Ishrat tayi ta shigo,ganin kowa na gidan ya fito Nainarh ce bata fito bane yasa ta zo duba ko lafiya.
da mamaki take kallonta kwance a ƙasa,har inda take kwance ta ƙaraso,a hankali ta shiga kiran sunanta,da alama tayi nisa sosai a cikin baccin yasa ba taji kiran da tayi mata ba,hannunta ta kai saman kafaɗarta da nufin tashin ta
wata irin zabura tayi haɗi da fasa ƙara,saurin toshe mata baki Ishrat ɗin ltayi tana faɗin “nice Aunty Nainarh” wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Ishrat a kusa da ita,gaba ɗaya a tsorace take.
kafeta da ido Ishrat tayi “lafiya ki ke Aunty Nainarh?” gyaɗa mata kai Nainarh tayi “lafiya lau nake” gyaɗa kai kawai Ishrat tayi ba dan ta yarda da abunda Nainarh ta faɗa mata ba,tashi tayi daga duƙen da take.
bed ɗin su ta fara gyara masu,tashi Nainarh tayi ta nufi bathroom,mirror ta nufa da sauri,kallon lips ɗinta da shoulder ɗinta da su ka yi jawur tayi,wasu irin hawayen baƙin ciki ne su ka wanke fuskarta,tayi data sanin sanin yumnah a rayuwarta,bata taɓa expecting haka daga gareta ba,ta kai tsawan five minutes a gaban mirror kafin ta cire kayan jikinta,ruwa ta tara a bathtub,wanka ta shiga yi,kamar zata fasa fatar jikinta haka take dirzarta da sponge,gaba ɗaya ƙyanƙyamin jikinta take saboda abunda yumnah tayi mata.
sai da jikinta ya fara mata zafi tukun ta dakata,fatar tayi jawur kamar wacce aka watsama tafasasshen ruwa, fashewa tayi da wani irin kuka mai ban tausayi “mi yasa ƙaddara ta haɗani dake yumnah,mi na aikata ne wannan abubuwan ke faruwa da ni” ta faɗa cikin ƙunar rai,ta kai tsawan 30 minutes a toilet tana aikin ku ka kafin ta wanke jikinta ta fice,har time ɗin hawaye ne ke zarya a fuskarta.
lokacin data fito bata samu Ishrat ba harta kammala gyara masu ɗakin ta fice, dressing room ɗin su ta nufa, idanunta ne su ka sauka akan ƙaton kwalin da su ka yima momynta shopping ita da yumnah,yau su ka yi za su kai mata ziyara amma ta ɓata komai,kauda kai tayi daga kallon kwalin ta nufi wardrobe ɗin su,ɓangaren da kayanta su ke ta nufa,doguwar rigar atamfa ta ɗauko haɗe da hijab,zura kayan tayi a jikinta,
shaf shaf ta shirya a cikin kayan, bag hanger su ta nufa, ƙaramar side bag ta ɗauka, wayarta da atm dinta ta saka a cikin jakar.
parlor mom ta nufa ta yi mamakin ganin falon tsit babu kowa har ta juya da da nufin zuwa bedroom ɗin mom,Ishrat ce ta fito daga kitchen,kallon Nainarh dake ƙoƙarin shiga bedroom ɗin mom tayi “mom ba ta nan” ishrat ta faɗa,dakatawa tayi tare da sakin handling ɗin kofar,dawowa tayi cikin parlorn tana faɗin “ok bari na shiga na gaishe da daddy”
“shima baya nan” Ishrat ɗin ta bata amsa,da mamaki Nainarh ke kallon Ishrat ɗin “to ina suka tafi,Aunty laatifa fa??”
“suna hospital gaba ɗayan su har da Aunty yumnah,Aunty Kainart ce bata da lafiya”
“Aunty Kainart!?” Nainarh ta faɗa jinjina mata kai Ishrat ɗin tayi alamar Eh
gyaɗa kai Nainarh tayi tana faɗin
“Allah ya bata lafiya, amma tun yaushe suka tafi?”
