x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 46 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 135001 words
  • 138000 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 475

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
muyi maganar” kallonta Mrs Malika take ba tare da tace komai ba, lamarin ne ke matuƙar bata mamaki,ta kasa gane me Nailar take nufi da wannan halin,ita dai a iya saninta ta san bata mata wani laifi da zaisa ta gujeta ba.
“baby ko dai nayi maki wani abun ne ba tare da na sani ba?”
“babu abunda ki ka man”
“to me yasa nake ganin kamar kina guduna,tsawan fa two month kenan bama tare amma kamar ba kiyi kewata ba”
“momy nayi kewarki mana”
“idan har da gaske ki ke to ki barni a nan na fi buƙatar kasancewa tare dake sama da komai” ta faɗa fuska a marairaice.
bed Nailarh ta nufa ta zauna bata san ya za tayi mata ba ta gane ko ganinta ba ta son yi.
bed ɗin Malika ta nufa,zama tayi kusa da Nailarh,hannunta ta kai saman hannun rigar dake jikin Nailarh,saurin ture hannunta Nailarh tayi tana faɗin “please mom,bana so” ran Malika ne ya ɓaci har bata san lokacin data rufe Nailarh da faɗa ba abunda bata taɓa mata ba kenan.
kuka Nailarh ta fashe mata da shi,hakan ba ƙaramin ƙara ɓata ran Malika yayi ba,ganin idan ta biyema Nailarh zata iya mata wani abun ne yasa ta fice daga ɗakin rai a ɓace.
Tana fita Aunty Sophia na shigowa kusan duk abunda ya faru a kunenta,rufe Nailarh da faɗa itama tayi dan me zatama Malika haka.
“Aunty Sophi bana sonta,na tsaneta,bana son taɓa jikina da take”
“kar na sake jin bakin ki ya sake furta baki sonta,karki manta Aure za ku yi nan da two weeks”
“a iya sanina baki son abunda take man,me yasa zaki sauya yanzu Aunty Sophia”
“ke ce ki ka sauya Nailarh,ki sani momynki na sonki,kuma wannan abun ba wani abu ba ne,nima ada ban fahimci son da take maki bane yasa bana so”
“ni dai bana sonta kuma bazan taɓa Aurenta ba”
“waza ki Aura kenan?” Aunty Sophia ta faɗa da sigar tambaya
“CEO ni shi nake so ba ita ba” wani irin kallo Aunty Sophia tayi mata “kin san kuwa abunda ki ke faɗa baby,mutumin da yayi sanadiyar kwanciyarki hospital shi ki ke so?” jinjina mata kai Nailarh “ina matuƙar son shi,ji nake bazan iya rayuwa ba idan babu shi” jin jina kai Aunty Sophia ta shiga yi,lamarin Nailarh ya fara bata tsoro,idan ba neman tashin hankali da momynta take ba taya zata faɗi haka.
lallashinta ta shiga yi tana nuna mata hakan ba mai yiwuwa ba ne,amma sam Nailarh ta kasa fahimtar ta.
Aunty Sophia ba su sake sanin abun na Nailarh da gaske ba ne sai data fara wasan ɓuya da momynta,duk wata hanya data san zata haɗata da ita tayi blocking,Malika tun tana ɓoye damuwarta harta kasa ga wata muguwar sha'awar Nailarh dake ɗawainiya da ita gashi Nailarh ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata.
karshe data kasa haƙura mamayar Nailarh tayi cikin dare ai kuwa ranar taga tashin hankali dan sosai Nailarh ta nuna tsanar da tayi mata a fili.
hakan kuwa baƙaramin ɓata ran Malika yayi ba har ya kaita da marin Nailarh abunda tunda uwarta ta haifeta wani bai taɓa mata ba,sosai saɓani ya shiga tsakaninsu Nailarh na iƙirarin komai Malika za tayi sai dai tayi amma Aurenta da CEO kamar tayi ta gama kuma sai ta bar mata gidan a yau.
murmushin Malika ta saki tana faɗin “yau na sake tabbatar da cewa Nailarh baki san ko wacece Malika ba,amma you will see the other side of me,zan tabbatar maki da ko ni wacece,you will regret” Malika ta faɗa tana gyaɗa kai.
wani shegen kallon Nailarh ta mata “i don't care about ko wacece ke,na riga na yanke hukunci bani babu ke,komai za kiyi Malika kin daɗe ba kiyi ba” Nailarh ta faɗa tana nufar dressing room ɗinta Dan ta rantse yau komai zai faru saita bar gidan.
