kai duban su gareta har ta ƙaraso gaban bed ɗin Nailarh
“hi Miss Nailarh,how was ur body,hope u feel better now” ta faɗa cike da kulawa tana sakar ma Nailarh murmushi,jin jina mata kai Nailarh kawai tayi,kallon Mrs Malika da Aunty Sophia tayi “good morning” da ƴar fara'a Aunty Sophia ta amsa mata,Mrs Malika kuwa ko kallon inda take ba ta yi ba,dan yanzu gaba ɗaya haushin su take ji, warmers ɗin dake kan trolley ta shiga buɗewa,Wheat Bread,Greek Yogurt,cup of milk,fresh fruit,Chicken and etc.
wani kallo Mrs Malika ta watsama nurse ɗin ganin tana shirin sarving Nailarh tace “hi! wait,We also brought food for her,so take yours and go out”ɗan murmushi Nurse ɗin tayi
“sorry ma'am na sani,amma wannan shi ne ya dace ta ce saboda lafiyarta”
“mu ma wanda mu ka zo dashi zai taimaka ma lafiyar ta,kawai ki kwashe kayan ki”
“I'm sorry ma'am hakan bazai yiwuba”
“saboda mi”
“umarnin CEO ne wannan shine abincin da za taci”
“u and your CEO idiot” murmushi kawai nurse ɗin tayi tana maida hankalinta kan abunda take
“She won't eat this food” Mrs Malika ta faɗa tana nufo bakin bed ɗin,da sauri Aunty Sophia tace “please ma'am kiyi haƙuri,sun fi mu sanin mi ya dace da Nailarh Please”
“baza taci wannan abincin ba Sophia” tsayawa Nurse tayi tana kallon Mrs Malika cike da mamaki tunani ma ta fara anya lafiya take,dan duk wanda ke zuwa hospital ɗin nan ya san cewa su ke ba patient abinci to miye matsalar wannan matar
“sophia haɗa mata coffee ki Bata,ke fita da kayan ki”
“mom please enough” Nailarh ta faɗa da ɗan tsawa duk da rashin ƙarfin jikinta,da sauri ta nufi Nailarh“am very sorry,kawai bana son abunda zai cut...” Bata ƙarasa ba Nailarh ta ɗaga mata hannu
“bana son jin wata hayaniya,be quite” saurin kama bakin Mrs Malika tayi tana faɗin “okay ok ” kallon Nurse ɗin Nailarh tayi a hankali ta furta “sarv me” murmushi Nurse ɗin ta sakar mata, sarving ɗinta ta shiga, milk ta fara haɗa mata kafin ta ɗaura mata two sliced of Wheat Bread a saman plate sai Greek Yogurt with berries sai boiled chicken drumsticks,bayan data kammala haɗa mata,tai maka mata tayi zuwa toilet dan ta wanke bakinta,a hankali take taka ƙafarta har zuwa toilet ɗin,sai da tayi brush ɗin tukun su ka dawo ɗakin,kan bed ɗin Nailarh ta koma yayinda Nurse ɗin ke nufar food trolley ɗin,cup of milk ta fara miƙa mata
“thank u” ta faɗa tana amsa,wani banzan kallo Mrs Malika ta watsama nurse ɗin tana kauda kai gefe,sai data sha ɗan rabin cup tukun ta janye baki
“I'm sorry duka zaki shanye” Nurse ɗin ta faɗa kallonta Nailarh tayi “it's CEO'S odar” murmushi Aunty Sophia ta saki ganin yanda Nailarh ta wani juya ido alamar an dameta fa,tsaki kawai Mrs Malika ta saki tana kallon gefe itafa ba komai ke damunta ba sai kishin Nailarh,ta tsani taga wani na raɓarta,tas ta shanye milk ɗin kamar yanda Nurse ɗin ta faɗa mata, Wheat bread ta nuna mata,sliced ɗin ta ɗauka ta ci,bowl ɗin farfesun kaza ta miƙa mata,Aunty Sophia ta miƙama bowl ɗin,amsa Aunty Sophia tayi,a hankali ta shiga bata,tas ta shanye shi dama dai dai wanda zata iya shanyewa ne,robar greek Yogurt ɗin ta miƙa mata,Aunty Sophia ta buɗe roɓar haɗe yake da fresh barriers,Aunty Sophia ta shiga bata sai ɓata fuska take saboda ba zaƙi unsweetend ne,murmushi kawai Aunty Sophia ke saki,wayar Miss Malika ce ta fara ringing, da sauri marry ta miƙo mata wayar data ciro daga cikin jakan Mrs Malika,amsar wayar tayi tana duba sunan mai kiran nata,ɗan murmushi ta saki tana picking call ɗin,can cikin ɗakin ta nufa dan amsa wayar,sosai ta sha Yogurt ɗin duk da bawai yayi mata daɗi bane sai takura matan da Aunty Sophia tayi,sai da tasha da yawa tukun Nurse ɗin ta shiga bata magungunan ta, injection ɗin dake ciki kuma sai anjima idan Dr ya zo,wurin Mrs Malika ta nufo da waya a hannunta,miƙama Nailarh wayan tayi “baby dady na magan” saurin kallonta Nailarh tayi,hakama Aunty Sophia “amsa mana, yana so ya ji ya jikin ki” kauda Nailarh tayi yanayin fuskarta na canzawa zuwa tsantsar ɓacin rai “please baby ki amsa mana” Mrs Malika ta sake faɗa, ko kallon in da take Nailarh ba tayi ba,wayar tasa a speaker daga cikin wayar Muryar mutumin ta bayyana
