ƙarasawa yayi bakin bed ɗin,kallon fuskarta yayi, baccinta take hankali kwance, murmushi ya saki yana shafa gefen fuskarta, motsi tayi kamar zata farka hankan da tayi ba ƙaramin tafiya yayi dashi ba, ya san da idonta biyu daya bani da ƙorafi.
a hankali ya duƙa yayi kissing forehead ɗinta ai kuwa ta buɗe ido dama idonta biyu kawai tayi kamar tana bacci ne ko nocking ɗin da yayi tana ji, sauri tashi yayi tsaye “dama ba bacci ki ke ba?”
“eh, ya Irfan wai mi nayi maka ka ke gudu na wannan time ɗin, ko dai bakayi farincikin zuwana bane??” ta faɗa a shagwaɓe
“nayi farincikin zuwanki mana”
“to mi yasa kake guduna” ta faɗa tana sauka daga saman bed ɗin ta nufo in da yake,faɗawa tayi jikinshi tayi hugging ɗin shi
“ko nayi maka wani laifi ne?” shafa bayanta ya shiga yi a hankali
“ba kiyi man laifin komai ba Noor, kawai wani uzuri ne ya riƙe ni”
“amma ai ba haka kake man ba duk muka zo, kofa zaman one hour ba muyi ba, a da da kake ɓata kowane lokacinka a tare da ni” tana a kwance saman ƙirjinshi take faɗar haka,cike da salon bariki take manna mashi ƙirjinta a nashi,hakan da take mashi ba ƙaramin jefashi a yanyi take ba,ɗago da kanta yayi yana kallon kyakyawar fuskarta,turo baki tayi kamar zata fashe mashi da kuka.
“kasan yanda nake ji kuwa saboda guduna da kake?” bai bata amsar tambayar da tayi mashi ba sai manne bakinsu da yayi waje ɗaya, ai kuwa da sauri ta kama tongue ɗinsa tana kissing dama abunda take so kenan,wasu irin hot kisses su ka shiga bama juna kamar za su haɗiye juna, cikin ƙanƙanin lokaci suka fita a hayycin su suna a wannan yanayin ne Nainarh ta faɗo ɗakin, Yumnah tace ta zo nan su kwanta kar a bar Noor ita ka ɗai.
wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi da sauri ta juya masu baya gabanta na wani irin duka kamar zai faɗo ƙasa, da sauri Noor ta tureshi tana faɗin Nainarh! , saurin kai duban shi yayi gareta,da gudu ta fice daga ɗakin...
______________________________
wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi da sauri ta juya masu baya gabanta na wani irin duka kamar zai faɗo ƙasa, da sauri Noor ta tureshi tana faɗin Nainarh! , saurin kai duban shi yayi gareta,da gudu ta fice daga ɗakin.
A jiyar zuciya suka shiga saukewa kamar wanda su kayi tseren gudu
“amma ba kince man ke kaɗai bace?” Irfan ya faɗa
“eh, ban san ya a kayi ta zo ba”
juyawa yayi ya nufi ƙofar fita,saurin kamo Arm ɗinshi tayi
“when zaka dawo,saboda kaifa zan kwana?”
“zuwa safe” ya bata amsa yana wani lumshe ido,gaba ɗaya jinshi yake a wani irin yanayi na daban ƙafarshi ma da ƙyar yake ɗagata
“shikenan saika dawo ka kula man da kanka” jinjina mata kai yayi ya fice daga ɗakin.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kama igiyoyin rigarta ta ɗaure,switch ɗin ɗakin ta nufa ta kashe bulbs ɗin bedside lamps su ka kawo, kwanciya tayi saman bed ɗin,lumshe idanunta tayi tana jan iska haɗe da fesarwa,wani irin yanayi take ji a jikinta, kwata kwata ba taji kunyar ganinsu da Nainarh tayi ba sai ma haushin katse masu jindaɗi da tayi, tsaki taja tana gyara kwanciyarta.
