Ɓangaren da jeweleries su ke su ka nufa,basu sha wata wahala ba wajen zaɓo mata ɗan kunne da sarƙa sai Agogo da chain ɗin ƙafa.
Turo ƙofar ɗakin a kayi aka shigo tun kafin ta ƙaraso ta san ko wacece ita ka ɗai ce a cikin ma'aikatan gidan ke da lasisin shigowa part ɗin ta ba tare da ta nemi izinin ba, su kansu na'urorin dake sarrafa part ɗin sun san da zamanta.
kyakkyawar matashiyar dattijiwa ce ta shigo,baturiya ce, sai dai duk da manyantar ta hakan bai nuna a fatarta ba,fatarta kamar ba ta tsohuwa ba, kyakkyawa ce ajin farko ,hancinta tsaye yake babu lanƙawasa bakinta ɗan dai dai, launin idonta sak irin na Nailar Acme white grey.
long sleeve shirt ce a jikinta tare da A_line skirt wanda ya wuce gwiwarta,sumar kanta dake da jefi jefi na furfura sai sheƙi take tana ɗaukar ido, simple make_up ne a fuskarta ba ƙaramin kyau yayi mata ba jikinta sai fitar da wani ni'imtaccen ƙamshi yake.
Aunty Sophia kenan ƴar ƙwalisar tsuhuwa ko budurwa bazata gwada mata iya ɗaukar wanka ba wasu abubuwan duk a wurinta masu Aikin Nailar ke koya,ta san ta kan fashion.
In da Nailar take ta ƙarasa fuskarta ɗauke da murmushi wanda yaba dimples ɗin ta damar lotsawa,ta cikin mirror Nailar ke kallonta, Murmushi itama ta sakar mata.
cikin girmamawa masu Aikin su ka shiga gaishe da Aunty Sophia,harara ta ɗan watsa masu da sauri su ka sadda kai saboda sanin laifin su na ƙin faɗa mata Nailar zata fita, hugging ɗin ta tayi ta baya.
“i miss U so much Aunty sopi,jiya shi ne kwata kwata baki neme ni ba ko?” Nailar ta faɗa a shagwaɓe kamar ba ita ba, murmushi Aunty Sophia tayi tana miƙewa tsaye haɗi da juyo da stool ɗin da Nailar ke zaune.
“my baby na shigo fa kina bacci,bana son na takuraki ne shiyyasa na fice”
ɓata fuska Nailar tayi “dama na san babu wanda zai kashe man ear phone sai ke”
“nayi laifi kenan?” taɓe baki Nailar tayi“ dan kin san baki laifi a wajena shiyyasa ki ke yanda ki ka ga dama”
ƴar dariya Aunty Sophia ta saki wacce ta bayyanar da kyawawan haƙoranta.
juya mata baya Nailar tayi tana turo baki,kallon masu Aikin tayi da ido tayi masu alamar su fice,kayan dake hannunsu su ka ajiye saman table su ka fice.
cikin ɗakin Aunty Sophia ta nufa, ɓangaren underwears ta nufa,bandeau style top ta ɗauko mata haɗe boyshorts masu matuƙar jan hankali white color.
dawowa tayi wurin Nailar,miƙa mata tayi “am sorry idan na ɓata ran Queen,ga wannan kisa sai na idasa shirya gimbiyar tawa da kaina” turo baki Nailar tayi
“ƴata fa yanzu budurwa ce dole ta koyi wasu abubuwan da kanta,ba sai masu aiki sunyi mata ba”
tashi Nailar tayi sai ɓata fuska take ta amshi kayan dake hannun Aunty Sophia, murmushi Aunty Sophia ta saki,cikin ɗakin ta nufa sai turo baki take.
saman ɗaya daga cikin stool ɗin Aunty Sophia ta zauna tana sakin murmushi ita ka ɗai ke kema Nailar haka a zauna lafiya,tana da matuƙar ƙima a idanun Nailar,a kwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin su, Nailar ta ɗauketa tamkar mahaifiyarta tun tana ƴar ƙaramarta Aunty Sophia ke kula da ita,Nanny ɗinta ce hakan yasa su ka shaƙu,wani lokacin har cewa masu Aikin gidan keyi suna kama.
Dawowa Nailar tayi in da Aunty Sophia take ta cire bathrobe ɗin pant da bra ɗin ne kawai a jikinta, a gaban Aunty Sophia tazo ta tsaya,da sauri Aunty Sophia tasa hannu ta rufe fuskanta hakan da tayi ba ƙaramin dariya yaba Nailar ba.
