x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 34 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 99001 words
  • 102000 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 468

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
yumnah ta faɗa kamar za tayi ku ka,sadda kai tayi ƙasa hawaye na bin cheek ɗinta ɗan ajiyar zuciya mom ta sauke,kama hannunta tayi
“tashi muje kiyi sallah kinji” bin mom ɗin tayi har bedroom ɗin ta, bayan su su Nainarh su ka bi amma mom tace su wuce kawai wajen dady,juyawa su ka yi zuwa part ɗin dady,sun ɗan jima a part ɗin dady kafin su ka fito duk da ba karatu yayi masu ba,tun da Nainarh ta ƙone ba suyi karatu ba yaune ma taje part ɗin dady dan ta gaishe da shi.
Laatifa bayan da ta gama sallah asuba,kwanciya mom tace tayi ta hutu ita kuma ta fice zuwa part ɗin dady,a zaune ta sameshi kamar yanda ta barshi,ƙarasawa tayi har gaban shi,zama tayi kamar mai ɗaukar karatu, littafin dake hannunshi ya ajiye yana kallonta “lafiya dai ko katte?” ɗan ajiyar zuciya ta sauke tana bashi labarin ganin laatifa da yanayin da su ka ganta
“da alama anan ta kwanta,na tambayeta amma bata bani amsa ba,kasan halin hashim yanzu haka wani abu ya haɗa shi da ita har yayi mata abunda yasa ta bar gidan cikin dare” tunda mom ta fara magana dady ke Binta da ido ƙala baice ba,amma kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar ɓacin da ranshi yayi
“ban san wane irin uba bane ba hashim,kwata kwata bai san role ɗin shi ba a matsayin shi na mahaifi,ya ɗauki karan tsana ya ɗaura ma yarinya saboda Sam,in banda abun shi yaushe rabun Sam ma da ƙasar da zai zauna yana gallaza ma yar sa saboda shi,wallahi har ga Allah bazan iya yafe ma wanda yayi ma Sam wannan ƙazafin ba,sun hana ni zama da ɗana, duk sun ɗauki karan tsana sun ɗaura mashi” ta faɗa kamar zata sa kuka, da alama abun ya daɗe yana damunta
“waye ya ce maki ya tsani Sam?,shifa tamkar ɗan su ne taya za su tsane sa?”
“basa son shi mana,duk kai ka basu ƙwarin gwiwa,da baka wulaƙanta ɗan naka a gaban su ba,ka ƙi tsayawa ka fahimce shi a lokacin da yake buƙatar taimakon ka da duk hakan bata faru,da kaima yanzu haka kana tare da shi,ban san mi yasa kun cika son kanku da yawa ba,ya kamata ku riƙa bincike kafin ku yanke hukunci” nannauyar ajiyar zuciya dady ya sauke “ya isa haka Zulaihart,bana son kina tada abunda ya wuce,komai daya faru kuskure ne,na riga da nayi kuskure,kuma dan kinga Laatifa baki da tabbacin saboda hakan ne yasa ta fito gida” girgiza kai mom tayi
“wallahi ni na san baƙin halin hashim,babu abunda tayi mashi bayan wannan”
“ya isa haka dan Allah,yanzu ina Laatifa take?”
“na barta a ɗaki tana bacci”
“to shikenan,zan kira Hashim ɗin,zanji mike faruwa” taɓe baki mom ɗin tayi ba tare da tace ƙala ba,wayarshi dake ajiye saman sofa ya ɗauka, Number uncle Hashim ya shiga dialing harta katse baiyi picking ba sake kira yayi still bai ɗauka ba.