“hello Nailarh” wani ɗan iskan kallo Nailarh ta watsama wayar without answering him
“baby are you hear me” ya sake faɗa,banza Nailarh tayi da shi,ajiyar zuciya ya sauke, a hankali yace “ya jikin naki,fatan da sauƙi,ina nan shigowa next week na dubaki” wani ɗan iskan tsaki taja tana ƙoƙarin sauka daga saman bed ɗin,saurin riƙeta Aunty Sophia tayi tana girgiza mata kai,ran Mrs Malika ba ƙaramin ɓaci yayi ba ta tsani wannan wulaƙancin da Nailarh ke mashi “baby are u Angry with your dady?” ya faɗa cikin kwantar da murya,hararar wayar tayi “who are you to said that,you will never be my father forever”
saurin cire wayar Mrs Malika tayi a speaker tana kara ta a kunenta “I'm sorry I will call u later” Bata jira jin mi zaice ba tayi rejecting call ɗin,rai a ɓaci ta kalli Nailarh
“baby mi yasa ki ke haka,ya damu da ya san halin da ki ke ciki shine zaki mashi haka??” ko kallonta Nailarh ba ta yi ba “mi yasa ko wane lokaci ki ke son wulaƙantashi,shifa Kamar mahifinki ne” sai a sannan Nailarh ta kalleta “he's not my father,I hate him”rai a ɓace Mrs Malika ta buɗe baki da nufin magana Nurse ɗin tayi saurin cewa “Be patient Ma'am, this may affect her health, I'm sorry” sai da nurse ɗin tayi magana tukun ta tuna da condition ɗin Nailarh,iska mai zafi ta furzar daga bakinta,har ta nufi sofa sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin rai a ɓace,ko kallonta Nailarh ba tayi ba,kwantar da kanta tayi jikin pillow haɗi da lumshe idanunta,Aunty Sophia just looked at her without saying anything,hannunta ta kama,note ɗin dake jikin hannunta Aunty Sophia ta zubama ido,buɗe ido Nailarh tayi tana kallonta,rufe mata hannun kawai Aunty tayi ba tare da tace mata komai ba itama Nailarh ɗauke idonta tayi, ficewa Nurse ɗin tayi,bayan kamar 2 minutes da fitarta wata Nurse ta shigo ɗauke da gown da body lotion cikin ɗakin ta nufo,gaishe da Aunty Sophia tayi kafin ta kalli Nailarh,ya jiki ta fara tambayarta kafin tace “It's time to take a bath ma'am” Nailarh looked at her before she looked away, da sauri Aunty Sophia tace “ok, bring the gown and I will help her to take a bath, thank you” ba tayi musu ba ta bata gown ɗin,zama tayi kan chair dake gaban bed ɗin, taimaka ma Nailarh Aunty Sophia tayi zuwa toilet,Sosai toilet ɗin ya haɗu kamar a gida,duk wani abu da za su buƙata akwai a ciki,ruwa Aunty Sophia ta haɗa mata,sanin halin Nailarh da koda tana lafiya ba wanka take da kanta bane yasa Aunty Sophia ta taimaka mata tayi,wani iri Aunty Sophia taji wannan shine the first time tayi ma Nailarh wanka bayan ta girma,hawaye ne su ka taru a idanunts lokacin da ta tuna yarintar Nailarh,da sauri tasa hannu ta goge kafin Nailarh ta gani,shaf shaf ta taimaka mata tayi wanka har ta canza mata rigar jikinta ta shafa mata lotion,ficewa su ka yi zuwa ɗakin,Nurse ɗin kaɗai su ka samu su luna sun fice da alama wajen Mrs Malika su ka nufa, taimaka mata tayi ta koma saman bed,kwanciya tayi,duvet Aunty Sophia ta ja mata ta rufe mata rabin jikinta,lumshe ido tayi kamar mai bacci,gown ɗin Nailarh ta cire Nurse ɗin ta kwashe ta fice.