A masifance Malika ta figota gaba ɗaya ta kifa ƙasa ƙugunta da kanta su ka bugu da ƙasa,ƙara ta saki ta azabar zafi,Aunty Sophia ce ta faɗo ɗakin hankali a tashe,luna ke sanar da ita abunda ke faruwa da Malika da Nailarh.
Malika bata damu da halin da take ciki ba ta fara magana.
“ke har kin isa kici Amanata, idanma bacci ki ke to ki farka,ki sani duk wani gata dana baki da ji dake da nake inayi ne dan biyan ɓuƙatata bawai dan kin kai matsayin nayi maki hakan ba,ke ba kowa bace a wurina face abun biyan buƙatata,ki sani akan biyan buƙatata zan iya kawar da duk wanda yace zai kawo man cikas,dan haka ke baki isa lokaci ɗaya ki sauya man ba,Aure tsakani na dake kamar anyi shi an gama,kuma shi wannan mutumin da ki ke magana ki sani daga yau babuke babu shi,idan kuma kin musa ki sani zan iya kawar dashi daga doran duniya?”
tashi Nailarh tayi daga ƙasa tana kallon Malika hawaye kwance cikin idanunta
“malika ban damu da abunda za kiyi ba amma ki sani muddin ki ka kashe shi nima saina kashe ki❗”
dariya Malika ta kwashe da ita “haka ki ka ce ko?”
“haka nace Malika,kuma a yau ba sai gobe ba zan bar maki gidan ki” jin jina kai Malika tayi “big mistake Nailarh” harara Nailarh ta watsa mata tana juyawa zata shiga dressing room ɗinta.
saurin riƙo hannunta Aunty Sophia tayi “Nailarh kina hauka ne,da mahaifiyar taki ke ke faɗa akan mutumin da baki san ko shi waye ba,ba kuma kisan dalilin da yasa ya shiga rayuwarki ba har ki ke iƙirarin zaki bar gida, kuskurene wannan Nailarh idan kin bar gidan ina zaki,kaf duniya baki da kowa bayan mahaifiyar ki,idan wani abu ke damunki tun wuri ki dawo hayyacinki”
“ban damu da dalilinshi na shiga rayuwata ba,ko shi waye iya abunda na sani ina sonshi ko da kuwa da wata manufa ya shiga rayuwata”
“baby wannan hauka ne, mahaifiyar ki ba abar da zaki wulaƙanta bace”
“Aunty Sophia wannan matar ko zata kashe ni bazan mata abunda take so ba,na tsaneta kima bar ɓata bakinki” tana gama faɗa ta shige dressing room ɗin.
kallon Mrs Malika Aunty Sophia tayi harta buɗe baki za ta yi magana Malika tayi saurin ɗaga mata hannu
“ba sai kince komai ba Sophia dole na nunama Nailarh kuskurenta,zan tabbatar mata da ƙarfin ikona akanta,sai tayi data sanin sanina a rayuwarta” hankalin Aunty Sophia ne ya tashi jin abunda Malika tace,ta san ko wacece Malika zata iya aikata komai akan biyan buƙatarta.
“ma'am Nailarh yarinya ce,idan ki...” bata ƙarasaba Malika tayi saurin ɗaga mata hannun “ko me za kice Sophia bazan saurareki ba,nafi ki sanin Nailarh yarinya ce amma zan nuna mata tsantsar yarinta” tana gama faɗa ta nufi ƙofar fita ta fice,da kallo Aunty Sophia ta bita tana jin wani iri a zuciyarta dama ta san dole hakan ta faru idan har Malika ta san Nailarh ba ita take so ba,tashin hankalinta hukuncin da Malika zatama Nailarh.
dressing room ɗin Nailarh ta nufa tana kiran sunanta.
samun Nailarh har ta sauya kayan jikinta ta shirya wasu kayan cikin box.
lallashinta Aunty Sophia ta shiga yi tana bata haƙuri akan ta zauna,amma bata bi ta kanta ba dan yanzu har ita haushinta take ji,dan gani take kamar tana goyan bayan Malika ne,tana gama ɗaukar duk abunda zata ɗauka taja box ɗinta ta fice ba tare da ta ko kalli Aunty Sophia ba.