“baby ya kamata ki riƙa jin kunya ta fa, yanzu ke ko a jikinki ki tsaya haka a gabana”
“dan me zanji kunyarki,ni bana jin kunyar kowa”
“dama taya za kiji kunya bayan wannan tsinannun na maki wanka har yanzu” ta faɗa yayin da take zame hannunta daga saman idanunta
ƴar dariya Nailar ta saki “Aunty sopi wai har yanzu baki daina jin haushin Lara da Lolah ba”
“taya zan daina jin haushin su,wasu ƙatti da su kamar ƴan dambe kullum suna gane man jikin baby” ta faɗa tana tsuke fuska
tsawan shekaru abun na cimata tuwo a ƙwarya dan dai kawai bata da yanda za tayi,da tana iya hana Nailar wankan da aike mata da tuni ta hana hatta masu aikinta haushin yanda Nailar ta sakar masu komai na rayuwarta take ji ,ace comon sutura su za su cire su sa mata.
“zaki fara ƴan tunane tunanen naki ko,su fa basa da laifi,nice mai laifi sai dai idan ni zaki hukunta”
“zan hukuntaki ne mana idan har baki daina wannan san jikin banza ba”
“shikenan yanzu tunda kin korar mansu sai ki ƙarasa aikin na su”
dungure mata kai Aunty Sophia tayi tana ɗaukar rigar da zata sa,ɗan sosa in da ta dungureta tayi “ karfa garin wannan fushin naki ki ɓata man gyaran gashi na”
zura mata rigar Aunty Sophia tayi,ta zuge mata zip,kallon yanda rigar tayi mata tayi a mirror
“yanzu haka zaki je maza suyi ta kallon jikin ki”
“iya kar su kallon,kuma ma Ni da nake zaune a office ina ruwana da su”
“kafin ki shiga office ɗin maza nawa zasu kalle ki musamman wannan ƴan iskan security guard ɗin naki masu fuskar shaiɗanu”
“to yanzu wane kaya ki ke so na sa?”
Na jikinta ta nuna mata dariya Nailar ta saki “ kina so ajina ya zuba ko,ace na zama tsohuwa”
“zaki zama tsohuwar ne mara kunya” murmushi kawai Nailar ta saki,idan har kaji dariyar Nailar to tana tare da Aunty Sophia ko momyn ta,Aunty Sophia baturiya ce amma ɗabi'unta sun banbanta dana turawa.
sun ɗan ɗauki tsawan lokacin wajen shiryawa,ba ƙaramin kyau Nailar tayi ba kamar ka saceta ka guda,sosai rigar tabi shape ɗin jikinta,ƴar pose Aunty Sophia ta ɗauko mata tare da sunglasses mai shegen kyau pose ɗin taji adon stones multicolors sai ɗaukar ido take,wata ƴar locker Nailar ta nufa,ɗan duƙawa tayi saitin wata ƴar na'ura dake jikin locker ɗin,idanunta ta saita a jikin na'urar da alama Eye ID ne a jikin ƙofar,nan take ƙofar ta buɗe,ƙananan guns ne a ciki nau'i daban daban tare da bullet ɗin su,watama idan ka ganta zaka ɗauka lipstick ne,ɗaya daga cikin su ta ciro.
bullet ta ɗauka guda biyar ta zuba a ciki kafin ta ɗaga rigar dake jikinta,wani ɗan belt dake jikin boyshorts ɗin dake jikinta ta saka bindigar da alama anyi shi ne saboda haka.
maida locker tayi ta rufe,juyowa tayi tana kallon Aunty Sophia da tunda ta buɗe locker ta kauda kai,bata ma san ganin abunda ke ciki, murmushi Nailar ta saki tana ƙarasowa inda take.
A tare su ka fice daga ɗakin Aunty Sophia na faɗin ji take kamar kar Nailar ta fita Ita kuwa sai sakar mata murmushi take.
A parlor su ka samu masu aikinta su biyu na jiran su kowacce su ta ɗauki wankan suit black color,tunda su ka fito Aunty Sophia ke banka masu harara sai kace sune za fita da Nailar ba ita bace zata fita da su ba.