*ABUJA NIGERIA*
gaba ɗayan su ne a bedroom ɗin mom ya Naeem,ya Adnan sai Irfan,mom na daga zaune gefen bed ɗin ta yayin da ya Adnan ke zaune saman stool a gaban mirror sai ya Naeem dake zaune kan sofa shida Irfan,tunda su ka fara magana kan Auren shi da Noor ƙala baice masu ba kanshi na ƙasa,ɗaya bayan ɗaya yake sauraren su
“idan har ba so ka ke kaga ɓacin raina ba,ka ƙyale masu ƴarsu kawai kaje ka nemi wata,Allah zai baka wacce ta fi ta” mom ta faɗa tana kallon Irfan ɗin
“akwai ƙanwar Usman abokin aikina yarinyar tana da hankali ga tarbiyya,Ni zan mashi magana sai kaje ka ganta idan tayi maka shikenan a gidan shi take zaune” ya Naeem ya faɗa yana kallon Irfan ɗin
“idan ba tai maka ba ma ga Kairiyyah nan ɗiyar Aunty Adama sai ka nemeta,tama fi Noor natsuwa da komai,kuma Mahaifinta bazai hanaka ba ko ita Aunty Adama” a cewar ya Adnan
“gaskiya bazan iya da tashi hankalin mama Ameenah ba,kawai ni nayi mashi alƙawarin ƴata indai har yana so,dama tuna farko ita nake da burin ya Aura ba Noor ba” sai a lokacin Irfan ɗin ya ɗago ido ya kalli mom,gaba ɗaya su ka zuba ma mom da tai magana ido,ya Adnan ne yace “dama kina da wata ƴar ne bayan Yumnah bamu sani ba?”
“NAINARH nayi mashi alƙawarin ta muddin yana so” tunda mom ta fara magana gaban Irfan ya faɗi,wani irin mugun ɓacin rai ne ya rufeshi, mom tama rasa wa za tace ya Aura sai wannan yarinyar,ya Adnan da ƙyar ya haɗiye wani abu daya tsaya mashi a maƙoshi,kwata kwata baiyi tunanin mom za tace haka ba,ajiyar zuciya ya Naeem ya sauke yana faɗin
“gaskiya tana da hankali da natsuwa uwa uba tarbiyya da Ilmi, gaskiya naji daɗin jin haka mom,wlh ni ban ma yi wannan tunanin ba saboda ganin halin da take ciki,kinga idan ya Aureta hakan zai rage mata raɗaɗin rashin iyayenta,amma mom dangin Mahaifinta kina ganin za su Amince?”
“wannan ba matsala bace Naeem,tunda mahaifinta ya rasu su ka datse duk wata alaƙa dake tsakanin su da ita”
“duk da haka mom,dole su sani”
“zan sanar da su amma sai in ya Amince itama ta aminta da shi tukun,idan duk sun amince sai na sanar da su yanda idan ba su amince ba ina da right ɗin da zan maka su a Court” kallon Irfan ɗin ya Naeem yayi “kaji abunda tace,minene ra'ayinka akan hakan,kana sonta ko dai mu bari kayi tunani”
“yaya mi yasa baza ku fahimce ni ba, ni gaskiya bazan iya son wata ba bayan Noor” da mugun sauri su ka shiga kallonshi, wato duk bayanin da suke da bashi haƙuri ba fahimtar su yake ba “dan mom fatilah Bata son Auren ai ba ita zata ban Aurenta ba kuma ba da ita zan zauna ba ni gaskiya Noor nake so,dukan ku ba wanda hakan bata faru ba lokacin Auren shi kuma ai kuna zaune lafiya,sai ni za a hana ni,ni gaski...” bai ƙarasa ba ta dalilin marin da ya Naeem ya ɗauke shi da shi,dafe cheek ɗin shi yayi yana kallon ya Naeem da kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar ɓacin da ranshi yayi,tashi Irfan ɗin yayi rai a ɓace ya nufi ƙofa,kuka mom ta fashe dashi,da sauri ya Adnan ya nufo inda take,hannunta ya kama cikin nashi “dan Allah mom Kar wannan abun da yayi ya ɓata ranki,wallahi ko yana so ko bai so bazai Aureta ba” tashi ya Naeem yayi ya nufi Irfan ɗin dake bakin ƙofa
“wannan yanayin ka ke son gani a tare da ita,to bari kaji na faɗa maka, kai baka isa ta dalilinka ka hana mata zaman lafiya ba,dan mun zauna muna baka haƙuri it doesn't mean cewa bazamu iya tursasamaka ba,wllh kaji na rantse baka ba wannan yarinyar”
“haba second father dukan ku kun Auri muradin ranaku sai ni ne zaku hana”
“ka dai ji abunda na faɗa maka,idan kuma ban isa ba to”yana faɗa hakan ya bar wurin ya nufi mom,ya Naeem yana da saurin fushi amma yana da saurin sauka.
