ne sport center, garden babu abun da babu a ciki, duk wani abu na more rayuwa a kwaishi a cikin estate ɗin.


a ƙalla sunyi tafiyar kusan minti biyar kafin su ka kawo bakin wani ƙaton luxury Villa wanda yafi ko wane gida dake cikin estate ɗin girma haɗuwa da tsaruwa, yana yin shi ma da ban yake da gidajen dake ciki shi ba'a jere yake da sauran gidajen ba yana a tsakiyar su yana fuskantar gate ɗin estate ɗin, water falls ne masu matuƙar kyau da ban shawa'a a bakin villa ɗin da a ƙalla ya kai hawa biyar, parking motocin su kayi...
_*Episode 5_6*_



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘



___________________________



A zaune take saman royal sofa mai mazaunin mutum uku dake a katafaren main parlorn dake villa ɗin,faɗa maku tsaruwa da haɗuwar parlorn ɓata lokaci ne,royal sofas ne a cikin shi set uku, komai na cikin parlorn white and golding color ne,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke tashi a cikin parlorn haɗe da sanyi AC,parlorn iya haɗuwa ya haɗu.



duguwar rigar lace ce a jikinta ɗinkin bubu,wuyanta yasha adon sarƙar gold hakama hannuwanta da ƴan yatsunta da suka sha ƙunshin jan lalle sunsha zobunan gold masu tsadar gaske, fara ce mata ƴar duma duma ba laifi kyakyawa ce,gashin attachment ne a kanta ya zubo har gadon bayanta,wani daddaɗan ƙamshine ke fita daga jikinta wanda ya haɗe da na fresheners ɗin dake parlorn ya bada wani ni'imtaccen sanyin ƙamshi.




tsadaddiyar wayarta ƙirar company Samsung ce kare a kunenta da alama waya take,cikin maganarta ta ƙasaita da isa take faɗin

“nayi matuƙar jin daɗin wannan daddaɗan labarin daga gareka”

bana iya jin mi na cikin wayar ke faɗa, murmushi ta saki tana cigaba da faɗin

“kar ka damu in dai nice zaka samu harda gyara ma, fatana dai sirrin mu ya cigaba da ɓoyiwa”

jin jina kai tayi har ta buɗe baki za tayi magana ƙarar dirar motocin su ya katse ta, da sauri ta miƙe daga saman sofa ta nufi bakin window cikin taƙun izza da ƙasaita, yaye curtains ɗin dake jikin window tayi,a hankali ta sauke idanunta a compound ɗin gidan,kusan a tare aka buɗe motacin dake tsakiyya, brisster zulaihat ce ta fito ɗayan ɓangaren kuma nainarh ce ta fito dafe da kai yayin da yumnah ta fito daga bayan motar dake bayan ta su,daga ganin yanayin fuskarta ba ƙaramin ku ka tasha ba.


main entrance ɗin gidan su ka nufo wannan security guard ɗin ce ta shiga gaban su yayin da mazan su ka rufa masu baya har bakin entrance ɗin villa ɗin,wani ɗan card security guard ɗin ta ciro daga aljihun wandonta ta zura a jikin wata ƴar na'ura dake jikin ƙofar , cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar ta shiga zugewa,zare card ɗin tayi, kama Nainarh mom tayi, ciki su ka kunna kai ban da security guard ɗin maza, juyawa su kayi su ka koma in da su ke zama.




Taɓe baki matar tayi tana sakin curtain ɗin ta juya zuwa cikin parlorn, ya mutse fuska tayi

“sorry kaji ni shiru, dangin yahudawan ce ta dawo, matar nan akwai ɗan banzan taurin kan tsiya,babu abun da ta rasa a rayuwa amma saboda tsabar zubar ma da kai aji ina ita ina aikin lawyer dukiya mulki babu wanda Allah bai bata ba, daga gidan mijin har gidan iyaye da ƴaƴa amma ta zaɓi wannan aikin wahalar”

jinjina kai tayi can ta kwashe da dariya tana faɗin

“no ba haka nake nufi ba, kaima ai kafi ƙarfin shi kawai ra'ayi ne irin naku kai da ita”


dariya ta sake saki tana faɗin “ok bye bye, take care of ur self for me sai na sake jinka” tana gama faɗa ta janye wayar daga kunnenta, mazauninta ta koma ta zauna tana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani jijjiga ƙafarta dake manne da chain na gold, ƙafar sai sheƙin ƙunshin jan lalle take.