tashi mom tayi ta fice daga ɗakin,bedroom ɗinta ta koma,with full of surprise mom ke kallon Laatifa dake yafa mayafin abayar dake jikinta,sakin ƙofar tayi ta ƙarasa cikin ɗakin
“lafiya dai ko Laatifa,ina ki ke shirin zuwa haka?” saurin kallon mom tayi sai kuma ta sadda kanta ƙasa,har in da take tsaye mom ɗin ta ƙaraso,hannunta ta kama zuwa bakin bed,zaunar da ita tayi itama ta zauna
“lafiya laatifa,mi ya sa ki ka bar gida cikin dare,ina kuma ki ke shirin zuwa yanzu??” mom ta jera mata tambayoyin tana kafeta da ido cike da son jin amsa daga gareta,duƙar da kai laatifa tayi a hankali tace “mom mun samu saɓani ne da dady”kaf abunda ya faru bata ɓoye ma mom ba,ba ta yi mamakin jin abunda uncle Hashim ɗin yayi mata ba dama ta san zai iya fiye ma da hakan,kamo hannunta tayi cikin nata “amma ai Laatifa da baki fito a wannan lokacin ba ko dan saboda mahaifiyarki”
“mom bana da wani zaɓi ne,bazan iya jurar ganin saɓani a tsakanin su ba saboda ni”
“haka ne amma kinga dare ne,ke macece bai kamata ki fito a wannan lokacin ba” shiru kawai Laatifa tayi ba tare da tace komai,ɗan ajiyar zuciya mom ta sauke “yanzu ina ki ke shirin zuwa dana ga kina yafa mayafi” shiru laatifa tayi tana wasa da gefen mayafinta without answering her “baza ki faɗa man ba” ɗan ɗagowa tayi ta kalli mom ɗin sai kuma ta maida kanta ƙasa“California” ta faɗa a hankali, mom was surprise da magananta “mi za kiyi a can?” mom ta jefa mata tambaya tana tsareta da ido “wajen Sam zan je” wani kallo mom ta jefe mata,tama rasa mi za ta ce mata,ɗan ɗagowa tayi ta saci kallon mom ɗin,kauda kai gefe mom tayi “shi yace maki ki zo,ko kawai ke ki ka yi deciding ki je?”mom ta jefa mata tambaya
“shi yace na zo” ta bata amsa
“kunyi waya da shi kenan?”
“eh tun jiya munyi waya” ɗan ajiyar zuciya mom ta sauke
“Laatifa!” ta kira sunanta in a serious tolk,ɗaga kai tayi ta kalli mom ɗin ba tare da tace komai ba
“laatifa a matsayinki na mace wacce ba muharramarshi ba bai dace ace kije wurin sa ba,ko kin manta shine dalilin wannan matsalar da ki ke samu da dadyn ki??”
“mom dady bazai yafe man ba,kuma zan koma S N J T ne na cigaba da aiki a can”
“a ina zaki zauna kenan?”
“gidan ma'aikata”
“look laatifa maganar zuwanki California wurin sam ma bata ta so ba,ki yi zamanki anan har Allah yasa mahaifinki ya sauko”
“amma mom...” da katar da ita mom tayi
“karki ce komai,kiyi haƙuri dadynku zai yi magana da dadynki, idan ma bai sauka ya yafe maki ba,kiyi zaman ki anan a tare dani har lokacin da Allah kema zai baki miji kiyi Aure,amma maganar zuwa wurin sam ki barta”
“ya riga yayi man booking flight tun jiyan”
“karki damu zanyi magana dashi,ki kwantar da hankalinki kinji”
“to Nagode mom”
“yawwa ki kwantar da hankalinki ni ma momynki ce,zan zauna dake har Aurenki laatifa,nan ma fa gidan mahaifinki ne kuma darajarar ƴa mace gidan mijinta idan ba tayi Aure ba gidan mahaifinta,ki kwantar da hankalinki kinji”
“momy bata san ina nan ba”
“karki damu zan kirata yanzu,bari nasa Ishrat ta kawo maki breakfast” gyaɗa kai tayi a hankali,ficewa mom tayi daga bedroom ɗin,da kallo laatifa ta bita.
komawa tayi ta kwanta,lumshe ido tayi kamar mai bacci.
*Wai waye*
Bayan ta ajiye wayar ta shiga toilet,ta shafe kusan 10 minutes a toilet ba tare da tana wani uzuri ba,tunanin yanda zata samu mafita daga wannan tashin hankalin kawai take,saƙe saƙe take kan yanda zata samu mafitar abun,zuciya bata da ƙashi babu irin tunanin da bai zo mata ba amma data tuna illar dake cikin hakan sai ta ture shi gefe.
