x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 42 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 123001 words
  • 126000 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 476

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
parking, securitys ɗin shi ne su ka shiga fitowa ɗaya bayan ɗaya,kafin su ka buɗe back seat ɗin motar ya Naeem ɗin.
fitowa ya Naeem ɗin yayi, zagayawa yayi da kanshi ya buɗe ɗayan side ɗin motan,hannunshi ya miƙa mata ta kama ta fito,yumnah na daga can tsaye tana kallon su,da gudu ta nufo parking space ɗin ganin Nainarh tare da ya Naeem wacce kallo ɗaya zaka mata ka fahimci bata hayyacinta,jikita sai wani rawa yake kamar wacce sanyi ke kaɗawa.
“second father daga ina ku ke haka,Nainarh lafiya ki ke?” yumnah ta faɗa lokacin data ƙaraso in da su ke
“bata jin daɗi ne,matsa” shine kawai abunda ya Naeem ɗin yace mata yana jan hannun Nainarh su ka nufi cikin gidan,bin bayansu yumnah tayi.

*Abunda ya faru lokacin da wannan mutanen su ka rufe motar su Nainarh.*

kamar yaƙi haka su ka shiga sakar ma motar bullet,anguwar ba kowa kamar anyi shara,sauƙin su ɗaya da motar ta kasance bulletproof ce.
tsoro da ƙarar harbi ne yasa Nainarh suma,tunda take bata taɓa tsintar kanta a tashin hankali irin wannan ba,ko lokacin da aka kashe dadynta bata tsorata irin na yau ba.
zufa ce ta ko ina ta shiga keto ma driver,tsabar karfin hali yana a duƙe yake ci gaba da dialing number CM,still tana ringing amma baiyi picking ba, bai gajiya ba haka ya cigaba da aika mashi kira,shi kan shi bai san iya adadin kiran da yayi mishi ba.
gajiya suka yi da harbin motar ganin dai babu alamun glass din zai fashe,gashi so suke su gama abun da ya kawo su ba tare da wani ya gansu ba,ganin dai idan ba wani abun suka yi ba har wani ya zo ya same su a wurin ne yasa majiya karfin da ke cikinsu suka nufi wani katon dutse da ke bakin hanya,kama kama suka yi suka ɗauko dutsen,gadan gadan suka nufi glass din gaban motar za su buga mishi dutsen,sai dai kash Allah maji roƙwan bawansa kafin su aikata hakan karar motar sojoji haɗe da harbi ya cika kunnensu,ba shiri suka yarda dutsen a 360 suka nufi motocin su dake wurin,ko kafin motocin sojojin su ƙaraso sun shige motocin su,key su ka yi ma motocin a 80 suka bar street ɗin,lokacin da su ya Naeem suka karaso sai dai suka hangi motocin su tuni sunyi nisa,mota biyu ta sojojin ta bi bayan motocin su,parking ɗin motocin su suka yi, da sauri ya Naeem ya fito ya nufi motar,back seat ɗin motar ya buɗe, a kasan motar ya ga Nainarh babu alamun numfashi a tare da ita, jijjiga ta ya shiga yana kiran sunanta, wata irin wawiyar ajiyar zuciya driver ya saki jin muryan ya Naeem da sauri ya buɗe driver seat ya fito,jikinshi sharkaf da zufa,hannu biyu ya Naeem yasa ya ciro Nainarh,back seat ɗin motar shi ya nufa da ita,usman ne ya ɗauko mashi ruwa daga cikin mota ya miƙa mashi.
A hannu ya zuba ruwan tukun ya shafa mata a fuska,dogon numfashi taja haɗi da zabura zata fita daga motar,da sauri ya riƙota yana kiran sunanta,saurin kallon fuskarshi tayi “lafiya, mi ya faru,mi yasa ki ka fito daga gida??” da ido kawai ta bishi amma ta kasa amsa mashi tambayoyin da yake mata
“ba nace duk inda zaki ki dunga sanar dani ba,mi yasa ki ka fita ba tare da kin faɗa man ba?” ƙalla ba tace mashi ba,banda bin shi da ido ba bu abunda take,ƙyaleta yayi ganin har lokacin bata dawo hayyacinta ba, drivern ya tambaya daga ina suke da kuma abunda ya faru,kaf ya kwashe komai ya faɗa masa.
jinjina kai kawai ya Naeem ɗin yayi ya shiga back seat ɗin kusa da ita,ganin haka ne yasa kowa shiga motar shi su ka bar wurin,motar da su ka zo driver ya shiga.
ta yarda akai ya Naeem ta san suna wurin,bayan kiran da driver yake mashi dama tun ranar daya kira Nainarh gidan shi yasa mata bididdiƙi a wayarta wanda ke sanar da shi location ɗin da take duk wani motsinta yana sane da shi.