*Ep 41_42*
____________________________
Ficewa Irfan ɗin yayi rai a ɓace,karo su ka yi da juna,gaba ɗaya mug ɗin Coffeen dake hannunta ya zube mata a jiki,sakin trayn tayi tana fasa wata irin gigitaciyar ƙara saboda azabebben zafin daya ziyarci ganganr jikinta,gaba ɗaya coffeen ya wanke gaban rigarta da hannunta da ƙafarshi,kuka take sosai tana yarfe hannu,kallo ɗaya yayi mata ya bar wurin,A 360 mom ya Naeem, ya Adnan da dady wanda kusan akan idonshi komai ya faru su ka faɗo parlorn, dan ƙarar da Nainarh tayi har cikin ƙwaƙwalen su, gaba ɗaya kanta su ka yi,a ruɗe ya Adnan yake tambayar mi ya sameta,daƙyar ta iya faɗa masu abunda ya faru da ita, sannu su ka shiga jera mata, ya Adnan ji yake kamar ya cire mata azaban da take ji, kamata yayi zuwa sofa, bin bayansu su ka yi zuwa cikin parlorn, kuka take sosai har ga Allah ba ƙaramin zafi take ji ba
“sannu kinji kukan ya isa haka muga hannun”dady ya faɗa, mayafin dake kanta daya rufe hannun mom ta janye tana kallon inda ta ƙone,wurin yayi ja sosai, da sauri ya Adnan ya miƙe ya nufi kitchen, da gudu Yumnah ta faɗo parlorn ita da Fa'iza, wurin Nainarh su ka nufa hankali a tashe “sister mi ya sameki?” Yumnah ta faɗa kamar itama za tayi kukan
“mom mi ya sameta?”a cewar Fa'iza
“ƙonewa tayi” mom ta bata amsa, zaro ido Yumnah tayi tana yarfe hannu “wayyo Allah nah, garin yaya ki ka ƙone!?” a hanzarce ya Adnan ya dawo parlorn ɗauke da ɗan madaidaicin silver bucket mai ɗauke da ƙanƙara, da sauri yumnah ta tashi daga gaban Nainarh, hannun Nainarh data ƙone ya kama yasa a cikin ƙanƙarar,sake fashewa da kuka tayi tana faɗin “wayyo hannuna, mom zafi”
“sannu kinji, zai daina in sha Allah” a cewar dady
“yumnah bani towel” ya Adnan ya faɗa, da gudu ta tashi ta nufi bedroom ɗin mom sai gata ta dawo riƙe da ɗan madaidaicin towel, miƙa mashi tayi da sauri ya amsa yana sakashi cikin bucket ɗin,sai da yayi kamar five seconds tukun ya ciro shi, ɗan ruwan dake jiki ya matse, gaban rigar Nainarh ya nufa, da sauri mom ta amshi towel ɗin ganin abunda yake shirin yi “ya isa haka” ta faɗa
wallahi gaba ɗaya a ruɗe yake shi kanshi bai san mi yake shirin yi ba burinshi kawai ta samu sauƙi, har cikin zuciyarshi yake jin kukanta, gyalen dake saman kanta mom ta zame, ɗan zaro ido tayi ganin wurin yayi ja sosai fatar wurin har ta ɗan taso, da sauri ta ajiye towel ɗin, kama hannun Nainarh tayi tana faɗin “tashi muje hospital kawai,Yumnah ɗauko mana hijab, Adnan muje hospital kawai” da sauri su ka miƙe gaba ɗayan su, bedroom ɗin su Yumnah ta nufa a hanzarce “lafiya dai ko barrister?”