ganin ɓatama kanta lokaci kawai take kowace mafita zata zo mata da illa a cikin ta,haƙura tayi ta fito tana share hawayen ta,gaban dressing mirror ɗinta ta nufa,zama tayi saman stool ɗin dake wurin tana kifa kanta saman mirror table ɗin, ringing ɗin wayarta ne yasa ta ɗan ɗagowa,ɗaukar wayar tayi ganin mai kiran nata ne yasa tayi saurin picking call tana ƙara wayar a kunne,cikin muryarta da tayi laushe saboda kukan data sha tayi mashi sallama,cike da kulawa ya amsa “how are u,I hope u are fine” a hankali tace mashi “am fine”
“what are doing in this time da ba kiyi bacci ba?” ya tambaya,shiru tayi ba ta bashi amsa ba “laatifa!” ya kira sunanta a hankali,lokaci ɗaya taji wani kuka ya zo mata wanda ta kasa controling,kawai ta fashe mashi da kuka,ajiyar zuciya ya sauke “dama naji a jikina akwai abunda ke faruwa dake a cikin daren nan that's why I call u, please stop cry and tell me what happens to u kinji” kuka kawai take tama kasa buɗe baki ta sanar dashi abunda ke damunta, ajiyar zuciya ya sauke in a cool voice yace “stop cry please,it's paining me” jin abunda yace ne yasa ta sassauta kukan da take tana sauke ajiyar zuciya
“ke da dadynki ne?” ya jefa mata tambaya,gyaɗa mashi kai tayi kamar tana a gabanshi “ya yi man iyaka da ƙanwata” kaf abunda ya faru ta sanar da shi sai dai bata sanar dashi a game da soyayya Balqis ba.
“i told u in several times Laatifa,that guy u think is your father baya sonki ki bar masa gidan sa but kin ƙi fahimta”
“sam saboda momy nake zaune”
“but hakan ya hana tsanar da yayi maki ne?”
“A'a,amma...” da katar da ita yayi
“wait,give me a tow minutes I will call” ok tace mashi, rejecting kiran yayi,tagumi tayi tana zuba ma wayar ido,bayan kamar five minutes sai ga kiranshi ya shigo wayar, picking tayi ta kai wayar a kunne “nayi maki booking flight At eight o'clock in the morning zai tashi,ki bar masa gidansa,kije wajen mom ki kwana in the morning sai ki tafi airport ɗin,I will send the ticket for u” bata da wani zaɓi bayan tayi nesa da dadyn nata ko hakan zai sa ya yafe mata “ok, thank u Sam”
“u have a special place in my heart,see u California soon,make sure u live that house,take care,bye” yana gama faɗa yayi rejecting kiran,zubama wayar ido tayi kamar zata ganshi,ta gumi ta zuba ba komai take ji ba face momyn ta,tasan ba za ta juri rashinta a kusa da ita ba amma bata da wata mafita bayan tayi nesa da dadyn ta ko hakan zai sama mata salama a rayuwarta da shi kanshi dadyn nata,ta ɗan jima tana a haka kafin ta miƙa ta shiga haɗa duk wani abunta mai mahimmanci,box biyu tayi na kayanta,kafin ta ɗauki passport ɗinta,bayan data kammala haɗa kayanta,ta ɗan jima tana kallon ɗakin kafin ta fice,a parlor ta ci karo da laure kamar yanda lauren ta sanar ma momy,bayan ta yi bankwana ta roƙeta da kar ta sanar da kowa ta fice daga gidan baki ɗaya,a motar ta ta tafi gidan big dady, Estate tsit kamar babu kowa a cikinta sai yan tsirarun securitys dake kai kawo,lokacin data shiga gidan bata haɗu da kowa,da tayi deciding zuwa ɗakin Yumnah amma sai ta fasa kawai tayi zamanta a parlorn tunda zuwa safe zata wuce ko boxs ɗin ta a booth ta barsu.

*Back to story*

“look Sam,wai kai baka san matsalar dake cikin zuwanta nan ba ne?,karka manta har yanzu Uncles ɗinka da wannan tabon su ke kallon ka,kai ko dan saboda hakan baza ka ƙyale masu ƴar su ba”
“mom i don't care about yanda su ke kallona,ni wannan bai shafe Ni ba,saboda babu wani wanda yake da wani mahimmanci a rayuwata, Please ki bar Laatifa ta zo,zata cigaba da aikinta ne a nan”
“wai mi yasa ka kasa understanding abunda nake son ka gane ne,zuwanta zai ƙara masu tabbaci akan zargin da su ke maka,mi yasa ba zaka gane ba ne,Sam bana son abunda zaiyi affecting mutuncinka,kai wai ba ka jin komai ne da ka yi nesa dani??”