girgiza kai kawai Aunty Sophia tayi bata san me zatama Nailarh ta gane kuskuren faɗa da Malika da take ba,bin bayanta tayi tana shiga bedroom ɗin wasu jibga jibgan ƙati daga cikin securitys ɗin gidan na shigowa Malika na bayan su,hannunsu ɗauke da ɗan wani madaidaicin box,wani irin faɗuwa gaban Aunty Sophia yayi da sauri ta nufi Malika
“please ma'am na roƙe ki karki kiyi haka,Ni da kaina zan shawo maki kanta karki kice zaki hukuntata”
ko kallon inda Aunty Sophia take Malika ba tayi ba.
box ɗin dake hannunta ta ajiye buɗe box ɗin tayi,kwalaben allura ne ciki sai tururi suke na sanyi
“kar kiyi haka Malika Nailarh na sonki kawai yarinta ce ke damunta,amma idan ki ka ce zaki mata allurar nan lafiyarta zata samu matsala, Please karki mata allura”
“sophia miye matsalarki da abunda zan yi mata, Nailarh ƴata ce ina da ikon hukuntata yacce na so” tunda su ka fara taƙaddama Nailarh na tsaye tana kallonsu ko a jikinta iya abunda ta sani ko mai zai faru bazata bari suyi mata allurar nan ba.
“na sani Madam,amma ki sani idan ki ka kasheta babu abunda zai sauya,Please kiyi tunanin” murmushi Malika ta daki “nafi ki sanin babu abunda zai sauya Sophia,bana buƙatar Nailarh a yanzu,samun wacce zata maye man gurbinta ba abu bane mai wahala a wuri na” Malika ta faɗa tana miƙama ɗaya daga cikin security allura,da kai ta basu umarni da suyi ma Nailarh allura.
hawaye ne su ka wanke fuskar Aunty Sophia Bata taɓa tunanin Malika zata iya kawar da Nailarh ba.
gadan gadan wanda babu allura ya nufi Nailarh,yana kai hannu zai riƙota ta kai mashi naushi a ido saurin ja da baya yayi yana dafe idonshi,saurin ajiye allurar dake hannunshi ɗayan yayi yana nufarta,da gudu ta juya ta nufi ƙofar toilet ɗinta sai da kafin ta buɗe ƙofar har ya cimmata,damtse hannunta ya kamo ya fisgota baya,gaba ɗaya ta tafi ƙasa,ɗagowar da za tayi ta sakar mashi naushi a gefen ciki,dambe ta shiga yi da su kafin Allah ya bashi sa'a ya sauke mata lafiyyan mari da gaba ɗaya ta faɗin kan floor,rintse ido Aunty Sophia tayi hawaye na bin cheek ɗinta,wata ƴar iskar dariya Mrs Malika tayi tana faɗin “good job,kumata dukan mutuwa idan taƙi tsayawa”
wanda ta dakar ma ido ne ya ɗagota,wani wahalallan naushi ya kai mata aciki,jini ne ya shiga fitowa ta hancinta,da gudu Aunty Sophia ta fice daga ɗakin dan bazata iya jurar ganin rashin imanin da Malika tasa su yima Nailarh ba,shiyyasa kullum take bata shawara amma Nailarh ba taji ba,ta san wacece Malika sosai,muguwace ta ƙarshe amma Nailarh ta kasa fahimta.
Kamar sun samu jaka haka su ka shiga dukanta sai da su ka ga ta daina motsi tukun su ka ƙyaleta, Malika na daga zaune tana kallonsu,ko a jikinta hakan ma ba ƙaramin daɗi yayi mata ba.
da kanta ta ɗauki allura tayi mata,umarni taba security da su ɗauketa,a kafaɗa ɗaya ya saɓata su ka fice daga ɗakin.
wayar Nailarh da laptop ɗinta Malika ta ɗauka ta bi bayan su,a bakin ƙofa ta samu Aunty Sophia,kuka kawai take musamman da taga yanda su ka fito da Nailarh.
wuce Malika tayi,part ɗinta ta nufa,a tsaye ta samu security a bakin ƙofar wani daki dake part ɗinta.
buɗe ƙofar ɗakin tayi suka shiga da ita ciki,cikin ɗakin su ka shiga da Nailarh,ɗakin baya da girma,ɗan ƙaramin bed ne a ciki ko window ɗakin baya da ita kamar ɗakunan prison.
a saman bed ɗin ɗakin ya jefar da ita,ficewa su ka yi daga ɗakin,maida ƙofar ɗakin Malika tayi ta rufe haɗi da dannan wasu Numbers jikin ƙofar wanda ba tantama security ne tasama ƙofar..