Elevator su ka shiga ta kai su a salin main parlor gidan wanda in ka shigo dashi zaka fara cin karo.
main entrance ɗin gidan su ka nufa,yanzu ma sai da ƙofar tayi scanning fuskar Nailar kafin su ka fice harda Aunty Sophia.
Harabar gidan ƙwanyar take da haske kamar da rana,motocin ne guda biyar a bakin ƙofar fitowa,huɗu baƙaƙe ne ƙirar HYUNDAI yayin da ɗayar ta kasance fara ƙirar Mercedes benz s class a tsakiyar su.
rissinawa security guard da masu aikin dake yawo jefi jefi su kayi suna gaishe da Nailar da Aunty Sophia,cikin kulawa Aunty Sophia ke amsa masu.
har gaban Mercedes benz ɗin Aunty Sophia ta raka Nailar,da kanta ta buɗe mata door ɗin ta shiga tana mata fatan dawowa lafiya,kissing hannunta Nailar tayi tana faɗin saina dawo,a dawo lafiya Aunty Sophia ta faɗa tana rufe mata marfin motar.
Motocin security guard ɗin su ka shiga tare da masu Aikin Nailar,Aunty Sophia na nan tsaye har su ka nufi gate ɗin gidan,sai da taga bata ganinsu tukunna ta koma ciki,ranta duk a jagule, ji take inama zata iya hana Nailar fita.
_*HEART OF VEGAS CLUB AND CASINO*_
Tun daga nesa zaka fara hangen hasken sparkling bulbs na haska saman building ɗin in da aka rubuta _* heart of Vegas club and casino*_ da wani irin style.
Tsarin ginin building ɗin ma kawai abun kallo ne,
A katafaren parking lot na club ɗin da ke cike da tarin rides masu shegen kyau da tsada su kayi parking a wajen parking ɗin motocinta wanda ya kasance nata ne ita kaɗai.
Dai dai ta parking ɗin su su kayi, security guard ɗinta ne su ka fara fitowa tare da masu aikinta,ɗaya daga cikin su ne yazo ya buɗe mata marfin motar.
A hankali ta zuro ƙafafunta,kafin ta ƙarasa fitowa,gaba tayi suna biye da ita a baya,da wasu jibga jibgan security guard dake sanye cikin baƙaƙen kaya ƙugunsu soke da bindigu su ka ci karo a bakin entrance ɗin shiga,tun kafin ta ƙaraso su ka bata hanya suna ɗan rissanar da kansu Alamar gaisuwa,ko kallon in da suke ba tayi ba ta nufi security door ɗin shiga.
Wata irin katafariyar ƙofa ce wacce kai daga ganinta kasan ba ƙaramin waje bane,ƙofarce ta fara magana cikin harshen turanci
“welcome to Heart of Vegas,ur Access card please” da sauri ɗaya daga cikin masu aikin ta ciro wani ɗan card a pose ɗin Nailar dake hannunta ta mannashi a jikin ƙofar.
dan da nan ƙofar tayi acknowledging card ɗin tana faɗin“welcome miss Nailar”
nan take ƙofar ta shiga zugewa,ciki ta kunna kai suna biye da ita.
wani irin katafaren club ne su ka shigo,yaji kayan alatu kamar baza'a mutu ba,yana yin tsarinshi yasha ban ban dana sauran clubs.
mata ne a tsaye a stage strippers cikin wata irin shaiɗaniyar sutura suna poll dance sauti na tashi,ga mata ga maza wasu a zaune wasu a tsaye suna taka rawa ana spraying dollars,wasu na shan giya,wasu na shaƙar cocaine,ga customize azul na yawo ta ko ina suna kaima waɗanda suka yi order, gawasu designs na shisha wanda a irin waɗan nan clubs ɗin kawai ake samun su, ga vape anasha suma,idan kashigo club din kai kanka kasan ana barin kuɗi, ga wasu irin security guards dake a different corner tsaitsaye da communicative devices a kunnensu kai kace gumaka ne yanda suka tsaya kiƙam ko alamar fitar da breath ba su yi.