Direct bedroom ɗin su ya nufa da ita,tura ƙofar yayi,ganin su Ishrat na gyaran ɗakin ne yasa shi juyawa ya nufi wanda ke kusa da nasu,har bakin bed ɗin ɗakin ya nufa da ita “ki kwanta ki huta kin ji” ya faɗa,ba tayi mashi musu ba ta cire takalman dake ƙafarta ta hau gadon,ita kanta zata so tayi baccin ko kunnuwanta za su dai jiyo mata ƙarar tashin hankali da tashiga,ficewa yayi daga ɗakin yana faɗin “ina zuwa” zama yumnah tayi kusa da ita “sister Nainarh wai mike damunki,daga ina ku ke haka?” ƙala Nainarh ba tace mata ba sai ma rufe idonta da tayi, zuba mata ido yumnah tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.
Ya Naeem ne ya dawo hannunshi riƙe da magani da robar ruwa,bakin bed ɗin ya ƙaraso kiran sunanta yayi, a hankali ta buɗe idonta “tashi ki sha wannan maganin sai ki kwanta” tashi tayi kamar yanda yace,amsar maganin tayi da ruwan,miƙa mashi robar tayi bayan ta sha
“to koma ki kwanta,Auta tashi za ki yi ki bata wuri tana buƙatar hutu” to yumnah tace
a tare su ka fice daga ɗakin, kasa haƙuri tayi har sai da ta sake tambayarshi mi ya samu Nainarh daga ina su ke,duk tabi ta damu da halin da Nainarh take ciki
“ki kwantar hankalinki babu abunda ya sameta,bata jin daɗi ne amma in sha Allah data farka zata dawo dai dai”
“Allah ya sa haka” kawai tace ba wai dan ta yarda da bakomai ɗin da yace ba, bedroom ɗin su ta nufa dan ta watsa ruwa.
Nainarh da shan maganinta ko two minutes ba ta yi ba bacci yayi awan gaba da ita.
Dady lokacin ɗaya shigo gidan ba ƙaramin tashi hankalinshi yayi ba da yayi arba da motar da su Nainarh su ka fita.
A main parlor yaci karo da ya Naeem,hankali a tashe yake tambayarshi lafiya dan yaga yaranshi a kusa da motar,bai ɓoye mashi komai ba ya sanar dashi abunda ya faru
“innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,amma su waye su,miye haɗin su da ita da za su nemi kasheta⁉️”
“shi ne abunda ke ɗaure man kai dady,amma in sha Allah asirinsu zai to nu,nasa a bi bayan su”
“Allah ya kyauta gaba,yanzu a wane hali Nainarh take ciki?”
“lafiya lau take,kawai dai ta tsorata ne sosai,amma na bata maganin bacci in sha Allah data farka zata dawo dai dai”
“Allah ya ki ya ye gaba” da Ameen ya Naeem ɗin ya amsa.
sallama su ka yi dady ya nufi cikin gidan shi kuma ya fice.
Uncle Ahmad lokacin da yake gidan Abbah,rufe shi da faɗa Abbah yayi sosai kan abunda zaabith ɗin ya aikata dan yana ganin sakacin shi ya fi yawa a ciki,ba komai ya ƙara ɓata ran Abbah ba sai yanda mutanen gari ke faɗan munanan kalamai akan uncle Ahmad ɗin musamman abokan hamayyarsa na siyasa,wa su ma wanda su ke da kusanci da Abbah harda kiran shi su ka yi a waya,dake sharrinshi ne babu in da abun bai zagaya ba lungu da saƙo,mutane sun fi saurin yaɗa sharrin mutum sama da Alkairin shi,da ka shiga social media maganar da ake kenan,wasu harda ƙara ma zancen citta wasu ma maganganun da su ke faɗa ba su da alaƙa da al'amarin wa'iyazubullah
ya ƴan uwa mu zamanto masu ƴada Alkairi ba sharri ba.
faɗa sosai Abbah yake mashi yama ƙi bashi Accesse ɗin da zai ce komai,ban da haƙuri babu abunda ya ke bashi har ya gama mashi faɗa ya koma yi mashi nasiha,sai da Abban ya sauko tukun uncle Ahmad ɗin ya sake baki haƙuri yana sanar da shi Maganar Auren Noor da Irfan.