“to ƙone ne sosai, wurin har ya tashi”
“mom to ki bari a kira dr fawwar sai yazo ya dubata” acewar ya Naeem, da sauri ya Adnan yace “ko kafin ya iso wutan ya gama shiga jikinta, mu tafi kawai” a hanzarce Yumnah ta dawo riƙe da hijab ɗin Nainarh har ta zura nata a jiki, da sauri mom ta amsa ta sa ma Nainarh,bedroom ɗinta Yumnah ta nufa hijab ta ɗauko mata, Nainarh banda hawayen azaba babu abunda take har cikin cikinta take jin zafin, mug uku ne ya zube mata a jiki, dama da suka shigo ya Adnan ya ce ta kawo mashi coffee, ganin suna tare da ya Naeem da mom ne yasa ta haɗo da su dan bata ma san Irfan na gidan ba, coffeen da zafinshi yana turiri, shiyyasa take jin zafi sosai ga fatarta bawai ta saba da wahala bane,amsar hijab ɗin mom tayi ta zura a jikinta,Fa'iza gyara zaman mayafin dake jikinta tayi su ka fice dady kawai su ka bari,Ishrat yayi ma magana ta zo ta gyara wurin kafin ya wuce sama.
Motar ya Adnan su ka shiga, ya Naeem na kusa dashi yayinda yake zaune a mazaunin driver mom da Nainarh na baya, Yumnah kuwa motar Fa'iza su ka shiga, ficewa su ka yi daga estate ɗin, motocin securitys ɗin su na gaba wasu na baya,time to time yake leƙo back seat yana ma Nainarh sannnu ya Naeem sai kallonshi kawai yake.
Irfan yana ficewa daga parlorn motar shi dake parking space ya nufa, rai a ɓace ya buɗe marfin motar ya shiga,a tsiyace ya rufe motar kamar zai balla marfin,kifa kanshi yayi saman Steering wheel wani irin tafarfasa zuciyarsa ke mashi,sai a time ɗin ma ya ji zafin ƙonewar da yayi,kallo ƙafar yayi yana jan wani mugun tsaki,key yayima motar ya fice daga Estate ɗin,direct S I hospital ya nufa,wani mahaukacin horn ya buga lokacin da ya isa bakin gate din hospital ɗin,da mugun sauri securitys su ka buɗe mashi, a 80 ya shiga ciki kaɗan ya rage bai ture ɗaya daga cikin securitys ɗin ba,da ido su ka bishi, parking space ɗin da aka tanada domin su Dr's ya nufa, parking yayi,fitowa yayi bayan ya gama daidaita parking a zafafe ya maida marfin motar ya rufe,da ido ɗai ɗai kun mutanen dake kai kawo cikin hospital ɗin su ka bishi,yana da girma sosai hospital ɗin, abun kamar ba'a 9ja ba,ginin skyscraper ne hawa huɗu,ta ko ina ƙyallin glasses ne masu ɗaukar ido,cikin hospital ɗin ya nufa,yana shiga reception nureses ɗin dake wurin su ka shiga russunawa suna gaishe dashi,ko kallon inda su ke baiyi ba bare su sa ran zai amsa masu,da kallo kawai su ka bishi har ya shige elevator,da yawan ƴan matan dake wurin ji su kayi kamar su bishi suji mike damunshi,da yawansu dakwan wata irin azababbiyar soyayyar shi su ke amma ko kallon banza babu wacce ta ishe shi a cikin su.
katafaren office ɗin shi dake can 3rd floor na hospital ɗin ya nufa,a bakin ƙofar office ɗin ya tsaya,key yasa ya buɗe ƙofar office ɗin ya shiga,sanyayyan ƙamshin dake tashi a office ɗin ne ya daki hancinshi,dum light ne a office ɗin, switch ya nufa ya kunna,haske ne ya gauraye office ɗin, office ɗin yana da girma sosai ga wasu expensive office desk black color,ga book shelf mai matuƙar kyau,sai fridge, cikin office ɗin ya nufa,executive chair dake gaban desk ya nufa ya zauna,kifa kanshi yayi saman desk,wani iri yake ji a zuciyarshi kamar zata kama da wuta tsabar ɓacin rai, bakomai ke ƙara ɓata mashi rai ba face marin da ya Naeem yayi mashi da kafewa da su ka yi akan bazai Auri Noor ba,kawai dan yana masu biyayya it doesn't mean cewa zasu tauye