Kiɗan dake tashi ne ya tsaya,Dj ne ya shiga sanar da zuwan Nailar hakan yasa mutanen dake ciki kai duban su gareta,ihu da sowa ne ya fara tashi wasu na ambatar Queen wasu President,ƙayataccen murmushi ta saki tana ɗaga masu hannu,gungun wasu maza ne su ka nufo in da take sai tangaɗi suke alamar sun sha sun sha sunyi tatul,da sauri security guard ɗinta su ka dakatar da su, murmushi gefen fuska ta saki tana yarfa masu ƴan yatsunta haɗi da ɗan cizon ƙasan lips ɗinta so sexy,ba ƙaramin jan hankalin mazan dake wurin tayi ba harda ma mata,ca su ka yi mata da idanu kamar tsaffin mayu ga nama suna kallo amma ba halin tunkara.
fly kiss ta sakar masu tana nufar glass elevator dake cikin wurin, security guard ɗin ta na biye da ita.
Wani irin ƙato casino su ka shigo,yaji kayan alatu, uwar dukiya a ka narkar wajen gidanasa ba kaɗan ba ,da kaɗan ne bai ƙarasa girman club ɗin da su ka fara shigowa ba.
Wani irin casino Aesthetic ne mai matuƙar ɗaukar ido,ga wasu matsiyatan poker tables and gaming table haɗe da chairs ɗin su,casino cards ne a kowane table,a ƙalla ko wane table na ɗauke da chairs guda biyar.
Mata da maza ne zazzaune saman chairs ɗin, casino cards ne a gabansu suna buga caca ga tarin dollers da kowane a cikin ya ajiye a matsayin kuɗin wasan shi, nau'in beers ne masu tsadar gaske haɗe cigarettes wanda tsadar su ta kai mutum ya sayi gida da mota na mutunci ajiye a gaban su,wasu na shan giya wasu na zuƙar taba ana buga wasa kiɗa na tashi ƙasa ƙasa.
nan ma security guard ne a kowane corner tsaye ƙiƙam.
murmushi Nailar ta saki ganin yanda ake buga wasan,fito tayi wanda ya jawo hankalin mutanen dake wurin,ihu mazan dake wurin su ka saka suna faɗin QUEEN!!!!
dariya Nailar ta saki tana ɗaga masu hannu,wani ɗan corridor ta nufa,shuffle machines ne haɗe da slot machines, video poker and video lottery terminals a wajen, ma'aikata ne zaune saman poker chairs suna opreting ɗin su.
cikin girmamawa su ka shiga gaishe da ita kamar za su russuna mata,jin jina masu kai ta shiga yi, office ɗin ta ta nufa dake can floor ɗin ƙarshe,a bakin ƙofar shiga office ɗin security guard ɗinta suka tsaya masu aikin su ka bi bayanta.
wasu numbobi ta danna a jikin ƙofar nan take ƙofar ta buɗe,kutsa kai tayi ciki jelarta na biye da ita,wani irin katafaren office su ka shigo kamar na shugaban ƙasa,ga sanyin AC dake busowa kamar ƙanƙara,ƙaton transparent glass office table ne a ciki haɗe leather chair mai shegen kyau,laptop ce ajiye saman table ɗin haɗe office lamp,daga gefe 50gm ne na cocaine anyi packaging ɗin su sai Cuba Aliados cigarettes dake a cikin ƙana nan kwalayenta itama anyi packaging ɗinta sai kwalaben shisha nau'i daban daban masu tsadar gaske,ga ɗan madaidaicin bottle keeper wanda aka jera kwalabanan beers kala daban daban.
daga can gefe poker table ne wanda ke ɗauke da casino cards,sai faskekiyar glass computer dake ajiye anyi connecting ɗin ta da gaba ɗaya CCTV CAMERAS dake heart of Vegas.
Cikin office ɗin su ka ƙarasa,chair ɗinta ta nufa ta zauna yayin da masu aikin suka nufi wasu sofas guda biyu su ka zauna, laptop ɗin dake ajiye saman table ɗin ta buɗe,opreting ɗinta ta shiga yi a hankali.
Muryar na'urace ta karaɗe office ɗin tana sanar da zuwan MDs na gaba ɗaya club da casino ɗin, izinin shigowa ta ba da ta hanyar danna wani maddani a jikin table ɗin,a hankali ƙofar ta shiga zugewa,wasu murɗa murɗan ƙatti ne majiya ƙarfi su ka shigo cikin shigar baƙaƙen suit,gaban table ɗin Nailar su ka ƙara so.
gaishe da ita su kayi suna russunawa,amsa masu tayi tana nuna masu kujerun dake facing ɗinta,zama su kayi saman kujerun.
“is there any problem?”