Sosai Abbah ya yi farin ciki da jin mom ta haƙura “gaskiya naji daɗin jin haka,Allah ya sakama Zulaihart da Alkairi,su kuma Allah yasa ma Auren na su albarka,amma mi yasa ku ke son rabashi da na Waseef?,kamar zaifi ayi shi lokaci ɗaya??”
“ba komai Abbah,kawai saboda halin da Nurjahan ɗin take ciki ne,kamar ɗaura Auren na su zai taimaka ma lafiyarta tunda fasa Auren shi ne sanadiyyar ciwan nata zuwa bayan sallah sai ayi shagalin bikin tare da na Waseef ɗin”
“hakan ma yayi Allah ya bata lafiya in sha Allah zuwa gobe bayan sallar zuhur sai a ɗaura Auren,zan sanar da Shaikh Ibrahim da duk wani wanda ya kamata ya sani,Allah ya ba su zaman lafiya”
“Ameen Abbah,ni zan koma gida”
“to shikenan ba damuwa” har parking space Abbah ya rakashi,sai da yaga tashin motocin shi tukun ya koma ciki cike da farin cikin Auren Irfan da Noor da za'ayi, murmushi ya saki yana faɗin “Zulaihart Allah ya faranta maki kamar yanda ki ke farantama bayin sa Ameen.
Mom fatilah lokacin da su ka koma gida taruwa su ka yi ita da su mamy su ka yima masu aikinta shegen duka kan dole sai sun faɗa masu ubanda yaba Noor guba,Banda ku ka da faɗin ba su san komai babu abunda masu aikin suke,amma hakan baisa sun ƙyale su ba, ƙarshe da su ka gaji su ka kuma fahimci baza su taɓa faɗa masu gaskiya ba,da securitys ɗin gidan mom fatilah ta haɗa su,ai kuwa ba ƙaramar azaba su ka sha a hannunsu ba,ta in da Allah ya taimake su mai gadin gidan ne ya kira uncle mutallab ya sanar da shi abunda ke faruwa hakan ne yasa ya kira securitys ɗin yace su ƙyale su,hakan ba ƙaramin ɓata ran mom fatilah da su mamy yayi ba.
Kainart sosai ƴan uwa da abokan arziƙi ke zuwa gaishe da ita duk da har time ɗin bata farka ba, da yawan su sai sun zo gaishe da ita su ke sanin Noor ma bata da lafiya,wasun su sun samu ganinta wasu kuma sai dai su ka tafi akan za su dawo idan an fito da ita daga emergency ward,mama Ameenah ko da ta zo iyakarta wurin Noor amma bata shiga ta duba halin da kainart take ciki ba, hakan kuwa ba ƙaramin ɓata ran Abbah yayi ba da yake a tare su ka zo amma sai tayi kamar bata fahimci ranshi ya ɓaci da abunda tayi ba,tun ba yau ba basa ga maciji ita da uncle mustapha tun yana ƙaramin sa.
Nainarh sai bayan sallar isha ta tashi yumnah har ta gaji da zuwa duba ko ta tashi,gaba ɗaya ta damu da halin da take ciki, Alhmdllh ta tashi taji sauƙin abunda ke damunta ta dalilin baccin da ta yi, bedroom ɗin su ta koma, yumnah tasha ruwan mamaki ganin yanda Nainarh gaba ɗaya ta sauya mata,wata irin tsanarta ta hango a cikin idanun Nainarh,roƙon Nainarh ta shiga yi da bata haƙuri dan duk a tunaninta saboda ta tafi ta barta take wannan fushin sai data ga abun ya wuce tunaninta tukun ta fara zargin kanta.