Nainarh tana fita daga ɗakin da gudu parlor ta nufa tasan muddin ta koma bedroom ɗin da Yumnah take dole taji ba'asin abunda ya dawo da ita koma ta nufi ɗakin dan ganema idonta, a jikin pillar ta samu ta ɓuya, ajiyar zuciya ta sauke tunda take a rayuwarta bata taɓa jin haushin wani ɗan Adam ba kamar yanda take jin haushin Irfan da Noor a yanzu, ko wace irin taɓewace ta samesu haka,idan sun san suna son junansu danmi bazasu sanar da iyayen su suyi masu Aure ba amma zasu ɓige da neman juna ta ƙazamar hanya, ko basu san hakan babban zunibi bane, duk da take kallonshi daban da ƴaƴan mom batayi tunanin haka halayenshi su ke ba,a ido kamar mutumin kirki ko kunya basa ji yanzu da Yumnah ce ta shigo ta samesu da wane ido su ke tunanin zata kallesu.
wani irin tausayin mom da dady ne ya rufeta,mutanen kirki amma ƴaƴansu ke aikata laifuka irin haka,dady yafi bata tausayi ga Irfan ga Fa'iz mutumin ƙwarai mai riƙo da addini Allah ya jarabceshi da ƴaƴa haka, dama Allah baya barin bawansa haka ba tare da ya jarabashi ba ta hanya daban daban , ita kaɗai take sambatunta babu mai bata amsa.
tana a nan tsaye Irfan ɗin ya fito sai ƴan waige waige yake, harara ta watsa mashi kamar idanunta zasu faɗo ƙasa wani irin tsanarshi take ji a ranta,saida taga ficewarshi daga gidan tukun ta nufi bedroom ɗin ko ta kan Noor dake kwance bata biba ta juya mata baya itama Noor ɗin yi tayi kamar tana bacci.
A cikin mota ya samu Waseef har ya gaji da zaman jiranshi, yana isowa driver seat ya buɗe ya shiga kifa kanshi yayi, tunda yake a rayuwa bai taɓa jin kunyar dayaji ba yau, bai taɓa tunanin ko Yumnah ce ta ganshi zaiji irin wannan kunyar da yaji dalili ganin da Nainarh tayi masu, yayi fatan ace bata shigo ɗakin ba,damuwarshi yanzu da abun zata riƙa kallonshi za tayi mashi kallon mara kamun kai koma ta sanar da wani mussaman Yumnah.
dafa kafaɗarshi Waseef yayi
“lafiya dai?” ya tambaya
“babu komai” shine kawai abun da Irfan ɗin yace mashi
“Irfan indai irin wannan haɗuwar da kuke zata zama matsala mi yasa bazaka sanar da dady ba kana sonta,sai suyi maku Aure,bana son ku ƙetara in da bai kamataba, dan muddin ku ka cigaba a haka wata rana sai kunyi dakun sani mara amfani”
“bazan iya sanarda dady ba Waseef” Irfan ɗin ya faɗa ba tare da ya ɗago da kanshi ba
“bangane bazaka iya faɗa mashi ba, kana nufin ba sonta kake ba??”
“ina sonta mana Waseef, kawai dai bazan iya sanar da dady ba, lokuta da dama ko nayi niyyar sanar da wani a cikin su kasawa nake sai duk na rasa ƙwarin gwiwata”
“na fahimci sanar dasu ke baka wahala, ni ka bani dama na sanar da dady ko big dady nasan za suyi farin ciki da hakan”
“karka sanar da su nafi son suji a baki na”
“tayaya kenan?”
“zan sanar da su in sha Allah”
“shikenan, amma dai karka ja jiki” jin jina mashi kai Irfan ɗin yayi
“please kayi driving ɗin mu” Irfan ɗin ya faɗa yana ficewa daga motar, driver seat Waseef ya dawo shi kuma ya koma mazaunin shi dan a yarda yake jinshi zai iya watsar da su a titi, ba Noor bace damuwarshi Nainarh ce damuwarshi bai taɓa jin kunyar wani a rayuwarshi ba kamar yanda yake jin ta Nainarh yanzu,key Waseef yayi ma motar su ka fice daga estate ɗin baki ɗaya.