tana a nan zaune su ka shigo parlorn bakin su ɗauke da sallama, daga yanyin da su kayi sallamar zaka tabbatar da rashin natsuwar da su ke a ciki, yumnah har time ɗin kuka take,miƙewa matar tayi tana nufar su fuskarta ɗauke da wani shu'umin murmushi, tana ƙarasowa gabansu tace

“Ashe haka shari'a ta kasan ce?” banza mom tayi da ita kamar bada ita take ba

“dama duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba to tabbas tashi ko zafi ba za tayi ba,to Allah dai ya kyauta na gaba”

ta faɗa tana sakin murmushi,wucewa mom tayi ba tare da ta tanka mata ba ta nufi elevator,bin bayan ta su yumnah su kayi.


dariya matar ta saki tana faɗin
“ita ƙarya dama ai fure take bata ƴaƴa,salihan bayi kullum a cikin nasara suke, tsinanne kuwa baya taɓa nasara akan masu daraja”

mom na jinta amma tayi kamar bata san tana yi ba, wasu madannai ta dannan a jikin elevator, buɗewa ƙofar tayi su ka shige ciki,wata ƴar iskar dariya mata ta sake saki

“Allah ya la'anci yahudawa da nasarawa, duk wanda ya kasance cikin wa ƴannan da Allah ya la'anta yayi asara, Allah mungode maka da kayo mu cikin jinsi mafi daraja da ɗaukaka kayo mu a muslmai ba sabon tuba ba” dariya ta saki tana bin su mom da kallo har suka yi sama.


juyawa tayi da nufin komawa mazauninta,wata kyakyawar budurwace tsaye a bayanta fara ce sai dai ba irin sosai ɗinnan ba,gown ce a jikinta white color ta ɗan wuce gwiwarta yayinda kanta ke sanye da hular saƙa baƙa,manya idanunta farare ƙar ta zubama matar, tsuke fuskarta matar tayi tana wani yamutse fuska tace “miye ki ka wani tsare ni da idanu uwata?” girgiza kai tayi cikin ƙunar rai da takaici tace


“MAMY gaskiya abun da ki ke baki kyautawa, miyasa kullum ki ke son zubarma kanki da mutunci ne?, yanzu dan Allah abun da ki ka yima mom kin kyauta?, gaskiya mamy ki dai na wannan ba hali bane mai kyau,kina jawo ma kanki abun kunya damu kan mu”



“ehyye!,sannu uwata, nace sannu uwata faɗa za kiyi man?” ta faɗa kamar zata rufeta da duka

“mamy ba faɗa zanyi maki ba, ina faɗa maki gaskiya ne a matsayina na ƴar ki, hakan bai dace ba”

“to bana so” mamy ta faɗa

“mamy dole na faɗa maki gaskiya,idan har DADY ya san baki daina wannan ɗabiun ba bazai taɓa raga maki ba kin dai san halin shi, a kullum mom tana son ku zauna lafiya amma ke baki son haka, kullum burinki ki tada fitina, kuma mamy da ki ke mata gori kema fa ba rawa ki kayi Allah ya hallice ki muslmar ba sai kiga tafiki dacewa ita data shiga muslincin daga baya sama dake da aka haifa a cikin s...”

bata ƙarasa ba mamy ta daka mata tsawa tana faɗin “FA'IZA! ni ki ke faɗama wannan kalaman dan uwarki?”

“kiyi haƙuri mamy gaskiya ce”
riƙe haɓa tayi “ah gaba gaba duka zaki fara kaiman idan banyi wasa ba”

“Allah ya tsare ni da kai maki duka mamy, amma ki sani wallahi sai na sanar da DADY baki dai na cin mutuncin mom ba, kuma ma ai ya hanaki zama main parlor,kin dai san sauran idan har yazo ya sameki”

tana faɗar haka ta nufi elevator da su mom su ka hau da sauri dan ta san zamanta a wurin bazai haifar da ɗa mai ido ba, madannan dake jiki ta danna.




“ina zaki uwar iyayi?” mamy ta faɗa tana ɗan ɗaga murya
“zanje na lallashi mom ne”
baki mamy ta saki har fa'iza ta ɓace ma ganinta, jinjina kai tayi tana faɗin

“zan kama ki ne dan ubanki, sai naji uban dake zugaki kina faɗa man magana san ranki” ta faɗa tana nufar elevator dake ɗayan ɓangaren parlorn ta shiga, dan ta san muddin dady ya shigo ya sameta a main parlorn ranta idan yayi dubu to sai ya ɓaci.


ƙofar elevator ne ya buɗe, zuro ƙafarta tayi ta nufi wani ɗan corridor,wata ƙofa ta shiga,wani haɗaɗen parlor ne ta shigo,ya fi na ƙasan da su ka baro kyau da tsaruwa, komai na cikin shi ya kasance gloding color ne,set ɗin sofa biyu a cikin shi.