Uncle mutallab tun bayan tafiyar su dady ya kira waseef yaji ko su na tare da irfan,amma sai waseef ɗin ke sanar dashi shima rabonshi da irfan ɗin tun safe da su ka zo office,har office ɗin shi yaje amma baya nan kuma ya kira wayarsa bai same shi ba,mamaki ne ya kama uncle mutallab to ina Irfan ɗin ya shiga da har waseef bai sani ba.
sanar dashi halin da Noor ɗin take ciki yayi da kiran sunan Irfan ɗin da take
“dan Allah waseef idan ka ganshi kace na ce ya zo,ina son ganinshi” sosai hankalin waseef ya tashi jin halin da Noor ɗin take ciki,wani mugun tausayin su ne daga ita har Irfan ɗin ya rufe shi “in sha Allah uncle zan sanar da shi,Allah ya bata lafiya sai mun shigo”
“Ameen waseef,sai na ganku” da to waseef ɗin ya amsa yana mashi sallama. 
Number Irfan ɗin ya shiga kira still a kashe take,ficewa yayi daga office ɗin shi direct office ɗin Irfan ɗin ya nufa,a rufe ya samu office alamar bai dawo office ɗin ba,parking lot ya nufa motarshi ya shiga direct estate ɗin su ya nufa ci ke da sa ran zai samu Irfan ɗin a can,sai dai ko da yaje bai same shi ba,babu inda bai duba shi ba har gidajen su da za su zauna idan sunyi Aure dake kusa da gidan uncle Ahmad sai da ya duba amma baya nan rabonshi ma da estate ɗin tun ranar friday.
duk yanda ya kai wurin neman Irfan sai dai ya haƙura har dare yayi sosai Irfan bai dawo gidan ba kuma har lokacin wayarshi bata ta fiya dan dole tasa ya haƙura,gida ya koma ya shirya ya nufi asibiti wurin Noor da kainart da itama bai samu zuwa ya dubata ba, uncle mutallab bai ji daɗin rashin samun Irfan da Waseef ɗin baiyi ba,ya jima a hospital ɗin kafin ya tafi,heart of Vegas ya koma neman Irfan ɗin duk da yaje ɗazu,still bai zo ba Muhsin kawai ya samu,bai wani jima ba ya nufi gida,gaba ɗaya tashin hankalin in da Irfan ya shiga ya dameshi duk da ya san Irfan bazai ɓata ba dole wani wurin ya tafi.
Irfan bai dawo gida ba sai washe gari around 12 PM,Waseef na bedroom ɗin su yayi shirin fita ya shigo,da mamaki Waseef ɗin ke kallon Irfan ɗin da kallo ɗaya zaka masa ka fahimci baya cikin natsuwar shi.
Daga yanayin yanda yake tafiya zai tabbatar maka da he's drunk,ko kallon Waseef dake kallonshi baiyi ba yayi jifa da key ɗin motarshi dake hannunshi ya nufi bathroom,girgiza kai kawai Waseef yayi yana zama gefen bed ɗin su,daga bedroom ɗin yana jin yanda Irfan ɗin ke kakarin amai yana fitar da wani irin nishi,kallon ƙofar toilet ɗin yayi cike da tausayin ɗan uwan nashi.
ya shafe tsawan 40 minutes bai fito ba,tashi Waseef yayi ya nufi bakin ƙofar toilet ɗin
ganin har lokacin bai fito ba ga wani irin nishin wahala da yake fitarwa,ɗan nocking ɗin ƙofar toilet ɗin yayi yana kiran sunan shi “Irfan lafiya ka ke,mi ke damunka ne??” ya faɗa,tsit yaji Irfan ɗin ya daina nishin da yake sai ƙarar ruwa da yaji,barin bakin ƙofar yayi ya koma cikin ɗakin,a bakin bed ɗin ya sake zama,bai jima da zama ba Irfan ɗin ya turo ƙofar ya fito sanye da bathrobe,bed ɗin ya nufo jiki ba ƙwari ya faɗa saman bed ɗin,dafe cikin shi yayi yana ɗan ya mutse fuska,matsowa Waseef yayi kusa da shi “Irfan lafiya ka ke,ina ka kwana ne,jiya kasan irin neman da nayi maka kuwa??”