“gaskiya ban sani ba, amma ina tunanin tun cikin dare su ka tafi,dan da safe Aunty yumnah da Aunty Fa'iza sun zo sun ɗaukar masu breakfast,tace idan kin tashi ki kirata a waya tayi ma driver magana ya kai ki”
ok kawai tace mata tana nufar dining room,nufo dinning room ɗin Ishrat tayi da nufin saving ɗinta, dakatar da ita Nainarh tayi tana cewa “barshi kawai zan yi saving kaina” da to Ishrat ɗin ta amsa tana barin wurin, black tea kawai ta haɗa tasha,tashi tayi handbag ɗinta dake kan sofa ta nufa dauka tayi ta fice daga parlorn.
da mamaki Ishrat ke kallon warmers ɗin da ke kan dining,ganin Nainarh ba taci komai ba,tunani ta fara anya lafiya,musamman tsoratan da tayi lokacin da ta tashe ta daga bacci.
warmers ɗin suka shiga kwashewa ita da munirat suna kaiwa kitchen.
Nainarh tana ficewa daga parlorn direct compound ɗin gidan ta nufa ɗaya daga cikin securitys din gidan dake shawagi tayima magana a kan tana son zata fita ne,daya daga cikin drivers ɗin da ke zaune tare da maigadin gidan ya kwalama kira,a hanzarce ya taso ya nufo inda suke, cike da girmamawa ya gaishe da ita,da kulawa ta amsa mashi tana sanar da shi zai kai ta prison ne wurin mahaifiyarta, da ladabi ya amsa mata da to yana nufar parking space ɗin gidan,ɗaya daga cikin motocin dake parking space ɗin ya nufa key yayi ma motar tare da nufar inda take, back seat ta buɗe ta shiga, reverse yayi suka nufi main gate ɗin gidan,suna isowa securitys ɗin dake bakin gate ɗin suka dakatar da su,daya daga cikin security ne ya taso,da sauri driver ya sauke glass ɗin motar,gaisawa su ka yi da security yana tambayar ina za su “prison” ya faɗa, tambayarshi yayi shida wa yana nufar back seat,sauke glass Nainarh tayi da ladabi ta gaishe da shi amsa mata yayi cikin kulawa yana faɗin adawo lafiya haɗi da barin wurin,key driver yayi ma motar su ka fice daga Estate ɗin.
direct hanyar central Jail su ka nufa,sai da su ka yi nisa Nainarh tace “please idan ka samu mall a gaba zan ɗanyi shopping” da ok ya amsa mata.
a bakin wani haɗaɗɗen Mall na yan gayu yayi parking,fitowa tayi,ciki su ka shiga yana biye da ita a baya
within a five minute ta kammala shopping ɗin duk wani abu data san mahaifiyarta zata buƙata,wurin biyan kuɗi su ka nufa driver na tura cart.
Atm ɗin ta ta ciro bayan an gama calculating kuɗin kayan,ATM ɗin ta miƙa masu amma sai mutumin ya sanar da ita ai an biya kuɗin kayan,da mamaki take kallon mutumin “ban gane an biya ba” ta faɗa dan jin waye zai biya kuɗin kayan data saya
“afuwan ba'a bamu damar faɗa ba,zaku iya tafiya”taɓe baki kawai tayi koma waye matsalarshi damuwar da take ciki ma ta isheta,har parking lot ma'aikatan wurin su ka kai mata kayan,a booth driver yasa kayan, reverse yayi su ka bar mall ɗin.
within a time su ka iso Jail ɗin,ɗaya daga cikin securitys ɗin dake gadin Jail ɗin ya nufo motar,sauke glass ɗin motar yayi,gaisawa su ka yi da guard ɗin,daga yanayin gaisuwar ta su zaka fahimci sun san juna,umarni ya bada aka buɗe masu gate,cikin Jail ɗin su ka shiga.
A parking lot su ka yi parking,fitowaNainarh tayi,buɗe booth ɗin motar driver yayi, shopping ɗin da tayi ya ɗauko, office ɗin C G C suka nufa,a bakin ƙofar office ɗin su ka tsaya, ɗaya daga cikin securitys ɗin dake bakin ƙofar ne ya shiga dan sanar da zuwan su,fitowa yayi yana sanar da su za su iya shiga.
cikin office ɗin su ka shiga bakinta ɗauke da sallama, a zaune C G C yake saman chair ɗin shi,da fara'arsa ya amsa sallama da ta yi,ɗaya daga cikin chairs ɗin dake gaban desk ɗin shi ya nu na mata alamar ta zauna,zama tayi driver na ajiye kayan dake hannunshi.
fita drivern yayi,ruwa da lemu CGC ɗin ya ajiye mata, ɗan murmushi tayi tana faɗin “ina wuni uncle”
“lafiya lau Nainarh,yau sai ke kaɗai,ina barisster da yumnah?”