Wata ƙofa ta nufa wacce nake kyautata zaton kitchen ne,tura ƙofar tayi ta shiga makeken kitchen ne gari guda babu wani da babu a ciki,ma'aikata ne su shidda gaba ɗayan su mata ne, kowaccen su na sanye da uniform ɗinta riga da wando, rigar fara ce yayin da wandon ya kasance baƙi, kowannen su aikin gaban shi yake, bakinta ɗauke da sallama ta shiga, gaba ɗaya su ka ɗago suna kallonta, amsa mata sallamar su kayi suna ɗan rissinawa su ka gaishe ta, cikin kulawa ta amsa masu tana ƙarasawa cikin kitchen ɗin, ɗaya daga cikin su ce tace

“Aunty Fa'iza mi ki ke buƙata, ai da kin kira waya ba sai kin zo da kanki ba?”


dish rag ta nufa tana faɗin “karki damu ISHRAT zan ɗauka da kaina, kawai dai ina so ku haɗa ma su mom lafiyayyan abinci mai rai da lafiya”

“in sha Allah yanzu za'a kammla” jinjina kai tayi tana ɗaukar plate mai ɗan girma ta nufi fridge,kayan ci da sha ne shaƙe a cikin shi, duk wannan kayan ƙwalam da maƙulashe dake ciki ruwa da lemu kawai ta ɗauka ta ɗaura saman plate ɗin,ƙofar fita ta nufa ɗan dakatawa tayi.
“kina buƙatar wani abun ne?” ishrat ta faɗa
“A'a, wai yaushe ummah za ta dawo ne?”
“tace man yau ko gobe amma ba tabbas” ishrat ɗin ta faɗa, jinjina kai fa'iza tayi tana ficewa daga kitchen ɗin.



parlorn data shigo ta koma wata ƙofa ta nufa nan ma wani madaidaicin parlor ne, anan ta samu yumnah da nainarh,nainarh har lokacin kuka take yumnah kuwa ta dafe kanta da hannunta ɗaya yayin da idanunta ke a lumshe hawaye na fita,wannan security na zaune gefen nainarh tana lallashinta
“Assalamu Alaikum” ta faɗa tana ƙarasawa cikin parlorn,
“good morning ma” security guard ɗin ta faɗa
“morning”fa'iza ta faɗa tana nufar in da suke ,trayn dake hannunta ta ajiye saman table, zama tayi kusa da nainarh, dafa ƙafaɗarta tayi


“ba kuka ya kamata kiyi ba Nainarh, Adu'a ya kamata kiyi in sha Allah komai yayi farko zaiyi ƙarshe, in sha Allah babu abun da zai faru da momyn ki,zata dawo gareki in sha Allah”

lallashinta fa'iza ta shigayi tana faɗa mata kalamai masu daɗi, shiru nainarh tayi tana sauke ajiyar zuciya, kallon yumnah fa'iza tayi
“Autar dady da mom kukan ya isa haka sai kisa zuciyarta ta karaya, ki daina kinji” jin jina mata kai kawai yumnah tayi
“ku shiga ɗaki sai ku kwanata ku huta kunji, ga breakfast can nasa su ishrat su haɗa maku” da to su ka amsa mata, suna tashi itama
miƙewa tayi tana faɗin “mom na ciki ne?” da eh yumnah ta bata amsa.



trayn ta ɗauka,ƙofar dake kallon dama ta nufa, a hankali ta tura ƙofar bakinta ɗauke da sallama,masha Allah na furta a yayin da nayi arba da katafaren bedroom ɗin data shigo,expensive furniture's ne a cikin shi na alfarma,royal bed ɗin dake ciki kawai abun kallo ne,yasha blanket da bedsheet masu tsadar gaske, bed ɗin a cike yake da pillows, bedroom ɗin ba wani cike yake da kaya ba, bed ne kawai sai nightstand dake ɗauke da bedside lamps sai dressing mirror,sai sofas guda biyu dake can bakin sliding window sai ɗan round table dake tsakiyar su.