Heart of vegas su ka nufa saɓanin wurin dinner da su ka cema dady za su sun faɗin haka ne kawai dan su kare kansu,parking Waseef yayi,kusan a tare su ka fito shida Irfan ɗin su ka shiga ciki , a cike yake kamar kullum,third floor na club ɗin su ka nufa, wani irin ƙaton meeting room dake kusa da office ɗin Irfan su ka shiga,zungureren table ne mai ɗauke da chairs,manyan mutane ne su shidda a zaune a saman chairs ɗin zaman jiran Irfan ɗin kawai su ke, an cika masu gabansu da kayan sha kalar nasu na club, chair dake kallon duka chairs ɗin Irfan ya nufa ya zauna, Waseef ya zauna ata kusa dashi, system ɗin dake ajiye kan table ɗin ya buɗe haɗe da ɗaukar communicative device, yasa a kunnenshi.
gabatar da meeting suka shiga,cike da natsuwa Irfan yake gudanar da komai duk da baya da gogewa akan abun sai dai mubarak na taimaka mashi ta hanyar Bluetooth,sun shafe kusan Awa biyu a ɗakin meeting ɗin kafin su ka kammala around 2am
*WASHE GARI*
Ana kiran sallar farko ta farka hakan al'adarta ce tun tana gidan su, kallon Noor dake kusa da ita tayi, baccinta take hankali kwance, sauka tayi daga saman bed ɗin ta nufi bathroom, Alwala ta ɗauro, bakin bed ɗin ta dawo tashin Noor ta shiga yi, nauyin bacci gareta da ƙyar ta samu ta farka.
“ki tashi lokacin sallah yayi” ya mutse fuska Noor ɗin tayi tana juya kwanciyarta
“ki sani wannan baccin bashi da amfani,idan kin kammala sallah kina iya dawowa ki cigaba da baccinki”
“kiyi taki kawai zanyi” Noor ɗin ta faɗa, gyaɗa kai kawai Nainarh tayi, dressing room ɗin Yumnah ta nufa, kayan jikinta ta canza zuwa doguwar riga,bedroom ɗin ta dawo hannunta ɗauke da hijab da carpet, shimfiɗa carpet ɗin tayi, hijab ta zura a jikinta ta kabbar sallah, harta kammala raka'atanil fijir tayi sallah ta zauna tana azkar Noor bata tashi ba, mamakin momy Noor ne ya kamata, wace irin uwace ita da har ƴarta ke wasa da Sallah irin haka bata tsawatar mata ba, ta san da ace mahaifiyarta na kula da tarbiyarta da duk hakan bai faru ba a ganinta sakacin mahaifiyarta ne ba laifin Noor ɗin, Allah sarki ita lokacin da tana tare da iyayenta kullum mahaifinta sai ya tabbatar da ta tashi domin yin sallah yake nufar masallaci hakama mahaifiyarta bata yin sallah sai ta tabbatar da taga tashinta tayi Alwala tukun take komawa nata ɗakin tayi sallah.
wata irin kewar iyayenta ce ta kamata musamman mahaifinta a irin wannan lokacin tana part ɗin shi yana ɗora mata karatu, duk asubar duniya sai ya zaunar da ita ya bibiyi karatunta na islamiya ya koya mata abunda bata gane ba, rayuwa kenan yanzu bata da wanda zaiyi mata hakan kowane farin ciki na rayuwarta ya tarwatse.
saurin ɗago da kanta tayi dalilin dafa kafaɗarta da aka yi, Yumnah ta gani tsaye a gefenta
“lafiya ki ka zuba uban tagumi da asubar fari?”
“sister Yumnah ina ta so na tambaye ki?” Nainarh ta faɗa, juyowa Yumnah tayi tana fuskantar ta
“ina jinki?”
“wai babu islamiya ne a Estate ɗin nan?”
“akwai mana,kina so ne?”
“eh, amma mi yasa ke baki zuwa” ɗan ya mutse fuska yumnah tayi
“da ina zuwa na bari”
“saboda mi?”
“haka nan kawai”
“ya kamata ace kina zuwa, shifa karatun addini ba'a gamashi”
“zan koma amma sai idan da ke”
“karki damu,da zan samu ma wanda zai koyaman harda asuba ina so”
“in dai kina so zanyi ma dady magana, da yana koyaman na bar zuwa”
“ina so kuwa”
“shikenan idan munje gaishe shi sai nayi mashi magana”
“nagode sosai”
murmushi Yumnah tayi mata tana shigewa dressing room ɗin.
Sai da gari yayi haske sosai tukun su ka nufi part ɗin dady a zaune su ka same shi a parlor saman rug carpet,hannunshi riƙe da Qur'an yana karatu kamar kullum, zama su kayi har ya kammala, gaishe da shi su ka yi cike da kulawa ya amsa masu.