“mom ina ji mana,ke ki ka zaɓi mijinki sama dani”
“sam ina son mahaifinku dole na dawo gare shi” ɗan ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin “love birds,soyayyan da bata maki amfani ba”
“wait idan kana da matsala dashi ni bana da matsala dashi,mahaifinku is a kindnesses parson,har yau ka kasa fahimta hakan ka daina wannan fushin mara amfani da shi,ba dan yana so ba yayi maka haka,sai dan ƙin magana da kayi da kowa,kaƙi faɗan gaskiyar abunda ya faru Sam,har yau kaƙi magana da kowa sai fushi ka ke,baka san halin da ka ke jefa mahaifinka akan wannan fushin da ka ke da shi ba,kana son Allah ya yi fushi da kai saboda wannan halin?” dakatawa tayi tana sauraran ma zai ce,ɗan ajiyar zuciya ya sauke ba tare da yace komai ba, girgiza kai kawai mom tayi
“kasan haƙƙin iyaye akan yaran su Sam amma mi yasa ka ke haka,mahaifinka yana matuƙar sonka fiye da sauran ƴan uwanka,har yau ya kasa yafe ma kanshi akan abunda yayi maka,kullum cikin azabtuwa yake da soyayyarka,Sam baka san ya muke ji a zukatan mu ba saboda nesan da kayi da mu,please ka daina wannan fushin kaji,ka dawo gare mu, jin mu muke uncompleted saboda rashin ka”
“shikenan mom,yanzu ya maganan zuwan Laatifa” ya faɗa hakan ne kawai dan ya kauda zancen
“na riga na gama magana,baza ta zo ba” mom ta faɗa rai a ɓace
“ok,zan kwanta bacci sai anjima”
“baka bani amsa tambayata ba”
“mom bacci fa nace maki ina ji,yanzu fa 1:00 Am ne, mom I will call u” yana faɗa yayi rejecting kiran, girgiza kai kawai mom tayi ta san maganar ce kawai baya so.
tashi tayi daga parlorn ta nufi bedroom ɗinta,a kwance ta samu Laatifa bacci ya ɗauketa bayan ta kammala breakfast,wayanta ta ajiye saman Nightstand ta nufi toilet.
Nainarh zaune take saman bed kusa da Yumnah tunda ɗazu take tashinta saboda gyaran part ɗin sam da za suyi kasancewar yau Friday,tashinta take amma ko motsi Yumnah ta ƙi yi
“please Dan Allah ki tashi muje time fa na ƙurewa” ta faɗa tana kallon fuskar yumnah da ko motsi taƙi,ɗan bubbuga kafaɗarta tayi
“na san fa kina jina,dan Allah yumnah ki tashi” ya mutse fuska tayi tana juya mata baya “ki bari sai 10:30 tayi Please” wani kallo Nainarh ta mata ita tunda su ka yi sallah bata koma bacci ba saboda ƙwallafa rai da tayi na zuwa part ɗin amma yumnah na wani ja mata rai.
“wai minene haka ne Yumnah”
“bacci fa nake Nainarh,dan Allah ki ƙyale ni ki tafi wajen dady ki amshi key ɗin mana ni ba yanzu zan zo ba” hararar ta Nainarh tayi,wata dabara ce ta faɗo mata,da sauri ta kai bakinta saitin kunnen yumnah ƙara tayi wacce tasa yumnah tashi a firgice,fashewa da dariya Nainarh tayi,ɓata fuska yumnah tayi “gaskiya baki kyauta man ba,ji fa yanda ki ka tsorata ni”
“ai maganinki kenan sai magana nake kinyi banza dani”
“to ba sai kije wajen dady ki amshi key ɗin ba”
“ai ba ni ke amsa ba” harararta yumnah tayi “Allah sai nayi maganinki akan ya Sam,kin fa soma takura man akan shi”
“oho dai,ni dai yanzu tashi muje” tsaki yumnah taja,ba dan ta so ba ta tashi,hijab ta zura a jikinta,ficewa su kayi zuwa part ɗin dady,sai da yayi ma yumnah faɗa kan sun ja time,dariya Nainarh tayi mata.
lokacin da su ka isa part ɗin a bakin ƙofa su ka samu su Ishrat su kawai su ke jira,buɗe masu part ɗin tayi, Nainarh da su Ishrat kawai su ka shiga amma ita kitchen ta nufa wai zata sha coffee,part ɗin ta dawo bayan ta kammala haɗa coffeen,samun Nainarh tayi ta zage tare da ita ake aikin, murmushi yumnah tayi ta rasa wane irin ji Nainarh ke yima yayan nata.