Cikin ɗakin ta ƙarasa yayin da take yin sallama, a tsaye ta hango brisster zulaihat bakin window hannunta riƙe da curtains,girgiza kai fa'iza tayi cike da tausayawa ta nufi in da brisster take, sallama ta sake yi dan a tunaninta bata jita ba,kafe garden ɗin dake bayan villa ɗin tayi da ido yayin da hawaye ke sauka daga idanunta, a zahiri kallon shuke shuke dake cikin garden ɗin masu ɗaukar hankali take amma a zahirin gaskiya hankalinta kwata kwata ba'a kan su yake ba,babban tashin hankalin ta a wane hali yanzu aminiyarta take ciki sannan ya rayuwar nainarh zata kasance ba tare da mahaifiyarta ba, da sauri ta juyo jin an dafa kafaɗar ta.



kallon fa'iza dake tsaye a bayanta tayi
“Fa'iza yaushe ki ka shigo?”

“mom yanzu na shigo ina ta ƙwala sallama ba kijini ba, mom dan Allah ki daina sa damuwa a ranki kar wani abun ya same ki, in sha Allah momy zata fito”

ajiyar zuciya ta sauke,hannu fa'iza tasa ta shiga guge mata hawayen dake zuba daga idonta tana sake bata haƙuri, jan hannunta tayi su ka nufi sofas ɗin dake wurin.


Zama su kayi suna fuskantar juna
“mom in sha Allah zata fito, mom kinfi kowa sanin yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai ba shike nuna gaskiya baza tayi halinta ba,ba kuma shi ke nuna ba zata iya fitowa wata rana ba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki”

“Nagode fa'iza” shine kawai abun da brisster tace
“mom kinfi ƙarfin haka a waje na fatana dai ki rage damuwar a zuciyar ki, sannan nayi maki Alƙawari mom zan tayaki da Adu'a Allah ya bayyanar da gaskiya”


“Ameen fa'iza”
“sannan mom ina mai baki haƙuri akan abun da mamy tayi maki, bata kyauta ba dan Allah kiyi haƙuri”

murmushi brisster ta saki yarinyar akwai shiga rai ta na matuƙar burgeta

“fa'iza kenan idan da sabo ai yaci ace na saba da hakin mamyn ku, karki damu abun da tayi man kwata kwata bai ɓata man rai ba”

“shikenan mom amma duk da haka ina mai baki haƙuri a madadinta” murmushi brisster ta saki


trayn data shigo ta nufa, ruwa ta tsiyaya mata a cup
“mom gashi kisha, na sa chefs su haɗa maku breakfast dan na san haka ku ka fita bakuci komai ba”

”nagode fa'iza Allah ya biyaki da mafificin Alkairi”
“mom dan Allah ki daina gode man”
“ya zama dole ne fa'iza”
“ni dai dan Allah ki daina gode man, nifa ƴarki ce kuma mom kin san cewa babu godiya tsakanin iyaye da ƴaƴansu” murmushi brisster ta sake saki tana zubama fai'za ido, fa'iza badai iya tsara kalamai masu daɗi ba.


Turo ƙofar bedroom ɗin a kayi, da sauri su ka kai duban su ga ƙofar
a tsaye ya ke ya harɗe hannuwan shi a ƙirji,Army green ɗin shirt ce a jikinshi haɗe da Army trouser wanda ya tsaya mashi iya gwiwa , babban mutum ne da a ƙalla zai kai kimanin shekaru 56 zuwa da 8 a duniya, dogo ne sosai yana da jiki, ƙaƙƙarfa ne na gaske kamar ba dattijo ba, a ido idan ka kalleshi baza kace shi ke da waɗannan shekarun ba,fari ne kyakyawa kallo ɗaya za kayi mashi ka hango kamaninshi da fa'iza da yumnah,da gudu fa'iza ta nufe shi, faɗawa tayi jikinshi
“good morning dady”

murmushi ya saki yana jan kumatunta “har yanzu baki san kin girma ba ko fa'iza?, kina abu sai kace yumnah” ɓata fuska tayi kamar ƙaramar yarinya “dady nice ma yumnah” zuba masu ido brisster tayi tana kallon su baƙaramin birgeta suka yi ba, raba jikin su yayi yana faɗin
“ƙwarai ma kuwa”

cikin ɗakin ya ƙarasa, ƙofar fita fa'iza ta nufa tana faɗin
“mom sai na dawo, dady ka barta ta kwanta ta huta ta gaji” ta faɗa tana jan handle ɗin ƙofa
“na lura fa'iza kin raina ni da yawa” dariya tayi tana jan ƙofar ta fice, murmushi kawai mom tayi tana girgiza kai.


bakin bed dady ya nufa,zama yayi yana zuba ma barrister ido, ɓata fuska tayi kamar zata fashe da kuka ta nufeshi, tana ƙarasowa gabanshi faɗawa tayi jikinshi tayi hugging ɗin shi,hannu biyu yasa ya zagaye bayanta,shafa doguwar sumar kanta ya shiga yi
“Barrister lafiya?”
End Ads