“dady dama Nainarh ke son zaka riƙa biya mata karatu da asuba” Yumnah ta faɗa, kallon Nainarh dady yayi fuskar shi a ɗan ɗaure
“shine ba zaki iya tambayata ba har sai kin sa Yumnah?”
duk sai taji kunya
“A'a dady, kayi haƙuri”
“gaskiya banji daɗi ba nima mahaifinki ne zaki iya tambayata duk abunda ki ke so”
“kayi haƙuri”
“karki damu,duk lokacin da ki ka kammala sallah ki zo zan koya maki gwargwadon abunda na sani”
“in sha Allah dady, nagode” kallon Yumnah yayi
“Auta yanzu ko kunya ba kiji ba?” saurin sadda kai ƙasa tayi tana susar kai
“ai harda ni ba ita kaɗai ba” girgiza kai kawai dady yayi, sallama su ka yi mashi su ka fice.
tunda su Nainarh su ka shigo Mamy take laɓe tana sauraronsu,wani irin haushin Nainarh ne ya sake kamata,ji tayi kamar ta fito ta shaƙi wuyanta gani take kamar neman samun gindin zama ne da neman shiga wurin dadyn yasa ta ƙirƙiro da wai tana son dady ya koya mata karatu.
tsaki taja tana fitowa parlorn, ko kallon in da dady yake ba tayi ba ta fice.
*A fter some days*
Nainarh tun ranar da su ka yima dady magana kullum da asuba sai sunje ya ƙara masu karatu ita da Yumnah,islamiya ce kawai basu fara zuwaba sun bari sai wani weekend ɗin saboda school,Noor da su Ammar tun washe garin ranar su ka koma gida,Nainarh da Yumnah ne su ka maida su Ammar gida harda Jamal.
*UNITED STATE*
_*Las Vegas (Nevada)*_
A zaune suke a saman wasu haɗaɗɗun chairs dake katafaren garden ɗin gidan,Nailarh ta miƙe ƙafafunta saman ɗan madaidaicin table yayinda system ɗinta ke ajiye saman laps ɗinta tana operating fuskarta ɗauke da murmushi,hot pant ne a jikinta haɗe da ƴar shirt da bata wuce cibiyarta ba, Aunty sophia na daga gefenta zaune hannunta riƙe da mug ɗin coffee.
kallon fuskar Nailarh dake ɗauke da murmushi Aunty sophia tayi da alama ba ƙaramin nishaɗi take samu a tattare da system ɗin ba
“da alama yau kina cikin farin ciki,ko zan iya sanin abunda yayi dalilin sa wannan kyakyawar fuskar taki farin ciki?” Aunty sophia ta faɗa
ƴar dariya ta saki tana ɗaukar mug ɗin coffee dake ajiye kan table ɗin,sai data ɗan kurɓa tukun takai dubanta ga Aunty sophia
“ba komai yayi silar shigata wannnan farin cikin ba sai wasan da zamu gabatar a N R T ranar sunday, na samu ƙarin ƴan wasa daga California,abunda yayi matuƙar burgeni da ƴan wasan, details ɗin dawakan su da su ka turo, ji da kansu yayi matuƙar ƙyatar dani, a tunanin su canza tarihin N R T abu ne mai sauƙi sai dai basu san samun dokin da zaifi KING zimma da karsashi abu ne mai matuƙar wahala” ta faɗa cike da alfahari
Murmushi Aunty sophia ta saki tana ajiye mug ɗin coffee dake hannunta “baby na lura kina matuƙar ji da kanki kema,karki manta ba kullum mutum ke nasara ba,anyi gwaraza tun talataini kuma sun shuɗe,duk yanda ki ke ji da kanki akwai wanda ya fiki kuma dole a samu wani wanda zai karya tarihin N R T, kullum ke ke hawa akan mutane kema dole a samu wani wanda zai zama sama da ke”
wani irin kallo Nailarh ta jefa mata “Aunty sophia mi yasa ki ke faɗa man haka,kina baƙin ciki da nasarar da nake samu ne?” saurin girgiza mata kai Aunty sophia tayi
“ba haka bane baby,kawai ina son kisan cewa a rayuwa ba kullum mutum ke samun abunda yake so ba”
“please ki daina faɗa man haka raina ɓaci zaiyi”
“sorry ban faɗa maki haka dan ranki ya ɓaci ba,ina maki fatan nasara kamar ko da yaushe”
murmushi Nailarh ta saki “ko ke fa,da za ki ɓata man farin cikin da nake ciki,a round 5 pm jirgin momy zaiyi landing a airport”
yanayi fuskar Aunty sophia ne ya canza zuwa tsantsar damuwa,ba dawowar mahaifiyarta ta bane bata so ba, yana yin da take jefa Nailarh ne bata so
“ya dai Aunty sophia” Nailarh ta faɗa ganin yanyin da Aunty sophia ta shiga
“ban manta ba,yanzu nake shirin tashi na duba chefs, kema ya kamata ki ajiye aikin nan ki shirya dan kije airport ɗaukota”
“yanzu zan kammala”
“ok,bari na shiga ciki” Aunty sophia ta faɗa tana ɗaukar mug ɗin coffee da take sha ta nufi cikin gidan,direct kitchen ta nufa chefs ɗin ta fara dubawa har sun kusa kammala aikin dinner da suke,ficewa tayi daga kitchen ɗin ta nufi part ɗinta dake kusa dana ma'aikatan gidan,a corridor ta tsaya,wayarta ta zaro daga cikin Aljihun rigar dake jikinta.