*ABUJA NIGERIA*

yau ta kasance ranar juma'a ranar da uncle Jonas yace za su zo,tun jiya dady yasa yumnah tasa masu aiki su ka gyara part ɗin sam,bai sanar da su harda Sam za'a zo ba sai a yau da safe,zo kaga murna wurin yumnah musamman laatifa,kiran Number wayan shi ta shigayi amma bata samu ba,tunani ta fara ko har sun taho ne.
da gudu yumnah ta nufi ɗakin su dan ta sanar da Nainarh zuwan sam ɗin ta san dole tayi farin ciki may be ma haka yasa ta daina fushin da take da ita.
tana shiga ɗakin Nainarh na fitowa daga toilet,bathrobe ne a jikinta da alama wanka tayi,da gudu yumnah ta nufeta “sis labari mai daɗi” kallonta Nainarh tayi ba tare da tace komai ba,yar dariya yumnah tayi tana faɗin “kin san cewa harda ya sam a cikin masu zuwa,yanzu dady ke sanar da mu, Nainarh ba kiji daɗin da naji ba Finally dai Allah ya amshi Adu'ar ki ya Sam zai zo Nigeria bayan tsawan shekaru,am very happy to you” ta kai ƙarshen maganar tana sakin murmushi haɗi da kallon Nainarh,ga mamakinta ko a fuska ba taga alamun labarin yayi ma Nainarh daɗi ba,abun ya ɗaure mata kai,duk irin son da Nainarh kema sam amma ta faɗa mata cewa zaizo amma ba tayi farin ciki ba
“nainarh wai me ke damunki, ya sam fa nace maki yana hanya?” kauda kai Nainarh tayi tana raɓawa ta gefenta ta nufi dressing room ɗin su, hooking yumnah tayi a nan tsaye lamarin Nainarh ya fara bata tsoro,anya ba aljanune suka shiga jikinta ba,gaba ɗaya ta canza idan wani yace mata Nainarh za tayi action irin wannan idan taji labarin zuwan sam baza ta taɓa yarda ba.
bayanta tabi zuwa dressing room ɗin,harta kama handle ɗin ƙofar zata buɗe ta fasa,ta ƴar ƙofar dake jikin ƙofar ta leƙa cikin ɗakin,zaro ido tayi lokacin da idonta ya sauka kan Nainarh da tayi sujjudu shukur a tsakar ɗakin,bata gama fita daga mamakin ba Nainarh ta miƙe ta shiga taka rawa tana faɗin “Allah Alhmdllh, Alhmdllh Allah na gode maka,ya Allah kacika man buri na, Allah kasa na samu soyayyar shi cikin sauƙi, gaskiya nayi farin ciki Alhmdllh” ta faɗa tana sakin dariya kamar zautatta, yumnah bata san lokacin da itama ta saki dariyar ba ko ba komai ta san ƴar uwarta tata lafiyar ta lau kawai fushin da take da ita ne ya hana ta nuna farin cikinta.
saurin barin bakin ƙofar tayi dan karma Nainarh ta fahimce tana kallonta,ficewa tayi daga ɗakin.
shirye shirye su ka shiga yi na tarbar baƙi,dady kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar farin cikin da yake ciki hakama mom,su ya Naeem tun wuraren ƙarfe 10 na safe su ka zo gidan tare da su Aunty Nadeeya,mom Maryam ma ta zo tare da su Ammar,ta zo duba jikin kainart da taji labarin zuwan su sam ɗin ne yasa ta tsaya.
Ƙarfe 4 na yamma mazan suka nufi airport Dan tarbosu harda uncle mustapha,ƙarfe 5 jirginsu zai iso amma dady yace su tafi da wuri,ya ƙosa yayi ido biyu da sanyin idaniyarshi, yumnah babu yanda bata yi ba dan a tafi da su amma ya Naeem yace A'a, Laatifa ma ta so tare da su za'a je Airport ɗin amma da ya Naeem ɗin yace A'a sai ta hakura.
Ƙarfe biyar daidai aka fara sanar da isowar jirgin daya ta so daga los Angles California,zambur dady ya miƙe daga saman waiting chairs ɗin da su ke zaune,fuskarshi ɗauke da murmushi ji yake kamar ya nufi filin jirgin ya taraso a can,farin cikin shi ya kasa ɓoyiwa,zuba mashi ido su ya Adnan su ka yi ya Naeem na faɗin “gaskiya dady mun fara kishi,irin wannan damuwa haka” murmushi dady yayi mashi “baza ka gane bane Naeem” murmushi ya Naeem ɗin yayi yana girgiza kai.
passengers ne su ka fara ɓullowa ta ƙofar da aka rubuta Arrivals.
mutane ne suka shiga fitowa ɗauke da boxs ɗin su.
tunda passengers su ka fara fitowa su ka baza ido burin su kawai su ga ta inda za su ɓullo.