Irfan ɗin na jin shi amma bai ce mashi ƙala ba shi kanshi bazai iya cewa ga halin da yake ciki ba
“magana nake Irfan kayi shiru,wannan rayuwar da ku ka ɗaukar ma kanku ba mai ɓullewa bace,ku musulmai ne dukan Musulmin ƙwarai an san shi da yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,a rayuwa ba komai muke so mu ke samu ba,tunda har kaga abun ya zo a haka to Allah ne bai ƙaddara akwai Aure a tsakanin ku ba,ya kamata ace kunyi imani da ƙaddarar data same ku kunyi haƙuri,amma wannan halin daka jefa kanka ba mafita ba ne,idan da mutuwace ta ɗauki ɗaya daga cikin ku fa,ya za kuyi,ko wani zai bi ɗan uwanshi ne tsabar so??” Waseef ɗin ya faɗan yana ɗan yi ƙwafa haɗin da kallon fuskar Irfan ɗin,idanunsa a lumshe su ke amma duk abunda Waseef ɗin yake faɗa yana jin shi
“dan Allah Irfan ka dawo cikin hankalinka dubi halin daka ka jefa kanka,kullum cikin ɗurama kanka abunda zai zame maka matsala ka ke,gaba ɗaya nema ka ke ka mayar da kanka mahaukaci,kuma hakan ya sauya ƙaddarar da Allah ya ƙaddaro maku ne?” ya faɗan yana kallon Irfan ɗin da har lokacin bai motsa ba,girgiza kai yayi yana cigaba da faɗin “hakan bai sauya komai ba,Noor na kwance gadon asibiti tayi poisoning kanta duk dan saboda an rabaku still hakan bai sauya ƙaddarar ku ba” tunda ya ambaci Noor tayi poisoning kanta Irfan yai zambur ya miƙe yana kallon Waseef ɗin da yayi magana,kallo ɗaya zaka ma fuskarshi ka san abun ya taɓashi
“dan Allah ku dawo cikin hankalin ku kusan cewa duk abunda Allah yayi akan bawansa mai kyau ne,kar kuje ku rabu da imanin ku a banza” girgiza kai kawai Irfan ɗin yayi yana nufar ƙofar fita saurin riƙo hannunshi Waseef yayi yana faɗin “ina zaka a haka?”
“hospital”shi ne kawai abunda yace mashi yana zame hannunshi dake cikin nashi,sake riƙo hannunshi Waseef ɗin yayi “a haka za kaje wurin ta?”
kallonshi Irfan ɗin yayi “dan Allah Waseef ka ƙyale ni”
“gaskiya bazan taɓa bari ka fita a haka ba,ko ba kaga halin da ka ke ciki ba ne?”
“please Waseef! dan Allah” Irfan ɗin ya faɗa a hankali daurewa kawai yake amma shi ka ɗai ya san ya yake ji,ga kuma halin da Noor take ciki
“ka bari ka fara dawowa normal tuku”
“please Waseef”
“shikenan naji amma ka wuce ka sa kaya tukun” kallon jikin shi yayi can kuma ya juya ya koma cikin ɗakin, clothset ɗin su ya nufa,Waseef na tsaye har ya kammala shiryawa ya fito,key ɗin motarshi daya jefar ya ɗauka ƙofar fita ya nufa bin bayan shi Waseef ɗin yayi.
A parking space su ka haɗu da su dady da alama masallaci za su shi da Alhj Ja'afar da PA ɗin sa,har drivern shi ya buɗe masu mota amma ganin su Irfan ɗin ne yasa su ka dakata,ƙarasowa su ka yi cike da girmamawa su ka shiga gaishe da su,da kulawa su ka amsa masu uncle Ahmad na tsaida idonshi akan Irfan “Irfan Ina ka shiga jiya aketa nema ka?” sadda kai ƙasa Irfan ɗin yayi yana faɗin “ina tare da Amjad ne dady”
“amma shi ne ka kashe wayarka aketa kira ba'a samun ka?” shiru Irfan ɗin yayi baice komai ba,gyaɗa kai kawai uncle Ahmad yayi “ina za ku haka?” Waseef ne yayi saurin cewa “masallaci daga can zamu wuce hospital wurin Noor ne,bai san bata da lafiya ba” ɗan kallon Irfan ɗin uncle Ahmad yayi tukun yace “ohk mu ma masallacin zamu tafi daga can zamu wuce hospital ɗin,ku shiga mu tafi” da to su ka amsa suna nufar ɗaya daga cikin motocin su dady,su ma motocin su suka shiga.
key driver's ɗin su ka yima motocin su ka fice tare da motocin securitys ɗin su wasu na gaba wasu na baya,direct masallacin da su ke sallah su ka nufa.
A can su ka samu Abbah da dady da su uncle Hashim
End Ads