dialing wata number tayi,kiran har ya katse ba'ayi picking ba,maida wayar tayi cikin Aljihun rigarta ta koma kitchen.
Nailarh tana kammala aikin da take part ɗinta ta nufa shaf shaf masu aikinta su ka shiga shiryata ko sanda Aunty sophia ta shigo ɗakin har ta kammala shirinta
wani kallo Nailarh tayima Aunty sophia “dama ba tare dake zamu je ba?”
“eh Nailarh sai kun dawo” taɓe baki Nailarh tayi tana ɗaga kafaɗarta, ficewa su kayi daga ɗakin har compound Aunty sophia ta rakata sai da taga ficewarsu daga gidan tukun ta koma ciki.
Masu aikin ta fara dubawa saida ta tabbatar komai na tafiya yanda ya kamata kafin ta wuce part ɗinta, a bakin corridorn ɗazu ta tsaya number ɗazu ta sake dialing yanzu ma har kiran ya katse ba'ayi picking ba yanke shawarar turama number saƙo tayi, a hanzarce ta shiga typing message, da harshen Spanish take rubutun hakan yasa ban san abunda take rubutawa ba,tana tura message ɗin tayi saurin maida wayar Aljihun jin alamar kamar mutum a bayanta, saurin kai dubanta tayi bayanta.
ganin ba kowa ne yasata sauke ajiyar zuciya ƙofar part ɗinta ta buɗe ta shiga ina saurin na shiga dan na gane mana nida ku masu karatu amma tayi saurin murza key dan dole na tsaya a bakin ƙofa.
A round 5 pm agogon U S jirgin su yayi landing a katafaren Airport dake garin,Nailarh a zaune take ita da maƙarabanta saman waiting chairs.
Passengers ne su ka ɓullowa ta ƙofar da aka tanada domin su, momy Nailarh ce ta ɓillo a sanye take da suit black color sun bi shape ɗin jikinta, tana da diri sosai kamar matashiyar budurwa,ta rufe kanta da scarf idanunta a manne da baƙin glass,hannunta a riƙe da trolleynta, da gudu Nailarh ta nufeta securitys ɗinta na biye da ita a baya, sakin trolley dake hannunta tayi tana buɗe mata hannayenta, Nailarh na ƙarasowa ta faɗa jikinta, hugging ɗinta tayi tightly, murmushi securitys ɗin su ka saki ba Nailarh ba kawai suma sunyi matuƙar farin cikin dawowar miss MALIKA,raba jikin su tayi,kissing lips ɗin Nailarh tayi hakan ba ƙaramin ƙyatar da securitys ɗin da mutanen dake wurin tayi ba.
wani irin narkakken murmushi su ka sakar ma junansu wanda ke nuna tsantsar kewar juna da su kayi, hannun Nailarh taja da sauri securitys suka shiga rissinawa suna gaishe da ita,cike da kulawa ta amsa masu,trolley ta su ka ɗauka, in da su ka yi parking motocin su suka nufa Nailarh da miss Malika na gaba yayin da securitys ɗin ke take