Wani kyakkyawan baturen matashin tsoho ne ya ɓullo daga ƙofar,sanye yake cikin blue black ɗin suit, idanunshi a manne suke da farin glasses,sumar kanshi kamar ba ta dattijo ba sai sheƙe take tana ɗaukar ido,fuskarshi ɗauke da murmushi yayinda wasu zaratan samari masu jini a jika ke biye da shi su biyu,hannunsu riƙe da trolleys ɗin su,ƙananan kaya ne a jikinsu,Allah yayi su da surar jiki mai matuƙar jan hankali,fuskokinsu a rufe su ke da mask,walking majestically su ke nufo cikin filin airport ɗin.
su dady ne su ka nufo su fuskokinsu ɗauke da murmushi,hugging juna dady su kayi shida wannan dattijon yana masu barka da zuwa,raba jikinsu suka yi,kallon wannan samarin dady yayi fara'ar fuskarshi na daɗa ninkuwa,ɗaya bayan ɗaya suka shiga hugging ɗin su dady ba tare da sun zame mask ɗin dake fuskokinsu ba,kasa haƙuri dady yayi har sai da yace “wai baza ku ɓuɗe fuskokin ku ba ne” dan ya fara zargin wani abu daga muryoyinsu,zame mask ɗin su ka yi suna sakin murmushi da ya ƙarama fuskokinasu kyau,Masha Allah na furta a yayin da nayi arba da fuskokin kyawawan samarin,kyawawa ne na gaske,komai nasu iri ɗaya hatta gyaran gashin su iri ɗaya ne kamar twins haka su ke,launin fata ne kawai ya banbanta su sai zanen tatto da earring da ɗaya ke dashi wanda ko ba'a faɗa maka waye shi ba tsananin kamar da yake da dattijon nan da yumnah zai tabbatar maka da ɗan sa ne,ɗayan kuwa kallo ɗaya zaka mashi ka hango kamaninshi da mahaifiyar sa Aunty mariya.
yanayin fuskar dady ne ya sauya,a hankali ya furta “james,Alyar!” da fa'arsu su ka amsa mashi
“ina sam ɗin yake?” ya faɗa yana bin fuskokinsu da ido, kallon juna su ka yi fara'ar dake fuskokinsu na ɗauke,kasa ce mashi komai su ka yi,cikin ƙunar rai ya ce “yanzu ma bai zo ba?” jinjina mashi kai su ka yi “eh dady, uzuri ne na gaggawa ya taso mashi shiyyasa bai zo ba”
hawaye ne su ka taru a idonshi dama ya daɗe yana tunanin ta yarda sam zai biyo su cikin sauƙi ba tare da gardama ba.
cikin tsantsar ɓacin rai ya shiga faɗin
“wai me sam yake nufi da ni ne a rayuwar nan,me na aikata mashi da yake wannan fushin da ni,Ni mahaifinshi ne amma ya ɗauki karan tsana ya ɗaura man,irin tsanar da yayi man ko maƙiyinshi bai kamata yayi ma ita ba,na lura yafi son mutuwa sama da rayuwata,kullum cikin azabtuwa nake da soyayyar shi,amma hakan bai sa yayi man adalci ba,nayi ban haƙurin,nayi lallashin,ban san iya adadin zuwan California dan na ganshi ba,amma duk a banza haka zan ƙaraci zamana na dawo ba tare da na ganshi ba,me sam ya ke so nayi mashi wanda zai sa ya fahimci halin dana shiga saboda rashin shi a tare da ni,me zan mashi wanda zai sa ya fahimci irin son da nake mashi???” ya kai ƙarshen magana hawayen dake kwance cikin idonshi na bin cheek ɗin shi,da sauri uncle Jonas yasa hannu yana goge mashi hawayen,babu wanda jikinshi baiyi sanyi ba a wurin ba
“kayi haƙuri Tahir, uzuri ne ya taso mashi kamar yarda Alyar ya faɗa,da badan uzurin mai girma ba ne nima da bazan barshi ba,amma ya tabbatar man da yana nan zuwa kafin mu tafi,kayi haƙuri” uncle Jonas ya faɗa
“baya son ganina
End Ads