“tana da patient ne a hospital shiyyasa bata zo ba”
“Ayyah Allah sarki, Allah ya sawaƙa”
“Ameen,Momy fa uncle?” ta faɗa dan ta ƙagara taga momynta
“karki damu nasa ayi magana,yanzu zata zo”
jin jina mashi kai tayi
wasu chairs dake can ɗan nesa da desk ɗin shi ya nuna mata yana faɗin “you have 30 minutes” godiya tayi mashi tana tashi ta nufi chairs ɗin,tana zama ana buɗe ƙofar office ɗin officers mata ne guda biyu su ka shigo tare da momynta,da gudu ta nufi mahaifiyar tata ta faɗa jikinta haɗi da sakin kuka,wani irin sanyi jikin Hajiya Asma'u yayi lokaci ɗaya wasu zafafan hawaye su ka wanke fuskarta, hugging ɗin ta tayi sosai tana jin wani irin tausayin junansu, sun kai tsawan minti biyar kafin su ka raba jikinsu har time ɗin Nainarh kuka take itama mahaifiyarta hawayen dake fuskantar basu dai zuba ba,ƙarfin hali tayi wurin lallashin Nainarh, chairs ɗin dake wurin su ka nufa su ka zauna tana cigaba da lallashinta,shiru Nainarh tayi tana kwantar da kanta saman shoulder momyn ta ta
“ina barisster?” hajiya Asma'un ta faɗa
“ba ta zo ba,Momy dan Allah ina so na dawo wurin ki” ta faɗa tana ɗago kanta daga kafaɗar mahaifiyar ta ta
C G C na daga zaune saman chair ɗin shi duk wani abu da su ke faɗa yana ji haka ma officers ɗin da su ka shigo da hajiya Asma'un, wani irin kallo mai cike da tausayi hajiya Asma'un tayi mata “mi yasa ki ke son zama nan,wani abun ya faru dake ne,ko dai Zulaihart tayi maki wani abu?” girgiza mata kai tayi
“A'a kawai dai ina son zama tare da ke,na gaji da zama babu ke a kusa dani”
“Nainarh nima kaina bana jin daɗin rashinki a kusa da ni,amma ya za muyi haka Allah ya ƙaddaro a rayuwar mu,babu yanda muka iya dole mu karbi ƙaddarar mu hannu bibbiyu,kiyi haƙuri kinji,zamanki anan bazai yiwu ba” yanayin fuskar Nainarh ne ya canza har ga Allah abunda zai nisanta da yumnah take so a yanzu,sai dai ya za tayi dole tayi haƙuri tunda hakan ƙaddara ta zaɓar mata, lallashinta sosai momyn ta ta tayi,kamar yanda C G C ya faɗa 30 minutes na cika aka fice da Hajiya Asma'un bayan sunyi sallama da Nainarh ta ɗauki shopping ɗin data kawo mata,harda ku ka Nainarh lokacin da suka fice,sallama tayi ma CGC ɗin ta fice,a bakin ƙofar office ɗin ta samu driver,parking lot su ka nufa inda su ka yi parking motar su.
Ficewa su kayi daga prison ɗin har lokacin da ɗan sauran hawaye a fuskar Nainarh,wani irin tausayinta ne ya kama driver,tsit motar tayi har su ka kama hanyar da zata maida su Estate ɗin dama a haka su ka zo.
da mamaki yake kallon motar dake bayan su idan ba idanunshi ba ne basa gani sosai ba tun lokacin da su ka fito daga Estate ɗin motar take a bayan su,a lokacin bai kawo komai a ranshi ba amma yanzu abun ya ɗan ɗaure mashi kai,ta mirror ya kalli Nainarh dake back seat idanunta a rufe kamar mai bacci.
maida duban shi yayi ga motar har lokacin tana biye da su, street ɗin da zai sada su da Estate ɗin ya shiga still motar na nan biye da su,abun ne ya fara bashi tsoro,bai fita daga wannan tsoron ba sai ga wata mota ta tunkarosu gadan gadan,yayi matuƙar mamakin ta inda motar ta ɓullo, ƙoƙarin kauce mata ya shiga yi yana mamakin ko driver motar ya rasa birkinshi ne.
duk yanda ya kai ga ƙoƙarin kauce ma wannan motar abun yaci tura,duk in da ya matsa sai motar ta bishi.
wani irin mahaukacin burki ya taka har kanshi na haɗuwa da Steering wheel lokacin da motar ta daki gaban motarshi,bai san time ɗin da ya furta innalillahi wa Innah ilaihi raji'un ba salatin da yayi ne yayi sanadiyar buɗe idon Nainarh,ɗagowar da zaiyi yaga motoci har uku sun zagaye motar su “akwai matsala” shine abun da ya furta.
Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyar su shi da Nainarh dake zaro ido kamar wacce tayi ƙarya,ɗaya bayan ɗaya wasu samari masu ƙirar majiya ƙarfi su ka shiga fitowa daga motocin suna tunkaro motar su,da sauri driver yasa ma motar Lock, nocking ƙofar su ka shiga yi lokaci ɗaya Nainarh tabi duk ta ruɗe, da sauri takai hannu da nufin buɗe ƙofar motar,driver ne yayi saurin dakatar da ita “karki buɗe madam,akwai haɗari a tattare da mutanen nan”
a ruɗe Nainarh tace “idan su ka yo harbi fa,baka ganin gun ɗin dake hannunsu ne?,mu buɗe muji abunda ya kawo su”
“karki damu madam ko sunyi harbi babu abunda zai same mu,buɗe masu yafi haɗari”
cikin tashin hankali tace
“anya kasan mi ka ke faɗa kuwa!??”
tana ɗan ɗaga murya
“na sani madam motar tanada kariya daga harsashi,bari na sanar da C M abunda ke faruwa” ya faɗa yana ciro wayar daga front pocket ɗin shi ya shiga neman Number C M ɗin,Nainarh tsabar tsoron da take ciki kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito,shima kanshi driver a tsorace yake daurewa kawai yake Adu'a shi ya samu C M a waya.
wata irin razananniyar ƙara Nainarh ta saki lokacin da su ka fara sakar ma motar harsashi,gaba ɗaya ta kifa under seat,shi ma kanshi driver bai san time ɗin daya saki wayar dake hannunshi ba,ƙarar da Nainarh ta saki ta tsoratar da shi.
kamar yaƙi haka su ka shiga sakar ma motar bullet,gashi anguwar ba kowa kamar anyi shara,sauƙin su ɗaya da motar ta kasance bulletproof ce.
*POLICE STATION HEADQUTER*
Gama dai daita parking motocin su suka yi a parking lot ɗin dake headquarter.
ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fitowa daga cikin motocin,ɗaya daga cikin securitys ɗin ne su ka buɗe back seat ɗin motar dake tsakiyar su,ya Naeem ne ya fito ɗayan side ɗin A C M Usman ne ya fito,main entrance ɗin shiga P H ɗin su ka nufa, da sauri securitys ɗin su ka mara ma su baya amma sai ya Naeem ya dakatar da su hakan yasa su ka dakata,ciki su ka ƙarasa shida usman.
mai adaidaita ne yayi parking a bakin gate ɗin P H ɗin,wani dattijo ne ya fito wanda kallo ɗaya zaka mashi ka fahimci wahala ce ta mayar dashi tsoho sosai ba tare da shekarunshi sun kai ba.
ta ɗayan ɓangaren wata dattijuwa ce ta fito tareda wata yarinya da bazata gaza shekaru goma zuwa sha 12 ba a duniya wacce kallo ɗaya zaka mata ka fahimci babu isasshiyar lafiya a tattare da ita bayan halin na tsananin rayuwa da su ke ciki daga ita har iyayen nata wanda daga suturar jikinsu zaka tabbatar da haka.