jawo hannunta tayi “madam irin wannan haƙilo haka,sai anyi magana kice ke ba haka ba”
“yumnah bana son wulaƙanci,kawai aikin nake so ba wai dan wani abu ba”
“oh ni zaki maida bican ko”
“ke wallahi kin cika matsala,ni dai yanzu ki ƙyale ni”
“yanzu dai ajiye aikin soyayyar ga coffee ki sha” yumnah ta faɗa tana miƙa mata mug ɗin coffee dake hannunta, hararar ta Nainarh tayi tana amsar coffeen,zama su ka yi anan parlon su Ishrat kuma na ciki suna aikin.
nainarh jujjuya mug ɗin dake hannunta ta shiga yi ba tare da ta sha ba,kallonta yumnah tayi tana faɗin'
“ya dai mrs Samad, ko coffeen bai maki ba a canzo maki wani?” harara Nainarh ta watsa mata
“wai mi yasa kin cika wasa ne yumnah?” Nainarh ta faɗa babu alamun wasa, ƴar dariya yumnah tayi “kema mi yasa kin cika rainin hankali?” tsaki kawai Nainarh tayi mata
“Nainarh!” yumnah ta kira sunanta, kallon yumnah tayi ba tare da ta amsa kiran ba
“ina so na tambaye ki please yanzu ki faɗa man gaskiya” stuke fuska Nainarh tayi tun kafin taji ma mi yumnah zata faɗa
“maganar hankali ce za muyi naga kin wani ɓata rai, da gaske ne ba son ya Sam ke ki ba kamar yanda ki ka faɗa man ko dai kawai baki son sanar da ni ne??” yumnah ta faɗa tana wani tsareta da ido,mug ɗin da tun ɗazu bata sha ba ta kai bakinta tana kauda ma yumnah fuska,murmushi yumnah tayi tana ajiye mug ɗin dake hannunta saman table, amshe na hannun Nainarh tayi ta ajiye, da mamaki kawai Nainarh ke kallonta.
kamo hannunta tayi cikin nata
“please Nainarh ki faɗa man, ki ka sani ko da akwai wani abu da zan taimaka maki dashi” yar ajiyar zuciya Nainarh ta sauke
“yumnah idan nace maki bana son ya Sam nayi maki ƙarya, amma yumnah ke kanki kin san bazan samu soyayyar shi ba, wahalar da kaina kawai zanyi shiyyasa duk time ɗin da ki ka man magana nake kauda zancen”
“saboda mi ki ka ce baza ki samu soyayyar shi ba?”
“da bakin ki fa ki ka faɗa man shekarun da ya ɗauka rabonshi da ƙasar nan, kuma ni ko waya banga anyi da shi ba, sau ɗaya naji ya Naeem na waya da shi, a haka taya ki ke tunanin zan samu soyayyar shi?”
“ki ka sani ko Allah ya dubi zuciyarki wata rana kawai ya wanko ƙafa ya zo” murmushi kawai Nainarh ta saki tana girgiza kai
“kina ganin wasa ko?”
“babu wasa a cikin lamarin ubangiji, idan hakan ta kasance zanfi kowa farin cikin”
“in sha Allah wata rana zaki tuna wannan maganan dana faɗa maki”
“Allah ya Amince”
“Ameen,yanzu ki tashi muje mu shirya na san zuwa lokacin da zamu gama sun kammala gyaran”
“amma tun yanzu zamu tafi”
“eh akwai family meeting ne, shiyyasa zamu tafi da wuri”
“family meeting!,anya yumnah baza ku tafi ku barni ba,ni kawai prison zanje wajen momy”
“gobe fa mu ka yi dake zamu je,dan Allah karki man gardama ki zo kawai muje” tashi tayi su ka fice ba tare da ta sake cewa komai ba,sai da yumnah ta fara ajiye mugs ɗin da su ka sha coffee tukun.
shiryawa su ka yi, kamar yanda yumnah ta faɗa lokacin da su ka koma su Ishrat har sun kammala gyaran,rufe part ɗin kawai tayi ta maida key ɗin part ɗin dady da har ya fice daga gidan,bedroom ɗin mom su ka nufa, harta kammala nata shirin itama,Laatifa ce kawai ta so gardama ba zata ba amma ganin mom ta dage ne yasa ta shirya,a parlor su ka ci karo da Fa'iza itama ta shirya
“mom Irfan bai shigo ba ne?” fa'iza ta tambaya sanin duk za su tafi tare su ke
End Ads