“no ma,but kayan da Boss ta turo suna hanya,muna sa ran isowar su next tommorow around 2:00Am”
jinjina kai Nailair tayi“good,bayan nan babu komai?”
“yes”
“ok,take this” ta faɗa tana nuna masu packeg ɗin cocaine da cigarettes,miƙewa tsaye su kayi,ɗaukar kayan su kayi suna mata sallama haɗi da ficewa.
tura kujeran da take zaune tayi,ƙafafunta ta ɗaura saman table ɗin tana jinginar da kanta saman head ɗin kujerar,ɗaya daga cikin masu aikin ce ta miƙe,can cikin office ɗin ta nufa,bata jima a sai gata ta fito hannunta ɗauke da ƙatuwar kwalbar champagne haɗe da champagne tulip glass sai ice a cikin bowl,har gaban table ɗin Nailar ta ƙaraso,ajiyewa tayi,ice ɗin ta fara zubawa a cikin cup kafin ta buɗe kwalbar, tsiyaya mata tayi cikin cup ɗin ta miƙa mata,amsa tayi tana wani lumshe ido.
barin wajen tayi,komawa tayi ta ɗauko masu milkshakes guda biyu,duk yanda su ke son shan kayan shaye shaye Nailar ta hana sai dai su sha lemu ko milkshake.
wayarta ce ta fara ringing,kallon screen ɗin tayi love shine sunan daya bayyana, murmushi ne ya bayyana a fuskarta, picking call ɗin tayi tana kara wayar a kunne.
“sweetheart” shine sunan da Nailar ta furta,on the other hand murmushi ta cikin wayar ta saki
“baby nah ya ki ke,ya gidan” ɓata fuska Nailar tayi “babu daɗi,yaushe zaki dawo?"
“kinyi kewata ne?”
“i really miss u, please come back home” Nailar ta faɗa kamar zata sa kuka
murmushi ta saki
“i think next week,fatan kina office?”
“momy mai makon ki tambayi lafiyata amma ta office ki ke,wai tsaya dani da wannan business ɗin ma wa ki ka fi so ne?”
“nafi sonki sama da komai, sorry fatan kina lafiya”
ɓata fuska Nailar tayi
“yes,su Joseph sun sanar dani kayan da ki kayi order suna hanya?”
“yes, Please my baby ki kasance a wurin lokacin da shipment ɗin zai ƙaraso bana son any problem ya faru, kaya ne masu tsadar gaske, munada tarin customers a ƙasa wanda zuwan kayan kawai su ke jira”
“please momy,su Joseph za su iya ji da komai ba sai naje ba”
“no kije dai zaifi,zan turo maki komai ta email,ki tabbatar ba wani kuskure”
turo baki Nailar tayi ba tare da tace komai ba da alama ba taji daɗi ba,sallama su kayi, ajiye wayar tayi saman desk tana lumshe ido haɗe da sakin ɗan ƙaramin tsaki.
Sai Around 5:00Am ta koma gida a gajiye,ko kayan dake
jikinta bata cire ba ta faɗa saman bed,ficewa masu aikin su kayi bayan sun ajiye mata bag ɗin ta haɗe da wayarta.
Aunty Sophia da saurinta ta zo amma sai ta tarar tana bacci, murmushi kawai tayi taja mata blanket,kissing forehead ɗinta tayi ta fice daga ɗakin...
_Ep 13_14_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘
______________________________
*ABUJA NIGERIA*
Turus ta tsaya ganin ko kallon dinner ɗin da aka kawo mata ba tayi ba, kallonta ta kai zuwa bed ɗin dake ɗakin, a zaune take ta jingina da head bord ɗin gadon,photon mahaifiyarta tare da mahaifinta ne riƙe a hannunta sai aikin shafawa take yayin da hawaye ke sintiri a fuskarta.
girgiza kai Yumnah tayi yayin da take ƙarasawa bakin bed ɗin, zama tayi kusa da ita tana dafa kafaɗarta,cikin sigar lallashi ta fara magana.
“sister Nainarh na san abun da ciwo, nasan zai ɗauki lokaci kafin zuciyarki ta dake, sai dai ki sani yawan ku ka da sa damuwa a rai bashi ke maganin matsala ba Adu'a itace maganin duk wata matsala, a halin yanzu Adu'arki su ke buƙata sama da komai, in sha Allah komai daran daɗewa gaskiya za tayi halinta, in dai da rai wata rana a gabanki duk wani mai sa hannu a al'amarin zai zo