gate ɗin shiga headquarter su ka nufa,da sauri securitys ɗin dake wurin su ka dakatar da su,ɗaya daga cikin securitys ɗin ya nufo su “kai tsoho! wai kai wane irin mai taurin kai ne,sau nawa muke faɗa maka ka daina zuwa nan,ka tafi can divisions dake anguwannin ku ka shigar da ƙararka,nan ba wurin kawo ƙananu ƙananun ƙorafi bane irin naka??” dattijon kamar zai fashe da ku ka yace “yallaɓai can ma sunƙi karɓar ƙorafin mu,wata matace tayi mana kwatancen nan tace nan ana karɓar ko wane irin ƙorafi,dan sanku da Manzon rahama ku tausaya ma yarinyar nan tana buƙatar a ɗaukar mata fansar abunda aka yi mata,an zalunceta, ku taimaka ku tsaya mata” ya faɗa yana haɗe hannayenshi wuri ɗaya alamar roƙo, girgiza kai security yayi “matar data turoka saboda ta san baka da hankali shiyasa ta turo ka nan”
“wallahi ba haka bane yallaɓai,tace in nemi inspector hussein”wani daga cikin police din ne yace
“kai dattijo babu wani ma'aikaci inspector hussein a nan,kaja jikar ka ku bar nan ko muyi maku korar kare”
fashewa da kuka matar shi tayi “don Allah yallaɓai ku taimake mu” ja in ja suka shiga yi da police ɗin, sun ƙi bari su shiga su kuma sun ƙi su tafi, sun kafe akan dole sai sunga inspector hussein
suna a haka su naeem suka fito, da sauri securitys ɗinshi suka nufi motocinsu,back seat suka buɗe masu,key su ka yima motocin su ka nufi get ɗin headquarter ta cikin mota ya Naeem ya hangi wannan dattijon sai fama security suke da shi akan ya tafi amma ya ƙi, dakatar da drever shi yayi,hakan yasa gaba ɗaya motocin securitys ɗin suka dakata,umarni ya ba drever da ya je yaji me ke faruwa,direban na fita wani daga cikin police din na fisgar hannun wannan dattijon ya hankaɗar da shi gaba daya tsohon ya nufi ƙasa ya fadi,fashewa da kuka matar shi da yar shi suka yi,da sauri driver nufi tsohon,kamashi yayi ya miƙar da shi ,kaf abunda ya faru akan idon ya Naeem, buɗe side ɗin da yake yayi ya fito hakan yasa securitys ɗin shi da ACM usman su ka fito,kama dattijon da dreve ke riƙe dashi ya Naeem yayi yana mashi sannu,masifa usman ya shiga yi mo polis ɗin suna bashi hakuri Hadi da faɗin “yallabai wannan dattijon da kake ganin shi ya cika taurin kai da
naci mun ce mashi banan zai shigar da ƙorafi ba,ya tafi division dake anguwannin su amma yaƙikullum sai ya zo nan”
“saboda baku san darajar manyanku ba shiyyasa za ku ture shi,idan kullum yana zuwa baza ku iya mashi uzuri ba,ko ba kuga shekarunshi sun ja ba?”
“ayi haƙuri yallaɓai in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba” tsaki kawai yaja yana nufar ya Naeem da dattijon
“kayi haƙuri baba kamar yanda su ka faɗa maka ba nan zaka shigar da ƙorafi ba, division dake cikin yankin ku za kaje ka shigar da ƙorafinka”
“yaro can ma naje basu amshi ƙorfina ba sai ma kallon mahaukaci da su ke man,wata jami'a ce tace na zo nan na nemi inspector hussain zai taimaka man”
“duk da haka baba kayi haƙuri zanyi maka kwatancen inda ƙanina ke aiki in sha Allah nayi maka alƙawarin zai taimaka maka” sai a time ɗin ya Naeem yayi magana
“A'a Usman,baba wane ƙorafi ne ka ke son shigarwa” ya Naeem ya faɗa yana mai da duba shi ga dattijon,da sauri yayi ma matarshi da yarinyar alama da su zo,in da su ke suka ƙaraso, hannu yasa ya yaye hijab ɗin dake jikin yarinyar,da sauri ya Naeem da Usman su ka rintse ido suna ambatar innalillahi wa Innah ilaihi raji'un lokacin da idanunsu su ka sauka akan cikin yarinyar,da alama operation aka yi mata bata samu kulawar likita ba,wurin ya rure yayi jaga jaga ga wasu irin ruwa masu wari da yake fitarwa
“yaro kaga halin da yarinyar nan take ciki amma babu mai son ya taimaka mata,an cutar man da jikata” da ƙyar ya naeem ya buɗe idonshi amma ya kasa kallon yarinyar “baba mi yasa ku ka baro asibiti da ita,wannan babbar matsala ce!?”
ɗaya daga cikin police ɗin ne yayi carab wurin faɗin “abunda muke faɗa mashi kenan amma ya kasa fahimtar mu” cikin kwantar da murya ya Naeem yace “baba idan kuɗi ne matsalar ku taimako ya kamata ku nema,kuma ga asibitocin gomnati nan”
wasu irin hawaye ne su ka wanke fuskar dattijon